Showing 9001 words to 12000 words out of 296192 words
mai gidan ya ce ba'a bashi kuɗin ba, nan ma wata matsalar ce, yana gudun haɗa fitina a tsakanin ma'auratan, kuma dama shi kansa mai gidan akwai taƙama, ba ya son takura sam.
Haka Baba Hassan ya din ga tunani, amma ya kasa gano mafita gaba ɗaya.
**************
"Mummy wai Ina Fadila ne? Tun da na shigo ban ganta ba".
Mummy ta ce "zai wuce ace tana bacci ne?".
"Bacci a yanzu Mummy? Ƙarfe sha biyu da rabi fa"
"To ta fito ta yi breakfast, ta koma ɗaki ta kuma kwanciya".
"Amma Mummy kika ƙyaleta, da haka za'a Jami'ar?"
"To yanzu dai tun da ba Jami'ar ta shiga ba, ai ka bar ta ta huta ko? Gwanin na iya, sarkin hantara da zare idanu".
Girgiza kai ya yi ya ce "Idan ta shiga makaranta, wani sakarcin idan ance tayi ba za tayi ba".
"Ai ni shiyasa na so babanku ya kaita ƙasar waje, kamar yadda ake kai kowacce 'yar gata, amma ya ƙi wai rawar kanta ta yi yawa, da shikenan ba ruwanta da tashin hankalin Jami'oin Nigeria"
"Aikuwa tun da haka ba ta samu ba, dole ta koyo sabawa da tashin hankalin Jami'oin Nigeria, kuma ko ina aka kaita ba'a samun ilimi ta sauƙi".
Mummy da ta gaji da tsarin Khalil ta ce "Jeka na ji Babana".
Be kuma cewa Uffan ba ya fice.
Daga gida kuwa kai tsaye gidansu Abdul ya wuce, wanda ɗakinsa ya ke jikin gidansu da banɗakinsa da komai, dan haka Khalil ba sai ya shiga cikin gidansu Abdul ba.
Abdul yana zaune yana marking tes ɗin ɗalibai, Khalil ya yi sallama.
Abdul ya amsa masa tare da cewa "Daga ina haka?".
Khalil ya zauna ya ce "Wallahi da ga gida, ni duk garin ma ji nake ya isheni".
"To sai ka tattara ka koma in da ka fito, dama ni mamaki ma na ke, kawai ka baro aikin ka ka dawo gida ka zauna".
Khalil yayi murmushi ya ce "Har wani aiki ake? Ni Wallahi ginina ne ya dameni, ka san wannan Plan ɗin da muka fitar shi nake yi fa".
Abdul ya ce "Kai, amma fa zai ci kuɗi da yawa".
"Aikuwa yana ci sosai, amma ka san kuɗi ba matsala ta bane".
"Na sani, kana ta gini ba matar Aure, kuma maimakon kayi ginin a nan, amma ka tafi Abuja"
"To ba'a can nake aiki ba, Kano ina da gida, Yaushe za'a ƙarasa naka ginin ne malam Abdul?"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Abubuwa ne sai a hankali, ka san siblings ɗina, ni ke hidimar karatunsu, rayuwar sai Alhamdilillah, ga yaran Yaya Hameed da ya rasu ya bari, nine kamar babansu Yanzu, ni ke kula da su, ka ga ba zan bari su wulaƙanta ba dan ba ransa".
Khalil ya yi murmushi ya ce "Allah sarki, duk faɗan da muke yi da kunna ni da ka ke wasu lokutan, Halayenka abun koyi ne Abdul, Allah ya ƙara maka Arziƙi, Insha Allah da an samu wani space ɗin aiki zamu haɗe a Abuja".
Abdul ya ce "Kai Khalil, wannan aikin ma da na samu ta silarka na ke yi na ji daɗi, bani da bakin godiya, amma ka bar ni kawai, na nemi kasuwanci in haɗa".
"Wallahi ba ka isa ba, dole mu tafi tare, kuma filin jikin in da nake gini a Abuja, ka kawo half ɗin kuɗin, in cika maka kawai ya zama naka".
Abdul yayi dariya ya ce "Ba zaka ƙare a kai na ba, amma Allah yasa ginin da na ke a Kano ya burge Fadila, wai ni kana ma miƙa mata saƙon gaisuwata kuwa?"
Jikin Khalil ne yayi sanyi amma ya dake ya ce "Malam kawai ka rabu da wannan yarinyar".
