Showing 75001 words to 78000 words out of 296192 words

Chapter 26 - GABA DA GABANTA

kan a neme su a makaranta, a fara yi musu lesson.
Amina ta rage jin haushin Alhaji Ahmad a kan abin da iyalansa suke mata da kuma shima abin da yayi mata.
Ranar lahadi tun da ta idar da sallar Asubahi bata koma ba, ranar lahadi da su da masu gidan basu fiye tashi da wuri ba, saboda ba wanda yake fita a ranar.
Amina ita kaɗai ce idonta biyu, ta ɗora girki saboda Alhaji Ahmad zai fita.
Kan ƙarfe shida da rabi, Amina ta kammala girkin, har ta tsaftace falo ta kukkuna turaren wuta.
Tana ta sake goge kan dining, sai hamma take, saboda baccin da take ji.

"Sannu da aiki" ta jiyo muryarsa.
da sauri ta waiwaya, ta kalli in da yake tsaye "Ina kwana" ta faɗa tana ɗan lumshe ido. Maimakon ya amsa sai ya kuma maimaita mata "Sannu da aiki".

Ta fuskanci baya son yayi magana a share, dan haka ta ce "Yauwa na gode, ga breakfast ɗin".

Alhaji Ahmad ya ƙarasa ya zauna, ya kalleta ya ce "Afuwan na katse miki bacci" ta ɗan girgiza kai ta ce "Bakomai"
Ya bubbuɗe flask ɗin, yayi mamakin ganin ƙosai da soyayyen dankalin Hausa, da kuma koko.

Kawai sai ta ga murmushi ya mamaye fuskarsa. "Ke kika yi girkin nan?" Haka nan Amina ta tsinci kanta da tura baki, to wa yayi idan ba ita ba, saboda kawai ya raina mata hankali yake tambayarta.

"Hajiya am talking to you"

"Eh nina girka"

Ya jinjina kai, ya zuzzuba ya fara ci, yaji daɗin girkin nan sosai, yana son Abincin gargajiya sosai da sosai, amma sam Hajiya Zainab bata so, gashi na wuraren sayarwa baya masa daɗi sam ko a Lagos haka nan yake maleji ba daɗinsa yake ji ba.

Ya tsare Amina ya hanata tafiya, sai da ya gama, ta kwashe komai, sannan ya tashi zai tafi, Amina ta bi bayansa, har ya shiga mota ya hangota, ya tsaya yana jiran ƙarasowarta, ta miƙa masa wata jaka, be tambayi ta meye ba, ya karɓa ya duba, akwai manyan robar ruwa guda biyu a ciki, sai babban kwalin lemo, sai wata jarka guda ɗaya, ya ɗauko jarkar yana dubawa, fura da Nono a ciki.
Ya kalleta ya ce "Ina kika samu fura?"

"Mamana ce ta aiko mini da ita daga garinmu, na baka ne saboda hanya amma idan ba ka sha shikenan bani".

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Bayan wauta ashe kina da hankali, ga ruwa ga lemo ga fura duk an bani kar inji yunwa a hanya, Na gode sosai"

"Bakomai Allah ya sanya Alkhairi"

"Ameen ya Allah" ya zura hannu a aljijunsa ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ungo wannan, kya sayi wani abun na gode sosai" ga mamakinsa sai ta girgiza masa kai alamar ba zata karɓa ba.

"Meyasa ba zaki karɓa ba?"

"Baba zai mini faɗa, kuma yana bani kuɗi shima"

"Ke kuma sai ki gayawa Baban na baki kuɗi?"

Cike da wauta ta ce "Ai ni duk abin da aka yi sai na gaya masa, saboda idan nayi ƙarya yana ganewa"

"Ai yanzu ba zai sani ba, idan ma kika gaya masan, kice ni na baki"

"Ni dai a'a gaskiya, ban taɓa riƙe kuɗi me yawa ba, ba ruwana, kuma dama ai aiki nake kuna biyana meyasa zaka bani kuɗi?"

"Ai nima babanki ne, ki karɓa"

Girgiza kai tayi ta ce "Babansu Fadila ne, ni Baba ne Babana" shi mamaki ma ta bashi, yaran yanzu da son abin duniya, amma ta dage ba zata karɓa ba, baya son cigaba da takura mata, dan haka ya ce "Shikenan, na gayawa Baban idan na baki abu ba kya karɓa" ba ta ce komai ba ta juya sumi-sumi ta koma ciki.

