Showing 66001 words to 69000 words out of 296192 words

Chapter 23 - GABA DA GABANTA

irin turare mai ƙamshin gaske, ta shafawa Amina ita ma ta shafa.
Suna fita falo Ammi ta rungume Amina, "Kai Masha Allah da wannan kyakykyawar yarinya, bani wayata in mata hoto"

Amina har mamakin karamcin Maman Azima take yi, ita babu ruwanta kamar ba mai kuɗi ba, 'to kenan masu kuɗin ba kowane me irin halin su Hajiya Zainab ba?'

Da zasu tafi har harabar gidan Ammi ta rakosu, ta cewa direba "Ga su nan ka kula mini da su, ka kai su wurin walimar saukar, kar a bari magariba tayi, duk in da suka yi awa ɗaya da rabi, kai mayar da Amina gida, ga kaya nan na bata, ga wasu a ledar nan, ka yiwa Abbanta bayanin ni na bata, sai ku taho kai da Azima".

Amina tai ta yiwa Ammi godiya, tayi mamakin tsananin karamcinta, sam ba ruwanta da wata ɗagawa.

Haka kuwa aka yi, suka fara zuwa wurin sauka, aka yi walimar sauka a cikin ƙawayensu, Amina taji daɗin wannan fitar sosai da sosai.

Kamar  yadda Ammi tayi umarni, har gida aka mayar da Amina, direba ya yiwa Baba bayani kamar yadda Ammi ta umarce shi.
Bayan tafiyar su Azima, sai da Baba yaita yiwa Amina nasiha tare da gargaɗinta a kan ta iya talaucinta.

Khalil da ke zaune a mota yana shirin fita, ya zubawa Amina ido, bai taɓa ganinta ba hijjabi ba sai yau, rigar kamar da jikinta aka auna aka yi ta, saboda yadda ta zauna cif a jikinta, yana cikin motar ta zo ta wuce cikin gidan, hannunta riƙe da wata babbar leda.
Ajiyar zuciya ya yi, ya kunna motar ya bar gidan.

Amina a falo ta zauna, ta buɗe robar gugguru ta fara ci, ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ne ya fara cika wurin kan ya bayyana, ya turo ƙofar falon da sallama, Amina ta amsa  ƙasa ƙasa.
Duba falon yake yana son gane daga ina yake jin tashin ƙamshin wani turare na musamman. Har ya zo zai gifta kunnuwansa suka jiyo masa muryarta "Daddy sannu da zuwa" kallon in da Amina take yayi, sai dai ba shi tabbacin ko Aminan ce, saboda yadda ta ke haɗe cikin riga mai kyau, kuma shi da hasali ma yarinyar sai ta ga dama take gaishe shi, dan haka kawai ya wuce bai amsa ba.
  Amina ta gama ciye-ciyenta, sannan ta tashi da nufin ta je wurin Hajiya Zainab, ko da aikin da zata yi mata, saboda tana son ta shiga ɗakinta tayi rubutunta na Alqur'ani, wanda idan tana yi, bata buƙatar takura.
Kanta a ƙasa tana sauri, suka yi karo da Alhaji Ahmad dake ƙoƙarin fitowa daga sashin Mummy. Amina ta firgita sosai ɗan ƙaramin mayafin kanta ya sauka, tarin gshinta ya bayyana.
Ganin ya zuba mata ido ya sanya ita ma ta ɗan tsare shi da nata idanuwan, tana ƙoƙarin gyara mayafinta.
"Ba kya gani ne?" Ya furta yana kuma tsareta da ido.

"Yi haƙuri ban san ka taho bane" guntun tsaki ya ja, ya raɓa gefenta ya wuce. Amina ta taɓe baki ta ƙarasa ciki.

Bayan sallar isha'i, Khalil ya koma gidan su Hafsa, 'yan kwanakin nan ya sarƙi zuwa gidan, Jikin Mama yayi sauƙi sosai, Khalil ya ji daɗin yadda ya ganta, suka taɓa hira tare da sake yi mata sannu.
Yau ma bai kula Hafsa ba bata kula shi ba, sai da zai tafi Mama ta ce Hafsa ta raka shi.
Ba ta son yiwa Mama gardama, ta rako shi har gaban mota, ba tare da ta ce masa uffan ba, suna zuwa bakin motarsa ta juya zata koma gida abinta, cikin zafin nama Khalil ya riƙo hannunta, ya buɗe motar sa ya sakata a ciki, ya rufe ƙofar, ya zaga ɗaya site ɗin ya shiga.

