Showing 276001 words to 279000 words out of 296192 words

Chapter 93 - GABA DA GABANTA

dai ban sani ba ko kana cin tuwo, tuwon Shinkafa muka yi da miyar gyaɗa, sai lemon kwakwa"

Yazid ya ce "Alhamdilillah, ai a ƙoshe nake"

Daddy ya ce "A'a sai ka ci Abinci zaka tafi".

Yazid ya ce "Daddy a ƙoshe nake, zan ne na kai mata saƙonta tana jirana"

Amina ta ce "Kar ka damu, in dai furits ne, sai a haɗa maka ka tafi mata da su"

Ganin Yazid ya dage ba zai ci abinci ba, ya sanya Amina ta je Kitchen ta samo kwanuka ta juye masa abincin,ta haɗo masa Fruit da kayan tsarabarsu ta bashi, Daddy ya ɗora masa da kuɗi, sai dai dan yana jun kunyar Daddy ne, amma da ba zai karɓi kuɗin ba.

Daddy ya ce bari ya ragewa Yazid ɗin hanya, suna tafe ne Yazid ya ke cewa "Daddy, dan Allah ka janye Maganar ka a kan Fadila, ka bari na kawo ta gida ta ganku, tana cikin damuwa"

Daddy ya numfasa ya ce "Yazid, ni kaina ina kewar 'ya ta, amma da zarar na ce ta zo gidan nan,za a iya samun matsala zata iya cewa ba zata koma ba, ko kuma mahaifiyarta ta ce ba zata koma ba".

"Daddy Fadila ba zata yi haka ba, dan Allah ina nema mata afuwa laifin da tayi, dan Allah a sassauta mata"

Daddy yayi murmushi ya ce "Za'a duba in sha Allah"

"To Daddy godiya muke, Allah ya ƙara girma"

"Amin Yazid, ni ma ina yi maka godiya"

Yazid ji yayi kamar ya sanarwa da Daddy larurar da Fadila take fama, amma yayi shiru saboda kar ya ɗaga masa hankali.


A gida ya tarar da Fadila, ta yi masa sannu da zuwa, tana Alla Alla ya zo ya buɗe ledar da ya zo da ita ta samu abin da zata ci.
Ganinsa da abinci bai sanya ta tambayi ina ya samo ba, yana can yana wanka ta zuba abunta ta fara ci, sai fitowa yayi ya ganta ta na ta zuba loma.

"Ke baki san a ina na samo Abinci ba kin zauna kina ci?"

"Koma dai a ina ka samo shikenan, rabon da na ci Abinci har na manta, ni kamar ma na san irin wannan girkin"

Yayi murmushi ya ce "Gama ci tukuna"

Sai da ta gama cin abincin sannan ta kalleshi ta ce "Yauwa wai ina kaje ne, kuma a ina ka samo Abinci?".


Yazid bai ɓoye mata ba ya gaya mata. Tsuke fuska Fadila ta yi ta ce "Da na san ita ta bada wannan abincin, da ba zan ci ba"

Ya zuba mata ido ya ce "Saboda me?"

"Na tsani yarinyar nan, bana ƙaunarta ita ce silar rusa dukkanin farincikin gidanmu, kalli halin da jefamu a gidan nan" tayi maganar iya gaskiyarta.

Yazid ya numfasa sannan ya ce "Kina dana sanin aurena ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a amma meyasa kake tunanin haka?"

"Na ga da saka hannun ta a cikin aurena da ke, duk da ban san zaman da kuka yi a gidan ba, amma banga dalilin da zai saka ki tsaneta ba".

Fadila ta bashi labarin yadda Amina ta auri Mahaifinta.

Ya dubi Fadila a tsanake ya ce "To meye laifinta dan ta auri mahaifinki, na san zaki ga kamar na yi miki ba dai-dai ba, amma Fadila da ni na samu matan uba kamar irin taki, wataƙila da ban tagayyara haka ba, rashin tawakalli ke sanya mu ɓata wasu lokutan.
Kusan matsayi guda ne na Amina da Innata, matan babana suka kasa jurewa suka fara cutar da mahaifiyata, meye laifin Innata a kan su take?" Fadila ta girgiza kai alamar a'a.

