Showing 87001 words to 90000 words out of 296192 words
idanu in ga in da ka saka gaba, Hajiya Salma da Turai sun je duba shago, suka ganoka a gaban kaskon awara, suna kallonka kuka hau napep, saboda kalen tsiya kuka tafi, har wurin suka je suka tambayar mini, aka ce kana zuwa wurinta wai sonta kake, wallahi Khalil ka bani kunya, kamar bani na haifeka, ko ka manta matsayin ubanka a ƙasar nan? Babu 'yar wanda zaka kalla a manyan attajiran ƙasar nan a hanaka, amma saboda lalacewa da rashin sanin darajar kai, saboda tsiya, bama 'yar masu abinci a restaurant ba, mai soya awara a titi, ashe ita ce gayyara tsiyar da kazo da ita nan kana ci ran nan ko, an maka barbaɗe a ciki ka ci, idan takensu sammako ni a tafe na kwana, ni Zainab ban durƙusa na haifi ɗan da zai kawo mini jinin matsiyat ba, daga kai har ita zan yi maganinku, zan tsananta bincike a kan yarinyar".
Kamar Khalil zai ɗora hannu a ka cikin mariraicewa ya ce "Mummy, dan girman Allah kar ki yiwa Hafsa komai, ba ta da laifi ni na kai kana nace ina so"
"Zaka rufen baki ko saina falla maka mari, sakarai sususu, dalla ɓace daga gabana ka bar mini falo, zan ga uban da ya tsaya mata har ta liƙe maka"
"Dan Allah Mummy ni ki hukunta ni, marainiya ce fa"
"Khalil ni nake faɗa kana faɗa? Zan kwarara maka ashar fita ka bar mini falo" ta ƙarasa maganar a fusace tana nuna masa hanyar fita. A sanyaye Khalil ya fice, yana jin yadda wani abu ya tokare masa ƙirji saboda tsananin damuwa da ɓacin rai.
Amina ta sha jinin jikinta, ta tsorata da irin ƙyamar da take yiwa talaka, ta rasa me talaka yayi mata tayi masa wannan tsanar haka, ɗanta na cikinta ta saka a gaba, ta ƙare masa cin mutunci saboda ya nuna yana son 'yar talaka, ƙiyyyar ta wuce misali.
Fadila kuwa tana tare da Mummy aka kirata a waya aka sanar mata da anga Khalil, tare da mai awara, dan haka bata ji tausayin abin da Mummy ta yiwa Khalil ba musamman idan ta tuna yadda ya watsa mata ƙasa a ido, a kan soyayyar da Yusra take nuna masa.
Khalil kuwa wani irin gumi ne ya dinga tsatsatfo masa, saboda azanar tashin hankali, dama ya san a rina, amma yaso ace shi da kansa ya lallaɓata ya sanar da ita, amma wannan algunguman matan suka ɓata masa komai. A gaskiya yana son Hafsa, sai dai ya san babu yadda za ayi ya samu goyon bayan Daddy, muddin ba Mummy ce ta amince ba.
Ya tashi zaune yayi shiru, yana cigaba da tunani, wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, ya gama gwagwarmayar samo soyayyar Hafsa da ƙyar, a lokacin da ya ke ƙoƙarin ya miƙa hannu ya kamota kuma, Mummy na ƙoƙarin shiga tsakani.
Hafsa kuwa cike da murna ta dinga bubbuɗa kayan da Khalil ya saya mata, turaruka da kayan kwalliya, sai kuma kwalin sabuwar waya mai tsadar gaske.
Ta dinga murna tana jujjuya wayar nan, tana yiwa Allah godiya ashe ita ma zata yi ta'amalli da kayan zamanin nan.
Vibrating ɗin wayarsa ce ya dawo shi daga tunanin da yake yi, ya kai idanunsa kan screen ɗin wayar yaga beauty. Ji yayi kamar kar ya ɗaga, amma ya miƙa hannu ya ɗauka cikin dakiya ya ce "Baby"
"Sweetheart, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da alkhairi, waya na gani sabuwa dal har da layuka guda biyu, Allah ya ƙara maka lafiyar neman halal, Allah yaja kwanan mahaifanka, ya biya musu buƙatunsu na alkhairi ya kare su a duka in da suke, yadda kake faranta mini, Allah yasa ka shiga aljanna kafaɗa da kafaɗa da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kamar yadda ya alƙwaratawa masu kula da maraya"
Gaba ɗaya jikin Khalil yayi sanyi, idan Allah ya karɓi Addu'ar Hafsa, yasan ya gama dacewa a duniya da lahira, macen da tun kan ya aureta komai ƙanƙantar kyauta ta dinga kwarara masa addu'a kenan, ina ga idan ya aureta, Hafsa bata taɓa roƙarsa komai ba, kai hasali ma ita kanta tana ƙoƙarin ganin ta bashi kyautuka, duk da arzikin da yake da shi, lokaci lokaci, sai ta saka masa katin ɗari biyar wai ga rabonsa nan, yau tayi ciniki sosai.
