Showing 261001 words to 264000 words out of 296192 words
a yadda suke nunawa su farincikin 'yar su ya fiye musu komai. Suka nuna masa kar ya takura kansa duk abin da Allah ya bashi ya kawo musu.
Sun sami fahimtar juna sosai da soyaya a tsakaninsu. Yusra kullum cikin yi masa zancen Fadila take, na haryanzu ba a san in da take ba.
Yayi ta rarrashinta yana kwantar mata da hankali, yana nuna mata ai Fadila ba wani abu ne ya sameta ba, tun da dai Daddy ne ya ɗauketa.
Khalil yana ta shirin komawa Abuja, amma yanayin jikin Hafsa ne ya hana su tafi, dan wataran sai Mama ta zo ta wuni tare da ita, tana shan wahala sosai da sosai akan laulayin nan.
Gefe guda kuma zuciyarsa na matuƙar tausayin Mummy, duk ta firgice kamar wadda aka ce an sace Fadilan.
Da kansa ya kira Daddy a waya, yana masa magiyar yayi haƙuri ya taimaka ya gayawa mahaifiyarsu in da Fadila take.
Alhaji Ahmad ya ce "Kana ji na Khalil?"
"Eh Daddy"
"Tun tasowarku, na kasance ina biyewa abin da kuke so da wanda mahaifiyarku take so, na yi haƙuri na ɗau hakan bakomai ba, dai daga baya na gano illar da hakan da yake da shi a rayuwarku, mussaman Fadila da take mace, Fadila 'ya ta ce, ba zan yi abin da zan cutar da ita ba, dan haka ka ƙyaleni ina sane da abin da nake yi, hakan tamkar hukunci ne ga mahaifiyarku da ita kanta Fadila, kana sane da yadda suka saka na karɓi kuɗin auren mutane, suka dawo daga baya wai ba sa so, an san bata so aka kawo mini shi?, Kar ka ga laifina Khalil, da ku da mahaifiyarku duk ina ƙaunarku, duk abin da nake yi zuciyata bata mini daɗi da alaƙar da ke tsakanina da matata ta fari, amma ba yadda na iya da halinta, kayi haƙuri lokaci na nan zuwa da zan faɗi in da take"
Khalil ya ce 'Shikenan Daddy. Na kammala aikin da ka sakani, kuma nima a satin nan zamu koma Abuja in sha Allah"
Daddy ya ce "Masha Allah, Allah ya dafa a gaishe mini da ɗiyata".
"Za taji in sha Allah, a gaida Antyn"
"Zata ji in sha Allah"
Baba Hassan tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, saboda murnar ya ji zai je Saudiyya, masu taya shi murna nayi, masu yaƙe na yi, dan zukatan su Baffa babu daɗi zinƙire yake da hassada a kan yadda Allah ya ɗaga 'yarsa duk da suna cin arzikinta, dan kusan duk wata kayan Abinci da kuɗi na tafe, kuma tare da su ake ci amma basa gani.
Yazid ya kammala sallolin darensa kenan, da addu'oi, Kamar yadda ya saba ya ɗora hannunsa a kan Fadila, yayi ta mata addu'a sannan ya kwanta.
Ya kwanta babu da daɗewa, yaga Fadila ta tashi, fitsari ya tasheta, har ta nufi banɗakin cikin ɗaki, amma ta fasa saboda tsoro take ji, saboda ba wuta gashi bata san in da fitilarsu take ba, dan haka ta tafi banɗakin tsakar gida.
Shi ma kasa shiga banɗakin tayi, ta tsuguna a tsakar tayi fitsarinta, ta tashi tana wanke ƙafarta, tayi arba da wata mage ɗirkekiya.
A guja ta ƙwala ihu ta shiga ɗaki da gudu, ta faɗa kan Yazid tana rirriƙe shi.
A rikice ya ce "Lafiya menene?"
"Mage ce" ta bashi amsa.
"Kuma sai ki dinga gudu haka? Maimakon kiyi addu'a"
Cikin shagwaɓa ta ce "Mhmmm ni tsoronta nake ji, dan Allah ka tashi ka koreta, ka rufe mana ƙofa karta shigo".
