Showing 219001 words to 222000 words out of 296192 words

Chapter 74 - GABA DA GABANTA

suka fice.
Ɗaya gidan nasa suka tafi, ta haɗa musu breakfast, bayan sun kammala suka sake shiri a tsanake suka fita.
Gidan Ammi suka fara zuwa, Ammi tayi murna da ganin Amina, ta yi ƙiba sosai ta ƙara kyau.

Amina ta hau yiwa Ammi mitar, ita bata dawo ba, Azima ma bata je ba.
Ammi ta ce "Ai bai kamata mu dinga yi miki zarya a wannan ƙadamin ba, ita ma nan suka shirya da 'yan ajinku da zasu je miki, nace kar suje tukuna kar wannan abokiyar zaman naki ta tsinkaki a gabansu"

Amina ta ce "Ni da yake ma bata tata nake yi ba, idan tayi mini ba raga mata zan yi ba, kullum ni ba mai zuwa wurina, ita Azima ai da ko ita sai ta dinga zuwar mini".

Azima ta ce "Ni rabani da zuwa gidan matar aure, ta koreni ta ce mini mijinta ya dawo"
Bata wani jima ba, Daddy ya kirata ya ce ta zo suna da wurin zuwa sosai, haka tayi sallama da Ammi da Azima suka tafi.
Daddy gidajen wasu daga abokansa na Kano, ya kai Amin suka gaggaisa da iyalansu, tare da yi musu bangajiyar zuwa walimar bikinsu.
Amina tayi mamakin yadda Daddy yake da jama'a, amma babu mai iya takawa gidansa saboda masifar matarsa.

Sai azahar suka ɗauki hanyar Shanono, Amina sai daɗi take ji, kamar yau zata fara zuwa garin.

Inno da bata san da zuwansu ba, ta rasa ina zata ajiyesu dan daɗi, nan da nan aka yiwa Baba waya aka ce Amina ta zo, Baba ya rufe shago ya nufo gida cike da ɗokin son ganin tilon 'yar ta shi.
Abin kunya sai ga su Baffa Bala, sun biyo sahun masu zuwa su gaida mijin Amina, kamar ba iyaye ba sai gasu suma.
Sai a yau Amina taga sabon gidan da aka sayawa su Baba, manyan gidaje biyu ne aka saya aka haɗesu, aka ƙawata su, ga aiken kayan Abinci da Daddyn yake yi musu.
Ba ƙaramin kima Daddyn ya daɗa a wurin Amina ba, ita a rayuwarta duk wanda yake son iyayenta to ya samu zuciyarta.

Aikuwa duk wanda ya zo akwai alherin da Daddy zai yi masa, Amina ta sake sosai a gida tare da Inno da Baba, suka yi ta hirar yaushe gamo.

Bayan sallar la'asar suka nufo cikin garin Kano.


Hajiya Zainab kuwa bayan ta farka ta nemi Alhaji Ahmad ta rasa, ta kira wayarsa ya sanar mata yayi sammako sun fita da Amina.
Haka ta dinga zage-zage ita kaɗai a gida, ta zari mayafi ta tafi gidan Hajiya Turai, suka sake tattaunawa a kan batun magungunan wurin malamin, aka tambayeshi ko za a iya amfani da maganin a kifi, ya ce musu a'a lallai a Nama ake so.

Har ta dawo da yamma su Amina basu dawo ba, ta zauna a falo ta kasa tsare tana jiran taga ta ina zasu shigo.

Aikuwa tana nan zaune, sai gashi sun dawo, Daddy na riƙe da jakar Amina, Zakiru kuma ya shigo da kayan tsaraba, da suka zo da su daga ƙauye.

Ba kunya ba mutunci haka Hajiya Zainab ta cigaba da tsigale masa a gaban kowa.
Amina tafiyarta tayi ta bar su, dan ta lura ita dai Hajiya Zainab idan har za a biye mata kullum sai an yi tashin hankali da ita.

Amina bata san yadda suka ƙare ba, dan tana zuwa sashen ta rage kayan jikinta tayi, ta shiga tayi wanka tayi alwala ta zo ta tada salla.
Bayan ta idar Daddy ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata yana cikin damuwa, kuma ta san Hajiya Zainab ce ta kunno shi.

