Showing 240001 words to 243000 words out of 296192 words

Chapter 81 - GABA DA GABANTA

ki kawo mini mijin da zaki aura, idan ba haka ba zan ɗau matakin da ya dace".

Cikin rashin Fahimta Hajiya Zainab ta ce "Ban gane me kake nufi ba".

"Ai da hausa nayi maganar, ba da wani yaren ba, dan haka kin ji, idan kun ƙi na zaku ƙi ganin hukuncin da zan yi ba" yana gama maganar ya bar ɗakin.

Hajiya Zainab ta ce "Ƙaryar banza, ba wani abu da zai iya yi, sannu ya kike jin jikin naki, ko mu tafi Asibiti?" Fadila ta girgiza kai tana lumshe ido, saboda a hankali ta ji ƙirjin nata yana saki.

Sai dai Maganar Daddy ta shiga kai komo a kanta, ita ina taga wani saurayi yanzu da zata ce zata aura, dan farin jinin samari kam akwai su Allah yayi mata su, amma duk wulaƙanci take yi musu ba ta saurarensu, babbar damuwar ta da bata san wane irin mataki Daddyn zai ɗauka ba kamar yadda ya ambata.
Har zuwa dare gaba ɗaya ta kasa sukuni, dan sai da Mummy ta kira Doctor Aliyu ya zo gida, ya kuma dubata, ya yi mata allurai tukuna.

Yau Daddy yana wurin Hajiya Zainab, sai dai tun da ya shiga wurin nata take dakon, taji ya ce mata wani abu a kan batun kuɗin auren Fadilan, amma ta ji yayi shiru bai ce mata komai ba, yau har ƙofar bedroom ɗinta ta bari a buɗe, amma ya ƙi shiga yayi zamansa a falo Kamar yadda ya ta saba yi masa, ta rufe ƙofarta a Duk lokacin da yake wurinta sai dai ya kwana a falo.
Tana cikin bedroom ɗin tana shirin kwanciya, sai ga kiran Hajiya Salma, sai da gabanta ya faɗi, amma ta dake ta ɗaga.

"Zainab yanzu ni zaki wulaƙanta a duniya, duk alkhairi da nake miki a rayuwa, ni zaki ciwa mutunci"

Cikin pretending Hajiya Zainab ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Salma meyafaru ne?"

"Dole kice mini maiyafaru mana, ɗazu mijinki saboda tsabar wulaƙanci da tozarci, ya zo har gida ya samu baban Salim, wai maganar auren nan ayi haƙuri, wai Fadilan bata so"

Hajiya Zainab ta ce "To Salma ni ya zan yi, kwanciyar Asibitin nan da tayi ne, da aka ce jininta ya hau likita ya cewa babanta wai wani abu ne yake damunta, da aka matsa sai cewa tayi auren nan ne bata so, ba yadda ban yi da ita ba, amma ta tubure shi kuma kin san halinsa a kan 'ya'ya ya ce dai a haƙura da auren nan, in an kwana biyu ta warware idan tana so sai ayi, na kaɗa na raya amma kasancewar yana ji da shegen taurin kai sai yayi mini banza, ashe mayarwa yayi, aikuwa dole na san abin yi dan ba zan bari zumuncinmu ya ɓaci ba"

Hajiya Salma ta ce "A'a, ai aikin gama ya riga ya gama, shi ma Salim ai ɗan gata ne, babansa ba zai bari a wulaƙanta shi ba, Allah ya haɗa kowa da rabonsa".

Hajiya Zainab ta ce "Aikuwa ba za ayi haka ba, daga Fadilan har baban nata basu isa ba, ina yabonta salla zata kasa alwala zata watsa mini ƙasa a ido?"

Hajiya Salma ta ce "Ai fa sai dai muyi haƙuri Zainab, a tara a gaba, mu dai tun da mun riga mun shirya, zamu saka ya nemo wata ya aura*.

"Dan Allah kuyi haƙuri Salma, ba yadda na iya ne"

"Bakomai kar ki damu sai da safe"

Bayan katse wayar, Hajiha Zainab tayi ajiyar zuciya ta ce "Alhamdilillah, na kashe wannan wutar!".

Washegari bayan sallar asuba Hajiya Zainab ta tafi ɗakin Fadila ta tashe ta.
Fadila ta tashi tana kallon Mummy tana mamakin dalilin zuwanta a yanzu.
"Fadila, ya mayar musu da kuɗinsu, na nuna mata cewar kawai ke kika nuna ba kya so, shi ya sanya ya mayar  musu da kuɗin".

