Showing 270001 words to 273000 words out of 296192 words

Chapter 91 - GABA DA GABANTA

Allah ku zauna kuyi sulhu a tsakanin ku"

A fusace ta ce "Babu sulhu a tsakanina da wannan mutumin, dama ai kune kuke shirya kowane munafunci, kuma kuke ƙara goya masa baya, komai yayi ai daidai ne a wurinku, tunda ni ba 'yar ku bace ba dole ku dinga goya masa baya, to wallahi na gaji da baƙin cikin da mutumin nan yake ƙunsa mini a cikin gidan nan, wallahi ƙararsa zan kai muddin bai dawo mini da 'ya ta ba, ai ba shikaɗai ya haifeta ba" ta tashi fuuuu ta bar falon.

Su Kawu sun yiwa Daddy faɗa sos6, tare da nuna masa rashin kyautawar abinda ya aikata na aurar da Fadila ba tare da ta sani ba, ko a lokacin su kansu sun yi masa magana a kan wannan wane iri aure ne bagatatan kamar yaƙi, amma ya ce musu yana da dalili, ya yi ta basu haƙuri dai suka tafi.

Ba ƙaramin tausayin Hajiya Zainab ya ji ba, shi kansa ya ga uwar ramar da tayi bayan dawowarsu, ya san tana cikin damuwa, amma yanzu da zarar yayi wani yunƙuri ci masa mutunci za ta yi, amma bai haƙura ba, ya nufi sashinta, duk dan ya samu a zauna lafiya, amma yana shiga ta dinga zazzaga masa masifa da tashin hankali, sai da ya gwammace bai je in da take ba. Yana bata haƙuri da lallaɓata tana buntsirewa tana cin mutuncin sa dana kwaunnan sa. Take ya ji zuciyarsa ta kuma bushewa, bama ya dana sanin auren da ya yiwa Fadilan, a ransa ya sake ganin hakan shi ne daidai.
Da ya aurar da ita ta je tana irin halin mahaifiyarta, gara da Amina ta bashi Shawarar yin haka.
Yana zuwa sashin Amina kuma, ya tarar da ita a toilet, tana ta sheƙa uban amai, kamar zata amayo kayan cikinta. Take ya manta da zafin da Hajiya Zainab ta haɗa masa, ya tattara hankalinsa a kan Amina, ya shiga toilet ɗin ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito yana mata sannu.
Ta kalleshi ta ce "Dear ina su Kawun ko har sun tafi?"

Daddy ya ce 'Eh sun tafi"

Ta ce "Subhanallah, yanzu ya kuka yi ni da muka dawo gani nayi ta rame sosai, yakamata kawai a gayamata gaskiya in da Fadila take"

"Meenal, kin san halinta lokacin da ake lallaɓata a lokacin take wulaƙanci, dan haka ki nar wannan zancen tukuna tun yaushe ne ba ki da lafiya?" Tunani tayi idan ta ce masa ta kwana biyu zai ji babu daɗi, dan haka ta ce masa "Yaune kawai na tashi cikina babu daɗi, nake ta amai"

Ya ce "Shirya muje Asibiti a duba mini ke, na tsorata da wannan aman".

Babu musu ta shirya, suka fita domin zuwa Asibiti, a hanya ne Amina take bashi shawara yakamata ya kira Yazid ya ji suke, idan da dama ma ya je da kansa ya duba su"
Daddy ya ce "Ai da muna Lagosa na kirashi, ya ce mini babu matsala, ba zan je ba yanzu zan kuma kiransa dai a waya, ko na gayyace shi gida na ji abin da yake wakana, amma ba zan je ta ganni ba zan iya mayar da aikin baya"

Amina ta ce 'Kuma haka ne, to Allah ya jishe mu alkhairi"

Ya amsa mata da Amin.

Bayan gwaje-gwaje da yakamata ayi mata, likita ya tabattar da tana da ciki. Dama ita ta sani, Daddy sai murna yake yi, sai dai ta wani fannin Amina bata wani murna, saboda zata fara zuwa makaranta, gashi da alama cikin mata ya zo da laulayi, sai dai ba ta son ta ɓatawa Daddy rai, dan haka ta biye masa yana ta murna yana Addu'a Allah ya bar masa.


