Showing 15001 words to 18000 words out of 296192 words
amma ta yaya zata iya daƙile wannan Auren? Tana cikin kukan wani tunani ya faɗo mata, cikin hanzari ta miƙe tsaye. Sai dai murayar da ta jiyo ana kwaɗa sallama ce ta sanya gabanta ya faɗi, ta dafe ƙiji tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"!
Domin gyara sharhi ko shawara
08081012143GABA DA GABANTA
Page 5
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Litatafaina na AƘIDATA DA RUƊIN ƘURUCIYA duk na kuɗi ne Please.
Ta taga Amina ta leƙa, sarai ta ɗau Muryar su waye, kasa amsa sallamar ta yi dan bata san da wani idon zata kallesu ba.
Yadda suke kwaɗa sallamar ba ƙaƙƙautawa ne ya sanyata amsawa, tare da fitowa daga cikinu ɗakin.
Kallo ɗaya ta yi musu gabanta ya faɗi, dan bata san da wacce suka zo ba, 'ya'yan Malam Rabi'u jarmai ne, wanda ƙawayen ta ne, sai dai su duk sun yi Aure, har da mai yara biyu, Iklima da Shema'u.
Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Shema'au sannunku da zuwa, ku shigo".
Iklima ta ce "Ji munafuka, mu shigo ina, algunguma ki rasa wanda zaki aura a garin nan dan rashin ta ido sai mahaifinmu, Wallahi kin ji kunya Amina".
Shema'u ta karɓa da "Ai zuwa mu ka yi mu ja miki kunne, Wallahi baki isa kiyi kishi da iyayenmu ba, gidanmu kamar kabari ne, Wallahi kika shiga azaba da wahala sai sun koreki da ƙafafuwan ki, gara tun wuri ki san abin yi".
Jiki a sanyaye Amina ta ce "Shema'u ku yi haƙuri, ni kai na ba son Auren nan nake ba Wallahi, kuma har yanzu ban ji a jikina zan iya Auren mahaifinku ba....
"Ba wani nan rufe mana baki, kwaɗayi ne ya sanya zaki auri baban mu ba wani abu ba".
Amina ta ce "Wallahi ba haka bane, ku tambaya ku ji Wallahi ni ba son mahaifinku nake ba".
"Yi mana shiru munafuka, har akwai yarinyar da ta isa ta ce ba ta son babanmu, zaki aure shi dan kwaɗayi, an yi kwantai a gari an ƙare a hanyar boko, ba abin da bokon ta amfana miki, kin gama gantalinki za a liƙawa babanmu, Wallahi ki ka aure shi ƙannenmu sai sun illata ki".
Amina ta ce "Naga ina ta lallaɓa ku kun kasa ganewa, to bari in fito muku a yadda kuke so, ni bana son mahaifinku shine ya nace mini sai ya aure ni, sai wani ihun kwaɗayi kuke yi, meye a gidan naku kuɗin baban naku da ba ci ake ba, tuwo safe rana dare, miyar gidanku kamar ruwan tsarki, kullum a wahala kuke, ya auri wannan ya saki waccan, insha Allah babu abin da zai sa in Auri babanku iyayenku ma fama suke, ta kan su suke yi".
Shema'u ta ce "Kutt, baban namu kike gayawa haka?".
"An gaya masa ɗin, yayi zuciya ya daina mayar da 'ya'yan mutane dan yana da kuɗi".
"Gara namu uban an san aure yake yi yana saki, wayasan me naki uban yake aikatawa a birni".
"Bakomai tun da ba'a san me yake ba, naku uban kuwa kowa ya san me yake yi, me ake da mutumin da bai san martaba da darajar Aure ba" ganin Amina ta fisu baki ya sanya suka fita suna ƙananun maganganu.
Amina ta koma ɗaki tayi shiruu, tana tunanin mafita, tabbas ta san idan ta auri Malam Rabi'u kashinta ya bushe, dan a gidan nan babu kalar yaran da babu dan wasu daga manyan 'ya'yansa yayyen su Shema'u 'yan daba ne, ga uwar gidansa ita ce babbar masifaffiya, gidansa tuwo kwano uku zuwa biyar ake tuƙawa, idan ranar girkin ki ce ke zaki tuƙa wannan tuwo, sai a kwan uku ana cinsa.
"Kai ba zai yiwu ba, Wallahi ba zan yadda in auri wannan mutumin ba".