"Saboda me? Ko dai ba zaka bani ita bane, saboda ni talaka ne?"
"Kai haba dai, wace irin magana ce wannan, ni ba ruwana ka nemi soyayyarta kawai, zan wuce maka gaba gurin Daddy, yanzu dai ka tashi muje yawo".
"Yawo kuma? Kai zaka mini aikin marking ɗin?".
"Kai dalla ka dena takurawa kan ka malam, zo muje Chilling kawai".
"Gaskiya ka hanzarta ka zo ka koma in da ka fito, duk ka addabeni tun lokacin da ka dawo".
"Wallahi sai ka taso"
Abdul ya ce "To Jarababbe ai ka bari in tashi in kintsa ko a haka zan fita?".
"To kintsa mu fita".
Khalil yana jin daɗin abotarsa da Abdul, iyayen Abdul talakawa ne, ƙoƙarin sa da kuma rahamar ubangiji ya sanya ya samu Scholarship, na karatu a Malesia, wanda a nan suka haɗu da Khalil, Mahaifiyar Khalil ba ta son mu'amalarsu Saboda shi ba ɗan masu kuɗi bane, amma Khalil ya nacewa Abdul.
Abdul ya fuskanci Mahaifiyar Khalil ba ta son sa, dan haka ba ya son zuwa gidan sam, Khalil yana da izza irin ta yaran masu kuɗi, saboda ko ba komai ɗabi'a naso take, amma bai san yana yi ba, kuma sam baya nunawa Abdul Izzar.
Babban abun da yasa yake son Abdul shine, mutum ne mai wadatar zuci, ga girmama mutane, dan idan mahaifin Khalil yana gari, wataran ya kan sai abun da yake da shi, yaje ya gaisheshi, hakan yasa shi kansa mahaifin Khalil yake son Abdul.
Ganin ba yadda Hajiya Zainab ta iya ne, ya sa ta ƙyalesu suke abota, hatta motar da Abdul yake hawa, Khalil ne ya bashi.
Mahaifin Khalil shine ya samarwa da Abdul aikin lecturing, ya yin da nasa ɗan ke can Hukumar Land a Abuja.
Abdul ya daɗe yana son Fadila, amma ya kasa gaya mata, saboda yanayin yadda ta ke gudanar da al'amuranta. Hakan ya sanya ya gayawa Khalil yana son ƙanwarsa, Khalil ya ji daɗi, amma ya san ba abune mai yiwuwa ba, saboda yadda ahalin su ke ƙyamar talaka!.
**************
Yau ta kasance ita ce ranar Fadila ta farko a Makarantar Jami'a, sai da aka sha yaƙi da ita, sannan ta tashi ta shirya da safe, tamkar wata ƙanƙanuwar yarinya.
Mummy sai mita take tana in dai haka Fadila zata cigaba, Wannan karatun ba mai yiwuwa bane ba sam.
Da kanta tayi driving motarta zuwa School, sai dai ta dinga bin 'yan ajin nasu da wani irin kallo mai kama da na ƙasƙanci.
Guri ɗaya ta ware, can gefe guda ta yi zamanta, ba tare da ta shiga sabgar kowa ba, sai hura hanci kawai da take yi.
Malamar farko da ta shigo fara yi musu lectures, ta yi musu nasiha sosai a kan mahimmanci mai da hankali a kan karatu, da irin yanayin yadda rayuwar Jami'a ta bambanta da ta sakandare.
Ba laifi malamar ta sha gayu tsaf da ita.
Ajin ya haɗa da waɗanda suna kammala Sakandire suka samu gurbin karatu, da waɗanda suka shafe lokaci a gida ba a samu gurbin karatu ba, a taƙaice dai ajin ya haɗa yara, matasa da kuma dattawa.
Ƙarfe sha biyu, Fadila ta ɗau jakarta ta koma gida, ba dan an gama lectures ɗin ba, sai dan yadda gaba ɗaya zaman makarantar ya ishe ta, ga warin hammata da wasu daga cikin samarin ajin suke yi, duk da wadattaciyar iska da fankoki da suke ajin, amma bai hana wasu idan suka gifta taji ba, wanda hakan ya sa ta fara jin tashin zuciya ta ce ba zata iya zama ba.
***********
Kamar kullum bayan sallar magariba sannan kayan sana'ar Hafsa suka ƙare, ta tattara kayanta ta nufo gida, sai dai tun daga yadda ta ji Mama ta amsa mata sallama ta san jikin Maman babu daɗi.
