Showing 189001 words to 192000 words out of 296192 words
hankali, ta dinga kuka tana masa ihu, tashi yayi ya kunna fitilar wayarsa ya haskata kawai ya zuba mata ido, idanunta har sun yi Ja, saboda kuka.
"Amina me nayi miki ne kike mini wanan kukan?" Haushi ne yakamata, tambayarta ma yake me yayi mata, saboda tsabar ya raina mata hankali.
"Ni ka tashi ka buɗe mini ƙofa in tafi"
Shi kansa Daddy haushin ne ya kama shi, kawai yayi tsaki yai kwanciyarsa ya ƙyaleta.
Ya ɗauka lamarin Aminan na ƙare ne, amma ya ga she's so much serious about it, bai san lokacin da ta gama koke koken tayi bacci ba. Da Asuba yana fita salla, ta fice daga ɗakin ta koma nata.
Bayan ya dawo daga sallar ne ya nemeta ya rasa.
Bai sake fitowa ba sai da gari yayi haske, ya tarar da ita a falo, idonta duk ya kumbura.
A ransa ya ce 'Yarinyar nan tana da hankali kuwa? Ko haryanzu bata yadda aurenta nayi ba?"
Ya ƙarasa wurin da take ya zauna, ya dinga aikin rarrashi, da ƙyar ta haƙura har taje Quiz ɗin ranar, sai dai ta kasa sakin jiki tayi wani abun arziƙi.
Ta daina kulashi gaba ɗaya ta daina saurarsa, sai ranar da taga likita ya zo har gida ya duba shi, sannan ta koma wurinsa ta bashi Abinci da magani.
Sai dai daga wurin bashi Abincinma, ya kuma riƙeta ta kwana a ɗakinsa, ya maimaita mata abin da ya mata a qan, amma Still Amina ta kuma yi masa kamar yadda tayi masa wancan karon. Aikuwa ta tubure masa a kan lallai ita sai ya mayar da ita gida tun da. Ba zai daina yi mata abin da ba ta so ba.
Daddy ya barwa ransa cewar da Amina zai koma Lagos, ba zata koma Kano ba, saboda shirmenta yayi yawa.
Ya ƙwace mata wayarta, sannan ya sanar mata da cewa da ita zai tafi Lagos, ta dinga kuka wai saboda ya mayar da ita karuwa, bai tare da ita ba amma yana yawo da ita a gari.
"Karuwa ko, zaki ga karuwa ganin idonki, kuma kan ki tare ɗin saina tabattar da kin san kina ɗauke da aurena a kanki, fitsararriya, tashi ki shirya ki rakani unguwa, idan kuma ba haka ba.... Kin san sauran"
Suna tafe a hanya yana waya da Hajiya Zainab, sai da Amina taso tayi abin da zai sa Hajiya Zainab ta san suna tare, saboda kishin tsiya.
Bayan ya gama wayar ya kalleta ya ce "Amma fa baki da kunya, ke ina ruwanki da ni ne? Ina waya da matata kike jin haushi, ke da kike mini ihu, kike cewa ina yawo da ke kamar karuwa, meye na jin haushi dan nayi waya da matata abar ƙaunata, ai ke 'yar aikinta ce kawai dan haka ki daina kishin mijinta"
Fuska duk hawaye ta ce "Ba zan daina ba, ai nima matarka ce"
Dariya yayi ya ce "A'a 'yar aikin matata dai, kuma karuwata. Am missing my zee so much"
Wani dunƙulallen baƙin ciki ne ya tokarewa Amina a ƙirjinta. A fusace ta ce "To daga nan ka tashi ka bita can Saudiya mana, kuma muna komawa gida sai na faɗa mata aure mukayi, komai zai faru ya faru"
"Yarinya kina gayamata ƙauye zaki koma, dan cewa zan yi ban san zancen ba"
Amina ta kumbura fuska tayi fam, kamar zata fashe, dan ƙarin abin takaici ya ɗauko wayarsa yana mata video.
Ajiye wayar yayi ya matsa kusa da ita ya riƙo hannunta ya ce "Karuwar Ahmad"
"Ni ba karuwa ba ce wallahi, matarka ce" ta faɗa cikin tsiwa.
Dariya yayi ya ce "Akwai ki da ƙarfin hali yarinya. Meenalina kin gama mallake zuciyata, ƙiris ya rage miki, kuma sai wasa kike da damar, ina ga so kike na ƙara wani auren ko?"
