Showing 174001 words to 177000 words out of 296192 words
ance kin yi nasara a cimpetiton da ake duk shekara a Abuja, amma baki yi mana ko walima ba"
Amina ta ce "Ai ma idan nace kuzo, na san ba zuwa za kuyi ba, ni irin cake ɗin da ki ke yi nake son na iya, mun taɓa oreder sa da 'yan ajinmu yana mini daɗi sosai"
"In dai Cake ne, idan na fara classes ɗin, ki zo na koya miki kyauta, idan na koma gida zan bayar a kawo miki".
"Dan Allah dagaske?"
Yusra ta jinjina mata kai.
"Kaii amma naji daɗi wallahi, Allah ya saka da alheri, aikuwa zan zo, idan kina so nima sai in koya miki abincin gargajiya, irin su dambu, Alkubus, tuwo kala kala, normal tuwo da na masu kamar ciwon sugar, har da su gurasa fa na iya su sinasir da sauransu" ɗan shiru Yusra tayi tana nazartar Amina ta ce "Dagaske duk kin iya wannan girke-girken?"
"Wallahi duk na iya, Inno ta koya mini girke-girke, har su yadda ake haɗa kwaɗon salak, kwaɗon rama da abubuwa kin san sun fi lafiya"
"Gaskiya ne, ko zamu shirya wani business tare ne? Muyi join classes, ki dinga koyar da Abincin gargajiya"
Cikin sauri Amina ta ce "Eh zan iya wallahi" Hajiya Zainab ta fito tana faɗin muryar wa nake ji ne haka?"
"Nice Mummy, na zo Amina ta tsareni da surutu, ina ga ma zamu fara join class tare, tun da na ga ta iya girkin gargajiya"
Haɗe rai Mummy tayi ta ce "Ke da wa? Sai ki ɗau wannan ƙazamar a cikin harkar sana'arki, wa zai mini aikin gidan nawa, shareta dan Allah ya gidan naku ya Mummynki?"
"Tana nan lafiya Mummy, ya hanya?"
"Lafiya lau, Fadilan tana ɗakinta. Ke kum wuce kije kiyi mini abin d ana saka ki, sai shegen surutun tsiya duk wanda ya zo ki tsareshi da surutan banza"
Amina ta juya rai a ɓace, ta bar falon.
Saura kwanaki uku kacal su Amina su fara WAEC, gaba ɗaya a gajiye take, Hajiya Zainab ta tsiro da sabbin salo na muzguna mata saboda taga jarrabawa take fuskanta, tayi ta sakata aiki ta hanata sakat balle tayi karatu, sai dai ta bi dare tayi karatun.
Yau da aka tashi daga makaranta, gidan Daddy ta wuce, domin ta zauna ta huta da yamm sai ta koma gida.
Sai dai tana zuwa ta tarar da Daddy a gidan.
Yayi mamakin ganinta, mussman yadda ya ganta a gajiye.
"Babyna lafiya kuwa?"
A gajiye ta ce "A gajiye nake ne, zuwa nayi na huta na san da naje gida, matarka ba zata bari in huta ba, za tai ta sakani aiki, ni kuma a gajiye nake hutu nake so, jarrabawa zamu fara"
Cikin matuƙar tausayinta ya miƙe ya janyota jikinsa yana mata sannu.
Ta lumshe idanunta ya zare mata hijjabin jikinta, yana ɗan matsa mata jikinta a hankali.
"Da na sani na zo na ɗauko ki daga makarantar, ni gani nayi ma kina ramewa"
"Ba dole in rame ba, wannan matar ta sakani a gaba, kullum cikin zagi da hantara"
"Am sorry on behalf of her, bari in kawo miki ruwa" ya tashi ya ɗauko mata ruwa, ya kawo ya bata ta sha, yayi mata order Abinci.
Kusan tun da Hajiya Zainab ta dawo, basu sake samun damar haɗuwa ba sai yau.
Ta nemi wuri ta kwanta cike da gajiya da rashin bacci da ya sanya mata ciwon kai.
Daddy ya duƙufa Sosai, yana ta aiki a system, Amina ta ce "Daddy aikin me kake yi ne?"
"Lissafi nake, a cikin Azumi zan fitar da Zakka in Sha Allah"
"Mhmm dama kana bada zakka?"
"A'a wannan karon zan fara" yayi maganar yana hararata
Tayi murmushi ta ce "Wa zaka bawa?"
