Showing 246001 words to 249000 words out of 296192 words

Chapter 83 - GABA DA GABANTA

tayi ta kira Alhaji Ahmad, yana ɗagawa cikin fushi ta fara tambayarsa ya taji haryanzu shiru.

Daddy ya ce "Ai nace ki kwantar da hankalinki, tana hannu na gari, Fadila bata Dutse, babu wani abin ƙi da zai sameta kiyi haƙuri ni Yanzu haka ina Lagos ma!!!




Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YA TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA.



75

Wani uban zagi Hajiya Zainab ta maka, amma Daddy ya katse kiran ya ƙyaleta.
"Ni zaka ciwa mutunci, wallahi baka isa ba, wato ka ajiyeni ka mayar da ni hoto banza, ina jiran ka kawo mini 'ya ta, amma ka zaunar da ni ka ɗau wannan yarinyar mai kama da karuwai ka tafi da ita, to wallahi baka isa ba". Haka ta cigaba da masifa ita kaɗai tana bambami.


Yazid kuwa da ƙyar ya lallaɓa Fadila ta ci abinci.
Yazid ya kalleta cikin kulawa ya ce "Fadila yakamata na dafa miki ruwa kiyi wanka, mu kuma zaga ki ga gidan naki".

Fadila ta yamutsa fuska ta ce "Ina ne gidan, wannan ne gidan? Wannan ai bai yi kama da gida ba".

Yazid ya ce "Na ji, amma ki daure ki shiga kiyi wanka ki sauya kayan jikinki" sake takurewa tayi a wuri ɗaya taƙi kallon Yazid.

Tana kallonsa ya kwashi akwatunanta, ya kai cikin bedroom ɗin, ya shirya mata kayanta a sip guda ɗaya, ɗaya kuma nasa ne.

Ya dawo falon ya wuceta, ya shiga ɗan ƙaramin Kitchen da yake tsakar gidan, ya kunna risho ya ɗora ruwan zafi.

Mintuna kaɗan, ruwan yayi zafi, ya juye a bokiti ya sirka, ya dawo ya ce "Dan Allah ki zo ki watsa ruwan kya ji daɗin jikinki" gaskiyar Yazid, tana buƙatar ta watsa ruwa dan gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, dan ko a gida Fadila gwanar wanka ce.

Banɗakin da ke tsakar gidan ya kai mata ruwan, ta tarar da banɗakin wani ɗan tsukakke da shi, a ƙuntace ga kan fanfo sai masai pit latrine.
Wasu hawayen takaici ne suka zubowa Fadila, ta kalli in da sabon kwandon wanka yake, da soso da kuma sabulu.
Haka ta durƙusa tayi wanka, ta zuro kayanta ta fito.
Ko da ta fito, Yazid baya nan ya fita, ta shiga bedroom ɗin, ta ƙarewa ɗakin kallo, ƙatuwar katifa ce a ɗakin, sai sip da mudubi, sai wata cupboard ɗauke da uban litattafai na addini da na zamani kamar Library a ɗakin.

Taɓe baki tayi, ta buɗe akwatinta, bata ɗauko mayukanta na shafawa ba a ciki. Tsaki tayi, ta tashi ta duba kan madubin ta ga Vaseline, gaba ɗaya warin vaseline ɗin bai yi mata ba, haka ta daure ta shafa.

Ta duba ta ɗauki wata 'yar riga me sauƙin nauyi, ta saka ta koma ta nemi wuri ta yi shiru tana tunanin yadda aka yi Yazid ya aureta, da yadda Daddy yayi mata wannan irin maƙasƙancin auren haka.
Ta saka hijjabi, tayi sallar azahar, ta idar ta cire hijjabin ta zauna, ta tsunduma duniyar tunani.
Sallamar da Yazid yake yi ne ta dawo da ita hayyacinta, ya shigo falon riƙe da ledoji a hannunsa.
Kallo ɗaya tayi masa, ta ɗauke kanta zuwa wani wurin daban.

Ya shiga Kitchen ya ɗauko plate, ya zazzage mata wata lafiyayyiyar shinkafa da naman kaza. Ya saka mata cokali ya ce "Ga Abinci"

"Ni fa ba abincinka nake buƙata ba, ka mayar da ni gidanmu na gaya maka".

"Fadila, furucin mahaifinki abu ne mai girma, wanda zai iya yin tasiri a rayuwarki, kiyi haƙuri idan komai ya lafa zan mayar da ke gida da kaina kin ji ki ci Abincinki"

"To yaushe zaka mayar da ni?"