Kallonsa tayi da sauri ta ce "Wallahi ka ƙara aure ba zan zauna ba"
"Idan ba kya son na ƙara aure, ki daina taurin kai da gardama, ki dinga yin yarda da abin da nake so" shiru tayi ta ƙwace hannunta daga nasa.
Wani katafaren gida suka isa, mai ɗan karen kyau.
Waya Daddy ta ɗauko, ya kara a kunnensa ya ce "Eh gamu mun iso"
Babu daɗewa wani mutum da zai yi sa'an Daddy, ne ya fito yana ganinsu ya faɗaɗa murmushinsa ya ƙarasa "Suka gaisa da Alhaji Ahmad" Amina ta gaishe shi.
Ya amsa cikin fara'a yana faɗin "Sannu amarya ba kya laifi" ta sunkuyar da kai saboda ita kunya ce ma ta kamata.
Suka shiga katafaren falon gidan, suka zauna, suka cigaba da gaisawa.
"Sweetheart, ga Engineer Abubakar Salihu Dutse, abokina ne tare muka yi karatu, yanzu shi ne ƙaramin ministern shiga da fice na ƙasa"
Kasancewar a kusa da shi take zaune, tayi ƙasa da muryarta ta ce "To shi ne zaka ce mini sweetheart a gaban mutane?"
Murmushi Engeener Abubakar yayi, ganin yadda tayi ƙasa da murya tana yiwa Alhaji Ahmad raɗa.
Wata hamshaƙiyar mata ce ta fito, fara tas da ita sai zuba ƙamshi take.
"Manya baƙi, yau a gidan namu?"
Daddy yayi murmushi ya ce "Uwargida sarautar mata"
"Na'am ya gida ya iyali?"
Daddy ya ce "Alhamdilillah" ta ɗan ƙurawa Amina ido sannan ta ce "Wannan ce amaryar ta mu?"
Daddy ya ce "Eh ita ce, na kawota hargida"
Amina ta kalli matar ta ce "Ina wuni?"
Matar ta ƙurawa Amina ido a ranta ya ce 'Lallai watan ƙarshen Zainab ya kama, ya so cin mutuncinta tun da ya auri wannan 'yar yarinyar, bari in yi amfani da wannan damar in ɗora yarinyar nan a hanya ko ba komai na rama abin da Zainb tayi mini ta hanyar wannan yarinyar.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
60
Sai da Amina ta sake gaida matar, sannan matar ta farga ta amsa mata cikin sakin fuska.
Ta kalli Alhaji Ahmad ta ce "Engineer, a ina ka samo wannan 'yar caras ɗin ka aureta?"
Daddy ya kalli Amina yayi murmushi ya ce "Haɗin Allah mana"
Matar ta ce "Ba shakka, Tubarkallah 'yar kyakkyawa da ita, ya sunanki"
"Sunana Amina"
"Masha Allah, bari mu zo mu baku wuri, mu mu wuce daga muyi hira da amarya, Blessing" ta Ware murya tana kiran 'yar aikinta.
Wata matashiyar yarinya ce ta fito, ta kalleta ta ce "Rakata bedroom ɗina" ta mayar da idonta kan Amina ta ce "Amina bita kinji, ina zuwa" Amina ta tashi ta bi blessing, Daddy ya bisu da kallo har suka shige.
"Kai Engeener sai kace za a sace maka ita" Alhaji Abubakar yayi maganar cikin zolaya.
Matarsa Hajiya Maryam tayi murmushi ita ma ta ce "Ashe dai kaima ka lura, wannan ƙauna haka Engineer"
Dariya Daddy yayi ya ce "Hajjaju ni dai gata nan, a ɗan koya mata duk abin da ya sawwaƙa, na san ba a rasa abin gaya mata ba"
Hajiya Maryam ta miƙe ta ce "Kar ka damu, bari in saka a kawo muku Abinci" ta wuce tabi hanyar da su Amina suka bi.
Amina na zaune a kan Carfet ɗin ɗakin, ga ruwa da lemo a gabanta da blessing ta kawo mata.
"A'a Amina ya kika zauna a ƙasa kuma, ga bakin gado nan dan Allah tashi ki zauna"
Amina ta ce "A'a bakomai anty, nan ɗinma yayi"
"A'a tashi maza dan Allah" ta saka Amina ta koma gefen gado ta zauna, ta janyo kujerar gaban mudubi ta zauna a gaban Amina, sannan ta ce "Amina 'yar wani gari ce ke?"