"Ke Amina, au zama ki ka yi kina koke-koke, har da surutai ba zaki dangana ba?" Ta jiyo muryar Inno.
Cikin kuka Amina ta ce "Wallahi Inno ba zan auri Malam Rabi'u ba, yanzun nan su Shema'u suka bar gidan nan, ba ki ga cin mutuncin da suka yi mini ba, wai kar in auri babansu ni ce musu nayi ina son babansu, Inno wallahi bana son Mutumin nan ki gaya musu".
"Amina ta yaya zan ce musu ba kya son sa ni a wa? Yanzu haka da na dawo ya tsareni a ƙofar gida, wai sun karɓi kuɗin Aurenki, da kuma kuɗin gonar mahaifinki, wai za'a kawai Jamila dillaliya dubu hamsin a samo miki gado ɗan hannu, a kaiwa Liti kafinta shima wai idan da kujeru na hannu a sai miki, an saka sati uku bikin".
Fashewa Amina ta kuma yi da kuka ta ce "Wallahi ba zan auri wannan mutumin ba, tun yanzu 'yan'yan sa sun fara zuwa suna ci mini mutunci, kuma dan tsabar mugunta an siyar masa gonar babana da arha ya siya, kuma a siya mini kayan ɗaki 'yan hannu, dan an mayar da ni mara galihu".
Bakinta Inno ta gwaɓe ta ce "Dan ubanki 'yan uwan mahaifin naki kike gayawa haka, salon su zo su ji suce ni nake ziga ki? Ke a rayiwarki ba ki san tawakalli ba da duk abin da Allah ya tsarawa bawa ba shi da ikon kuskurewa ba, kamar iyaye suke a gurinki fa".
"Ni Wallahi ba iyaye na ba ne, tin da suke son kassara rayuwata, da tozarta mahaifina an cutar da shi an raba shi da gonarsa ba da saninsa ba".
Inno ta bi Amina da kallo, Amina kenan akwai haƙuri wasu lokutan, wasu lokutan kuwa akwai gardama da taurin kai, dan Inno ta fara fagabar yadda Amina ke cigaba da adawa ƙarara da Auren da ake son a yi mata.
*****************
Kamar kullum sun kammala lectures, lecturer ya ce zai yi musu wata test, amma ya bawa kowa damar ya yi amfani da wayarsa wurin samo amsar tambayoyin da zai yi. Suka dinga murna ɗaliban, malamin ya rubuta tambayoyi uku, a kan allo ya ce su amsa a mintuna goma kacal!
Nan da nan suka duƙufa suka ɗauko wayoyinsu, suka fara binciken aikin da aka ba su.
Rarraba idanu ya shiga yi, dan ba shi da wayar da zai amfani da ita wurin gudanar da aikin, ya juya hagu da damansa kowa ya duƙufa yana yi, amma ban da shi.
Takarda ya samu ya sunkuya ya fara rubutun sa cikin nutsuwa. Fadila ta ɗago ta kalleshi, yana ta rubutu amma ba daga waya yake kwafa ba. Ta taɓe baki ta taɓo ƙawarta Ta nuna mata shi ta ce "Kalli ko mai yake rubutawa oho, mutumin da ba turanci ya iya ba, kuma ba waya ce da shi ba amma yana ta rubutu shi dole ga ƙwaro" kamar yadda suka saba suka kwashe masa da dariya.
Bai ko ɗagoba ya cigaba da rubutun, sai dai duka bun nam da ake, ɗaliban suka gaza samo amsoshin tambayoyin a Google, ƙarshe abin da ya sawwaƙa suka rubuta lokaci ya cika suka bayar.
Fitar malamin ke da wuya, ɗaliban suka fara ƙoƙarin fita daga ajin, tafiya yake sannu a hankali, babu gaggawa gashi ita kuma sauri take, so take ta bar ajin ya tsare mata hanya kuma ya ƙi sauri.
"Dalla malam ka bani hanya, sai tafiya ka ke kamar mace, ko nan ɗakin ka ne?"
Tsayawa ya yi, ya waiwayo ya kalli Fadila ido cikin ido, ya rasa mai ya tsarewa yarinyar nan haka, bata hanya ya yi yace "Bisimillah, wuce" ratse shi ta yi ta wuce tana cigaba da mitar yadda yake tafiya kamar mara lafiya.
Shi dai bece mata uffan ba, ta wuce.