Ya ɗan nisa ya ce "Mai rabo"
Amina ta ɗan nisa ta ce "Ina son dan Allah a taimakawa 'yan garinmu da wani abu daga cikin zakkar, muna da mabuƙata sosai"
"Shikenan, za a duba in sha Allah Meenalina"
"Godiya muke, Allah ya ƙara arziki"
"Amin Sweetheart, jibi in Allah ya kaimu zan koma"
Ta ɗan zabura ta ce "Haba dai?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh"
Kamar tayi kuka ta ce "Daddy why?"
Ya riƙo hannunta ha ce "Meenalina, am so much addicted to your care. Idan ina cigaba da ganinki, asirnmu zai iya tonuwa, sannan bana jin daɗin yadda wasu abubuwan suke gudana, alhalin ba zan iya baki kariya ba. Idan na koma na yi nesa da ke, maybe zan fi samun nutsuwa iyakaci dai zan yi matsananciyar kewarki".
Shiru Amina tayi, amma kusa maganar Daddy haka take, idan suna cigaba da ganin juna, kusancinsu sake ƙaruwa yake yi, kuma a kowane irin lokaci, Asirnsu yana iya tonuwa, dan a dawowar Hajiya Zainab, da taƙi yadda su haɗu, har Kitchen ya bita.
"Maganarka haka take Daddy, Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi, nima ba zan so asirnmu ya tonu ba, amma kar ka manta alƙawarrukan da ka yi mini"
"In sha Allah ba zan manta ba, zan yi Kamar yadda nayi alƙawarin, zan san hanyar da zan sama mana, kiyi karatu da kyau my love" yayi maganar yana rungumeta yana jin yadda yayi kewarta sosai.
Suna tare har Yamma liƙis, sannan ya kai ta gida ya ajiyeta a bakin layi, ya wuce.
Da daddare Hajiya Zainab tana ta hira da ƙawayenta a waya, Daddy yana gefe yana cigaba da lissafinsa, gefe guda kuma kewar Amina tana damunsa, duk baya walwala. Hakan bai damu Hajiya Zainab ba, ganin yana lissafin kuɗi ya sanya ta matsa kusa da shi ta ce "My dear ya batun zuwa nema wa Khalil aure ne?"
"Ki ɗan bani lokaci tukuna" yayi maganar ba tare da ya kalleta ba.
"Amma kai fa kace idan mun dawo zaka nema masa"
Daddy ya ce "Yanzu abubuwa sun yi mini yawa, ki ɗaga mini ƙafa sai na koma na dawo tukuna"
A ɗan hasale ta ce "Amma dai ka san na riga nayi maganar da uwar yarinyar ko?"
"Kinga idan ba zaki jira kamar yadda nace ba, ki je ki nema masa auren da kan ki"
"Ta yaya ma e zata nemi aure, wannan ai sai su zata ko ƙarya nake yi?" Shiru yayi bai ce mata komai ba.
Ta sake kallonsa ta ce "Wai lissafin me kake ta yi haka ne?"
"Kuɗin na Zakka ne" ya bata amsa.
Murmushi tayi ta ce "Wow, ashe fa lokaci ya kusa, zan yi magana da Turai, a san abin yi a bayar a gidauniyarta"
"A'a wannan karon, da kaina za bawa waɗanda suka dace" ya bata amsa kai tsaye.
"Kamar yaya, ni ba wanda suka dace ɗin nake bawa ba?"
"Wannan karon haka na ga dama"
Gaba ɗaya tunda ta dawo, ta kasa gane kan Alhaji Ahmad, gaba ɗaya ya canza, sai wasu muzurai yake yi mata, duk maganar da tayi masa, sai yayi fushi ya hayayyaƙo mata abin da ba yayi mata.
"Wai ni Ahmad me kake nufi da ni ne? Babu damar nayi Magana sai ka hauni da masifa, kana wani cika kana batsewa me nayi maka ne? To bari na gaya maka, kuɗin zakkar nan ba wanda za a bawa wallahi, ga in da aka saba bayarwa duk shekara, kawai wannan karon kace ba haka ba".
Bai ce mata uffan ba, ya tashi ya bar mata wajen.
Hajiya Zainab ta sako shi a gaba da tijara kala kala, ta yau daban ta gobe daban, ta tsiri salo salo na rashin mutunci. Hakan ya ƙara rura wutar sanya shi ya koma ya bar mata gidan.
Amina ta makaranta, ya biya yayi mata sallama ya tafi, aikuwa sai da tayi kuka.