Wata irin miƙa Fadila take tana nishi, sai jujjuya kai take yi, Yazid ya dinga karanta mata Alqur'ani ta dinga mimmiƙewa tana wani irin gunjin kuka, ya daɗe a rungume da ita yana yi mata Addu'a, kan Allah ya taimake shi jikinta ya saki ya yi sanyi ta hau bacci.
Mamaki ya shiga yi, dama Fadila na da iska ne? Amma shi bai taɓa ganin alamar hakan a tare da ita ba to yaya aka yi haka ta faru?

Hajiya Zainab kuwa ji tayi kamar ta sha guba ta mutu dan baƙin ciki, ta rasa in da zata saka kanta bata san da me zata kwatanta irin abin da Alhaji Ahmad yayi mata ba.
Kamar yadda ya zame mata kamar wahayi duk abin da ha sameta sai ta sanar da su Hajiya Salma, haka ta ɗau mota ta tafi shagon Hajiya Salman, aikuwa ta tarar da ita da Hajiya Turai duk suna tare.
Suna ganin a yadda ta zo suka san akwai damuwa. Aikuwa ta zazzage musu duk abin da yake faruwa.

Hajiya Salma ce ta kwarara ashar ta ce "Ban taɓa ganin azzalumin mutum da baya tsoron Allah ba, yanzu ƙiyayyar har ta kai ga haka? 'yar da ya haifa, wallahi mutumin nan baya tsoron Allah, kuma ko ki yarda ko karki yarda wannan sheɗaniyar Yarinyar da yake tare da ita, ita ce take yi masa asiri, gara tun wuri ki bazama ki nemi abin yi, idan ke ba zaki iya ba mu sai muje mu nemo miki taimako. Kina kallo yanzu ko kuɗaɗen da kike samu a wurinsa yaushe rabon da ki samu? Duk ta toshe komai ita kaɗai take samun komai ta nayar da ke hoto, wai ma wa ya aurawa Fadilan?"

Jiki a sanyaye Mummy ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba"

Hajiya Turai ta ce "Ni na ma rasa bakin magana, ƙarshen raini da wulaƙanci dai yayi miki shi, dole ki san duk yadda zaki yi ki nemo 'yarki"

Yadda suka dinga zigata suna nuna mata Daddy ya gama wulaƙantata ne ya sanya ya kuma hawa, har take jin a duniya ta ƙara tsanar uban 'ya'yan nata.




Yazid kuwa kusan raba dare yayi yana yiwa Fadila Addu'oi. Da Asuba ko sallar asuba bai fita ba a gida yayi salla, ya tasheta tayi salla, da yayi mata batun ya jikinta? Sai ta ce masa ai ita lafiyarta ƙalau babu abin da ya sameta gaba ɗaya.
Yazid ya bar maganar a ransa, sai da ya saka mata ido sosai, wurin kula da ibada da Addu'oi, duk da wasu lokutan sai sun yi faɗa dan tana cewa ya takura mata.
Kwana kusan biyar, ta ware sosai ya kuma taso mata da maganar za suje Rano.
Ita kwata kwata bata son zuwa Ranon nan, dan ba ta ga abin da Yazid zai koma yayi a garin da suka nuna basa buƙatar sa ba.
Ita kanta Hajiya mita ta dinga yi, a kan Yazid ya haƙura da Ranon nan, amma yayi ta lallaɓata yana bata haƙuri.

"Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri ki bari na je, na kai musu Fadila ma su gaisa, tun da 'yan uwana ne babu yadda na iya, yakamata ta san suwaye dangina, idan aka kwana biyu kuma sai mu je Jalingo"

Hajiya ta ce "Dan dai ka matsa ne Yazid, amma ni banga amfanin mutanen nan a tare da kai ba, bayan ƙiri-ƙiri sun nuna ba ƙaunarka suke yi ba"

Yazid ya ce "Duk da haka Hajiya, ko ina so ko bana so ai 'yan uwana ne"

"Eh na san 'yan uwanka ne, amma matarka da zaka ɗauka ka kai musu fa, dama ita ma gata ga yadda take, kuma kaje su kunyata ka a gabanta kai baka tunanin haka kwata kwata?".

Yazid ya ce "Hajiya ai ya san komai na gaya mata"

"Ka gaya mata kuma, shikenan Allah ya tsare, amma ban yadda ka kaita ku je ka kwanar musu da 'ya a wannan garin ba, kar su yi mata wani abun"

Yazid ya ce "In sha Allah ba kwana za mu yi ba, a ranar zamu dawo".

