Showing 99001 words to 102000 words out of 296192 words

Chapter 34 - GABA DA GABANTA

daɗe suna chatting basu san dare ya yi ba, ita kanta tana mamakin kanta yadda ta yi wani irin sabo da Khalil, wanda har ya kai idan Khalil baya son abu, har rawar jiki take ta daina, duk abin da ta san zata yi yayi farin ciki tana masa. Haka shima ɓangaren sa tattalata yake tamkar ɗanyen ƙwai a kan dutse, shima yana kaucewa duk wani abu da zai sanya ta ɓacin rai ko damuwa, yana matuƙar tausayinta, hakan ya sanya yake tattalinta yake gudun abin da zai ɓata mata rai ko tayi fushi.

A Hanyar Yazid ta tahowa makaranta, suka haɗu da class Captain ɗinsu, ya ɗauko Yazid a babur ɗinsa, suna tafe yana bashi labarin faɗan da Amra da Fadila suka kusa yi jiya, a kan abin da Amran tayi masa.
Yazid dai bece komai ba, sai ɗan murmushi da yayi, Captain ya cigaba da bashi haƙuri, a kan irin abubuwan da wasu daga cikin 'yan ajin suke masa.
Zuwansu yayi dai-dai da tsayuwar motar Fadila.

"Ahh Yazid ga Bestynka nan ta ƙaraso"

"Wace kuma Besty na?" Yazid yayi maganar cikin ko in kula.

"Fadila mana"

Ta rufe motar ta ɗan tsaya tana jiran ƙarasowarsu.

"Captain" ta faɗa tana ɗan murmushi.

Captain ya ce "Na'am tsigai, sarkin tsiwa"

"Kaga ka kiyayeni bana so"

Yazid yaƙi ko kallon in da Fadila take.

Ya yin da ita kuma take satar kallonsa, Captain ya ce "Bari in yi gaba ku gama ganawa, dama zan karɓo mana Assignment, sai kun taho" yayi gaba ya bar su a tsaye.

Captain na barin wurin, Yazid shima ya yi tafiyarsa ya barta a wurin, gaba ɗaya sai taji babu daɗi shareta da ya yi, ko dai Kankiya ya kira shi ya yi masa warning ne a kanta, shi ya sanya ya daina kulata?.
Ɗan taɓe baki tayi, ita ma ta nufi aji tana cigaba da zancen zuci.

Sai yau Azima ta dawo daga hutu, suka rungume juna ita da Amina suna ta murna. "Azima shi ne kika ƙi dawowa sai yau?"

"Ke bari, munje hutu da Mummy ne, sai jiya muka dawo"

Amina ta ce "Masha Allah, ya Mummyn?"

"Mummy na nan lafiya, ya Baba da mutanen gidanku marasa mutunci"

Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Meye haka?"

"Ba dole in faɗa ba, mutuncin ne da su? Wallahi matar nan ta bani mamaki Amina, a gaskiya kina haƙuri sosai, Allah ya ƙara miki haƙuri"

"To Azima idan ban yi haƙuri ba yaya zan yi? Tun da karatu nake son nayi"

"Ke zan yiwa Mummy magana, wallahi da zaki yadda ki dawo gidanmu, ki daina wannan aikin, Mummy zata dinga biya miki kuɗin makaranta, meye dubu sittin Allah na tuba, Mummy zata biya miki"

Waro ido Amina tayi ta ce "Azima dubu sittin kuma? Dubu sittin ne kuɗin makarantar?"

"Au ke da baki sani ba? Dubu sittin ne fa kawai duk term, sai sauran abin da ba a rasa ba, Mummy tana da kuɗi sosai, ga shi Daddynmu ya mutu ya bar mana kuɗi, ni da Yaya Sagir da nake gaya miki, wallahi da zaki yadda Mummy cewa tayi zata ɗauke ki ki dawo gidanmu, ita tana sonki"

Shiru Amina tayi tana tunani, Yanzu duk term naira dubu sittin Alhaji Ahmad yake biya mata na makaranta, kuma gashi ance na shekara ya biya mata, ga kuɗin litattafai da sauransu.

"Ya naji kin yi shiru? Zaki yadda ki dawo gidanmu?"

Firgigit Amina ta dawo daga tunanin da ta tafi, ta ce "Azima Baba ba zai yarda in nisa da shi ba, nima ba zan so hakan ba, amma naji daɗi da ƙauna da karamcin da Mummy take nuna mini, shi wannan aikin da nake na lokaci ne, watarana sai labari. Kuma in Allah ya kaimu next year fa zamu gama, da an gama wannan competition ɗin fa za'a fara yi mana lesson ɗin Jamb da na Waec da Neco, Kinga lokaci kaɗan ya rage mana".