Abin da ya faru tsakanin Hajiya Zainab da Alhaji Ahmad, ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, tsawon shekarun da suka shafe a tare, bai taɓa mata abu makamancin haka ba, ya kan yi fushi wasu lokutan, amma ko tayi laifin shi me yake bata haƙuri. Duk abin da ta ce ayi shi yake yi, amma a wannan karon, gaba ɗaya ya sauya mata, sai wani ji da kai yake yana hura hanci.
Da fari tayi tunanin ta gaya wa su Hajiya Turai, amma sai taga yin hakan kamar ta faɗo ne da nuna gazawa, ace kamar ita miji ya yiwa wulaƙanci, dan haka ta ƙudurce zata ɗau mataki da kanta.
A yau ne su Fadila suka koma makaranta suma, domin cigaba da karatun sabon zango.
A wannan karon ma, da result ya fito babu mai grade ɗin Yazid, shi da wani ɗan level 4 duk department ɗin babu mai grade ɗin su.
A wannan karon ranar da aka dawo makaranta, ranar Yazid ya dawo shi ma, sai dai yayi ƙalau da shi ya ƙara haske ya ƙara kyau.
Tun kallon farko da yayi mata, lokacin da ya shigo ajin, ya hanzarin kawar da kansa, a ransa yake faɗin "Tubarkallah, masha Allah". Tayi masa kyau sosai da sosai.
Babu wanda ya kula wani, ƙarewa Yazid yi kamar babu wata alaƙa da ta taɓa shiga tsakaninsa da ita.
Kusan wata guda kenan an shiga na biyu, da komawar Daddy Lagos, Amma duk da yadda Amina ta mayar da hankali a kan karatunta, amma tana jin kewar Alhaji Ahmad sosai da sosai. Sai dai kusan kullum cikin waya suke.
Yana cigaba da kwantar mata da hankali yana rarrashinta. Ya zo gari sau ɗaya cikin Azumi suka haɗu da Amina, ba tare da kowa ya sani ba, sai guards ɗinsa na ɗayan gidan.
Kwanansa biyu idan Amina ta tashi daga makaranta sai ta tafi wurinsa,tayi masa girkin abin shan ruwa, sai bayan an sha ruwa ta tafi gida, sai ta yiwa Baba ƙaryar cewa tana gidansu Azima. Kafin Daddy ya koma, ya tura mata kuɗi masu yawa a account ya ce ta sai kayan salla.
Hajiya Zainab ta sha mamakin rashin nemanta da Alhaji Ahmad bai yi ba, tun da ya tafi ko flashing bai yi mata ba, sai dai ya kira Fadila.
Ita ma kuma Hajiya Zainab girman kai ya hanata kiran sa a waya.
Shiru² bai dawo ba ba suyi waya ba, balle su sake tattaunawa a kan Auren Khalil.
Tuni Amina kuma sun riga sun gama Waec, Neco suke facing, ana ta yi musu lesson a makaranta.
Yau Asabar ce amma zata shiga makaranta, suyi karatu.
Har ta fito falo, Hajiya Zainab ta dubeta ta ce "Ina zaki?"
Amina ta ce "Makaranta ne ake nemanmu, muna ta shirin fara jarrabawa"
"Babu in da zaki, baƙi zan yi girki zaki yi mini"
Haushi ne ya kama Amina ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Wallahi bana jin daɗi, kuma zuwana makaranta yana da muhimmanci".
"Ke ta shafa, na gaya miki aiki zaki yi mini, idan kika fita kuma zaki ga abin da zan miki" ta wuce ɗakinta ta bar Amina a falon. Tana shigewa sashenta, Amina ma ta sa kai tayi ficewarta. Dan yanzu kawai tana ɗagawa Hajiya Zainab ƙafa me, amma ta fara ƙulewa. Kuma bata tsoronta.
Baba baya nan yaje ƙauye, tun da aka yi Azumi bai je ba, har salla aike kawai ya yi musu, dan haka a Wannan karon ya samu damar zuwa. Amina tayi tafiyarta makaranta. Ba tare da sake bi ta kan umarnin Hajiya Zainab ba.
Fadila tana ganin Yazid, amma yadda baya kulata, haka ita ma ba kulashin take ba, duk da hakan yana damunta kuma tana da burin taimaka masa kamar yadda tayi niyya da farko.
Hankali kwance Amina ta dawo gidan, kamar ta dawo gidan ubanta.
