Showing 42001 words to 45000 words out of 296192 words
da hira da Abdul.
Fadila kuwa keɓe kanta tayi a makaranta, ta sha karatu sosai da sosai, duk wasu abubuwan sun mata tsaurin da ba ta gama gane su ba, tana buƙatar wanda zai ƙara yi mata bayani. Tana kallon yadda aka haɗa group group, Yazeed yana sake yiwa ɗaliban bayanin abin da ba su gane ba, amma taƙi zuwa gani take idan ta je ta faɗo.
Sai bayan la'asar Sannan ta bari school ta tafi gida, a Falo ta tarar da Khalil da Abdul suna kallon ball suna hira.
Tana ganin Abdul ta wani haɗe rai, Abdul kuwa faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Sannu da Zuwa".
Cikin ko in kula ta amsa, dan ya fidda ran zata amsa ma.
Khalil bai kulata ba ta wuce ɗakinta, sai da ta bar falon sannan ya ce "Dan Allah Abdul ka daina shiga sabgar yarinyar nan tana yarfaka".
"Kawai dai kace in haƙura ba zaka bani ita ba?".
"A'a ni bance ba, amma yarfin da take maka yayi yawa"
"Ba komai a hankali zamu daidaita".
"Ai sai kai tayi"
Sai da aka yi sallar magariba sannan suka bar falon, suka tafi masallaci domin yin salla.
Bayan sun fito daga sallar ne Khalil ya cewa Abdul "Muje ka rakani in nuna maka abin da nake gaya maka, amma mu fara biyawa in gaida Mama"
Abdul ya ce "To muje, Allah ya sa abin kirki zaka nuna mini, ba shiririta ba".
"Ni ne ma nake maka shirirtar?"
"To ai kai ɗin ne wasu lokutan sai a hankali, muje dai in gani"
Haka suka tafi, suna tafe suna faɗa suka isa unguwar su Abdul, suka shiga Khalil ya gaisar da Maman Abdul, kamar yadda yake ɗabi'arta ta karɓi Khalil hannu bibbiyu, tana ta kwarara musu Addu'a da sa musu albarka, saɓanin mahaifiyar Khalil idan ta ga Abdul, ta dinga masa kallon banza kenan tana hura hanci.
Bayan fitowarsu daga gidan su Abdul, Khalil ya ja mota zuwa unguwar su Hafsa, wanda take a gaban ta su Abdul, bai yi parking a ko ina ba sai a wurin suyar awarar Hafsat.
"Wai mai za muyi a nan ne?" Abdul ya tambayi Kahlil yana kallonsa.
"Zo muje zaka gani"
Suka fito daga motar suka tunkari wurin mai awara.
Abdul ya kasa haƙuri ya sake cewa "Wai wurin wa zaka ne?".
Khalil bai bashi amsa ba, sai janyo hannunsa da yayi suka ƙarasa. Hafsa na ganin Khalil ta tsuke fuska, tana ɗauke kai.
Sallama Khalil ya yi, Hafsa ta amsa tamkar an mata dole, suka zauna a bencin da ke wurin, Abdul kuwa sai bin Khalil yake da kallo ransa cike da tambayoyi.
"Barka da warhaka 'yan mata" Khalil ya faɗa yana murmushi.
Wani irin kallo Hafsa ta yi masa, wanda bai gane ko na meye ba, sai dai kawai yaji tsigar jikinsa ta tashi da kallon da tayi masa.
"Ke baki gaishe ni ba, kuma na gaishe ki kin ƙi amsawa".
Hafsa ta ce "Ni gaskiya malam takura mini kake yi, wai me kake nema a wurina ne?".
Khalil ya ce 'Ban taɓa ganin wanda ba ya maraba da coustomer ba sai ke Hafsa" ɗagowa tayi da sauri ba tare da ta yi niyyar magana ba ta ce "Waye ya gaya maka sunana?"
"Ban sani ba" ya bata amsa.
Ɗan ɗage kafaɗa tayi ta cigaba da fifitar wutarta, Abdul dai sai bin su yake da kallo.
"Zuba mana ta dubu ɗaya" yayi Maganar yana kallon zobunan hannunta.
"Ba zan sayar ba, sai dai in baka ta iya canjinka ɗari biyar da ka bar mini"
Khalil ya ce "Ƙadiran ala man yasha'u, wai ke wace irin Yarinya ce haka, Wallahi ba zan karɓi ɗari biyar ɗin nan ba, ki zuba mana ta yadda na ce mu tafi".