Washegari da sassafe Yazid suka shirya, suka nufi tasha.
Tun da Fadila take bata taɓa zuwa tasha ba, galibi a jirgi suke zirga-zirga, sai kuma Dutse da sukan je a mota.

Fadila tana cikin dogon hijjabi, har da face mask a fuskarta, ba a ganin fuskarta. Warin da wasu da ga cikin matafiyan suke yi ne da warin fetur, ya sanya zuciyar Fadila tashi, ta riƙo hannun Yazid ta ce "Zid"

"Na'am Baby, menene?"

"Zuciyata tashi take, wannan warin fetur ɗin ya dameni, ga wani wari da na kasa gane kona menene"

Cikin kulawa ya ce "Ko wani abun zan sai miki ki saka a bakinki?"

Ta ce "Eh sai mini"

Kafin su fara tafiya, Yazid ya sauka, ya sayo mata kwakwa da dabino, da aya fal, ya kawo mata.
Cikin hijjabinta ta shiga ta jingina da jikin Yazid, tayi ta ciye-ciyen ta, har aka fara tafiya.
Ƙarfe sha ɗaya na safe suka isa garin Rano, suka samu wata motar suka ƙarasa.
Garin gwanin ban sha'awa sun yi noman rani, ko ina koren ganye, ga su da hanyoyi masu kyau, ko ina titi ha fitlinsi na solar duk a kan titunan.

Duk da gidan su Yazid ginin ƙasa ne, amma tun daga ƙofar gidan zaka san me gidan yana da rufin asiri,ginin ya ginu doguwar katanga ce sosai. Ga soraye sun kai takwas kan ka dangana da cikin gidan.

Gidan yana ɗauke da ƙaton tsakar gida iya ganinka, da ɗakuna kashi-kashi a ciki. Ko da yake ginin na da ne, amma ka san talaka ba zai iya irin wannan ginin ba.
Suna wuce sorayen Yazid yana mata bayanin wasu daga abubuwan da suka faur a baya.

Da sallama suka shiga gidan, suka tarar da yaran gidan suna ta kaiwa da komowa a tsakar gidan.
Wata budurwa ce ta amsa sallamar, tana ƙarewa su Yazid kallo.

Yazid ya ce "Haulat ina mutan gidan ne?"

Wadda aka kira Haulat ta ce "Ba sa nan an kai Baba Uwani gidan mai magani, amma yanzu zasu dawo"

Ya ce "To bamu abin zama kan su dawo"

Ba musu ta shiga ta ɗauko musu tabarma, ta dawo ta shimfiɗa musu. Suka nemi wuri suka zauna.
Fadila na cigaba da ƙarewa gidan kallo.

"Zid ina ne ɗakin Inna?"

Yazid ya nuna mata da hannunsa ya ce "Gashi can, naga ma yanzu shirgi suke tarawa a ɗakin"

Ta ce "Allah sarki, Allah yayi musu rahama baki ɗaya"

"Amin my wife, na gode sosai"

Suka cigaba da hira, yana bata labari, kasancewar ya san yanayin gidan nasu sai a hankali, hatta ruwan da zata sha sai da ya saya mata.

Suna nan zaune suna hira, 'yan ƙanan jikokin gidan da yaran maƙota suna ta kaiwa suna komowa a gidan.

Hayaniya suka fara ji, ana ƙoƙarin shigowa da wani abu, gaba ɗaya hankalin Yazid da na Fadila ya koma kan hanyar shigowa.
Wasu samari ne suka shigo da abu a cikin tabarma, sai daga baya Yazid ya lura da yayyensa mata da suka shigo daga baya.
Abin da aka ajiye a cikin tabarmar ne ya ɗan tsorata Fadila, mace ce ƙafarta ta kumbuta himmm, da cikinta fuskarta duk wasu irin ƙuraje, gashi tayi baƙi sosai.
A gigice Yazid ya tashi ya nufi in da matar take yana faɗin "Baba Uwani, meya sameki haka?" Da ƙyar matar ta iya ɗaga kanta ta kalli Yazid ta ce "Gwani kai ne yaushe ka zo?"

"Tun ɗazu muka zo matar da na aura na kawo muku ku gaisa, amma meya sameki haka?"

