Showing 216001 words to 219000 words out of 296192 words
sake ɗiba ta ci, taji yayi mata daɗi sosai da sosai.
Jan kujera tayi ta zauna, ta dinga tsamar naman nan tana ci, kan kace meye wannan ta ci ya kai rabi.
Hajiya Zainab kuwa sai lallaɓa Daddy take yi, tana yi masa kwarkwasar da sai zai bata kuɗi yake ganinta.
Ta sha uwar kwalliya, sai ƙamshi take tayi masa jagora zuwa falo, sai hira take yi masa.
Turus tayi lokacin da suka ƙaraso dining, taga Amina zaune da spoon a hannunta tana cin naman da ta tanada saboda Alhaji Ahmad.
"Ke, wani irin wulaƙanci ne wannan da rainin hankali, na girka wa Mijina abun ki zo ki zauna kina ci?" Ɗan saroro Amina tayi sannan ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ban zaci ke kika dafa masa ba, nayi zaton Hajara ce......
"Ko kuma uwar Hajara ba, saboda tsabar rashin mutunci ko Hajarar ce ta dafa ba kya bari a baki iznin ci ba, zaki zauna na yiwa mijina girki ki cinye"
Amina ta ce "Ya salam, amma nace kiyi haƙuri ni wallahi ban san ke kika girka ba, saboda ban taɓa ganin kin yi ba, raina ne ya biya amma ba damuwa ai sai na girka masa wani".
A cikin tsananin fushi Hajiya Zainab ta kalli Daddy ta ce "Wallahi tun wuri ka taka wa Yarinyar nan burki, wannan wane irin iskanci ne da rashin mutunci,? Yaya za ayi na dafa abu saboda kai ta zauna ta na ci, yanzu nayi magana ace na fiye kishi da neman rigima ita kuma wannan me tayi?"
Daddy ya kalli Amina ya ce "Meenal, meyasa ki ka ci bayan kin san ba ke kika ajiye ba, kin san fa bana son neman magana"
"Wallahi Daddy ban san naka ne ta ajiye maka ba, ji nayi ina son ci shiyasa"
"Eh tunda gaki mayya ba, dangin mayu kinga nama idan baki ci ba mutuwa zaki yi".
Amina ta ce "Ni ba mayya bace, danginmu kuma babu mayu, dan hak.... Ba ta ƙarasa ba Daddy ya ce "Ya isa haka, ki bata haƙuri kawai a wuce wurin"
"Amma Daddy tunda kuka fito fa nake bata haƙuri, me kuma take so nace mata?"
A ɗan hasale ya ce "Ki bata haƙuri nace, bana son gardama"
Amina ta sunkuyar da kanta ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ban san ke kika girka ba"
Daɗi ne ya kama Hajiya Zainab, ganin yadda Daddy ya fara acting, ya sanya taji a ranta ai maganinta ya fara ciksa, dan ma bai ci wannan naman ba, in da Allah ya taimaketa akwai sauran maganin.
Ta haɗe rai ta ce "Gaskiya dai ka sake ja mata kunne, kar ta sake yi mini irin haka, idan kuma ta kuma komai nayi mata ita ta saya"
Daddy ya ce "Kiyi haƙuri, ba zata sake ba in Sha Allah, kuma in dai nine kar ki damu, na karya haka na gode sosai da kulawa"
Amina kuwa miƙewa tayi, ranta babu daɗi garin ta bar wurin, ta kifar da sauran naman ya zube a ƙasa.
Daddy ya kalleta ya ce "Ina zaki? Ba zaki zauna ki karya ba?"
Hajiya Zainab ta ce "No, bana buƙatarta a nan, daga ni sai kai nake son muyi breakfast, ta samo dai abu ta gyara wannan abin da ta zubar" ko sauraransu Amina ba tayi ba, tai musu banza tayi tafiyarta.
Ɗaki ta koma ta nemi wuri ta kwanta, taji yadda naman da taci yake taso mata, ga shi taji kamar tana ƙaurin hayaƙin nan da ta fito ta tarar ya turnuƙe falo.
Guntun tsaki ta ja ta na juyi a kan gadonta, daga bisani wani irin bacci yayi awon gaba da ita.