Yazid ya ce "Da zarar komai ya lafa zan mayar da ke in Sha Allah, amma ranar Monday zamu koma school ko?"

Ta kalleshi ta ce "Ni da makarantar nan har abada"

"Saboda me?"

"Ba zan sake zuwa ba, na gama makaranta"

Ya kuma kwantar da murya ya ce "Haba Fadila kin zaɓi kiyi asarar shekarunki da kika fara na karatu?"

"To ina ruwanka? Kai kayi asarar su ko ni?"

Yayi murmushi ya ce "A'a, ga Abincin".

Ba kunya ta karɓe masa Abinci ta fara ci, gefe ya koma shi ma ya fito da ɗan ƙaramin fulask, ya zuba kunu a kofi yayi Bismillah ya fara sha.

Bata ci da yawa ba ta ajiye, ta ɗan tsurawa Yazid ido sannan ta ce "Dan Allah meyasa ka aureni, bayan ka son bana sonka?"

Murmushi yayi ya ce "Ikon Allah mana, kina mamaki ko? Nima haka nayi mamakin yadda abin ya kasance, amma ki Kwantar da hankalinki dan Allah".

"Ba zan kwantar ba" tayi maganar tana hararsa.

Haka suka wuni kamar kurame, Babban abin da ya bashi mamaki yadda bata cigaba da yi masa tijara ba, sai tsiwa da hararsa da take ta yi, haka kurum yake yi mata kwarjini, ta kasa cigaba da yi masa rashin mutuncikHausawa suka ce, ba faɗa da malam ba daren) ko da yake ba abin mamaki bane ba, dan Yazid sosai ya duƙufa yake addu'a a kan zaman nasu tare da fatan Allah ya sa ta dangana ta zauna dashi. idan ta ɓangare guda Fadila ta tuna maganar Daddy sai gabanta ya faɗi. Tunani ta shiga yi ko a wane hali Mummy ke ciki yanzu oho.
Jikinta yayi sanyi, hawaye ya shiga zubo mata.
Cikin kulawa Yazid ya ce "Dan Allah ki daina wannan kukan zuciyata bata so?"
Da ɗan ƙarfi ta ce "Kar ta so ɗin, da baka son kukana ai da baka aureni ba".
Bai kuma tanka mata ba har zuwa dare, ya kawo mata abinci daga gidan Hajiyarsa. Nan ma ta ci abin ta, tayi sallar isha'i ta nemi wuri a falo ta kwanta.

Yazid ya shigo ya kalleta ya ce "Ki shiga ki kwanta, nan akwai sauro sosai" bata ce masa uffan ba, ta tashi ta shiga bedroom ɗin. Kasancewar tana jin bacci sosai, ta kwanta a kan katifar.
Can cikin bacci ta waiwaya, taga Yazid yana rage kayan jikinsa, rintse idanunta tayi tana tunanin ko mafarki take yi.
Amma ta sake buɗe idonta, taga ya hau kan katifar. Zumbur ta tashi zaune ta ce 'Meye haka?" Yazid ya kalleta ya ce "A ina?".

"A ina zaka kwanta?"

Yazid ya ce "A kan katifa mana"

"Gaskiya ba zan kwana wuri ɗaya da kai ba, ni ban taɓa kwana da wani ƙato a kan shimfiɗa ɗaya ba, kawai ka tashi"

Yayi murmushi ya ce "To a ina zan kwanta?".

"Ka koma ƙasa ka kwanta"

Ba musu ya tashi ya ɗau pillow ya kwanta a ƙasa.
Hakan ya sa ta ɗan sake, ta kwanta bacci mai nauyi ya ɗauketa.

Idon Yazid biyu, yaji saukar numfashin Fadila alamun tayi bacci, ya tashi tsam ya koma kan katifar ya kwanta a bayanta, ya janyota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, ya saka hanunsa a saitin zuciyarta, ya dinga karanto Alqur'ani yana addu'ar ubangiji Allah ya bata juriya da dangana, dan shi kansa ya san wannan auren na su jarabta ce a gareta, dan bashi da ƙarfin iya aurenta.
Ita kuwa jinta a jikin mutum ta zata mafarki take, ta ƙara sakankancewa.