Cikin azama Hafsa ta shiga ɗakin tana faɗin "Mama ya naji muryarki haka? Jikin ne?".
Mama dake kwance ta tashi zaune da ƙyar ta ce "A'a lafiyata ƙalau Hafsa har kin dawo" ta yi maganar tana haki.
"Mama gashi kina haki, amma kice mini lafiyarki ƙalau? Bari in ɗauko miki maganinki"
Hafsa ta tashi da sauri ta nufi in da take ajiyewa Mama magungunanta, Mama kuwa bin Hafsa tayi da ido, cike da tausayawa.
Hafasa na duba gurin magungunan babu sai fankon ledar maganin, ta kalli Mama jiki a sanyaye ta ce "Mama dama maganin ya ƙare baki gaya mini ba?"
"Bana son tayar miki da hankali ne, kuma dama kin ce jari yayi ƙasa, bashi yayi yawa, kinga dole a lallaɓa kar mu cinye jarin gaba ɗaya".
"Haba Mama, ai lafiya gaba take da komai, kuɗi kona waye ai gara in taɓa in sai miki magani, bari im je gurin Magaji, idan yana nan ya zo ya duba jinin naki, sai in taho miki da maganin".
"To Hafsa, kar ki daɗe amma, kiyi maza ki dawo ga wani Abinci can na ajiye miki"
Hafsa ta ce "To mama, daga nan ta fice".
Kai tsaye chemist ɗin Magaji ta tafi, ta tarar ba kowa a shagon sai shi da wani abokinsa, wanda duk unguwarsu ɗaya.
Tayi musu sallama suka amsa mata, ta kalli Magaji ta ce 'Magaji dan Allah so nake a duba mini awon jinin Mama, idan ya hau ne sai a bata maganinta, na dawo na tarar tana haki".
Magaji ya ce "Gaskiya ina da abun yi yanzu".
"Don Allah ka taimaka, bata da lafiya sosai" tayi maganar cikin damuwa.
Magaji ya ce "Ashe alfarma tana da daɗi Hafsa? Ai da har gida nake zuwa ina yiwa mahaifiyarki gwajin, amma na nuna ina sonki, ba kunya kika nuna ba kya sona, kuma saboda kina da kunya shine kika kuma dawowa neman alfarma a gurina".
"Ita Alfarma ana nemanta ne a in da ya dace, ana alfarma akan komai amma banda So, ban taɓa keta bulle na na nemi Alfarmar wani ba, saboda gudun ƙasƙanci sai a gurinka, kuma ka nuna mini iyakata, daga yau ka rubuta ka ajiye, idan ni Hafsa na kuma neman Alfarma a gurinka, kai mini duk cin mutuncin da ka ga dama" tana gama faɗin haka ta juya ta bar Chemist ɗin.
Tana tafiya Magaji ya ce "Aikin banza, yarinya ba 'yar uban kowa ba, sai izza da girman kai, tana 'yar talaka futuk, tana suyar awara akan kwalbati, amma zan nuna ina sonta ta wulaƙantani".
Abokin Magaji mai suna Nura ya ce "Nikam burgeni take, ba ruwanta da shirme da rawar kan 'yan matan unguwar nan, a nutse take".
"Kai dalla ware, ba wata nutsuwa, duk buge ce, ni ban ma san tsautsayin da ya kaini cewa ina sonta ba, bayan ma 'yar mace ce, har wata nutsuwa ko tarbiyya ce da 'yar mace?".
Nura ya ce "A'a Magaji, da ta yarda da soyayyarka, ba zaka kirata 'yar mace ba".
Haka Magaji ya cigaba da sukan Hafsa, Nura yana karewa.
Hafsa kuwa ganin kuɗin hannunta ba su da yawa, ta san ba zasu isa ta kai Mama Asibiti ba, haka ta haƙura taje wani Chemist ɗin ta sai mata irin maganinta, duk da akwai buƙatar a sake gwada jinin amma babu yadda ta iya.
Khalil ne ya shigo ya tarar da Fadila tana gayawa Mummy yadda 'yan ajinsu suke, da yadda wasu suke addabar su da warin hammata.
Khalil ya ce "Zaki ga warin hammata, kije ki yi musu hauka suyi miki dukan tsiya, dan ba kowa zai ɗau rashin kunya ba".
"Aikuwa da na saka an kulle mini yaro kowaye ubansa a garin nan" Mummy tayi Maganar tana zazzare ido.