Ya ce "A'a nima gaskiya tsoronta nake ji"
"Dan Allah ka tashi"
Shima ya shagwaɓe murya ya ce "Ni gaskiya tsoronta nake ji, kuma naga kamar ta shigo ma"
Sake ƙanƙame shi tayi ta na jin tsigar jikinta na tashi, saboda bata son mage. Hakan ya bawa Yazid damar nufin cikar kuɗirinsa a matsayinsa na mijinta.
Yadda hannunsa ke yawo a jikinta, ya sanya ta sake shiga tsoro da firgicin gaske.
Kamar wadda aka cirewa kuzari, ta kasa kayaɓus balle tayi yinƙurin hana shi, sai da taji abin nasa ya wuce tunaninta.
Lokaci guda burkin sarrafa kansa ya ƙwace masa, sai da ya kai ga samun abin da zuciyarsa ta makance a kan samu.
Fadila ba ta jin haushin Yazid kamar yadda ta ji haushin kanta ba, tana jinjina sokonci da wautar da tayi, na barin Yazid yayi awon gaba da abu mafi daraja a tare da ita, yanzu sai ya ce dama abin da take so kenan.
Haka ya taimaka mata ta kintsa, yana jiran kwandon bala'in da zata sauke masa, amma tayi masa shiru ba ta ce komai ba.
Washegari da safe ko abin karin da ya bata bata karɓa ta ci ba, ya gama surutansa da rarrashinsa amma ko kallonsa ba tayi ba.
Gashi yana da jarrabawa ƙarfe sha ɗaya na safe. Ba yadda ya iya haka ya fita ya barta.
Yauma yarinyar nan Maryam ita ta shigowa Fadila, Fadila ta ji daɗin zuwanta, tayi mata shara da wanke wanke.
Yau Yazid saboda sauri, ko gyaran gidan bai yi ba, ya ƙare a zaman rarrashinta.
Da kanta ta shiga bedroom ta tattare kayansa da ya cire ya ajiye, ta kwashe nata ma, ta gyara ko ina, tunawa tayi a gida wataran a falo ma take yada komai, sai dai a kwaso a biyota da shi, bata son ƙazanta amma bata iya gyara sai da ayi mata. Haka nan duk da jikinta babu daɗi ta gyara ɗakin.
Ta dawo ta ɗauko musu abincin safen da ya dafa, suka ci ita da Maryam.
Suna ta hira har sha ɗaya, ta lura yarinyar a nutse take, a hirar tasu ne ma, yarinyar take gaya mata Yazid malaminsu ne a makarantar dare, har take bata labarin 'yan ajinsa ajin sauka sunce zasu gidansa, da irin kirkin Yazid, ko a makaranta.
Fadla ta ce "Suwaye 'yan ajin saukar?"
Maryam ta ce "waɗan suka yi sauka, suka kuma dawowa?"
"To ya za ayi maza su zo gidana?"
Maryam ta ce "Ai ba maza bane, 'yan mata ne fa manya, suma suna koyarwa, ai zasu zo ki gansu".
Haka nan Sai Fadila ta ji babu daɗi, har da ɗan ɓata rai.
Can Maryam ta ce 'Anty, ba zaki ɗora girki ba?"
Fadila ta ce "Kin iya girkin ne?"
Maryam ta ce "Eh ina yiwa Antyna"
Fadila ta ce "Ina mamanki?"
"Ta mutu, shi ne yayata ta ɗaukeni"
Tausayinta ya kama Fadila ta ce "Allah sarki, Allah ya jiƙanta to me kika iya dafawa?"
"Duk abin da kike so na iya"
"To tashi mu je Kitchen ɗin"
Fadila saboda zama da Yusra, ta iya wasu abubuwan a girki, dan haka ta wayance, tana ganin yadda Maryam ke girkin, saboda ko bakomai yakamata Yazid ya dinga hutawa, ta dinga rage masa ayyuka.
Taliya suka dafa da miya, sai azahar lokacin islamiyya sannan Maryam ta tafi, Fadila ta rasa me zata bata, dan yarinyar tana taimaka mata, alhalin ba wanda ta shiga a layin ta yiwa sallama ta ce gata ta tare, ba Yadda Yazid bai yi da ita ba, amma taƙi zuwan.
Yazid ya sha mamaki da ya dawo, ya shiga Kitchen amma ya tarar da abinci. Ya dawo don ya tambayeta, duk da tunda ya dawo harara ce kawai take shiga tsakaninsu.
"Sweetheart, a ina muka samu abinci".