A cikin baccin nata ne, taji yadda cikinta yake murɗawa, ta farka ta tashi zaune, abu kamar wasa cikinta ya dinga murɗawa, ta dinga juyi a kan gadon nan, daga baya kuma sai amai. Tun tana iya tashi daga kan gadon ta tafi toilet, har ta nemi wuri ta zauna a toilet ɗin, ta dinga kwara aman nan ba ƙaƙƙautawa, duk ta fita hayyacinta kamar wadda tayi cholera.
Babban abin da ya bata haushi bai wuce yadda Daddy ko ya leƙo yayi mata sallama kan ya fita ba, alhalin idan yana wurinta, sai ya je yaga Hajiya Zainab koda kuwa zata ci masa mutunci ne.
Bayan fitar Daddy, Hajiya Zainab ta ɗau waya take bawa su Turai labarin abin da ya faru a group. Suka tayata murna saboda alamu ya nuna kamar maganin ya fara aiki, amma Hajiya Turai ta ce "A gaskiya naji haushin cin naman nan da wannan shegiyar 'yar tayi, Allah ya sa shi ne ajalinta"
Salma ta ce "Amin dai, sai ki sake dafa masa wani, amma ki tabattar daga ke sai shi a ɗaki, ki bashi ya ci".
"Haka za ayi, na fara na turaren nan ma, ni na naman na damu ya ci, kuma shi yafi son kifi fa a kan nama, saboda hawan jini"
Turai ta ce "Haka nan zaki lallaɓa shi, sai yaci, mu dai fatanmu buƙatar mu ta biya"
Ta ce "Haka ne, in Allah ya yarda zan duk mai yiwuwa, naga na bashi ya ci, sonake naga ya kori Yarinyar nan korar wulaƙanci a gidan nan"
"Kar ki da mu, ke dai ki civaba6da gwada maganin" suka cigaba da zigata da baga shawarwarin yadda zata ɓullowa al'amuran.
Khalil kuwa ya dage sai shiri yake, yana narka kuɗi a gininsa, kamar wanda zai auro 'yar wani gwamna ko sarki, sannan yana turawa Hajiya Maryam kuɗi domin yi masa sayayar kayan lefe.
Sunata cigaba da tsara yadda biki zai kasance.
Abdul ya ga yakamata ya sanar da Khalil batun soyayyarsa da Yusra, kar ya zo yaji a wani wurin yaji babu daɗi.
Dan haka bayan sun gama hirar yadda abubuwa zasu kasance a bikin Khalil, sai Abdul ya fara sako masa nasa zancen ta hanyar cewa "Malam nima fa na kusa kai kuɗin Auren nan". Khalil ya ce "Are You serious?"
"Da gaske nake maka"
"Amma gayen nan baka da kirki, amma baka taɓa gaya mini ba, ko ka haɗani da ita mu gaisa ba"
Abdul ya ce "Ai ba wata bace a nesa, ta gida ce"
"Ok, wacece?"
Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Yusra ce, ƙawar Fadila".
Khalil ya ce "Ohhh Allah, Allah mai yadda ya so, lallai zaka sha iyayi da rawar kai, ka rasa Fadila amma kusan halinsu ɗaya Allah ya baka wuyanka ɗauka"
"Amin na gode da fatan alkhairi"
"Ahh haba bakomai, amma gaskiya ku bari a fara nawa sai ayi naku"
Abdul ya ce "Saboda wayo, to ban yadda ba"
Gaba ɗaya Abdul bai yi zaton Khalil zai ɗau abin so simple haka ba, a zatonsa zai nuna bai ji daɗi ba, saboda a baya ƙanwarsa ya nuna yana so.
Yazid kuwa ya kuma haɗuwa da Fadila a makaranta, sai dai fuskar nam babu yabo ba fallasa, da fara'arsa ya ƙarasa gareta yana mata murmushi.
"Alhamdilillah, naji daɗi da ban ganki kina kuka ba, amma ya aka yi kwana biyu baki shigo school ba?" Yayi maganar yana ƙoƙarin zama, amma ta matsa gefe dan bata son yadda jikinta ke rawa da sun samu kusanci.
Fasa zaman yayi ya ce "Ohhhh sorry, ina fatan yanzu kin watstsake?"
Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Yes Alhamdilillah"
"Tsarki ya tabatta ga Allah, mun gode masa bisa ni'inominsa da jarabbwowinsa. Kin san ita rayuwa sai ana yi ana taɓa ɗan Adam yake sake samun kusanci ga mahaliccinsa, kuka ba mafita bane ba sam, Addu'a da miƙa lamari ga Allah su ne mafita kin ji?"
