Showing 264001 words to 267000 words out of 296192 words
aka saka aka sayar da saniya guda, wai dama tawa ce ta wurin Innarmu tana da dabbobi a ƙauyen.
Aka sayar da ita kusan dubu casa'in da ɗoriya, sannan ta ce da ni zata tafi cikin garin Kano in da take aure a Kano. Tare da alwashin muddin tana raye ba zan wulaƙanta ba, dan tamkar ta wulaƙanta Inna wuro ne idan na wulaƙanta.
Ta tafi da ni Kano, gidanta inda take aure, sai dai bata taɓa haihuwa ba ita.
Kwanana biyu a gidanta, tana ta bani kulawa nace mata zan koma makaranta, tare muka je makarantar dan taga a in da nake, tare da sayayyata ta kayan Abinci fal.
Na koma makaranta ina ɗan jin daɗin na samu wurin zama idan na gama makarantata.
Alhamdilillah kwanci tashi asarar mai rai, na kammala makaranta, na koma Kano wurin Hajiya, sai dai zuciyata na gida wurin mahaifina.
Na sanarwa da Hajiya dan Allah ta rakani muje Rano, in ga Baba da sauran 'yan uwana, kuma idan laifi na yi masa ta tayani bashi haƙuri.
Yadda Hajiya ke nuna mini ƙauna abin ba a magana, dan haka ta shirya muka je Rano tare, kusan shekaru biyu rabona da garin, sai dai bata sauya zani ba, mahaifina a gaban Hajiya ya kuma maimaita baya ƙaunata.
Matan gidan nan ma da yara suka dinga zage-zage da habaici wai kamar maye tun da ya ce baya son ganina kar na sake zuwar musu gida.
Ran Hajiya ya ɓaci sosai, dan sai da suka yi sa'insa da mahaifina, ba ta taɓa zaton abin ya kai haka ba, ta ce in sha Allah ba zan sake zuwar musu gida ba.
Baba uwani ta ce in dai nine ita ma sai ta koreni, dan duk inda muka raɓa da uwata masifa ke bibiyar wurin.
Ba ta kula su ba, muka baro Rano zuwa Kano.
Mijin Hajiya ma mutumin kirki ne, ba zaka taɓa cewa basu suka haifeni ba, result ɗinmu ya fito Neco da Waec duk na yi nasara.
Mijin Hajiya ya shiga ya fita na samu admission a Jami'a na ɗora karatuna na Islamic studies, amma a hakan ina cigaba da zuwa Islamiyya ƙarin karatu. Duk da yadda na samu kwanciyar hankali kullum tunanina yana gida, da son ganin mahaifina ga kewar Innata da ƙanina da suka kasa barina.
Abinda na fuskanta a zamana da Hajiya shi ne ita kuma dangin miji ne basa ƙaunarta sam, tsanar da suke mata har ta shafeni nima. Ina level 2 Allah ya karɓi mijin Hajiya, sakamakon hatsrin mota da suka yi.
Bayan zaman makoki, Hajiya ta ce ba zata koma Jalingo ba saboda karatuna, kuma ba zan iya rayuwar can ba.
Dangin mijinta suka takura a raba gado, aka raba ta samu gidan da take ciki a yanzu.
Sai da na ji tamkar in haƙura da zuwa makaranta, saboda tsananin rayuwa, abubuwa suka ƙara tsanani.
Hajiya ba ta da wata babbar sana'a, nima sai faɗi tashi, sai da Hajiya ta dangana da zuwa naiman a taimako gidajen masu kuɗin unguwarmu a kan karatuna, amma abu ya ci tura, ta koma Jalingo aka kuma sayar da shanun Innata, da haka na kammala makarantar, har na je na yi service a Maiduguri.
Bayan na gama na dawo na yi remidial, na koma science, a haka na lallaɓa na yi computer science diploma bayan wancan degree. Duk wannan abun ba wanda ya taɓa nema na a danginmu.
Na samu Islamiyya na fara koyarwa, ɗan abin da na samo muna ci da Hajiya, tana ta mini fatan Allah ya sanya na samu aikin yi.
Wani mutum a unguwarmu ya zo ya samu Hajiya ya ce ya yaba da hankalina dan Allah yana son ya buɗe Cafe in dinga riƙe masa yana biyana.