"A kano nake, ƙaramar hukumar Shanono"
"Masha Allah, amma naji kamar maigidan nan ya ce baki tare ba, kuma na ganku tare da shi Engineer"
"Eh, na zo competition ne, shi ne ya zo shima"
Cikin salo na wanda suka kwana biyu a duniya, Hajiya Maryam ta ce "ok a kina gidanku kenan a zaune?"
"A'a, a gidansa nake, aiki nake a gidan ina karatu, mukayi aure sai na gama ya ce zan tare"
A ranta ta ce "Kan uba, wato idan ka ɗauki kanka a wani, idan Allah ya tashi nuna maka kai ba kowa bane, sai an tausaya maka, duk jiji da kai da izzar Hajiya Zainab ashe 'yar aikinta maigidan ya aura bata sani ba, duk bala'in nata da shegen bin diddigin amma bata iya ganewa ba, lallai watan girbar abin da ta shuka ne ya tsaya, a halin yanzu sai abin da ta gani"
Hajiya Maryam ta ce "Masha Allah, a nan ɗin tare kuke a wuri ɗaya da shi kenan"
Amina ta ce "Eh"
"Ahhh to ai ni yanzu kin zama ƙawata, hira zamuyi sosai" Amina ta ɗan waro ido tana kallon Hajiya Maryam, saboda ta san Hajiya Maryam ɗin ta haifeta.
"Ya kika zaro ido ne? Matar abokin mijinki ce ni fa, ai shikenan mun zama ƙawaye, hira za muyi irin ta manya, ki daina wani sinne kai ni ba kunyarki zan ji ba"
Amina dai ta sunkuyar da kai, tana wasa da hannun jakarta.
"Kinga Amina kalleni nan" Amina ta ɗan ɗaga kai ta kalleta.
"Ba wai ina son in ɓata zamanki a gidan aurenki ke da abokiyar zamanki bane ba, a'a ina son na ankarar da ke damar da Allah ya baki ne. Ai kin yi aiki a ƙarƙashin ta, kin san halinta na ƙwarewa a cin mutunci da wulaƙanta ɗan Adam ko bata yi miki?"
Amina ta ce "Tana yi mini"
"Yauwa, ki sa ranki Allah ne ya baki dama ki rama, ba wai ina nufin kiyi fito na fito da ita ba no, ki ƙwace abin da kuka haɗu ku kayi tarayya a kai, wato mijinku.
Kin ga Mijina abokin mijinki ne, tare suka taso, 'yan gari ɗaya ne, sai dai mijinki gidansu suna da wadata nawa mijin kuma talakawa ne, Engineer Ahmad ya bamu gudunmawa sosai a rayuwa, tun kan yayi aure lokacin mu munyi aure, na kusa haihuwa amma mijina ba shi da kuɗin sayan kayan jarirai, hatta hakikar da aka yankawa 'yata ta fari Engineer ne yayi, mutum ne managarci mai halaye na gari.
Tun da ya auri Hajiya Zainab, ya fara tara abin duniya ta sauya shi, baya jin maganar kowa sai tata, gashi azabtar da shi take yi, amma baya iya saurara kowa sai ita, ta raba shi da kowa nasa daga ita sai yaranta da ƙawayenta.
Da tana hulɗa da ni, tunda duk garinmu ɗaya, muka haɗu a wani biki, take nunawa ƙawayenta ni, wai ni matar yaron mijinta ce, bamu da komai sai mijinta yayi mana.
Ban ɗau abin serious ba, duk da naji haushi, ta haifi Fadila naje mata barka, ƙiri ƙiri ta nuna ba zata iya cigaba da hulɗa da ni ba a gaban mutane, rigar da na saya na kai mata mace a sakawa jaririya, ta ce Allah ya kiyaye ta saawa 'yarta wannan rigar, wannan riga ai sai dai irin 'ya'yana a gaban mutane, ina zan manta wannan?"
Amina ta jinjina kai tare da jinjinawa rashin mutunci irin na Hajiya Zainab ta ce "Gaskiya ba zaki manta ba"
"Ke dai bari, da nayi haƙur9 gashi komai ya wuce, ko da mijina bai kai nata kuɗi ba, kuma shi ɗin dai shi ne silar samun mijina wannan matsayin gani a cikin rufin Asiri da take ganin har abada ba zan samu ba.