"Haka ne Amina, Allah yasa mu gama lafiya"

"Ameen" Amina ta amsa.

Har aka tashi Yazid bai yi gigin zuwa in da Fadila take ba, gaba ɗaya sai taji babu daɗi, dan a 'yan kwanakin ta saba da shi da nacinsa, ba tare da ta shirya hakan ba.

Hajiya Zainab ta sha mamakin yadda Khalil ya iya daina shigowa cikin gidan, ko gaisheta yayi balle ya ci Abinci, duk dan saboda ta raba shi da wata 'yar matsiyata.
Dan haka a fusace yau ta tafi ɗakin nasa, ta tarar yana zaune  yana dannan system, walpaper system ɗn, hoton hannunsa da na Hafsa ne sanye da zobunan da ya saya musu.

"Sannu mara mutunci salamamme"

A razane ya ɗago ya kalli Mummy.

"Yanzu Khalil wuyanka har ya yi kaurin da dan nayi maka faɗa na hanaka kula wata matsiyaciyar yarinya zaka daina shiga harkata, ka daina shigowa cin abinci?".

"Mummy ba haka bane kaw ....

"Yi mini shiru, gaba kake da ni ko Khalil, ka kyauta ka cigaba kar ka fasa, wannan yarinyar ce dai ko, to na rabaka da ita har Abada. Idan kuma ka ƙi ji, ba zaka ƙi gania ba. Ta juya ta fice tana huci, ba ta jin zata iya yiwa Khalil sassauci a kan al'amarin nan sam.
Khalil ya dafe kansa da yayi masa wani irin nauyi, da har yake barazanar yi masa ciwo, ya rasa Wannan wace irin ƙiyayya ce haka Mummy take yiwa talaka, meye aibun Hafsa banda talauci, kuma ai komai na Allah ne.

Washegari ma a school, Yazid ya ƙi kula Fadil, ya cigaba da sabgoginsa, sun yi lectures na farko, sun samu break, Fadila ta kasa jurewa, ta tsinci kanta da tafiya wurin da yake a zaune, a can ƙarshen ajin.
"Ustaz wurinka na zo"
Ya ɗago ya kalleta "Waye kuma Ustaz?"

"Kai mana"

"Baki san suna na bane?"

"Eh sunan naka ne bana riƙewa" Yazid ya gane ba zata iya kiranshi da sunansa bane a gabansa, amma dan rainin hankali ba zata faɗa ba.

"Magana fa nake maka"

"Ba fa kurma ne ni ba, ina jinki"

"To ba zaka amsa ba"

"Ki faɗi sunana mana idan so kike in kulaki" yayi maganar ba tare da ya kalli in da take ba.

Share maganar tayi ta ce "Abu nake son ka koya mini dan Allah"

"Ba zan koya ba" ya bata amsa direct.

Ji tayi kamar ba taji daidai ba, dan haka ta ce "Me kace?"

Ya waiwayo ya kalleta ya tsuke fuska ya ce "Ba zan koya ba nace, idan kin koyi faɗan sunana sai in koya miki" Nan da nan ya ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta, kawai ta juya ta bar wurin, ranat yana mata suya, 'laifina ne da nuna na damu da kai, shi yasa har ka yi mini wulaƙanci' ta faɗa a zuciyarta.

Tana bada baya Yazid ya fara dariya ya furta "Yarinya ba wayo" yana ankare da ita har suka kammala lectures na biyu, sai cika take tana batsewa, taji zafin abin da ya yi mata sosai.

Sai da ya daidaici lokacin da yafi sakata a kwana, ya hautsina mata lissafi, ya dawo daga salla, lokacin da ɗalibai suka ragu daga ajin, wasu suka tafi salla wasu cin abinci, ya lura ko sallar babu alamar ta je, ta Kwantar da kanta a kan benci.

"Bestyna, what are you thinking about? Tashi muyi karatun ɗauko littafin muyi karatun"
Sarai ta gane muryarsa, amma tayi masa banza, taƙi ɗagowa.

"Common, ɗago mana" yayi maganar yana zama a kusa da ita. Da sauri ta tashi zaune, ta kuma matsawa ciki, tana haɗe rai.

"Ɗauko littafin muyi karatun"

"Kaga malam ka ƙyaleni bana so" ta faɗa tana jin kamar a lokacin ya ce ba zai koya mata ba.

