Showing 273001 words to 276000 words out of 296192 words

Chapter 92 - GABA DA GABANTA

kar su kuma yi maka wani abun, idan ba sa sonka ni ina sonka"

Murmushi ya yi ya ce "Kukan ya isa haka"

Ko Abinci da ƙyar ya tursasata ta ci, gaba ɗaya bata walwala, da magariba sai ga Hajiya ta zo gidan, dan ta kira Yazid wayar ba ta shiga.
Sai dai yadda ta ga Fadila kamar ta daɗe tana ciwo ne abin ya bata mamaki.

Ta kalli fuskokin duk babu walwala ta kalli Yazid ta ce "Yazid, me aka yi mata ne?"

Yazid ya ce "Bakomai Hajiya, kawai gajiyar tafiya ce"

Hajiya ta kalli Fadila ta ce "Gaya mini me suka yi miki, ko wani abun ya faru da kuka je?"

Fadila ta girgiza mata kai alamar a'a.

Ganin sun ƙi gaya mata komai, ya sanya tayi musu sannu da zuwa ta tashi ta tafi.

Wasa wasa ƙaramar magana ta nemi zama babba, dan kusan kwanaki uku Fadila a tsorace take, ta kasa sakin jikinta, ko fita ya ce zai yi sa taga kamar wani abu zai same shi, gaba ɗaya ya kasa gane kanta, sai koke-koke da take yi.
Gashi yanzu duk dare sai wannan ciwon kan ya tayar mata, sai ya kusa raba dare a kanta yana mata addu'a sannan take iya bacci.

Yau ma har ya fara bacci, ta fara mimmiƙewa tana kuka.
Yazid ya zaune ya riƙe kanta da hannunsa ya dinga karanto mata Alqur'ani.
Can tayi miƙa cikin wata irin murya ta ce "Dalla malam sakar mini kaina"

Yazid ya ce "Meye haɗinku da matata?"

Cikin wata irin murya ta ce "Kaga ba ruwanka da mu, aiki aka saka mu, kuma muke aiwatarwa dan haka kayi rayuwarka mu yi ta mu, ka barmu mu yi aikinmu"

"Waye ya saku aikin?"

"Babu ruwanka ka ƙyalemu"

Yazid ya ce "Ƙona ku zan yi, na daɗe ina zargin ko ku kuke shafarta, amma ban tabattar ba, yanzu tun da kun magantu zan ƙonaku ƙonawa ta har abada"

Girgiza kai ta hau yi, ta ce "A'a kar ka ƙona mu, dole mu cika aikin nan an riga an biyamu"

Yazid ya ce "Waye ya saka ku?"

"Amina ce ta je wurin uban gidanmu, shi kuma ya kiramu ya bamu aikin"

"Wacece Amina?" Yayi maganar yana sake riƙe kan Fadila.

"Wayyo Allahna, matar babanta wadda ta saka aka aura maka ita"


Cigaba da karatun Alqur'ani Yazid yayi babu ƙaƙƙautawa, wani irin kuka Fadila take yi tana gurnani kamar ba mutum ba.

"Wayyo Allah, kayi haƙuri ba Amina bace ba, ba ita bace ba"

Bai saurara da karatun ba, sai da jikinta yayi sanyi sosai, bacci ya kwasheta.


Ya zuba mata ido tausayin ta na ratsa shi, abin da Fadila take ta tsoro ya sameta.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kusan duk dare sai ta hana Yazid bacci, da safe kuma kusan wuni take da ciwon kai, ga yawan firgita da take yi, gaba ɗaya duk ta rame, gashi bata yarda ya yi nisa ya barta, in da Allah ya taimake shi an yi hutun makaranta lokacin.
Ba wanda ya san halin da ake ciki, kusan kullum cikin yi mata saukar Alqur'ani yake, da magungunan addinin musulunci.
Har ya ɗan samu ta fara warewa, ta rage yawan firgita da take yi.



Hajiya Zainab ta saka Daddy a gaba da tashin hankali da tijara, amma ya shareta ko a jikinsa, har Allah ya isa tayi masa amma yaƙi gaya mata in da Fadila take.
Amina kuwa yanzu Hajiya Zainab tausayi take bata, tayi-tayi Daddy ya sanar da ita in da Fadila take amma ya ce ba yanzu ba tukuna.


Yau Yazid bayan ya dawo daga makaranta, yana ta sauri kasamcewar tunda Fadila ta fara rashin lafiya baya fita ya daɗe, sai dai da ya je gidan ya tarar da shi a rufe, ya buɗe ƙofar ya shiga gidan da sallama amma shiru ba a amsa ba.
Ya yada ledar hannunsa ya shiga ɗaki da saur yana kiran sunan Fadila amma ba ita ba dalilinta!


(Tofa jam'a wa kuke tunanin ya yiwa Fadila turen aljanu! Kuma wane aiki aka saka su a kanta???)



