Showing 27001 words to 30000 words out of 296192 words

Chapter 10 - GABA DA GABANTA

ba alkhairi. Fitowa ta yi daga ɗaki tana faɗin "Lafiya kuwa?"

"Kya tambayi lafiya mana, munafuka ha'ina, ki zo ki fito mana da in da yarinyar nan Amina ta ke, dan babu yadda za a yi ta gudu ba tare da haɗin bakin ki ba".

"Haba Yaya Bala, ni meye nawa a ciki? Ya za ayi in goyi bayan Amina ta bijire muku, ko ta gudu? Nima fa Amina 'ya ce a wurina, ba zan goyi bayan ta aikata abin kunya ba, ni ban san in da take ba".

Bala ya ce "Ai kuwa ƙarya ki ke yi, kuma yadda ki ka haɗa baki da ita kika sa ta gudu, sai ki koma ki haɗo abin da ya samu a mayarwa da Jarmai kayan aurensa, tun da ta gudu".

"Meye haɗina da kayan auren Jarmai? Bayan kuɗinsa da komai ku ya dabƙawa kuma babu abin da kuka bamu a ciki?".

"Rufewa mutane baki, amma dai kin san abin da aka yi kuɗin ko? Kayan katako aka sayawa Amina da su"

"Amma yaya Bala, ina a kuɗin gonar mahaifinta aka saya mata kayan? Ni dan me za a ce in bada wani kuɗi"

"Au tuhumar mu zaki yi, to Wallahi sai kin kawo wani abu, dan sunan mu ba zai ɓaci a banza ba a dalilin ku ba, mutanen banza kawai"

Galala haka Inno ta bi su Lawan da kallon mamaki da kuma ƙarfin hali.




Amina aiki suke sha a gidan nan kamar ba gobe, kasancewar Amina nai kaifin ƙwaƙwalwa ya sanya nan da nan ta iya abubuwa, ita aikin fa suke ba ya damunta, dan in dai aiki ne ta riga ta saba da shi tun a ƙauye, dan sam ba ya mata wahala, ita wulaƙanci da kallon ƙasƙantattun da ake musu ne yake damunta, shima da tuna ga burinta da yake ranta wanda take sa ran cikawa sai ta yi ƙoƙari ta manta komai.
Dan kusan kullum idan ta je wurin Baba nasihar sa kenan a gareta, ta yi haƙuri.
Amina na ta saka ran ganin wanda zai kaita Makaranta ya dawo, amma shiru ba ta ga ya dawo ba, kuma ba ta ji ana batun dawowar ta sa ba, ta dai yi shiru ta danne abun a ranta, dan abin ya fara damunta, idan aka aiketa ita da Hajara, tana ganin 'yan Makaranta hakan ya tabattar mata da an koma Makaranta.

Yau sun gama aikin su kaf, sun gyara ko ina, wanda ƙarfin aikin ma Amina ce ta yi shi, ta zauna a falo tana kallon TV, sai ga Fadila ta dawo daga makaranta, ta shigo falon ba ko sallama, ta dire jakarta a falon, da mayafinta ta kalli Amina ta ce "Ki kawo mini su ɗaki".

Amina tabi bayan Fadila da kallo ta taɓe baki, a ranta ta ce "Kin shigo ba ki mini sallama ba balle sannu da gida, kuma kin yi dakon jaka da mayafi tun daga makarantar, ƙarasawa da su ɗakin ki shi ne aiki a wurinki, ai kuwa ba zan kai ba' daga haka ta tashi ta bar falon, tayi tafiyarta wurin Baba.

"Uwata, in ce ko dai kin gama duk ayyukan da aka saka ki kan zo nan?"

"Eh Baba, na gama komai".

"Yawwa Uwata ta kaina, banda ganda ko gardama dan Allah, yi nayi bari na bari".

"Insha Allahu Baba, nace yaushe zaka je ƙauye ne? Da na ji kace a wannan satin"

"Eh a wannan satin na so zuwa, amma nafi son in ga yaron nan da zai kai ki Makaranta ya dawo, an kai ki kin fara zuwa sai inje".

"Wallahi Baba kamar ka san abin da ke raina, na yi shiru ne kawai dan kar in takura maka, amma naga an koma Makaranta".