Khalil ya shirya, ya zo gida domin gaida Mummy, dan ko ba komai mahaifiyarsa ce.
Sai dai ko da yaje, ya tarar da ita bata duk tayi wani iri.
Bai samu wata kyakkyawar tarba ba, amma duk da haka bai hana shi cewa "Mummy lafiya kuwa? Meke damunki ne na ganki wani iri?"

Mummy duk da a ƙule take da shi, amma ta ce "Ba dole ka ganni a haka ba, kai da ubanka kun haɗa kai kuna yinƙurin ku kasheni, ya ɗauke Fadila ya kaita wani wurin daban sani ba, ya gaya mini Dutse ya kai ta zai ɗaukota, amma tsabar wulaƙanci wai na kira shi a waya, yace mini wai yana Lagos" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.
Cikin damuwa Khalil ya ce "Mummy dan Allah kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ki bi komai a sannu ki daina ɗaga hankalinki, Fadila Daddy ne ya haifeta ba zai cutar da ita ba".

Cikin fushi ta dakatar da shi ta hanyar cewa "Kai dalla can rufe mini baki, dama ai kai goyon bayansa dama kake yi, domin kai ma ya tsaya maka ka auri 'yar matsiyata, dole ka goyi bayansa a kan dukkan abin da yake aikatawa, ka kyauta tashi ka bani wuri" Haka Khalil ya tashi ya fita.


Zakiru da Hajara kuwa, jin ance za a biya musu umara da Khalil ya sanar musu a zuwansa gidan, suka dinga murna suna jin daɗi, Khalil ya gaya musu Amina ce ta saka a biya musu.
Suka dinga murna suna saka wa Amina da iyayenta albarka.
Khalil tare da Hafsa suka je Jigawa, suma suka je suka sanar musu yadda aka biya wa wasu umara, har da ƙanin mahaifin Hajiya Zainab.
Nan da nan labari ya karaɗe dangi, dan Alhaji Ahmad bai taɓa yi musu alkhairi makamancin haka a rayuwarsu ba.


Yazid dai kusan kwanaki biyu suna fafatawa da Fadila, kan ya samu ta ɗan kwantar da hankalinta, dan har hirar arziƙi ta kan shiga tsakanin su, ko da kuwa ba zata amsa masa ba.

Yau da safe ya dafa musu tea, ya zo da kayan tea, har da ƙwai.
Ya zuzzuba musu ya miƙa mata nata, ta saka hannu ta ɗauka ta karya.
Fadila bata aikin komai a gidan nan, Yazid ne yake zagewa yayi komai, daga shara wanke wanke gyaran toilet duk shi ne yake yi, hatta kayan jikinta idan ta cire shi ne yake haɗawa ya wanke, ba abinda ta sani sai dai ta ci ta ƙoshi ta saka shi a gaba tana koke-koke.

Ga Yazid yana ta ƙoƙarin sayen duk abincin da ya san zata iya ci.
Yanzu ma kukan take yi, tana zaune a kan kujera sai aikin kuka take yi.
Yazid ya ƙarasa kan kujerar da take zaue ya zauna a kusa da ita. Tun da Daddy ya kawota gidan nan, wannan ne karon farko da Yazid ya zauna a kusa da ita a ido biyu.
Jikinta ne ya ɗau rawa, kamar yadda take yi a baya, idan ya zauna a kusa da ita a school.

Haɗe rai tayi ta ce "Dan Allah ka tashi daga kusa da ni"

Yazid ya ce "Meyasa? Ya naga jikinki yana rawa?"

A fusace ta ce "Idan ba zaka tashi ba, matsa ni na tashi".

Yazid ya sake matsawa kusa da ita ya ce "Jikinki da nawa ne, tamkar ƙarfe ne da kuma mayen ƙarfe, jikinki tamkar mayen ƙarfe yake, a duk lokacin da na kasance a kusa da ke, sai jikinki ya fara rawa, kina buƙatar nawa jikin a matsayin ƙarfe, kamar dai haka" ya janyota jikinsa. Aikuwa take jikinta ya daina rawar, sai dai kuma bugun zuciyarta da ya ƙaru, har numfashinta ya fara yin sama.
Kasa motsawa tayi, sai shiru da tayi tana kokawa da numfashi.
A hankali ya kama gashin kanta da tayi parking ɗin sa.
Jin Yazid na neman wuce makaɗi da rawa, kuma gashi ta kasa hana shi, kamar yadda ta taɓa gani a mafarki yau a zahiri hake faruwa, bakin Yazid ne a cikin nata. lokaci ɗaya tayi wata irin zabura ta rabu da jikinsa, ta haɗe rai ta fice tsakar gida ta tafi bakin rariya, tana zubar da miyan bakinta tana tsaki. Ɗan kashingiɗa yayi yana murmushi. Yayi shiru yana tuna farkon ganinsa da ita, zuwa yau da Allah ya sanya cikin ikonsa ta zama matarsa.