Wani irin ƙaunarta ya ƙara dabaibaye zuciyarsa, a hankali ya ce "Tare da ke Babyna"
"Ya naji muryarka kamar baka walwala, lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙalau, bacci kawai nake ji"
"Ok, to bari in barka sai da safe, ka kwanta"
Yayi saurin cewa'No, ki yi mini hira mana, raina ne babu daɗi"
Cikin damuwa ta ce "Subhanallah, ko na ɓata maka rai ne kan ka tafi?"
"Haba, ni da kika faranta mini mana, ba abin da kika yi mini"
"To Alhamdilillah, Allah ya yaye maka damuwarka, ka san shi ɗan Adam dama ba a ƙyaleshi haka, sai dai ka kasance mai yawan godiya ga Allah, da kuma ambatonsa a halin daɗi ko akasin haka"
Khalil ya lumshe idanunsa yana sauraron bayananta sannan ya furta "Ina sonki Hafsa, dan Allah duk ƙalubalen da zamu fuskanta kar ki rabu dani, na saba da jin daɗin kasancewata da ke, musamman yadda kike kwantar mini da hankali. Kina da haƙuri sosai da hankali, ni dai ina sonki"
"Nima ina sonka, dan kama fini haƙuri, ka kwanta kayi bacci"
"Allah ya tashemu lafiya"
Ta amsa masa da Amin.
Ya ajiye wayar, ya rintse idanunsa yana hango irin halin da zai shiga, idan aka raba shi da Hafsa, ita kanta yana tausaya mata, saboda tana matuƙar son sa, kuma ta saka ran samun afuwar rayuwa ita da mahaifiyarta saboda shigowar sa rayuwarsu.
Hajiya Zainab kuwa har ta kwanata tana mita da banbami, a kan abin kunyar da a ganinta Khalil yake shirin janyo musu, musamman a cikin ƙawayenta, haka ta cigaba da communicating da su Hajiya Turai, suna cigaba da zigata, a kan duk yadda za tayi ta yi ta raba Khalil da yarinyar nan, dan kar ya ja nata abin kunya, kuma kar ayi masa asiri a mallake mata shi.
Amina kuwa ta gama tsinkewa da lamarin Hajiya Zainab, dan bata taɓa zaton al'amarin zai yi zafi haka ba.
Washegari Amina tayi shirinta cikin doguwar rigar da Maman Azima ta bata, ta tafi makaranta, kasancewar lesson ne kawai ba da uniform suke zuwa ba, bada ban Alhaji Ahmad ya rarrasheta a kan ta yi haƙuri, ta cigaba da Zuwa lesson ba, da babu abin da zai sanya ta kuma zuwa, dan gaba ɗaya ta gaji da yawon lesson ɗin nan.
Ta bayan layin gidan tabi, sai dai duk da kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce, akwai wanda suke masu ƙaramin ƙarfi ne a unguwar, wasu tsirarin mutane ta gano a ƙofar wani gida, ana ta fito da kayan cikin gidan waje, wata mata da tsohon ciki da yara kusan biyar suna gefe sunata kuka, yayin da wani mutum da alama shine mijinta, yake ta rirriƙe wani mutum yana bashi haƙuri tamkar zaiwa mutumin sujjada.