"Mu ƙara haƙuri dai, tun da ya ce za a kai ki, na san za a kai ki insha Allah"

"To shikenan Baba, amma nace mai zai hana idan zaka ƙauyen muje tare ina kewar Inno da yawa".

"So kike muje su sake riƙe ki ko?" Da sauri ta girgizawa Baba kai.

"To idan ba haka ba, ki cire rai da zuwa ƙauye, har sai Allah ya sa kin kammala sakandirenki"

"To Baba Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi".

"Ameen Uwata ta kaina"

Ta shantake abinta, ta cigaba da hira Baba, har sai da aka yi kiran sallar magariba, sannan ta koma ciki.

Kamar yadda Fadila ta bar jakarta da mayafi suna nan a wurin, Amina kuma bata bi ta kan su ba, ta wuce ɗakin da take.

Fadila ba ta tashi sanin Amina ba ta kai mata jakarta ɗaki ba, sai da ta tashi tafiya makaranta da safe, ta nemi jaka ta rasa, ta duba ɗakinta kaf ba ta jaka ba, dan haka ta fito falo tana neman Asabe, dan ta ji in da ta ajiye mata jaka bayan ta gyara mata ɗakinta, sai dai tana fitowa ta ga jakarta da mayafinta a in da ta ajiye su, buɗe baki ta yi da mamaki, bayan ta tuna taga 'yar mai gadi jiya a falo.

Cikin fushi ta fara ƙwalawa Hajara kira, Hajara da ke kitchen ta jiyo kiran Fadila ta taho da gudu, ta durƙusa.

"Ina wannan yarinyar da ku ke aiki da ita?".

Hajara ta ce "Wai Amina?".

"Ko ma wacece, ki kira mini ita yanzun nan".

"To bari in kirata, naga yau tun da aka yi sallar asuba bata fito ba, kuma ba ta saba hakan ba"

"Ke dalla ɓace mini daga gabana ki je ki kira mini ita, kin tsaya kina mini wasu surutan banza"

Cikin hanzari Hajara ta bar wurin, ta nufi ɗakin Amina, ta tsaya a ƙofa tana ƙwanƙwasawa.
Amina ta na zaune, tana rubutun Alƙur'ani a cikin littafin da ta taho da shi daga ƙauye. Saboda yau ji ta yi tana kewar makarantar Allo, da tana ƙauye da tuni tana nan ta wanke allonta, ta yi rubutu, dan haka yau ta zauna bayan sallar Asubahi ta fara rubutunta.
  Tana jin Hajara na buga ƙofa tana faɗin "Amina ki buɗe ƙofa, Fadila tana nemanki".

Yamutsa fuska Amina ta yi, tare da tura baki, ta cigaba da abin da take yi.

"Amine ki buɗe mana"

"Dan Allah Hajara ki ƙyaleni, kullum da wuri nake fitowa, yau wani aiki nake yi, kiyi abin da zaki iya, sauran ayyukan ki bar mini idan na fito zan yi"

"Ke bafa saboda aiki ba, Fadila ce take neman ki".

Tsaki Amina ta yi ta ce "Kwa ci kan ku, ba wanda ya isa ya ɗagani daga zaman nan idan ba Allah ba, ko Baba ne ya kirani ba".

Fadila ganin zata makara Hajara ba ta dawo ba, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice ranta a ɓace, ta ƙudurce a ranta idan ta dawo sai ta koyawa su duka biyun hankali.


Amina ba ta fito ba sai ƙarfe tara na safe, dan rubutunta ta zauna tai ta yi.

A kitchen ta tarar da Hajara, "Anty Hajaru sannu da aiki".

"Zaki ga Hajaru ganin idonki, yau kin caza mana bala'i, ba yadda ban ba ki fito amma ki ka yi mirsisi ki ka ƙi, ƙarshe sai tafiya ta yi, yau kashin mu ya bushe daga ni har ke idan ta dawo".

Amina ta ɗage kafaɗa ta ce "Oho, duk masifar 'ya dai na san ba zata ɗauki raina ba, sai dai tayi ta ci kanta ita kaɗai".

Buɗe baki Hajara ta yi tare da riƙe haɓa ta ce "Ke Amina dama haka ki ke?".

Amina ta share Hajara, ta nufi ƙofar fita tana cigaba da ƙunƙuni.