"Meye haka? Dan Allah ka buɗe mini in fita, sai kasa mutanen unguwa sun mini wani sharrin?"

"Idan sun miki sai me? Ke da mijinki ne ai ko? Hafsa meyasa kike mini haka ne, kin fi son in ta wahala ko baki damu da ni ba?".

Ta tura baki ta ce "Eh ai nima baka damu da ni ba, da na dinga kiranka ka ƙi ɗauka"

"Ba dole in ƙi ɗauka ba, Hafsa komai na baki ba zaki karɓa ba, sai kin yi mita da ƙorafi bana son abin da kike mini bana jin daɗi" ya ƙarasa maganar cikin marairaicewa.

Cikin shagwaɓa ta ce "To Shine sai ka daina kirana, kuma daina ɗaga nawa, dan ka sani damuwa"

"Dagaske kin damu kema da bama waya?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Kina sona kenan?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa.

Shiru ta ɗan yi, sannan ta kalleshi ta ce "Kana sona da gaske?"

"Ina sonki mana"

"Bari in fara gaya maka waceceni, da ƙaddarar da ta sameni, ban sani ba ko zaka iya cigaba da sona a haka".

Hafsat Usman Dikko, shi ne cikakken sunan Hafsa, mahaifinta haifaffen garin Kano ne, mahaifiyarta ma haka.
Mahaifin Hafsa shikaɗai mahaifiyarsa ta haifa a gidansu ta rasu wurin haihuwa, ya taso a tsakiyar 'yan uba, cikin tsangwama da kyara.
A haka a wahale yayi karatun Addini da na zamani, kasancewar Usman mutumin kirki, mai ladabi ga kowa da kowa ya sanya 'yan unguwarsu kowa yana son sa.
Ya haɗu da mahaifiyar Hafsa, mai suna Safiyya, a nan wani filin ƙwallo da yake zuwa, a nan cikin unguwar gwale. Sai dai itama basu da ƙarfi, dan marainiya ce, yayanta ne yake ɗawainiya da su.
A lokacin da  Usman ya auri Safiyya, ba shi da wata tsayayyiyar sana'a, sai dai mutum ne mai zuciyar nema, sai dai yana da kwalin degree har biyu amma babu aikin yi, gidan da suka tare ma a ciki, gadonsa ne na mahifiyarsa a nan cikin unguwar ɗorayi, wani ɗan ƙaramin gida, haka suke rayuwa.
Kwatsam, Chairman ɗin unguwarsu tsohon abokin mahaifin su Usman ne kan ya rasu, ya bawa Usman offer, a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa.
Yayi murna ba kaɗan ba, a lokacin 'yan uba suka sake sako shi a gaba, da sharri da jafa'i kala kala dan su cikinsu babu wanda ya yi karatun boko sai shk. Lokaci ɗaya Allah ya ɗaukaka shi a kan harkar aiki, ya mallaki gida da abin hawa, ya mallaki shaguna a nan cikin umgu su, wasu ya bada haya wasu ya zuba kasuwanci ya janyo 'ya'yan 'yan uwansa, amma suka dinga cutarsa. Amma duk da haka Allah bai sa yayi baya ba, kullum gaba yake yi, cikin ikon Allah a nasarorin da ya samu, har da karramawa daga fadar shugaban ƙasa, saboda gaskiyarsa da gudun rashawa.
Gidansa kullum cikin jama'a yake, masu neman taimako, hannunsa a sake yake hakan ya ƙara masa farinjini.
Kusan shekara biyar Safiyya na ɓari, bata haihu ba, sai da aka dage da addu'a da neman magani sannan Allah yasa ta samu cikin jikinta ya zauna, watanni tara Allah ya sa ta haihu, ta haifo ɗa namiji kyakywa mai kama da Usman sak, aka sha shagalin suna aka sanya masa suna Abubakar Sadik, sunan mahaifin Safiyya.
Sadik ya taso cikin gata da kulawa, shekararsa uku a duniya, dangin Usman suka dinga mita a kan Cewar ba a kai musu Sadik, a dinga kaishi saboda ya saba da 'yan uwansa. Ba dan Safiyya ta so ba, aka haɗa kayan Sadik, aka kaishi gidan wan Usman, mai suna Aminu, sai dai kwanan Sadik biyu aka dawo da shi wai bashi da lafiya, duk ya fita hayyacinsa, aka kaishi Asibiti aka yi gwaje-gwaje aka tabattar da wani abu yaci, kwana ɗaya ya rasu, daga Safiyya har Usman sun shiga tashin hankali na gaske, wanda a sanadiyar damuwa da rashin lafiya da Safiyya tai tayi, aka gano tana laulayin wani cikin, a haka ta haifo Hafsa. Lokacin da aka haifi Hafsa, Usman Arziƙi ya ninka na baya, Hafsa ta tashi cikin gata da kulawa. A can wurin aiki, abokan aiki suka sako Usman a gaba saboda cigaba da yake samu, mussaman ta fuskar tsayawa a kan gaskiya, a dangi kuma 'yan uba na ta son ganin bayansa, banda 'yan unguwa da tasu hassadar duk da tarin kyautatawarsa a gare su.
