Showing 177001 words to 180000 words out of 296192 words
ne mai sauƙi ba.
Wata zuciyar ta ce "Shegiya ai Allah ya ƙara mata, ba dai ta san ta liƙe wa namiji ba, ga sakamako nan ai"
Fadila ta kira doctor Aliyu a waya, ta sanar masa, ya ce mata baya kusa, amma da zarar ya dawo zai ƙaraso.
Hajiya Zainab ji take kamar a kanta Amina take, saboda rashin kunyar da tayi mata, so take ta koreta a ƙasƙance cikin wulaƙanci da tozarci.
Amina kuwa abu cigaba yayi, babu sassauci sam, tun da take ciwon mararta idan za tayi al'ada, ba ta taɓa wanda ya gigita kamar wannan ba, kuma haryanzu jinin bai daina zuba sosai ba.
Juyi kawai take yi a kan katifar, tana taune leɓenta na ƙasa, ƙarshe ta kasa jurewa ta fashe da kuka, sai juyi take tana kuka.
Bayan Fadila ta gama wayar, ta dawo falo ta tarar da Hajara tana kunna turaren wuta, saboda ya ɗauke ƙarnin jinin da Amina ta zubar.
Cikin damuwa Fadila ta ce wa Hajara "Nace ya jikinta, tana cikin hayyacinta dai ko? Kuma jinin ya daina zuba?" Saboda gaba ɗaya Fadila gani take, wannan faɗuwar da Amina ta yi ne ya haddassa mata wannan zubar jinin.
Hajara ta ce "Wallahi ban sani ba, bari naje na gani amma" ta tafi sashinsu dan duba Amina.
Ta tarar da ita, tayi ruf da ciki sai kuka take, tana kiran sunan Allah, tare da kiran Wayyo Allah Babana zan mutu, Daddy cikina".
"Au ke dan jaraba kina cikin wannan halin, amma kina kiransa bayan shi ya jefa ki a wannan halin, ko ince kika biye masa" Hajara ta faɗa cikin jin haushin yadda Amina ke kiran Daddy.
Amina ba ta gane me Hajara take cewa ba, ta cigaba da kukanta.
Hajara ta taɓe baki ta ce "Jinin ya daina zuba kokuwa" nan Amina tayi shiru ta cigaba da kukanta.
Ganin Amina bata da niyyar kulata, ya sanya ta koma falon ta samu Fadila ta ce mata "Gaskiya dai tana cikin ciwo sosai, nayi mata magana ma bata kulani ba sai kuka take yi"
"Na shiga uku, amma dai tana numfashi ko?"
Hajara a ranta ta ce 'Eh ashe kina tsoro dai" amma a zahiri ta ce "Ai har kuka take yi, tana numfashi"
"Ok shikenan na gode" Fadila haka halayyarta take, duk rashin mutuncinta bata son taga mutum ba shi da lafiya duk sai ta shiga damuwa da tashin hankali.
Hajiya Zainab kuwa ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta.
Fadila kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta dinga kiran Doctor Aliyu a waya, hanklinta bai kwanta ba sai da ya zo.
Yana zuwa ta saka Hajara ta kamo Amina, ta fito da ita falo.
Ya ɗan ƙarewa Amina kallo sannan ya ɗan yi mata tambayoyi.
Hajiya Zainab ta fito falon ta na jiran me Doctor Aliyu zai ce, ya gama ta bawa Amina kuɗin mota ta tafi ta bata wuri.
Doctor Aliyu ya ce "Gaskiya ta ɗan galabaita, jikinta yayi weak sosai, zan bata magunguna nayi mata allurai, zan rubuta mata scanic, da test taje tayi, gobe in Allah ya kaimu da safe zan dawo sai in duba".
Hajiya Zainab ta ce "Ban gane scanic ba, na meye scanic ɗin? Meya haɗata da scanic kuma?"
Doctor Aliyu ya ce "Ai dole ayi mata scaninc, aga musababbin zubar jinin, kin san akwai cututtuka da yawa da sukan kama mahaifa, dole a gano meye musababbin zubar jinin haka"
'Kaga ni ba wannan ne a gabana ba, kayi mata abin da zaka yi mata, kuɗin mota zan bata ta tafi garinsu ta bar mini gida".
