Showing 114001 words to 117000 words out of 296192 words

Chapter 39 - GABA DA GABANTA

sallar isha'i"

Amina ta marairaice ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, ban san me zan gaya wa Baba ba".

"To matso mu ci Abinci"

"Wallahi Daddy ban taɓa cin Abinci da wani a kwano ɗaya ba, ba zan iya ba" ta faɗa a rikice.

"Aminatu kenan, wasa nake miki, wannan rikicewar taki ce ke sani dariya. Amaryar Jarmai"

"Dan Allah Daddy a ina ka san Jarmai"

"Ina ruwanki? Juya ki daina kallona kar in ƙware" ta juya masa baya, ta daina kallonsa kamar yadda ya buƙata.

Tana juya baya ya dinga mata dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya ya rikita ta lokaci guda.

" 'yar Daddy" ya kirata.

Ta waiwayo ta ce "Na'am"

"Abinci yayi daɗi, Daddy ya gode sosai, zo ki ci naki"

"Daddy na ƙoshi, gida nake so na tafi"

"Sai kin ci Abinci zamu tafi, tafiyarku Abuja saura 2weeks, dan haka kan nu tafi zaki je garinku"

"Me zan yi a ƙauyen? Tsoro nake ji kar ina zuwa su Baffa Lawan su riƙeni suce saina Auri Jarmai"

"Idan har ina raye, ba wanda ya isa aura miki wanda ba kya so, zaki je ne dan ki musu sallama, kinga zaki tafiya mai nisa ne, zan saka Zakiru ya kai ki ki musu kwana biyu a dawo mini da ke"

"To kun yi maganar da Baba ne ya yadda da tafiyar?"

"Ba ruwanki da wannan, nace ki bar wannan maganar a hannuna ai"

Amina tayi murmushi ta ce "To Daddy, na gode Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ameen Meenalin Daddy, nima na gode sosai kina kula dani da lafiyata, duk da ƙalubalen da kike fuskanta a gidana, ki cigaba da haƙuri watarana sai labari kin ji"

"To Daddy"

"Yau, ci Abinci sai mu tafi gida, zanje in yi sallar la'asar, kwanukan kuma da komai ki bari za a gyara"

Ta jinjina masa kai, shi kuma ya miƙe ya bar ɗakin.

Ta zuba Abinci ta ci, ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, dama tana fashin salla, dan haka ta zauna zaman jiran dawowar Daddy.

Alhaji Ahmad na shigowa, Amina ta tashi tsaye, tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta.

Daddy ya kalli fuskarta, ya ce "ya na ganki a tsayem"

"Ba tafiya zamu yi ba?"

"Ban gama abin da nake ba" ya faɗa yana kallon agogon hannunsa.

Amina ta kwaɓe fuska ta ce "Haba Daddy, lokaci ya ƙure fa, huɗu fa" kallon yadda take maganar tsakani da Allah yake, wanda gaba ɗaya shagwaɓa take yi.

"Let me see your bag" yayi maganar yana miƙa hannunsa.

Fuskarta babu daɗi, ta miƙa masa jakarta.

Ya karɓi jakar ya nufi wani ɗakin.

Kwaɓe fuska Amina tayi, ta samu wuri ta zauna, gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci, so take ta tafi gida duk ta gaji, kawai ta ji wata irin ƙwalla ta taru a idonta.

Bai wani jima ba ya fito hannunsa ɗauke da jakar, ya nufo im in da take a zaune ta takure tana zumɓura baki.

" 'yar Daddy, kin gaji ko?"

Ta ɗaga masa kai.

"To tashi mu tafi, am sorry" ya faɗa cikin sigar rarrashi.

Ta tashi tsaye, ta ce "To Bani jakar"

"A'a bari in riƙe miki muje"

Amina ta ɗan kalleshi ta ce "A'a Daddy ai bai kamata ba"

Daddy ya yi gaba yana faɗin "To me is normal"

Amina ba ta da zaɓi sai na bin bayan Daddy.

Bayan fitowarsu ma'aikatan gidan suka nufo su suna masa barka da fitowa.
Gaba ɗaya sai ya sauya ya koma Alhaji Ahmad ɗinsa, kamar ba shi ne wanda ya gama zolayarta a ciki ba da suna su biyu.

Ya kalli wani daga cikin ma'aikatan ya ce "A shiga a gyara kitchen da sauran abin da aka yi amfani da shi"

"Ok sir"

Alhaji Ahmad ya buɗe motar, ya saka jakar Amina a ciki, Sannan ya kalleta ya ce "Bismillah"

Amina ta shiga ya rufe ƙofar, sannan ya zaga ya shiga motar shima.