Tana zuwa ɗakinta, ta nemi wuri ta kwanta, dan ta samu ta rintsa, cikin barci, taji hayagagar Hajiya Zainab a ƙofar ɗakinta.

"Uban waye ya ce a girka mini wannan abin a gida, gidan nan yayi miki kalar in da za a sha wannan kayan fitsarin da saka gudawar, taso ki fito ki girka mana wani abin da zamu ci" iya ƙuluwa Amina ta ƙulu ƙarshe, bata ga meye aibun koko da ƙosai ba, kuma banda wulaƙanci ga Hajara nan amma ba za a sata aikin ba sai ita.
A gajiye take matuƙa tana son hutawa, amma an tasheta da tijara, duk aikin da tayi a gidan kan su tashi ba su gani ba, haka ta fito rai a ɓace ta kuma shiga kitchen.


Ranar Litinin lectures da komai ya cigaba da gudana, amma ba Yazid babu dalilinsa. "Bismillah" taji sautin murayarsa ya shiga cikin kunnuwanta, a rikice ta kalleshi, sai ka ce Aljani sam ba ta ga shigowarsa ba sai zamansa a kusa da ita.
Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, tana son yin magana amma ta kasa.
"Ukty, ko nemana ba kya yi, ban dawo school ba babu ko cigiya"

"Ni nake biya maka school fees da zan damu da rashin zuwanka?"

"Kar mu fara haka dake daga dawowata mana, ya kike ya hutun?"

Ɗan kallonsa tayi amma taƙi magana, Sir Kankiya ne ya shigo ajin, hakan ya sa kowa shiga hankalinsa saboda ba shi da wasa sam ga kwarjini da yake da shi.
Yana ganin Yazid a zaune kusa da Fadila, ya haɗe rai "Kai malam babu wani wurin zaman ne, sai nan kusa da mace?" Yazid ya kalli ajin kowa in da ya ga dama yake zama, kuma ba wai matsarta yai ba, amma Kankiya na neman ya dizaga shi a cikin mutane.

Fadila ta ce "Tare muke zama da shi"

"Yaushe kika fara ƙarya? Ai ba dake nake ba, next time ka nemi wani wurin daban ka zauna" Yazid ya jinjina kai tare da sunkuyar da kai.

Fadila ba ƙaramin ƙular da ita Kankiya yayi ba, amma ta basar, aka cigaba da lectures. Mistakenly biron Yazid ya faɗi ƙasa, ya durƙusa ya ɗauko amma ya kuma jiyo muryar Kankiya yana faɗin "Kai wane irin mutumin banza ne, kalleka a haka kamar mutumin kirki, zo ka fita ka bar mini aji" Saroro Yazid yayi yana son gane laifin da yayi, gaba ɗaya idon 'yan ajin ya dawo kan Yazid.

"Zo ka bar mini aji nace" Yazid ya miƙe ya bar ajin, ba tare da yayi ƙoƙarin kare kansa ba.
Fadila taji haushin abin da Kankiya yayi, ya kammala lectures ɗinsa ya fice, ta ɗauki biron Yazid da littafinsa, ta nufi ofishin Sir Kankiya.

"Me Yazid yayi maka kake ta ƙoƙarin tozarta shi?" Tayi maganar cikin ɓacin rai.

"Yana bibiyar abin da nake so, idan yana son zaman lafiya ya kammala karatunsa hankali kwance a makarantar nan, to ya nesanta kansa da ke".

"Wai kai wane irin mutum ne? Ni nace maka ina sonka ne? Nayi maka kala da ajinka, nayi maka kalar auren mutum kamar kai? Babu wata alaƙa a tsakanina da Yazid, abokin karatuna ne kawai, dan haka kar ka ɓata masa career"

"Wannan ke ta shafa, da ke da shi, muddin ya cigaba da shiga sabgarki, zan iya kawo ƙarshen karatunsa a makarantar nan, idan kuma kin musa mu zuba mu gani, ba zan cutar da ke a harkar karatunki ba, Saboda ina sonki, amma gwargwadon wulaƙancin da kike mini, gwargwadon yadda zan cigaba da taka Yazid a cikin Jami'ar nan!!!

Ayshercool
08081012143GABA DA GABANTA

AISHA ADAM AYSHERCOOL

P 24_25


Iya wuya Fadila ta zo, saboda tsabar takaici da ɓacin rai, ta kalli Sir Kankiya ta ce "To mu zuba ni da kai, idan baka ɓata Career Yazid ba, ni zan ɓata taka rayuwar, na ga alamar baka san wacece ni ba, ba zan saka a hukunta min kai haka ba, kaci bulus, saina fara nuna maka ka ba kowa bane ba, face me sanye da rigar tsiya da zai ƙare a cikinta".