Kallonsa tayi amma bata amsa ba.
"Ya kika yi shiru?"
"Ina jinka ai"
Ya ce "Alright, yauwa dan Allah ina sake godiya da alherin da aka yi minina gidanku"
"Kaga bakomai kar ka damu kawai" ta katse shi.
Bai sake cewa komai ba ya bar wurin, ita ji tayi ma gaba ɗaya ta tsani zaman ajin, dan haka ta tashi ta ɗau jakarta ta fice.
Yusra ta kira a waya, Yusra ta sanar mata tana common room, dan haka ta wuce ta je ta tarar da ita a can.
Ta je ta samu Yusra a can, tana zuwa ta zauna ba tare da ta ce mata komai ba.
Yusra ta kalleta a nutse ta ce "Beb, meke faruwa ke ba a rasaki da damuwa menene?"
Kaar za tayi kuka ta ce "Komai ma Yusra, gaba ɗaya gidanmu babu daɗi, wannan yarinyar ta ɓata mana jin daɗin rayuwa, ko kin san Mummy sai da ta bar gida kwana huɗu ba wanda ya san in da take"
"Subhanallah, amma dai an ganta ko, ai ni baki gaya mini ba"
"Ta dawo jiya, baƙin ciki da ɓacin ran da Daddy yake sakata ne ya ta tafi, ba wanda ya san ina taje sai jiya ta dawo, Yarinyar nan munafuka ce, last week tunda na zo school ɗin nan nake kuka, baki ji cin kashin da take yiwa Mummy ba, kuma Daddy yana goya mata baya, da aka tashi daga school yazid ya kaini gida, saboda munafurci ta bashi abu ni ban san me ta bashi ba yake ta ayi mata godiya, da ni na bashi ba lallai ya karɓa"
Yusra ta ce "Au kun shirya da Yazid ɗin ne?"
"Ke oho masa, ni ba shi ya dameni ba, Yaya Khalil fa ko a jikinsa abin da Daddy yayi wa Mummy, yama koma wurin ta ita da Daddy, duk yadda zan gaya miki ba zaki gane yadda gidanmu ya tarwatse ba"
"No, ki daina faɗar haka, gidanku ba zai taɓa tarwatsewa ba, kuma komai zaa wuce da yardar Allah"
Fadila ta ce "Allah ya sa, ni ji nake dama muna da wasu 'yan uwa da muke zuwa gidansu, da can zan koma ba zan iya jure wannan tashin hankalin ba"
"Fadila Addu'a ita ce mafita a kan komai, dan haka ki miƙa lamuranki ga Allah, ki manta da komai"
Fadila ta nemi wuri ta kwanta a cinyar Yusra, tana ganin Yusra ba zata gane halin da take ciki ba.
Amina ba ƙaramin ƙulewa tayi ba da Daddy bai shigo ba, ta sha wahala sosai da ƙyar aman da take ya tsaya.
Wajen azahar taji ana bubbuga ƙofar bedroom ɗinta, da ƙyar ta taso ta buɗe. Sai taga Hajara a tsaye.
Hajara ta ce "Naga gaba ɗaya banga kin fito ba, shine nace bari na zo na duba ko lafiya".
Amina ta ce "Wallahi Hajara bana jin daɗi ne, dan Allah ida da gasarar kunu, ki damo mini ki kawon in samu na sha"
"Subhanallah, Allah ya sauwaƙe kina ɗaki baki fito ba shiyasa ba wanda ya sani, bari na kawo miki"
Amina ta ce "Yauwa na gode" ta koma taje ta kwanta.
Mintuna talatin da ɗoriya, sai ga Hajara ta dawo, ta kawowa Amina kunu, ta karɓa tayi mata godiya, ta zauna ta sha kunun sosai dan tana ji yunwa, amma bayan ta gama sha, tana tuna naman nam da ta ci, taji cikinta ya kuma hautsinawa taje ta amayar da shi.
Amina ta ce "Na shiga uku ni Amina, anya wannan naman da arziƙi ne, naje na ciyo wa kaina masifa da kaina"
Haka ta wuni tana malelekuwa, da kyar aman ya tsaya. Duk ta fita hayyacinta.
Wajen ƙarfe shida da rabi, tana kwance bacci ya ɗauketa, taji ƙamshin turaren Daddy. Ta buɗe idonta a hankali ta ganshi zaune a kusa da ita yana shafa kanta.