Bayan haihuwar Hafsa, Safiyya tayi ɓari yafi bakwai, wanda sai da likitoci suka bata shawarar, a ɗaure bakin mahaifarta ta haƙura da yinƙurin ɗaukar ciki saboda lafiyarta.
Kasancewar Hafsa ce 'ya ɗaya tilo a wurinsu ya sanya suka ɗora mata duk wata so da ƙauna, Safiyya take ta kulawa da ita, taƙi yarda ta saki jiki ta bawa su Aminu da iyalansu 'yarta.
Shekarar Hafsa goma sha ɗaya, aka yiwa Usman wani ƙarin girma, yaje Abuja aka yi walima, tun da ya dawo ya fara rashin lafiya, aka dinga yawon Asibiti amma babu wani cigaba ba a gano abinda ke damunsa ba, kullum ciwo gaba yake yi, wanda hakan ya yiwa 'yan uwansa daɗi, dan sam basu damu da halin da yake ciki ba, daga matarsa sai mahaifiyarta da wanta ne suke ta ɗawainiya da shi.
Shekara guda yana jinya, Allah ya karɓi abin sa, Safiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, tayi kuka kamar babu gobe, mutane aka cika gidan makoki dan an san za a ci a sha, tun kan a share sadakar uku, Aminu da 'yan uwansa Hadi da Ashiru suka fara maganar rabon gado, wani ɗan uwan mahaifinsu ya ce ai sa bari a rufa Arba'in.
Kwanaki Arba'in da ɗaya da rasuwar Usman, suka zo da wani mutum wai shine Alƙali zai yi rabon gado, gaba ɗaya sun sa ran dukiya ta su ce, saboda ba shi da ɗa namiji, Safiyya ta fito da wani rubutu da yayi kan ya rasu, yayi rubutu fiye da rabin dukiyarsa ya sakata a harkar cigaban Addini, manyan kadarorinsa kuwa duk ya saye su da sunan Hafsa, ya mallaka mata su, ɗan abin da ya bari babu yawa sam.
Nan fa suka ce basu yadda ba, ƙarya take ita ta rubuta, ganin suna neman su gwada mata fin ƙarfi, ya sanya ta garzaya kotu, Allah ya taimaketa Alƙali ya tabattar da wasiyyar da Usman ya bari.
Bayan Safiyya ta gama idda, ta dinga samun manema, amma ta ce ita ta gama aure a kan Usman, saboda ta san ba zata samu madadinsa ba.
Mahaifiyarta da ɗan uwanta suka dsge a kan dole tayi wani auren, wani mutum mai suna Musa, shi Safiyya ta tsayar, saboda yana da matuƙar kirki da halaye masu kyau kwatankwacin Usman.
Sai dai su Aminu yayyen Usman na jin batun za tayi aure, suka tada husuma, wai ba za tayi aure ta kai dukiyar marainiya wani wurin a cinye ba, ƙarshe ma suka ce sai dai ta basu Hafsa, ba zata yi agolanci a wani gidan ba, ko kuma ta auri Aminu. Da suka tada masifa da tashin hankali, mahaifiyar Safiyya ta ce tayi haƙuri ta auri Aminu, ko ba komai Hafsa ba zata tashi gidan wasu ba, ba dan Safiyya na so ba ta yiwa mamanta biyayya.
Bayan auren Safiyya da Aminu, yayanta shima ya rasu, ɓarayi suka tare shi a hanya, suka kashe shi, abubuwa suka sake yiwa Safiyya zafi, na rashin da tayi gaba da baya.
Bayan aurenta da Aminu, ya dinga basu kulawa da tattali, duk da a gefe guda iyalansa suna nuna musu tsantsar ƙiyayya da kyara.
A haka ya lallaɓa Safiyya, tayi musu gyaran gida, aka sai motoci biyu a gidan dan amfanin mazauna gidan. Ya dinga lallaɓata da kyautatawa da asiri, ya dinga karɓe dukiyar nan ɗaya bayan ɗaya, dan ba ta iya masa musu a kan komai, da ya ce ta bashi take bashi.
Sai da ya tabattar ya ƙwace komai, ya shiga bushasha shi da 'yan uwansa da iyalinsa, ya fara azabtar da Safiyya da 'yar ta, Hafsa da take 'yar gata gaba da baya, ba ta san wahala ba, amma a tilas aka mayar da ita tamkar baiwa saboda wahala da ita da mahaifiyarta.
Duk wata azabar aikin gidan nan suke yinta, ga hantara da wulaƙanci, Abinci sau ɗaya tal a rana ake basu, kuma Safiyya ba ta isa ta fita daga gidan ba ko wani ya zo in da take ba.
A haka duk wasu alamun girma suka bayyana a tare da Hafsa, kasancewar tana da jiki, duk da wahalar da suke ciki, bai hana surarta fitowa ba.