Kasancewar ba kowa a falon, ta wuce sashinsu, ta yi wanka ta nemi wuri ta kwanta, dan kwanan nan ta kasa gane kanta.
Ta so tabi Baba ƙauye, ko ta ɗan sarara da masifar Hajiya Zainab, amma ba zai yiwu ba, saboda wannan jarrabawar da take gabanta.
"Amina" Hajara ta kira sunanta lokacin da ta shiga ɗakin.
Amina ta ɗaga kai ta kalleta ba tare da ta ce mata komai ba.
"Ki zo Hajiya na kiranki"
Amina tayi tsaki sannan ta ce "Ina zuwa"
Ta miƙe a hankali, tana jin yadda mararta ke ƙullewa tana saki, wanda alama ce ta a kowane lokaci tana iya ganin period.
Ko gezau ba tayi ba, da tayi arba da idon Hajiya Zainab da ke jifanta da wani irin mugun kallo, ga Fadila ita ma a tsaye a falo.
Ta ƙarasa in da suke tana ɗan yamutsa fuska ta ce "Gani"
"Ke! Me nace miki ɗazu da zaki fita?" Hajiya Zainab tayi tambayar kamar ta mari Amina.
"Ai da kika sakani aikin na baki uzurina, baki taɓa sakani aiki na ƙi yi miki ba, komai wahalarsa komai gajiyar da nayi ba, a karo ɗaya dai ai ya kyautu kiyi mini uzuri".
"Ke! Ni kike gayawa haka? 'yar ƙauye matsiyaciya, ni zan saka ki aiki ki fice ki ƙi yi mini, sai ka ce kina gidan ubanki, to tattara kayanki zaki yi ki bi matsiyacin ubanki da be koya miki tarbiyya ba in da kika fito, tun da baki da mutunci baki iya cin arziki ba,. Shashasha 'yar talakawa"
Cikin dakewa Amina ta ce "Ina Arzikin yake, ai ban ganshi ba, kuma kar ki sake zagar mini uba, dan ya bani tarbiyyar da kika gaza bawa naki 'ya'yan.
Buɗe baki Hajiya Zainab tayi, ta kasa magana, ita tsoro da mamakine ma suka cikata.
Fadila ta rikice ta ce "Ke Mummyn kike gayawa haka? Ba 'yar matsiyatan ba ce ke? To wallahi sai kin bar gidan nan"
Hajiya Zainab ta ce "Gaskiya ne, da aka ce ɗan ƙauye bai iya samun wuri ba, ke jeki watso mini kayanta ta zo ta bar mini gida"
"Idan kin mutu ayi miki gammo, ki ɗora gidan a ka ki tafi kabari da shi. Haba tunda na zo gidan nan nake muku bauta, amma kullum cikin zagina kuke da cin mutunci, idan na tafi ki samu kofin ruwa ki haɗiye gidan. Kuma Allah ya isan Babana cin mutuncin da kuke masa ba yau ba gobe. Zan bar miki gidanki amma zaki ga abinda baki tsammani ba, saboda zan tabattar miki GABA DA GABANTA, kuma maganin biri karen maguzawa" Amina tayi maganar rai a ɓace, da alama ta daɗe tana jiran Irin wannan damar.
Ta juya zata bar falon, Fadila ta saka hannu ta fizo Amina a hasale, da niyyar ta kwaɗa mata mari, amma kasancewar jikin Amina babu ƙwari ya sanya ta faɗi, kanta ya bugu da Centre table.
Ba zafin buguwar da tayi ne ya ɗaga mata hankali ba, wani irin ƙullewa da mararta tayi ne, ta sanya ta zuba wani uban ihu ta rintse idanunta.
Saroro Hajiya Zainab da Fadila suka yi, ganin Jini yana gangarowa daga jikin Amina ya fara gudu a tsakar falon!!!
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Watpad@ ayshercool7724
Arewabooks@ ayshercool7724
56
Wani irin gumi ne yake tsatstsafowa daga goshin Amina, duk da yadda sanyin Ac ya bawa ɗakin sanyi.
Ta riƙe cikinta tana jujjuya kanta, saboda yadda take jin wani abu yana dunƙulewa a cikin mararta.
Ita kanta tayi mamakin yadda jini yake fita daga jikinta, dan bata taɓa period a haka ba.
"Ke Hajara!" Mummy ta kwaɗawa Hajara kira. Da sauri Hajara ta fito, sai dai tayi turus da ganin halin da Amina ke ciki.