Murguɗa baki tayi ta ƙi magana, ta cigaba da sallamar mutane.
"Sauri fa muke, ki sallame mu mu tafi" ya faɗa yana nazartar ta.
"Amma kamar ba ɗaure muku ƙafafuwa na yi ba ko?"
Khalil ya kwantar da murya ya ce "Zuciyata ki ka ɗaure, ba ƙafafuwana ba"
Abdul yayi gyaran murya ya ce "A taimaka a sallame mu ƙanwata, ya damu yana son cin awarar ne, shiyasa na rako shi".
Hafsa ta ce "Ba fa ci yake ba, yana zuwa wurin nan ne kawai dan takurawa rayuwata, bana son yi masa wulƙanci, amma gaskiya yana takura mini, sana'a nake bana son yadda maza suke taruwa a wurin nan, ba yadda zan yi ne, shi kuma sai ya zo ya sani a gaba da surutai".
Abdul ya ce "Kina da gaskiya, amma kiyi haƙuri dan Allah, Yanzu zuba mana sai mu tafi".
Hafsa ta ce "Ba zata kai ta yadda ya ce ba".
"To zuba mana wadda ta samu, sai mu tashi"
Hafsa ta zuba ta ɗari shida, ta kalli Abdul ta ce "Ta ɗari shida ce, akwai ɗari biyar ɗin sa a wurina, ɗarin kuma na bar maka"
Abdul ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ai mun cinye ribar, bari dai in biya"
Hafsa ta ce "A'a ka bar shi Wallahi, ka bashi ta ɗari biyar ɗin sa, wadda na baka kuma, ka ci ko ka bayar, ka yiwa mamana Addu'a Allah ya bata lafiya".
Abdul cikin tausayawa ya ce "Allah sarki, ubangiji Allah ya bawa Mama lafiya, ya sa kaffara ne"
"Ameen na gode" Sai Khalil ya zama hoto, yana mamakin yadda Hafsa, ta ɗan saki jiki ta yiwa Abdul magana, amma shi take nuna yana takura mata.
Suka miƙe zasu tafi, Khalil ya sa hannu a aljijunsa, ya ciro dubu uku, ya ajiye wa Hafsa.
Miƙewa tayi da sauri ta ce "Malam karɓi kuɗinka, ya zan yi da su?"
Khalil ya ce "Yi makama shi da su"
Yayi gaba abinsa, ta kalli Abdul ta ce masa "Dan Allah ungo ka bashi kuɗinsa, ni bana son irin wannan abun, meye haɗina da shi zai dinga yi mini haka?".
Abdul ya ce "Nima fa yanzu kika mini kyauta na karɓa, dan haka ba a mayar da kyauta, ki saiwa Mama lemo da shi ba yawa, sai mun sake dawowa" yayi gaba ya barta baki a sake da kuɗi a hannu.
Har suka fara tafiya, Khalil bai ce komai ba, can Abdul ya numfasa ya ce "Khalil, me kake nufi ne?
Khalil ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shi ne abin da haryanzu ban tabattar ba, a kallon Farko da na yi mata, na shiga wata duniya da na kasa tantance, tausayi ne ko menene"
"Khalil soyayya kenan fa"
"Ba zan musa maka ba Abdallah, abin da nake ji game da ita, yayi yawa ina jin zan iya komai dan in dinga ganinta a kusa da ni, haka kurum nake jin kishin sana'ar nan ta ta, tana zaune kiwa na kallonta".
Abdul ya ce "Tirƙashi, kai Izza ita miskilanci da rashin son raini".
"Ai Abdul baka ga komai ba, yarinyar nan tana da jin kanta, ga ta da ba kowa ba, sai jan aji, kamar zata wahalar da ni, amma na yi mamakin yadda tai maka Magana, ni sai dai ta harareni ta gaya mini baƙar magana"
Abdul ya ɗan murmusa ya ce "To ai kaine mutumina, kai ma izzar ce da kai da faɗan tsiya, mata kuma ba a musu haka, mussaman idan ana son farautar zuciyarsu. Idan har kana son Yarinyar nan ka ajiye taka Izzar, ka bita a yadda ta ke"
"Abdallah wai wace irin izza, bani da wata izza Wallahi".
"Haka dai kake gani, yanzun nan kana mini describing ɗin ta, amma kana cewa gata dai ba kowa ba, meye wannan idan ba izza ba, koma dai menene ai sonta ka ke"
"Au dan na faɗi haka izza ne?"