"Fadila ni kike gayawa haka dan ina son ki?"

"Na gaya maka ɗin, da na gaya maka ne? Me Yazid yayi maka? Koma menene tsakanina da kai ne, meye nasa, Wallahi ko na rasa mijin Aure ba zan auri mutum irinka ba" tayi maganar cikin huci, ta ja jakarta ta fice fuuuu kamar iska, ta bar office ɗin, cike da ɓacin rai.
  A haraba ajinsu ta hango shi, yana tsaye shi da wasu 'yan ajinsu, fuskarsa babu wata damuwa, kamar abin da ya faru bai ɓata masa rai ba.
Ganinta a tsaye tana kallonsa ne, ya sanya shi takowa zuwa in da take tsaye "Ukty daga ina?"
So take tayi masa magana amma ta kasa, ta miƙo masa littafinsa da bironsa.
Yayi murmushi ya karɓa ya ce "Na gode, ni nama manta da na ajiye su, da sa anzo wata lectures ɗin in tuna" Kallonsa take tare da tunanin wai shi a rayuwarsa baya fushi ne, babu wani abu da yake ɓata masa rai, taje ta gama baloƙoƙo a kansa, amma shi abin da ya farun ko a jikinsa.

Juyawa tayi ta nufi department ɗin su Yusra, dan tattaunawa a kan wannan matsalar.
Ta kira Yusra a waya, Yusra ta gaya mata a in da zasu haɗu. Tun da Yusra ta hango Fadila, da yadda ta ɗaure fuska ta san akwai damuwa, Fadila ta ƙarasa ta zauna tana huci.

"Baby me, waye ya taɓa mini ke ya sanya ki fushi haka?"

"Yusra zuciyata na raya mini wani abu, amma ina gudun aikatawa daga baya ace nayi laifi, shiyasa na zo wurinki".

"Subhanallaahi, me zaki aikata?"

"Wani lecture ɗinmu zan saka a kama mini"
Yusra ta zaro ido ta ce "Kina da hankali kuwa?"

"Na taɓa ciwon hauka ne? Malama Wannan Kankiyan zan saka a kama mini" Nan ta labartawa Yusra komai cike da ɓacin rai. Yusra ta jira Fadila ta gama baloƙoƙonta, sannan ta nisa ta ce "Yanzu duk a kan Yazeed ɗin kike wannan tada jijiyar wuyan haka? Karo na farko da naga tsantsar tausayi a fuskarki kodai kodai?x

'Yusra ya kike nema ki mayar da maganata shirme, ko wani abu daban? Ke da kinga Yazeed kin san ba masu hali bane, karatunma Allah kaɗai ya san da yadda yake yinsa, idan aka ɓata masa career saboda ni, an masa adalci kenan? Bafa mahaukaciya bace ni, zanje in aikata abin da ya dace tun da ba zaki bani shawara ba"
Yusra ta ce "Tuba nake, Allah ya baki haƙuri. Shawarata a gareki shi ne kamar yadda Kankiya ya buƙata kawai ki nesanta kanki da Yazid, ke har ki gama makarantar nan, kin da gatan da babu wanda ya isa ya taka ki, Yazeed kuwa fa, ko kuma kije ki kai ƙarar Kankiyan, a miki tsakani da shi" ɗan shiru Fadila tayi, daga bisani ta ɗauki jakarta ta kalli Yusra ta ce "Ni banji wannan shawarwarin naki, sun ratsani ba, zan san abin yi"

Yusra ta riƙo hannun Fadila ta ce "Fadila kar ki je aikata abin da zai janyo muku Matsala"

Fadila ta zame hannunta daga na Yusra ta fice.


Khalil ne zaune a Offi, sai jujjuyawa yake a kan kujera, hannunsa riƙe da waya ya saka a kunnensa, yana jiran Hafsa ta ɗaga.
"Assalamu alaikum" ta faɗa muryarta ƙasa-ƙasa.

"Sweetheart, ko bacci kike na tashe ki?"

"Bakomai, na ɗan koma bacci ne ina kwana?"

"Eyya am sorry, ban san bacci kike ba, na fito Office ne na kiraki in ji lafiyarki"

"Ina lafiya ƙalau, ya aikin?"