Amina ta jingina da jikin kujera ta ce "Washhh Allah"

"Sorry kin gaji ko?"

Jinjina masa kai kawai tayi, tana sake lumshe ido.

"Daddy" ta kira sunansa.

"Meenalin Daddy" ya amsa yana tuƙinsa cikin nutsuwa.

"Meyasa ka bawa Baba kuɗi ya dinga bani, yana zargin ni na roƙeka fa"

"Ai na gaya masa baki roƙeni ba, ni nayi niyya kawai na bayar nace ya dinga ƙara miki in zaki makaranta, bana son na baki ni da ke, na san ba zaki karɓa ba, kuma bana son wani zargi ya shiga, shi ya sanya na bashi, kuma ai ba kuɗi me mai yawa ba"

"Amma meyasa ba ka bawa Hajara sai ni?" Tayi masa tambayar a bazata.

Kallon Amina ya yi ya kawar da kai bai yi magana ba.

"Daddy ka amsa mana"

"Bana son yawan tambaya fa, matsayin Amina daban a wurina, ita ma matsayinta daban"

Amina ta ce "To meye banbancin matsayin namu ne? Naga duk masu aiki ne a gidanka"

"Ki ƙyaleni" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.

"Dan Allah Daddy"

"Kin raina ni ko? Ni kike titsiyewa hakam"

Da sauri ta ce "A'a"

"Baki san da wa kike tare ba ko? To idan nace bana son abu, bana so"

"To Allah ya baka haƙuri Daddy, ba zan sake ba in sha Allah"

"Good girl"

Ga mamakin Amina, Yau Daddy bai ajiye ta a ƙofa ba, sai da yaje bakin gate ya fara horn.

"Daddy bari in sauka mana" ta faɗa tana ɗaukar jakarta da taji ta ƙara nauyi"

"A'a sai mun shiga nayi parking" yayi maganar yana horn.

A ɗan rikice ta ce "Daddy kar Baba ya ganni, ko Hajiya fa".

"Ki tanadi abin gaya musu" maganar ta sa tayi daidai da buɗe gate da Zakiru yayi maimakon Baba ya buɗe.

Gaba ɗaya Amina ta rikice, sai dai ba taga Baba a harabar gidan ba, Alla Alla take yayi parking, ta fito kan wani a gidan ya ganta.

Bayan Daddy yayi parking, cikin hanzari Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma taji a rufe.

Tana waiwayowa ta kalli Daddy, taga ya kashe motar yana dariya.

"Daddy dan Allah ka buɗe, kar Hajiya ta ganmu"

"Kamar kin san idan ta ganki  kece a ciki, ni ba ruwana"

"To ka buɗe mini dan Allah"

"To ka buɗe mini dan Allah" ya kwaikwayi muryarta da tuni ta samu rauni, kamar tayi kuka.

Murmushi ya cigaba da yi yana kallonta, sai da yaga idanunta sun ciko da hawaye, sannan ya cire motar daga lock.

Da sauri ta fita daga motar, tana ɗan leƙa wurin zaman Baba, ko zata hango shi a wurin.

Daddy ya rufe motar ya ce "Ki nutsu, Baba baya nan wadda kike tsoron ma haka, ko kin manta muna tare ta mini waya?".

Ajiyar zuciya tayi ta ce "Na manta ne, ina tsoron ta mayar da ni ƙauye in rasa karatuna, dan da na yi laifi sai a fara cewa za'a mayar da ni ƙauye".

"Allah ya sa ta jiki, zaki yi mata bayani dalla-dalla"

"Allah  yasa na sauka daga motarka, balle in faɗi wani abu ka saukeni a hanya, da wani abu zan faɗa"

"Aminatu kin raina Daddy fa"

"A'a ban raina Daddy ba, Daddy yana da kirki ne sosai, ba kamar..." Sai kuma tayi shiru.

"Ba kamar wa ba? So kike muyi faɗa ko?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Hajara ce tayi turus a falo ganin Amina da Alhaji Ahmad tare, da alama tare suka shigo.

"Idan ba kya son muyi faɗa, to ki kiyaye abin da zan yi fushi"

"To na daina"

Ya jinjina kai ya ce "Go and have rest, see you later"

Baban abin da ya bawa Hajara mamaki shi ne, yadda ganinta bai sa sun farga sun daina hirar da suke ba, cike da wani yanayi da ta kasa fassarawa.