Department ɗin su Yusra ta tafi, kasancewar duk a makaranta ɗaya suke, ta yi sa'a ajinsu Yusra ba kowa dan haka ta shiga kan ta tsaye.
Yusra ta duƙufa ta na ta chatting a waya, Fadila ta zare wayar hannun Yusra, hakan ya tilasta mata ɗagowa, tana ganin Fadila ta yi murmushi ta ce "Beb daga ina haka?".
Fadila ta zauna tare da faɗin 'Daga class, nace bari in zo in ganki".
"Kai amma naji daɗi, ya lectures ɗin?".
"Alhamdilillah, muna nan muna fama, ya naku?".
"Alhamdilillah, muma hakan ne".
"That's good, da wa ake chatting ne haka?".
Yusra ta yi murmushi ta ce "Wallahi ba kowa, ina duba wani ankon da za muyi ne, na bikin Sister ɗina, so ina duba IG ne ko zan samu style".
Fadila ta ce "Ok na zata sabon kamu aka yi mana".
Yusra ta girgiza kai ta ce "Ba wani sabon kamu, samari akwai su, amma ni hankalina duk baya kan su".
"Don't mind girl, in dai brother na ne, insha Allah ina nan ina miki fighting ina ta kafa ki a wurin Mummy, mu bi komai a sannu zai amince ne".
"To beb, Allah ya amince. Ni wai ke ya ake ciki ne? Ko haryanzu ba ki da gwani"
"Hmm ni fa ba ta wannan shirmen nake ba, ni ban baki labari bama, wannan abokin Yaya Khalil ɗin Abdul yake kowa? Wai shine ya ke nuna yana sona"
"Ohh wannan abokin yayan naki da muka taɓa haɗuwa, wani mai abin dariya?".
"Shi fa"
"To meye aibunsa beb? Yana da kirki sosai".
"Taɓ, lecturer ne fa mai ya samu ya ci balle ya bani? Aikin ma fa Daddy ne ya samo masa".
"Ai ba wani abu Fadila, idan har kina son sa wannan duk ba abin damuwa bane".
'Bama na son sa dan ba class ɗina ba ne, wani baƙi da shi mara aji, sai surutun tsiya Mummy ma ba zata amince ba".
Yusra ta yi murmushi ta ce "To Ubangiji Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi gaba ɗaya".
"Ameen dear, tashi muje mu samu abin da zamu ci".
Suka rankaya gaba ɗaya suka fita daga ajin.
********
Saminu kuwa bayan tafiyarsa daga gidan su Amina, ya koma tasha, sarkin tasha ya sanar da shi an samu wasu 'yan biki da zasu je kai amarya can Lagos, a jira su kwana biyu a dawo da su, idan ya amince zai kai su zasu biya shi, biya mai kyau sun ce ba sa son Manyan motoci saboda tsaye tsaye.
Jin zai samu kuɗi masu yawa, ya sanya Saminu ya amince, ba tare da ya tuna saƙon Amina zuwa ga mahaifinta ba, washegari da Asubar fari ya ɗebi 'yan kai amarya yayi Lagos.
Amina kuwa ta din ga zuba ido taga ta ina Baba zai dawo gari, sai dai babu Baba babu alamar sa, kullum garin Allah ya waye cikin zuba ido take ta ga Baba ya dawo, amma shiru.
Gashi ta ƙara tsangwamar kanta, duk ta yi baƙi saboda damuwar da ta sanyawa zuciyarta, gashi 'ya'yan Rabi'u Jarmai kusan kullum cikin zuwa gidansu suke suna ja mata kunne a kan Auren mahaifinsu.
Ga su Kawu Lawan suma kullum da kalar ta su tijarar da suke zuwa su yi mata, hakan ya sa ta ƙara tsangwamar kanta, ko Abincin kirki ba ta iya ci sai kuka.
Gashi tuni su Kawu Bala suka karɓi kuɗin Aurenta, Naira dubu hamsin komai da komai har sadaki, kuma suka amshe kuɗin gonar mahaifinta.
Tana kwance a ɗaki da yamma, wani irin zazzaɓi ya rufeta, dama duk dare da shi take kwana, yanzu kuwa tun yamma ya rufeta, tana ƙudundune a bargo tana ta rawar sanyi, Inno na tsakar gida tana dafa mata rai ɗore ta bata ko zazzaɓin ya sauka, sai ga hayaniyar mutane.
