Showing 210001 words to 213000 words out of 296192 words
ta tsaya a ƙofar bedroom ɗin, ta dinga bugawa kamar zata karya ƙofar.
Amina ce ta fito da 'yar riga iya cinyarta, kanta ko ɗan kwali babu tana mutsutsuka idonta.
"Malama lafiya kike mana wannan bugun da safiyar nan?"
"Ke! Ba wurinki na zo ba, wurin mijina na zo yana ina?"
Amina ta rufe ƙofar bedroom ɗin sannan ta ce "Mijinmu dai ko? Bacci yake yi bai tashi ba ya aka yi?"
"Ba ruwana da bai tashi ba, ki bani hanya na wuce"
Amina ta tare ƙofar ta ce "Uban da ya saka kika masa rashin mutunci, ki ka koro mini shi nan, sai ya sa ki haƙura zuwa lokacin da zai dawo wurinki, kya gaya masa koma menene"
"Ke ni kike gayawa haka, sa'arki ce ni? Zaki bani hanya ko saina make ki"
Cikin rashin kunya Amina ta ce "Ba zan matsa ba, gobe idan ya kuma wurinki ki koreshi, yana zuwa zan caraf da shi ni. Ai ni Allah ne yayi mini gyaɗar dogo ma samu mijin shashasha, wadda bata da ra'ayin kanta sai na ƙawa, idan basu sa kin kashe auren nan ba ba zaki yi hankali ba"
"Ni kike gayawa haka? Dan kin auri mijina gani kike ni sa'arki ce, wallahi sai nayi maganinki"
"Allah da yayi ni shine maganina, ba ke ba, Allah sarki rayuwa, ba zan taɓa manta ranar da na zauna a kan kujerar falon mijinki ba, kika ƙare mini zagi da cin mutunci, amma da yake Allah ba yadda bai iya ba, sai gashi ƙirjinsa ne matashina, a kan ruwan cikinsa nake kwana, kin gama yi mini komai da kika sallama mini shi, Baby ya iya soyayya" ba tsoro balle kunya, Amina take gasawa Hajiya Zainab maganganu masu zafin gaske.
Jikin Hajiya Zainab har rawa yake, saboda azabar ɓacin rai ta ce "Ni kike gayawa wannan maganar?"
"Uwata ce ke da ba zan gaya miki ba? Ko kin manta lokacin da kike cin mutuncin ubana a gabana, ai kaɗan kika gani, ba zan fasa yi miki abin da na ga dama ba, har sai na tabattar da zuciyata ta samu nutsuwa daga baƙin cikin da kika dinga tura mini a zuciyata, abu mafi zafi a rai shi ne zagin ubana a gabana da kike yi"
"Na zagi uban naki, matsiyata 'yan ƙauye"
Amina ta ce "Ai ba zanji haushi ba yanzu, dan kin zagi Babana mussman da na san asalin balbela, kema daɗinta naki uban ba wani bane ba, da miji kike taƙama idan har za a kira maigadi matsiyaci ban san da wani sunan za a kira mai faskare ba, koda yake koba komai ko da goma ta lalace tafi biyar albarka, saboda rayuwata ta ginu nawa uban ya dage yake jure duk wani cin mutunci ake masa a gidan nan"
Cikin tsananin fushi, da zafin nama Hajiya Zainab ta fizgo Amina, ta hankaɗata ƙasa.
Amina kuwa ta ware baki, ta kurma uban ihu tana kiran "Wayyo Allahna Daddy ka fito kar ta kasheni, Daddy!Daddy matarka zata illatani"
Duk da sama sama yake jiyo ihun Amina, a sukwane ya farka daga baccin da yake, ya fito daga bedroom ɗin, aikuwa yaga Amina a ƙasa hawaye ya wanke mata fuska, Hajiya Zainab kuma na tsaye a kanta tana huci.
Ita kuwa Fadila, ta gama shirin makarantarta, ta ƙudurce zata je ta yiwa Daddy maganar kuɗin registration ɗin ta na makaranta, dan haka bayan ta kintsa, ta ɗauko jakarta ta nufi sashin Daddy.
Daddy kuwa kan Amina yayi da sauri, ya ɗagota yana faɗin Meenalina, menene meyafaru?"
