Showing 150001 words to 153000 words out of 296192 words

Chapter 51 - GABA DA GABANTA

seat ya ce "Da na huta kwana biyu, da yawan surutunki da rigimar tsiya"

Ta ɗan marairaice ta ce "Kenan takura maka nake"

"Eh to ba nace ba, surutunki bai fiye takura mini ba, kamar gaddama da rigimar rashin dalili"

"To ka saka a mayar da ni in da ka ɗauko ni tun da haka ne"

"As you wish, bari in yiwa direban magana ya sauke ki sai in ɗoraki a babur ki tafi"

Kwaɓe fuska tayi zata yi kuka ta ce "Au yanzu da gaske takura maka nake yi, kuma sai ka mayar da ni?"

Dariya yayi ya ce "Ji mini yarinya da rikicin gangan, ke fa kika ce na mayar da ke in da na sa aka ɗauko ki"

"To ni ba in da zan koma" ta faɗa tana haɗe rai tare da gyara zamanta.

"Haba Meenalin, meye na fushin kuma? Za a nemo kayan wainar fulawa idan ma cewa ki kayi in soya miki, sai in ɗaura zani in soya miki"

Dariya ce ta ƙwace mata ba tare da ta shirya hakan ba, ta ce "Wa yaga Daddy na soya wainar fulawa, da sai na maka hoto a haka" Dariyar ta ta kawai yake kallo, gwanin burgewa kamar kar ta daina.

Ya gyara zamansa ya ce "Kin san gidan ne tun da ba zama nake a cikinsa ba, ba bu kayan masarufi a ciki, tun lokacin da na riƙe muƙami a gwamnatin baya aka bani shi, idan ba na shigo Abuja ba bana zama a cikin sa, na cewa Khalil ya zauna a ciki, ya ce yayi masa nisa da wurin aikinsa, sai mun zo hutu kawai muke zama".

"Gidan me kyau kuwa, to a can Lagos ɗin ma kana da gida?"

Ya ɗaga mata gira alamar eh.

"Mmm lallai Daddy, kana jin daɗinka, ka dinga sawa ana Abincin sadaka kana rabawa mabuƙata, ka godewa Allah, Allah bai jarrabeka da tashin hankalin rashin muhalli ba" tayi maganar tana duba wayarta, ba da wani serious tayi maganar ba, amma maganar yaji ta shigeshi sosai.

Har ta manta da tayi maganar sai kuma ta ɗora da cewa "Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce 'Dukiyar me bayarwa bata taɓa tawaya saboda yana bayarwa. Ka lura a duk lokacin da ka yayewa wani damuwa, sai kafi wanda ka yiwan shiga farinciki, kyauta akwai daɗi, ka bawa mutum abu kaga yana murna, saifa ka gama shekarunka kana salla ba a karɓa, amma cikin rahamar ubangiji a sanadiyyar faranta ran bawansa ɗaya, sai ya yafe maka, ai shi Allah gafuru rahim ne"

"Haka ne sayyadata, shi yasa bana manta lokacin da kika mini kyautar fura da Nono da zan yi tafiya, tun daga lokacin kika ƙara kima a idona"

Tayi murmushi ta ce "Allah ya ƙara arziki, ka ci kaita bayarwa"

"Ameen ya Allah"

"Daddy na ji kace Khalil a garin nan yake aiki, ba zaka je ka ganshi ba, naga ha daɗe bai je gida ba"

"Aikuwa Yakamata in je ɗin, dan ya daɗe yana magiyar in je in ga gininsa, amma Allah bai sa na shigo Abuja ba, bari in kira wayarsa in ji, idan yana nan anjima sai in je"

Amina ta gyaɗa kai, Daddy kuma ya nemi wayar Khalil ya kira.

Sai da ga kusa yankewa sannan ya ɗaga, cikin numfarfashi yayi sallama.

"Khalil, lafiya kuwa naji kana numfashi da kyar?"

"Lafiya lau Daddy, bana jin daɗi ne kawai"

"Subhanallah, meke damunka?"

"Nima ban sani ba, ji nake dai kamar zuciyata ce take ciwo, bana iya numfashi sosai"

A rikice Daddy ya ce "Kana wane Asibitin?"

"Ina quarters ni banje Asibiti ba"

Daddy ya katse kiran yana mita "Wannan wane irin shahsahnci ne, ya zauna a gida yana fama da ciwo, yi sauri muje mu ajiyeta, mu wuce can wurin Khalil ɗin" yayi maganar cikin damuwa.