Amina sai ta tsaya tana kallon ikon Allah, wasu tsirarin mutane kasancewar safiya ce, suka tsaya suna taya mutumin bada haƙuri, shi kuma wanda ake bawa haƙurin sai kumfar baki yake yi "Wannan wane irin wulaƙanci ne? Tun yaushe kuɗin nasu ya ƙare, amma ƙaryar yau daban ta gobe daban yaƙi biya, gaskiya ba wani ɗaga ƙafa, akwai mutane a ƙasa suna neman gidan nan, kuma ma sayar da gidan zan yi"
"Dan girman Allah ka taimaka mini, maiɗakina tana watanta na haihuwa, idan Allah ya sauketa lafiya, kan nan na samu kuɗin biyaka, ka san asara na tafka kwanan nan a kasuwa, na gobara da ta ƙona mini kaya"
"Kaga ni fa sayar da gidana zan yi, idan ka samu kuɗinka kawai ka kama wani gidan"
Kasa jurewa Amina tayi, kawai ta wuce su ta tafi makaranta, tana tafe tana kuka, tare da tausaya wa mutumin nan da iyalansa, tabbas talauci babu daɗi, da ana taimako yadda Yakamata, masu kuɗin dake unguwar nan zasu iya sai wa kowane talaka gida, saboda sun ninka talakawan dake unguwar yawa, amma kowa kansa ya sani, sai ranar juma'a zaka ga can gidan ana rabon gurasa can gidan ana rabon alala.
Amina ta dinga jin inama ita wata ce, yadda ta san raɗaɗin talauci, idan Allah ya yi mata arziki ba zata taɓa barin na kusa da ita a wahala ba.
A haka ta ƙarasa makarantar, da tunane tunane daban daban a zuciyarta, tare da fatan Allah ya bata nasara a rayuwa ta zama wata.
Yazid ya nemi afuwar su Amra, na rashin samun damar tsayawa jiya ya koya musu assignment ɗin su, sai yau ya tsaya yana koya musu, Fadila na hango shi, amma ba ta nuna tama ganshi ba, balle ta kula shi, sai da ya gama da su sannan ya taho wurinta.
"Dan Allah yau ɗaya ki gaishe ni mana, ke kullum sana gaishe ki?"
Ta ce "Ni na saka ka gaishe ni?"
"A'a ni naga yakamata in gaisheki, in ji ya lafiyarki"
Maimakon ta bashi amsa ta ce "Yauwa nace ya ku kayi da Kankiya jiya?"
Yazid ya ce "Jiya har ƙarfe biyar ina school ɗin nan, amma bai dawo ba, yanzu haka ma da wuri na shigo yau, na je ofishin sa, amma sakatarensa ya ce mini baya nan, na zauna na jira shi amma bai zo ba"
"Kaga ka share shi kawai"
"Meyasa zan share shi? Ko wani laifin nayi masa ne dan Allah ki gaya mini?"
Fadila ta kalleshi ta ce "Ni ya za ayi in sani idan ma laifi kayi masa?"
"Saurayinki ne fa, zai iya gaya miki"
Haɗe rai tayi ta ce "Ni nayi maka kama da sa'arsa? Ai zaren ba kalar yadin ne, nafi ƙarfinsa dan haka kar ka sake haɗani da shi". Wani irin sanyi jikin Yazid yayi, lecturer ma fa kenan, ina ga shi karan kaɗa miya, bai ajiye ba, bai bawa wani ajiya ba.
"Meye naga ka wani yi shiru?"
"Bakomai, kawai ina tunanin dalilin da yasa yake kirana ne, ko dai zai ja mini kunne ne akan ki?" Da sauri ta kalleshi ta ce "Me kake nufi?"
"Ina nufin ya ce kar ya ƙara ganin mu tare"
A ranta ta ce 'kai wannan sai kace aljani, ya fiye saurin gane abubuwa'
"Ya kika yi shiru?"
"Ai ni da zai ya kiraka yayi maka warning ɗin, da ya taimaka mini, ka liƙe mini da yawa, na rasa irin wannan abun, kai gashi kome mutum zai maka ba fushi kake ba".
Murmushi yayi, ya sake matsawa kusa da ita, wanda hakan ya fara haddasa mata mutuwar jiki.
"Idan yayi mini haka bai mini adalci ba, kina daga cikin mutanen da zuciyata ta aminta da su shiga rayuwata, daga ranar da kika fara yiwa takalmin ƙafata dariya, zuwa rashin iya turanci na, ban ji ba daɗi a kan yadda kike mini dariya ba, sai wadda sauran 'yan aji suka yi mini, rayuwata da ke maybe temporary ne, da mun gama school shikenan, amma wataƙila in Allah ya ƙaddara ke matarsa ce tare zaku rayu har abada"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah Fadila, ki bashi haƙuri kar yayi Wani yunƙuri da zai raba abotarmu, let's be friends"
Ta ce "Kai ka gaya masa mana, kuma ina ka taɓa ganin ana abota tsakanin namiji da mace?"