Hajiya tayi ta murna, da fari da ta zo mini da maganar ban amince ba, amma ganin ita ta yarda da lamarin, ya sanya nima na anince kawai dan ba wani abin dama nake yi ba a wannan lokacin.
Abu kamar wasa ya buɗe mini Cafe, kusan a cikin unguwa dai, ni wurin ne kawai Cafe.
Nan da nan aka fara samun alheri, sai dai saɓanin yadda yayi alƙawari baya iya cikawa ta hanyar biyana hakkina yadda Yakamata.
Bance masa komai ba kuma kuɗinsa bai taɓa ciwon kai ba, sai dai hakan ina zuwa koyon gyaran mota a wani gareji, na samu ubangida mai ƙaunata, da safe na je gareji, da yamma na je Cafe da daddare na je koyarwa aikina kenan kawai.
A gareji nake samun 'yan kuɗaɗen kashewata, amma aka samu ɗan mutumin da ya buɗe mini Cafe Alhaji Hashimu ya je ya sameshi ya ce masa ina wadaƙa da kuɗin shagonsa.
Mutumin nan ya zo ya dinga ci mini mutunci a kan haka, na shawarci Hajiya ta ce in haƙura in ƙyale masa wurinsa ita ma ta amince.
Na je na sameshi na ce masa yayi haƙuri, ya nemi wani ya cigaba da kula masa da wurin Cafe ɗin, ni na daina.
Na bar wurinsa da kwana biyu, 'yan sanda suka je har garejin da nake koyon aikin gyaran mota, ban san me na yi ba sai da muka je na tarar da Alhaji Hashimu da nake kulawa da Cafe, wai ya shigar da ƙarata na kwashe masa computers kusan goma sha biyar bayan computer biyar ce a wurin, da injin photocopy da kuma almundahanar kuɗi na POs tsananin mamaki ya sanya na kasa kare kaina, saboda mamakin abinda mutumin nan yayi mini.
Aka yi ƙiyasin abin da na yi masa asara wai har naira miliyan da dubu ɗari da hamsin.
Hankalin Hajiya ya tashi fiye da tunaninki, tayi kuka ta ce ba yadda za ayi na yi sata ba halina bane ba, amma mutumin nan yayi mirsisi ya ce a biya shi kuɗinsa ko ya kai ni kurkuku.
Hajiya ta shirya ta tafi ƙauyenmu wurin Baba, ta sanar masa tana kuka ya taimaka kar a kaini kurkuku, amma Baba ya ce babu ruwansa, dan bai ma san haryanzu ina wurinta ba.
Ta koma Jalingo ta je ta sayar da duk ragowar shanuna har da nata, ta dawo a kwana uku, lokacin ana ta shirin kai ni kotu.
Mutanen unguwa suka ce ba yadda za ayi na aikata abin da ake zargina da shi, dan haka mai ɗari mai goma suna ta karo karo a biya Alhaji Hashimu kuɗinsa, amma da yake ya so tozartani ya ce ba zai karɓi kuɗi a tsinke ba. Cikin ikon Allah sai gani na yi Hajiya ta kawo kuɗin nan cif, ta ce idan sharri yayi mini, mun barwa Allah.
Muka koma gida, fita ma gagarata take saboda kunya, amma mutane suka dinga mini jaje suna fatan Allah ya saka mini abin da yayi mini.
Bayan faruwar lamarin ne, muka dinga jin mutane na faɗar halin Alhaji Hashimu marasa kyau.
Na mayar da hankali a kan rayuwata da zuwa garejina, sai dai tun da a ƙarƙashin wani nake, ba wani abu nake samu ba.
Ana haka na kuma cewa Hajiya da zan samu dama da na kuma komawa makaranta, Hajiya ta ce "Abu ne mai kyau ai, Allah ya kawo damar"
Kasancewar na san kan Computer na shiga na dinga neman tallafin karatun addinin musulunci a ƙasashen waje.
Sannan na nemi wani a Nigeria.
Tun ina saka ran zan samu har na cire rai.
Lokaci ɗaya na ji hankalina yayi gida, ina son zuwa naga babana, amma na san da zarar na gaya wa Hajiya, ba zata amince ba, dan haka na shirya bata sani ba, na tafi Rano ko da zan je Baba ya koroni na samu na ganshi na ji daɗi.