Tana fita harabar gidan ta hango Baba, ya shirya cikin wani milk ɗin yadi. Ta ƙarasa ta gaishe shi ta ce "Baba ya naga kamar fita zaka yi?".

"Eh mana, dama ke nake jira in ga fitowarki in yi miki sallama, ƙauye zani".

"Baba da gaske?".

"Ahh ji ja'ira zan miki ƙarya ne?".

"Wayyo Allah, Baba ka gaishe mini da Inno, na so zuwa in ganta, sannan dan Allah ka bata haƙuri, na san na sata a tashin hankali tahowar nan da na yi, bari inje cikin gida in ɗauko maka Abincin karina ka kai mata".

Baba ya ce "A'a ba za ayi haka ba, zan musu tsaraba a hanya".

"Baba dan Allah ka tsaya, yanzu zan dawo".

Amina ta ruga cikin gida. "Hajara, dan Allah bani leda in zubawa Baba Abincin karina ya kaiwa Innota".

"Au yau zai je garin naku?".

Amina ta ce "Eh yau zai je".

Hajara ta ce "Wane irin in baki leda, viva zaki samu, har kayan marmarin nan na cikin firinji da suka kusa lalacewa, duk ki bashi ya kai mata".

"Ahh Hajara sata fa kenan, ba a bani ba".

Hajara ta ce "Dalla bari kiga, idan ki ka tsaya sai sun baki, ba zasu taɓa baki ba, sai dai su ruɓe ki kwashe ki zubar, kuma ai ba ayi mana iyaka a kan Abincin gidan nan ba"

Hajara ta ƙulle soyayyen dankali kaya guda da miyar ƙwai, da manyan magwaro da lemo, ga uwar kankana har da su biscuit. Ita dai Amina taji a ranta duk babu daɗi, tamkar sata suka yi.

Hajara ta rakata suka kai wa Baba, Baba ya duba kayan nan ya ce "Amina wannan kayan fa, kin tambaya ki ka ɗakko?"

Hajara ta ce "Baba Hassan, ai ba ayi mana iyaka da Abincin gidan nan ba, kuma idan aka barsu ma a banza za su lalace, su ba su ci ba kuma ba su bayar ba, sai dai mu kwashe mu zubar".

Baba ya karɓa ya kama hanyar tafiya.



Fadila a gaggauce ta shiga ajinsu, kasancewar yau ta makara sosai, sai dai tana shiga ta tarar da lecturer ya na arranging ɗalibai, zai yi musu test.

Lecturer da farko ji yayi tamkar ya koreta, saboda ba ta da kunya, amma ya ƙyaleta ya sakata a bencin gaban Yazeed.

Sai wani haɗe rai take, tana hura hanci ita a lallai bata so aka ajiyeta a wurin da yake ba.

Nan malamin ya rubuta musu test ɗin, tare da sake tuna musu, test ɗin maki Ashirin ce, Attendance ɗin da yayi kuma maki talatin, zai yi jarrabawar sa maki hamsin. Sannan ya kawo wani lecture yayi invigilating ɗin su, shi zai je wani ajin yayi lectures.

A tambayar da ya yi musu ciki har da abinda Yazeed ya koya musu a aji, hakan ba ƙaramin farantawa ɗaliban rai ya yi ba.

Kowa ya duƙufa ya fara rubutu, amma Fadila ta shiga rarraba ido, kamar an kwashewa karya 'ya'ya.
Yazeed yana ta rubutunsa, yayin da malamin ke ta zagawa yana dudduba su.

Yazeed ne ya lura babu abin da Fadila ta rubuta, banda sunanta lambar Admission ɗinta da question.
Ya girgiza kai, a gurguje ya ƙarasa nasa, sannan ya waiga ya ga lecturer ba ya kusa da su, ya sanya bironsa ya taɓo Fadila.
"Dalla meye haka?"

"Ya naga ba ki rubuta komai ba?".

"To ina ruwanka da ban rubuta komai ba? Aikin banza ɗan sa ido kawai".

"Sorry ba sa miki ido na yi ba, bari in karanto miki".

"Bana so".

"A'a, kar ki manta fa bamu da Attendance ni da ke, kuma ya ce exams ɗin ma 50mrks ce, kar a kafe exams a ga kin faɗi, za a raina ki. Buɗe papern, in dinga karanto miki kina rubutawa".