Khalil ya girgiza kai ya ce 'To ni dai jibi in Allah ya kai mu zan koma gurin aiki".
Mummy ta ce "Allah ya kiyaye hanya, dama ka takurawa 'ya ta, gashi kuma next week babanku zai shigo gari".
Khalil ya ce "Allah bai yi zamu haɗu ba, ma yi waya da shi".
**************
Gaba ɗaya yau Amina ta wuni jikinta babu daɗi, wanda tsabar damuwa da kuka ya haifar mata da ciwon kai, yau 'yan ajinsu suke zana paper ƙarshe babu ita, haka ta sha kukanta ta godewa Allah.
Inno ta tursasa mata cin abincin dare, dan wuni tayi ba ta ci komai ba, sai kwanciya.
Tana tsaka da cin tuwon ne, ɗan gidan Baffa Lawan yayi sallama ya ce "Amina kije Malam Rabi'u yana sallama da ke a waje".
Amina ta ce "Ka je kace masa bana nan". Yaron ya juya ya fice.
Inno ta ce "Wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko?".
"Inno to ni ya ake so in yi? Ni Wallahi ba zan iya Auren wannan mutumin ba".
Suna cikin Magana Baffa Lawan ya shigo yana hayagaga yana ɗaga murya.
"Wato wuyanki ya yi kaurin da za'a ce ana sallama da ke ki ce aje ace ba kya nan? Zaki tashi ki je ko sai na kakkarya ki, sakarya yarinya mara Albarka".
Amina na kuka ta tashi ta Sanya hijjabinta, Baffa Lawan ya cigaba da sababi yana cewa Inno ce ke goya mata baya take rashin mutunci.
"Kuma ki san da saninki, na saka gonar babanki a kasuwa, an samu mai saye gobe za muje mu karɓo kuɗin, ai miki kayan ɗaki ds su, Hassan ko yana nan ko ba ya nan, zamu aurar da ke"
Ƙara fashewa da kuka Amina ta yi, ta nufi hanyar fita tana goge hawaye.
Malam Rabi'u yana tsaye a ƙofar gida, yana ganin Amina ta fito ya fara murmushi, duk da babu wadataccen haske a gurin, amma hakan be hanashi ƙare mata kallo ba.
"Amaryata barka da wannan lokaci, ya Mutanen gidan?".
"Yanzu tsakani da Allah ka yi mini adalci kenan? Dan me zaka takura sai ka Aureni? Nace maka ba zan iya aurenka ba, ana dole ne?".
Malam Rabi'u ya ce "Ai ko ba kya so na ni ina sonki, kuma wan mahaifinki ya ce ya bani ke, kuɗin Aure kawai zan kawo wani satin, kuma ba za'a sanya lokaci mai tsawo ba".
Wani haushi ne ya sake kama Amina, ba ta kuma ce masa uffan ba, ta juya ta koma cikin gida tana wani tunani a ranta.
***************
Ku san sati biyu da fara lectures, amma kullum sabbin ɗalibai zuwa suke yi, sai dai haryanzu Fadila ta kasa sakewa da 'yan ajin, sai wasu 'yan mata su biyu, suma dan ta ga irinta ne 'yan ƙarya yaran masu kuɗi, suma ba wani sakewa take da su sosai ba.
Ana tsaka da lectures, sai ga wani matashin saurayi ya shigo, dogo ne sosai wankan tarwaɗa, yana sanye da wani yadi ash, amma yadin nan yayi haske saboda tsufa, amma ya sha guga, kansa ya sanya hula tashi ka fiye naci, sai ɗan ƙaramin asuwakinsa a bayansa, hannunsa ya naɗa shi da wani ɗan ƙaramin carbi.
Sallama ya yi, wanda ya sanya gaba ɗaya hankalin 'yan ajin dawowa kansa, saboda yadda yayi Maganar Kamar cikin iyayi.
Aka amsa masa, lecturer ya ce "Kai Ustaz da ga ina?".
"Daga gida Malam" ya faɗa cikin girmamawa.
"Gida dama yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji?".
"A'a malam ayi mini afuwa dan Allah, Insha Allah ba zan sake ba"
Lecturer ya bashi iznin ya je ya zauna.
Ƙafarsa Fadila ta kalla, ya sanya takalmi soso irin na maza, takalmin duk ya cinye, ga ƙafarsa tayi futu-futu tamkar an haƙo shi daga rami.