"Haba Ukty, kefa kika fara wasan nan, kika ce idan ina da zuciya kar in sake kula ki, kuma ina da zuciya a ƙirjina, tana aiki kuma, kawo hannunki ki taɓa kiji" yayi maganar kamar zai riƙo hannunta.

"Wai meye haka ne, kar ka sake ka taɓa ni"

"Ashe kina tsoro, kawo muyi lesson ɗin kin ji Bestyna"

"Bana so, na gaya maka ka ƙyaleni zan maka rashin mutunci wallahi"

"To ni rashin mutunci wanne ne baki yi mini ba, duk haddace in kin mini ba haushi nake ji ba, ni ɗanawa nayi yau, amma ki yi haƙuri muyi da wasa nake miki"
Ɗauke kanta tayi, tana kallon gefe guda, irin yayi idan ya gaji ya tashi.

"Baƙin gashi, fararen idanuwa, dogon hanci, bakin tsiwa, matsakaicin tsayi, fa tubarakallahu ahsanul khaliƙin, You Are beautiful" murguɗa baki tayi tana kuma ɗauke kai.

"Shikenan, idan kin sakko kya kulani, ni na tafi gida, saurayinki ne zai shigo lectures yanzu, gara in fita in tafi, tun kan ya shigo ya dizgani a gaban mutane saboda ke".

"Kar ka sake cewa saurayina, na gaya maka"

"Saurayinki ne mana, idan ba saboda ke ba me nayi masa ya tsaneni, bai san ba wata alaƙace ta kirki tsakanina da ke ba, ki mini tsiwa lokacin da kike so, ki lallaɓani idan kina buƙatar wani abu a wurina, ko ba haka ba ne?"

"Kai ka sani"

"Dama ni na sani mana, ki kalli idona ki maimaita abin da kika faɗa in ba tsoro ba"
Sake kifa kanta tayi, tai masa shiru, tana jinsa ya ɗau biro, yana mata rubutu a jikin hannunta, taƙi ko motsi, sai da taji alamar ya tashi ya tafi, sannan ta ɗaga hannun ta duba, da larabci ya yi mata rubutu, sai dai ba ta gane meya rubuta ɗin ba.
Ɗaga kai tayi taga har ya kai ƙofa, a ranta ta ce 'A haka kamar baya magana, amma ya iya wulaƙancj kala-kala'.


Khalil ya rasa yadda zai yi da ransa, gashi ya cinye satinsa biyu, amma babu wani daidaito a tsakaninsa da Mummy, balle ya sanya ran zata fahimce shi.
Kusan ƙarfe goma na dare, yana kwance a kan gado, ya rungume pillow, yana ta zuba soyayya a waya shi da Hafsa.

"Baby, ina ga haryanzu Abincin da kika mini, bai gama narkewa a cikina ba, har yanzu bana jin yunwa"

"Ni dai ban yadda ba, idan ulcer ta kama mini kai, sai mun yi faɗa"

"Allah Hafsa bana son cin abinci, ga kewar ki ta isheni zan koma wurin aiki"

Ta Kwantar da muryarta ta ce "Eyya,  ai ba komai, ka kwantar da hankalinka, zamu dinga waya".

"Ai ni nafi sonki a kusa da ni Babyna, ginin gidanki ya kusa kammala insha Allah, idan na je zan ɗauko miki video ki gani, idan da abin da bai miki ba sai a sauya"

Hafsa ta ce "Wace ni in ce ga abin da bai mini ba, komai kai daidai ne, Allah ya yassare maka halal, ya tabattar mana da alkhairi"

"Ameen my sweet, yadda gari yake da sanyin nan, ace kina kusa da ni, kin dafa mana tea, ina sha ina kallonki cike da so da ƙauna"

Tayi dariya ta ce "Abin da ka hango kenan?"

"Eh mana, da mun yi aure ba ruwaa da bargo, kin isheni"

Ta ɗan tura baki ta ce "Zaka fara ko? To sai da safe" ya buɗe baki zai yi dariya, yayi tozali da Mummy a tsaye a kansa, wadda ganin bai shigo cin abincin dare ba, duk da faɗan da tayi masa ya sanya ta biyo shi ɗakinsa, ta zo ta tarar da shi yana waya da Hafsa.