Ya zauna yayi shiru ya rasa abin da yake masa daɗi, Amina ta ninke abin sallar, ta je ta zauna a kusa da shi, ta rungumo kansa jikinta, tana ɗan shafa bayansa cikin sigar rarrashi ta fara magana "Sweetheart, ni da yaranka da duk masoyanka muna buƙatar ranka da lafiyarka, dan Allah kar ka cutar mana da kanka, saboda wata damuwa da zaka iya ajyeta a gefe muyi rayuwarmu. Damuwarka na jefa ni cikin damuwa nima duk sai na rasa meyake mini daɗi, kayi haƙuri ka ji?"

Da fari ji yake kamar zuciyarsa zata tsaga ƙirjinsa ta faso, amma kalaman Amina suka dinga kwantar masa da hankali, sai da taga ya ɗan nutsu, sannan ta ƙyaleshi yaje yayi salla, ya nemi wuri ya kwanta.
Washegari yayi shahada ya je wurin Hajiya Zainab yi mata sallama saboda doguwar tafiya da za suyi, tana fara zage zagenta, ya fice ya tafi ya barta.


Ko da suka Dutse, danginsa tamkar zasu goya Amina, Amina gata da saurin sabo, ga ungo uban kayan zaƙi na gararta da aka kai musu kawai sai santi suke. Wasun su har suna ita wannan da ake gani ga karkara ce har da abin arziƙi na gara, uwar mulki kuwa ko barbaɗen gishiri ba ai kai mata ba.

Amina ta yadda Alhaji Ahmad ɗan gata ne, kuma ɗan dangi gaba da baya, amma saboda tsabar son zuciya na Hajiya Zainab ta sa ya watsar da kowa sai ita.

A family house ɗin su Daddy suka kwana, ya ɗauko mata hotuna yana nuna mata hotunan iyayensaa da 'yan uwansa da ya rasa, sai da ya zub da hawaye, saboda iyaye wasu duraku ne masu girman gaske a rayuwar kowane ɗan Adam.

Washegari da Azahar, aka kai su Alhaji Ahmad airport, inda jirginsu ya ɗaga zuwa Dubai.



Alhaji Ahmad ya samu isashshen lokacin hutawa, da nuna wa 'yar babyn amaryarsa kulawa da soyayya sosai da sosai, ya ɗan samu releif daga yawan hayaniya da tashin hankali da yake fuskanta na Hajiya Zainab.
Amina lallaɓa abinta take, ta mayar da shi kamar yaro dai-dai da shekarunta.
Ya dinga yawo da ita wuraren shaƙatawa daban daban yana kashe mata kuɗi.


Hajiya Zainab saboda azabar baƙin ciki da kishi, gaba ɗaya ta manta bata gayawa Fadila batun maganar aurenta ba, sai ma shirin sake komawa nijar da suke yi a karo na biyu, dan yin wani asirin tunda wannan bai yiwu ba.
Sai da taje tana yiwa Fadila sallama, tana sanar mata in da zata tafi ne, Fadila ta ce "Mummy, me kuma zaki je yi a nijar? Muda bamu da kowa a can?"

Mummy ta ce "Sirikarki zamu raka, zamu je harkar wani business ne"

Cikin mamaki Fadila ta ce "Sirikata kuma? Wacece sirikata?"

Mummy tayi murmushi ta ce "Hajiya Salma mana, ni mana manta ban gaya miki ba fa, iyayen Salim sun zo sun yi magana da babanki, ya ce ya basu kuɗi kawai zasu kawo a saka rana".

Saroro Fadila tayi tana kallon Hajiya Zainab, ta ce "Mummy yaya za a ba dani ga mutumin da duk abin nan da ake yi ko ganinsa ban taɓa yi ba"

Mummy ta dafa kafaɗar Amina ta ce "kar ki damu, an tura masa lambarki, za kuyi magana, ai na san ba zaki bani kunya ba, shi ya ce kin masa ai, bari in tafi kar suyi ta jirana, idan na samu dawowa a yau shikenan, idan ban samu ba, sai dai mun yi waya" ta ɗau jakarta ta nufi hanyar fita, ta bar Fadla da wani yanayi da ta kasa gane kanta, takaici ne ko mamaki.



Amina tana cikin bacci, tayi mafarkin wata baƙar mage, ta biyota, tana ta gudu tana kiran sunan Allah, amma duk da haka magen tayi tsalle ta kafa haƙoranta a cikin Amina.