Ta fashe da kuka, yayin da yayyen nasa kuma suke bin Fadila da ke zaune a gefe da kallo, fara tas da ita me kyau wai yake faɗin matarsa ce.
Ita kuwa Fadila ta haɗe rai, ta ja face mask ta rufe fuskarta, dan duk sai ta ji haushin su ya kamata, dan da alama yanayin tsayinsu da idanuwansu ya tabattar mata da yayyensa ne.

Matar ta riƙe hannun Yazid tana kuka ta ce "Yazid ka ga yadda Allah ya mayar da ni, hakkinka sai bibiyarmu yake yi ni da Hanne, yanzu ita tana can tana fama da ciwon miyagun baƙaƙen aljanu, jikana Sani ma an shanye masa hannu da ƙafa, nima ka kalli yadda Allah ya mayar da ni, kuma mai magani ya ce dole na nemi afuwar wanda muka yiwa asiri9"

Yaya Gaji da ke kusa da Baba Uwani ta ce "Baba dan Allah kiyi shiru, wannan ba abin da zaki tsaya kina faɗa bane ba dan Allah".

Baba Uwana ta girgiza kai ta ce "Bar ni Gaji, nikaɗai na san me nake ji ban sani ba ko gaya masan ya sanya na samu sauƙi"
ta kuma mayar da idonta kan Yazid da fuskarsa ta bayyanar da damuwa ta riƙo hannunsa ta ce "Yazid dan Allah ka yafe mana, bayan auren mahaifiyarka muka ɗora mata tsana, ta fara haifar ka facaloli suka ziga mu wai idan ba muyi a hankali ba sai ta haifi maza duk ta kwashe dukiyar mahaifinku, muka fara bin malamai, a kan a kashe ka amma abu ya gagara, mahaifinku ya ɗora ransa a kanka, Babarka ta zo ta sake haihuwar Huzaifa, hankalinmu ya sake tashi. Muka cigaba da bibiyar malamai aka yiwa Babarka sihiri aljani ya dinga bibiyarta yana feso mata da wasu ƙuraje a haka har ta rasu.
Bayan tafiyarka makaranta, muka cigaba da bin malamai a kanka ka lalace, amma abu ya gagara sai muka koma yiwa babanka asiri a kan ya tsaneka, abun ya fara kamashi, aljanin da yake aikin ya ce sai an bashi jini shi ne zai yi aikin har ƙarshen rayuwarsa ba zai sake ƙaunarku ba, hankalinmu ya tashi muna tunanin yadda za ayi, saboda idonmu ya rufe buƙatarmu muke son ta biya kawai. Muka sadaukarwa da aljanin Jinin shanun mahaifinka goma yayi asararsu suka mutu, bayan mutuwar babarka muka dinga gallazawa Huzaifa a gidan nan, ƙarshe muka saka Sani ɗan wurin Gaji ya ja Huzaifa bayan gari, ya hankaɗashi rijiya ya tafi ya bar shi.
Mu muka yi Asiri mahaifinku ya tsaneka ya koreka, muka dinga asirin sai ka lalace ko kai ma ka mutu, amma abin bai yiwu ba aka zo babanku ya rasu, muka dinga tattara kayansa muna sayarwa muna rabawa dan kar a raba gado ka samu dukiyarsa da yawa, babanka kan ya mutu asirin ya bar jikinsa ya ce ba zai yafe mana ba, amma dan Allah kai tun da kai kana raye ka yafe mana ko ma samu sassauci" Sunkuyar da kai Yazid yayi, hawaye na zuba daga idonsa ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Baba Uwani ta rirriƙe hannunsa tana kuka.

Yazid ya ce "Baba kar ki sake cewa wai kune kuka yi mana wani abu, babu wani bawa da ya isa ya yiwa wani kowane irin abu sai abin da Allah ya ƙaddara zai samu bawa, ubangiji Allah ya yafe mana baki ɗaya.

Miƙewa Fadila ta yi, ta saka takalmanta, ta je in da Yazid yake ta fizge hannunsa daga na Baba Uwani ta ce "Be yafe ba, Allah ya saka musu, in sha Allah sai kin fi haka wulaƙanta kan ki mutu, da ke da Wanda duk suka cutar da baiwar Allah da ba ta ji ba bata gani ba, ka tashi mu tafi"

Yazid ya ce "Fadila me kike yi haka ne? Allah yana son bayinsa masu yafiya, ina son na dinga zumunci da 'yan uwana".