Doctor Aliyi ya kalleta ya ce "A wannan yammancin? Baki ga yadda jikinta yayi bane? Idan wani abu ya sameta a hanya fa? Kamata yayi fa tun a lokacin ku kaita Asibiti, ta kwana a can bai kamata ma a barta a gida ba, kiyi haƙuri a gano meke damuntax
Amina ba ta ce komai ba, sai lumshe ido da tayi, a ranta ta ce "Ji Azzaluma, kamar ba ke da 'yar ki ne ya sanya koma menene ya faru da ni ba, ai wallahi ba in da zanje sai na warke'
Fadila ta kwantar da murya ta ce "Mummy, tun da likita ne yayi suggesting ɗin ya zauna, kiyi haƙuri a fara gano matsalar tukuna"
Da ƙyar ta haƙura ta ƙyale Amina, yayi wa Amina allurai, ya bata magunguna ta sha, nan da nan wani wahalalalen bacci yayi awon gaba da ita.
Da magariba, Hajara ta taro napep ta saka Amina suka tafi yin scanic ɗin, Amina da kuɗi a wurinta ta biya kuɗin, da ɗaya test ɗin ya rubuta duk aka yi mata. Baya biye son sanin meye a test ɗin ba, suka karɓo result suka dawo gida.
Da daddare tana jin ringing ɗin wayarta, ta san kuma Daddy ne yake kiranta, amma ta ƙi ɗagawa dan data ɗaga zai gane bata da lafiya ya tashi hankalinsa.
Shi kuwa Daddy jikinsa ne ya dinga bashi kamar akwai wani abu na faruwa mara daɗi, shi ne yake ta kiran Amina, amma bata ɗaga ba.
Sai ya koma ya nemi Fadila a waya, ta ɗaga kiran suka gaisa. Ya tambayeta ba dai wata matsala a gidan komai lafiya? Sai da gabanta ya faɗi, amma ta ce masa ba matsala ba komai.
Da daddare da ƙyar Amina ta iya cin Abinci, duk jikinta babu ƙwari kuma ba ta daina zubar da jinin ba, sai dai ba yawa kamar da haka yake zuba.
Wurin ƙarfe goma na safe, Doctor Aliyu ya zo, Hajara taje ta kira Amina, ta kira Fadila.
Doctor ya karɓi tes da scanic, ya duba ya kalli Amina da ta ɗashe, ya maida idonsa kan Fadila ya ce "Kira mini Hajiyar"
"Ba dai wata matsalar ce ba ko Doctor?"
"Eh ba matsala, kije ki kirawo ta dai"
Amina ta kalli Doctor Aliyu jiki a sanyaye ta ce "Doctor ba dai wani abu ne ya sameni ba ko?"
Ya ce "Eh kar ki damu".
Ya shafe kusan mintuna Ashirin yana jira, sai gata ta fito, ta falon ta zo ta samu wuri ta zauna.
"Hajiya ina kwana?"
"Lafiya lau doctor, ya gida ya aiki?"
"Alhamdilillah ya mai jiki?"
"Gata nan ka tambayeta mana" ya ɗan girgiza kai ya ce "To, sakamakon dai jininta yayi ƙasa gaskiya, sai dai akwai buƙatar a yi mata ƙarin ruwa da magunguna in Allah ya yarda komai zai zama normal, sannan sacanic ɗinta ya nuna, ɓari ne tayi kuma akwai saura, sai an yi wankin ciki"
Hajiya Zainab ta kalleshi kamar tana kallon soko ta ce "Ban gane ɓari ba, me ta ɓarar ne?"
"Hajiya ɓari dai na ciki, wata biyu da kwana Ashirin da huɗu"
Ras! Gaban Amina ya faɗi, amma ta dake ba ta nuna girgizar a fili ba.
"Kana nufin cikin shege kenan?"
Doctor Aliyu ya ya ce "Bana ce ba, tun da ban san a yadda aka same shi ba"
Tafa hannu ta shiga yi tana salati, tana kallon Amina, Fadila kuwa tamkar an dasata haka tayi saroro tana kallon Amina, tana mamakin me Amina ta sani har taje tayi ciki, ko ita da take kusan shekaru Ashirin da huɗu ba tayi Aure ba, bata yi abin da Amina tayi ba.
"Wallahi ba a gidana ba, idan ranki ne yake fita yana dawowa sai kin bar mini gida a yanzun nan ba sai anjima ba. Daga ɗakkoki cin arziki kizo ki ɓata mini sunan zuri'a, dama ba makaranta kike zuwa ba yawon iskanci kike?, wallahi tashi sai kin bar mini gida".
Doctor Aliyu dai sallama yayi musu, ya kwashi kayansa ya tafi, tare da ba su shawarar su kaita Asibiti.