"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Daddy ka taimakeni" Daddy da yake banɗaki yana wanka, kansa yayi wata irin sarawa, sai da ya dafa bango, da ƙyar ya iya lalubar towel ya ɗaura ya fito.
A gigice ya ƙarasa gadon da Amina take, wanda gaba ɗaya ya wanke da jini, ga jikinta sai rawa yake, kan ya ƙarasa in da take yaji jiri yana neman kayar da shi.


WANDA KUKE FITAR MINI DA BOOK, NA GODE SOSAI 🙏 ALLAH YA NA KALLONMU DUKA, DAN BA MUYI HAKA DA KU BA.

AYSHERCOOL
08081012143NA KUƊI NE ₦500 VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI EVIDENCE OF PAYMENT TA
08081012143

68

Dafe kai Daddy yayi, ya ɗan jingina da bango, yana kallon Amina, yana kallon yadda jikinta ke ta karkarwa, 'yar rigar baccin jikinta, duk ta ɓaci da jini, farin bedsheet ɗin da ke kan gadon shima yayi kaca kaca da jinin.

Da ƙyar Daddy ya ja jikinsa, kansa na cigaba da sarawa.

A hankali ya furta "Meenal"

Yayi maganar yana ƙarasawa in da take kwance. Ƙanƙame shi tayi tana kuna, jikinta na cigaba da rawa.

"Meenal meyasameki haka?"

"Daddy tsoro nake ji"

"Tsoron me?"

Muryarta na rawa ta ce "Wata mage ce take cizona"

Bai damu da yadda ta ɓata shi da jini ba, ya sake ƙanƙameta ya ce "Meenal ba wata mage a wurin nan"

"Kayi mini Addu'a, zafi nake ji sosai"

Ya jinajina mata kai, amma ya kasa furta komai da sunan Addu'a, sai kansa da yake ta juayawa, yaga komai na juya masa, suka sake ƙanƙame juna, ji take kamar numfashin ta zai ɗauke, mararta kamr zata haifi dutse haka take jinta.

Amina ce tayi ƙarfin halin fara karanta Adduoi a zuciyarta, a hankali kuma ta fara furtawa a kan harshenta.
Sun daɗe a haka, kan daga bisani su ji su tamkar wanda suka farka daga barci.

Jin kan ya ɗan lafa masa ya sanya ya ɗan ɗaga Amina daga jikinsa, idanunta duk sun yi wani iri saboda kukan da tayi.

"Ya jikin naki?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Da sauƙi"

"Bari in taimaka miki ki gyara, sai mu tafi Asibiti"

Daddy har tausayi ya bata, saboda yadda shi ma yake fama da kansa, amma sai kaiwa yake yana komowa, da kansa ya wanketa tsaf, ya gyara bedroom ɗin.

Duk da jikinsa babu daɗi, haka ya saka Amina a gaba suka tafi Asibiti, Daddy yayi mamaki da aka gwada sigansa da jininsa duk lafiya lau, duk sauran teses ma da aka yi masa komai ya nuna lafiya lau.
Sai dai babban abin da ya tayar masa da hankali, bai wuce yadda aka sake tabattar masa da cewar Amina ta sake samun ɓarin juna biyu ba. Shi baya sanin da cikin sai dai yaji ɓari, ji yayi kamar yayi kuka, saboda yana daga abin da yake buri shi ne samun yara.

Ɗakin da take kwance ya shiga, ya tarar da ita da drip a hannunta, ta ƙurawa wuri ɗaya ido.
Sallamarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da take yi. Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙo hannunta a cikin nasa ya ce "Sannu Meenal"

"Yauwa Daddy, ya jikin naka? Ina fatan ba wata matsala?"

Ya jinjina mata kai ya ce "Eh, sun duba komai normal, amma sun gaya miki meyafaru da ke?"

"Eh sun gaya mini, wai na kuma samun abortion ko?"

Cikin tausayawa ya ce "Eh haka ne, amma kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"

Ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Daddy, ai bakomai Allahn da ya bani shi ya karɓa, duk na san ina son na haifi abin da ke cikin, amma Allah ya san dalilin da ya sa suke zubewa"

"Haka ne Meenal, amma Meyasa baki gaya mini kina da juna biyu ba?"