"Ni na isheka zumuncin, wallahi ko ka yafe mata Allah ba zai yafe musu ba, shirka suka yi ai wallahi ko ka yafe ni ban yafe musu ba, ka tashi mu tafi"
Fadila ta yi maganar tana kuka, saboda yadda abin da Baba Uwani ta faɗa ya girgizata, rashin imanin ya wuce tunaninta.

Gaba ɗaya bin Fadila suka yi da kallo, Yazid ya miƙe tsaye ya ce "Fadil...

"Ni karka kira sunana kawai ka taho mu tafi kawai"

Jikin Fadila har rawa yake yi, saboda bata taɓa jin zunzurutun rashin imani irin wannan ba.
Ganin da yayi tana neman ta fice daga gidan, ya sanya ya bi bayanta, sai da suka je waje sannan ya cimmata.

Yana ƙoƙarin yi mata magana, amma ta fashe masa da kuka ta ce ita ya zo su tafi.
Ganin yadda ta burkice gaba ɗaya ne ya sanya Yazid rarrashinta ya ce tafiya za su yi.

Cikin gida kuwa Baba Uwani fashewa ta kuna yi da kuka tana miƙa hannu tana cewa su kira mata Yazid, ya zo ya yafe mata ko zata daina jin zafin da jikinta yake yi mata.

Yaya Uwani ta ce "Kinga ni ko Baba, yanzu meye amfanin gaya masan kawai kin tonawa kanki asiri".

Cikin tsananin zafin ciwo Baba Uwani ta ce "Gaji baki san me nake ji ba a ciwon nan, kamar ƙonani ake a cikin naman jikina, ku cire mini ciwon nan ko na tsine muku" haka ta dinga kururuwa tana ihu.

Fadila kuwa har suka je gida kuka kawai take yi, dan gaba ɗaya sai da hankalin mutanen motar ya dawo kansu.
Har suka je gida bata iya cewa uffan, saboda tsananin tsoro da tashin hankali.

Har suka isa gida gefin la'asar, Fadila ko magana bata iya yi.
Bayan sun yi sallar la'asar, ya tashi ya fara ƙoƙarin ɗora girki, dan ya san tana jin yunwa.


Sai dai tun da suka dawo ɗin, Fadila ta kwanta tayi shiru a falo, tana jinjina tsananin rashin tsoron Allah na wasu mutanen.
Tunani take ta yi, ta gano laifin da mahaifiyar Yazid ta yi wa mutan gidan, da har ta cancanci wannan zalunci daga garesu, sai dai ta kasa ganowa.
Kamar dai Daddy daya auri mai aikin Mummy. Zuciyarta ta tuna mata.
'kai ai ko Mummy da aka auri 'yar aikinta, bana tunanin zata yi abin da wannan mutanen suka yi'.

Yazid ya dawo falon, ya ɗago Fadila da ke kwance, ya rungumeta a jikinsa ya fara yi mata magana cikin taushin murya "Fadila, dan Allah ki Kwantar da hankalinki, ni kaina ban san zamu tarar da wannan tashin hankalin ba, amma ko na yafe musu ko ban yafe ba, Allah ya hukunta su, ba kiga halin da take ciki ba"

Bakinta na rawa ta ce "Zid na tsorata, wallahi tun da nake a rayuwata ban zata ana yiwa mutum asiri da gaske ba, dan Allah kar ka yafe musu"

Ƙwalla ce ta taru a idon Yazid, yayi murmushi ya ce "Shikenan, amma Fadila shi Asiri gaskiya ne, an yiwa annabin rahama ma, shiyasa nake son ki dinga kula da ibada a kan lokaci da kuma azkar"

"Zid sun cutar min da kai, ni ba zan yafe ba" ta ƙarasa maganar hawaye na kuma bin gefen idonta, ga wani tsoro da yake kuma shigarta.

"To kiyi haƙuri, shima Yazid ɗin na ki Allah ya miƙawa lamuransa shi ya sanya ya kare shi, amma a cikin 'yan uwana akwai wanda basu da laifi, kuma ko bana so 'yan uwana ne".

"Ni na isheka, ni da Hajiya, kuma sai na gaya mata kar ta kuma barinka ka je,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login