Uwargidan kawu Bala da ta Kawu Lawan ce suka shigo, suka kalli Inno suka ce "Ke Hanne kayan Amina muka kawo, ki gyara wurin da za a ajiye".
Inno ta ce "Ga filin tsakar gida nan, a zo a ajiye su".
Nan fa samarin 'ya'yan su suka fara kokowa da shigo da kayan, wasu irin ruɓaɓun kayan gado ne, aka yi musu fentin ha'inci, dan garin shigo da su ƙasan sip ya ɓare, zanin kujerun nan kuwa daƙal daƙal, ga ƙamshin fenti ga warin rima kayan suna yi, kai da gani ka san na ha'inci ne.
Inno ta yi shiru tana bin kayan nan da kallo, duk sun ɓare garin kokowar shigowa.
Uwargidan kawu Bala ta ce "To Inno, su Malam sun fita sun yi iya yin su ga kayan gadon Amina nan, saura kema naki ɓangaren aga irin bajintar da zaki yi a ɗakin amarya".
Inno ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Haka ne, Allah ya nuna mana ya sa ayi da mu".
Suka amsa da Ameen, suka ringa guɗa, suka gama hayaniyar su suka fice.
Amina ta ɗaga labule ta fito daga ɗakin su, ta kalli kayan nan, ta kalli bayan sif ɗin nan, yadda wani wurin ya kusa burmawa, da in da ya ɓare wurin shigo da kayan, shi kansa allon gadon, sari ya cinye wani wurin aka liƙe shi da fenti.
Ta fashe da kuka ta ce "Yanzu a kan wannan matsiyatan kayan aka siyar da gonar Baba? Wallahi sai Allah ya saka mana".
Inno ta ce "Dan Allah ki rufa mana Asiri, kar su dawo su ji abin da ki ke faɗa"
"To su ji ɗin ina ruwana, Wallahi su da Allah, duk cikin yaransu da aka aurar, ba wadda aka yiwa wannan wulaƙanci sai ni, kalli wasu irin kaya kamar wata mara galihu, Allah ka saka mini" tayi maganar kamar zata shiɗe, saboda yadda haƙoranta ke haɗuwa saboda zafin zazzaɓi.
Inno ta ce "Ni dai haƙurin nan dai shi zan baki, ki barwa Allah Komai dan Allah karki wani abu da zai sanya su zo su ɗaga mana hankali".
Ta share hawayenta ta ce "Inno, anya Saminu ya gayawa Baba halin da ake ciki?"
"To gashi dai har yanzu shiru ba muji ɗuriyarsa ba"
"Inno ko bokonmu zanje, wurin malamanmu in ari waya in kira Baban?".
"A'a ni bana son abin da zai janyo magana, ko kin manta da sun hanaki zuwa bokon nan, ki kiyayeni. Zan shiga banɗaki ki ɗau kofi ki tsiyayi rai ɗoren can ki sha, ki ɗau Abinci ki daure ki ci". Amina ta jinjina kai. Tana ganin Inno ta shiga banɗaki, ta ɗau hijjabinta ta fice daga gidan.
Duk da yadda take jin jiri, kanta yana juyawa, amma zuciyarta ta bushe, sai zuba sauri kawai take yi.
Uwar tafiya ta kwasa ba ta wasa ba, ta isa ƙaramar tashar garinsu, cikin rukunin direbobin nan taje ta gaishe su.
Suka amsa wani mai suna Lado kan kara ya ce "Ya aka yi ne? Amarya da yawo ke da aka kusa ɗaura miki Aure?".
Banza ta yi masa ta ce "Dan Allah Saminu nake nema".
Wani ya ce "Saminu ya je Ikko, amma ya kamo hanyar dawowa gida".
"Dan Allah ko zaku taimaka ku kira mini shi a waya, na bashi saƙo zuwa wurin Baba amma na ji shiru".
"Ba matsala, bari a kira shi" cewar Lado. Amina ba tayi niyyar tankawa Lado kan kara ba, amm ganin zai taimaka mata ya sanya ta ɗan saki fuskarta.
Ya kira Saminu ya miƙa mata wayar, cikin azama ta karɓa ta koma gefe.
"Salamu Alaikum, Saminu Amina ce 'yar wajen Baba Hassan".
Saminu ya rafka salati ya ce "Amina, dan girman Allah kiyi haƙuri, Wallahi na manta shaf da saƙonki na tafi ikko, amma kin ganni a hanyar dawowa, na miki alƙawarin yanzun nan, zan kira Baban in sanar masa".