"Aiki Alhamdilillah, bari in barki ki huta, anjima mayi waya, koma ki cigaba da baccinki"

"No ai na riga na tashi, gara in tashi in fara shirin kayan sana'ata"

"Hafsa" ya kira sunanta.

"Na'am" ta amsa.

"Bana son fitar da kike titi"

"To idan ban fita ba me zamu ci?"

"Haba Hafsat, ni haryanzu ban gane ba, kin ƙi ki bani dama yadda Yakamata, Wallahi Hafsa dan abin da zaku ci, zuwa abin buƙatar ku ba zai gagara ba"

Hafsa cikin sanyin muryarta ta ce "Ba hakkinka bane, ka bari zuwa lokacin da Allah ya sa ka aureni, ko me kai mini a wannan lokacin ba laifi, amma yanzu..

"Shhhh Hafsat, kina kokwanton ba zan aureki bane? Wallahi ina matuƙar kishinki fiye da yadda kike tunani, zuciyata bata mini daɗi sam ganinki a titi Wallahi".

"Ka raina matsayin da Allah ya ajiyeni ne?"

"A'a subhanallah, ba haka nake nufi ba Sweetheart, da haka ne ai ba zan tunkareki da batun soyayya ba, dan Allah ki bani haɗin kai, ɗaukar ɗawainiyarku ba komai bane, muna da kuɗi sosai, mijinki ya tara muku kuɗi, ki kwantar da hankalinki mu ci guminmu"

Murmushi Hafsa tayi ta ce "Rana ta fara yi, bari in tashi in ɗora girki, ka kula mini da kanka sosai"

"Wayo zaki mini ko?"

"Ba wayo bane"

Khalil yayi murmushi ya ce "A girka dani, in an gama a zo a ciyar da ni a baki, ina kallon kyakywar fuskarki"

"Kayi aikinka My, see you later" ta katse kiran. Khalil ya sumbaci wayar, tare da ƙanƙameta a ƙirjinsa.


Amina tuni ta fara zuwa extra lessons da suke a cikin hutu, ta mayar da hankalinta sosai a kan zuwa makaranta. Duk da yau juma'a bata iso gida ba sai ƙarfe biyar na yamma, ta dawo a gajiye, a falo ta tarar da doctor Aliyu yana gwada BP Alhaji Ahmad.
Saroro ta tsaya tana kallon Alhaji Ahmad, da doctor Aliyu, gefe ga Hajiya Zainab a zaune, tana so tayi magana, amma taga hakan tamkar shishshigi ne, dan tsaf Hajiya Zainab zata iya dizgata, dan haka ta yi musu sallama ta wuce ɗakinta.
Ta isa ɗakinta, ta canza kaya tayi salla, amma ta kasa cin abinci, haka nan taji tana son sanin meyafaru ake masa gwaji.
Ta sake fitowa falon, a wannan karon Hajiya Zainab hankalinta na kan TV, Alhaji Ahmad kuma yana kwance a kan kujera, ya lumshe idanunsa, lokaci lokaci yana ɗan yamutsa fuska.

Amina a ranta ta ce "Wata ƙila bashi da lafiya"
Amina ta je ta nemi Abinci ta ci, ta fito ta tafi wurin Baba, suna nan zaune suna hira ita da Baba, tana son tayi masa maganar Alhaji Ahmad, amma ta fasa ta cigaba da hirarta.
Wani razananne horn da ake yi tamkar yaƙi, ya sanya a gigice suka miƙe ita da Baba, Baba ya nufi gate ɗin, yana kiciniyar buɗewa, amma aka cigaba da horn ɗin.
Baba ya buɗe gate ɗin, Fadila ta kwararo motarta tamkar zata bar doron ƙasa ta tashi sama.
A hasale ta fito, dan kallo ɗaya zaka yi mata ka san a fusace take, ƙiris take jira dama, ta nufo Baba cikin masifa, Amina ta miƙe cike da shirin ko ta kwana, ta shirya mayarwa da Fadila duk wani rashin mutunci da take shirin aiwatarwa.

"Ka kurmance ne bamu sani ba?" Baki a ɗan sake ya girgiza kai ya ce "A'a"

"To wulaƙanci da rainin hankali ne ya sanya zan zo in tsaya ina horn ka ƙyaleni?"

"Amma naga ai ba wani daɗewa ki kayi kina horn ɗin ba, kuma baki ga jikin girma ba, kan ya buɗe gate ɗinma ai sai a hankali".