Cikin kuka Amina ta ce "Dukana za tayi, hankaɗe ni tayi ni ƙafata da bayana ciwo suke, dan kawai nace mata bacci kake yi ba zan tasheka ba"
Aikuwa ran Daddy ya ɓaci, ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Wai meyasa baki da girma ne? Kina cewa nayi abin kunya na auri 'yar cikina, ke kuma me ki ka yi? Zaki yi dambe da 'yar cikinki? A irin haka fa kuka je ke da 'yar ki kuka saka tayi ɓari, duk kashedin da nayi miki a kan Yarinyar nan baki ji ba, so kike sai kin illata ta hankalinki zai kwanta?"
"Kai baka san meyafaru ba kawai daga fitowarka zaka hauni da masifa, kai wani irin mutum ne, na dake ta ɗin kayi abin da zaka yi"
"Zainab na gaji da kawar miki da kai, koma menene ke kika zo in da take ai, ba ita taje in da kike ba, zan aikata abin da baki tsammani ba, muddin kika cigaba da takurawa rayuwarta, ba ita tayi miki laifi ba, nine da na aureta, komai zaki yi mini, zanniya jurewa bai dameni ba, amna ba zan lanunci cin zarafin 'yar mutane ba dan kawai ina aurenki ba, ita ma matata ce dan haka ki kiyayeni"
Ai gaba ɗaya sai Hajiya Zainab taji kamar ƙafafunta sun gaza ɗaukarta.
Ya kalli Amina cikin kulawa ya ce "Sannu Meenal, tashi muga"
"Ni ƙafar ciwo take mini, ka ɗaukeni muje ka ja mini" ya sunkuya ya ɗauketa kamar 'yar baby, ta kalli Hajiya Zainab tayi mata gwalo.
Fadila da taji abinda ya faru, kawai ta juya ta fice kan Mummy ta fito tana kuka.
Ikon Allah ne kawai ya kai Fadila makaranta, saboda tuƙi take amma sam ba a hayyacinta take ba, kuka kawai take yi.
Daddy kuwa a kan gado ya sauke Amina, ya zauna yana matsa mata ƙafar yana cewa "Sannu, ince ko dai bayan ƙafar ba abin da yake miki ciwo?" Amina ta jinjina kai.
Ya cigaba da ja mata yatsun ƙafar, yana faɗin "Sannu babyna, kar ki dinga biye mata dan Allah, kar ta illata mini ke, idan tayi miki wani abun ni ki gaya mini na ɗau mataki, amma dan Allah karki dinga biye nata tayi miki illa"
Cikin shagwaɓa ta ce "Nifa ba biye mata nayi ba, kawai daga cewa bacci kake ta hankaɗeni"
"To kiyi haƙuri cutyna" yayi maganar yana shafar fuskarta zuwa kan hawayenta.
Hajiya Zainab kuwa har ta nufi ɗakinta zuciyarta na yi mata zafi, ta juyo ta dawo ta banka ɗakin.
Tana bankawa ta tarar da Amina ta ɗage rigar jikinta, ta ɗora santala santalan ƙafafuwanta a kan nasa, tana goge hawaye, shi kuma sai lallaɓata yake yana kwantar mata da hankali.
Kamar zata afka kans Hajiya Zainab ta ce "Kai Ahmad na gaji, na gaji wallahi, na gaji da wannan cin kashin da kake mini. Wallahi ko ni ko wannan sheɗaniyar yarinyar, zaka gane baku da wayo daga kai har ita"
Saroro suka yi suna kallon Hajiya Zainab, sai masifa take kamar ta haukace, sai da ta yi ta gama ta fice daga ɗakin.
Rarrashin Amina ya cigaba da yi, yana kwantar mata da hankali, a kan in dai yana nan babu abin da Hajiya Zainab za tayi mata.
A yadda Fadila ta shigo aji, idnuwanta jawur duk sun kumbura, gaban Yazid ya faɗi ya juya yana binta da kallo.
Haka aka yi lectures, yana yi yana kallon Fadila, tana ta share hawaye.
Haka suka yi lectures wuni guda, hankalin Yazid yana kanta, yana mamakin menene ya sanyata a wannan halin haka.
Ko fita cin abinci bai ga tayi ba, kuma tsawon awannin nan, hawaye take zubarwa, kowa sabgar gabansa yake a ajin.
Koda aka tashi ma, Yazid yana zaune yana kallon in da take zaune, kowa ya watse amma sai ɗaiɗaikun mutane, ita kuwa tana zaune ta kifa kanta.
Miƙewa yayi ya nufi in da take zaune, ya ɗan daddaki kan teburin, amma bata motsa ba.
Ya kira sunanta a hankali "Fadila" kamar wadda take bacci haka tayi firgigit ta tashi.