"To kusan haka ne, na san wataƙila kin taya Mummy kishi a kan aurenta da Daddy yayi, amma kema a kanki take? Ya aka yi kika san ta tarwatsa muku farinciki? Laifi kika yiwa Daddy ya ɗau matakin aura mini ke, amma ki sawa ranki cewa dama Allah ya ƙaddara zan aureki ko da ita ko babu.
Kin san babbar musiba a rayuwa? Ace mahaifinka yana biye biyen mata shi ne babbaan bala'i da tashin hankali, amma dan dai ya yi aure da sauƙi, tunda ya kare mutuncinku da nasa a idon duniya, idan kika ce kin tsaneta mahaifinki ne ya ajiyeta. Kuma Fadila baiwar Allah nan tana da kirki sosai, ki kamanta ta da nawa matan uban ya isheki misali Fadila"

Ɗan yamutsa fuska tayi ta ce "Na ji, dan Allah mu bar wannan zancen bana so"

Ya ce "Shikenan, an bar shi"

Daga nan suka shiga wata hirar, yake gaya mata ai Yusra ta ce masa aure zata yi, zata auri abokin Khalil.

Fadila ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, he's my ex Allah ya sanya alkhairi, gayen nan ya soni sosai"

"Amma ai zaki bikin idan lokacin bikin ya yi ko?"

"To gani nan dai" ta faɗa jikinta a sanyaye.


Alhamdilillah, jikin Fadila ya ɗan yi sauƙi da yawan iskar da take yi, saboda yawan Addu'oi da Yazid yake yi mata kuma yake koya mata.



Hajiya Turai ce da Hajiya Salma zaune a falon Hajiya Zainab, Hajiya Turai ta na yi mata baynin wasu garin magunguna.
"Zainab, tun da dai shi mijin nan naki haka Allah ya yi shi , ki bishi ta yadda yake so, wannan wasu zafafan kayan nata ne da ga Chadi, kiyi amfani da su ki lallaɓa shi ko Allah ya sa ya faɗi in da Fadilan take, tun da dai kin masa tashin hankali amma yaƙi yarda"

Hajiya Zainab ta ce "Hmmm ai ni lamarin sa yanzu tsoro yake bani, ban taɓa tunanin haka yake da masifar taurin kai ba sai yanzu a wannan karon".

Hajiya Salma ta ce "Rabu da shi, ai ta ko ina ɓullo masa za muyi, ga wannan kayan hayaƙin suma ki dinga yi, ita ma Fadila ta bani mamaki da tsawon wannan lokacin ta kasa waiwayar gida, ta je ta zauna, ko wa ya aurawa ita oho?"

"Koma wa ya aurawa, zan bishi a sannu na gano in da 'ya ta take.







Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA DOMIN SAYEN NASA.
08081012143


83



Washegari Yusra ta aikowa da Yazid kayan cake fal, har da Abinci, babban dalilin da ya sanya Yusra ta bawa Yazid kayan nan haka shi ne saboda Fadila ta ce mata tana son ta dinga taimakawa Yazid amma babu lallai ya amince.
Shi kansa yayi mamakin uban abin da ta haɗo ta aiko masan, Fadila kuwa da ya je da kayan tamkar ta yi rawa dan murna, wuni ta yi tana aikin ciye ciye, saboda dama ba abinci take ci ba, sai dai tana ci tana amai amma ta ƙi haƙura ta dinga tura cake ɗin.
Ba ƙaramin tausayi take bawa Yazid ba, duk da fatarta ta sake murjewa amma tayi rama saboda laulayi.



Daddy kuwa bayan ya koma gida, Amina ta ke yi masa Congratulations, cikin rashin fahimta yake tambayarta meyafaru?

Amina ta ce "Mutuniyarka fa ina kyautata zaton an gamu ne".

Cikin rashin Fahimta ya ce "Ban fahimta ba"

"Ina ga cikine da ita fa"

Da sauri Daddy ya ce "Haba dai?"