Aikuwa Fadila ta tuntsire da dariya, gaba ɗaya aka juyo ana kallonta, shima waigowa yayi ya kalleta, ya ga ƙafarsa take kallo tana cigaba da dariya, ganin abun da take wa dariya, ya Sanya wasu daga cikin ɗaliban suma yin dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya sai wata kunya ta kama shi, sai ya ji babu daɗi sam akan abi nda Fadila ta yi masa.
Lecturer da ya juyo ya ga Fadila ce tayi wannan dariya, bai tsaya jin me take yiwa dariya ba ya ce ta fita ta bar ajin.
Domin gyara sharhi ko shawara
08081012143
Kar a manta ayi following account ɗina na Arewabooks
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P4
Arewabooks
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
Watpad Ayshercool 7724
Ko a jikinta, Fadila ta ɗauki jakarta, ta fice daga ajin.
Shi kam wannan bafulatanin ustazu, ya nemi guri ya zauna, yana ɓoye ƙafarsa, dan ba ƙaramin kunya ce ta kama shi ba, a saboda dizgin da Fadila tayi masa.
Fadila kuwa gida tayi tafiyarta abin ta, hankali kwance dan tama manta da abin da ta aikata, kuma ba ta damu da korarta da malami ya yi daga aji ba, dan ita gani tayi ma ya taimaketa.
************
A 'yan kwankin nan da dangin mahaifi, suka sako Amina a gaba, duk ta rame ta yi zuru zuru, ga rashin samun damar zana jarrabawa, gashi Kawu Bala ya hanata zuwa ko ina shi da Kawu Lawan idan ba aike ba, ciki har da makarantar allo, kuma dan wani tsabar wulaƙancin, daga can cikin gidan ma, gurin iyalansu, sai a aiko taje a aiketa, ko a sata wani aiki mai wahala, duk dan a cuzguna mata a ɓata mata rai, abin duniya ya haɗu yayi mata yawa, gashi ba ta da waya balle ta kira Baba ta sanar da shi halin da take ciki, gashi su kawu sun matsa a kan lallai ko yana nan ko ba ya nan, sai sun siyar da gonarsa sun mata Aure.
Abin da yake ƙara mata damuwa shi ne, bayan aikin gadin nan, da ɗan gurin da suke zaune a cikin gidan nan, to da Allah suka dogara da Wannan gona kuma guda ɗaya tal, siyar da ita na nufin tozarta Mahaifin Amina ne.
"Amina, wai ke sai kin ɗorawa kan ki wata rashin lafiyar saboda wannan tunanin da kike, sannan hankalinki zai kwanta?"
Cikin damuwa Amina ta ce "Ba haka bane Inno? Tunanin ne yake zuwa ko ban shirya ba".
"Yo dama wani tunani ne zai tsaya jiran sai kin shirya? Na san ba zai wuce tunanin boko ba".
Amina ta girgiza kai ta ce "Inno ni na haƙura da karatun boko ma, ni yanzu auren nan nake tunani bana son Auren nan sam, sai kuma gonar Baba da zasu sayar, dan Allah Inno ki saka baki, su ƙyale mana gonarmu"
Buɗe baki Inno ta yi ta ce "Ni kaza! Rufamini asiri, kin san ko mahaifinki ba ya jayayya da maganar kawu Bala, balle ni 'yar karo da aka auro".
"To ko ni inje in same shi, in masa maganar?, bamu fa da Komai sai gonar nan, kuma ni wallahi ba zan yadda ayi mini wannan auren ba".
"Ke ki rufawa kanki asiri, kin ga Amina kiyi haƙuri ki runugumi Auren nan, tun kafin su yi miki wani sharrin, kin san kawu Bala da kaidi kamar mace"
"Aikuwa a aurawa wata ba dai ni ba, dan Wallahi da raina da lafiyata ba zan auri Wannan mutumin ba, mara imani wanda bai san darajar Aure ba, mata nawa ya mayar zaurawa, ya auri mace ya saketa ita da 'ya'yanta banda 'ya'yan da ke gidansa, duk kaka sai ya saki mata ya auri wasu haka kurum a kashe mini rayuwa".
"Rigimar ki tayi yawa Amina, ke ba a gaya miki gaskiya ki bi, amma ki rubutawa babanki wasiƙa a kai tasha, gara ya zo garin nan a san abun yi, ya san halin da ake ciki".
Amina ta yi murmushi ta ce "Ashe dai bokona na da muhimmanci Inno, amma