"An tashi kowa ya tafi, amma kina zaune, lafiya kuwa?"
Ta girgiza masa kai, ta fara duba jakarta.
Zama yayi a kusa da ita ya kalleta ya ce "Ukty meke damunki haka?"
"Ban sani ba" ta faɗa cikin tsiwa.
"Yi haƙuri, amma tun da kika zo fa kike kuka, me yayi zafi ne haka?"
"Na ce maka ban sani ba, ina ruwanka dani ne? Ba kace bani ba kai ba ka rabu da ni mana"
Yazid yayi murmushi ya ce "Eh na faɗa, amma ke kika fara ai. Zuciyata ta kasa daurewa, bana son ganin mutum cikin damuwa, yanzu haka ji nake kamar na tayaki, meke faruwa can You share it with me?" Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa.
"Fadila nima zaki sani kuka, dan Allah ko menene yake damunki, kiyi haƙuri yi ta maimaita innalillahi wa innalillahi raji'un" yayi maganar a raunane.
Kallonsa Fadila tayi, da gaske yake zai tayata kukan, saboda yadda idanunsa suka sauya.
"Ni gida zan tafi, bani wuri" tayi maganar tana share hawaye.
Jakarta ya ɗauka ya ce "Muje na rakaki mota" tashi tayi tai gaba, yabi bayanta.
Har suka isa motarta, kuka take bata fasa ba.
Yazid ha ce "Bana tunanin zaki iya tuƙin nan, bani mukullin na kai ki gida"
Abin mamaki bata yi masa musu ba, ta miƙa masa mukullin, ba tare da tana tabbacin ya iya jan motar ko bai iya ba. Ya karɓa ya buɗe motar ya buɗe mata ta shiga, shima ya shiga ya kunna motar.
Ya ɗan kalleta ya ce "Ina ne adress ɗin?"
Nan tayi masa kwatance, ya yi addu'a, sannan ya fara jan motar a hankali.
Ganin ta ɗanyi Shiru, tana kallon gefen hanya, ya sanya Yazid ya ce "Yanzu gaya mini, meke damunki kike wannan kukan?"
"Wai kai ina ruwanka da abin da yake damuna, bayan kace ba kai ba ni, meya dameka da ni?"
"Hmm kin ji babu daɗi kenan, ai ke kika ce mini zaren ba kalar yadin bane"
Cikin tsiwa ta ce "To da kalarsa ne?"
Ya ce "A'a sorry. Tunda kin daina kukan Alhamdilillah, ita rayuwa haƙuri ake yi da ita, kuma komai yayi zafi magainsa Allah"
Yana rarrshinta, amma ji take kamar yana fama mata abin da yake mata ciwo.
Yazid ya sha uban mamaki, ganin uban danƙareren gidan su Fadila, yayi horn aka buɗe masa gate, ya shiga da motar ciki.
Sai dai yana shiga da motar, taji kamar ya dawo da ita cikin baƙin cikin da take ciki tsundum.
"A ina zan yi parking ɗin?"
"Kayi a ko ina ne ma"
Yazid ya yi parking, amma kan ya farga, tuni Fadila ta buɗe motar ta fice.
Amina tana falo tana ƙoƙarin fitowa, Fadila ta dawo ta wuceta fuuuuu kamar korarriya.
Amina ko a jikinta ta fito, tana fitowa taga Yazid a tsaye da mukullin mota a hannunsa.
Yazid ya ce "Sannu dai"
Amina ta ce "Yauwa sannu da zuwa, wa kake nema?"
"Amm dama Fadila na kawo gida, kuma bata tsaya ta karɓi mukullin motar ba, naga ta fice ta shiga gida"
Amina ta ƙare masa kallo sannan ta ce "Ko kai ne Yazid?"
Yazid ya ce "Eh ni ne"
Amina ta ce "Masha Allah, sannu da ƙoƙari bani mukullin na bata"
Yazid ya bawa Amina mukulli, har zai juya ya tafi ta ce "A'a ka tsaya a baka ko ruwa ka sha mana"
Yazid ya ce "A'a na gode"
Amina ta ce 'A'a ba zanji daɗi ba gaskiya, dan Allah ka jirani ina zuwa"
Yazid ya ce to.
Amina ta nufi cikin gida, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
66
A falo Amina taga Hajara tana aiki, Amina ta ce "Hajara, ɗan biyoni dan Allah zaki tayani wani ɗan aiki"
Hajara ta ce "To uwar ɗakina" tabi bayan Amina. Hajara ta tsaya a falo tana jiran Amina.