Nan samarin gidan suka fara kai mata hari, suna nema su keta mata haddi. Ta kasa gayawa Mama, sai dai tai ta kula da kanta, tana koke koke. Duk san Hafsa da makaranta ƙarshe sai da suka rabata da Makaranta.
Saboda yawan kuka da Safiyya take ba ji ba gani, ya Sanya ta haɗu da wani matsanancin ciwon ƙirji, da ya haifar mata da larurar numfashi.
Cikin samarin gidan nan ba wanda yafi uzzura mata, kamar Najib, Najib bashi da mutunci ko ɗa'a, ya samu dukiyar marainiya a wurin mahaifinsa kullum cikin yawo da abokai da shaye-shaye yake, bashi da burin da ya ga Hafsa yayi ƙoƙarin haɗata da jikinsa, ganin taƙi amincewa da hilatarta da yake yi, ya sanya ya fito ya ce Aurenta zai yi, yana sonta.
Babansa ya ce ya bashi, sadaki kawai za'a bayar a ɗaura Aure, ai 'yar uwassa ce. Hafsa idan abu na damunta ba ta fiye faɗa ba, ita hasali ma bata magana sai ta ga dama, dan haka sai dai tayi ta faman kuka.
Aka aiko wa Mama cewar mahaifiyarta babu lafiya, da ƙyar Aminu ya barta ta je, amma ya ce ba zata tafi da Hafsa ba.
Haka ta rarrashi Hafsa ta shirya ta tafi, sai dai ko da taje gida, ta tarar jikin mahaifiyarta yayi tsananin, da ba zata iya komawa gida ba, ta barta a halin da take ciki ba.
Har dare Mama bata dawo ba, hakan ya jefa Hafsa cikin damuwa, tun tana jiran dawowar Mama, har ta haƙura ta kwanta bacci.
Cikin dare taji mutum  a kanta, tana ƙoƙarin tashi, aka danne ta ana ƙoƙarin rabatabda suturar jikinta, shaƙa mata wani abu aka yi, ba ta shaƙi abin sosai ba, jikinta yayi sanyi ƙalau ta kasa motsawa, sai gani take dishi-dishi, wani abu mai nauyi yana rinjayar kanta. Tabbas ko ba a gaya mata ta gane shi, Najib ne ba wani ba.
Ba ta sake farkawa ba, sai da garin Allah ya waye, gari yayi haske, ta ji saukar ruwa a fuskarta, ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon Mama da ke kanta a rikice tana kuka tana tambayar Hafsa meyasameta?.
"Mama Najib ne" shi ne kawai abin da ta iya furtawa.
Mama tayi kuka tamkar ranta zai fita ita da Hafsa, ta taimakawa Hafsa ta gyara jikinta, ta kama hannun Hafsa zuwa wurin Aminu, mahaifin Najib, ta gaya masa abin da ɗansa ya aikata. Amma ya hau bala'i, sai da ya janyo hankalin mutanen gidan, uwar Najib ta ce sun yiwa ɗanta sharri.
Mama ta ce "Tun da haka ne, wurin 'yan sanda zata kai ƙara" Aminu ya hanata fita, ya cigaba da azabtar da su, kullum Hafsa cikin kuka take ita da Mama, Mama tun bata magana, har Mama ta buɗe baki ta yiwa Aminu Allah ya isa a gaban iyalansa.
Babu tausayi ko imani, ya ware ƙwanji ya dinga dukanta, Hafsa taje cetonta, ya haɗa da ita da Hafsa ya dinga jibgarsu, duka na wulaƙanci kamar dabbobi sannan ya haɗawa Mama da saki uku ba tausayi ba tsoron Allah.
Haka suka koma gidan da mahaifiyar Mama ke jinya, ba Abinci babu mai basu kulawa, ita ma ta zo ta rasu, hakan ya jefa Mama cikin tsananin damuwa ta haɗu da larurar hawan jini, da ya haɗu da Asma suke addabar rayuwarta tamkar zata rasa ranta.
Duk da haka Najiba bai fasa bibiyar Hafsa ba, saboda rashin Kunya, Mama ta kaisu wurin 'yan sanda shi da mahaifinsa, amma yayi amfani da dukiyarsu ya toshe bakin 'yan sanda, saboda Najib, Mama ta sayar da gidan da suke ciki na mahaifiyarta, suka tashi suka koma ɗorayi, gidansu na farko da ta rayu ita da Usman farkon Auren su.
Da kuɗin gidan, ta mayar da Hafsa Makaranta, sai dai Hafsa ta ƙara rasa kuzari da shiga damuwa, tun bayan Najib ya keta mata haddi. Zamansu a gidansu Najib da tashinta cikin tsnagwama da takura, ya ƙara nesanta da farinciki ko cikakkiyar walawala ba ta yi, balle fara'a.
Ƙarshe suka cinye ragowar kuɗin, babu mai basu Abinci, duk da tarin alkhairan mahaifinta ga al'umma, babu wanda ya dube su bayan rasuwar su, da ƙyar Hafsa ta kammala karatun sakandare, daga baya Hafsa ta fara wannan sana'ar ta sayar da awara.