Mugun kallon da ke masa ne ya sanya shi, rikicewa ya katse wayar yana kallonta"

AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL




PAGE36

Cikin rikicewa da inda-inda Khalil ya ce "Mu..mmm...Mummy dan Allah ki tsaya ki ji"

"Me zan tsaya in ji banda wanda na ji Khalil, ai naji komai ka saurari matakin da ni kuma zan ɗauka".

"Innalillahi, Mummy dan Allah kar ki yiwa Hafsa komai, marainiya ce"

"Eh marainiya ce, kai ne baitul mali ai, kai ne mai arziƙin ɗaukar nauyinta a ɗora maka wahala, kana nan kana gina mata gida ko? Sai ta shiga in gani, kaje ta dafa abu tayi barbaɗe barbaɗe ta baka kaci, zaka gamu dani" ta fice fuuu ta bar ɗakin.

A sukwane Khalil ya bita, yana kiran sunanta. Ya cinmata a falo.

"Mummy dan Allah kar a yiwa Hafsa wani abu, ni ki hukuntani, ba zata iya ɗaukar hukuncin da zaki mata ba"

"Rufen baki Khalil, ni zaka mayar ƙaramar yarinya, wato har Asirin da suka yi maka ya fara tasiri a kanka ko? Matsa ka bani wuri kan in make ka"

Ya haɗa hannayensa biyu cikin magiya ya ce "Dan Allah Mummy ko sau ɗaya ki saurareni, wallahi mun shaƙu Hafsa bata da wani aibu, dan Allah ko sau ɗaya ki saurareni"

Shareshi tayi ta wuce ɗakinta, Khalil ya zauna a kan kujera ya dafe kansa, wani irin gumi ya tsatsafo masa a goshi, duk da a yanayi ake na sanyi.

Amina da ke gefe tana kallon Tv tayi shiru, jikinta yayi sanyi tamkar ita ake yiwa faɗan, gaba ɗaya taji babu daɗi, Saboda Hajiya Zainab ta iya tijara.

Ita Amina abin har mamaki ya bata, ɗanta ma ba ta ƙyaleshi ba, duk dan ya ce yana son 'yar talaka ake wannan dambarwar bala'in.

Jiki a saɓule Khalil ya miƙe, ya bar falon yana tunanin meye mafita, bai taɓa yiwa Mummy turjiya a kan wani abu ba, amma a wannan karon zuciyarsa na raya masa ya tirje, tun da Aurensa da Hafsa bai saɓawa Addini da kuma Al'ada ba, gani yake idan ya fasa aurenta bai mata adalci ba, kuma bai san wani irin hali zata shiga ba kuma bai san hannun wa zata faɗa ba, babban abin daya ƙara tsaya masa shi ne, bai wataƙila idan ya rabu da ita halin da zata shiga na damuwa ya fi na baya, tun da dama shigarsa rayuwarta ne ya bata ƙwarin gwiwa sakewa da rage mata damuwar da take ciki.

Washegari Daddy ya fito falo, ya tarar da Amina a zaune, tana jiran lokaci ya cika ta tafi makaranta "Ina kwana" Amina ta gaishe shi.

"Lafiya ƙalau, yau ban hararekin ba ko?" Murmushi tayi tana sake janyo jakarta jikinta.

"Har kin shirya tafiya makarantar?"

"Eh jira nake lokaci ya cika"

"Ok, school ɗin ku sunyi mini waya, a first term za a yi muku registration ɗin Jamb da SSCE ko?"

Amina ta ce "Eh haka suka ce mana"

"To ki ƙara dagewa, idan result ɗinki yayi kyau, hope baki manta da sirrinmu ba  ko?"

Cikin murmushi Amina ta ce "Eh, ban manta ba, zan yi karatu sosai in sha Allah"

Daddy ya ce "Good girl" hakan yayi daidai da fitowar Fadila, cikin shirin tafiya makaranta.

Ba ta kawo komai a ranta ba, ta zauna, ta zuba Abinci ta fara ci.

"Ina Mummynku ne?" Daddy ya tambayi Fadila.

"Bacci take, ta ce kar wanda ya dameta"

"Ok, nima fita zan yi yanzu".

"To Daddy a dawo lafiya" Fadila ta faɗa tana shan tea.

Da ido ya yiwa Amina alamar, ta biyo bayansa.

Amina ta miƙe ta saɓa jakarta, tabi bayan Daddy.

Sai da suka fito daga falon, sannan ya tsaya Amina ta ƙarasa in da yake, ya dubeta ya ce "Muje in ajiye ki a School ɗin, sai in wuce in da zani"

Amina ta ce "Amma Ba wani wurin zaka ba? Kar ka makara fa, zan hau Napep"

Yadda ya tsareta da ido ne, ya ɗan tsuke fuska ya sanya ta yin shiru, yayi gaba ta cigaba da bin bayansa.