"Baka ji yana cewa ba ta da lafiya ba, tana masa lissafin abin da zai sai mata ba"

Daddy ya ce "Alhamdilillah, Allah ya tabattar ya amince, ikon Allah zan ɗau ɗa na ɗau jikoki dan ina kyautata zaton Hafsa zata riga haihuwa"

Amina ta ce "Hmmmm ko kunya baya ji, ana haifa masa jikoki kuma za a haifa masa 'ya'ya gaskiya daga wannan a barwa yara su yi"

Daddy ya ce "Ke kin isa ma? Ko goma zaki haifa mini ina so Meenal, ke ta mussaman ce sosai a wurina, kin zo mini da alkhairi da dama a cikin rayuwata"

Ta shafi dogon gemun Daddy tana murmushi ta ce "Ina sonka Yallaɓai"

"Ina sonki sosai Meenalina, next week za a kawo motarki in sha Allah, and ina son jin idan kina da intrest a kan wani business, sai in san abin yi"

Ta yi murmushi ta ce "Ban rasa komai ba daga gareka, ga gidan gonata can a garinmu, ka sa ana kula mini da shi, a yanzu dai bana buƙatar komai, karatuna zan mayar da hankali a kai sosai for now".

"To Allah ya dafa yayi miki jagora 'yar Babyn Ahmad"

Murmushi tayi tare da jinjina masa ta ce "Godiya nake ranka ya daɗe"





Yazid ya na zaune ya kammala karatun sa, ya dubi in da Fadila ke zaune tana kallonsa, "Fadila" ya kira sunanta.

Ta kalleshi ta tsuke fuska ta ce "Meye kuma na kiran sunana haka kai tsaye?"

Yazid ya ce "Magana ce mai muhimmanci, ina son zamu je Dutse ne mu je mu gaishe su"

Fadila ta tsuke fuska ta ce " Ni ba zani ba"

"Amma saboda me?"

"Kaga nifa ba wani sabawa na yi da su ba, me zan je na yi musu?"

Yazid cikin mamaki ya dubi Fadila ya ce "Ba family ɗinku ne duka a can ba, both na Daddy da na Mummy?"

"Eh amma ba wani zuwa nake yi ba, ni ba wani sabawa na yi da su ba".

Yazid ya ce "Haba gaskiya baki kyauta ba, zamu je mu gaishe su daga nan sai mu tafi Jalingo" Jiki a sanyaye Fadila ta ce "Idan muka je Dutse, Mummy zata san mun je, kuma idan ta san mun je sai ta nemi in da nake, kuma idan ta gano in da nake, zata iya samun saɓani da Daddy.
Ina kewar Mummy, amma idan ta san in da nake za a iya samun matsala".

Yazid ya tashi ya koma kusa da ita, ya rungumeta a jikinsa ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri kin ji Babyna, komai zai wuce ko da Albarkacin biyayyar da kika yiwa Daddy da kuma biyayyar aure da kike yi mini, ba zaki wulaƙanta ba, komai zai wuce"

Fadila ta kalleshi ta ce "Da gaske ina yi maka Biyayya Zid?"

"Alhamdilillah, kina yi mini daidai gwargwado, ban taɓa zaton zaki yi mini biyayya ba, duba da yanayin ki muna school, ga tsiwa ga rashin ta ido, ban zaci zaki zauna da ni ba ba tare da kin bujure kin bar gidana ba. Mussaman duba da yadda kika ce ba kya sona na shiga damuwa sosai, sai gashi cikin iko na Ubangiji Allah ya mallaka mini ke".

Fadila ta yi murmushi ta ce "Hmmm, Duk da tarin samarina ciki har da wanda Yusra zata aura yanzu, babu wanda ya taɓa burgeni, kowa sai in ga yana da irin tasa matsalar da ba zan iya son shi ba, ko bai kai matsayin da zai iya aurena ba.
Ka san bayan dariyar da nake yi maka na rashin iya turanci, lokaci guda ka kwance mini lissafi lokacin da na je masallacin juma'a, na ji kana huɗuba da larabci, yadda ka ke yi mini larabci, da yadda kake iya kwafar handwriting ɗina ya sanya ka fara burgeni. Lokaci guda sai na dinga mafarkinka, har da rana fa, ga abubuwan ban mamaki da kake yi ciki har da signing ɗina, da kuma yadda jikina yake yin rawa idan ka zauna a kusa da ni, ni fa har na fara tunanin ko ba mutum bane ba kai, ni dan Allah me kayi mini ne?"

