Showing 57001 words to 60000 words out of 296192 words
ba zai ƙara zuwa ba insha Allah, kuma kinga ai Khalil ya sa an mana tsakani da shi".
Mama ta ce "Ni kuwa naga kwana biyu ko kiranki ba ya yi a waya, ko wani abun ki ka yi masa ne?"
Hafsa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "A'a babu abin da nayi masa".
"Ai maganrki ba abar yadda ba ce wasu lokutan, bana raba ɗaya biyu wani abun ki ka yi masa, ai shikenan kan ki kika yiwa, sai muyi ta jerawa a gida, 'yan unguwa suna mana ƙazafi, Da kin amince wa yaron nan, na tabattar zai riƙe mini ke amana, yaro mai rufin asiri kamar wannan, ya liƙe miki alhalin ke ba kowa ba, ai kuwa Wannan son shine na gaskiya".
Gaba ɗaya jikin Hafsa ya yi sanyi, ta tuna maganganun da ta gayawa Khalil, kan ya tafi duk da abin arziƙin da yayi mata, wanda ba dan shi ba, da bata san iya wulaƙancin da Najib zai yi mata ba. Ko ya dai na sona ne, tunda ya daɗe haka bai kirani ba? Ta tambayi kanta. 'gara ma ya haƙura ya daina sona, dan ba zai iya aurena ba' ta sake bawa kanta amsa.
Khalil kuwa daurewa kawai yake yi, amma zuciyarsa na raya masa ya kira Hafsa yaji lafiyarta, kar yaje wani abun ya sake samunta, amma idan ya tuna da shawarwarin Abdul, sai ya haƙura da kiran nata.
Har washegari Amina bata sake ba, tana jin ɗacin abin da aka yi mata a zuciyarta, sai da taje makaranta ne ma, ta ɗan haɗu da ƙawayenta shine ta ɗan sake, amma cikin zuciyarta babu daɗi sam.
SHANONO.
Can garin su Amina kuwa, facalolinta matan su Bala, suka sakota gaba, da zagi da kums habaice habaice, tare da yiwa Innon fatan masifu daban daban, a kanta da kuma Amina da Baba Hassan.
In anjima suma su Lawan ɗin da kansu suke zuwa su isketa suyi mata bala'i, suka tattara wani tsohon keken Baba na hawa suka sayar, suka harhaɗa dan biyan Jarmai kuɗinsa, saboda yadda ya sako su a gaba, da fitina da cin mutunci, abu har gaban mai gari ana musu sulhu.
Ƙauye dama tuni ya ɗauka, batun guduwar Amina birni, dan tayi karatun boko, mutan ƙauyen nan suka dinga Allah wadai da abin da Amina da babanta suka aikata.
Yau su Fadila suka kammala jarrabawar wannan zangon karatun, ji take kamar gama makarantar tayi, saboda yadda duk jarrabawar ta takurata.
Sir Abdulmaleek Kankia, wanda suke kira da Sir Kankia, ya zo wucewa ya kalli Fadila da ke tsaye, tana ƙoƙarin kiran waya cikin nishaɗi.
"Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta. Ta ɗaga kai ta kalleshi, shi ne lecturer da ya so ya kori Yazeed a kan littafi ranar, zuba masa ido tayi ba tare da ta ce komai ba.
"Ko ba sunanki bane?".
"Suna na ne mana"
"In ba zaki damu ba, ina son ganinki a office ɗina".
"For what?" Tayi maganar tana kallonsa.
"For something very important to discuss"
"Ka faɗa mini a nan mana, meye sai na bika Office?"
"Abu ne da ya shafi jarrabawar ki".
"Jarrabawata kuma?" Ta faɗa da mamaki.
Ba tsammani ta ɗaga kai, ta hango Yazeed ya zuba mata idanunsa, ta rasa wani irin kallo ne, na tuhuma ne, ko kuma na menene ta kasa ganewa.
Bayan sir Kankiya tabi da kallo, a hankali kuma ta ja jiki ta nufi wurin da Yazeed yake tsaye ya ƙureta da ido.
"Fadila meya ke ce miki ya tsare ki haka?
Fadila ta tsuke fuska ta ce "Meye na tuhumata kuma ina ruwanka?".
"Da ruwana Fadila, ki gaya mini dan Allah".
Ta ce "Cewa yayi wai in je, a kan wani abu ne da ya shafi jarrabawata".
"Meya faru da jarrabawarki?".
"Nima ban sani ba, ko dan mun yi iri ɗaya ne da kai" tayi maganar cikin sanyin jiki.
