Showing 288001 words to 291000 words out of 296192 words
Yayi Maganar yana kallon Hafsa.
Ta ce "A'a duk kanwar ja ce, ɗan larabcin nawa na ƙawa'idi ne kawai"
Dariya suke yi sosai, kawai suka ga Mummy tare da Hajiya Turai a tsakiyar falon.
Sai da Hafsa ta zabura da ganin Mummy, haka Fadila ma.
Idonta ne ya sauka a kan Fadila dake jingine da jikin Yazid.
Ayshercool
08181012143https://youtube.com/@CoolhausaNovels
Subscribe my YouTube channel, to get the latest hausa Novels.
86
Sarai ta gane Yazid, amma sai kanta ya kulle ta ce "Fadila, waye wannan?"
Cikin girmamawa Yazid ya risuna yana cewa "Mummy ina wuni"
Bata amsa masa ba sai cigaba da tambaya da tayi.
Khalil ya aro jarumta ya ce "Mummy, dan Allah ki kwantar da hankalinki, bari na yi miki bayani, ba wani abin tayar da hankali bane ba, amma ki fara zama ki ga jikan naki"
"Kai dalla rufe mini baki, sai zuba kake kamar jefaffe, tambayarku nake waye shi?"
"Mummy mijina ne, Yazid kenan shi Daddy ya aura mini" Fadila ta bata amsa.
Hajiya Zainab ta riƙe ƙugu ta ce "Turƙashi, dama a kan wannan ɗin kika watsa mini ƙasa a ido? Wannan abun shi ne mijin naki? Lallai Ahmad ya shirya tozartani"
Hajiya Turai ta ce "Taɓ, da wannan ba gara Salim ɗan gidan Hajiya Salma ba, yaro da kuɗinsa da mutuncinsa, dan Allah kalli meye abin son a wannan? Kalli rigar wuyansa ba dan a wanke take ba ai baifi ka yi duster da ita ba, to ban ƙi ba ko wannan hasken da gemun take yiwa amma wannan dai ba sa'an aurenki bane ba Fadila, har da miƙewa ki ƙunshi ciki"
Rai a ɓace Fadila ta ce "Ba ruwanki da mijina kar ki sake zagar mini shi, ni ina son sa a haka" tayi maganar cikin tsiwa.
Buɗe baki Hajiha Turai ta yi ta ce "Fadila ni kike gayawa haka?"
Fadila ta buɗe baki za ta yi magana Hajiya Zainab ta ce "Idan kika kuskura kika kuma faɗar wata Magana ta rashin kumya sai na ɓarar da ke, wawuya mara wayo me wanan ya ci balle ya baki, kalleshi a gajiye" Khalil ya rasa bakin magana, saboda gaba ɗaya sun riga sun gama cin mutuncin Yazid.
Amina da ke gefe da uban cikinta ta ce "Wallahi idan ki ka cigaba da biyewa ƙawaye, sai sun saka yaranki sun tsaneki, Mutanen nan hassada kawai suke yi miki. Banda abin kunya sirikinki ne fa ya zaki tsaya kina gaya masa wannan maganganun ba kya tunanin nan gaba a zo aji kunya"
"Ke kuma wa ya kasa dake 'yar hau, 'yar bani na iya ai duk wani munafunci ke kike kitsa shi, kin tsallake tsiya da talauci kin zo kin aure mata miji kina zuba mulki kin kassara mata gida".
Amina ta ce "Au har da su kaza a cin danƙo, ke kuma a wa kare da gudun layya? Ai mace sai ta kai take iya shimfiɗa mulki a gidan mijinta, faɗi ki ƙara ni na saka aka yi wannan aure, kuma Allahn da ya haɗa shi ka raba shi, idan kuma ba aje makaranta ba sai a cigaba da jayayya da ikon Allah".
"Zaki rufe mini baki ko saina ɓarar da ke banza" Hajiya Zainab tayi maganar kamar zata kaiwa Amina duka.
"To ɓarar da ni mana, tijarar mai gidan ma ta isheki, kece duk abin da ki ka yi abin kunya ne a gareki, duk sirikanki ne a nan da nake alfahari da su, kuma Alhaji Ahmad yake alfahari da su, amma lokaci yayi da zaki gane cewa wannan ƙawayen naki cutar ki kawai suke yi".