Sai dai da na je Rano na tarar da Baba cikin hali na rashin lafiya, ga rashin kulawa, Mutanen gidan sabgar gabansu kawai suke yi, suna wadaƙa da kuɗinsa.
Cikin damuwa na samu uwargidan Baba, nace mata "Baba Uwani meyasa ba a kai Baba Asibiti ba? Meya same shi haka?"
Cikin masifa ta ce "Ban sani ba, kai da kazo ai sai ka kai shi, jarababbe ya koreka ya koreka amma ka nace sai ka ce ɗan jaraba, ko da yake ai jinin maita da ka tsotsa a jikin uwarka da rashin zuciya" ban ji haushi ba na tafi wurin ƙannensa, sai dai da ƙyar suka amince aka kai Baba Asibiti.
Kan a kai shi Asibiti, na gyara masa Jikinsa, dan a cikin ƙazanta same shi. Jininsa ne ya hau sosai, baya iya komai da kansa. Aka karɓe shi aka kwantar da shi a Asibiti.
Sai daga baya na kira Hajiya, na sanar da ita abin da ake ci. Aikuwa ta yi faɗa sosai da sosai a kan dan meyasa na tafi ban gaya mata ba. washegari ta biyoni, dan da nufinta ma ta taho da ni, amma halin da ta tarar da Baba a ciki ya sanya tayi sanyi.
Duk wahala da ɗawainiya da Baba ya dinga yi da iyalansa da 'yan uwansa lokacin yana da lafiya, yanzu ba shi da lafiya sun gaza kulawa da shi.
Kuma suka hana a firfito da kayansa da kuɗaɗensa ayi masa magani.
Haka na dinga fama dan ganin Baba ya samu lafiya.
Ko magana baya iya yi, sai dai idan ya buɗe ido ya kalleni yayi ta kuka, har a wannan lokacin ina jin soyayarsa a raina, gaba ɗaya na manta abin da yayi mini, burina kawai na ga Allah ya bashi lafiya.
Jikinsa ya fara kyau yana sauƙi, duk da bakinsa yayi wani iri, amma a haka ya lallaɓa ya fara yi mini magana.
"Gwani, dan Allah ka yafe mini abubuwan da suka faru, ni kaina ban san yadda aka yi hakan ta dinga faruwa ba, a cikin zuciyata ina so da tausayinku amma a zahiri bana iya komai. Dan Allah ka yafe mini Yazid wallahi ina ƙaunarka"
Na rungumeshi a jikina na ce "Baba ka daina wannan maganar, ina ƙaunarka sosai Allah ya baka lafiya".
Ya kuma numfasawa ya ce "Allah ya jiƙan mahaifiyarka da ɗan uwanka. Yazid ba zan yafewa matana ba, ban taɓa tunanin zasu mini abin da suka yi mini ba, sun haɗa kai da 'yan uwana sun cutar da ni duk saboda wannan rufin Asiri da Allah ya yi mini" ya ƙarasa maganar hawaye.
Na rungumeshi ina share masa hawayen, ina jin soyayarsa na sake ratsani da farincikin ganina a tare da shi.
Sai dai ashe sauƙin tafiya ne, da har na samu yayi mini magana, kamar yadda Huzaifa ya cika a kan idona, haka Baba ma ya koma ga Allah a rungume a jikina.
A wannan lokacin zuciyata bushewa ta yi, na kasa kukan ma sai na zuci. Ina ji ina gani gidanmu yanzu bani da kowa, 'yan uwana kuma ganina suke kamar bare a cikinsu.
Sai da aka yi sadakar bakwai, sannan na dawo gida wurin Hajiya.
A daidai wannan lokacin ne kuma, na samu scholarship da na nema na Nigeria, na shiga makaranta da muka haɗu da ke. Kuma mace ta farko da na ji na yarda ki shigo cikin rayuwata, duk da ina jin tsoron sharrin mutane.
A Wannan lokacin, idan bani da kuɗin motar zuwa makaranta, da an idar da sallar asuba, nake fara tafiyar ƙasa in ci ƙarfin tafiya sosai kan na hau mota na ƙarasa. Wataran na tafi cikina babu abinci, ga ciwon so na damuna, ga budurwar tawa da tsiyar tsiwa, kuma malaminmu ya sako ni a gaba. Ya ƙarasa yana murmushi duk da hawaye a fuskarsa.