Ta ɗan gyara kwanciyarta ta ce "Nima ban san akwai ba, tunda nayi wancan ɓarin, ban sake period ba, ban san ina da wani cikin ba"

Ya shafa kanta ya ce "Shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ina ga zamu ɗan ƙara kwanaki kan mu koma Nigeria, sannan ina son idan mun koma muje kiga ƙwararen likitan mata"

"Amma meyasa zamu ƙara zama a nan, kaga a gida baka gaya mata ba"

"Amina, bana son damuwa ne, na shafe shekaru ina karatu, neman kuɗi, kula da iyali da suaran hidindumu ina buƙatar hutu ƙwarai da gaske, yanzu muna komawa gidan, ba zata sauya zani ba, zata cigaba da tayar mini da hankali ne kawa, dan haka ki barmu mu huta sosai ma koma, kinga kya ga likitan matan ma a nan kawai"

Haka Amina ta haƙura ta ƙyaleshi. Duk gwaje-gwaje da yakamata an yiwa Amina, babu wata matsala da ta nuna cewar ita ke haddasa mata ɓari, a ka sallameta aka bata magunguna suka koma gida.

Ita kanta Amina tayi mamakin yadda aka yi hakantake faruwa, cikin farko dai ta san faɗuwar da tayi ne, na biyun nan kuma daga wannan mafarki ta tashi ta ganta cikin jini.
'ko dai aljanu ne zasu shafeni, dan amce suna saka mutum ɓari?' tayi wa kanta tambayar a zuciyarta.
Da sauri ta kawar da tunanin ta bawa kanta amsa da ai tana azkar, dan haka babu abin da zai sameta sai abin da Allah ya ƙaddara mata.

Kwanaki biyu a tsakani suka ware, suka cigaba da shan soyayya ita da Daddy, ta mayar da shi tamkar ƙaramin yaro daidai ita, yayi ta biyewa shirirtarta, yawo kuwa wuri wuri hake suk tafiya, wataran suyi tseren keke, da makamantansu wanda hakan ya ke ƙara musu kusanci da kuma ƙaunar junansu.


A gida kuwa Hajiya Zainab taje ta kuma karɓo wasu asirin, gaba ɗaya hankalinta baya kan Khalil yanzu burinta shine ta wargaza auren Daddy. Sai dai ta jefa Fadila ma a cikin cakwakiya, dan tunda tayi mata zancen za a kawo kuɗin aurenta da mutumin da bata sani ba, ga shiga tashin hankali, dan sam bata jin ƙaunar abin a ranta.
Kamar yadda Mummy ta gaya mata, sun bawa Salim lambar wayarta, dan har ma yayi mata magana ta what's app, amma yaƙi tura mata hotonsa, gaba ɗaya sam a tsarin yanayin kalamansa ma bata ji yayi mata ba, hakan ba ƙaramin jefata yayi a damuwa ba.

Mummy ta sakata a gaba, tana ta tsara mata yadda zata shiryawa bikinta, domin daga shi ta san ba zata kuma aurar da ɗa ba, amma taga gaba ɗaya Fadilan ta ɓata rai.

"Fadila, wai meyake damunki ne?"

Kamar ta taɓo wa Fadila in da yake mata ƙaiƙayi ta ce "Ni wallahi Mummy bana son auren nan, dan Allah ki barni in cigaba da karatuna kawai"

Mummy ta ce "Haba Fadila, so kike na mutu banga jikokina ba, meye aibun kiyi auren yanzu ki cigaba da karatun naki a gidansa?"

"Ni Mummy auren ne bana so, dan Allah kawai a bar maganar nan"

"To yanzu Fadila so kike naje na samu Hajiya Salma nace mata ba kya son auren, bayan an riga anyi magana? Ki duba kiga abin da babanki da yayanki suka yi mini, kema watsa mini ƙasa a ido zaki yi kenan? Duk cikinku babu wanda zan raɓa naji daɗi, hankalina ya kwanata kenan?"
Ganin yadda gaba ɗaya mood ɗin Mummy ya sauya ne, ya sanya Fadila a sanyaye ta ce 'Mumny kiyi haƙuri dan Allah, ba haka bane ba, shikenan naji na haƙura zan aure shi in dai zaki ji daɗi".

"Yauwa 'yar autata, ai na san ke ba zaki bani kunya ba, ba zaki zuba mini ƙasa a ido ba, Allah yayi miki albarka, shi kuma ɗan uwanki shi ma ina nan ina faɗi tashi, dan ba za ayi auren nan ba"

Fadila dai bata sake iya cewa komai ba, ta tashi ta koma ɗakinta, ji tayi kamar ta saka hannu a ka ta kurma ihu, saboda amsawa Mummyn da tayi zata auri Salim, alhalin har ga Allah ita bai yi mata ba sam.