Yazid ya yi murmushi ya ce "Ni ba abin da na yi miki, kwarjini kawai nake yi miki. Tun a lokacin nan da na kamu da sonki, na kasa jurewa na gaya miki, amma ki ka ce ba kya so na, sai da na yi kuka.
Ni a rayuwata harkar karatuna na sanya a gaba, lokaci guda ina ganinki na ji wata irin soyayyarki mai ƙarfi ta kamani, amma kika ce ba kya sona, ranar da na dawo gida a ɗaki na wuni, kamar ƙaramin yaro haka na kasa cin Abinci, sai da na zubar da hawaye sosai".

Tashi zaune Fadila ta yi, ta tallafo fuskar sa tana kallonsa ta ce "Allah sarki My Zid, am very sorry sweetheart, tun muna school na fara sonka, sai dai a lokacin ni ɗin sai a hankali, na fara tunanin yadda zan shiga rayuwarka na taimaka maka, ba yadda na iya Mummy ta kawo wani wanda take son na aura. Komai dai ya riga ya wuce tun da gashi Allah ya ƙaddara aurena da kai"

Shima ya shafi gefen fuskarta ya ce "Haka ne, Allah mai kyauta da ƙari, ya bani ke a lokacin da ban zata ba, kuma ga Baby zai bani, fatana Allah ya sauke ki lafiya"

Fadila ta kalli cikin nata sannan ta kalli Yazid ta ce "Zid wai ya sunan Inna na gaskiya?"

Yazid ya ce "Sunanta Khadija".

"Allah ya bani 'ya mace na saka mata sunan Inna"

"Da gaske idan Allah ya sa kika haifi mace, sunan Innata zaki saka mata?"

Fadila ta ce "In sha Allah, idan har macece sunan Inna zata ci, ban taɓa ganinta ba amma na ji a raina ina ƙaunarta"

"Allah sarki my wife, ina godiya da wannan karamci na ki"

Ta yi murmushi ta ce "A wurinka na koya ai in dai karamci ne"

Suka cigaba da hira suna tsara yadda tafiyarsu za ta kasance.



Kasancewar yau Daddy yana ɓangaren Hajiya Zainab, ya sha mamakin yadda ya ga tana ta wani nan nan da shi, dai lallaɓa shi take yi, ƙarewa yau da kanta ta kai masa kanta.
Abin ya bashi mamakin yadda ya ga tayi ladab, sai dai ya san banza ba ta kai zomo kasuwa, ba a banza take ta masa wannan ladabin ba dan ya san halinta sarai.

Ya dubeta ya ce "Mhmmm wannan ladabin fa? Na san da wata a ƙasa".

Ta dube shi ita ma ta ce "Haka ma zaka ce, shikenan na ji na kuma yarda, dan Allah Ahmad ba dan ni ba ba kuma dan halina ba, ka dawo mini da 'ya ta dan girman Allah, ko tausayina ba ka ji ne?"

Yayi murmushi ya ce "Kin fasa kaini ƙarar kenan?"

"Dan Allah ka bar wannan maganar, na yi ta ne cikin fushi, kuma ko ƙarar taka na kai na san ni ce a ƙasa, dan girman Allah ka dawo mini da 'ya ta"

Daddy ya ɗan gyara kwanciyarsa sannan ya ce "Ki daina zancen fa na dawo miki da 'yar ki, na gaya miki aurar da ita na yi ai, sai dai ta zo ta koma, shima sai da izinin mijinta dan ba zan goyi bayan ta dinga aikata abin da kike yi ba"

"Wai da Allah da gaske aurar da Fadila ka yi? Ahmad yanzu ƙiyayyar da kake yi mana har ta kai ga haka, wane irin aure ne haka kamar auren tsuntsuwa? Shikenan tunda ka auri yarinyar nan ka mayar da ni wata mara amfani ni da yarana? Wannan ai kamar ka wulaƙanta 'yar ka ne da nuna cewa bata da kima da daraja ga wanda ka bawa airen nata".

Daddy ya ce "Ban bayar da aurenta ga mutumin banza ba, kuma 'yar da ta fi kowace 'ya gata ma, 'yar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ba ayi mata abin da kike burin sai kin yi a auren taki 'yar ba".