Ya ɗora da cewar "Ganin tsananin da wahalar ta yi mini yawa, ya sanya Hajiya ta ce lallai na je garinmu ayi batun rabon gado, a raba a bani dan da alama 'yan uwan mahaifina kansu suna zalamar dukiyar kar su cinye su bani abin da suka ga dama.
Ni dai nace ta ƙyaleni kawai, na rasa iyayena balle wata dukiya. Ganin bani da niyyar zuwa ya sanya ita ta je da kanta, suka din ga yi mata gori wai ita a wa?
Aikuwa ta ce tunda ba zasu raba su bani nawa ba, Next da jami'an tsaro zata zo.
An kai ruwa rana kan su yarda a raba gadon nan, dan duk sun cinye abubuwa da dama, ciki har da filina da na Huzaifa da ya saya mana, bayan suna Baba ya gina wa matan ƙaton gidan gona ya ce nasu ne.
Sai a shekarar nan aka raba aka bani abin da ya sauwwaƙa, dan ni ban san yadda aka yi rabon ba. Dan Hajiya ta so ta ɗaga maganar filin Huzaifa na ce ta yi haƙuri ta ƙyalesu.
Bai fi watanni da rabon ba, sai gashi Allah ya kawo aurena da ke, Hajiya ba ta so, saboda abin da ya faru tsakanina da Alhaji Hashimu gani take masu kuɗi duk basu da kirki duba da wahalar da muka sha a baya da gaza samun taimako, amma na ce tayi mini Addu'a ni ina so.
Aka je aka sayar da abin da na samu na gado, aka sai wannan gidan da duk kayan da ki ka gani a ciki.
Fadila ba ta san iya adadin hawayen da ta zubar ba kan Yazid ya gama bata labarin ba, bata tunanin ta taɓa jin abin ban tausayi kamar wannan, ko lokacin da gari ya cika da labarin Widad 'yar gidan Alhaji Nasir Daula irin wahalar da mijinta Yusuf ya sha a rayuwa bata tunanin ta kai wadda Yazid ya sha. (Mai son ya ji waccece ƙaddarar Widad da Yusuf ya nemi book ɗin Aƙidata)
Sosai Yazid yake kuka, har ya fara tari, Fadila ta saka hannayeta biyu ta tallafo fuskar Yazid ta na goge masa hawaye.
A sanyaye ta ce "Allah ya jiƙan Inna da Huzaifa da kuma Baba"
Jinjina mata kai yayi ya kasa Magana.
"Bari na shimfiɗa mana bargo a falo, saboda na ji kana tari akwai zafi a nan sosai" ya ɗaga mata kai.
Ta ɗau bargo, ta je falo ta shimfiɗa musu, ta kai musu pillow.
Ta dawo cikin kulawa kamar ta goya Yazid, ta kamo hannun Yazid zuwa falo, ya nemi wuri ya kwanta yayi shiru yana jin yadda komai ke dawowa kwanyarsa kamar yanzu ake yi.
"Dan Allah ka daina kuka ka ji" ya share hawayen fuskarsa ya ce "To"
Ta cigaba da goge masa hawayen, wani irin tausayinsa na ratsa lungu da saƙo ma zuciyarta.
Taɓa shi ta kuma yi, ta ji yayi bacci ma a haka. Ta tashi zaune tana kallon in da yake kwance.
Ta saka hannu ta toshe bakinta, ta koma gefe ta fashe da kuka.
A hankali ta ce "I don't know what you are going through, na sake jefa ka a damuwa, na dinga yi maka wulaƙanci. Allah sarki kullum fuskarka cikin murmushi ba mai cewa you are going through all this hardship.
Na dinga yi wa yanayinka dariya, kana taimakona, kana kulawa da ni, amma nake ta maka wulaƙanci, ƙila da a lokacin na san halin da kake ciki da na taimaka maka.
Mutane da yawa muna ganin murmushinsu, ba tare da mun san meye a ƙasan zukatansu ba, wani kyautatawarmu ita kaɗai ce silar farincikinsu.