Gaba ɗaya yanayin da take ciki ya nemi ya shafi karatunta, sam bata mayar da hankali, ɗan karatun da take ƙoƙarin yi ma ta kasa, da ta fara sai tunani, Yazid yana ankare da ita, sai dai baya son yawan shiga sabgarta tana yarfa shi, amma kowa ya kallta ya san akwai damuwa a tare da ita.

Ɓangaren Maman Hafsa kuwa, tana ɗan shirninta, da ba a rasa ba, duk da an ɗauke musu kayan ɗaki, amma hankalinta ya kasa kwanciya, saboda bata ajiye ba, ba kuma ta bawa wani ajiya ba. Dama ta san dangin mahaifin Hafsa babu uwar da zasu tsinana musu, mutanen da suka ƙi karɓar kuɗin aurenta, suka dinga ɓata ta a wurin sirikinta, yaushe za a sanya ran zasu yi musu wani abu.
Ga unguwa ta ɗauka, wai Liman ne ya karɓi kuɗin auren Hafsa, sa ƙanan maganganu suke yi, wai anya ma kuwa tana da uba, 'yar halak ce, dan idan da dagaske mahaifinta rasuwa yayi, ba za a rasa danginsa da zasu karɓi kuɗin Aurenta ba.
Wasu abubuwan ma dai, Hafsan ce take kwantarwa da Maman hankali a kan wasu abubuwan.

Khalil kuwa ya zage sai faman ƙoƙarin hattama gininsa yake da kayan lefe, dama gini ne ya ɗauko shi na manya, dan haka sai fama yake yi, 'yan uwan Daddy da abokanansa sai bashi gudunmuwa suke yi. Shi da Abdul suke tsara komai, kayan lefe dama Hajiya Maryam yake turawa kuɗin tana saya wa Hafsa, idan ya tambayeta me take so ayi mata a gidanta, ko na lefe sai ta ce masa ita komai ya sakamata ta gode, juyin duniya Hafsa ba zata taɓa ce masa ga abin da take so ba.
Akwai abubuwa da yake buƙatar shawarar Hajiya Zainab, amma ba halin ya tuntuɓeta, ko kiranta a waya baya iya yi, saboda yana tsoron abin da ka iya haifarwa. Aikuwa hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, ga Daddy da ya ce zai yi kwana goma ya shuɗa, ko nemanta a waya baya yi, shima Khalil ɗin haka.
Da kanta ta kira Khalil a waya, yana ganin wayarta ya shiga cikin tashin hankali, dan bai san dalilin kiran ba.

Aikuwa kamar ya sani, dan yana ɗagawa ta dira masa bala'i.

"Khalil ka zama ɗan kanka ko? Gaba ɗaya ka mayar da ni a bar banza, bani da wata kima a idonka, bani da mutunci saboda ubanka ya goya maka baya ka auri 'yar matsiyata, to duk abin da kake ka ajiye ka dawo gida ina son ganin ka"

A ɗan rikice  Khalil ya ce "Mummy, aiki yayi yawa a nan, sai na nemi excuse tukuna"

"Ba ruwana da wani excuse, kai ta shafa, ka dawo mini gida, ina son ganinka"

Jiki a sanyaye ya ce "To shikenan, zan dawo in sha Allah"

Tayi tsaki ta kashe wayarta.

Alhaji Ahmad dai sai da ya shafe sati uku shi da Amina, daga kwana goma, sannan suka yi shirin dawowa Nigeria, tunda suka fara shirin tahowa Nigeria, Daddy ya shiga cikin damuwa, saboda ya san da sun dawo zai cigaba da fuskantar tashin hankali daga Hajiya Zainab.

Amina ta lura da yanayin da Alhaji Ahmad yake ciki, kuma ta san bai wuce a kan Hajiya Zainab bane ba, ba ta fiye son yi masa shishshigi a kan abinda ya shafe shi da Hajiya Zainab ba.

Haka suka gama shirinsu, suka koma Nigeria.
Ko da suka sauka, gidan babu kowa, Fadila tana makaranta, Hajiya Zainab ta tafi nata gantali.

Hajara ce ta tari su Amina, cikin murna da sakin fuska, nan da nan ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login