Showing 207001 words to 210000 words out of 296192 words
musu da shi, a ka tura shi Naija state service.
Komai daga gidansu Ahmad ake kai mata, Gwaggo ta saka a canza mata makarata ta cigaba da zuwa.
Bayan aurensu Ahmad ya fuskanci Zainab ba ta da kunya ko kaɗan, Shegiyar tsiwa ce da ita, amma yayi haƙuri saboda kullum Gwaggo cikin ja masa kunne take.
"Ahmad Zainab amanat ce, idan kaci amana amanar mahaifiyarka kaci, kaga marainiya ce, idan ka zalunceta Allah zai saka mata" hakan ya sanya ya dage duk abin da Zainab take so shi yake yi mata.
A haka ya gama service, ya kan gayawa Abokinsa Abubakar abin da Zainab take masa na rashin kunya, kasancewar shi Abubakar ya riga shi aure, amma yayi ta bashi baki yana bashi haƙuri.
Anyi aurensu babu daɗewa, mahaifinsu Ahmad ya rasu, aikuwa sun girgiza ba su kaɗai ba har mutanen unguwa, da sauran iyalinsu.
Kowa yafi tausayawa Ahmad, kasancewar sa ɗan gaban goshin Alhaji Musa.
Bayan sadakar bakwai, ya koma garin da yake bautar ƙasa.
Bayan mahaifinsu yayi arba'in, aka raba musu gado, aikuwa sun sami dukiya kamar kamar me, ya samu dukiya mai yawa, Zainab sai buɗa hanci ake.
Duk da rashin kunya na Zainab, amma tana girmama Gwaggo sosai da sosai.
Ahmad ya dawo ba daɗewa, ya nemi ya cigaba da karatu, ya samu admission a BUK, ya ce yana son ya tafi karatu. A wannan lokacin Zainab ta samu cikin ta na fari, lokacin ko Sakandire bata kammala ba.
Kasancewar Ahmad ya samu rumfuna a kasuwannin Kano, ya sanya ya haɗa karatunsa da kasuwanci a Kano.
Bayan ta haihu ta haifi namiji, Ahmad ya sakawa yaron sunan mahaifin Hajiya Sadiya Ibrahim ake kiransa da Khalil.
Tun bayan da Zainab ta haihu, ta fara tsiro da rashin mutunci iri iri, ko gidanta bata son aje, dama 'yan gidansu wulaƙantasu take yi son ranta.
Tana gama Sakandire, tabi Ahmad Kano, in da ya sai musu gida a can suka zauna.
Zuwanta Kano ya sanya ta sake kilewa, ta fara tsiro masa da rashin mutunci, tun bayan haɗuwarta da su Hajiya Turai da Salma.
Suka dinga hure mata kunne, da nuna mata dangin miji da iyayensa ba abin riƙewa bane, shi kansa mijin idan ta fiye sake masa sai ya rainata.
Daga baya suka koya mata ko inda take ya zo, sai ya biyata kuɗi kan ta amince da shi, iskanci kala kala.
Tun yana haƙuri har ya fara gayawa Hajiya Halima, saboda yafi ɗasawa da ita fiye da Gwaggo.
Tayi wa Gwaggo maganar, amma ta ce yayi haƙuri, marainiya ce.
Ya zamana ta watsar da su Gwaggon ma, ta daina bi ta kansu, idan 'yan uwan Ahmad suka zo, ta dinga haɗe rai kenan tana yi musu wulaƙanci, tare da kora hali.
Su Hajiya Turai suka koya mata bin malamai, duk yadda Ahmad yake da biyayya da son iyayensa, amma sai ya shafe lokaci bai je ba.
Hajiya Sadiya ta fara magantuwa, saboda shaƙuwarta da Ahmad, tayi ta mita Gwaggo tayi ta bata haƙuri.
A haka Gwaggo ma tayi ciwo na sati biyu Allah ya karɓi abarsa.
Ahmad yayi kuka kamar babu gobe, a haka aka share zaman makoki.
Nan rashin mutuncin Zainab ya ƙaru, dama Saboda Gwaggon ne ya sanya take ɗaga ƙafa a wasu abubuwan.
Bayan rasuwar Gwaggo, Ahmad sai ya shafe wata biyar bai je Jigawa ba, dan tun bayan da ya kammala karatu, yaji daɗin Kano yayi zamansa, shima Hajiya Zainab ce ta takura masa ita ba zata koma Jigawa ba ya barta a Kano. Haka shima ya zauna a Kano.