Cikin sanyin jiki Fadila ta ce "Amma Mummy, nifa hankalina a tashe yake".

"Tashin hankalin me? Ba kin ce ba kya so ba kuma an mayar musu da kuɗin, menene kuma?"

Fadila ta ce "Mummy baki je me Daddy ya ce ba? Wai nan da Alhamis na kawo mijin aure ko kuma ya ɗau matakin da ya ga dama ba, Mummy ban San me zai iya yi ba, kuna kinga ni bani da wani wanda zance shi ne tsayayye"

Tsaki Mummy ta yi ta ce "Ke dalla can, idan har ina nan ba abin da zai iya yi miki, ki kwantar da hankalinki, ki cigaba da walwala, kinga exams zaki fara ki manta kawai barazana ce yake yi".

Fadila tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan Mummy, na Gode sosai da goyon bayana da kika yi".

"Bakomai, Allah ya ƙara miki lafiya".

Fadila tayi murmushi ta ce "Amin Mummyna"

Alhaji Ahmad kuwa da hanzari yaje sashin Amina, ko tashi ba ta yi ba, ya tasheta.

Amina ta tashi tana tura baki ta ce "Meyasa ka tasheni?"

"Breakfast zaki haɗa mini"

Cikin shagwaɓa ta fara tuttura ƙafa, tana tura baki ta ce 'Amma ba a wurina kake ba fa, baccin nan yayi mini daɗi sosai"

Hannu biyu ya saka sauketa daga kan gadon, ya janyo hannunta zuwa kitchen yana faɗin "Oya a dafa mini koma menene".

Amina ta ce "Tom na ji, amma sai ka tayani aikin, wallahi kwanan nan bana son yin aiki"

Murmushi yayi ya ce "Faɗa mini da mai zan tayaki? In mun gama kayana nake son ki shirya muni, ƙarfe sha biyu fa zan tafi Lagos" da sauri ta kalleshi ta ce "What?! Meyasa?"

"Baƙi zan yi da gaggawa, akwai buƙatar in halarta shiyasa"

"Yanzu tafiya zaka yi ka barni?"

Ya ce "A'a, ba daɗewa zan yi ba, da na gama abin da nake, zan dawo ki gaya mini suwa kika yanke a biyawa umara zamu tafi"

"Mhmmm zan yi missing ɗinka, ni bana son ka tafi"

Yayi wannan ya ce "I will miss you too" tare suka yi girkin, Suka gama ya karya ta shirya masa kayansa suka fito falo, har sashin Hajiya Zainab ya je, ya kuma yi mata kashedi a kan abin da ya faɗa na Fadla ta fito da miji, sannan yayi mata sallama a kan cewar zai je Lagos, ko ƙurar da ya biyo ya shigo sashen nata bata kalla ba, balle ya sanya ran zata kula shi. Bayan fitarsa ita ma ta shirya ta fice zuwa gidan Hajiya Salma, da sake lallaɓata a kan fasa auren da aka yi.

Ko da Fadila taje makaranta, 'yan ajinsu suka yi ta mata sannu, ciki har da Yazid da yafi kowa murnar ganinta cikin ƙoshin lafiya.
Bayan ta koma gida da Yamma, Hajiya Zainab ta ɗauki Fadila suka je gidan Khalil. Duk da halin rashin lafiya da Hafsa ke ciki tayi ƙoƙarin sakin fuska ta karɓe su, amma Hajiya Zainab tayi burus, ta dira wa Hafsa wulaƙanci da cin mutumci, tare da zageta wai 'yar matsiyata.
Abin ya yiwa Hafsa ciwo, amma ba yadda ta iya haka tayi shiru, dan ta fara tunanin anya ba zata rabu da Khalil ba, ko dan ta huta da wannan wulaƙanci, amma tayi tunani idan ta rabu da shi ta koma ina? Kuma kwata-kwata yaushe tayi auren ma.

Fadila har da cewa idan tayi zuciya, ta koma gidan matsiyatan iyayenta, ta rabu da Khalil.

Suka gama cin mutuncinsu suka tafi, bayan tafiyarsu ta sha kuka sosai da sosai, ga rashin lafiya ga kaɗaici da damuwa, dan bata shige-shigen gidan kowa, kullum tana gida.
Da daddare Khalil ya kirata, suka yi waya suka gama, amma ba ta gaya masa rashin lafiyarta ba balle zuwan su Hajiya Zainab.


