Showing 237001 words to 240000 words out of 296192 words

Chapter 80 - GABA DA GABANTA

ki gode Allah ma aurenki zan yi, sauran matan da nake kulawa holewa kawai muke, kin san rayuwar turai, irin wannan abun duk cikin soyayya ne kawai"

Yayi maganar yana ƙoƙarin rungumeta, hannunsa ɗaya kuma yana ƙoƙarin ɗaga doguwar rigar jikinta.

"Wayyo Allahna Mummy" tayi maganar cikin ihu, hakan yasa taji tamkar ana buga mata guduma a kanta.

Ba kunya ba tsoron Allah yake ƙoƙarin haike mata, gashi ta kasa ihun saboda azabar ciwon kai, sai kokowa suke.

Jin alamun za a buɗe ƙofar ya sanya ya ƙyaleta, Ba tsammani Mummy ta buɗe ɗakin ta shigo, turus tayi tana kallon Salim, ga Fadila da take ta hawaye shi kuma yana tsaye a gefen gadon.
Da sauri ya sha jinin jikinsa, ya fara kame kame "Dama gani nayi kamar ruwan baya tafiya, shi ne na gyara mata, bari naje Mummy"

Bata kai ga gano meke faruwa ba ta ce masa "Shikenan, ka gaida Salman"

Ta mayar da dubanta ga Fadila ta ce "Ke dai kin fiye rakin tsiya, da kin ji ciwo sai kuka?".


Fadila bata amsa mata ba, ta goge hawayen fuskarta, ta ɗauko wayarta dake ringing ta saka a kunnenta.

Muryar Yazid taji a sanyaye ya ce "Kina lafiya kuwa?"

Ta ce 'Eh meye?"

"Gabana ne yake faɗuwa, kamar wani abu ya faru da ke, ko yana shirin faruwa da ke"

Mamaki ne ya kama Fadila ta ce "Ba abin da ya sameni, kuka nayi kaina yana ciwo"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ina miki sannu, Allah ya sauwaƙe".

Ta ce "Amin na gode"

Mummy ɗorawa tayi da yi mata mita, a kan ta gaji da wannan kiran wayar da kuma zuwan da Yazid yake yi.
Tana cikin maganar doctor Aliyu ya shigo, hannunsa riƙe da bp machine, yana yiwa Fadila sannu.

Ya ƙarasa ya duba jikin Fadila, ya tarar jininta ya kuma hawa.

Ya kalli Fadila ya ce "Fadila, Ya haka ne? Jininki ya kuma hawa, gaya mini meke faruwa?"

Kawai ta fashe da kuka.

Doctor Aliyu ya ce "Gama kukan ki gaya mini"

Ya dinga lallaɓata yana rarrshinta, a hankali ta kalli Doctor Aliyu ta ce "Mummy ce".

Mummy ta ce "Ni kuma?"

Aliyu ya ce "Shhh, Mummy ba ruwanki, magana muke yi"

"Gaya mini, me Mummyn tayi?"

"Zata haɗani aure da wanda bana so, ina ta ƙoƙarin ɓoyewa na danne dan na aure shi hankalinta ya kwanta, amma ya dinga kai ƙarata yana cewa ina masa wulaƙanci, bata bibiyi meyasa bana son shi ba ta daina kulani, ta daina shiga harkata sai yanzu da bani da lafiya sannan ta cigaba da kulani. Bana iya bacci da cin abinci yanzu kuma da yazo dubani" ta nuna musu yadda ya karceta da farcensa a gefen wuyanta a ƙoƙarin sa na saka hannunsa a rigarta.

Cikin kuka ta cigaba da magana "Wallahi ni bana son sa, Mummy bana ƙaunrsa wallahi, tuntuni ma bana son sa, har hoton jikinsa yake turo muni, duk baki bincika ba kike ta fushi da ni" tayi maganar cikin kuka.

Mummy ta ce "Subhanallah, ai ni baki mini wannan bayanin ba"

Doctor Aliyu ya ce "Gaskiya Mummy baki kyauta ba"

Numfashin Fadila ne ya fara yin sama, ta ce "Aliyu kaina ciwo yake"

Aliyu ya ce "Bari nayi miki allura"

Mummy ta zauna kusa da ita tana ta rarrashinta.

Ya sake yi mata allurai tayi bacci. Ƙarshe dai ba a sallami Fadila ba sai washegari, da yamma.