"Ba ayi, amma ina son mu mu fara" yayi maganar muryarsa can ƙasa.
Share shi tayi ta cigaba da danna wayarta.
Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kanta yana kallonta, ko ƙiftawa baya yi.
"Dan Allah ka daina kallona haka, ni gaskiya ka takurawa rayuwata wallahi" ta faɗa a tsiwace tana jujjuya ido.
Ya ce "Kamar bani da zuciya ko?"
"Dama ina ka ganta" murmushi yayi bai ce komai ba, ya tashi tsaye ya bar mata seat ɗin.
"In kana da zuciya kar ka sake zuwa wurin da nake, kuma kar ka sake kulani" bai waiwayo ba, yayi gaba yana murmushin da shikaɗai ya san ma'anarsa.
Amina ta na aji ana lesson, ƙarfe sha ɗaya na safe, malaminsu ya shigo ajin, ya kalli Amina a ya ce "Amina ɗauko jakarki ki zo" cikin mamaki ta bi malamin da kallo, ta ga dai lokacin tashi bai yi ba, to ina zata?
Haka ta ɗauko jakarta, ta biyo bayansa cikin mamaki.
Ga mamakinta Daddy ta gani a tsaye a ƙarshen barandar ajinsu.
Ƙarasawa ta yi ce "Daddy lafiya kuwa?"
Maimakon ya amsa sai ya ce mata "Ina kwana"
Ɗan sosa kai tayi sannan ta ce "Yi haƙuri, ina kwana?"
"Ai ni na fara gaishe ki, yau bamu haɗu ba sai yanzu, kuma na riga gaishe ki"
Amina ta ce "Yi haƙuri"
"Ai ba laifi ki ka yi mini ba, amsawa kawai zaki yi"
"Ai kunya nake ji, ba zan iya amsawa ba" tayi maganar tana sunkuyar da kai.
Dariya yayi ya ce "Zo mu tafi"
Ba musu tabi bayansa, zuwa mota, ya buɗe ya ce ta shiga.
Mamaki ya mamaye mata, tana son ta tambayeshi, amma tana tunanin kar tayi wani laifin.
Sai dai kasa jurewa tayi ta ce "Daddy ina zamu je ne?"
"Sayar da ke zan yi" ya bata amsa.
"To ai idan ka sayar da ni ba zan yi tsada ba"
Ya ɗan buɗe baki ya ce "Inji wa? Tsada za kiyi sosai, har an biyani kuɗin ma" dariya Amina tayi tana cigaba da kallon titi, sai dai ga mamakinta, sai taga ba hanyar gida suka nufa ba.
Ta sake kallonsa ta ce "Amma Daddy..
"Shhh" ya katseta.
Haka ta zubawa sarautar Allah ido, sun ɗan yi tafiya mai nisa, suka shiga wata unguwa, titunan unguwar kanta sai lokaci lokaci ababen hawa ke wucewa.
Gaban wani ƙaton gate Yayi parking, wani ɗan sanda ya leƙo, sannan ya koma ya buɗe gate ɗin.
'yan sandan sun kai huɗu a cikin gidan, suka dinga ɗaga masa hannu suna gaishe shi, amma bai kula su ba.
"Daddy suna gaisheka fa" Amina tayi maganar tana waiwayawa.
"Eh na gani"
"To ya baka amsa ba?"
"Kai ke kam tambayoyinki sun yi yawa" bata kuma magana ba tayi shiru.
Yayi parking a ƙatuwar harabar gidan, ya kashe motar ya fice.
Amina zamanta tayi a cikin motar, tana waige waige.
Ya buɗe motar ya kalleta ya ce "sauko mana"
A ɗan tsorace ta ce "Daddy dan Allah ina ne nan?"
"Wurin wanda ya saye ki na kawo ki"
Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta bi idonsa da kallo.
"Sauko mana" ya kuma maimaitawa.
Jiki a sanyaye, ta sauko daga motar, tana bin gidan da kallo.
Yayi gaba tabi bayansa, gidan yafi wanda suke ciki girma sosai da sosai, kuma ya tsaru, ya ciro mukulli ya buɗe ƙofar shiga cikin gidan. Wani irin ƙaton falo ne, da sai ka taka steps Sanan zaka isa ga kujerun.
Fuskantar da Amina tayi babu mutane a gidan ne, ya sanya jikinta yayi sanyi, ta ɗan tsorata.
"Shigo mana" yayi maganar yana kallonta.