Kwanaki huɗu da tafiyar Daddy, Amina bata jin daɗin komai, taje ta saka Hajara ta soya mata dankalin hausa, ta ɗauki wani ta feraye ta dawo falo ta zauna tana cin ɗanye.
Hajara ta soya dankali ta kawo mata, ta dinga yi masa cin yunwa, ta wuni tana ci tana shan ruwa.

Washegari Amina ta tashi da ciwon ciki da amai, saboda dankalin da ta yiwa cin yinwa jiya.
Daddy ta kira a waya, ta sanar masa zata je Asibiti ulcer na damunta, ya bata izini.

Ta shirya ta saka Zakiru ya ɗauketa domin kaita Asibiti, sai da suka zo wurin unguwar gidan su Khalil, ta tuna sun kwan biyu ba suyi waya da Hafsa ba, dan haka ta ce "Zakiru, dan Allah muje gidan Khalil ko a gurguje mu gaisa".
Ba musu Zakiru ya wuce da ita gidan Khalil. Ta ɗan jima tana knocking har ta fidda ran za a buɗe, dan ta kira lambar Hafsa amma bata ɗaga ba, har ta juya kuma sai Hafsa ta buɗe gate ɗin.

Murmushi tayi da taga Amina tayi mata sannu da zuwa. Amina ta kalleta da mamaki ta ce "Hafsa lafiyarki ƙalau kuwa?".

Hafsa ta ce "Me kika gani? Mu shiga daga ciki dai".

Suka shiga falon, Amina na cigaba da kallon Hafsa.

"Ya gida ya Daddy?"

"Daddy baya nan, Hafsa kalli yadda kika yi wani iri, duk kin rame ko wani abun ne ya haɗaki da Khalil ɗin?"

Hafsa na shirin yin magana, amai ya taso mata, ta tashi da sauri ta bar falon, Amina ta tashi ta bita, ta taimaka mata ta gyara jikinta.

"Hafsa menene?"

Hafsa ta fashe da kuka, Amina ta ce "Hafsa, kar dai auren naki ne ya samu matsala daga yi?"

Hafsa ta girgiza kai ta zauna, Amina ta zauna, Hafsa ta ce "Ban gayawa kowa ba sai ke, Khalil ya koma aiki, tun da ya tafi bani da lafiya, bai ma san bani da lafiya ba, amma Mummy ta zo Ita da Fadila suna ta ci mini mutunci, zuciyata tana raya mini na haƙura da auren nan"

Ran Amina yayi mummunan ɓaci, tana tunanin Hajiya Zainab wace irin macece.

Cikin tausayawa Amina ta ce "To kin ci Abinci ne?".

"A'a bana iya cin komai, komai naci amai nake yi, a kwance nake wuni wataran saboda jiri a kwance nake salla".

Amina ta jinjina kai ta ce "Amma kike zaune a gida? To kin ganni dama asibiti zani nima, bari na dafa wani abun ki ci, mu tafi Asibitin tare.

Hafsa bata musa ta ba, Amina ta shiga Kitchen da kanta, ta dafa musu indomie mai yajin tsiya da dankalin turawa, da kifi.

Suka zauna suka ci tare, suna ci suna zare ido ita da Amina, saboda azabar yaji, amma daɗinta suke ji a haka.
Hafsa taji daɗin zuwan Amina sosai, dan ji tayi ciwon nata ya ragu.

Hafsa ta shirya suka tafi Asibiti tare, sai da a motar ma, amai ta cigaba da yi saboda warin fetur. Can Asibitin da Daddy yake ganin likita suka tafi.  Yadda likita ya yiwa Hafsa tambayoyi, ya tabattar ta galabaita ta daɗe tana ciwo, aka yi mata gwaje gwaje, ga ciki ga jininta yayi ƙasa ga malaria da tayi mata mummunan kamu.
Likita yayi faɗa sosai da sosai, a kan yadda Hafsa tayi zamanta a gida tana fama da ciwo.
Ita kanta Amina ranta ya ɓaci, aka kwantar da Hafsa, aka dinga saka mata ruwa da allurai.

Yadda likita ya zazzage musu haka Amina ta kira Daddy a fusace tana faɗa, ta zayyane masa duk abin da Hajiya Zainab tayi, da yadda ta tarar da Hafsa, dan ita ta manta da tata larurar ma gaba ɗaya.

Daddy kansa bai ji daɗin abin da ya faru ba, ya ce "Ban da abin ki Meenali, ai bani na kar zomon ba, amma zan ɗau matakin da ya dace, Allah ya baki haƙuri".

