Showing 6001 words to 9000 words out of 296192 words

Chapter 3 - GABA DA GABANTA

yana ci, Fadila sai surutu ta ke masa".

Zuwa ƙarfe huɗu na yammaci, Khalil ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice, da ƙudurin tafiya gidan su Abdul ya je ya ƙare masa rashin mutunci.

Yau kwana guda, da Baba ya roƙi Alhaji Ahamad kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin jarrabawa, kuma ya bashi damar ya karɓa a gurin matar gidan, amma sanin halinta ya sanya shi a fargabar yadda zai tunkare ta da wannan maganar.
Amma a rashin tayi akan bar arha, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemi Alfarmar, ko Allah yasa ya dace.

Jiki ba ƙwari, ƙasan zuciyarsa yana Addu'a, ya tunkari babban falon gidan.
Da sallama ya shiga falon, sai dai duk da girman nan nasa da shekarunsa, baya hana shi shiga fargaba, idan har yayi tozali da Fadila, saboda gudun tozarci da wulaƙanci, kamar yadda ta kasance yanzu, ya tarar da ita hakimce a falon tana aikin na ta, na danna waya wanda a shi tafi ƙwarewa, danna waya kallon talabijin kai lomar Abinci sai kuma bacci da tarin rashin mutunci.

"Barka da yamma ranki ya daɗe" Baba yayi Maganar yana risunawa.
Ba ta ɗago ta kalleshi ba ta amsa sa da 'Yawwa'.

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah hajiya fa".

"Tana sashinta".

'Dama Alhaji ne ya aiko ni gurinta".

"Sai ka zauna ka jirata, sai ta fito".

Bai ce komai ba, ya rakuɓe a falon, yana rarraba ido.

Fadila ta kara waya a kunneta tare da faɗin "Uwar bacci, tun ɗazu na ke kiranki a waya, amma shiru ba kya ɗagawa, dama ce miki zan Brother ya shigo gari fa, gara ki shirya ki bayyana".

"Girl are you serious?".

"Amma kin san bana miki wasa a irin wannan lamarin ko".

"Wow, Alhamdilillah aikuwa zaki ganni yanzun nan" suka yi shewa a tare, sannan suka yi sallama.

Baba Hassan tun yana zaman da marmari, sai da ƙafafunsa suka yi sanyi, ya gaji sosai, dan a ƙalla ya kai awa guda a zaune.

Ba tsammani sai ga Hajiya Zainab ta fito, ita ma ɗauke da waya a kunnenta.

Ta zauna ta cigaba da wayarta, ba tare da ta saurari in da Baba Hassan yake zaune ba, hirar kasuwancinta kawai take yi, tare da ambaton Manyan kuɗaɗe a cikin wayar.

Sai da ta ƙare wayarta sannan ta kalleshi ta ce "Malam lafiya ka shigo mini falo ka ƙwafe haka kamar ana zaman fada?".

Baba Hassan ya gyara zamansa ya ce "Amm, dama gurinki na zo Hajiya, Alhaji ne ya aiko ni".

"Ya aiko ka, ya ce me?"

"Dama na kira shi a waya ne, yarinyata zata zana jarrabawa, bani da kuɗi, shine ya ce in zo in karɓa a gurinki".

"Kai kuwa malam Hassan, yakamata ka dinga jin tsoron Allah, yaushe aka baka albashi har da zaka dawo ka ce ga zance ga magana?"

Cikin rauni Baba Hassan ya ce "Dan Allah Hajiya ki taimaka, ni ko rance ne, bana son karatun 'ya ta ya samu naƙasu, idan ya so sai a cire a albashi na".

"Allah wadaran halin talaka, sam ba ku da godiyar Allah, mutum ko naman jikinsa ya ke yanka yana baku ba zaku gode ba. To ni bani da cash a hannuna, sai ka haƙura sai zuwa lokacin da aka ɗakko mini kuɗi a banki".

Ya sake duƙawa ya ce "Hajiya ki taimaka, za su rufe karɓar kuɗin ne".

Fadila a ƙufule ta ce "wai baka ganewa ne? Babu kuɗi a hannunta Yanzu, amma sai magiya ka ke".

Baba Hassan ya ce "to shikenan Hajiya, Na gode" ya tashi jiki a sanyaye ya bar Falon.