Amina ta shiga bedroom ta buɗe wardrobe ɗin Daddy, ta ɗauko galla gallan shadda guda biyu, da turare ta saka kuɗi a envelope ta fito ta miƙawa Hajara ta ce "Biyoni" suka fito in da ta bar Yazid a tsaye, ta karɓi kayan hannun Hajara ta miƙawa Yazid ta ce "Gashi muna godiya sosai da sosai"
Yazid ya ce "A'a gaskiya ba zan karɓa ba, na gode sosai"
Amina ta ɗan tsuke fuska ta ce "Meyasa, ka san babu kyau a baka kyauta ka ƙi karɓa faɗar maznon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ce"
Ba dan Yazid ya so ba ya karɓa ya ce "Na gode sosai"
"Bakomai malam Yazid, Allah ya saka da alheri" Yazid ya jinjina kai, yayi gaba ya fita daga gidan.
Hajara ta ce "Uwar ɗakina, wannan kuma waye?"
Tayi murmushi ta ce "Nima dai ban kai ga sani ba tukuna, amma wani abu ma shirin faruwa, da zai bawa kowa mamaki"
Cikin rashin fahimta, Hajara ta ce "Ban gane ba"
"Zaki gane ne Hajara" daga haka ba ta kuma cewa komai ba, ta wuce sashinta.
Fadila bayan ta gama koke-kokenta, ta shiga tayi wanka, ta sauya kaya ta fito taje taga a wani hali Mummy take ciki.
Sai dai tana zuwa ta tarar da Mummy bata nan. Hanyar Kitchen ta nufa tana kwaɗawa Hajara kira.
Hajara ta fito ta ce "Gani"
"Ki sama mini abin da zan ci" Hajara ta ce to. har ta juya zata tafi. Fadila ta ce "Kin san in da Mummy ta tafi ne?"
"A'a ban sani ba" "Shikenan je ki, kiyi sauri ina jiranki" Fadila ta koma kan dining, ta zauna tana kiran layin Mummy.
Amina ce ta sake fitowa, da ɗan ƙaramin plate a hannunta, ɗauke da yankakaen lemo.
Tv ta kunna, ta harɗe ƙafarta tana ciye-ciyen ta tana kallo.
Amina na ɗaga ido, suka yi ido huɗu da Fadila, Fadila tayi mata wani irin mugun kallo.
Amina ta ce "Oho, a dake dai ba zan daku ba, sai dai kallon banzan daga nesa"
Tsaki Fadila tayi, ta cigaba da danna wayarta, Amina kuma ta cigaba da ciye-ciye.
Hajara ta fito ta kawowa Fadila Abinci ta ajiye, Fadila ta fara ƙoƙarin cakalar Abincin ta ci, sai dai sam baya yi mata daɗi.
Ga lambar Mummy ta ƙi shiga gaba ɗaya.
Daddy ne yayi sallama a falon, Amina ta amsa masa ta ɗaga kai tana kallonsa tana murmushi.
"Meenal, sannu da hutawa"
"Sannu da zuwa Ranka ya daɗe" tayi maganar tana tashi tsaye. Ta ƙarasa gabansa ta karɓi ledar hannunsa tana binsa da wani irin kallo tana murmushi.
Ya riƙe hannunta suka wuce, ba tare da ya ko kalli in da Fadila take ba, kamar yadda ita ma bata ko yi masa sannu da zuwa ba, saboda kwata kwata ba ta shiga sabgar Daddy gaba ɗaya yanzu.
Ganin sun wuce ɗaki abin su hankali kwance, ya sanya Fadila ta tashi ta bar Abincin, tana jin wani abu mai ɗaci yana kai komo a maƙogwaronta saboda baƙin ciki.
Shi kuwa Daddy, tun da ya shige wurin Amina bai sake fitowa ba, sai da aka kira magariba.
Hajiya Zainab kuwa, tana fita gidan Hajiya Salma ta wuce, Hajiya Salma na ganinta ta san ba lafiya lau ba.
A ɗan rikice ta ce "Zainab, meyafaru ne na ganki a wannan birkice haka?"
"Ba dole ki gannin a birkice ba, na gaji wallahi Salma na gaji, ƙarar Ahmad zan yi ya sake ni, wannan matsiyaciyar Yarinyar da ace ita ta koreni daga gidan, gara ace ni na bar shi, yarinya kamar karuwa ga sharri, nuna mini yake a kanta zai iya sakina fa"
"To ke maye ya haɗaki da ita ma?"