Amina cikin kuka ta ce "Dan Allah ka taimake ni Saminu, kar a wulaƙanta rayuwata"
"Kar ki damu Amina, zan sanar masa Insha Allah" suka yi sallama ta bawa Lado wayarsa, ta yi musu godiya ta kama hanyar gida.
Tun a hanya duhun magariba ya fara rufawa, ba ta damu da yadda sanyin dogayen zangarniyar bishiyoyin hatsi ke kaɗawa suna ratsata ba, wanda hakan ya ƙara asassa tsananin zafin da jikinta ke ɗauka, ga gefen cikinta da ya ƙulle, saboda yunwa amma ba ta damu ba, sai sauri take yi, in da ba mutane ta kwasa da gudu dan ta isa gida da wuri.
Allah ya taimaketa ba wanda ya ganta suruf ta shige gida.
Ta tarar Inno bata nan, ta shiga banɗaki tayi alwala ta koma ɗaki ta tayar da sallar magariba.
Inno ce ta shigo gidan tana 'yan maganganu, tana ɗaga labule ta hango Amina na salla, aikuwa ta rafka salati ta ce "Ke daga ina haka? Kika ɗaga mini hankali nake ta yawon nemanki?".
Amina ta idar da salla ta yi Adduointa, sannan ta kalli Inno ta ce "Inno tasha naje ko Saminu yana nan, wai ashe bai gayawa Baba saƙon nan ba, yana Ikko ma, aka kira mini shi a waya, shine ya ce mini zai gaya masa".
"Kuma shine sai ki tafi baki gaya mini ba, kin ɗaga mini hankali, nan suka aiko suna neman ki, amma ba kya nan na rasa ƙaryar da zan musu, wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko? Ke duk abin da zai sa su zo su ci mana mutunci kin san shi kuma zaki aikata ko?" Shiru Amina ta yi taƙi magana, Inno ta yi ta banbaminta ta gama, Amina ba tace komai ba.
Baba Hassan kuwa kusan suman zaune yayi, bayan Saminu ya kira shi a waya ya wassafa masa irin katoɓarar da 'yan uwansa suke shirin aikatawa, na cefanar da gonarsa da kuma aurar masa da tilon 'yar sa ga mutumin banza da suke shirin yi.
Baba Hassan bai iya cewa Komai ba sai kashe wayar da ya yi, ya san nan duniya ko me zai yi bai isa ya hana wannan auren ba, sayar da gonarsa bai ɓata masa rai ba kamar yadda ake shirin salwantar da rayuwar 'yar sa, dan abin da ya shirya shine, shekara mai zuwa ya biya mata kuɗin jarrabawar, kuma ya dinga tattala 'yan kuɗaɗe saboda harkar makarantar ta, sai dai kash ga abin da 'yan uwansa ke shirin aikatawa.
Amina har zuwa sallar isha'i zazzaɓin jikinta bai sauka ba, ga wani irin koren amai mai ɗaci da take tayi, Inno sai jiƙe-jiƙe take tana ɗura mata, Amina mirsisi ta ƙi sha, saboda wannan jiƙe-jiƙen da take sha su suke ƙara sanyata amai.
Yarone yayi sallama, wai Amina ta je in ji Malam Rabi'u Jarmai.
Inno ta ce "Ka je ka ce masa ba ta da lafiya".
Yaron ya fita ba jimawa, ya dawo ya ce "Wai Kawu Lawan ya ce idan ba ta je ba ya zo sai ya zane ta".
Inno ta kalli Amina ta ce "Amina, lallaɓa kije, bana son fitina da tashin hankali".
Amina ta buɗe baki za tayi Magana, Inno ta girgiza mata kai ta ce "Yi haƙuri, daure kije" haka ta ɗau hijjabinta tana kuka, ga zazzaɓi a jikinta ta fita.
Jarmai na ganinta ya washe baki yana faɗin "Amaryata ba faɗa mai ya kawo gaba fisabilillahi?".
"Kaga saurara mini, Azzalimi kawai aka sayar maka da gonar Baba ka saya, alhalin ka san kuɗin gonarsa ba haka yake ba, to Wallahi ba zan auri Azzalimin mutum irinka ba, ga yaranka marasa tarbiyya da suke mana zarya a gida suna zagina,