Ana haka abokin mahaifin Ahmad, ya sa aka yiwa Ahmad ɗin Minister, da ƙananun shekaru, zo kaga bakin Zainab mijinta ya zama Minister.
Duk ranar da yaje Dutse, abune mawuyaci Hajiya Saidya ba tayi kuka ba, tana son Ahmad kamar yadda take son 'ya'yanta, ba zata manta karamcin mahaifiyarsa a gareta ba, amma ƙiri-ƙiri mace ta raba su, duk da shaƙiwar dake tsakaninsu.
Wataran tare suke kukan ya ce "Hajiya ki dinga yi mini Addu'a, ki daina yi mini kuka"
Ta kan ce "Addu'a kullum cikinta muke, Allah yayi maka albarka"
Ya tattara Zainab suka koma Abuja da zama.
Sai dai ya fara damuwa da rashin haihuwa da ba ta sake yi ba, ga Khalil ya girma, saboda Ahmad mutum ne mai matuƙar son yara.
Ta kance kar ya dameta Allah ne bai kawo mata ba, nan kuwa planing tayi, sai da Ahmad ya shekara Bakwai sannan ta samu ciki.
Bayan ta haihu, ta haifi mace ya ce tunda Gwaggo bata raye, bari ya yiwa Hajiya takwara ya sakamata Sadiya, aikuwa tayi tsalle ta dire ta ce bai isa ba, ba za a sakawa 'yar ta wannan sunan ba Fadila take so a saka mata.
Saboda a zauna lafiya, haka ya sakawa yarinyar Fadila, duk so da ƙaunar da familynsu ke da shi, a junansu haka suka zuba masa ido, suka bar shi da iyalinsa, kowa ya daina zuwa in da suke saboda tijarar Zainab.
Duk kyautar Alhaji Ahmad, da son 'yan uwansa, daga baya sai wanda ta ga dama yake iya yiwa kyauta, gashi Allah ya ɗaukaka shi a danginsu, babu mai kuɗinsa da shahararsa ga shi suna matuƙar ƙaunarsa, amma mace ta mallake shi.
Aka bata shawarar kar ta sake haihuwa, yara biyu sun isheta rayuwa, tun da Allah ya bata kowane jinsi, aikuwa haka ta dinga zabga planing sai da haihuwa ta ɗauke gaba ɗaya.
Tun Alhaji Ahmad yana saka ran zata kuma haihuwa, har ya fidda rai.
Duk ranar da Allah yasa suka je Jigawa, Hajiya Sadiya kamar ta cinye Fadila, tana ƙaunar 'yar Yarinyar saboda tana kama da Gwaggo, amma Zainab ta dinga nuna kamar ƙyamarsu take ma. Dama tunda mahaifinta ya rasu, ta watsar da 'yan gidansu, ko ta kansu bata bi.
A haka har rasuwar Hajiya Sadiya, zuwa wannan lokaci Zainab haka take shimfiɗa mulki son ranta, sai abin da take so za ayi.
Wasu lokutan Alhaji Ahmad saboda maganar mahaifiyarsa, yake ɗaga mata ƙafa, da tayi ta ja masa kunne a kan maraicin Zainab, wasu lokutan kuma shi kansa bai san yadda wasu abubuwan suke faruwa ba.
Amina sai da ta zubar da hawaye, na tausayin Alhaji Ahmad da iyayensa mata, mussaman da taji Hajiya Sadiya har kuka take yi, saboda rabasu da ɗansu da Hajiya Zainab tayi.
Sai la'asar sannan suma mota ta kwashe su zuwa gida.
Bayan Amina ta gyara part ɗinta, ta dinga tunani a kan yadda zata ɓullowa al'amuran.
"Lokaci yayi, da komai zai zo ƙarshe da yardar Allah!"
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA. GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
65
Daddy bai dawo ba sai bayan magariba, abin da ya bashi mamaki, bai wuce yadda ya tarar da su Hajiya Turai a gidan ba. Suka bishi da kallon banza. Wanda a baya har rige-rigen gaisheshi suke yi.
Bai kulasu ba, ya wuce sashinsa, inda Amina take.
Tun daga hanyar sashin, wani irin sassanyan ƙamshi na musamman yake dukan hancinsa, ya shiga falon da sallama, amma bata nan.
Ya miƙa ya nufi bedroom ɗin, yana buɗewa kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Amina tana rera Karatun Alqur'ani mai girma.