Kallo ɗaya tayi masa ta ture hannunsa, ta juya masa baya.
"Meenal lafiya kuwa?"
Amina ta ce "Ni ka ƙyaleni"
Ya kwantar da murya ya ce "Haba 'yar babyna, nine fa Daddy ne"
"Ba wata 'yar babynka, da ka mini wulaƙanci a gaban matarka, ka goya mata baya dan an dafa maka abu na ci, har da wani yi mini faɗa naman ma da naci ya kusa kasheni, kuma wai wunin yau ko ka leƙo ka ganni, bayan idan kana wurina ko zata maka wulaƙanci ita kana leƙawa ka ganta wuni nayi ina ciwon ciki amma banga ka zo in da nake ba"
Cikin rarrashi ya ce "Haba Meenal, ya zan bata rashin gaskiya bayan kin san kin yi laifi, zata dinga ganin bana yi mata adalci. Wallahi ina ƙoƙari Amina idan na biyewa son zuciyata ba zan muku adalci ba, saboda na san ina miki son da ni kaina yake bani mamaki. Kuma naje mun yi maganar auren Fadila ne da iyayen wannan yaron, ban zaci zan daɗe haka ba, amma dan Allah kiyi haƙuri" banza tayi masa tana cigaba da zumɓura baki.
"Babyna, ko in tsuguna ne? In dai hakan zai saki farinciki sai na durƙusa na baki haƙuri, dan Allah ki daina fushin nan wallahi ni kaina wunin yau babu daɗi nayi shi, nayi missing ɗinki abubuwane suka sha kaina dayawa, amma am sorry Dear"
Ya ƙarasa maganar yana juyo da ita ta fuskance shi.
Saboda tsabar shagwaɓa sai ta hau kuka har da hawaye, tana tura baki, Daddy kuwa ya lalace a wurin rarrashinta, yana share mata hawaye.
Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ya ce "Yauwa Meenalin Daddy, ko ke fa saura kuma ki yi mini murmushi zuciyata ta samu nutsuwa"
Ta noƙe masa kafaɗa.
"Please Baby"
Ta ce "Ina da sharaɗi"
"Wane sharaɗin ne?"
"Gaskiya kar ka sake ka ci nama a kwanakin nan, ka san dai kana kan dokokin likita ko?"
"In dai wannan ne, shikenan ba zan ci ba i promise, yi murmushin na gani"
Murmushin tayi tana share sauran hawayen fuskarta.
Murmushin shima yayi ya ce "To yanzu me zaki ci?"
"Gasashen Kifi nake so, manyan nan mai miya"
"To shikenan, amma taso muje ki ɗan tattaka, ko kya ji dadin jikin ki".
Ta ce "Ni ba tattakawa zan yi ba, ban yi wanka ba, duk jikina ciwo yake mini saboda ciwon ciki"
Daddy ya miƙe, ya cire babbar riga, ya saka Amina gaba zuwa toilet.
Har mai shi ya shafa mata, ya taimaka mata ta sanya wasu kayan, ya kalleta ya ce "Ko muje Asibiti dai, naga jikinki yayi weak?"
"Ai ya daina yi mini ciwon, ka sayo mini kifin kawai"
"To shikenan, kwanta ki huta yanzu zan dawo"
Ta ce "To a dawo lafiya"
Ya jinjina mata kai ya fice, yan fita falo ya haɗu a Hajiya Zainab, ta kalleshi ta ce "Dama kana gidan nan tun ɗazu? Nifa bana son munafunci, amma dai ka san yau a wurina kake ko?"
Alhaji Ahmad ya ce "Haba Zainab, dan ina wurinki shikenan ba zan leƙa in ga ya take ya ta kwana ba? Yarinyar nan tunda na fita ashe bata da lafiya, hakkinta a kaina yake dole naje naga jikinta"
Cikin ɓacin rai ta ce "dole ko? Yayi maka kyau" ta wuce fuuuu ta bar shi a wurin.
Da fari ji yayi kamar ya bita, da ya tuna Amina ko Abinci bata ci ba wunin yau, kawai sai ya fice ya tafi saya mata kifinta da ta nema.
Hajiya Zainab iya ƙuluwa ta ƙulu, amma ta danne saboda ta sake dafa wani namn, so take ya ci.
Amina kuma zaman ɗakin ne ya gundureta, ta ɗan ji daɗin jikinta, dan haka ta fito da niyyar zuwa kitchen, ta dafa tea idan Daddy ya kawo mata kifin, ta samu abin haɗawa.