Cikin hargowa da hayagaga Hajiya Zainab ke masifa "Tashi sai kin bar mini gida wallahi, Munafuka 'yar iska"
Amina ta lumshe idanunta tana jin zafin maganganun Hajiya Zainab, da yadda suke sukarta a zuciyarta.
"Ki tashi ki tafi gidan ubanki nace"
Amina ta ce "Ko baki koreni ba zan tafi, amma akwai buƙatar ki san wake da alhakinsa"
"Ina ruwana da ko na ubanwaye? Lokacin da ki ka kai kanki na sani ne? Tashi wallahi sai kin bar mini gidana a yanzun nan, tashi kije ki haɗo tsummokaranki ki fita, lumbu lumbu wutar ƙaiƙayi, kin ƙunso masifa da abin kunya zaki zauna mini a gida, gara da Allah ya toni asirinki ai"
Amina ta miƙe a hankali ta tafi sashinsu, Hajiya Zainab ta cigaba da yaɓa mata maganganu marasa daɗin ji.
Ita dai Fadila kasa magana tayi, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.
Amina na zuwa ɗaki, ta rufe ƙofar ɗakinta, ta kira Daddy a waya ta sanar masa da abin da yake faruwa.
Hajiya Zainab kuwa sashinta ta koma tana bala'i, tana cigaba da kwashewa Amina albarka.
Kiran Alhaji Ahmad ta gani, kamar ta share shi, saboda tunda ya sa ƙafa ya tafi, bai sake bi ta kanta ba. Ta ɗaga wayar ta kara a kunneta tana ta huci ba tare da tayi magana ba.
"Lafiya dai ina magana kika yi shiru?"
"Ehh, dole ka tambayeni mana, tunda sai yau ka ga damar kirana tun da ka tafi"
Cikin hikima da son bugun cikinta ya ce Ya ce "Wait, huncin me kike yi haka ne?"
"Ba dole nayi huci ba, ka san yar iskar yarinyar nan, 'yar gidan wannan mutumin banzan, yawo take yi?"
"Yawo kamar yaya?"
"Jiya na sakata aiki, tayi mini rashin kunya, daga Fadila ta ture ta ta faɗi, shikenan jini ya ɓalle ashe cikine da ita har wata biyu"
Daddy ya ce "Subhanallah, ita Fadila waye ya aiketa, da da ƙarar kwana fa ta janyowa kanta wata matsalar?"
Ta ce "Ai gara da hakan ta faru, Allah ya tona mata Asiri, da tuni yadda ta ƙunso abin tsiyarta haka zata raine shi a gidana, to a yau zan bata kuɗin mota tabi ubanta in da suka fito"
Alhaji Ahmad ya ce "No, ba za ayi haka ba, tun da mahaifinta baya nan bai kamata ayi masa haka ba, idan aka yi haka ba ai masa adalci ba, ki bari in dawo gidan muga abin da yakamata ayi"
"Ban gane me kake nufi ba, ka dawo kayi me, wallahi sai ta bar mini gida, ina ruwana da babanta ba zai ji daɗi na, ta san da hakan ba ta tausaya masa ba taje take iskanci"
Daddy ya ji zafin maganganun Hajiya Zainab, amma ya dake ya ce "Zainab, nima uba ne, kuma na haifa idan wannan tsautsayin ya faru a kan tawa 'yar aka yi mini haka, ba ayi mini adalci ba, ki bari zan zo gidan da kaina"
"Allah ya sauwwaƙe ya faru a kan 'yata, sai dai a kan irinta ga rashin gata ga rashin tarbiyya da watsewa"
Gaba ɗaya ya kasa controlling ɗin Hajiya Zainab. Ƙarshe sai katse kiran yayi ya kira Amina a waya.
Ta ɗaga wayar tasa tana ta ƙoƙarin haɗa kayanta.
"Meenal, kina jina kiyi haƙuri ki bar mata gidan, kar ta illata mini ke, ki jira a waje, zan aiko a ɗauke ki, kije can gida ki jirani, zan dawo anjima in sha Allah, komai dare zan kai ki Asibiti, ki kwantar da hankalinki kin ji Dearna, komai zai tafi daidai, amma dan Allah karki gayawa kowa komai"
A taƙaice Amina ta ce "Shikenan" hargowar Hajiya Zainab ta cigaba da jiyowa, tana tunkaro ɗakinta.