Zuwa ya yi ya zauna a kusa da ita, ta cigaba da karatunta, a hankali ya kwanta a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa yana jin yadda take zuba karatun Alqur'ani da ka.
Sai da ta kai aya ta idar, sannan ta kalleshi ta ɗan shafi gemunsa ta ce "Babyna, sannu da zuwa"
"Yauwa sayyada, kamar kar ki daina karatun nan Meenal"
Murmushi tayi ta shafa kansa ta ce "Meyasa baka dawo gida ba kaci Abinci?"
"Bana son na takura miki ne, naga kina da baƙi, naje na saka a gyara in da aka sauki baƙi, na tarar sun gyara komai fes, ya kika ga familyn namu, ina fatan dai ba wata matsala?"
"Ba wata matsala, naji daɗin zuwansu sun ɗebe mini kewa sosai, yaushe zaka kaini Dutse?"
"Very soon, ina son muje honeymoon ko 2weeks ne, da mun dawo sai na kai ki"
Amina ta ce "Mmm, meye Honeymoon?"
"Ban sani ba, Baby zamu samo" dariya tayi tana jan hancinsa, sannan ta ce "Amm na manta, ga kayan garata can, ina son a ɗebar musu nasu, a samu ko aika musu ne ayi"
Tashi yayi zaune da mamaki ya kalleta ya ce "Gara kuma, wace irin gara?"
"Gara mana da ake yiwa mace idan tayi aure"
"Haba Amina, wato zuwa kika yi kika saka Baba a gaba yayi miki gara ko, ni nace miki ina son gara ne?"
Tsuke fuska tayi ta ce "To ni na san zasu kawo ne, kawai fa gani nayi an kawo"
"Na san halinki, ki gaya mini gaskiya"
Kwaɓe fuska tayi za ta yi masa kuka, ya ce "Ya isa shikenan, zan saka a kwashe a mayar gaskiya, ai abin kunya ne a gareni ace dan na auri 'ya sai an mata gara"
"Yanzu Daddy ko kara ba zaka yi mini ba sai kasa a kwashi kayan a mayar? Wato kafi ƙarfin iyayena su bamu abu ko? Kar ka manta ni kaɗai suka mallaka komai suka samu dole ni zasu yiwa, amma bakomai na gode"
Ganin tayi fushi ya sanya ya sassauta murya ya ce "Babyna ba haka nake nufi ba, kiyi haƙuri dan Allah, na fasa a mayar ɗin komai ya wuce please"
Sake haɗe rai tayi ta kawar da kai.
Ya sake kwantar da murya ya ce "Haba tawan, smile mana, i have some candy for you"
"Cin hanci zaka bani"
"Eh, mana in dai zai sanya ki huce"
"Hmmm to shikenan, na haƙura tashi muje aci Abinci" ya miƙe ta riƙo hannunsa suka fita falo.
Bayan ya gama cin abincin ya nutsu ta ce "Daddy lefe na yayi kyau sosai, Allah ya ƙara arziƙi, ina ga da zai yiwu da Khalil ma ya tara nasa a wurin Anty Maryam, ba laifi ta iya zaɓe ta san kan kaya"
Daddy ya ce "Haka ne, wannan kuma ke zaki baki shi shawara, ni yanzu damuwata gininsa da ya tsaya yi masa iyayi da ƙaƙale, ya hanzarta yayi abin da zai yi ayi bikin, tun kan uwarsa ta hana"
Amina ta ce "Ta hana kuma, Daddy sai ka bari a fasa auren idan ta hana duk da kaje kayi magana ka kai musu kuɗin aure?"
"To Meenal ya zan yi? Kina kallon yadda nake ta fama da ita ai, tunda Allah ya sanya ta san aure muka yi, take tayar mini da hankali, ita kanta taƙi bari nata hankalin ya kwanta, na ma rasa yadda zan yi"
"To ai koma menene yake faruwa duk laifinka ne"
"Laifina kamar yaya?"