"Kaje can ka nemi Sweetheart ɗin ka"
"To Allah ya baki haƙuri, waye ya kawo mana abinci?"
"Dafawa nayi" ta bashi amsa.
"Wow, inyee ashe ta iya girki babyn"
Zumɓura baki tayi ya shareshi.
Duk yadda ta so ta basar da Yazid, amma ya zuba abincin, ya dinga zuba mata santi, ta ji daɗin yabawar da yayi, amma ta shareshi dan haushinsa take ji.
Tashi tayi ta koma bedroom ta kwanta abinta.
Yau da daddare ta tubure ba zai hau mta katifa ba saboda ƙarfin hali, falo ya koma ya ƙyale mata ɗakin ma gaba ɗaya.
Tayi juyi ya kai sau biyu, amma Yazid na kan sallaya yana ibada.
Ita yawan ibadar Yazid har mamaki yake bata.
Ji tayi yayi shiru da karatun da yake yi, ya tattara hankalinsa a kan wani abu, da bata san ko menene ba.
Ƙasa ƙasa taji Kamar Yazid kuka yake yi.
Kasa kwanciyar tayi, har ta fito ta je daf da shi, bai sani ba. Hannu ta saka ta zare hoton da yake hannunsa.
Wata kyakkyawar Bafulatana ce a jiki, mai matuƙar kyau na ɗaukar hankali.
"Wacece wannan?" Ta jefo masa tambayar.
Shiru yayi ya zuba mata ido, ya kasa furta komai.
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓeni domin saya.
Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YA TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA.
08081012143
79
Yazid ya sake numfasawa sannan ya ɗora da cewa "Na ƙarasa gaban gadon da Huzaifa yake da sauri, ina kiran sunasa cikin tashin hankali, na ga jikinsana wata irin karkarwa, idanunsa na ƙaƙƙafewa, na tafi ina ture likitocin ina riƙe Huzaifa, sai dai jikinsa ya yi sanyi ƙalau.
A fusace ɗaya daga likitocin ya kalleni ya ce "Ina baban naku da ka ce zaku taho tare, kun tafi kun bar yaro babu kowa a kansa ga jikinsa ya rikice"
Cikin rashin sanin abin yi na ce masa "Ba ya gari baban namu"
Ya dubeni ya ce "Allah wadaram halin mutumin ƙauye da bai san komai ba sai dai yayi jima'i ya haifi yara ya sake su kamar kaji"
Ba zan iya misalta baƙin ciki da ɓacin ran maganar da likitan nan ya faɗa ba, sai dai me banga laifinsa ba tun da an rasa mai zuwa ya nuna kulawa ga ɗan uwan nawa. Amma lamarin yadda lokaci ɗaya mahaifinmu ya watsar da mu na cigaba da ɗaure mini kai, na kasa manta yadda ya ke shiga damuwa idan waninmu ba shi da lafiya, akwai lokacin da kunama ta taɓa cizon Huzaifa, salla ce kawai take fitar da Baba, amma yana gida yana taya Inna jinya, amma yau Huzaifa a halin ya rayu ko ya mutu, Baba ya gaza zuwa ya ganshi.
Likitocin suka cigaba da masifa, suka ɗan yi masa abin da zasu iya, suka bar ɗakin suka barni da ga ni sai Huzaifa.
Na yi kuka kamar ba gobe, saboda halin da yake ciki, bani da halin taimaka masa, a halin yanzu ko motsi baya iya yi, kawai dai gashi nan a kwance. Na gama kukana na tashi na yi alwala, na samu wuri na dinga salla ina yiwa Huzaifa Addu'a samun lafiya.
Sai dai cikin dare Allah ya yiwa Huzaifa cikawa. Yazid ya ɗan yi shiru ya bawa hawayen da yake idonsa damar zubowa, ya sanya hannunsa ya share, ya cigaba da cewa "Mahaifinmu ya kasa zuwa ayi yadda za ayi a ɗauko gawar Huzaifa, sai yayansa na roƙa, shi ne ya zo Asibitin da kyar aka ɗauko Huzaifa aka kawo shi gida aka yi masa sutura aka binme shi.
A baya na kan yi mamakin yadda mahaifina baya jituwa sosai da 'yan uwansa, daga baya kuma na fuskanci kamar suna ɗan jin haushin mahaifina saboda dukiyar da Allah ya bashi.