********

Zuwa yanzu Amina ta gama fidda rai da samun kuɗin da zata biya na jarrabawa, dan yanzu haka tana zuwa makaranta ne kawai, kafin wanɗanda suka biya kuɗin jarrabawar su fara.
Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, haka take tafiyar, tana ƙoƙarin shiga gida ta hangi Kawu Bala, a ƙofar gida yana alwala, kai da ganin alwalar ta sa kasan jahilci ya samu gindin zama a tare da shi, saboda yadda watsa ruwan alwalar nan ko ta ina.
Tana ƙoƙarin durƙusawa ta gaishe shi cikin masifa ya ce "Ke Amina zo nan".

Ba musu ta zo ta durƙusa ta ce "Gani kawu".

"Da ga gidan ubanwa ki ke?".

"Daga makaranta"

"Yawon barbaɗa da ta zubar ba?" Kallon Kawu Bala tayi, tare da jin haushin mummunar kalmar ta zubar da ya jinginata da ita.

Ya kalleta ya ce "Ina son sanin dalilin da yasa, Malam Rabi'u ya nuna yana sonki, amma dan iskanci ki ka yi masa rashin mutunci".

Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kawu, ta yaya zan iya Aurensa, mata nawa ya aura ya saka a garin nan? Kalli yadda yaransa suke babu cikakkiyar kulawa, idan na Aureshi yayi yaya dani? Kuma ban fa gama Makaranta ba har yanzu".

"Kinga idan na kuma magana kika yi mini zancen bokon nan, saina karairaya ki, shashasha mara kan gado, na fuskanci akan bokon nan kike wannan iskancin, na fuskanci a can suke hure miki kunne, to ba zai yuwu ba, ubanki ya tsallake ya tafi nasa guri ya bar mu da ke, ke kuma ki ɗakko mana abun kunya ba, saboda wata boko ba, dan haka daga yau na kuma ganin kin je makarantar boko, Wallahi sai na saɓa miki kin ji na gaya miki.
Kuma kiji da kunnenki, zamu karɓi kuɗin Auren Malam Rabi'u, ba zaki cigaba da gandamewa a gida ba, sa'oinki na gidan Aure suna neman aljanna, ke kuma kina tamɓele a titi da uwar jaka da sunan boko, shegiyar bokon da ke ba kuɗi a ke baki ba sai wahala, da wannan wahalar banzar gara in ba zaki yi Auren ba, ki shiga cikin maza a dinga zuwa da ke gona kina noma".

Tuni hawaye ya wankewa Amina fuska ta ce "Dan Allah kawu kayi haƙuri, ku bari in ƙarasa makaranta, ko ina gamawa ne sai in yi Auren, in ya so ku aura mini wanda ku ke so, amma banda Malam Rabi'u dan Allah".

"Au ke zaki faɗi abunda ki ke so ayi?, ai kuwa ba ki isa ba, ko Hassan ubanki bai isa ya ja da maganata ba balle ke, tashi ki bani guri, Allah ya ƙara nuna mini kin fita daga cikin gidan nan da sunan wata makaranta, wuce ki bani guri, da ido kamar gujjiyar mayu".

Cikin kuka Amina ta shiga cikin gida, kai tsaye ɓangarensu ta wuce, ta tarar da Inno tana surfe.
Sakin taɓaryar Inno ta yi, ta nufo in da Amina ta shigo tana kuka, tare da faɗin "Ke Amina lafiya? Waye ya rasu kike wannan kukan?".

Cikin kuka Amina ta ce "Kawu Bala ne wai ya ce kar in sake zuwa makarantar boko, wai Aure za suyi mini".

Tsaki Inno tayi ta ce "Shine za ki shigo kina mini wannan uban ihun, bokon banza da na wofi, matsa daga kusa da ni kar in makeki".

"Haba Inno, kema haka zaki ce? Yanzu kin yarda su aura mini Malam Rabi'u baban su Furera?"

Zaro ido Inno tayi ta ce "Malam Rabi'u kuma? Wannan mara mutuncin?"

"Shi fa, kawu Bala ya ce wai za su karɓi kuɗinsa na Aurena".

Jiki a sanyaye Inno ta ce "To Amina kiyi haƙuri, kin san duk gidan nan babu wanda yake musu da Kawu Bala, ciki kuwa har da mahaifinki, shi yasa na so kafin su farga su yanke makamancin wannan hukuncin, ki fitar da mijin Aure, amma yanzu lokaci ya ƙure Amina, kin san tun da ya waiwaye ki ba wanda ya isa ya sanya shi canza Magana".