Hajiya Turai ta ce"Kinga bar wannan mahaukaciyar, ki kamo wannan mara wayon mu tafi gida"
Khalil sai basu haƙuri yake yi, amma Hajiya Turai na ta zigata tana sake zubar da mutuncinta a gaban sirikai.
Ta kalli Fadila ta ce "Zaki taso mu bar gidan nan ko kuwa?"
Fadila ta riƙe hannun Yazid ta ce "Dan Allah Mummy ki ƙyalemu, ina son sa wallahi"
"Ni ki ke gayawa kina sonsa, talakan Fadila? babu shakka ubanki ya jiƙa wata tsiyar ya baki kin sha, zaki taso ko saina zo? Aini gara da Allah ya sa na zo ɗin na bi shawarar ki Turai"
Kuka Fadila ta fashe da shi ta ce 'Mummy ba juya miki baya zan yi ba, amma a halin da nake ciki ba zaki iya kulawa da ni ba, dan Allah Mummy ki yi haƙuri maraya ne ina son mijina"
Khalil ya ce "Dan Allah Mummy ki yi haƙuri ki ƙylesu, kalli yadda take kuka kuma wallahi Yazid mutumin kirki ne"
Mummy ta ce "Ka auri 'yar gidan babu shi ne kake so itama sai ta haɗa zuriya da talaka ko?"
Mama da tun ɗazu take jin abin d ake faruwa ba ta ce komai ba, Fadila ta bata tausayi da Yazid, yadda Fadila ke ta kuka tana rirriƙe Yazid, shi kuma yayi shiru ga cin mutuncinsa da aka yi.
Mama ta ce "Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, shi ɗan yau ba ayi masa haka, ka samu mai riƙe maka ɗan ma wani ni'imar ne, dan Allah ki daina wannan maganganun a gaban sirikanki".
Hajiya Turai ta yi farat ta ce "Ke kuma waya kasa da ke, ita kuma wacece wannan?"
Khalil ya nuna Hajiya Turai ya ce "Sirikata ce, kuma ki kiyayi harshenki kar ki sake ki zageta uwace a wurina"
"Khalil Turan kake gaya wa haka?" Yazid ne ya ɗago da sauri, yana nanata sunan Turai.
Khalil ya ce "Mummy wallahi gaskiya Anty Amina take gaya miki, mutanen nan ba ƙaunarki suke yi ba, hassada suke yi miki"
"Ni kake kalli kake gaya wa haka Khalil?".
Amina ta gyaɗa kai ta ce "Hmm a dai juri zuwa rafi, wannan yaran da kike taƙama da su, sai wannan matan sun saka sun tsaneki"
Yazid ya miƙe tsaye jiki a sanyaye, zai bar falon.
Mummy ta ce "Kai tsaya, ka bani takardar sakin 'ya ta, dan ba zata cigaba da rayuwa da kai ba".
Khalil ya ce "A'a Mummy, dan Allah kiyi haƙuri kar ki yi haka"
Fadila kuwa ta rirriƙe hannun Yazid ta ce "A'a dan Allah Zid kar ka sakeni, ina sonka dan Allah Mummy ni ki ƙyaleni zan iya zama da shi".
"Ni kike gayawa haka Fadila? Kin zaɓi wannan matsiyacin a kaina".
"Mummy ba haka ne ba, muna son juna tun a makaranta, dan Allah ki ƙyalemu wallahi ina son sa"
"Fadila ni zaki watsawa ƙasa a ido ko? To muddin kika zaɓe shi babu ni babu ke".
Gwanin ban tausayi Fadila ta ce "Wallahi Mummy ina sonki, amma ina son mijina ma, Zid dan Allah ka gaya mata ina sonka dan Allah kayi haƙuri kar ka sakeni".
Turai ta ce "Wallahi sai ya sake ki, shashasha mara tunani, kai da ganin wannan ka ga wahalalle" ta yi maganar tare da fizge hannun Fadila daga na Yazid.
Yazid da yake ta sunkuyar da kai, ransa ba daɗi ya ɗago idonsa, ya kalli Hajiya Turai ko ƙiftawa ba ya yi.
Take ta ji jikinta ya hau tsuma, kamar zata fita daga hayyacinta ta kasa gane a wane yanayi take.
Ya miƙawa Fadila hannu, ta fizge hannunta daga na Turai ta riƙe na Yazid.