"Da ita da yaranta duk a ƙarƙashin ka suke, amma ka sakar mata ragamar gidan, sai abin da ta zartar, yakamata ka dinga tauna tsakuwa dannaya taji tsoro, ba a komai ya kamata ka dinga bari ana jayayya da kai ba, ba zigaka nake ba amma when it comes to serious issues, you have to be so serious, ba wai sai abin da suke so ba, batun auren Khalil idan ka bari aka fasa saboda mahaifiyarsa ba ayiwa yarinyar adalci ba"
Daddy ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Haka ne maganarki, in Allah ya yarda babu wani abi da zai faru, za ayi auren da yardar Allah, ni ban gaya miki wani abu bama, wani abokina ne da matarsa ta rasu, yake neman ya samu mace mai hankali wadda zata iya kula masa da yaran, duk da yaran ba ƙanana bane ba duk sun manyanta, wallahi nayi masa sha'awar auren sirikar Khalil, matar ba wata babba bace tana da ƙuruciya sosai gata jajirtacciya kuma nutsatsiya, bana son yin magana taga kamar na yi mata wulaƙanci ko na rainata, da na haɗa su"
Amina ta gyara zama ta ce "Kai amma naji daɗi, nifa tun da ka gaya mini halin da suke ciki, nake jin rausayinsu wallahi.
Yanzu abin da za ayi shi ne, ka yiwa abokin naka maganarta, amma sai ka ɗauke shi kuje a matsayin kun je da niyyar batun auren su Khalil, irin ko suna buƙatar wani abu, ko kuma dai makamnacin haka, kaga zai ganta a nan, idan tayi masa daga baya shi sai ya koma, idan ta amince shikenan idan bata amince ba shikenan".
Daddy kawai yayi shiru yana kallon Amina.
"Ya kuma naga kana kallona?"
"Kawai ina jinjinawa basirarki ne, ke har kin lissafa kin samo solution, to shikenan hakan za ayi, Allah ya sa su daidaita".
"Amin Daddy, kaima Allah ya baka lada"
Da daddaren ya sake komawa wurin Hajiya Zainab, wannan karon ya tarar da ƙofarta a buɗe.
"Meyasa kike rufe ƙofar ki ne?"
"Saboda bana ƙaunar ganinka"
Daddy ya ce "Ai ba sai kin faɗa ba na sani. Na zo ne na sauke nauyi, duk da yakamata na haɗaku nayi muku nasiha, amma na san halinki sai kinyi abin da zaki zubarwa da kanki mutunci a gaban yarinya, dan haka nazo na sameki ni da ke. Ina magana ne a kan batun rabon kwana ke da abokiyar zamanki, tunda babu buƙatar spending seven days ɗin nan, tunda koma dai menene ya riga ya faru".
"Dawa kake tunanin zaka raba kwana ni? Ba dai ni ba ka daina wannan tunanin kuma ka tashi ka bar mini ɗakina tun muna sheda juna da kai, kaje na sallama mata bana buƙatar ka"
"Idan ke ba kya buƙatata, ni ina buƙatarki, ba zaki saka in zalunceki ki barni da hakkinki ba"
Ta kalleshi sheƙeƙe ta ce "Au, wai kai nan har wani hakki ka sani, ka san daida da ba daidai ba? Kai ko kunya ba ka ji ba, dan Allah ɓace mini daga ɗakina, bana buƙatar ko kallon fuskarka"
"Shikenan, kiyi abin da kike so, ni zan yanke abin da naga ya dace, sannan ina saka ran next week zamu bar ƙasar nan tare da Amina, amma ba zamu daɗe ba, baifi muyi 2weeks ba mu dawo".
"Ku bar duniyar ma idan kaga dama, aikin banza kawai, kuma wallahi ina sake jan kunneka a kan auren da zaka yiwa Khalil, wallahi idan baka janye Maganar nan ba komai ya biyo baya ka kuka da kanka"
Daddy ya girgiza kai ya ce "Ɗanki ne dai, idan kika yi masa baki Allah ya jarrabeshi da auren mace irinki, kanki abin zai dawo"
A fusace ta miƙe ta ce "Me kake nufi da auren mace irina? Kana nufin ni mutuniyar banza ce?"
"Wannan kuma ke zaki wa kanki alƙalanci" ya juya ya fice ya bar mata ɗakin.
"Kan uba, lallai ma mutumin nan"
Daddy wurin Khalil ya nufa, ya tarar da shi a falonsa, yana ta waya har Daddyn ya shigo bai sani ba.
"Kai Magana na zo muyi fa" Khalil yayi firgigit, ya katse wayar ya hau sosa kai ya ce "Yi haƙuri Daddy, ban san kana nan ba.
"Dama ina zaka san na zo, kana nan kana soyayya" shafa kai Khalil yayi yana shafa kansa.
Daddy ya zauna a kusa da Khalil ya ce "Ya 'yar tawa, ina fatan tana nan lafiya"
"Tana lafiya lau, kalau Daddy, tana cewa ma in gaisheka"
"Amma ai baka gaya mini" Khalil yayi murmushi yana shafa kai.