Daddy ya nufi hanyar sashinsa, Hajara ta risuna tana "Barka da zuwa" ɗaga mata hannu kawai ya yi, fuskarsa a haɗe, kamar ba shi ne ya gama ƙarewa Amina kallo yana murmushi ba.

Waiwayowa tayi ta kalli inda Amina take, Amina ta kalleta sama da ƙasa, ta nufi na su sashin, sai kuma ta tsaya ta kalli Hajara ta ce "Kiji ki ƙi ji, ki gani kuma ƙi gani, idan ki ka matsa kuma hmmm" sai tayi murmushi kawai ta wuce Hajara, ta barta a tsaye sororo tana kallon Amina.




AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD ayshercool 7724

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid026t2vzuetnW2Fw4oD3AtFx8ssrmVz8MvDoQw62FEKNmt4Mc6YNC9ccxnCrk7CoCSNl&id=100089289690624

_Assalamu alaikum 'yan'uwa masu albarka_

_Muna roƙon arziƙi ku shiga wannan link ɗin ku yi mana sharhi kan labarin idan kun karanta, ku danna like sannan ku yi share ɗin shi, Allah Ya saka muku da alheri Ya ba ku tukuici da gidan Aljanna maɗaukakiya._

_SANARWA DAGA: GAMAYYAR MARUBUTAN JIHAR KANO (GAMJIK)_

*Dan Allah masu nema daga farko, ko wasu pages ɗin, su duba Watpad ayshercool7724 ko Arewabooks ayshercool7724, zaku samu daga farkon, aikin babu sauƙi, in yi typing, nayi share kuma ace na bayar daga farko*


40

Saroro baki buɗe, Hajara tabi Amina da kallon mamaki, gaba ɗaya gani take kamar ba Aminan da ta sani ba ce, wani ɓoyayyen abu take gani a kan fuskar Amina mai kama da ƙudurin da zata iya jurewa kowace irin barazana. Banda haka, ta yaya zata shigo falon matar gida tare da maigidan cikin wani yanayi da haryanzu ta rasa muhallin da zata saka shi.
Soyayya ce kenan? Ta tambayi kanta.
'a'a ba zai taɓa yiwuwa ba, mutumin da yake aiki a wani gari daban gari mai cike da goggagun mata masu ji da kansu, mai ɗumbin dukiya mai tarin yawa, ta yaya zai ɓige da son 'yar cikinsa, 'yar cikin nasa kuma mai aiki 'yar ƙauye?.

Sukuku haka Hajara ta bi hanyar da Amina tabi, tana tunanin yadda zata samo zaren labarin, ta gane a wani ma'auni zata ajiye alaƙar Amina da Alhaji Ahmad.

Cike da tsananin gulma da take cin Hajara, ta bi Amina ɗakinta, ta tarar da Amina ta cire uniform ta ɗaura towel zata shiga wanka.

Hajara ta kalli Amina tana ƙaƙalo murmushi ta ce "Wai nikam Amina, ban gane me kike ce mini ɗazu ba, naji kamar wata karin magana ki ka yi"

Amina tayi murmushi ta ce "Idan baki gane ba, ki barshi a haka kawai"

"Ba zaki mini bayani ba kenan, yau naga kin daɗe a makarantar"

"Eh, ai kin san muna zama yin lesson, shi ya sanya"

Hajara ta ce "Haka ne, tare kuka dawo da shi Alhajin kenan?"

"Eh Hajara, tare muka dawo, yaje ya ɗauko ni daga makaranta ne, shikenan? Ina son zan shiga wanka"

"To bari in baki wuri, Lallai Amina kin shigo gidan nan da ƙafar dama"

Amina bata kuma saurarrta ba, ta shige banɗaki ta bar Hajara.

Hajara ta riƙe haɓa tana sake jinjina kai, ga labari amma babu bakin bayarwa, dan ta san ko giyar karnuka ta sha, ba ta isa ta tunkari Hajiya Zainab da wata magana makamanciyar Wannan ba, dan ta san kome zai faru tare da ita zata kwaɓewa, to ta isa ma tayi wani yinƙuri na furta wani mummunan abu a kan maigida meye hujjarta?'

A fili ta ce "Allah ma ya ƙara, ni tsorona Allah ya sa ba lalubeta yake yi ba, ita matar gida tana can gantali kamar 'yar akuya kullum tana tafe kamar iska"

Ɓangaren Hafsa kuwa, ta rame tayi duhu, gaba ɗaya ta daina walwala, waccan rayuwar tata ta baya ta sake dawo mata sabuwa fil, cike da sabon salo mai ɗauke da ciwo irin na soyayya.
Tun daga koke koken nan da tayi, take fama da ciwon kai, tayi ta ƙoƙarin kawar da tunani da damuwa da Khalil, amma abu ya gagara tun tana ɓoyewa kar Mama ta gane, har abu ya zo ya zarce mata da zaɓi mai zafin gaske.
A hakan Mama ta gane, saboda ganin yawan kwanciyar da Hafsa take yi, ga rashin cin Abinci.