Sai dai kamar ɗazu da safe, yanzu ma falon warin wannan hayaƙin yake yi.
Da sauri ta ƙarasa kitchen, saboda jin yadda tari ya fara taso mata.
A gurguje ta dafa tea ɗin, ta koma ɗakinta tana tsaki, saboda ita bata ga amfanin wannan hayaƙin ba, bata san ta ina yake shigowa falon ba, dan sam bata yi zaton Hajiya Zainab ke kunna shi ba.
Da magariba Daddy ya dawo da kifin Amina, ta dinga murna da ganin kifin nan, ya zauna ya sata a gaba ta ci sosai sannan ya ce "Alhamdilillah, tun da kin samu kin ci kifin sosai, Allah ya baki lafiya, gobe in Allah ya kaimu nake son muje mu yiwa 'yan uwa bangajiya, har Shanono nake son muke, jibi in Allah ya kaimu kuma, zamu je Dutse ta can zamu tashi".
Murmushin fuskarta ne ya ƙaru cikin murna ta ce "Amma naji daɗi sosai, Allah ya kaimu da rai da lafiya"
"Amin ya rabb, bari na tashi naje wurin Yayarki"
Ta gyaɗa kai ta ce "Ok, shikenan kace ina gaisheta"
"To zata ji" ya tashi ya tafi. Ta ji daɗin jikinta mussaman yanzu da ta samu ta ci wani abin ya zauna a cikinta.
Tashi tayi ta duba littafinta da take rubutun Alqur'ani a ciki, ta sanya hijjabinta ta ɗau biro ta zauna, tana karantawa a hankali tana rubutawa.
Ba dan Hajiya Zainab ta so ba, ta saki fuskarta, bayan Daddyn ya rarrasheta a kan Amina ce bata jin daɗi.
Ta kawo masa abinci tare da wani farfesun naman, ya kalli naman ya ce "Naman nan a bar shi, zuba mini Abincin kawai"
Ta kalleshi ta ce "Saboda me?"
"Likita ya hanani cin jan nama, saboda shekaru da yanayin jikina"
Ta ɗan rausayar da murya ta ce "Amma sai da ka bari na dafa zaka ce ba zaka ci ba, dan Allah ko kaɗan ka ci mana" ganin duk ta damu ta ɓata fuska, ya sanya ya ɗau fork ya ɗebo naman, murmushi yayi kan ya kai bakinsa, ya tuna da tare za su ci Abinci da Amina, zai fara cin Abinci ƙura masa ido za tayi sai taji yayi Bismillah, idan kuwa bai yi ba sa ta riƙe masa hannu tana haɗe rai kamar wani ɗanta.
A hankali yayi Bismillah, ya kai yanka ɗaya bakinsa, sai ya tuna alƙawari yayi wa Amina ba zai ci ba, dan haka ya ce ya ishe shi.
Kissar duniya da rarrashi ba wanda Hajiya Zainab ba tayi ba, amma ya ce ba zai ƙara ba ya ƙoshi.
Ji tayi kamar ta tsinke shi da mari ta huta, amma ta shareshi.
Abu ɗaya ne ya ɗan faranta mata rai, shine maganar da yayi mata na cewa iyayen Salim sun zo ya haɗu da su, sun ce zasu kawo kuɗin Aure da zarar ya dawo, shi kuma ya ce ya basu, sannan zai cigaba da saurarensu.
Wannan maganar ce ta ɗan faranta mata rai, amma duk da haka ta shareshi, saboda rashin cin naman nan ba ƙaramin ƙuluwa tayi ba.
Da daddare har sun kwanta, yake gaya mata cewar gobe in Allah ya kaimu zasu fita shi da Amina, jibi kuma za suje Dutse daga nan zasu bar ƙasar kwanaki goma ma kawa za suyi su dawo.
Sai da Daddy ya gwammace bai yi nata zancen ba, saboda azabar bala'in da ta dinga yi masa a ka, tamkar zata dake shi. Ƙarshe sai juya mata baya yayi, tayi mai isarta ƙasan zuciyarta kuma tana Mamakin yadda aka yi maganin bai fara aiki yadda take so ba.
Hajiya Zainab tana can tana bacci, Daddy ya lallaɓa ya tafi wurin Amina, dama ranar girkinta ne, yayi wanka ya shirya ko karyawa ba suyi ba, ya ɗauketa