Cikin tsawa Fadila ta ce "Na saka da ke ne? Jikin tsufa waye ya masa dole ya zauna, ku koma in da kuka fito mana, idan ya san ba zai iya ba sa ya bari amma sai ka ce..

"Fadila kar ki kuskura ki faɗi maganar banza a kan mahaifina, uba talaka da mai kuɗi duk ubane, dan haka kar ki sake ki zagar mini uba a gabana, na gaji"

"Idan na zageshi me zaki yi, baki da abin da zaki ja da ni, ki ka sake kika yi mini wani rawar kai, a yau ba sai gobe ba sai kun bar gidan nan daga ke har shi, shashasha, wawuya 'yar ƙauye kawai"

Jikin Amina har wani rawa yake yi, Bana ya riƙo Amina, yana girgiza mata kai, tare da hanata Magana, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sintiri a kan kuncinta.
Fadila ɓacin ran da Kankiya ya cusa mata ta zo ta sauke a kan Baba Hassan. Fadila na gama saukalen rashin mutuncinta, ta shige cikin gida.

Amina takaicin Baba ya hanata magana, ya sanya ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan, A falo ta tarar da Fadila zaune a kusa da Daddy tana masa sannu.
Amina ce ta shigo fuuu, idanunta jawurr tana kuka. Haka nan hankalin Daddy ya koma kan Amina, da ta wuce idanuwanta jawur, yana tunanin meyafaru da ita take wannan kukan haka?.

"Ke zo nan" ta jiyo muryar Hajiya Zainab. Ran Amina a matuƙar ɓace ta tsaya cak, saboda ji take tamkar ta jiyo, ta zazzagi Hajiya Zainab ita da Fadila.

"Ko ba zaki zo ba ne kina jin ina kiranki"

Amina ta dawo falon ta tsaya, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Hajiya Zainab ba ta damu da kukan da ta ga Amina tana yi ba ta ce "Je ki kira mini Babanki" Amina ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta sauke a kan Amina.

"Ko ba zaki bane ina miki magana saboda salon iskanci kina jina kin yi shiru" Amina ta jiya jiki a sanyaye, ta koma harabar gidan ta samu Baba yana jin radiyo.

"Uwata lafiya kuwa kukan dai kike? Ko wani abun suka sake yi miki?"

"A'a cewa aka yi ka zo"

"Ba dai wani abun kika yi ba ko?"

"Eh, kawai cewa aka yi ka zo" Baba ya miƙe yana faɗin "Muje to Allah ya sa lafiya"

Suka koma falon tare, ta ƙasan ido yake kallon Amina. Amina ta tsaya tana jiran taji me za'ace wa Baba kuma. Alhaji Ahmad tashi yayi ya wuce ɗakinsa, dan baya son hayaniya.

"Gidan Hajiya Turai zaka je, ka karɓo mini saƙo, kaje ka dawo da wuri kar ka barni ina jira" Cewar Hajiya Zainab da take kallonsa a wulaƙance.
Cikin girmamawa Baba ya fice, dan aiwatar da aiken da Hajiya Zainab tayi mata.

Amina tun da ta ƙule ɗaki bata sake fitowa ba, ko Abincin dare ba ta samu ta iya ci ba, saboda yadda ranta yake a ɓace, Amina ta rasa dalilin da yasa Fadila ba ta da abin da yake mata daɗi irin cin mutuncin Baba a kan buɗe ƙofa, Babu wani laifi da Baba yake yi ta ci mutuncin sa sai a kan buɗe gate.
Bayan sallar isha'i, Amina tayi kwanciyarta, ba tare da ta nemawa cikinta abin da zata ci ba, amma ta ɓige da juye-juye bacci ya gagara, har dare ya raba, ga ɓacin rai ga yunwa da ta uzzurawa cikinta.
Ba shiri ta tashi ta nufi falo, dan neman abin da zata zuba a cikinta, ta fara alwala tare da gabatar da salla raka'a biyu, sannan ta kwaso litattafanta ta fito falo, ta yanke shawarar zuwa barandar waje, tayi karatun a can, ta san idan tayi hakan zata iya mantawa da damuwarta ta fuskanci gobenta a kan karatun da ta saka gaba, daga ranar da ta kammala karatun sakandare zata bar gidan nan, dan ji take tamkar kan tabar gidan nan sai ta yiwa Fadila dukan da sai an kaita Asibiti.

Amina tayi nisa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login