Ba kunya ta ware paper, ta gyara zamanta, yana karanto mata tana kwashewa a ta ta paper.

Cikin rashin sa'a, invigilator ya hango su, aikuwa yana zuwa ya rubuta wa Yazeed -10 marks a paper ɗin sa, ba tare da ya hukunta Fadila ba. Babu wanda ya san mai ya faru, sai Fadilan da Yazeed, dan lecturer bai yi magana ba, kawai zuwa ya yi kan Yazeed ya tsaya, yayi masa minusing, yana yi masa minusing ɗin kuma, Yazeed yai submitting paper ya tashi ya fita.
Fadila kuwa ko a jikinta, ita dai tun da Allah ya sa ta samu abin da ta rubuta shikenan, Yazeed yayi asarar maki arba'in a test.




Inno kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ganin Malam Hassan a gida, ta dinga murna, nan ta tashi ta fara ƙoƙarin ɗora girki, ya ce "Ba sai kin dafa komai ba, dafa ruwan zafi ga kayan shayi na taho da shi, 'yar ki kuma ta bada kayan kari a kawo miki".

Inno ta ce "Aikuwa Malam ina ta baza ido in ganku tare, ni nan Saminu ya ce mini tana wurinka, ko dai ƙarya yayi mini?".

"A'a bai miki ƙarya ba, ke dai gama ki zo mu yi Magana".

Bayan Inno ta dafo ruwan zafi, Baba Hassan ya ajiye mata tulin soyayen dankali da miyar ƙwai, Inno ci take tana santi, tana anya na taɓa cin abinci mai daɗin wannan a duniya? Baba Hassan ya yi murmushi, ya ce "bani labari, yaya aka yi da ba na nan game da Amina?".

Nan Inno ta kwashe komai ta gaya masa, har zuwa ɓatan Amina.

Shima nan ya warware mata cewar, Amina wurinsa ta je, kuma ga hukuncin da ya yanke a kanta.

Inno ta ce "Amma malam kaja ganin hakan daidai ne? Yarinyar nan ba ta ɓatawa kanta suna ba kuwa? Kun ɗau bokon nan kun sa a ranku kai da ita kamar ibada".

"Hannatu, boko ba ibada ba ce, amma ba zaki gane rashin boko na cutar mu ba, sai kinji birni kin ga amfanin boko, insha Allah zamu yi alfahari da ilimin da Amina za ta samu".

"To ubangiji Allah ya sa".

"Salamu Alaikum! Salamu Alaikum!" Aka shiga kwaɗa sallama. Murayar kawu Lawan ce yake kwaɗa sallama shi da Bala.

Baba Hassan ya fita cike da fara'arsa yana musu sannu da zuwa, ya shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, suka zazzauna Baba Hassan ya gaida su cikin mutuntawa a matsayin su na yayyensa.

Maimakon su amsa sai kallon Banza da Bala ya yi masa ya ce "Ina fatan labri ya iske ka na abin kunyar da 'yar ka ta yi? Mun zaɓa mata miji za muyi mata aure, amma ta tsallake ta gudu ta shiga yawon duniya".

Baba ya ce "Ashsha, ba yawon duniya ba dai Yaya Bala".

"To yawon me ta tafi? Waye ya san in da take, ta bi ta ɓata mana suna da zuriyar mu a gari".

Baba ya ce "Yaya ba ina goyon bayan abin da Uwata ta aikata bane, amma sanin kan ku ne duk garin nan ba wanda bai san Jarmai ba mutumin kirki ba ne, maiyasa za a bashi Aurenta?"

Lawan ya ce "Idan ba a bashi ba haka za a barta ta cigaba da yawo a gari soƙai-soƙai sa'ar iayyenta ba aure, saboda wata matsiyaciyar bokon banza, to ka sani idan ta dawo daga yawon banzan nata ba dai a gidan nan ba, ta je idan dai bariki ce, na baya ma ba su ci riba ba".

Baba ya ce "Subhanallah, Amina dai ba wani ta tafi ba, tana tare da ni a in da nake aiki a can birni, kuma gidan da nake sun ɗauketa aiki, da albashinta zasu dinga biya mata kuɗin Makaranta".

Tafa hannu suka shiga yi suna salati.