Ana sallamarsu gida suka wuce, Mummy tana ta tunanin yadda zata ɓullowa lamarin Fadila, saboda har ga Allah tana son rayuwar Fadila, ƙarshe ta yanke shawarar saka Daddy ya mayar musu da kuɗin auren a mazaunin shi ne baya son auren.


Bayan komawarsu gida kuwa, 'yan dubiya suka dinga zuwa duba Fadila, ciki har da Yazid, Yusra da Abdul.

Amina ta takura Daddy cewar ya tashi ya rakata sashin Fadila ta dubata, dan bata son fitina, kar taje ita kaɗai suyi faɗa da Mummy.

A falo suka tarar da Hajiya Zainab tare da Yazid tana ce masa "Mun gode, zaryar haka ta isa dan Allah, mungode Allah ya saka da alheri, idan kuma abin da kayi mata ne kake son a biyaka ka faɗa, wannan sintirin ya ishe ni idan ba wani abun kake nema ba".

Jikin Yazid yayi sanyi, har ya kai ƙofa Amina ta kira sunansa.

Tsayawa yayi ya waiwayo, yana ganin Amina yayi murmushi, ya gaisheta ita da Daddy.

Daddy ya ce "Waye wannan ɗin?"

Amina ta ce "Ɗan makarantar su Fadila ne, kwanaki shi ya kawo ga gida ma"

Daddy ya ce "Allah sarki, mun gode sosai kaji Allah yayi albarka"

Yazid ya amsa da Amin, ya fita.

Daddy ya kalli Amina ya ce "Jeki ki dubata" ya mayar da idonsa kan Hajiya Zainab bayan ya sallami Amina, ya fara ja mata kunne a kan wulaƙanta mutanen da ke zuwa gidan.

Sallama Amina tayi ta shiga ɗakin Fadila, Fadila taƙi amsawa ta shiga bin Amina da kallo.

"Fadila ya ƙarfin jiki kuma?".

"Ban sani ba, algunguma ƙila ma so kika yi ace na mutu, to da raina, abin da kike fatan bai faru ba. Kar kuma ki sake zuwar mini ɗaki bana son munafunci bana ƙaunar ki, bana ƙaunar ganinki".

"Fadila ba zuwa nayi muyi musayar yawu ba, dubaki na zo yi, kuma harshenki ya kiyayi furta miyagun kalamai a kaina, ni ɗin nan da kike gani sa'a ce da ni, ina zaune Allah zai kawo abin da zan fanshe wannan wulaƙancin da kike yi mini, ni da gyatumarki muke gwarawa dan haka ki bar shiga hurumina, tun ban saki a aji na koya miki darasin da na koya wa babarki".

"Dalla fita ki bani wuri, ke kin isa kiyi mini wani abu, banza 'yar ƙauye duk wata larura da ta sameni da koma menene, duk ba silarki bane, daga zuwa cin arziƙi kin aure mana uba, kuma in sha Allah sai kin koma gidan matsiyatan da kika fito".
Har Amina ta yunƙura za tayi magana, taji muryar Alhaji Ahmad a bayanta tana faɗin "Na gode Fadila, ba ita kike yiwa ba ni kika yiwa, kuma ki sani taki uwar ma da take ɗoraki a kan wannan aƙidar daga gidan matalautan ta fito, na gode sosai"

Ya ja hannun Amina, suka bar ɗakin.

A falo ma Hajiya Zainab ce take tata tijarar, duk da Amina bata san yadda suka yi da Daddy ba.

A falo suka zauna yana bawa Amina haƙuri, a kan abin da Fadila tayi mata, amma tayi murmushi ta ce kar ya damu ba komai.


Daddare Fadila ta saka Mummy a gaba tana tambayarta "Mummy, to yanzu wani hukunci kika yanke a kan maganata da wannan Salim ɗin?"

Mummy ta ce "Ai ban san mutumin banza bane, kuma tun da ba kya son sa dole a bar maganar, babanki zan bawa kuɗin ya mayar musu, bari ya shigo".


Kasancewar yau Alhaji Ahmad yana wurin Hajiya Zainab, tun da magariba suka yi sallama da Amina.


Washegari da safe, Alhaji Ahmad ya shiga wurin Amina, sai dai taga fuskarsa babu walwala sam.

Cikin damuwa Amina ta ce "Yallaɓai lafiya kuwa?"