Cikin dare Mama ta tashi, domin yin sallar dare, ama ta dinga jin sheshsheƙar kukan Hafsa, ta miƙa hannu zata yaye abin rufar Hafsa, amma taji jikinta zafi rau.

"Hafsa meye haka? Meke damunki ne?"

"Mama bakomai"

"Kamar yaya babu komai, ji yadda jikinki yayi zafi, Hafsa kin ɗora kanki damuwa kina nema ki hallaka kanki, Hafsa ƙaddara ba zata samu bawa yayi tawakkali ba?"

Hafsa ta ja jikinta da ƙyar ta zauna, ta ce "Mama ba laifina bane ba, kawai rashin lafiya nake yi"

"Haba Hafsa, nifa na haifeki ba ke kika haifeni ba, na sani kin shaƙu da Khalil haryanzu kina son sa, amma ki cigaba da Addua, Allah ya kawo miki mafita, bana jin daɗin ganinki a wannan yanayin ko Abincin kirki ba kya ci, kuma ni baki gaya mini baki da lafiya ba" Hafsa dai tayi shiru, ba tace komai ba.

"Tashi ki lallaɓa kiyo alwala, ki zo ko raka'a biyu kiyi, kiyi Addua Allah ya bamu mafita gaba ɗaya, ina da guntuwar gasara sai in dama miki kunu ki sha, sai in baki paracetamol"

Cikin yanayi na jin jiki Hafsa ta ce "A'a Mama, dare yayi sosai, bari in sallar kawai"

"A'a ba komai, bari in dama miki, yunƙura ki tashi"

Hafsa ta yunƙura za ta tashi, ama jiri ya kwasheta ta koma luuuuu zata faɗi.
Duk da Mama bata da cikakkiyar lafiya, haka ta yunƙura ta rungumo Hafsa, suka kusa faɗuwa.

Cike da damuwa Mama ta ce "Hafsa har jikin naki ya kai haka?"

"A'a Mama, jiri ne kawai ya ɗan ɗebe ni"

Mama ta kama Hafsa ta zauna, sannan ta ce "Kinga zauna, bari in je in dama miki kunun, in baki maganin, zuwa in Allah ya kaimu sai mu tafi Asibiti".

Hafsa ba ta ce komai ba, sai lumshe idanunta da ta yi, tana sake jin jikinta babu daɗi.

Bayan sallar isha'i Amina tana ƙoƙarin buɗe jakarta ta ciro litattafanta, ta ci karo da tarin kayan ciye-ciye na biscuit da chocolate, da wani turare da kwalinsa kawai abin kallo ne, jan kwali ne kwalbar turaren ma ja ce, mai matuƙar ɗaukar hankali.
Ta fesa turaren a hannunta ta sansana, wani irin sassanyan ƙamshi ne da turaren mai kwantar da hankali. Ko ba a gaya mata ba ta san turare ne mai tsada sosai.
Murmushi Amina ta yi, tana sake jujjuya turaren da kallon tarkacen kayan ciye-ciyen.
Wani murmushi Amina tayi, wanda ita kaɗai ta barwa kanta sanin ma'anar murmushin.

Fadila kuwa a ɗakinta ta ci Abinci ita kaɗai, tayi wanka tana saka kayan bacci tana shafa mai, ta kalli turarukan wurin Yazid, ta zuba musu ido tana kallonsu tamkar Yazid ɗin take gani a wurin, tunani ta shiga yi a kan barkwancinsa, da yadda yake ta nuna mata kulawa daga fara shirin su zuwa yanzu, mutum ne mai haƙurin gaske da kawaici, ta tuno yanayin da ya shiga a lokacin da ta gaya masa tafi ƙarfin sa, har aka tashi jikinsa babu wani kuzari. Guntun tsaki tayi a fili tana tunanin sai me dan tayi masa warning a kan ya fita daga harkarta, ai ya san ruwa ba sa'an kwando bane, kuma kamar yadda Yusra ta gaya mata, sanyin halin Yazid da kyautatawarsa zata iya sawa ta fara son shi ba tare da shirya hakan ba, gara ma tun wuri ta raba gari da shi.