Shiyasa nake gaya miki, dama ce Allah ya baki, kuma jihadi zaki yi, danginsa mutane masu matuƙar son nasu, ga zumunci, amma sai da ta shiga ta fita ta sanya ya zamana babu wanda yake iya raɓar gidansa, idan kuwa kaje ƙarshe ka fito da ɓacin rai.
Dan haka yanzu abin da nake so da ke, tun da har Allah ya sanya kuna tare ke da shi, ki yi ƙoƙari kiyi amfani da wannan damar, wajen shawo kansa ki nusar da shi illar watsi da zumunci, sannan ki nusar da shi illar abin da ya ke yi, amma ki sani hakn ba zai samu ba sai kin mallake shi a hannunki kamar yadda tayi a baya, amma ke kibi hanyar da ta dace wurin mallakar ta sa, wato biyayya da kuma Addu'a.
Na san Engineer farin sani, mutum ne shi mai haƙuri, haƙuri na gaske makuwa, ga sauƙin kai da son mutane, kinga tun da Allah ya sanya duk cikin matan da ke kai kawo a kamfaninsa da manyan matan da ke Kano, Lagos da Abuja da sauran garuruwan da yake zuwa, babu wadda ya gani tayi masa ya aura sai kez to ki tabattar da ba ƙaramin so yake miki ba, dan haka biyayya duk abin da yake so bi shi ki fi shi son abun, in dai bai saɓa wa Addini da al'ada ba, ko kuma ki ga akwai cutarwa a ciki ba, zai zama naki ki jiya abinki yadda kike so"
Amina ta ɗan kalli Hajiya Maryam, da mamakin maganarta ta ƙarshe, ta yaya zata juya Daddy wai yadda take so.
Hajiya Maryam ta ce "Eh mana, ke ba kya karanta litatafan hausa ne?"
Amina ta ce "Da ina yi, amma ya ƙwace mini waya"
"Me ki ka yi ya ƙwace wayar?"
Cikin wauta Amina ta ce "Faɗa muka yi"
"Au kika zauna ku kayi faɗa har ya ƙwace miki waya, baki yi masa kissa kin karɓo ba? Ke baki karanta littafin Wata kissar sai mata ba ne? Baki ga yadda jarumar littafin ta yiwa mijinta ba"
Amina ta ce "Ban karanta ba"
"Karɓo wayarsa a tura miki, bari a kawo miki Abinci ki ci, ke dole mu yi zama na musamman da ke, akwai karatukan da yakamata nayi miki, karɓo wayar ta sa".
Amina ta tashi ta koma falon, ta tarar da Daddy sun sakankance suna ta hira shi da Alhaji Abubakar.
Yana ganinta ya mayar da hankalinsa kanta, taje ta zauna a kusa da shi, ya kalleta ya ce "Ya dai in zo ne?"
"A'a waya zaka bani aro"
"Nawa zaki biya?"
Murmushi tayi ta ce "Yi mata kuɗi"
Shima murmushin yayi, ya ajiye mata wayoyinsa uku, ya ce "Wacce zan ara mikin?"
Ta saka hannu ta ɗau guda ɗaya, ta tashi ta koma.
Alhaji Abubakar ya ce "Kai malam, gaskiya yarinyar nan tayi gaba da zuciyarka da yawa"
"Bari kawai nake gaya maka, har mamakin kaina nake yi, Yarinyar ce akwai shiga rai sosai"
Hajiya Maryam ta saka Amina a gaba, ta dinga koya mata abubuwa, da bata shawarwari, ta saka aka kawo mata Abinci.
Tun la'asar suka je gidan, amma sai gasu har bayan goma na dare, suna gidan, Amina ta ƙaru da Hajiya Maryam sosai da sosai, ta rubuta mata lambar wayarta ta ce idan ta samu lokaci ta kirata a waya zasu dinga tattaunawa.
Sannan ta buɗe jakar Amina ta saka mata wata leda a ciki ta ce "Gashi nan, wannan kyauta ce tsakanina da ke, kar ma ki bari ya san wannan, kayan gyara aure ne, waɗan nan na ledar kuma bakomai idan kin bari ya sani"
Amina ta ce "Nagode sosai Anty, Allah ya saka da alheri ya sa ki fi haka"
"Bakomai Amina, Allah ya baku zaman lafiya ya sanya tsohuwar gida ce, Allah ya sa ki riƙe mana shi amana kamar yadda muke tsammani daga gareki, dan Allah kiyi amfani da maganganun da muka yi da ke"
"To in sha Allah Anty, na gode"
"Bakomai kar ki damu, duk abin da ya shige miki duhu, ki kirani ki tambayeni"
Ta rako Amina har falo, suka fita tare da su Daddy, har harabar gidan Joseph ya fito da motarsu.