Ranar da ya fara shiga ajinsu a jami'a, kansa a ƙasa, ya shawo uwar tafiya mai nisa da ƙafarsa, saboda rashin wadataccen kuɗin mota a hannunsa. Yana shiga aji mutum na farko da ya fara sanya idonsa a cikin nasa ita ce Fadila.
Ras! Gabansa ya faɗi, ta ƙare masa kallo ta fashe da dariya, amma hakan bai hana shi ganinta ɗauke da wani kyawu na musamman ba, da tun da yake bai taɓa kallon wata mace har ta burgsehi ba, sabgogin gabansa ne suka dame shi.
A haka yayi ta'awizzi ya nemi tsari daga sheɗan, amma kamar wasa ƙaramar magana ta nemi komawa Babba, har Alla-Alla yake garin Allah ya waye ya je makaranta dan ya ga Fadila.
Komai nata burgsehi yake yi, duk da kasancewarta 'yar wulaƙanci ga izza da girman kai, amma zuciyarsa bata fasa begen Fadila ba. A haka har yayi ta maza ya fara kulata. Duk da da fari bata saurarsa sai wulaƙanci, amma bai gaza ba har zuwa ranar da rashin lafiya ta same shi ta kai shi Asibiti, ji yayi tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan farinciki.
Daga lokacin da suka samu saɓani kuwa, ta ce ita ba kalarsa bace, a 'yan kwanakin nan ko Abinci baya iya ci, har Hajiya sai da ta gane, ta saka shi a gaba da tambaya amma ya ce mata bakomai.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, tare da ƙalubale kala-kala, amma kullum sake jinta yake yi a ransa.
Hakan ya sa ya duƙufa da Addu'a, ya san shi ba ɗan kowa bane ba, kuma ba shi da shi. Sai dai yana Addu'a Allah ya cire masa son Fadila a ransa, amma kullum ƙara sonta yake yi.

Ranar da Yazid ya kai Fadila gida, Amina ta ganshi sai ta ga yayi mata kama da mutane nagari, duk da kayan jikinsa sun nuna waye shi, amma a nutse yake sosai.
Kasancewar Amina ta kan ji Fadila na bawa Mummy labarinsa, kuma ba zata manta ranar da taje ɗakin Fadila ta tarar da ita tana surutan bacci tana kiran sunan Yazid ba, da yadda Fadila ta tayar da jijiyoyin wuyanta a kan Yazid lokacin da ya samu matsala a makaranta.
Amina ta gane Yazid yana son Fadila ne, amma Fadilan tana ganin ita ba ajinsa ba ce, amma ko a zahiri sai Amina taga sun dace da aure, duk da Yazid yayi kalar haƙuri, amma Fadila na buƙatar jajirtaccen miji mai ilimin addini, idan ba haka ba duk wanda ta aura zai sha wahala ne kawai, saboda gaba ɗaya bata samu kyakkyawar tarbiyya ba, sai dai duk wannan tunanin na Amina ta san ba mai yiwuwa bane ba, kasancewar an riga an kawo wa Fadilan kuɗi. Amma zuciyarta ta cigaba da raya mata Yazid ya dace da auren Fadila, haka na sai ta tsinci kanta da yi musu Addu'a.
Bayan Daddy ya dawo ne, ya ci Abinci ya nutsu, Amina ta sako masa maganar Yazid ta kalli Daddy ta ce "Baby na yi maka laifi fa".

Yayi murmushi ya ce "Ai ba kya laifi beutyna, meyafaru?"

"Na buɗe ma'ajiyarka na ɗauki shaddoji masu kyau biyu, da kuɗi dubu ashirin nayi kyautarsu wa sirikinka"

Ya ce "Duk yadda kika yi daidai ne, ai kayana naki ne, amma wane sirikin nawa kenan?"
Amina tayi murmushi tare da gyara zama ta ce "Ina wanda Fadila ta kiraka a waya muna Abuja a kansa, ana shirin ɓata masa jarrabawa wani Yazid?"

Ya ce "Ok na tuna"

"To ai shine ya kawota"

Dasu ya ce "Allah sarki, to babu laifi".