Amina ta ɗora hannu a ka, ta zunduma ihu ta durƙusa a gurin ta na faɗin "Wallahi idan aka aura mini mutumin nan an gama da rayuwata, sunana bazawara, dan Allah ku ƙyaleni in yi karatuna".

Inno ta ce ki rufa mana Asiri, kar ki sa su ɗauka wani abun ne, ki sa su shigo su yi mana tijara".

Miƙewa Amina tayi ta shige ɗakinsu, tana cigaba da kuka har cikin ranta.

********

Tamkar wasu taɓaɓɓu haka suke ta shewa a falon.
Wata siriyar yarinya ce Kamar Fadila, cikin skirt high west, da wata body hook, sai hula a kanta, ta yi simple make up.
Hatta yanayin rawar kanta da iyayinta irin na Fadila ne. Dama hausawa suka ce, sai hali yazo ɗaya ake abota.
Fadila ta kalli ƙawar tata ta ce "Yusra kin ga yadda ki kayi kyau kuwa? Ni kaina na yaba, ina ga shi wanda aka yiwa kwalliyar?".

Yusra ta ce "Girl brother nan naki sai a hankali, Allah ya sa in ishe shi kallo".

Fadila ta ce "dalla kar ki damu, zai yaba haba sai kace ba namiji ba, dole ya ƙyasa, yanzun nan zai shigo, muje ɗakina in ƙara gyara miki kwalliyar nan, a ƙara powder da turare".

Haka kuwa aka yi, suka shiga ɗakin Fadila, da yake Fadila gwanace gurin kwalliya da gyaran jikinta, tsaftar muhalli ce komai sai dai ayi mata.

Yusra ta kuma fitowa ta yi ras da Ita, suka dawo falo suka cigaba da hira.

Suna tsaka da hirar ne, suka ji shigowar mota gidan, Fadila ta leƙa ta window, da sauri ta dawo tana faɗin "Girl, gashi nan, shine ya dawo".

Cikin hanzari Yusra ta sake feffesa turare, da sake gyara zama.

Khalil ne ya shigo falon, hannunsa riƙe da wayarsa da makullin mota.

Yana shigowa gaba ɗaya Yusra ta rasa nutsuwarta, saboda tsananin kwarjinin da Khalil yake da shi.

"Ina wuni Brother" Yusra ta faɗa cikin fargaba.

"Yawwa sannunki" ya amsa yana ƙoƙarin shigewa.

Fadila ta ce "Brother, baka gane ta bane? Yusra ce fa".

Khalil yayi murmushi ya ce "Na ganeta mana, ai nace mata Hi ko?".

Yayi Maganar yana hararar Fadila.

Ba Yusra ba, Fadila kanta ta ji haushin yadda Khalil y nunawa ƙawarta halin ko in kula, duk da wannan tarin hoda da turare da ta saka saboda shi.

Gyara sharhi ko shawara
08081012143
Ayi following account ɗina a Arewabooks@ Ayshercool7724
Da kuma Watpad Ayshercool 7724

Share Please 🙏GABA DA GABANTA

       Page3

             
By Aisha Adam (Ayshercool)

(Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?, Wanda yake daga gamayyar alƙaluma uku, daga haziƙan marubuta uku, Zee kumurya, Nimcyluv da kuma Ayshercool, kar ku bari a baku labari, ku mallaki na mu akan Kuɗi Naira 300 kacal. *DARE DA DUHU*

_Allahamdulillah Babu Abinda bright pens za su ce sai godiya a gareku. Kun amshi littafin fiye da kima. Duk cewa Fiction story amma da yawan Labarin abune na da muke fuskanta reality🌚😢_

*DARE DA DUHU*
₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750)

DADICATED TO BRIGHT PENS

Saroro suka yi gaba ɗaya suka bi bayan Khalil da kallo.
Yana shiga sashin Mummy ya dawo falo, ya kalli Fadila ya ce "Ke ina Mummy ne?"

Fadila ta tsuke fuska ta ce "Ba ta nan".

Ya ce "ok"

Yusra ba ta gajiya ba ta ce "Yaya a dawo lafiya".

"Ameen thanks" daga haka ya fice.

Fadila ta ja wani uban tsaki, ya yin da Yusra ta yi shiru tana tunani.

Fadila ta ce "Girl, ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari insha Allah sai Brother ya so ki".