A hasale ta ce "Amma ai ka kashe kuɗi ka yiwa Yarinyar da ka aura, saboda ita ce 'ya Fadila kuma ba 'ya bace ba ko?Tun da ta zo gaba ɗaya ta tarwatsa mini gida"

"Amina walimar kammala karatunta kawai na yi mata, kuma ita ma Fadilan da tabi umarnina, ta fito da miji a lokacin da na bata da haka ba ta faru ba"

Fashewa ta yi da kuka cikin sheshsheƙa ta ce "Ahmad ba ka san me nake ji a zuciyata ba ko? Wallahi muddin wani ciwon ya kamani ko na mutu kaine sila, ko baccin kirki bana iya yi, ban san a in da 'ya ta take kwana take tashi ba, ba ka tausayin halin da nake ciki, mun doshi wata na huɗu ban san in da 'ya ta take ba, ba ka yi mini adalci ba"
Tausayinta ne ya kama shi, sai dai wasu lokutan ita ɗin ba abin tausayi ba ce ba sam, saboda halinta.

Daddy ya ce "Shikenan, zan kawo miki Fadila ki ganta, amma ba zan gaya miki takamaiman lokaci ba, idan har na kawota ba kya nan kin tafi yawonki, shikenan kin yiwa kanki zata koma gidanta ne"

Jinjina kai ta yi cikin amincewa, tana goge hawaye.



****
Yazid kuwa sun gama shirinsu tsaf, shi da Fadila suka tafi gidan Hajiya, domin tare da ita za su tafi Jalingo.
Suna zuwa suka tarar da ita ta gama girki tana kwashe abinci.
Yazid ya ce "Hajiya girki kuma kike yi?"

Hajiya ta ce "Eh na yi mana girki ne, saboda kar mu rasa abin da zamu ci a hanya, kuma ga mai juna biyu".

Yazid ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.

Hajiya ta fito da tukunyar Abincin a hannunta zata kankare ta wanke tukunyar, dan bata son ta tafi ta bar datti a gidan.

Hajiya na shirin zuba ruwa a kan ƙanzon, Fadila ta yi sauri ta ce "Hajiya dan Allah kar ki zuba ruwa a ƙanzon ina so"

Hajiya ta ce "Me zaki da shi?"

"Hajiya so nake, sha'awa ya bani zan ci"

Yazid ya kalleta ya ce "Ci kuma, ƙanzon?"

Ta ce "Eh ɗin ina ruwanka"

Yazid ya ce "Wai ban gane ƙanzo ba, idan yunwa kike ji, a zubo miki Abinci mana"

Fadila ta tura baki ta ce "Ni ba abinci zan ci ba, ƙanzon nake so"

Hajiya ta yi murmushi ta ce "Ai ciki ba abin da ba ya sawa, a me zan zuba miki ƙanzon"

Fadila ta yi murmushi ta ce "A zuba mini a leda, sai a zuba mini yaji a kai, mu tafi da shi"

Yazid ya buɗe baki ya ce "Wai hanya zamu tafi kina cin ƙanzo Fadila?"

Fadila ta ce "Ba fa a hanya zan ci ba, sai mun hau mota".

Hajiya kuwa ta biyewa Fadila, ta kankarewa Fadila ƙanzon nan tas, ta zuba mata a wani ɗan fulas mai murfi, ta zuba mata mai da yaji, Fadila sai haɗiye yawu take tana murna wai ƙanzo da mai da yaji.
Yazid kuwa sai bin ta yake da kallo, tausayi ma gaba ɗaya take ba shi, lallai mata na shan wahala, amma banda lamarin ciki, me mutum zai yi da ƙanzo?.


Ƙarfe goma na safe suka ɗau hanyar Jalingo, suna tafe a hanya Fadila rungume da fulas ɗin ta na ƙanzo a hijjabi, suna tafe sai ta shige hijjabi ta ci ƙanzonta ta fito.
Tun ana tafiyar nan ta marmari,har Fadila ta gaji, gaba ɗaya jikinta ko ina ya yi mata tsami, tun tana ɓata rai har ta fara share hawaye a wayance. Ganin Hajiya ta yi bacci ne ya sanya Yazid ya riƙe hannun Fadila, murya ƙasa-ƙasa ya ce mata "Kiyi haƙuri kin ji, mun kusa ƙarasawa in sha Allah, da ina da kuɗin jirgi da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login