"To bari in je in gaida Baba"

"Ki sauri" ya faɗa tare da nufar in da motocinsa suke.

Amina ta isa wurin Baba, ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi.

"Lafiya ƙalau Uwata, kin tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau Baba, ya aikin"

"Alhamdilillah, zaki tafin ne?"

Amina ta ce "Eh, amma wai ya ce zai ajiyeni a makarantar"

Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Shi wa?"

"Baban su Fadila"

Baba ya ɗan yi shiru, saboda ya lura a 'yan kwanakin nan akwai wani ɓoyayyen abu tsakanin Alhaji Ahmad da Amina, yanzu bata tsoronsa kwata-kwata, ga wata shaƙuwa a tsakanin su. Ga yawan kyautata mata da yake yi, ya yita sayen abubuwa yana bawa Baban ya bata, tuna miyagun fatan da su Bala suka dinga yi a lokacin da ya sanar da su Amina zata taho birni karatu.
Kan Baba ya ce komai, Alhaji Ahmad ya ƙaraso in da Baba yake da mota, ya sauke glashin motar, Baba ya taso da sauri, suka gaisa da Alhaji Ahmad.

Ya ce "Zan sauke Amina a makaranta sannan in wuce"

Baba yana matuƙar jin nauyin Alhaji Ahmad, mussaman duba da irin alfarmar da Ya yi masa a kan Amina, haka ya danne ya ce "To shikenan babu laifi, Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ahh kar ka damu babu komai".

Amina ta zaga ta shiga mota, Daddy ya ja motar suka bar gidan.

"Daddy a kashe Ac nan sanyi fa" Amina ta faɗa tana duunƙule jikinta saboda sanyi.

Kwaikwayon muryarta ya yi ya ce "Ba za a kashe ba zafi nake ji"

A ɗan shagwaɓe ta ce "Allah sanyi nake ji, mura zan yi idan baka kashe ba"

"Mayar da ita ɗumi, ai kina kusa da wurin" yayi maganar yana mayar da hankali a kan tuƙinsa.

Ta ce "Ai ban iya ba"

"Ohh Ashe fa 'yar ƙauye ce"

Ta ɗan zumɓura baki, tana kallonsa ta gefen ido.

Miƙa hannunsa ya yi, ya canza zuwa ɗumi, tamkar zai taɓata, hakan yasa ta takure jikinta har da ɗan rintse ido. Yayi murmushi kawai sannan ya ce

"Kin gane kan wayar taki kuwa?"

"Eh na gane, wayar tana da kyau sosai, ga Camera mai kyau, duk nasa lambar ƙawayena da ta Baba a ciki, har what's app aka buɗe mini"

"Waye ya buɗe miki?"

'
"Ƙawata Azima"

"Kar ki sake zuwa da wayar makaranta, kuma ban yadda ki saka lambar wani  namiji a ciki ba"

Ta ce "Dama sau ɗaya naje da ita makarantar, ba zan sake ba, amma har lambar mazan ajinmu ma ba zan saka ba? Kuma an sani a wani group fa na makarantarmu gaba ɗaya".

Daddy ya ce "To daga haka kar a ƙara, idan ba haka ba what's app ɗin ma zan hana"

"Tom na gode sosai, zan kiyaye in sha Allah"

"Kin sa lambar ƙawaye Amma kika kasa ko yi mini flashing a wayar taki, ko kuma da safe ki gaisheni a wayar, bayan har kuɗi na saka a layin, kuma da lambata a ciki"

Amina ta zaro ido ta ce "Haka kurum, in kiraka ta ɗaga in ce mata me?"

"Ita wa?"

"Au, ba kowa"

"Saifa kin faɗa, ita wa?"

"A'a, haka kurum in faɗa in je ka ajiye ni, a titi" Kawai yayi dariya ya cigaba da tuƙi.

A ƙofar makarantar ya ajiye ta, ya ce "In an tashi zan turo a ɗauko mini ke, ko in zo da kaina"

Amina ta kalleshi ta ce "A ɗauko ni a kaini ina? Ina da kuɗin mota fa"

Ya haɗe rai ya ce "Haka nace"

"To Allah ya baka haƙuri, Allah ya kaimu a tashin" ta ƙarasa maganar tare da buɗe motar ta fice.

Ƙarfe goma da rabi ma safe, sannan Mummy ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login