Aka share makokin Huzaifa, zuciyata a cunkushe da damuwa, tsakaninsa da Innarmu wata biyu ne kawai, zaman gidan mu babu daɗi, saboda takura da hantara da nake fuskanta ga ƙiyayyar da mahaifina yake nuna mini a zahiri kamar ɗan gaba da fatiha ba ɗansa ba.
Gaba ɗaya na ji zaman gidan ya isheni, na ɗaura aniyar komawa makarantarmu, sai dai tuna bani da abincin da zan ci a makarantar ya sanya jikina yin sanyi, ga shi a tsukin lokacin ciwona na asma na yawan tashi, ko magani bani da shi.
Mahaifina kuwa babu fuskar da zan tambayeshi, ɗakin Innarmu na sake duddubawa na samu abin da yayi saura na tattara, na je na sayar da sauran kuɗin hannuna na koma makaranta.
Sai dai kuɗin hannuna na san ba in da zasu kaini, na dinga tattala su, lokaci lokaci mussaman ranar juma'a na kan shiga cikin gari, don duba sana'ar da zan yi na samu kuɗin riƙewa, sai dai da na yi aikin wahala sosai sai na kwanta ciwo.
Haka na cigaba da karatu cikin tsananin wahala, ga ni ni bana aboki, saboda kar aboki ya bani abin da zai mini gori a gaba. Sai gashi wanda suke zuwa da wurin su ci a baya duk sun watse saboda a lokacin bani da shi.
Idan abin ya tsananta gareni na kan tafi kibiya in da Kakata ta wurin uba take aure, idan na je ne sai ta ɗan harhaɗa mini abin da take da shi ta bani.
Watarana kakata ta gama haɗa mini ɗan kayan Abincin da take da shi, ta ga ina ta shiri zan tafi ta kalleni ta ce "Ba zaka bari sai rana tayi sanyi ka tafi ba?".
Na ce mata "Rano nake son na ƙarasa, idan Baba yana nan na ganshi na gaishe shi"
Cikin tausayawa ta ce 'Yazid ka yi haƙuri, ka koma makarantar ka kawai ita ce rufin asirinka"
Cikin damuwa na kalleta na ce "Amma saboda me?"
"An riga an shiga tsakaninka da mahaifinka, dan haka kayi haƙuri ka cigaba da addu'a kawai nima ita nake yi".
Cikin rashin Fahimta na ce mata 'Kenan Baba ya gaya miki laifin da na yi masa ya sanya ya dai na kulani, ni yaƙi gaya mini me na yi masa".
Ta ce "Bayan abin da ya faru na rasuwar Huzaifa, na kirashi na yi masa faɗa tare da tambayar daliin da ya sanya ya bari har Huzaifa ya mutu bai je kansa ya biya kuɗin aikin ba, amma ya ce dani shi ma bai san dalili ba, kawai dai ba ya ƙaunar ganinku ne gaba ɗaya".
Jikina a sanyaye na tambayeta ko wani abun muka yi masa, amma ta ce "Ba wani abu da kuka yi masa, ka cigaba da addu'a. Dan an shiga tsakaninku da shi ne" Ni dai a lokacin ban gane ne take nufi da hakan ba, na dage ni tafiya zan yi yanzu.
Bayan mun yi sallama cike da son ganin mahaifina na tafi Rano, sai dai ba zan manta da wanan ranar ba, a gabana babana ya ce kar na ƙara zuwar masa gida, baya ko ƙaunar ganina. A tsakar gida a gaban 'yan uwana, suka dinga mini dariya, suna cewa Allah ya ƙara baƙin jinin uwata da baƙin halinta ne yake bibiyata da ƙanina. Kuma a haka zan ƙare cikin wahala
Na riƙe ƙafar Baba ina kuka na ce "Dan Allah Baba idan laifi na yi maka ka yi haƙuri dan Allah, dan girman Allah ba za sake ba kar ka rabani da kai kai ne kawai ka rage mini ba Inna ba Huzaifa"
Tsananin tausayina da soyayyata na gani a cikin idonsa, amma a zahiri a kan fuskarsa ya dinga yi mini masifa, ya ce na tashi na bar masa gida baya son ya sake ganina.