Daddy ya ce "Hajajju a bani matata haka mu tafi"
Hajiya Maryam ta ce "Ni zuwan nan yayi mini kaɗan, zan zo ma dai da kaina kan ku tafi Lagos ɗin, ban gama da ita ba"
"To yanzu dai ban kayata mu tafi, kar ta fara mura wannan gidan naku mai sanyi"
Hajiya Maryam ta ce "Lallai mutumin nan ka samu kanka wallahi, sai na gaya wa Uwargida"
"Sai kin dawo".
Daddy ya ce "Meenalina, ki yiwa abokina godiya, ya saka miki dubu ɗari a account, ya ce kya sai turare"
Amina ta ce "Kai har dubu ɗari kuma, ai dubu ɗari tayi yawa a sai turare"
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya, Hajiya Maryam ta ce "kar ki damu, ku gaida gida kar kiyi mura ace a gidana kika kwasa"
Amina dai ta yi masa godiya, sannan Daddy ya buɗe mata mota ta shiga, shima ya zagaya ya shiga, suna ɗaga musu hannu suka tafi.
Suna tafe a hanya ta kashingiɗa da jikin Daddy, kasancewar ta san password ɗin wayarsa, ta buɗe wayar ta fara karanta littafin Wata kissar sai mata.
Koda suka isa gida, ta san ba wani abu zata yiwa Daddy ba, ta nemi wuri ta cigaba da karatun littafinta.
"Wai ke ba zaki kula dani ba kin saka waya a gaba?"
"Daddy kamar wani Baby, me zan maka naga a ƙoshe kake fa"
Miƙa mata hannu yayi ya ce "To Bani wayata, tun da ta fini muhimmanci"
Ɓoye wayar tayi a bayanta tana tura baki.
Ɗagata yayi cak zai karɓe wayar, ta hau ɓoyeta, cakulkuli yayi mata, ba shiri ta saki wayar tana dariya.
Ya ɗau wayar yana cewa "Me kike a wayar ne?"
"Wani littafi fa aka tura mini nake karantawa, dan Allah ka bani"
Yayi murmushi ya miƙa mata wayar ya ce "Shikenan, idan kin gama kije ki kwanta, ni bacci nake ji"
Ta ce "Shikenan, goodnight"
"Yau ba zaki tayani kwana ba?"
Ta noƙe masa kafaɗa, ya ce "Ai shikenan, have a sweet dream, i love you" yayi maganar yana kissing ɗin goshinta, Amina har cikin ranta take jin daɗi idan ya ce yana sonta, amma ita ba ta iya gaya masa. Ya tafi ɗakinsa yaje ya kwanta.
Amina ta gyara kwanciyarta a kan kujera, ta cigaba da karatun littafin nan.
Sai da kammala tayi wata irin ajiyar zuciya, ta duba agogo ƙarfe ɗaya na dare, ta tashi ta tafi ɗakinta, tayi alwala tayi nafilfili, ta karanta Alqur'ani tare da yin Adduoi, ta nufi ka gadonta.
Abin da ta karanta a cikin littafin da maganganun Anty Maryam take ta jujjuya a ranta.
A fili ta furta lallai Mufeeda jaruma ce, kuma tayi rawar gani, wayyo Allah ina ma zan iya yiwa Daddy abin da Mufeeda take yi. Ni da Daddyna ma mai sauƙin kai ne, ba kamar mijin Mufeeda ba, kuma fa shekarunumu ɗaya da ita, kai to ya aka yi ita bata jin kunyar mijinta, kai wallahi kunya nake ji, amma kuma ai Anty Maryam ta ce idan ina son na mallakeshi sai na dinga yi masa biyayya. Idan fa ina yi masa kalaman soyayya zai ji daɗi, wayyo Allah ta ina zan fara kunya nake ji wallahi. Amma in sha Allah zan yi ta ƙoƙari in ga ya aurawa Khalil yarinyar da aka je aka ciwa mutunci,ai sai na rama wulaƙancin da aka yi mana ni da Baba" haka tayi ta saƙe saƙenta, har tayi bacci.
Cikin baccin ta ji an ɗagata zaune, "Dama na sani, ba lallai kin yi bacci da wuri ba, har