"Eh amma ai matarka da ɗanka ne suka yi, kuma yakamta ayi gaggawar takawa Fadila burki a kan abin da take yi"

"Na ji, ina nan zuwa garin gobe in Allah ya kaimu zan dawo gida, na gama abin da nake a nan ɗin. zan yi hukuncin da ya dace".

Ruwa aka dinga ƙarawa Hafsa ba ƙaƙƙautwa, saboda ko Abinci bata iya yi, ko ruwa ta sha sai tayi amansa.

Daddy ya kira Khalil ya dinga yi masa faɗa a kan tafiyar da yayi, ya bar Hafsa a wannan halin.
Khalil ya tabattar masa da cewa Mummy ce ta saka shi. Daddy ya ce Lallai lallai, ya dawo gida yazo ya kula da matarsa.
Sai Yamma sannan Amina ta koma gida, bayan Mahaifiyar Hafsa ta iso Asibitin.

Kamar yadda Daddy ya faɗa, washegari ya dawo gida, ya dawo ya tarar Hajiya Zainab na can nata yawon, Fadilan kuma bata dawo daga makaranta ba.

Khalil kuwa a gigice shi ma ya dawo gida, jin batun Hafsa bata da lafiya tana asibiti. Sai dai babban abin da ya faranta masa, jin batun cikin Hafsa.

Amina  ta zaunar da Daddy, ta sake gaya masa abin da Hajiya Zainab ta dinga zuwa tana yiwa sirikar ta, kuma ta dinga ziga shi a kan lallai ya aiwatar da shawarar da ta bashi.

Sai dare sannan Hajiya Zainab ta dawo, ba ta san ma Daddy ya dawo gidan ba.
Suna zaune ita da Fadila, suna shan tea a falonta, sai ganin Alhaji Ahmad tayi.
Kallo ɗaya tayi masa, ta kawar da kanta ta cigaba da abin da take yi.

Fadila ce ta ce "Daddy sannu da zuwa"
Bai amsa ba, ya nemi wuri ya zauna.

Ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Labari ya iskeni, a kan duk abin da kika aikata, ban san wace irin zuciya ce ba a ƙirjinki Zainab, Allah ya shiryeki. Bari in gaya miki, wallahi muddin kika sake shiga sabgar gidan Khalil, ko ki kayi dalilin rabuwar auren nan, wallahi ki tabbatar kin salwantar da naki auren ne"

Da mamaki ta kalleshi ta ce "Ni kake gayawa aurena zai salwanta? To idan ya salwanta sai me, kuma Khalil ɗana ne, dan haka ina da ikon yanke duk wani hukunci a kansa, dan haka shiga sabgar aurensa yanzu na fara, idan ka ga dama ma, a yanzu ma ka sakeni sai menene? Uwar me ka tsinana mini a zamana da kaia banda zunzurutun baƙin ciki da nadama, babu abin da nake yi, aikin banza da na wofi kawai"

"Ni kike gayawa aikin banza da na wofi?".

"Na faɗa, ka sakeni a yanzu idan ka ga dama, 'ya'yana ne ba zasu rayu da matsiyata ba, kuma sai na yiwa Khalil aure da wadda nake so" tana gama maganar ta miƙe ta shiga bedroom.

Cikin jin zafin abin da Hajiya Zainab tayi masa, ya kalli Fadila ya ce "Ina maganarmu, na ki kawo mini mijin da zaki aura?" Fadila tayi shiru tana sunkuyar da kai. Ya jinjina kai ya ce "Da kyau".

Washegari Juma'a, bayan Daddy ya dawo daga sallar juma'a, Fadila ma dawowart kenan daga school, tayi wanka ta sauya kaya, sai ga Daddy tare da Amina a ɗakinta.

Daddy ya kalli Fadila cikin hanzari ya ce "Tashi maza ki haɗa kayanki, ki haɗa duk abin da zaki iya buƙata"

Cikin rashin Fahimta ta ce "Daddy ban gane ba, ina zamu?"

"Ki tashi kiyi abin da nace, kin tsaya kina tambayata". Dariyar mugunta Amina take yi mata, a bayan Daddy.

Miƙewa Fadila tayi tana bin Daddy da kallo. Cikin tsawa da bin umarni ya kuma maimaita mata abin da ya ce.

Nan ta sauke akwati, tana zuba kayanta cikin damuwa, tana son tambayar Daddy, amma a rikice take saboda yadda ya haɗe rai.