Abdul ya ce "Khalil kenan, Amma tsakaninka da Allah, son Aure kake mata, ko dai wani abu daban?".
"Haba Abdullahi, ka taɓa ganina da harkar banza ne?"
"Ba haka nake nufi ba, akwai so wanda kake wa mace dan ka aureta, wata kuma burgeka take kana son ka mu'amalance ta kamar ƙanwarka, wata kuma tausayinta ka ke ji kawai"
"Nifa da gaske nake, Aurenta zan yi tayi mini".
Abdul ya ce "Ina muku fatan Alkhairi, Allah ya tabbatar da alkhairi" a ransa kuwa yana jinjina yadda iyayen Khalil zasu amince ya auri mai 'yar talakawa mai suyar awara a bakin hanya.
Fadila shirye shiryen fara exams ya yi nisa, tana ta fama da karatunta, sai dai girman kai ya hana ta koyi abin da ba ta iya ba, a ganinta hakan tamkar ƙasƙanci ne a gareta.
Tana zaune ita kaɗai a seat ɗin baya, ta ƙurawa littafi ido, Yazeed gabansa na faɗuwa ya tunkari in da take a zaune, sallama ya yi mata, ta amsa a ciki ba tare da ta kalleshi ba.
"هل يمكنني الجلوس"
(Can i seat)
Kallonsa ta yi, ta ɗauke kanta, Yazeed ya zauna a kusa da ita, ya kalli littafin hannunta ya ce "Sannu da ƙoƙari".
"Dan Allah malam kar ka zo ka isheni karatu zan yi".
Yazeed ya ce "Nima karatun zan yi ai" ya ciro jottersa ya ce "Ban miki godiya ba, naga kin rubuta mini duk abubuwan da aka yi bana nan, Na gode sosai ubangiji Allah ya ƙara basira. Amma dan Allah ina son ki ɗan yi mini bayani, akwai abin da ban gane ba".
"Baka iya karatu bane da sai na maka bayani ko yaya?".
"Karanta rubutu a rubuce ba shi ne ba, ka gane me ake nufi ko da ba ka iya karantawa ba shi ne mafi mahimmanci".
"Dan Allah ka tashi ka bani wuri".
"Ok, zan tashi amma bari in nuna miki wani abu"
Ya ɗauki littafin gabanta ya kalla sannan ya ce "Ba wannan topic ɗin yakamata ki duba ba, idan har ki ka gane bayanin wannan topic ɗin shikenan, malamin ba zai tsawwala tambayoyi a nan ba". Ya buɗo wani topic ɗin ya ce a "A wannan yakamata ki fi mayar da hankali"
Yamutsa fuska tayi, tare da tura baki kamar zata yi kuka.
Yazeed ya ce "Ya dai?".
"Ni fa na gaji da karatun nan, kaina kamar zai fashe bana gane komai ma"
"Kece kika wahalar da kan ki, ki ke karanta abin da ba shikenan ba, idan Malami yana bayani, ki dinga rubuta abin da kike fahimta a game da darasin, idan kika koma gida sai ki faɗaɗa bincike, sai ki haɗa ki tsinci abin da zaki tsinta ki haɗa, amma idan ki ka ce handout zaki haddace baki fuskanci darasin ba, zaki iya samun idea escape ma a wurin exams. Dan haka idan ana lectures a daina yiwa malamai tsiwa ana korar mutum daga aji, wani abin idan har aka yi baka nan ya riga ya wuceka kenan"
Murguɗa masa baki tayi, jin statement ɗin sa na ƙarshe, tare da cewa "Ina ruwanka da an koreni, bana son sa ido, ban littafina".
"Zan baki littafinki, amma kan in baki duba wannan, sai in ƙara yi miki bayani, zaki ga yafi sauƙi a kan wanda kike yi" kallon rubutun nasa tayi, har da wani larabci a ciki.
"Kaga nifa bana gane larabci" tai maganar tana wani basarwa.
Aikuwa Yazeed kamar an kunna fanfo, ya dinga zuba yana mata bayani tana saurarensa, babban abinda ya sanya shi farinciki, bai wuce saurarensa da take yi ba.
Sai da ya gama, tayi ajiyar zuciya, dan idan ta ce ba ta gane me yayi mata bayani ba tayi ƙarya, dan duk abin nan da ake, haddacewa kawai take ba ganewa ta yi ba.
"Na fahimta, Na gode sosai".