Yusra ta ce "Till when dear? Wallahi ba zaki gane yadda nake son Yayan nan naki ba, amma kwata-kwata ya ƙi damuwa dani".

"Kin san me? Kar ki damu, You know he is very classic, shi komai nasa baya son raini, shi yasa amma zamu shawo kansa very soon".

Yusra ta ce "Shikenan, Allah yasa, bari in wuce gida".

Fadila ta ce "Muje in raka ki" suka fito harabar gidan, suna cigaba da tattauna yadda za su ɓullowa lamarin Khalil.

****************

Ta gama shirinta tsaf, cikin dogon hijjabinta, sai dai ta janyo kujerar tsugono ta zauna, ta zubawa kayan gabanta ido.

"Hafsa, ya har yanzu baki tafi ba, ko almajirin da zai taya ki ɗaukar kayan ne bai zo ba?".

Hafsa ta ce "Mama, jarin mu ne yayi ƙasa, ana samun ciniki Alhamdilillah, amma kin ga a ciki muke komai, har magungunanki a ciki muke siya, kuma jarin ba ƙaruwa yayi ba,  itace ma bashi na karɓa, mai ma kuɗin rabi na bayar aka bani, na cika sauran daga baya idan nayi cinikin yau".

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Na sani Hafsa, ni babban abun da ya dameni, shi ne mu zamana bamu da taro ko sisin da muke juyawa, amma insha Allah komai zai wuce, watarana sai labari, Allah ya kawo dalilin da zai rabaki da wannan siye da siyarwar bakin hanyar, bana so raina ba ya mini daɗi".

"Bakomai Mama, Allah ya kawo mana mafita ya baki Lafiya, dangin mahaifina abun da suka yi mana, Allah ya ninka musu" ta ƙarasa Maganar hawaye na zubowa daga idanunta, alamun tana cikin damuwa.

Mama ta girgiza kai ta ce "A'a Hafsa, Allah ya shirye su kawai, ki daina kukan nan" Mama tayi Maganar tana share mata hawaye.

Hafsa ta share hawayenta ta ce "Naji tsayuwar Napep a waje, bari in tafi kar in yamma, me zan taho miki da shi?".

"A'a bana buƙatar komai, Allah ya tsare, ki kula da kan ki, kar ki wasa da mutuncinki".

"To Mama insha Allah" ta kwashi kayan sana'arta, ta fita da su.

**********
Fadila na falo tana kallo, duk tayi kaca_kaca da falon, in da suka ci Abinci ita da Yusra sun bar komai a falon, ga tarkace duk ta tara shirgi, Asabe na ta kaiwa tana komowa tana gyarawa, ita kuwa ta hakimce akan kujera tana ciye-ciye.
Mummy na zaune a gefe, tana danna wayarta, tana chatting da abokan kasuwancinta.
"Hmm, wai kin san me Yaya Khalil yayi mini kuwa Mummy?".

"A'a sai kin faɗa".

"Gaba ɗaya ya gama yarfani yau ɗin nan, mussaman na yiwa Yusra waya akan ya zo gari, ta bar abun da take ta zo gidan nan, amma kin ga da ta gaishe shi da yadda ya amsa?".

Mummy ta ce "Ai ni na rasa gane kan yayan nan naki, sam ba shi da alƙibla, yarinyar tana da kirki da hankali, gata 'yar masu kuɗi, sam banga aibunta ba".

"Kema dai kya faɗa Mummy" suna tsaka da hirar sai ga Khalil yayi sallama".

Mummy ta amsa ban da Fadila, da ta kuma haɗe rai.

Khalil ya ce "Mummy na dawo ɗazu ki bani National id card ɗina, zan cike wasu takaddu, amma ba kya nan".

"Eh naje duba shagona ne na zoo road, sun yi mini waya wai wasu kayan sun ƙare".

Khalil ya sauke idanunsa a kan Fadila ya ce "Yawwa, ke kuma na dawo gareki, daga yau idan yarinyar nan ƙawarki ta kuma zuwa, ki ka sa tana mini shishshigi sai na makeki a gabanta".

Mummy ta ce "wai kai shikenan ba'a masa abun Arziƙi kenan? Meye laifin Yusran nan ne?".

"Ba na son raini, kawai sai in fara Soyayya da ƙawar ƙanwata, dan abun Kunya? Wata bushshiya da ita ba fasali".

"Kai dai ba'a yi maka abun arziƙi, ban da wulaƙanci meye laifin yarinyar nan? dan ma ka samu ance ana sonka da wannan masifar taka da zafin rai".