"Ai ba jarrabawarsa ce muka yi iri ɗaya ba, amma kije kiji mai zai ce".
"Am scared gaskiya" ta faɗa da rauni.
"Meye abin tsoro kuma babbar yarinya, ai babu damuwa ina jiranki, kije ki dawo"
Fadila duk tunaninta a kan jarrabawar su ne, haka ta nufi hanyar da zata tafi office ɗin Sir Kankiya.
Ƙwanƙwasa ƙofar Office ɗin yayi, "Yes come in" A hankali ta tura ƙofar Office ɗin, ta shiga. Tun da ta shiga ya zuba mata ido, har ta ƙarasa cikin Office ɗin. Haushi ne ya kama Fadila, saboda ta tsani kallo a rayuwarta.
Zuwa tayi ta tsaya tana kallonsa ta ce "Gani"
Kankiya ya yi murmushi ya ce "Zauna mana".
Ta ɗan hura hanci, ta ja kujera ta zauna, tare da basar da Kankiya.
"Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta.
Ta ɗago fararen idanunta ta kalli Sir Kankiya.
"Ke 'yar garin Dutse ce?" Ya tambayeta yana kallonta.
"Babana ne ɗan garin" ta bashi amsa a daƙile.
"Garin babanku ai garinku ne".
"Sir dan Allah meyasa ka kirani? Meya faru da jarrabawata?".
Sir Kankiya ya ce "Eh to, ba wani abu bane na damuwa da tashin hankali, akwai yiwuwar komai zai daidaita, amma ki rubuta mini lambar wayarki".
"Me yasa zan bada lambar wayata?"
"Saboda idan da buƙatar sake neman ki sai in neme ki kai tsaye"
"To ai ni har yanzu ban san meya faru da jarrabawar tawa ba".
"Zaki sani nan gaba kaɗan, ki rubuta mini lambar wayarki" ba tunanin komai, Fadila ta rubuta masa lambarta, sannan ta tashi ta fice daga Office ɗin.
A harabar rukunin ofisoshin malaman ta tarar da Yazeed, ta kalleshi da mamaki, ta ɗauka tuni ya tafi.
"Yaya aka yi? Meyafaru da jarrabawar?" Ya tamabayeta cikin ƙosawa.
"Nima ban sani ba, bai gaya mini ba, sai dai karɓar lambar wayata yayi, ya ce idan akwai buƙatar a neme ni, za a kirani".
Yazeed ya kalleta da mamaki ya ce "Ya karɓi lambar wayarki?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Hmm Mutumin nan sonki yake yi, ba wata jarrabawar ki da ta samu matsala".
"What, ka san me kake cewa kuwa?"
"Eh mana, think, idan wani abu ne ya faru da jarrabawarki shi ke da alhakin kiranki, You have all his attendance, kina da Attendance ɗinsa, teses ɗinsa kina da 25mrks, ga exams ɗinsa kin rubuta, meye matsalar kuma?" Ita babban abin da ya bata mamaki, ya a kayi Yazeed ya san makinta na test da kuma Attendance, ita wasu lamuran nasa ma tsoro yake bata. Gashi ya wani haƙiƙance sai masifa ya ke yi.
"Idan ma sona yake ina ruwanka?" Ta faɗa cikin tsiwa.
Cikin dakewa da maziya, Yazeed ya ce "Babu ruwana, Allah ya sanya Alkhairi, ya kaimu lokacin aure Mrs Kankiya".
Wani mugun kallo Fadila ta yiwa Yazeed, tare da jan guntun tsaki tayi gaba.
Da sauri ya sha gabanta, ya ce "Am sorry Please, yau fa zamu tafi hutu, Yakamata mu rabu lafiya ko ƙanwata?".
"Ni ka ƙyaleni" tayi maganar a ɗan hasale.
Zuba mata idanunsa tayi, wanda hakan ya sa taji wani abu na yawo a jikinta, da bata san menene ba.
"Fadila me yasa kika tsane ni, me nayi miki, kina gani bana iya sakewa da kowa a makarantar nan, duk da ba kya ƙaunar ganina, amma ni ina jinki tamkar ƙanwata ciki ɗaya, dan Allah ki sassauta tsanar da kike mini, ko nayi miki wani laifin ne?" Shiru Fadila tayi, tana bin Yazeed da kallo, a hankali ta lumshe idanunta.
"Fadila" ya kira sunanta.
Ta ɗago ta kalleshi. "Me nayi miki kika tsane ni ne? Ko dan ni bagidaje ne, ban iya wanka ba, kuma ban iya turanci ba?" Ya ƙarasa Maganar yana kallonta.
Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta kasa ko motsawa. "Let's be friends" Yazeed ya faɗa cikin sigar rarrashi.
Ɗan tura baki tayi tana fici fici da ido, wata irin kasala na cigaba da tsirga mata, tun daga kanta har ƙafafuwanta.
"Talk Fadila" ya faɗa yana marairaicewa
"To wai ni me zance?" Ta faɗa tana tura baki gaba.
"Be my sister" ya furta saɓanin abin da yake zuciyarsa.
"Kaga, dan Allah ka bani hanya in wuce, gida zan tafi" tayi maganar a shagwaɓe. Babu tsammani, suka ga Kankiya ya ɓullo daga wajen da ofisoshin nasu suke, ya ɗan yi turus yana kallon su. Tunani Fadila ta shiga yi, da gaske mutumin nan sonta yake ya karɓi lambarta, amma da ya rainawa kansa hankali, wannan suka jero ai cewa za'a yi mai aikinta ne, wani sirirn tsaki ta ja ba tare da ta san ya fito ba.
Wucesu ya yi ba tare da ya ce musu uffan ba, duk suka bishi da kallo, har ya bar wurin.
Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kaga ni na tafi"
"Ok muje, nima tafiyar zan yi" ba wanda ya kuma cewa wani uffan, kowa yana saƙawa da warwarewa a ransa.
Ta buɗe motarta ta shiga, Yazeed ya kalleta ya ce "To ayi hutu lafiya, kar a ajiye litattafai a daina karantawa, i will miss you ukty"
Kallon Yazeed tayi, ta ɗan yi murmushin gefen baki.
Har motar Fadila ta ɓacewa ganin Yazeed, yana tsaye yana kallonta, yana jin yadda zai yi kewarta.
Da yamma Amina na harabar gidan, wurin Baba, tana ta zuba masa surutu, gabanta ga littafi da biro, tana karatun jarrabawa.
Horn ɗaya aka yi ƙwaƙƙwara, Baba ya miƙe jiki na rawa, yaje ya buɗe gate ɗin, Zakiru direban Alhaji Ahmad, ya silalo da hancin motar, cikin harabar gidan.
Ɗan dakatawa Zakiru yayi da motar, Baba ya ƙarasa Alhaji Ahmad ya sauke glashin motar suka tsaya magana da Baba.
Amina haushinsa take ji yanzu, tun da Allah ya sa 'yar sa taci wa babanta mutunci, kwasar litattafanta tayi, ta bar wurin dan karma ta gaishe shi, ta shige cikin gida, a falo Hajiya Zainab ta dakatar da ita "Ke daga ina haka nake ta nemanki?".
"Ina wurin Baba ne".
"Ke nifa bana son sakarci, idan baban naki kika zo yiwa aiki, sai ki koma can bakin gate wurinsa, idan ya so ya dinga biya miki kuɗin Makarantar".
Fadila da ke kwance a kan doguwar kujera, ta ɗan taɓe baki tana kallon yadda Amina ta haɗe rai.
Alhaji Ahmad ne ya yi sallama a falon, zumbur Fadila ta miƙe jin Muryar mahaifinta, da sauri ta ƙarasa in da yake ta rungume shi "Oyoyo Daddy".
"Welcome sweetheart" yayi Maganar cike da kulawa yana sake rungume Fadila.
Hajiya Zainab ta ce "Ashe ka sauka?".
"Wallahi kuwa, kin ganni nan sai yanzu"
Amina tabi Fadila da kallo, Yadda ta ƙanƙame mahaifinta cikin kulawa da ƙauna. Ji tayi ina ma zata iya zagin Alhaji Ahmad, Fadila taji abin da ta ji, lokacin da taci mutuncin nata mahaifin, sai dai kash hakan ba tarbiyyar Amina bace, ko da wasan wasa ba zata iya aikata hakan ba, haka ta wuce ta bar musu falon suna cigaba da farincikin dawowarsa.
Hafsa fa ta ɗan shiga damuwa, saboda rashin kiran wayarta da Khalil ya daina yi gaba ɗaya, gashi kuma ita ba zata iya kiransa a ta ta wayar ba, saboda a ganinta hakan bai dace ba.
Amina ma sun fara jarrabawa a makaranta, ayyuka sun ɗan yi mata sauƙi, kasancewar yanzu Fadila bata zuwa Makaranta, ta rage tashin sassafe.
Tun da Alhaji Ahmad ya dawo basu haɗu ba, har ta tafi makaranta bai fito ba, wasu lokutan baya dawowa sai dare sun kwanta.