Yazid ya kalli Hajiya Turai ya ce "Baki da hurumin da zaki cigaba da zagina, idan ita Mummy ta yi ta isa ne, sannan ina son sanar da ke cewa saƙonku ke da Hajiya Salma yana isowa gareni, kuma reshe na daf da juyewa kan mujiya, abin da kike ji ɗin nan a yanzu ka iya kawo ƙarshen abin da kuke aikatawa daga ke har ita, zaɓi ya rage naku ko ku janye ku nemi afuwar wadda kuke cutarwa, ko kuma ƙarshen abun yayi muni. Sannan Ina son Fadila bani na nemi aurenta ba, Daddy ne ya aureta ya kuma bani amanarta. Idan har ya dawo ya ce na bashi amanrsa zan dawo masa da ita, amma for now dan Allah kiyi haƙuri Mummy"
Ya juya zai fice, Fadila ta ƙara riƙe hannunsa gam, suka yi waje, har da ɗan gudunta.
Amina da ke gefe ta ce "An dai ji kunya wallahi, su Balama an yi asarar kunnuwa, baku da aiki sai sintirin gidan Mutane kuna zigata a kan abin da ku ba haka kuke aikatawa a naku gidajen ba, ta ƙarasa maganar tana tashi tsaye da ƙyar.
Hajiya Turai kuwa jikinta sai rawa yake yi, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, ji take yi tamkar zata haukace ko ta bar duniyar.
Da ƙyar Amina take takawa ta bar falon, ta fice daga gidan gaba ɗaya, ta je ta samu abin hawa ta hau dan ta koma gida, ba zata iya jiran Daddy ba, saboda abin Kunyar da Hajiya Zainab ta aikata yayi yawa, abin da Kunya.
Hajiya Zainab kuwa a saɓule ta bar gidan, ba tare da ta iya cewa komai ba, ko a mafarki ba ta yi zaton Fadila zata aikata abin da ta yi mata ba a yanzu, ta kunyata a gaban Mutane.
Daddy cikin mamaki yake tambayar Amina dan me zata hau napep a wannan halin da take ciki, tafiya da ƙyar.
A ɗan hasale Amina ta ce "Ba dole na dawo ba, matarka ta je tana abin kunya a gaban sirikai da mutanen gida, wallahi Zainaba ba zata taɓa hankali ba, zuwa ta yi gidan Khalil ta tarar da Fadila da mijinta, ka ga cin mutuncin da suka yiwa Yazid ita da ƙawarta Turai take ko Afrika? Suka ci mutuncin bawan Allah nan suna ce masa matsiyaci, cin mutuncin bai tsaya a kansu ba har da mahaifiyar mai jego, wace irin rayuwa ce haka?"
Daddy yana matuƙar jin Yazid a ransa, yana ganinsa tamkar ɗansa, nan da nan ransa ya ɓaci, hankalinsa ya tashi ya fice fuuuuu.
Amina ta taka ta bi bayansa tana kiran sunansa.
A falo ya tarar da Hajiya Zainab tana zaune rai a ɓace, Hajiya Turai na yi mata magana.
"Uban wa kika tambaya kika je gidan Khalil, har kika ciwa mijin 'yar ki mutunci?".
Hajiya Zainab ta kalli Amina da ke bayan Alhaji Ahmad a tsaye ta ce "To jikar munafukai, har kin zo kin sanar masa kenan, to na je ɗin kuma na yi ɗin, kuma wallahi Fadila ba zata cigaba da zama da wannan matsiyacin ba".
"Kafin ta kaimu ga haka, Zainab na sake ki, saki ɗaya ki bar mini gida, tun da ni nake aureki ba ke kike aurena ba"
Ba Hajiya Zainab ba hatta Turai sai da ta yi turus, basu taɓa kawo Alhaji Ahmad zai aikata haka ba.
Hajiya Zainab ta ce "Ai na ci dubu sai ceto Ahmad, yau ka tabattar mini da cewa ka riƙa, dan haka na ji na gode amma wallahi ba zan bar gidan nan ba, sai dai kai ka fita".
Daddy zai yi Magana Amina ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kai ta ce "Dan girman Allah kar ka sake magana, sheɗan ne yake sake zigaka kr ka kuma furta komai, yi haƙuri" Amina tayi gaskiya, dan a yadda ya ke ji zai iya cikasa mata saki biyun. A matuƙar fusace Daddy ya bar falon, Amina ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ai dama ƙarshen alewa ƙasa, dama auren na ki suke yiwa baƙin ciki, kinga biyu babu ba miji ba 'ya'ya duk sun zama nawa, yanzu dai kin ga abin da 'yar ƙauye Jahila 'yar talakawa ka iya yi ai dama ita GABA DA GABNTA, kuma Allah ba yadda bai iya ba, abin da kike gudu gashi nan ya baibaye ki. Yanzu ya rage naki, ko dai ki nutsu ki koma ga Allah ko kuma yanzu ki ka fara gani".