Nan ta gayawa Hajiya Salma abin da yafaru da safiyar ranar.
"Lallai Ahmad ya wuce yadda muke zato, gaskiya mun yi sake da har ya iya ƙara auren nan ma"
Hajiya Zainab ta ce "Ai ni na gaji ma, ya sakeni kawai ba zan zauna baƙin ciki ya kasheni ba"
Hajiya Salma ta ce "Kut, baki da hankali, ya sake ki kije ina, ai duk wata hayaniya ayi ta da ke, gidan naki a zo a tarar da ke kice ya sake ki, ba zai yiwu ba, Dole mu nausa Nijar a gobe in Allah ya kaimu, a karɓo asirn da sai ta bar gidan nan da ƙafarta, ki cigaba da mulkinki son ranki"
"Ke nifa damuwar tawa da yawa, ya zanyi da batun auren Khalil, yaron nan ƙiri-ƙiri goyon bayan ubansa yake, kuma ubansa ya ɗaure masa gindin ya auri wannan Yarinyar"
Hajiya Salma ta ce "Kwantar da hankalinki, duk idan muka je Nijar ɗin za a san abin yi, Sannan kamar yadda na gaya miki, a satin nan baban Salim zai dawo, yana dawowa zan saka shi yaje ya sameshi suyi maganar auren su da Fadila. Kuma mu haɗadu ko ta wayane kan Allah ya sanya ya dawo gari"
Hajiya Zainab tayi ajiyar zuciya ta ce "Naji, da tunanina idan muka dawo, ko gidansu Yarinyar nan zamu nema, muje na ciwa uwatta mutunci idan suna da zuciya ai sai su ƙyale mini ɗana"
"Ke Ina! Yadda yake a kan tsinin nan yake rawar kai, sai ya ɗau matakin da ya ga dama a kanki ai, ki fara bari muje mu karɓo abin da yakamata, idan ya ci sai mu koma kan Khalil, ko kuma idan ma ba hakan ba, idan sai ya auretan, ki hanata sukuni ki hanata sakat sai rabu da ɗanki, kinga ta komawa iyayenta a ƙaranar bazawara idan kwaɗayi abin yi ne sa ƙara".
Hajiya Zainab ta ce 'Kai Salma, har na ɗan ji daɗi wallahi, yanzu abin da za ayi shi ne, ba zan koma gidan nan ba, sai mun dawo daga nijar, na koma da ƙwarina, yanzu idan ina gidan nan, zan iya babbake mu gaba ɗaya kowa ya huta"
Hajiya Salma ta ce "Kashe wayoyinki kiyi zamanki wallahi, yaje ya ƙarata".
Wasa-wasa har ƙarfe tara na dare zuwa goma, wayar Hajiya Zainab bata shiga, kuma bata dawo gida ba, hankalin Fadila ba ƙaramin tashi yayi ba, tun tana daurewa har ta kasa. Har goma da rabi ba Hajiya Zainab babu dalilinta, hankalin Fadila ya tashi ƙwarai, ta tashi ta tafi sashin Alhaji Ahmad.
Da sallama ta shiga falon nasa, ya amsa mata shi da Amina da ke kwance a kan cinyarsa suna kallo.
Ta tsaya tayi shiru ba tare da ta ce komai ba.
Daddy ya ce "Lafiya ki ka zo, kika tsaya mana a ka?"
"Dama, tunda na dawo gida ne, na duba banga Mummy ba, ina ta kiran lambarta amma bata shiga, kuma haryanzu bata dawo ba"
Ya ce "Hmm Fadila kenan, sai da buƙatarki ta tashi sannan kika san da zamana, kin ɗauki gaba dani ke da mahaifiyarki kamar wanda ya wofantar da ku, ai shikenan ni bata gaya mini in da zata je ba, nima naje sashinta bata nan, na kira wayarta bata shiga" jiki a sanyaye Fadila ta fice daga falon, tare da mamakin yadda Daddyn ya nuna halin ko in kula da rashin sanin in da mahaifiyarta take.
Amina ta ce "Yauwa Sweetheart, ni fa nayi maka laifi"
"Meenalina, ai ke ba kya laifi a wurina amma me kika yi?"
"Ma buɗe wardrobe ɗinka, na yi kyauta da sabbin shaddoji guda biyu, na kuma ɗebar maka kuɗi dubu ashirin na haɗa na bayar"
Daddy ya ce "To ya na iya da ke Meenalin, Allah ya haɗamu a ladan,