Cikin matuƙar ɓacin rai ya ce "Yanzu abin da Zainab tayi ta mini adalci kenan? Ta san Fadila bata san yaron nan, amma ta kawo shi ta ce shi take so ta aura. Na karɓi kuɗinsu an tsayar da Magana, amma tana gaya mini wai Fadila ba ta so shiyasa take rashin lafiya, ta san da haka amma ta sa na karɓi kuɗinsu aure bai fi wata ya rage ba, kalen ta zubar mini da mutunci a idon mutane".

Amina tayi murmushi, tare da ƙulla wani abu a ranta, a fili ta ce "Zauna yallaɓai" Alhaji Ahmad ya zauna yana huci.


"Gaskiya idan har ka mayar da kuɗin nan, mutncinka zai zube, sannan kuma bai kamata a yi mata auren dole ba, aure ba zai yiwu da ƙiyayya ba, amma a wannan karon ya zama dole kayi playing role ɗinka na uba, ka nunawa Hajiya Zainab da Fadila kaine a saman su, bai kamata koda yaushe sai abin da suke so ba,. Yakamata a hukunta su saboda gaba".



Cikin damuwa ya ce "Meye abin yi? Ni yadda zan tunkari mutanen nan ne ya dameni, tun da ba zan mata auren dle ba,"

Amina tayi murmushi ta ce ga wata shawara........




(WACE SHAWARA KUKE TUNANIN AMINA ZATA BAYAR MUJE ZUWA)



AYSHERCOOL
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA NA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA
08081012143


73

Daddy ya yarda da shawarar da Amina ta bashi, saboda tsabar takaici ko Abinci bai ci ba, dama Hajiya Zainab ko ya kwana a wurinta ko bai kwana ba, a wurin Amina yake cin abinci.
Sai da ta bashi ya ci ya ƙoshi sannan ta bari ya fita.

Khalil kuwa bai ma san Fadila tayi rashin lafiya ba. Yana nan yana ta ƙoƙarin ganin yadda zai kwantarwa da Hafsa hankali a kan tafiyar nan da Mummy ta sanya yayi ya bar Hafsa.
Shi kansa ba a san ransa ba.
Ya dinga rarrashin Hafsa yana kwantar mata da hankali, a zahiri ta nuna masa bakomai amma ƙasan zuciyarta babu daɗi, tana son kasancewa da mijinta, su samu shaƙuwa da fahimtar juna, amma Hajiya Zainab ta zo ta gindaya masa wannan sharaɗi, tana ji tana gani, haka Khalil ya tsallake ya koma aiki ya barta, aikuwa yana tafiya ta dinga kuka, saboda zaman da suka yi yana bata kulawa sosai da sosai.

Alhamdilillah, Fadila ta ɗan warware daga rashin lafiyar da take yi, taji daɗin jikinta saboda magungunan da take sha, tana ganin yadda Salim ke kiranta a waya, amma taƙi ɗagawa ta share shi, ganin taƙi ɗaga wayar ya sanya ya koma tura mata saƙonnin amma shima Fadila taƙi amsawa.

Gaba ɗaya Fadila jira take taji Mummy tace mata an mayar da kuɗin Aurenta da Salim, amma taji shiru.

Gaza jurewa tayi, taje ta samu Mummy a sashinsa, Mummy na ganinta cikin kulawa ta ce "Fadila ya jikin naki ne?"

A hankali ta ce "Mummy da sauƙi" tayi maganar tana zama a kusa da Mummy.

Ta kalli Mummy ta ce "Mummy, haryanzu fa Daddy bai ce komai ba, ga lokaci na cigaba da ja, kuma sai faman damuna yake a waya, dan Allah Mummy kiyi wani abu a kai mana"

Mummy ta ce "Kiyi haƙuri Fadila, bana son nayi wani abu da zai sanya Hajiya Salma ta ji haushi a ne, nafi son na nuna mata cewa mahaifinki ne ya nuna baya so. To kuma kinga dai yadda nake fama da shi a kan abubuwa a cikin gidan nan, a duniya abu idan ba wanda ya shafi waccan banzar Yarinyar bace ba, baya ba shi muhimmanci ko kaɗan, amma kiyi haƙuri zan cigaba da yi masa magana, ki yi blocking ɗin lambarsa, zan hura masa wuta dole ya san abin yi, amma daga yau idan abu yana dmaunki kamata yayi ki mini magana mu tattauna".