Hajiya Turai ta ce "Dalla saurara waye ya saka da ke, kin kashe mata aure kin ji daɗi, ki bi bokaye kin mallake miji kin saka ya saketa"
Amina ta yi murmushi ta ce "Ai tun kan na fara bin boka take yi, kin san shi ma asirin iyawa ne, wani ya daɗe yana yi amma bai ci ba"
Hajiya Zainab da ta yi shiru, zuciyarta na bugawa cike da fargaba.
Yazid kuwa har suka je gida Fadila tana kuka, Yazid kuwa ya kasa magana, saboda zuciyarsa babu daɗi sam.
Ko da suka je gidan ma, Yazid bai ce wa Fadila komai ba, hakan ya ƙara jefa Fadila a damuwa, dan sosai ta ga damuwa a fuskar Yazid.
Jiki a sanyaye ta dafa shi ta ce "Zid, dan Allah ka yi haƙuri da abin da ya faru, haka Mummy take a baya na biye mata, yanzu kuma na gane kuskurenmu, amma dan Allah ka yi haƙuri ita ma zata gane".
Yazid ya ce "Kar ki damu Fadila, ni ba yau na saba gamuwa da irin wannan ƙalubalen ba, duk abin da za ayi mini barin abin da aka yi mini ne a gidanmu, ni wannan Hajiya Turai ɗin ce ta tsaye minin a rai".
Fadila ta ce "Yauwa a ina ka san su ne?"
Yazid ya numfasa ya ce "Kar ki damu da wannan, amma da gaske sune ƙawayen Mummy?"
Fadila ta ce "Eh, ƙawayenta ne, nima tashi na yi na gansu tare"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Da ta san illarsu a gareta da cutarwar da suke yi mata, data rabu da su tuntuni amma shi ramin ƙarya ai ƙurarrene, kamar yadda Amina ta faɗa, Hassada suke yi mata".
Fadila ta Kwantar da kanta a jikin Yazid ta ce "Nima da ta faɗi hakan na yi wannan tunanin, ita fa Hajiya Salman nan ita ce da aka ce da zan auri ɗanta, aka fasa na ce bana so Daddy ya Aura mini kai, su yi ta saka Mummy tana basu kuɗi, kuma ta na yiwa Daddy rashin kunya".
Yazid ya dakatar da Fadila, ya sauya zancen da wani.
Ita Hajiya Zainab sai abun ya zame mata goma da ashirin, dan wani irin matsanancin ciwon baya da na ciki take fama da shi, amma ta kasa mayar da hankali a kan ciwonta sai a kan yadda zata fanshe tozarcin da Alhaji Ahmad yayi mata.
Ranar suna aka sha shagalin sunan jairiryar su Khalil, aka saka mata sunan mahaifiyar Hafsat.
'yan Dutse suma sun je suna sosai, an ci an sha an yi buduri sosai, kuma Hafsa sun samu abin arziƙi sosai kama daga kuɗi zuwa ga sutura.
Hajiya Zainab ta girgiza da abin da Daddy ya aikata mata na sakin nan, ta rasa in da zata saka kanta, Hajiya Salma sai zigata take tan cewa ai ba kanki farau ba, kar ki damu amma zai gane kuskurensa.
Amina kuwa bin Daddy take tana roƙonsa a kan ya taimaka ya mayar da Mummy amma yayi burus. Sai da ƙyar dan sai da tayi fushi ta daina kula shi, sannan ya mayar da Hajiya Zainab.
Yazid ya dage iya ƙoƙarinsa, ya buɗe inshoran lafiya, saboda haihuwar Fadila, da ya samu 'yan kuɗi, sai ya ɗauketa su je su ɗan sayo kayan jarirai.
Fadila kwana Biyar da shigar cikinta watanni tara, ta ji cikinta na ciwo kaɗan kaɗa , ta yi wanka ta shirya ta ce wa Yazid "Zid ina ga fa haihuwa zan yi, ta shi muje Asibiti na haihu"
Yazid ya kalleta ya ce "A haka zaki haihun?"