"To yanzu kai meye shirinka? Kasan ba a saka wani dogon lokaci ba"
"To, dama Daddy batun ginina na ajiye cigaba da ginina saboda a baya naga kamar ba zan samu Hafsa ba, amma to yanzu dai zan cigaba da ginin, sai kuma batun kayan lefen".
Daddy ya ce "Ai kaine Khalil, wannan gida naka ka janyo ƙaƙale ƙaƙale da yawa, bana tunanin zai kammla kan lokacin, amma lefen Amina ta ce nata da Hajiya Maryam ta haɗa mata sun yi kyau sosai, ko kaima kuɗin zaka bayar idan ya so ta faɗi duk abin da take so a saya mata"
"Shikenan Daddy, duk yadda ka ce yayi, idan kuɗin ne sai na tura"
"To babu laifi, sai kuma magana ta biyu, duk yadda ake ciki ka tattara kayanka ka bar garin nan gobe in Allah ya kaimu, idan ba haka ba kuwa mahaifiyarka zata iya hana auren nan"
Khalil yayi saroro yana kallon Daddy.
Daddy ya ce "Ƙwarai kuwa, tun wuri ka koma duk abin da ake ciki ma dinga waya kawai"
Khalil yayi ajiyar zuciya, dan har ga Allah yana son cigaba da zuwa wurin Hafsa, dan su cigaba da samun shaƙuwa da fahimtar juna.
Jiki a sanyaye ya ce "To shikenan Daddy, zan koma in Allah ya yarda"
"Yauwa, Allah ya taimaka ya sanya albarka"
"Amin Daddy na gode sosai"
Daddy ya yi masa sallama ya koma wurin Amina.
Bayan tafiyar Daddy, Khalil ya ƙudurce gobe da Safe zai ɗau mota ya koma Abuja, ba sai ya jira jirgi ba, karma Mummy ta zo da wani batun da zai zama barazana ga aurensa.
Idan yana tare da Amina mantawa yake da komai, yaji kamar babu abin da yake damunsa, saboda yadda take tattalinsa take kula da shi, shi kansa har mamakin irin tsananin son da yake mata yake.
A duk lokacin da ta ganshi cikin walwala da fara'a ta kan yi amfani da wannan damar, wurin tuntar da shi abubuwa, da ɗora shi a kan hanyar da ta dace, yadda yakamata yayi wa kansa guzurin lahira a dukiyarsa tun yana raye.
A 'yan kwanakin da ya kasance tare da Amina, tunda ta tare duk wanda ya zo gidan nan, sai Amina ta bashi kuɗin mota, sai tayi girkin Abinci ta bawa mutum ya ci ya ƙoshi, sannan ya baka kuɗi.
Daddy yana ajiye kuɗi a ɗakinta sosai, kuma ya mata izinin yin amfani da su, dan haka ta samu damar yin kyauta sosai.
Washegari ta kasance Litinin ce, Khalil ya kintsa kayansa ya tafi wurin Mummy da sassafe zai yi mata sallama ya tafi.
Wani irin kallon bamza tayi masa sanan ta ce "Daga zuwanka har ka gama kwanakin zaka tattara kayanka ka koma ko Khalil. To ina sake jadadda maka ina nan daram a kan bakana, muddin kayi wannan auren sai dai ka nemi wata uwar, dan ba zan cigaba da amsa sunan uwarka ba, tunda ka zaɓi ubanka a kaina, shi yake hure maka kunne"
A sanyaye ya ce "Mummy ba haka bane ba, wurin aikine ake nemana"
"Rufe mini baki ni, koma waye yake nemanka kaje ka ƙarata, amma zaka dawo ka sameni, kuma aurene ba ka isa ka auri 'yar matsiyata ba, zan gani idan ina da muhimmanci a wurinka"
Jiki a saɓule Khalil ya tashi, ko wurin Abdul bai je ba, saboda safiya ce, balle Hafsa duk ya bari a ransa yayi musu sallama ta waya, shirye-shirye kuma sa cigaba da yi ta waya, amma jikinsa yayi sanyi da inkarin da Mummy take, na idan yayi auren nan ba shi ba ita.
Tayi mamaki ƙwarai, da Khalil bai nuna wata nadama ba, ya sa kai ya fice babu alamar zai janye batun auren nan.
Abin ya ƙular da ita sosai da sosai, miƙewa tayi ta nufi sashin Daddy, tana zuwa