"Hassan, yanzu abin da ka aikata ka yiwa kan ka adalci kenan? Yanzu wannan zabgegiyar budurwa ka kai birni ta yi boko? A ƙauyen ma ya muka ƙare da ita, har muna faɗa ta faɗa saboda ta yi boko, shi ne ka kaita birni ta yi boko?" Cewar Lawan yana zazzaro idanuwa.

Bala ya ce "Ka kyauta da kuka haɗa kai da 'yar ka kuka ɓata mana suna, mun gama shirin biki da gayawa jama'a ɗaurin Aure, amma ta gudu, ga Jarmai ya ɗaga mana hankali mu biya shi kuɗinsa.
Amma in Allah ya yadda, tun da aniyar alkhairi muka yi niyyar ɗaurawa, amma kasa ƙafa ka rusa kai da ita, ku ka nuna bamu isa ba, insha Allah naku burin ba zai cika ba, in Allah ya yadda sai ta yi cikin shege a birnin nan, sai ta dawo da mummunan abin kunyar da sai ka kasa haɗa ido da mutane, sai bokon nan ta zame muku bala'i da masifa kai da ita!!!"

Dafe ƙirji Baba ya yi ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

Inno da take ɗaki tana jiyo su ɗora hannu ta yi a ka, jin jafa'in da ake janyowa Amina.

Lawan ya ɗora da cewa "Ai yadda ya ja mana abin kunya a garin nan, sai 'yar ta sa ta janyo masa abin faɗa da nunawa, ka ɗau balagaggiyar yarinya ka kaita cikin wani ahalin da ba muharammanta ba, wai dan ta yi boko, muna nan za aje a dawo da abin nunawa, zaku gani daga kai har ita, hakkinmu ba zai bar ku ba da kai da ita, muna nan mun zuba ido, zaka gani. Yaya Bala tashi mu tafi".

Gaba ɗaya jikin Baba yayi sanyi ƙalau da mugun bakin da yayyaensa suka yiwa Aminan, anya ba za a haƙura da bokon nan ba Amina ta dawo ayi Auren nan ba?!


Domin samun update a kan lokaci, Follow me at Arewabooks
Ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724

Ayshercool
08081012143GABA DA GABANTA

   P9

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Haka su kawu Bala suka ƙaraci faɗansu, kamar zasu tashi sama, suka kaɗe rigunansu suka fice.
Baba ya yi shiru ya rasa abin da yake masa daɗi. Inno ce ta fito jiki a sanyaye tana kallon Baba.
"Malam, an ya ba za'a haƙura da wannan karatun ba, ka dawo da Amina gida ba, irin wannan mugun alkaba'i da suke janyowa yarinyar nan, nifa gaba ɗaya jikina ya yi sanyi Wallahi".

Baba ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Insha Allah, babu abin da zai faru sai alkhairi, ina sa ran a sanadiyyar Amina mutanen garin nan su ga amfanin ilimi mussaman ga 'ya mace".

"Amma Malam, ni fa na karaya wallahi".

"Ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai samu Amina sai alkhairi Insha Allah".



Hajara na dininga tana kwashe kwanukan da aka karya a kai, Amina kuwa duk ta sauke kayan kallon falon, tana musu duster saboda ƙurar da suka yi.
Hajiya Zainab ta fito daga sashenta, tana ƙarewa falon kallo, dan ta samu wani laifi da zata sauke musu masifa amma ba ta samu ba, zuwa yanzu ta fara jin daɗin aikin Amina, dan sam bata da ƙyuya, kafin ace ta yi ma tayi, kuma ba ta son ƙazanta sam.

Hajiya Zainab ta ce "Yawwa Hajara, in an jima Khalil zai dawo, ki ɗauki mukullin sashinsa a shiga a gyara masa, sannan ku sanarwa da Isyaku ya wanke masa motarsa, dan na san da ya dawo zai buƙaci ya fita da ita, sai kuma a yi girkin rana da shi, ni zan fita wataƙila har ya dawo ban dawo ba".

Hajara ta risuna cikin ladabi ta ce "To Hajiya, insha Allah za ayi yadda ki ka ce, sai kin dawo".

Har Hajiya Zainab ta kai bakin ƙofar falon, ta waigo ta kalli Amina da take ta aikinta ko kulasu ba ta yi ba ta ce "Ke, wato

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login