Why would I do all this to him, bai kamata ba abin da na yi, bayan wahalar da yake ciki".
Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi ta koma kan shimfiɗar su, shi tuni yayi baccinsa ma.
Kwanciya ta yi a jikinsa, ta rungumeshi sosai tana kuka.
Allah sarki wataƙila akwai ire-iren wanda suke a irin halin da Yazid ya ke ciki, suka je neman taimako gidansu amma Mummy ta hana.
Lokacin ji take da zata haɗu da waɗanda suka zalinci Yazid a rayuwarsa sai ta rama masa.
"Am sorry Yazid, in sha Allah ba zan rabu da kai ba, ina son ka yi farinciki ba zan sake barin na kuma kuskuren saka ka a dmauwa ba, wadda ka shiga a baya ma ta isa" haka tayi ta surutai tana kuka!.
Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA
08081012143
80
Gaba ɗaya idon Fadila ya bushe, bacci ya ƙaurecwa idonta sai tunani da koke-koke, Yazid kuwa baccinsa yake dan yau ko damar tashi sallar dare bai yi ba.
Sai gefin Asuba sannan ta samu bacci ya ɗauketa.
Kan Yazid ya fita sallar Asuba ya tashe ta, amma har ya je ya dawo ba ta tashi ba.
"Habibty, ki tashi gari ya yi haske amma baki yi salla ba". Da ƙyar Fadila ta iya tashi, saboda yadda jikinta duk ya mutu, ga kuma rashin bacci da ba ta samu ba jiyan.
Da ƙyar ta iya tashi tayi alwala ta zo ta yi salla, tana idarwa ta kuma kwanciya a kan bargon ta takure jikinta ta cigaba da bacci.
Yazid ya 6 "Fadila ko azkar fa baki yi ba, kika kuma kwanciya" yayi maganar yana ɗagota.
'Ni dan Allah ka ƙyaleni bacci nake ji" tayi maganar a shagwaɓe tana sake lumshe ido.
Cikin rarrashi ya ce "Dan Allah a tashi ayi azkar, sai ki cigaba da baccin". Zamewa tayi daga jikinsa, ta kuma kwanciya tana lumshe ido, kallonta yayi yana murmushi, yana sake jin sonta da ƙaunarta a cikin zuciyarsa.
Amina kuwa kwanakinsu huɗu a Saudiyya, Amina jinta take kamar ba ita ba, wai ita ce yau a ƙasa mai tsarki Allah sarki rayuwa.
Babban abin da ya ƙara farantawa Amina rai, shi ne yadda Alhaji Ahmad ya biya kuɗin umara har Inno, ga Hajara da su Zakiru.
Amina ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, sai dai tun a Nigeria Amina ta fuskanci tana da ciki, sai rashin lafiya ta ke yi a tsaitsaye, amma tayi shiru da bakinta ba wanda ta bari ya gane, ga zazzaɓin dare da yake damunta, amma ta mayar da hankali a kan ibadarta sosai da sosai, tana gaya wa Allah buƙatunta.
Khalil ma ya bar Kano, suna can Abuja da shi da Hafsa, yana tattalinta da kuma cikin da yak jikinta, gefe guda kuma ga shirin bikin Abdul da suke ta yi.
A hankali tayi juyi, ta jiyo Yazid yana ta aiki a tsakar gida, ya gama komai na aikace-aikace, ta tashi jikinta duk a mace, ta naɗe bargon ta kai ɗaki, ta shiga toilet ɗin bedroom ta hi brush ta dawo tsakar gida ta kalleshi ta ce "Sannu da aiki"
Ya ɗago ya kalleta ya ce "Yauwa Madam, baccin ya isheki?"
'Alhamdilillah, ya isheni yunwa nake ji dai"
Yazid ya ce "Ga kunu na dama, na sayo mana dankali naga kamar kin gaji da ƙosan"
Fadila ta ƙarasa tana leƙa Kitchen ɗin ta ce "Nuna mini yakake dama kunun?"
Yazid ya ce "Ai na gama, da kin ta so tun ɗazu da kin gani" kuma leƙawa ta yi, ta hango ɗan ƙaramin buhun shinkafa, da galan ɗin mai ga kuma kayan miya, duk a Kitchen ɗin.
Zama tayi a kusa da shi ta ce "A