Cikin ƙyama Hajiya Zainab ta ce "Janye mini ita daga nan, karta cigaba da ɓata mini wuri ki zo ki gyaran Wannan ƙazantar da tayi"
A rikice Fadila ta ce "Mummy, kalli fa yadda take zubar da jini, anya ba za a kai ta Asibiti ba, kar fa wani abu ya sameta"
A hasale ta ce "To ya sameta ɗin mana, ina ruwana ba yanzu a gabanki ta gama ci mini mutunci ba, ko sharafa take zata mutu sai ta bar mini gidana yau. Ke ba zaki janye mini ita bane!" Ta yiwa Hajara maganar cikin tsawa.
Hajara taje kan Amina, zata ɗagata amma ta kasa, Amina ta riƙe hannun Hajara hawaye na zubowa daga idonta.
"Hajara zan mutu, wani abu na yawo a marata, dan Allah ki taimaka mini, ki kira mini Baba kar in mutu in nemi yafiyarsa kar in mutu"
Hajara ta ce "Daure ki tashi, kinga kina ɓata wurin"
"Ba zan iya ba Hajara, cikina ciwo yake mini, wani abu ne ya dunƙule a ciki"
"Daure dai ki tashi, na rakaki ki gyara jikinki"
Amina ta yunƙura ta tashi, amma jinin ya cigaba da zubowa, Amina ta kuma durƙushewa, tana jujjuya kai.
"Mummy this is serious fa, you have to do something, duk abin da ya sameta fa ni za ace, ni ban taɓa ganin period ya yiwa mutum haka ba, dan Allah kiyi wani abu a kai"
"Ni me zan mata, ba abin da zan yi mata, koma menene ya lafa mata ta kwashi kayanta ta bar gidan nan, idan ma pretending take yi, ta gama ta bar mini gida"
"Mummy ba pretending bane, tayaya mutum zai dinga zubar da jini haka, bari na kira Doctor Aliyu ya zo ya dubata, kan wani abu ya sameta kar jininta ya ƙare ta mutu"
Sai kuma jikin Hajiya Zainab yayi sanyi, dan ita ma jinin ya bata tsoro.
Ta ce "Shikenan, ki kirashin"
Da ƙyar Hajara ta iya kai Amina ɗaki, ta shiga banɗaki, ta cire kayan jikinta, sai dai abin da ya ƙara tsoratar sa ita bai wuce yadda jinin yake zuba da guda-guda ba. Amina ta waro ido tana tunanin wani irin ciwo ne haka yake damunta.
Ta kalli mudubin da yake banɗakinta, taga yadda gefen goshinta ya kumbura, saboda buguwar da tayi, wurn sai zafi yake yi mata, ga kanta da yake mata ciwo dama tun kan hakan ta faru.
Ji tayi jiri ya fara ɗibarta, dan haka ta nemi wuri ta zauna, tana addu'a a zuciyarta Allah ya sa ba wani mugun ciwon ne yakamata ba.
Tunani ta dinga yi, tunda Hajiya Zainab ta koreta, ta tafi gidansu Azima tayi zamanta, zuwa lokacin da zata kammala Neco, ko ta zauna a gidan Alhaji Ahmad, ta ƙarasa jarrabawarta, kuma ta kanainaye shi ta hana shi zuwa inda Hajiya Zainab ɗin hake.
Duk da halin ciwon da take ci, sai da tayi ƙwafa ta ce "Zaki ga tsiya, zaki ga matsiyaciya 'yar ƙauye kuma 'yar talakawa, idan takenki rashin mutunci, da kuma wulaƙanta ɗan Adam, zan nuna miki gaba da gabanta, zan rama abin da kike mini ni da mahaifina hankali kwance, da ni kike zancen".
Jiki babu ƙwari, ta wanke jikinta, ta fito tana bin bango, ta shiga ɗaki ta saka pad, ta saka wata rigar ta nemi wuri ta kwanta, saboda a zaune ma jirin take ji.
Hajara taje ta zage, ta gyara wurin da Amina ta ɓata da jini, Hajara ta fara zargin wannan jinin kuwa ba ɓari Amina tayi ba.
'Innalillahi wa innalillahi raji'un, idan haka ne yarinyar nan ya babanta zai ji? Gaskiya wannan lamari akwai matsala, da rabon asiri zai tonu. Da Hajara ta fara jin tausayin Amina saboda yarintarta kuma ɓari ba abu