Duk kashedin da ake mata a kan zuwa wurin Baba tayi zamanta, ba ta ji ba, dan yau ma tana wurinsa suna hira, kasancewar yau Asabar, Baba yana gyara flowers ɗin harabar gidan, tana taya shi.
Ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ya cika wurin, Baba ne ya miƙe da sauri fuskarsa ɗauke da murmushi, yana yiwa Alhaji Ahmad barka da fitowa.
"Ina wuni" Amina ta faɗa kamar an mata dole, dan ta san Baba zai iya yi mata faɗa idan bata gaishe shi ba.
Ya waiwaya ya kalli in da Amina take "Lafiya ƙalau, ya school ɗin?".
"Lafiya ƙalau".
"Good" ya mayar da dubansa kan Baba ya ce "Malam Hassan ya aikin? Babu dai wata matsala ko?"
Baba ya ce "Babu matsalar komai ranka ya daɗe".
"To Alhamdilillah, Allah ya yi jagora".
Baba ya amsa da "Ameen".
Amina a ranta ta ce "Shi dai gashi nan, shima yana da wannan taƙamar, sai dai baya wulaƙanci kamar yaransa da matarsa' ta ɗan taɓe baki ta cigaba da sabgar gabanta.
Fadila ce zaune a kan gadonta, tana zazzage jakarta ta Makaranta, ita kanta bata san me take nema ba, wata takarda ce mai ƙyalƙyali ta faɗo daga tsakanin litattafanta.
A hankali ta miƙa hannunta ta ɗau takardar ta buɗe, rubutun larabci ne a jiki, an cika paper da rubutun larabci. Ba rubutun kowa bane face na Yazeed, tamkar inji ne ya tsara rubutun ba hannun mutum ba, ta dinga jujjuya takardar amma ba ta fahimci komai ba, sai sunansa da ya rubuta da Larabci da signing, haka nan taji tana son sanin me takardar ta ƙunsa, ƙarshe ma sai ta fara tunanin ya aka yi takardar ta shiga jakarta?.
Bacci take ji sosai, dan haka ta watsa litatafan ƙasa tai kwanciyarta a kan takadar, wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
"Ukty, yau kin yi kyau fiye da koyaushe, idanunki kamar ƙara musu kyau ake masha Allah" ya faɗa yana murmushi.
Haɗe rai tayi tana kauda fuskarta gefe guda, matsawa yayi jikinta Sosai yana mata magana. Jikinta ne ya hau rawa, taji tamkar ta fashe da kuka, ga wannan baƙon yanayi da yake kaiwa yana komowa a jikinta.
Fuskarta duk hawaye ta kalli Yazeed "Wai ni meyasa nake jin haka idan ka masto kusa dani?".
Ya ɗora kansa a kan kafaɗarta ya ce "Me kike ji?"
"Nima ban sani ba" ta faɗa muryarta na rawa.
Bakinsa yake ƙoƙarin sakawa a nata, amma ta fara ƙoƙarin kauda kanta, sai dai riƙon da yayi mata bana wasa bane. "Yazeed dan Allah" ta faɗa fuskarta duk hawaye, jikinta kuma na cigaba da rawa.
Sai da Yazeed ya yi galaba a kanta, wurin saka bakinsa a nata. Ba zata iya misalta ko rarrabe wane yanayi haka suka wanzu a ciki ba ita da Yazeed.
"Yazeed" ta faɗa da ƙarfin gaske, ta tashi daga baccin a razane, fuskarta duk hawaye, tana haki.
Amina dake durƙushe tana tattare litattafan da Fadila ta zubar a ƙasa ta kwashe ta gyara ɗakin, sai da ta razana, ta saki litattafan. Ita ma ta maimaita "Yazeed kuma"
Fadila sai haki take tana rarraba ido, ta kai hannu fuskarta taji hawaye.
Ta kalli in da Amina ke tsaye tana binta da kallo.
Ji tayi tamkar yawun Yazeed ne a bakinta, saboda bata taɓa zaton mafarki ne ba gaske ba. Da sauri ta duro daga kan gadon, ta tafi banɗaki tana zubar da yawun bakinta.
Amina tabi bayanta da kallo, tana tunanin dama ana mummunan mafarki da rana tsaka haka? Kodayake in mutum baya Addu'a ba abin da ba zai sameshi ba.
Haka Fadila ta dinga zubar miyau, tamkar a gaske mafarkin ya faru, har irin ƙamshin turaren da ke jikinsa, take ji a hancinta. Bata haƙura ba sai da ta sa brush ta wanke bakinta, sannan ta fito daga banɗakin.