Wayarta ce ta kawo haske, ta kalli in da wayar take taga message ne ya shigo, ta ɗaga wayar ta duba sai taga missed calls biyar, duk na Kankiya saboda wayar na silent bata san ya kira ba.  Ta duba saƙon ta ga roƙonta yake  wai yana son ta bashi dama ya zo gidansu.
Dire wayar tai tana harar wayar tamkar ita ta turo mata saƙon, "Zan ɗau mataki a kanka, idan ya so ka yiwa Yazid ɗin abin da ka ga dama ku ta shafa" tayi maganar tana ƙoƙarin kauda wani abu mai kama da tausayi a ranta game da Yazid.

Mummy ce ta faɗo ɗakin Fadila babu ko sallama fuskarta cike da damuwa.
Fadila ta kalleta ta ce "Mummy ya dai?"

"Kin yi waya da Khalil ne?"

"Mummy wane Khalil kuma, wayar me zan yi da shi bayan yana gidan nan"

Mummy ta ce "Khalil baya gidan nan, sai yanzu na farga, tun safe banga gilmawarasa ba, na duba babu motarsa, naje in tambayi wancan shashashan tsohon when last Khalil ya fita, amma na tarar baya nan, sai direban babanku ne ke buɗe gate ɗina, wai ya nemi iznin babnku ya tafi ƙauye, shi kuma bai san lokacin da Khalil ɗin ya bar gidan nan ba"

Fadila cikin mamaki ta ce "Ikon Allah, to Mummy ki kira wayarsa mana"

"Na kira taƙi shiga sam, gaba ɗaya hankalina ya ɗaga"

"Ko ya koma wurin aiki ne?" Fadila ta sake tambaya.

"To wa ya sani ne? Kuma sai ya koma wurin aiki bai mini sallama ba, yaya hakan zai yiwu, kar inje a sace mini ɗa a banza, sai sa na gaya wa babanku, ya samar muku da security, yawonmu haka a gari is not safe, duba sa matsayin da ya riƙe a ƙasar nan, amma ya ce mini no need, ai ga irnta nan"

Fadila ta ɗanyi shiru sannan ta ce "Mummy, bana tunanin sace Yaya Khalil aka yi, wataƙila ya tafi wani wurin ne dan huce haushin abinda kika yi wa yarinyar da yake so"

Cikin mamaki Hajiya Zainab ta ce "Kuma haka ne ko? Yanzu sai Khalil ya bar gidan nan ya tafi wani wurin ba tare da na sani ba saboda haka? Aikuwa idan haka ne da ya ci ubansa, sai na nuna masa nice uwarsa kuma dole ya bini"

"Mummy kibi a hankali, kar garin neman gira a rasa ido"

"Rabu dani da wata ido da gira, zan cigaba da bincikawa muddin na tabbatar haka ne idan bai yi wasa ba saina ci mutuncinsa".

"Amma me Daddy ya ce?"

"Rabu dani da Daddyn nan na ku, nayi masa Magana amma bai mayar da abin serious ba, wai Khalil ba yaro ne ƙarami ba, duk in da yaje zai dawo kar in damu kaina"

"Mummy, gaskiya Daddy ya faɗa, ki kwantar da hankalinki zuwa Allah ya kaimu da safe mu ga yadda hali zai yi"

Jinjina kai Mummy ta yi ta bar ɗakin Fadila, gaba ɗaya ta rasa nutsuwarta saboda rashin sanin halin da Khalil yake ciki, da kuma a ina yake, ta ɗora alhakin duk wannan abun a kan Hafsa, wadda take can tana fama da kanta.

Da safe wajen ƙarfe tara na safe, Mama ta shirya ta dafawa Hafsa ruwan wanka, da ƙyar Hafsa ta rarrafa tayi wanka, kasa cin Abincin ma ta yi, Mama ta taimaka mata, ta shirya suka tafi Asibiti.
Tashin farko teses kawai sun yi na dubu biyu aka rubutawa Hafsa, aka yi mata likita ya tabbatar da jininta ya hau, ga malaria mai zafi da ulcer.
Mama ba tayi mamaki ba jin Hafsa tana da hawan jini, likitan ya ɗan nazarci fuskar Hafsa sannan ya ce "Ƙanwata meke damunki a 'yan shekarunki kika kamu da hawan jini, jininki ya hau fiye da yadda za a iya cewa ko zafin zazzaɓin ne ya sanya jinin ya hau"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana muza yatsunta na hannu.

"Magana fa nake" ya sake maganar yana ɗan dukan teburin gabansa.

Hawaye ne ya taru a idon Hafsa, Mama ta ce "Likita

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login