"Daddy ka kwantar da hankalinka, Allah ya bashi lafiya, ni ka sani a napep a kaini gidan"

Ya girgiza kai ya ce "No, muje a kai ki tukuna"

Amina ta ɗan ƙura masa ido sannan a ranta ta ce "let me see if I can do something, Hajiya Zainab Gaba akwai gabanta"



AYSHERCOOL
0808102143GABA DA GABANTA
               BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL


49

Sake kallon Daddy Amina tayi, taga yadda damuwa ta mamaye ilahirin annurin da yake ci da, ta ɗan yi ƙasa da muryarta ta kira sunansa "Daddy"

Ya waiwayo ya kalleta, ba tare da ya amsa mata ba.

"Dan Allah ka kwantar da hankalinka, in sha Allah yana nan lafiya, naga duk ka shiga damuwa"

Ya ɗan sake kallonta ya ce "Yanzu har damuwa ta bayyana a fuskata?"

"Eh mana, ga damuwa nan kwance a fuskarka ina gani"

Ya ɗan shafi fuskarsa ya ce "Dole in damu, yanzu kamar Khalil da girmansa da komai, ba shi da lafiya amma ya kasa zuwa Asibiti, kuma ya ƙi gayawa kowa haka ake yi, idan ya cutar da rayuwarsa fa, wannan ai shirme ne"

"Haka ne, amma ka kwantar da hankalinka, ka fara jin ta bakinsa kafin ka yanke masa hukunci, ka bi komai a hankali ka gano kan rashin lafiyar ta sa, akwai malaminmu da ya gaya mana, akwai cututtukan da sukan faru da basu da alaƙa da magani, nutsuwa da kwanciyar hankali kawai mara lafiyan yake buƙata"

Daddy ya gyɗa kai ya ce "Haka ne"

"Yauwa dan haka dan Allah ka kwantar da hankalinka, idan kaje kar kayi masa faɗa, sannan kuma ka ɓoye wannan damuwar da ke fuskarsa kar ka sa ya karaya, kuma kaga kai ma baka da cikakkiyar lafiya"

Kallon Amina yake yi, 'yar ƙarama sai hikima, tana ta ƙoƙarin taga ta kawar da tasa damuwar.

Ya ɗan ja numfashi ya sauke ya ce "To shikenan, na gode sosai"

Hakan yayi daidai da tsayuwar motar a ƙofar gidansa, har zata sauka ya ce "Ki rubuta duk abin da kike buƙata, ki bawa Joseph, zai sayo miki"

"To wanne ne Joseph ɗin?"

"Dogon mai suma"

Amina ta jinjina kai ta fice daga motar.

Kai tsaye quarters ɗin Khalil yake su Daddy suka nufa, suna zuwa Daddy ya tarar da wani abokin aikin Khalil ɗin tare da shi.
Khalil ya rame yayi baƙi, cikin girmamawa abokin Khalil ɗin ya gaida Daddy, Daddy ya amsa masa sannan ya mayar da dubansa kan Khalil ya ce "ya aka yi ka zauna haka ba ka je Asibiti ba?"

"Daddy naje, idan na sha maganin bana jin komai, shi ya sa na daina zuwa"

A fusace Daddy ya kalleshi ya ce "Kuma saboda shirme, da rashin sanin ciwon kai ka kasa kirana ko mahaifiyarka ka sanar mana, kawai kayi zamanka kana fama da ciwo, da sa dai ace mini in zo in ɗau gawarka? To idan kai baka buƙatar rayuwarka ni ina buƙata, ku kenan ku biyu Allah ya bani ka zana kana wasa da lafiyarka, tashi mu tafi ni muje Asibiti"

Khalil wani irin jiri yake fama, da ƙyar ya iya miƙewa tsaye, ƙarshe sai sa shi aka yi a mota, suka tafi Asibiti.
Suna zuwa aka yi masa gwaje-gwaje aka tabattar da jininsa ne yayi ƙasa sosai Hypotension, haka sugansa ma saboda rashin cin abinci.