Dan haka ta miƙe, tana jin jiri ta saka hijjabinta, ta ɗau wayarta da jakarta ta nufo hanyar fita tana dafa bango.
A corridor suka haɗu da Hajiya Zainab, ta kalli Amina a wulaƙance ta ce "Ina zaki je ki bar mini kayanki, ki wuce ki kwaso tarkacenki ba zaki bar mini dauɗa da ƙazanta a gida ba, Allah wadaran halinki"
Amina ta kalleta ta ce "Ki daina zaƙewa a kan abin da baki sani ba, kar ki zo kiji kunya, wataƙila abin da kike kira da ƙazantar yana da alaƙa da gidanki, ma'aikatanki ko kuma wani makusancinki. Yanzu idan na kai ƙararku a kan sanadin salwantar cikina ko da yake na gaba da alfatiha ne, sai an bi mini hakkina saboda kun taka doka"
"Ke kina da arziki ko madafar da zakiyi jayayya da ni, matsiyaciya kamarki me kike da shi me kika bawa wani ajiya. Karki fasa kaimu ƙarar, kuma can kije ki nemi wanda yake da alaƙa da abin kunyarki bani ba, fisararriya, ni banda kar inje ki mace mini, da saina tuburbuɗa miki jikinki kan ki bar gidan nan, karuwa kawai"
"Na gode, sai dai ki sani kamar yadda na bar kayana a gidan nan, ina nan dawowa tare da wanda yake da alaƙa da cikin, Ɗanki ko kuma wanda baki zata ba, kuma dole ki karɓemu tun da mai faruwa ta riga ta faru"
"Ƙarya kike yi, ni ban haifi ɗan iska ba, babu abin da ɗana zai yi dake ƙazama kamarki, fice ki bar mini gida munafuka" Amina ta bi hanyar falo, ta fice.
Tausayin Amina ya kama Hajara, taji kamar ta bi bayanta, dan bata san ina zata je ba. Amma taji tsoron kar daga nan Hajiya Zainab ta ce ita ma ta bita.
Tana zuwa ƙarshen layin, bata wani daɗe ba, mai ɗaukarta ta ya zo, ya ɗauketa ya kai ta can gidan Alhaji Ahmad.
Sai wajen ƙarfe shida Alhaji Ahmad ya dawo gida, gaba ɗaya a ruɗe yake cikin tashin hankali ya isa gidan nasa.
A bedroom ɗin da suka saba zama ya tarar da Amina a kwance.
Da sauri ya ƙarasa gaban gadon yana kiran sunanta.
Ya ɗagota jikinsa, fuskarta duk ta ɗashe tayi wani iri.
Nan da nan ya ɗauketa suka tafi Asibiti, Asibitin da ta taɓa rakashi, yaga likita.
Suka sake duba Amina, suka tabattar masa cikin ya riga ya lalace, zasu bata magani sauran ma ya ƙarasa fita, idan bai yi ba kuma sai sun mata wankin ciki.
Amina ta sha wahala sosai a kan ɓarin nan, suka dinga sakamata ruwa da allurai.
Tana kwance a kan gadon marasa lafiya, ga ruwa a saƙale, Daddy na kusa da ita a kan kujera, ya riƙe hannunta a nasa.
A hankali ta buɗe ido, ta farka daga nanauyan baccin da tayi.
Ta kalleshi ta ce "Daddy baka tafi ba?"
"Eh Meenal, idan na tafi wa zai kula mini da ke?"
"Daddy na sha wahala sosai"
"Na gani Meenalina, Allah ya ƙara miki sauƙi, ina fatan yanzu ba kya jin ciwon komai?"
"Bana jin ciwo yanzu, jikina ne ba ƙwari sosai"
Daddy ya ce "Bari in ɗagaki in baki Abinci"
Tayi murmushi ta ce "Zan iya tashi ai"
"No bari in taimaka miki" ya ɗagota zaune, ya jinginar da ita, ya zauna ya dinga bata Abinci da kansa.
Ƙarshe dai shi ya kwana da Amina a Asibiti.
Wajen sha ɗaya saura, aka sallamosu da ga Asibiti, jikinta yai sauƙi sosai jinin ya tsaya sai abin da ba a rasa ba.
Bai wuce da ita ko ina ba, sai gidansa.
Hajara ce ta fara ganinsu, sun dawo tare, Hajara ta ce "Lallai yau mutumin nan ya shirya bala'i a gidan nan"
Amina ta zauna a falo, ya ce mata yana zuwa, Hajara kuma ta shigo tana yiwa Amina sannu, tana son tambayarta ya aka yi amma taga Amina ta tsuke fuska.