"Never mind ranki ya daɗe, bari inje masallaci"
Ta jinjina masa kai, bayan tafiyarsa, ta ɗau jakarta ita ma tayi waje ta nufi gida.
Khalil an fara yi masa way da ga wurin aiki, a kan lallai ana buƙatar sa, ji yake kamar ya ce Ya fasa komawa, saboda yadda yake jin Hafsa a zuciyarsa, ji yake kamar ba zai iya tafiya ya daɗe bai ganta ba.
Ana gobe zai koma, ya je gidansu Abdul ya yi masa sallama, suka sake tattaunawa a kan yadda Khalil zai ɓullowa Hafsa, suka yi sallama Khalil ya tafi wurinta.
Wannan karon ba Mutane sosai a wurin nata, dan da alama ta kusa tashi ne ma.
Yana yin sallama a wurin, ta haɗe rai tare da amsawa ta ɗauke kai.
"Ina wuni tun da ke baki iya gaisuwa ba".
"To ai nima bance ka gaishe ni ba".
Khalil ya numfasa ya ce "shikenan, ba faɗa na zo muyi ba, sallama na zo muyi zan koma wurin aiki insha Allah".
Hafsa ta ce "To ni ina ruwana da zaka tafi?".
"Amma dai at least ai kya yi mini A dawo lafiya ko?".
Hafsa ta ce "To Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen Hafsat, ya jikin Mamana?"
"Wace maman taka?".
"Mamanmu mana, mamanki ai mamana ce ko abin ba kara ne?".
"Jikin Mama da sauƙi".
Khalil ya ce "Masha Allah, Alhamdilillah, amma sauƙi na bahaushe ko kuma ta warke?"
"Da sauƙi sosai" Hafsa ta bashi amsa a lokacin da hankalinta ya koma kan wata coustomer.
Khalil ya sa hannu ya ɗau wayarta mai madannai, wadda ta sha jiki da yawa, lambarsa ya sa a wayar, ya kira lambarta ta fito a tasa, ya ajiye mata wayar.
Ya yi gyaran murya, wanda ya sanya ta waiwayo. Ya ce "Ko zamu je in duba Maman ne?"
Ta ɗan waro idanunta ta ce "Saboda me? Ince ga wa ya zo dubata?".
"Coustomer ɗinki, mai takura miki, kuma wanda yake fatan ya Aureki. Duk da ban gaya miki dalilin da ya sanya na nace ina ta bibiyarki ba, Hafsa ina sonki ne, kuma Wallahi da gaske nake, ni Aurenki zan yi, ina kishin ganinki a wurin nan kina wannan aikin"
Ai tuni ɗan annurin yau da ya gani a fuskarta, saboda zancen Mama da ya yi, ya gushe daga fuskarta, ta haɗe rai sosai da sosai tayi shiru taƙi magana.
"Hafsa maganata ce ta ɓata miki rai?"
"Dan Allah ka rabu dani, kar ka sake zuwa in da nake, ni ban fito sana'ata dan wani ya tausaya mini ba, ba ruwanka da sana'ata, kuma kar ka sake zuwa wurin nan, idan ba haka ba zan iya dena zuwa ni, in bar maka wurin".
A ɗan rikice Khalil ya ce "Amma Hafsa...
"Malam bana son jin wata magana, ka ƙyaleni" tayi maganar a hasale.
Haka Khalil ya tashi ya baro wurinta, jiki a sanyaye, yana mamakin halayen Hafsa, wace irin Yarinya ce haka, dan ance ana sonki ki birkice ki kama masifa?.
A sanyaye haka ya koma gida, yana tunanin mafita, amma dole ya san abin yi, da zuciyarsa ba zata iya haƙuri da Yarinyar nan ba.
Da ya koma gida, a Falo ya tarar da Mummy, da Fadila suna kallo, suna hira, Amina nata gyara dining, in da suka ci Abinci suka bar wurin.
Fadila na ta bawa Mummy labarin Yazeed, yadda ya iya larabci amma bai iya turanci ba hadda cewa "Mummy kin gan shi kuwa, kayan da yake sakawa? Amma sai ƙwaƙwalwa kuma baya iya turanci a baki".
Mummy ta taɓe baki ta ce "Wasu lokutan dama haka ne, yaran nan marasa galihu da suke tashi a wahala, suna da ƙoƙari, sai dai na banza ne, dan ko sun gama karatun ba aiki suke samu ba, sai da su zama masinja a manyan ofisoshi".