"Ni dai ka tashi, kar na haihu a wurin nan, a Asibiti ance da mun ji ciwo muje Asibiti"
Yazid ya tashi ya ɗau akwatin da suka haɗa na kayan jarirai, Fadila ta ce suje su kira Hajiya, amma ya ce "A'a su je tukuna su ji me za ace a Asibitin".
Haka suka tafi Fadila na ta zuba hira a napep, suka je Asibiti Fadila ta faɗi abin da yake damunta.
Nurse ɗin ta kalli Fadila ta ce "Lallai kam"
Da za su je A dubata har da kallon Yazid ta ce "Kar fa ka yi nisa, yanzun nan zan haihu na fito" shi dai Yazid duk da bai san yadda ake haihuwa ba, amma ana faɗar da wahala amma Fadila dumur da ita tana cewa haihuwa za ta yi.
Aka shiga labor room aka ce ta hau gadon ta kwanta a dubata, ta hau ta kwanta da uban dogon wandonta a jikinta.
Nurse ta kalleta ta ce "A haka zaki haihun? Malama sai kin cire wannan wandon"
Fadila ta waro ido ta ce "Kai wando kuma? ta ina zan haihun?".
"Ta in da cikin ya shiga" ta bata amsa tana haɗe rai.
Fadila ta ce "Kinga kar ki raina mini Hankali mana, bance ki zageni ba, nifa sai in fasa haihuwar nan a nan in koma gida".
Nurse ta cire safa ta ce "Ba haihuwa zaki yi ba".
Nurse ɗin ta je ta samu Yaizd ta ce "Wannan Yarinyar ba haihuwa za ta yi ba, idan ta fara naƙudar ta dawo"
Kan yayi magana sai ga Fadila ta fito tana tura baki.
Yazid ya ce "Habibty, ya aka yi ne?"
Fadila ta kalleshi ta ce "Ni zata gayawa baƙar magana daga tambayarta, ni kuwa na ce na fasa haihuwar a nan, a gida zan haihu"
Yazid ya ce "Anya Fadila, ki tsaya su yi miki abin da ya dace".
"Ba zan zauna ba gaskiya, mu tafi gida kawai"
Yazid ya ƙyaleta suka koma gida, suka koma ta danƙari Abincinta, ta sha tofin da Yazid yake yi mata, ta yi kwanciyarta ta hau bacci.
Bayan azahar Fadila ta tashi, ta ji mararta na ciwo har ƙafafuwan ta, ta dake ta yi salla, ta cigaba aiki, abu kamar wasa tana jurewa, abu har ya gagara, Yazid ya dawo daga makarantar dare, ya tarar da ita da ƙyar take iya magana.
Shi ya zata ma mutanen ne zasu tayara mata, ya zauna yana yi mata Addu'oi.
Cikin numfarfashi ta ce "Zid ka kaini Asibiti, zan mutu" a gigice ya fita neman abin hawa ya rasa, ya tafi gidan Hajiya ya sanar mata.
Hajiya ta je ta ƙwanƙwasawa wani maƙocinsu ƙofa, ya ɗauko mota aka saka Fadila da kayanta, zuwa Asibiti.
A wannan karon Fadila babu gardama, abin da aka ce ta yi shi take yi, duk da haihuwar da saura, amma suka ce a bata gado Yazid ya riƙeta su yi ta zagayawa.
Hajiya ta koma gida, ta dafo ruwan zafi ta dawo Asibiti.
Suna zagaye idan ciwo ya lafa tayi ta surutu, idan ciwo ya tashi sai bakinta ya mutu.
Wasa-wasa tafiyarma ta gagari Fadila, sai kuka da take yi.
Hajiya ta ce "Kiyi haƙuri Fadila addu'a ake yi, ba kuka ba".
Fadila ta ce "Hajiya baki san me nake ji ba"
Hajiya ta ce "Ki yi haƙuri to, yi ta Addu'a".
Tafiya ta gagari Fadila, aka shiga da ita labor room, sai dai laborn nata kamar ana jansa, sauri yake sosai kamar ba haihuwar fari ba.
Ta ce a kira mata Yazid, Nurse ɗin ta ce maza ba sa shigowa, aikuwa ta dinga kurma ihu tana ƙwala masa kira.
Ba shiri Nurse ɗin ta kirawo shi, kasancewar ita kaɗai ce ke laborn a labor