"Hmmm ka san wani abu kuwa?"

Daddy ya kalleta ya ce "Sai kin faɗa".

"Shifa son Fadila yake yi, wasu lokutan na kan ji tana bawa mamanta labarinsa, yana da ilimin addini sosai da sosai, kuma kasan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce idan ɗayanku ya zo neman auren 'ya'yanku, idan har kun yarda da addininsa ku aura masa"

"Haka ne malamata, amma ita Fadila ai sun kawo wanda suke so ta aura"

Amina ta ce 'Mmm haka ne, amma ka san wanda suke so ta aura ɗin basu taɓa ganinsa ba fa, ina mata sha'awar nagartaccen mutum wanda yake sonta sosai, ba kowa zai iya jure halinta ba, am sorry to say ba ina son muzanta maka 'ya bane ba, amma gaskiya Fadila tana buƙatar auren miji mai sonta sosai mai ilimi da zai iya haƙuri da ita".

Daddy ya ce "Maganarki na kam hanya Meenal, amma yanzu muddin na tsiro wannan zancen ba zamu wanyeta ƙalau da mahaifiyarta ba, tunda sun kawo wanda suke so shikenan, duk abin da ya biyo baya ba ruwana"

"A'a Daddy, ita matsala kan ta faru ake maganinta, komai ya biyo baya da ruwanka, ai alhakin sama mata miji nagari a wuyanka yake, ba wuyan babarta ba, yakamata a duba sama mata miji nagari, ba kuma lallai ne dan kana mai kuɗi, sai ita ma ta samu mai kuɗi ba, ita rayuwa babu yadda bata juyawa"

Daddy ya jinjina kai alamaraa gamsuwa, suka shiga wata hirar.
Tun daga ranar Amina ke cigaba da kwaɗaitawa Daddy aurar da Fadila ga mutumin ƙwarai, saboda tana taisayin irin rayuwar da mahaifiyarsu ta ɗora su a kai, muddin ta je gidan wani musamman mutum mara cikakken ilimk da nutsuwa da Wannan halin, to za tayi ta aure ana sakinta ne.
Shi kansa Khalil albarkacin auren Hafsa, ya sanya ya fara sauyawa sosai da sosai, duk da ita kanta ba mai son mutane bace ba, amma tana ta nuna masa muhimmancin girmama mutane.

Daddy ya fara yadda da maganar Amina, tun bayan yadda Hajiya Zainab ke wulaƙanta shi da cin zarafinsa ko a gaban uban waye.
Amina ta kan ce masa "Kaga yadda Hajiya Zainab ke yi maka, Fadla ma haka zata je tana yi a gidan miji, tunda haka ta tashi ta ga ana yi a gidansu, kuma ka san ba kowane namiji ne zai ɗauka ba"

Amina bata gaza ba tana roƙawa Fadila, ya bata miji wanda yafi alkhairi da zai zauna da ita saboda Allah yayi haƙuri da hakayenta na banza, amma ita tana fatan ta auri Yazid. Ana haka har kawo rashin lafiya da Fadila tayi, Yazid yake ta zarya a kanta.
Zuwa ranar da Daddy ya haɗu da Yazid, Hajiya Zainab tana korarsa, sunansa da Amina ta kira ya sanya Daddy gane shi ne.
Dan haka ya sa Amina ta wuce ta duba Fadila, shi kuma yabi Yazid waje.

Yazid yayi mamaki da ya tsayar da shi, Daddy ya dube shi ya ce "Yazid mun gode sosai da kulawarka a kan 'ya ta, kayi haƙuri da abin da mahaifiyarta tayi maka"
Yazid yayi murmushi ya ce "Bakomai Daddy, ni nayi laifi ma, na shiga matsala a makaranta, Fadila ta kiraka ka warware mini, na so na zo har gida nayi maka godiya amma Fadila ta ce mini ba ka gari"

Daddy ya ce 'Wannan ai ba wani abu bane ba, kai ma ɗana ne, bari na baka kuɗin mota" Yazid ya girgiza kai ya ce "A'a ai ina da kuɗin mota Daddy"

Daddy ya matsa kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa ya zura masa kuɗi a aljihunsa ya ce "Ba a mayar mini da kyauta, na ji irin ɗawainiyar da kake da Fadila na gode sosai ka gaida gida"

Bayan Daddy ya koma, a sashin Fadila, yaji yadda take zagin Amina, bayan sun koma sashin Amina ya gama bata haƙuri yake ce mata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login