Na tashi na nufi ɗakin Inna, na zauna na yi kuka na kwashi sauran kayana, na tattare kayan Inna na litattafanta, da hotunanmu na fito na bar gidan har na yi nisa sosai, ina tafe ina kuka na ji ana kirana, na tsaya na waiwaya na hangi 'yar autar su Baba Anty Sa'a.
Ta ƙaraso in da nake idonta cike da ƙwalla, duk da tana cikin wanda suka nunawa Inna ƙiyayya, amma ta dafa kafaɗata ta ce "Yazid na ji abin da yaya yayi maka, dan Allah kayi haƙuri kayi ta addu'a a duk in da kake, Allah ya sa ya dawo hankalinsa, ga wannan ka riƙe ka tafi da shi makarantar idan ba dole ba, ka daina zuwa gidan nan gaba ɗaya, kar kai ma su yi maka abin da suka yiwa Huzaifa".
Yazid ya ce "Me suka yiwa Huzaifa?"
"Bakomai, ba sai ka bincika ba, ka tafi kawai Allah ya tsare" ta danƙa mini kuɗi a hannuna ta juya ta tafi.
Na riƙe kuɗin na tafi tasha na hau mota na koma makaranta.
Haka rayuwa ta cigaba, ina ji ina gani na rabu da mahaifina, ina aji biyar Sakandire Kakata da take ɗan tallafa mini ita ma ta rasu, nake ta wahala. 'yan uwan mahaifiyata su na zuwa gidanmu wurina, amma sai matan mahaifina suka ce musu wai na gudu na bar gida, ba wanda ya san in da nake na shiga duniya.
Tun suna zuwa har suka daina, dan ko mutuwar Huzaifa ba wanda ya gaya musu, sai da ga baya sannan suka sani.
Al'amura suka cushe mini, wataran sai na wuni na kwan ban ci abinci ba, har shugaban makarantarmu ya kan tambayeni, wai ina Babana kwana biyu ya daina zuwa in da nake saɓanin da baya rufa wata bai zo ba, na ce masa ayyuka ne suka yi masa yawa shi ya sa. A aji na uku lokacin da zamu yi Waec, abubuwa suka cakuɗe mini, in da Allah ya taimakeni na ci qualifying saura Neco. Aka canza mana wani shugaban makarantar, wanda aka kawo ya ga yadda nake da ƙoƙari, sai ya dinga amfani da ni yana neman scholarship a wurin Manyan mutane, wai a taimakawa rayuwata ina da ƙwazo kar ƙwazona ya tafi a banza, idan aka ce a kawo takarduna sai yayi ciwa-ciwa ya bada sunan wani da sunana ya karɓi kuɗi, ni da ban san me ake yi ba, sai daga baya a bakin ɗalibai na ji.
Idan aka je musabaƙa, duk abin da aka samu ba ya bani wani abin kiri, naga kamar yana nema ya koma business da Alqur'ani, dan haka na daina zuwa musabaƙar, na ce ba zan sake zuwa ba, aikuwa ashe ya ƙulu, bayan qualifying ta fito na ci, amma daga baya sai ya ce ai ba duka aka biya mana kuɗin jarrabwar ba, dan haka mu nemo kuɗi.
Ban yi gangancin zuwa gidanmu ba, na je wurin wani abokin mahaifina, ba dan raina yana so ba, amma ganin a kan harkar karatu ne, ya sanya na je ya taimaka mini. Amma ya ce ubana ma ya gaza ɗaukar ɗawainiyata balle shi? In yi haƙuri ba shi da shi.
Rabona da garin su Inna tun tana raye, da kyar na samu rancen kudi na tafi garin nasu, sai dai na sha wahala kan na samo su dan sun koma Maraya sun bar riga. Da suka ganni tamkar su goyani dan murna, sai koke-koke suna tuna 'yar uwarsu.
Yayar Inna da take bi Hajiya tana nan lokacin ta je ganin gida ta ce mini "Ina ka tafi, muka dinga zuwa garinku aka ce wai ba a san in da kake ba?"
Da na so yin ƙwauron baki, amma naga bani da wata mafita, mussaman da idan na gama makaranta bani da wurin zuwa.
Nan na gaya musu duk yadda ake ciki, a lokacin kakata ta tsufa, kakana kuma dama tun kan a haifeni ya rasu.
Hajiya sai da ta yi kuka da ta ji irin wahalar da nake sha, suna nan basu sani ba, a ranar