La'asar liƙis, Khalil ya shigo garin Kano, salla kawai ya tsaya yayi, kai tsaye gidansu Hafsa ya nufa.
A ƙofar gida ya tsaya yana sallama, Mama ce ta leƙo da kanta, tana ganin Khalil ta fara murmushi, ya duƙa har ƙasa ya gaida ita, ta amsa masa cike da kulawa tana faɗin "Khalil kwana biyu"
"Mama ayyuka ne suka yi mini yawa, kuma da yake ba a nan Kano nake aikin ba, shiyasa".
"Allah sarki to Allah ya dafa, kuma gashi bata nan, tana wurin bikin wata ƙawarta"
Khalil ya ce "Dama Hafsa na ƙawaye?".
Mama ta ce "Kaima ka fuskanci halinta kenan, tana da su irin wanda suka yi Makaranta a baya".
"To Mama ina ne wurin bikin?"
Mama ta gaya masa yayi mata godiya ya tafi.
Ba tsammani taga lambar Khalil yana kiranta, duk da bata yi Saving lambar ba, amma ta haddacce ta tsaf.
Cikin hanzari ta ɗaga wayar, sai dai bata iya jin komai saboda hayaniya.
Tashi tayi ta fita harabar wurin bikin, jikin wata mota ta tsaya, ta saka wayar a kunnenta tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam, Baby ya kike?" Taji maganarsa a bayanta. Da sauri ta waiwaya taga Khalil a tsaye a bayanta.
"Ya aka yi ka san ina nan ka zo?" Ta faɗa cikin mamaki.
"Miracle" ya faɗa yana dariya.
Ƙare mata kallo ya shiga yi, tana sanye da riga da skirt na atamfa, ta kashe ɗauri, hannunta ya sha lalle.
"Ina wuni" ta faɗa a taƙaice.
Maimakon ya amsa mata sai ya shiga ɗaukarta hoto a wayarsa. Haɗe rai ta yi ta ce "Ka bari bana so".
"Tom na bari, kin yi mamakin ganina ko kya ce na fiye naci, ba laifina bane, laifin zuciyata ne". Hafsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
"Kin yi shiru, ashe biki kuke babu labari. Nayi mamaki da mama tace mini bikin ƙawarki ne, ashe kina da ƙawaye?".
Abinda ba ta taɓa yi masa ba tayi, murmushi wanda sai da dimples ɗinta da bai taɓa sanin tana da su ba suka lotsa.
A hankali ya furta masha Allah beautiful.
"Ina da ƙawaye mana, kana mini kallon bani da kirkin da zan yi ƙawaye ko? Babbar ƙawata ce tun muna yara muka tashi tare shiyasa na zo bikinta".
"Ashe ma bikin namu ne, duk da ba a gayyaceni ba muje, a bani wurin zama da Abinci daga Abuja nake ko gida banje ba Wallahi" ɗan zaro ido tayi dama ga idanun nata tubarkallah.
"Me yasa baka je ka huta ba?".
"Ganinki nake son yi" ta jinjina kai, ta shiga gaba ya bita a baya, wurin taron yayi kyau da tsari, ta sama masa wurin zama, tasa aka kawo masa Abinci da abubuwan sha.
"Shikenan ko kana buƙatar wani abun?".
"Eh ke nake buƙata a kusa da ni, ki zauna idan kika tafi ban san kowa ba, kar ace na zo gayyar soɗi. Ta ɗan murmusa kaɗan ta samu wuri ta zauna.
Ba kunya Khalil ya fara cin Abincin nan, duk da hakan ba ɗabi'arsa bace, cin kowane irin Abinci, kuma a gaban mutane, amma so yake Hafsa ta sake da shi, dan haka ya zage yana ziri.
"Allah ya nuna mana ranar bikinmu, muna kan high table kamar wannan couples ɗin, wane irin kaya zamu saka?"
Shiru tayi masa tare da ɗan taɓe baki.
"Hafsa meyasa ba kaya sona ne?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa.
Ta ɗauke kai tamkar ba ta ji abin da yace ba.
Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Tashi muje in mayar da ke gida, tara saura yanzu".
"Dama jira nake ka gama, yanzu zan tafi nima".
"Na gama muje" ba tare da ko sallama ta tsaya ta yiwa Amaryar ba suka fito ita da Khalil.
Suna zuwa inda motarsa take ta ce "To ka gaida gida".
"Me kike nufi?"
"Zan hau Napep in tafi gida"
Khalil ya ce "Ke kin isa ma? Dan Allah kar muyi haka da ke" da ƙyar Khalil ya lallaɓata, ta amince ta shiga motarsa.
Suna cikin tafiya ta ce