Akwati ɗaya ta zuba ɗan abin da zata buƙata, ya kalleta ya ce "Ki zuba kayan da zasu wadaceki malama" nan da nan jikinta yayi sanyi ta cigaba da ɗibar kaya hawaye na gangarowa daga idonta, ga Mummy bata nan balle taji ba'asin hakan.

Ta zubo kayanta a akwatuna biyu, babba da ƙarama. Daddy ya miƙa mata hannu ya ce "Bani wayoyinki"

Cikin rawar murya Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ina zamu?" Tayi maganar tana bashi wayoyin.

"Biyoni a baya, idan mun je kya gani" Daddy yayi gaba cikin sauri.

Amina ta kalleta tayi murmushi ta ce "Ina fatan zaki ɗau darasi a sabuwar makarantar da zaki shiga nan gaba kaɗan, kuma ina miki fatan ya zame miki izina game da cin mutuncin mutane saboda suna talakawa. Idan ke a rashin mutunci kika ƙware to Yau zan tabattar miki da GABA AKWAI GABANTA!!!



Ayshercool
08081012143LITTAFIN NAN NA KUƊI NE, MAI BUƘATA YA TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA.
08081012143


74

Muryar Daddy suka jiyo yana cewa "Ki ɗago ƙafa ke nake jira" duk da yadda hawaye ke bin fuskarta, hakan bai hana Fadila watsawa Amina harara ba, Amina bata nuna ta damu ba, tayi mata dariya, Fadila kuma tayi gaba tana jan akwatuna.

Ko da suka fito falo, kallon sashin Mummy take kallo, tana ganin ko Mummy zata fito, amma ina Mummy bata nan tana can nata gantalin.
Motar Daddy ta shiga, ta saka akwatunanta a cikin motar ya fara driving yana yi yana duba wayarsa.

Cike da karaya ta kuma marairaicewa ta ce "Dan Allah Daddy ina zamu?"

Shiru Daddy yayi mata, ya cigaba da tuƙi, haka ta ka bakinta tayi shiru, don ganin Daddy ba shi da niyyar ya bata amsa.
Ɗaya gidan nasa suka nufa, yana zuwa aka buɗe masa gate ya shiga, yayi parking ya fita daga motar.
Ya dubeta ya ce "Fito" Fadila ta fito tana rarraba ido, kamar bata san gidan ba.

Ya dubeta ya ce "Wuce ki shiga ki jirani zan dawo".

Salo-salo Fadila ta nufi cikin gidan, kamar wadda aka yiwa mummunan baki.

Daddy kuma ya ɗaukar wata motar ya sake fita.

Zaman dirshen Fadila tayi a falon, tana ta tunanin meke shirin faruwa ne, me Daddy ke shirin aikatawa haka? Gashi ya karɓe mata wayoyinta balle ta kira Mummy.
Haɗe kai tayi da gwiwa tayi shiru tana nazari.

Fadila na nan zaune a cikin falon, aka yi sallar la'asar, ta tashi ta lalubi banɗaki, ta shiga tayi alwala tayi sallar la'asar, wata irin yunwa ce ke sakatar cikin Fadila, ta dudduba ta samu Fruit a fridge ta ɗan ci.
Wasa-wasa har magariba Daddyn bai shigo ba.
Tun tana saka ran Daddy zai dawo, har ta fidda rai ta cigaba da zama, ta fara saka ran ko dai Daddy ke niyyar hukuntata, shine ya kawota nan dan ya hukunta ta.
Bayan sallar isha'i, sai ga Daddy ya shigo.
Zumbur ta miƙe tsaye tana jin sanyi a zuciyarta, ganin Daddy ya shigo.

Ya kalleta ya ce "Oya taho mu tafi" a ranta Fadila taji cewar ko gida zasu koma? Amma da tuna uban akwatunan da Daddy ya sanya ta haɗo sai kuma jikinta yayi sanyi.

Amma ga mamakinta, sai taga bai nufi hanyar unguwarsu ba, ya ɗau wata uwar doguwar tafiya a titi.
Kallon Daddy tayi, tana son tayi magana, amma taga ya haɗe rai babu annuri a kan fuskarsa.

Haka ta cigaba da saƙe-saƙe a cikin zuciyarta.
Tun Fadila tana jiran taga Daddy yayi burki, har ta zubawa sarautar Allah ido.
Wata irin unguwa suka shiga, wadda tudu da kwarinta kawai sai da ya sanya Fadila jiri.
A ƙofar wani ɗan ƙaramin gida Daddy yayi parking.
Ya buɗe motar ya ce "Ta fito".

Fadila ta fito tana ƙarewa unguwar kallo, ko

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login