Fadila ta langaɓe kai ta ce "Mumm, ba ƙin saurarata kika yi ba, kawai ki ka fara fushi da ni ba"

Mummy ta ce "Shikenan, koma dai menene yakamata ki dinga sanar da ni, kuma fa kawai ɓoye miki nayi ban gaya miki ba, nifa na raina kuɗin nan da suka kawo miki na aure, dan dai kawai kar nayi magana ne, abu yazo ya zama jangwam, amma ai kin fi ƙarfin dubu ɗari, ni Hajiya Salma ta bani mamaki, da ta iya bari aka kawo wannan ɗan kuɗin, nayi shiru ne dai kawai ban yi magana ba"

Fadila ta ce "Mhmm, ai shiru dai kawai nayi dan kar na ɓata miki rai, amma ko ba komai a tsiyace ma na zaci ko 200k za a kawo, amma duk matsayin Ubana wai aka kawo mini 100k saboda wulaƙanci sai kace 'yar talakawa".

"Koma dai menene idan aka mayar musu da tsiyarsu saje can su ƙarata"

Suka cigaba da hira suna tattaunawa.

Tun da Khalil ya koma wurin aiki kuwa, Hafsa take rashin lafiya, amma tunda suke waya bata taɓa gaya masa ba, a ƙalla a rana sai suyi waya sama da sau huɗu, sai dai bata yadda suyi Video call sai da daddare, saboda kar ta ɗaga masa hankali da rashin lafiyar da take yi.
Ko waya tayi da Mama, ita ma baya gaya mata ga halin da take ciki, ko gaya mata batun komawar Khalil da Mummy ta sa shi a gaba ya koma bata gaya mata ba, saboda bata son ta dinga tayarwa da Maman Hankali, tana murna tayi aure, ta fara kai mata ƙorafi.
Ko tambayarta da mama tayi, lokacin da tazo gidanta, ya zamanta da uwar mijinta, sai tace mata lafiya lau babu wata matsala.

Ga rashin lafiya, ga tsananin kewar mijinta da take damunta, bata taɓa tunanin haka take matuƙar ƙaunar Khalil ba sai da ya tafi ya barta ɗin nan.
Shi ma a nasa ɓangaren, haka yake fama da kewarta, yana son ta kasance a tare da shi, yadda zasu sake sosai ya mantar da ita irin wahalar da ta sha a rayuwa a baya, amma Mummy ta hana. Babban abin da yake tsoro, bai hana idan ya gama gininsa ya nemi ta koma can Mummy ta hana ba.
Duk da hakan, Hafsan ita ce take kwantar masa da hankali tare da yi masa nasiha a kan su yi wa Mummyn biyayya hakan ne kawai zai sanya su ji daɗin rayuwar aurensu.

Kusan kwanaki biyar kenan, Alhaji Ahmad bai yi magana a kan mayar da kuɗin auren Fadila ba, gashi har tana shirin komawa makaranta, kuma Hajiya Salma nata mitar yadda abubuwa suke gudana game da auren nan da ake shirin yi.

Har Falon Amina Hajiya Zainab taje ta iske Daddy, yana zaune yana kallon labarai, Amina kuma na kusa da shi tana tsifar kai.
Babu ko sallama taje ta tsaya musu a ka, Amina dai bata ko ɗaga kai ta kalleta ba, Alhaji Ahmad ne ma ya dubeta ya ce "Lafiya?"

"Lafiyar kenan, wai kuwa Ahmad kana tsoron Allah kuwa kana tsoron Azabarsa? Kai yanzu gaba ɗaya wannan Yarinyar ita ce a gabanka, abin da take so shi ne a gabanka ka tattarani ka watsar da ni da 'ya'yana?"

Daddy ya ce "Ita ce a gabana, tun da nima ba tayi watsi da lamarina kamar yadda kika yi ba, sannan ban gane in da maganarki ta dosa ba".

"Ai dama ba zaka gane ba, magana nake a kan kuɗin auren nan, nace maka ka mayar musu da kuɗinsu Fadila bata son yaron nan, amma kayi burus su kuma suna can suna shiri"

Daddy ya kauda kansa ya ce "Lokacin da kuka yanke zaku haɗasu ai baku yi shawara da ni ba, baki bari nayi playing role ɗina na uba ba, da nace zan yi wani abu a lokacin, cewa zaki bani da mutunci ban kyauta miki ba, dan haka yadda kuka haɗa abinku suka kawo kuɗi, sai ki koma ku warware su zo su karɓi abin su".