Ƙarara yaga tsoro kwance a fuskarta, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba.
Babu tsammani taji ya riƙo hannunta cikin nasa, aikuwa ta tsorata, tamkar zata zura da gudu.
Murmushi yayi ya ja hannunta, zuwa wani tangamemen kitchen, sannan ya saki hannunta ya kalleta ya ce "Amina, ke 'ya ta ce, kar ki saka a ranki zan wani abu da zan cutar da ke, amma duk da haka naji daɗin reaction ɗinki akan hakan, kiyi haƙuri na ɗauko ki ba tare da na gaya miki dalilin hakan ba, nan gidana ne galibi ina saukar baƙina a ciki, Abokaina zasu zo garin nan, shi yasa na ɗauko ki ki musu girki dan Allah, bana son yin order na restaurant saboda na yadda da girkin ki, amma idan kinga da takura bakomai, ki bar shi".
Jiki a sanyaye ta ce "Zan yi"
"In kin san na takura miki ki bar shi kawai"
Ta girgiza kai ta ce "A'a, baka takura mini ba, amma me zan girka" tayi maganar tana jin yadda kaɗaicewarsu ta takurata.
"Ko me kika girka yayi, zuwa azahar zasu zo insha Allah, na ajiye komai, idan kina buƙatar wani abu sai ki mini magana" ta jinjina masa kai alamar to.
Ya juya ya bar kitchen ɗin, sai da Amina ta tsaya ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, tana tunanin to ita Hajiya Zainab zaman me take, da mijinta zai yi baƙi amma ba zai kaisu gidanta ba ayi musu girkin a can, sai a nan ba? Ganin bata da amsa, ya sanya ta fara tunanin abin girkawa.
Khalil kuwa jinsa yake tamkar mara lafiya, gaba ɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi, sai da yunwa ta ishe shi, sannan ya shiga cikin gidan neman abin da zai ci, sai dai jin Abincin yayi tamkar magani, ya ajiye Abincin ya tashi, shi babbar damuwarsa, kar Mummy ta ce zata yiwa Hafsa wani abu, gashi har ɗakinta ya je ya sameta ya sake bata haƙuri, yayi mata bayani, amma taƙi saurararsa, ta ƙare masa zagi ta koreshi.
Ba zato babu tsammani, Sir Kankiya ya shigo ajin su Fadila, yana muzurai ya fara yi musu bayanin cewa yayi musayan lokacin gabatar da darasi, da malamin da yakamata ya shigo ajin, ya wuce ya ajiye litattafan hannunsa ya fara ƙoƙarin ciro maker daga aljihunsa, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu da Yazid.
"Kai jiya bance maka kaje office ɗina ina son ganinka ba?" Yayi Maganar yana tsare Yazid da ido.
"Naje sir ban sameka a office ba, har kusan biyar ina jiranka"
"You Are very stupid, ni zaka yiwa ƙarya?"
"Ba ƙarya nake ba sir"
"Shut up, tashi ka bar mini aji, kar ka sake attending lectures ɗina, mara ɗa'a kawai, and mark you no 75% attendance no exams"
Gaba ɗaya Fadila sai ta rasa me ma zata yi ko tace, abubuwan na Kankiya sun wuce misali sun zama hauka.
Ga mamakinta Yazid ko yunƙurin bawa Kankiya haƙuri baiyi ba, ya tashi ya bar ajin.
Kan azahar tayi, Amina ta gama girkin da Daddy ya sakata, duk ta gaji, ta wanke dukkan abin da ta ɓata. Ta bi hanyar da suka shigo ita da Daddy, ta koma ƙaton falon nan, sai dai baya nan, kitchen ta koma tayi alwala ta dawo carfet ɗin falon tayi salla. Bayan ta idar Alhaji Ahmad ya shigo, ya kalleta ya ce "Sannu da aiki"
"Yauwa, na gama, sai in tafi gida ko?" Tayi maganar a ƙagauce.
Yayi murmushi ya ce "Zaki tafi gida, yanzu dai ga ɗakin da zaki kai abincin can, zaki jirani, idan sun kammala sun tafi, sai mu koma gida tare.
Amina ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba ɗaya bata son wannan ƙeɓewar ta su.
Da kansa ya tayata suka shirya komai a ɗakin, ya bubbuɗe kulolin Abincin sai ƙamshi yake yi.
Ya kai Amina wani ɗakin, bayan ya sa ta ɗebi Abincin, ya rufeta a ɗakin.