Amina da ke aiki a ranta ta ce "Ji mata da mugun baki, wato ɗan talaka ba zai huta ba, iyayenmu su yi muku bauta, muma muyi muku da 'ya'yanku, insha Allah ta Allah ba taku ba'
"Khalil lafiyarka kuwa, ka zo ka zaun kayi shiru haka?".
"Mummy bakomai".
"Ya fa bakomai? Ga yanayinka duk ya canza".
"Mummy wata Yarinya ce" sai kuma yayi shiru.
"Mai Yarinyar ta yi?" Mummy ta tambaya cike da zaƙuwar son jin ƙarshen zancen.
"Mummy Bakomai" ya faɗa cikin damuwa.
"A'a ka fara magana kace bakomai, ko dai ka fara Soyayya ne?".
"Eh to, Yarinyar ce dai haryanzu ban samu shawo kanta ba".
Mummy tayi murmushi ta ce "Ikon Allah, dama akwai lokacin da zaka samu macen da tayi maka, sarkin kushe kushe? A ina take kuma 'yar waye? Ina fatan ba gidan tsiya zaka je ka ɗauko mana sirika ba?"
Gaban Khalil ne ya faɗi, be bawa Mummy amsa ba ya miƙe, ya ce "Idan komai ya daidaita za muyi maganar".
Fadila kuwa wani takaici ne ya mamayeta, da tausayin Yusra da take ji, gaba ɗaya haushin Khalil ya kamata, ta tashi ta bar falon ita ma.
Haka Khalil ya kwana yana tunanin dalilin da ya sanya, Hafsa ta canza fuska dan kawai ya ce yana sonta, shi dai ya san ba muni ne da shi ba, dan ƙarewa ma mata ne suke rushing a kansa, bai taɓa tunanin Soyayya zata iya kai shi wurin mai awara ba, dan da shi a yadda yake tsara rayuwarsa, macen da ta kammala degree ma yake so, very matured lady, haka yayi bacci rabi da rabi.
Washegari tun sassafe, Fadila da Mummy zasu je unguwa, dan haka suka raka Khalil airport, su kuma suka wuce in da zasu.
Hajara ma shiri tayi, ta tafi kasuwa saboda akwai kayan da babu, mai zuwa kasuwar sayowar kuma Hajiya Zainab ta koreshi.
Amina taje wurin Baba suka sha hira, daga nan ta koma cikin gidan, tana ɗan ƙara dudduba abin da za tayi.
Ta dawo babu daɗewa aka fara bubbuga ƙofar falo. Amina ta je ta buɗe ƙofar falon, wasu mata ta gani su huɗu, sai yara su ku san biyar.
Amina ta ce "Sannunku da zuwa"
Suka amsa mata da yauwa, ta basu wuri suka shiga falo, suka zazzauna.
Ɗaya daga cikin matan ta ce "Ahmad ɗin yana nan ne?" Amina ta ɗan yi jimm, tana tunanin wanene Ahmad.
Matar ta ce "Me gidan"
Amina ta ce "Au, ai ba ya gari bai dawo ba, sai da ki kai magana naga kuna kama, 'yan uwansa ne ku?".
Matar ta yi murmushi ta ce "Eh ƙannensa ne da iyayensa".
Amina ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah sarki, sannunku da zuwa gashi duk ba sa nan, sannunku" nan da nan Amina ta tafi kitchen, ta dinga jido ruwa da lemuka a fridge, tana kawo musu, ta koma ta haɗo musu fruit a ƙaton faranti, ta zo ta zube musu, cikin hanzari ta koma kitchen, ta ɗora girki, ta sake dawowa falo tana musu sannu da zuwa.
Ɗayar ta kalli Amina ta ce "Amma dai ke baƙuwa ce a gidan nan ko?".
Amina ta ce "Eh baƙuwa ce, aiki nake yi ban cika wata biyu bama".
"Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya yi miki Albarka. Mun zo duba wani ɗan uwa ne da aka kwantar a Asibiti, muka ce bari dai mu biyo mu duba Ahmadu, tun da shi ya watsar da mu mu bari muzo".
Amina ta ce "Allah sarki, ai kuwa kun kyauta zumunci ai Akwai daɗi". Nan da nan kamar sun san juna tun tuni, Suka saba da Amina, abinka da wanda ya ce maka ungo.
Ta shirya musu lafiyayyen girki, yaji uban nama, ta kawo ta ajiye musu, aikuwa suka zage, suka ci Abincin nan,