A fusace ta ce "Wallahi yanzu na sake tabattar da 'ya'yan naka ma baka ƙaunarsu, tayi maka asiri ta rabaka da su"

Amina kuwa haushi ya kamata ta ce "Ai asirin ma iyawa ne, kema ki yi yayi mana".

Daddy ya ce "Meenal, kar in kuma jin bakinki"
Amina ta kashingiɗa da kujera ta cigaba da tsifarta hankalinta a kan Tv.

Hajiya Zainab ta ce "Yanzu ka gwammace jinin Fadila ya cigaba da hawa, ta rasa ranta kayi mata auren dole saboda son zuciyarka?"

Daddy ya ce "A'a, saboda son zuciyarki dai"

"Kaga, zaka mayar da kuɗin nan ne ko kuma a'a"

"Ba zan mayar ba, tun da ku kuka kawo shi a matsayin wanda zata aura, ni ba zan zubar da mutuncina a idon duniya ba".

"Kai har wani mutunci ne yayi maka saura a idon duniya, ai tun daga lokacin da ka auri wannan 'yar tsatsitsiyar a bar, ba kunya babu tsorn Allah ka dinga yawo da ita a gari, kuka gama watsewa a titi, ai tun daga nan kayi asarar wani abu wai shi mutunci. Ka fifita son ranka a kan yaranka, zakaga abin da zai faru ka cigaba kar ka fasa, ka cigaba da ƙona muni rai"

Bai sake tanka mata har ta fice, a hankali ya ce "Kinga halin matar nan ko Meenali, ba zata canza hali ba"

Amina ta ce "Rabu da ita, kayi abin da nace maka kawai, a nan zaka tabattar mata da kaine gaba da ita. Kuma hakan ne zai sanya yaranka su san menene rayuwa. Amma idan aka cigaba a haka, ko wanda take so ɗin ta kawo daga baya, idan ya aureta yadda mahaifiyar ta ke yi maka ita ma haka zata yi a nata gidan, kuma ka san dai mazan nan na ƙarshen zamani, ba kowa ne zai ɗau hakan ba"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne, hakan za ayi da ni suke zancen"

Fadila kuwa na ɗakin Mummy, tana jiranta ta zo ta bata feedback na yadda suka yi da Daddy.
Sai dai Mummyn na shigowa ta kalli fuskarta ta san babu nasara, cikin karaya ta ce "Mummy ya kuka yi?"

Ta girgiza kai ta ce "Ke lamarin ubanki yafi ƙarfin tunanina yanzu, mirsisi yaƙi amincewar"

Ɗora hannu Fadila tayi a ka ta fashe da kuka, hakan ya saka kanta sarawa ta durƙusa a wurin tana kuka ta ce "Ni wallahi Mummy bana son shi, zuciyata zata iya bugawa, dan Allah Mummy kiyi wani abu a kai, kin san bana son shi, Wallahi na aureshi mutuwa zan yi, zuciyata zata fashe"

Mummy ta ce "Ke Fadla nutsu mana, kinga an yi auren ne, kin manta baki da lafiya sai kin kuma kwanciya tukuna". Ai kan ta rufe baki, Fadila ta riƙe ƙirji tana kuka, ta fara numfarfashi sama sama.

A gigice Mummy ta riƙeta tana faɗin "Ke Fadila meye haka?" Bata amsa mata ba ta cigaba da kuka tana dafe ƙirji.

A gigice Mummy ta ɗai wayarta ta kira Daddy, kamar na zai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga.

A ruɗe ta ce "Kayi sauri ka zo, jikin Fadila ya tashi"

Da sauri ya ajiye wayar, ya fito ya nufi sashin Hajiya Zainab, yana zuwa ya tarar da Fadilan a kwance, tana kuka ga hannunta ta riƙe ƙirjinta.
Hajiya Zainab ta kalleshi kamar zata fashe da kuka ta ce "Ka gani ko? Kaga abin da ka ja ina neman na rasa 'ya ta, wallahi duk abin da ya sameta kaine kuma na zan yarda ba"

Ya kalli Fadila da ke numfarfashi ya ce "Duk dan saboda ba kya san auren ne kike nema ki halaka kanki?" Tayi shiru tana kuka ba tare da ta furta komai ba.

Ya dubeta ya ce 'Ba kya son auren ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Shikenan naji, dama ku kuka kawo shi, aka ce na aura miki, zan mayar musu da kuɗin aurensu, amma bisa sharaɗi, yau muna Alhamis, na baki nan da zuwa ranar Alhamis

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login