Hafsa ta rushe da wani irin kuka, jikinta har karkarwa yake yi, Khalil ya yi shiru, ya kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi.

Ayshercool
08081012143

RUƊIN ƘURUCIYA

https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8

_*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA? Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_


Ayshercool.GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

*Littafina Aƙidata da kuma Ruɗin ƙuriciya, na kuɗi ne, sauran duk free me*


20-21

Wani irin abu mai bala'in ɗaci ne, ya shiga tsirgawa Khalil tun daga maƙogwaronsa zuwa cikinsa, duk da sanyin AC dake cikin motar, bai hana shi tsatstafar da wani irin gumi ba, idanunsa suka yi jawur. Yayi shiru ya rasa abin da zai ce, sai kukan Hafsa da ya cika motar ya ke masa amsa kuwwa a cikin kunnunwamsa.
Tamkar mai koyon magana ya fara shirya jimlar da zai rarrashi Hafsa da ita, sai dai suka maƙale a iya wuyansa, ya kasa furata su a kan harshensa.
Da ƙyar ya iya cewa "Is ok, kukan ya isa haka, kije gida, ki samu wuri ki kwanta ki huta" Hafsa ta kalli Khalil tana son karantar wani abu a fuskarsa, amma ta kasa kasancewar, ya kauda kansa gefe. Cikin ɗan ragowar kuzarin da ya rage mata, wanda take jin tamkar ba zai iya ɗaukarta ba, ta buɗe murfin motar, ta ja ƙafafuwanta da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login