A ɗaki ya tarar da Hajiya Zainab, tana ta shirin fita yawonta.
Ta kalleshi ta ce "Daga ina haka?"
Bai amsa mata ba ya ce "Zainab bance miki karki kori yarinyar nan ba?"
Ta kalleshi ta ce "Na koreta ɗin, nawane kuɗin ubanta a cikin kuɗin daka haɗa ka gina gidan, me zata zauna tayi mini?"
Ya ce "Tun da gina ne, na dawo da ita, ba zata bar gidan nan ba sai mahaifinta ya zo, zan danƙa masa 'yar sa"
Hajiya Zainab ta daki mudubi ta ce "Wallahi ba a gidana ba, kaje can ku haɗu a titi ya karɓi 'yar ta sa"
Ta yi waje ta fice daga ɗakin.
Bayanta ya bi yana kiran sunanta, bata saurareshi ba, ta ƙarasa falo.
Ta sha mamakin ganin Amina a falon.
"Ke bance ki bar mini gida ba? Meya dawo da ke?"
Amina tayi shiru tana binta da ido.
"Zainab ki nutsu ki bi komai a hankali dan Allah"
"Ba zan bi koman a hankali ba, wannan mara mutuncin da jiya kamar zata dokeni, Wallahi sai ta fita" tayi maganar cikin tsawa.
Jin hayaniya ya sanya Fadila fitowa, ta tsaya tayi saroro tana ganin ikon Allah.
Ta sake kallon Daddy ya tareta daga kaiwa ga Amina ta ce "Wai Ahmad, meye alaƙarka da uban yarinyar ne? Ba fa zata zauna mini a gida da najasa ba, tayi ɓarin shege nan gaba haihuwa za tayi, wallahi sai ta fita"
"Ba zata fita ba, babu in da zata je?" Yayi Maganar cikin fushi.
"Saboda me zata zauna mini a gida?"
"Saboda ba a waje tayi cikin ba, yana da alaƙa da gidan nan, dan haka ba zai yiwu wannan abu ya faru ba sannan a tura masa 'yar sa a haka ba, idan aka yi haka ba ayi masa adalci ba, gara komai zai faru ya faru"
Ɗan saroro tayi tana kallonsa ta yi ƙasa da muryarta ta ce "What do you mean?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Am responsible of it"
Ƙara Fadila ta saki, saboda jin maganar ta diro ta in da ba ta zata ba, gaba ɗaya suka waiwaya, dan basu san ta shigo falon ba.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Follow my Arewabooks account through this link.
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
57
Cikin tsawa Daddy ya kalli Fadila ya ce "Get out from here" Saboda gaba ɗaya bai san Fadila tana falon ba.
Jiki na rawa ta juya ta bar falon, tana jin tamkar mafarki take yi, tana tantamar anya kuwa Daddy ya san meyake faɗa?.
Tsatstare Alhaji Ahmad Mummy tayi da ido, ita bata motsa ba kuma ba ta ce masa komai ba.
Shi ma kallon nata yake yi, domin yaga wani mataki zata ɗauka.
"Zainab" ya kira sunanta, ba ta bari ya faɗi wani abu ta ɗaga masa hannu ta dakatar da shi, ta kalli ƙwayar idonsa ta ce "Ahmad, ka bari in gama nazartar ka ko Allah zai sa in gano wace irin ƙwaya ka fara sha mana, ko kuma in ce giya ka san abin da kake gaya mini kuwa?"
"Na sani, bani da wani da zaɓi da ya wuce na gaya mikin, cigaba da ɓoyewar ba shi da amfani"
"Lallai ka riƙa wuyanka ya isa yanka, kai saboda rashin kunya sa rashin sanin darajar kai ka tsaya a gaban ka kalli tsabar idona kake gaya mini ka yiwa mai aikin gidana ciki?"
"Idan na ɓoye miki, ai ba zan ɓoyewa Allah ba"
"Ta tabbata kenan kai ne ka yi mata cikin?" Tayi maganar tana nuna Amina, da ke bayan Daddy a tsaye.
Alhaji Ahmad ya daidaita tsayuwarsa ya ce "Dan Allah Ki tsaya ki fahimceni, kuma ki mini adalci kafin ki yanke mini hukunci".
"Rufe mini baki munafuki, mara mutunci ni zaka tonawa asiri ka ciwa mutunci