Nan da nan likitoci suka yi ta kai kawo a kan Khalil, ana saka masa ruwa da allurai, sai ga shi ya ɗan farfaɗo har yana iya zama da kansa, Daddy da kansa yaje ya nemowa Khalil Abinci, ya zauna ya sa shi a gaba, yana zare masa ido ya ci, kamar wani ƙaramin yaro (Iyaye masu daɗi, Allah ya ƙarawa iyayenmu lafiya da nisan kwana, wanda suka rasu kuma Allah ya yi musu rahama)

Sai da ya tabbatar Khalil ya ƙoshi, har ya iya shiga banɗaki yayi alwala ya dawo ya yi salla.
Daddy ya cigaba da yi masa faɗa.
"Ni ban san ma dalilin da yasa ko gida da kake zuwa ƙarshen wata ka daina ba? Gaba ɗaya ka ɗauko wasu sabbin ɗabi'u, nema ma kake ka cire kanka daga cikinmu, mahaifiyarka na ta complain a kan ko kiranta baka yi a waya"

Kamar Khalil zai kuka ya ce "Daddy ya zan yi, ko na kirata a waya sai ta nemo abin da za tayi mini faɗa, ta rabani da yarinyar da nake so, wai yanzu wata zata aura mini"

"To sai me, a kan hakan kake nema ka kashe kanka? Ba zaka yi mata biyayya ba, naga dai ba zata zaɓi abin da zai cutar da kai ba" Shiru Khalil yayi Daddy ya cugaba da banbanminsa, dama ya san Daddyn ba zai goyi bayansa ba, duk abin da Mummy ta shirya masa shi kawai yake aiwatarwa.
Sai bayan sha ɗayan dare aka sallami Khalil, a kan sharaɗin, zai koma washegari ya sake ganin likita.

Daddy bai koma gida ba sai sha biyu saura na dare, abin mamaki yana zuwa ya tarar da Amina a falo ba tayi bacci ba tana jiranshi.

Da sauri ta tashi tana masa sannu da zuwa.

"Ya aka yi baki kwanta ba?"

"Ai kona kwanta ba zan iya bacci ba, baka dawo ba kuma ban san a wane hali Khalil ɗin yake ba, nayi ta ƙoƙarin kiranka a waya, amma bani da network gaba ɗaya"

"Jikinsa da sauƙi sosai, na mayar da shi gida ma sun sallemshi daga Asibitin".

"Allah ya bashi lafiya, kaje ka kintsa ka zo ga Abinci na maka"

Ya kalli inda ta nuna masa fulasan abinci ya ce "A ina aka samu Abinci?"

Ta ce "Sautun kayan wainar fulawata nayi da kuma abin da zan dafa maka, ga tuwon Alkama nan da miyar kuɓewa sai kuma Coffee, sai kuma Fruit ka ci duk wanda kake so"
Lumshe ido yayi, Amina duk ta gama sanin abubuwan da yake so, da kuma lokacin da yake son su.
Ya ɗan buɗe idonsa ya ce "Me zance miki ne Meenalina? Allah ya saka miki da alkhairi, idan kin yi Aure ya baki ikon yiwa mijinki biyayya"

"Yaushe zan yi Auren bayan ka hanani yin saurayi" Murmushi yayi yayi gaba, dan baya son ta ƙaƙalo rigima, ya shiga ɗakinsa yayi wanka ya canza kaya, ya fito ya sake tarar da ita a zaune tana jiransa.

Sai dai kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta, kasancewar dogon wando ne a jikinsa sai shirt baƙa. Yana ankare da ita amma ya basar ya kunna Tv sannan ya zauna ya ce "Yauwa serve me"
Kamar mara gaskiya haka ta sunkuyar da kai tana zuba masa Abincin, cikin son kawar mata da yanayin da ta shiga, ya fara bata labarin irin sakarcin da Khalil ya yi.

Ta kalleshi ta ce "Yanzu ba shi da lafiyan kayi masa faɗa?"

"Ba dole in masa ba, kin ga yadda yaron nan ya koma kuwa?"

"Hmm, to ka tambaye shi meyake damunsa?"

"Shiritarsa ce dai, wai babarsa ta hana shi auren wata wadda zata aura masa daban"

"Eh ai da gaskiyarsa, gaskiya yakamata kayi wani abu a kai"

Ya ce "Me zan yi a kai?"

"Ka duba abin da yake so kayi masa idan har bai saɓawa Shari'a ba, ba ita kaɗai take da haƙƙi a kansa ba, yakamata a ce...."

Kan ta ƙarasa maganar ya ce " Ɗan ki ne ko ɗanta? Ta fiki sanin ne ya dace shi, haryanzu yaro ne bai san meye ya dace da shi ba"

Sak Amina tayi tare da yin shiru, ba ƙaramin ɓata mata rai maganar ta sa tayi ba, ta ɗan jinjina kai ta ce "Haka ne, ɗanku ne bai kamata in dinga shishshigi a kan abin da bai shafeni ba, amma idan ka cigaba a haka watarana zaka ga abin da ba ka so a gidanka" ta tashi fuskarta ɗauke da ɓacin rai ta bar falon.