Khalil ya ce "Dama bance ace ana sona ba, a bar ni in samo Yarinya daidai da ni, wadda ta yi karatu me zurfi mai hankali da tunani".

Mummy ta taɓe baki ta ce "Ka ji da shi dai, a garin zaɓen zaka zaɓo mummuna, ni dai fatana a samo mini 'yar babban gida, kar a kwaso mini 'yar talakawa, wanda ba su san mutunci ba".

Khalil ya ce "Mummy kin ga yadda ginina na Abuja yayi nisa kuwa? Tunanin yarinyar da ta dace da gidan nan nake".

"A samo wadda za'a iya kai maka kayan Arziƙi dai shine fatana"

Khalil ya kalli Fadila da ta haɗe rai ya ce "Ke yaushe zaku fara lectures ne?".

"Saura sati biyu" ta faɗa tana cunkusa baki.

"To ki maida hankali dai, dan Jami'a ba gurin zuwa ayi sakarci bane".

Hararsa ta yi a fakaice, dan ya gama ƙular da ita yau ɗin nan.

"Ki yiwa yaran nan magana su kawo mini Abinci na kan dining, and Abdul ya ce yana gaisheki".

Fadila ta ce "Waye wani Abdul kuma?".

"Ban sani ba" Khalil ya bata amsa.

"Nifa ya dena wani rawar kai a kaina, me zan yi da shi?, yana lecturer mai na sama ya ci balle ya bawa na ƙasa?".

"Fadila me kike cewa?" Khalil yayi Maganar a fusace.

"Ai nima naga cewa kayi ba ka son ƙawata, ita da tafi wani Abdul komai, nima dan me zan so shi, kuma shima ya san ni ba kalarsa ba ce, Nasan albashinsa ko mayukana da turaruka na ba zai siya ba".

Khalil zai yi Magana Mummy ta dakatar da shi ta ce "Kar ka takura ta ƙyaleta, nima ban goyi baya ba".

"Amma Mummy me yasa? Naga Abdul ɗin nan abokina ne, tare muka yi School, kun san halayensa gaba ɗaya".

"Kai babanka ne ya biya maka kaje karatu, shi kuma gwamnati ce ta bashi tallafi, aikin da yake ma ba babanka ne ya samo masa ba? Idan yana da kunya ai ya san Fadila ba sa'ar sa ba ce".

Shiru Khalil yayi jin Mummy ta goyi bayan Fadila, amma har ga Allah bai ga aibun abokin nasa ba, kuma ya san da Fadila za ta Aure shi, za ta ji daɗi saboda yana da kirki, kuma yana matuƙar sonta, amma ya kasa gaya mata saboda yadda Izzarta take masa kwarjini.

************
Amina ce zaune a ɗaki, ta sanya langar koko a gaba, tana ta uban kuka tamkar wadda aka cewa babanta ya mutu.
Inno ce ta ɗaga labulen ɗakin ta ce "Wai ba zaki daina kukan nan ki tashi ki karya kumallo ba?".
Shiru Amina ta yi, ta cigaba da raira kukan ta".

"Ji min 'yar abar da malam ya hana ni faɗa, ba magana nake miki ba, ai ni Kawu Balan ya gama yi mini komai da ya hanaki zuwa bokon nan".

Sake fashewa da kuka Amina ta yi ta ce "Haba Inno, haka zaki ce?".

"Eh haka nace, me ake da wata boko? Ki tashi ki karya ki zo ki ɗebi kayan wankin nan, ki je ki wanko mana su".

Haka Amina ta tashi, ta ɗauki kokon nan ta kafa kai, babu siga sam a cikin sa ga gasarar ta yi tsami sosai, amma haka ta kafa kai tana zuƙarsa kaɗan-kaɗan.

**************
Baba Hassan ya zabga uban tagumi, ya san ko ba'a gaya masa ba, Amina na can a cikin damuwa akan kuɗin da ta tambaye shi, amma babu yadda ya iya dan yayi iya yin sa, amma bai samu ba, kuma ya san da gayya Hajiya Zainab ta hana shi kuɗin nan, ba wai dan babu kuɗin ba.
Yana ganin shige da ficen Khalil a gidan, amma ba zai iya tambayarsa ba, duk da ya san idan ya tambaye shi zai bashi, amma yana jin nauyin yaron sosai.
Gashi ya san idan ya kira

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login