Dan haushi tana zuwa ɗakinta, ta haye gado, ta ja bargo tana jin yadda zuciyarta tayi mata babu daɗi da abin da Daddy yayi mata.

Sam bacci ya kasa ziyartar idanunta, tana ta saƙawa da warwarewa, ji tayi an turo ƙofar ɗakin, sake dunƙulewa tayi cikin tsoro, dan bata san waye ya shigo ba.
A hankali ya tako ya ƙaraso gaban gadon, ya sanya hannu zai janye bargon, ta riƙe bargon gam tare da sakin ihu, da sai da ta ɗan razana shi.

"Ke lafiyarki kuwa?"

"Meyasa zaka zo mini ɗaki yanzu ka yaye mini bargo, ka san a halin da nake?" Tayi maganar da iya gaskiyarta.

Ya ce "Haka ne, ban kyauta ba, tashi muyi magana".

"Ni ba wata magana da zamu yi, bacci zan yi".

"Idan baki tashi ba zan yaye bargon, and I mean it"

Buɗe ido tayi ta ce "To ɗauko mini hijjabina gashi can a ninke"

Kallonta yai ya ce "Are You commanding me?"

"Idan baka ɗauko mini na saka ba, zan yi kwanciyata"

"Ok shikenan, bari in yaye bargon in ɗauko ki"

"Wayyo Allah Babana, dan Allah ka bari"
Juya mata baya yayi, yayi murmushi ya ɗauko mata hijjabin ya bata.

Ta ziro hannu ta karɓa sannan ta ce "Ka juya to in saka hijjabin" tayi maganar a shagwaɓe.

Ya juya mata baya domin ta saka, sai dai abin da bata sani ba shi ne, yana kallonta ta jikin mudubin ɗakin, har ta gama saka hijjabin a kan kayan baccinta.

"In juyo kin gama?"

"Eh"
Ya juyo ya ƙaraso gefen gadon zauna, ita kuma ta sake matsawa baya, ya share ya ɗora da maganarsa "Ɗazu kina mini magana a kan Khalil, na katseki, kuma akwai buƙatar in jira ki gama bayanin"

"A a Ni da ba ɗana ba, me zai sa in yi shishshigi ba ruwana na tsaya matsayina na 'yar aiki"

"Look Amina, am serious, na san ban kyauta ba kiyi haƙuri, amma ni ina tunanin duk abin da mahaifiyarsa ta yanke a kansa ai daidai ne"

Amina ta ɗan yi Jimm sannan ta ce "Daddy meyasa kai da iyalanka kuke gudun talaka ne? Ko ka tambayi mahaifiyarsa meyasa bata son yarinyar da yake so? Maybe na san ka sani, saboda basu da ƙarfi ne, meye aibun dan ya aureta? A sanadiyar son ka kyautata mini, ka saiwa iyayena kayan Abinci masu yawa muka tafi da su ƙauye, maƙotanmu da 'yan uwanmu sun amfana da Abincin nan sosai, Allah kaɗai ya san iya mutanen da ka samu ladansu, ko iya wannan idan ya duba ya karɓa maka a ayyukanka sai ya yafe maka.
Daddy ina maka kwaɗayin al'umma su amfana da dukiyarka, ita yarinyar ance awara take sayarwa, idan ya aureta ya mayar da ita makaranta kamar yadda ka mayar dani makaranta bai taimaketa ba? Atleast zai taimaki iyayenta ma, ko ba komai an rage yawan talauci.
Kuma ka san wani abu Daddy, a yadda basu shi ɗin nan, abu ne mawuyaci ta kasa yi masa biyayya, saboda ta san ita wacece, amna idan ya auri wadda suke level ɗaya tan da kuɗi yana da su, is hardly ta bishi yadda yakamata.
Dan Allah Daddy ku daina ƙyamar talaka muma 'ya'ya ne, kaine jagora a gidanka da iyalanka damu duk a ƙarƙashinka suke, abin da kace dole abi, ni nafi jin tausayin yarinyar har fa wurin awarar matarka taje ta ci mata mutunci a gaban mutane, abin fa babu daɗi Daddy, akwai zafi a zuciya a wulaƙantaka dan baka da shi, kar Allah ya jarrabeku fa".

"Da gaske Zainab taje ta ci mutuncin 'yar mutane?"

"To ni dai ba a gabana aka yi ba, amna Khalil naji yana gaya wa Fadila"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Meenal, Ki kwanta kiyi bacci, sai Allah ya kaimu safe zamu cigaba da Magana"

"Allah ya tashemu lafiya"

Ya amsa da Amin, ya tashi yana cigaba da lissafa maganganun Amina, ya bar ɗakin.

Tabi bayansa da kallo, sai da ya fita ta ce "Ya ubangiji Allah ka cika mini burina, ka ɗorani a kan bawan nan naka, Allah ka amfanar da mabuƙata a cikin dukiyarsa".


Fadila kuwa ta ɓangare ɗaya taji daɗin yadda Allah ya sanya Yazid ya tsallake tarkon Kankiya, amma ta rasa dalilin da ya sanya ta damu matuƙa da jin batunsa na ya rabu da ita, gashi suna da interval daga waccan jarrabawar zuwa wata, ko ta ɗauki waya da niyyar ta kira shi, sai ta kasa tana tunanin idan ta kira shi me zata ce masa.
Ɓangare guda kuma rashin Amina ma a gidan na ƙara ɓata mata rai, gab ɗaya tafi son aikin Amina a kan Hajar, Amina komai ka sakata ba ƙyuya babu komai, wani abun ma baka sakata ba zata ta yi maka shi idan ta ga dama.
Hakan ya sa komai Hajara tayi mata sai ta gwale ta, ko tayi ta hantarar ta, ko wurin Mummy bata fiye zuwa ba, saboda da taje Mummy take sako mata zancen ɗan gidan Hajiya Salma, ita kuwa ko zancen ba ta son ji, balle ta ganshi har ayi wata maganar Aure.

Da safe Amina ta fito, ta na ɗan gyare-gyare, Kitchen ta shiga ta duba sauran kayan Abincin, cikin nutsuwa ta fara aikin girkinta, tayi ta kammala, ta koma ɗaki tayi zamanta tana danna wayarta, sai takwas na safe sannan ta sake fitowa.
Jinta tayi wani iri cikinta duk babu daɗi, ga tashin zuciya da yake damunta.
Yau cikin suit ya fito baƙaƙe, ɗan ƙura masa ido tayi, ba zaka taɓa cewa ya haifi wannan 'ya'yan ba.

"Meye kike kallona haka?"

Ɗauke kanta tayi tana murmushi ta ce "Kwalliyar zan saya, ta tafi da ni sosai"

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Nawa kika saya?"

Ta ɗan sake ƙare masa kallo daga sama har ƙasa ta ce "Eh to, na sayeta da delicious food"

"Saboda kin mayar da ni acici ko?"

Dariya tayi ta ce "Ahh babu laifi kam, Minister akwai karrama ciki"

Yayi murmushi ya ce "Aifa shikenan, ni kin riga kin gama rainani, kina ganin haƙorana ko?"

Ya ɗan lumshe idanunta ta buɗesu a kansa ta ce "Ba rainaka nayi ba, ina jin daɗin in tsokane ka in ga kana irin wannan murmushin"

Murmushin ya kuma yi ya ce "To zan daina, ki dinga biyana sai in miki murmushin" yayi maganar yana kallonta, yana jin tamkar ya furta abin da yake masa nauyi a zuciyarsa game da ita.

"Me za mu yi order ne? Ni zan fita in koma wurin Khalil duk da mun yi magana ya ce jikinsa da sauƙi"

"Ga breakfast nan nayi, ga bread an sayo, ka zauna ka karya mana"

"Masha Allah, Allah ya yi miki albarka, sauko mu karya"

Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Ka ci kawai, ni naci anjima"

Cikin kulawa ya ce "Ya dai, naga kina yamutsa fuska?"

"Cikina ne yake ciwo da ƙirjina"

Nan da nan ya rikice "garin yaya? Kuma meyasa baki gayamini ba? Kema kina wasa da lafiyarki ko? Tashi ki sako hijjabi muje Asibiti"

Ita mamaki ma abin ya bata, "Ba fa wani abin damuwa bane ba, jiya wani yaji suka sayo mini mai zafi, na ci wainar fulawa da shi, shi ne yake damuna kuma na sha anti acid"

"Are you sure?"

"Da gaske nake, ba gani garau kana gani ba"

"Idan kin san da matsala mu tafi Asibiti"

"Daddy babu wata matsala

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login