Littafin kuɗi ne, a biyani hakkina kan a karanta.
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA
08081012143
82



A gigice Yazid ya cigaba da duddubawa yana kiran sunan Fadila, gaba ɗaya ya rikice sanin Cewar bata da lafiya, a gigice ya rufe gidan, ya nufi gidan Hajiya dan ya sanar da ita halin da ake ciki.

A tsakar gida ya tarar da Hajiya tana aiki, ɗagowa tayi ta kalli Yazid, ganin tamkar an wurgo shi babu ko sallama.

"Yazid Lafiya kuwa?"

Kamar zai fashe da kuka ya ce "Hajiya, Fadila ban ganta ba na je gida bata nan"

"To kuma shi ne zaka ɗaga hankali haka?"

Cikin damuwa ya ce "Hajiya ba ta da lafiya fa, Hajiya, Fadila Amana ce a wurina na je gida bata nan"

Ganin yadda idanunsa suka yi ja kamar zai fashe da kuka, ya sanya ta ce "Ikon Allah, lallai soyayya ruwan zuma kai da ita ban san wanda ya fi wani son wani ba, nan ta saka wata yarinya ta rakota, ba ta da lafiya babu kunya tun ɗazu take cewa wai haryanzu baka zo ba na kira mata kai?"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Tana ina?"

Hajiya ta ɗan yi murmushi ta ce "Tana ɗaki"

Da sauri ya shiga ɗakin, ya tarar da katifar Hajiya a falo, Fadila tana kai tana bacci gefe ga ledar magunguna.
Yazid ya durƙusa ya kai hannunsa jikinta, wani irin hucin zafi yaji yan fita daga jikinta.
Ya kai hannunsa wuyanta, ya ji tamkar an kunna oven saboda zafi.

Cikin magagin ciwo Fadila ta ce "Hajiya, Zid ɗin bai dawo ba?"

Yazid ya ce "Fadila, kin ganni nan sannu"

"Yauwa, Zid jikina zafi"

Cikin kulawa ya ce "Sannu, na je gida ba kya nan" miƙa hannu tayi, ta janyo nasa ta saka a wuyanta, tana lumshe ido.

Hajiya ce ta yi sallama ta shigo falon, ta dubi Yazid ta ce "Yazid ina ganin mu kaita Asibiti, nan suka zo ita da wata yarinya, wai ta je ta tarar da ita tana amai, wai tsoro take ji ta cewa Yarinyar ta rakota gidan nan"
Idanun Fadila a rufe ta ce "Maryam ce, ita na ce ta rakoni"

Yazid ya ce "To sannu"

Ta ce "Yauwa"

Hajiya ta ce "Kuɗin hannuna ba su da yawa, shine nace bari kafin ka dawo a san abin yi, na kira Nurse Sadiya, ta yi mata allurar zazzaɓi, ɗazu har ya ɗan sauka, amma yanzu ya kuma dawowa, sai kuma amai da take ta yi".

Yazid ya ce "Bari muje Asibitin akwai dubu huɗu a jikina"

Hajiya ta ce "Ni ma akwai dubu biyu a hannuna, amma ka je gida ka ɗauko mata wasu kayan, nayi-nayi ta cire rigar na bata zani taƙi, duk ta kuma ɓata rigar da amai, ka je ka kawo rigar ka taho da kayan shayi ta ɗan ci wani abu sai mu tafi"

Yazid ya amsa da to, ya koma gida ya ɗaukowa Fadila kaya, ya sayo kayan tea ya dawo.

Da ƙyar Fadila ta iya tashi zaune, tana jin yunwa sosai ga ƙishirwa saboda zazzaɓi, dan haka shayin nan da zafinsa da komai, ta kafa kai ta finga zuƙa ko sauke kofi ba ta yi, tana gamawa ta dawo da shi, tayi ta amai ba ƙaƙƙautawa.

Sosai Yazid yake jin tausayinta, ya gyara mata jikinta ya sauya mata riga, ya fita ya samo abin hawa, suka tafi Asibiti.
Wani ƙaramin Asibiti suka fara zuwa, nan da nan aka ce a kwantar da ita a saka mata ruwa, sannan a ka rubuta mata teses.

Fadila sai surutai take saboda zafin zazzaɓi, ta kira sunan Hajiya, ta kira Yazid, in anjima ta kira Daddy.
Hajiya ce ta cire hular kan Fadila ta dinga jiƙata da ruwa tana shafa mata.

Likitan ne ya shigo da sakamakon gwaje-gwajen a hannunsa, ya kalli Yazid ya ce "Kai ne mijinta?"

Yazid ya ce "Eh ni ne"

"To tana da ciki ne, yaushe ne period ɗinta na ƙarshe?"

Yazid ya ɗan yi shiru ya ce "Ai ina ga tun da muka yi aure ba tayi ba".

"Ok, wata nawa kenan?"

Yazid ya ce "Wata uku"

Likitan ya ce "Wow, so congratulations, but gaskiya akwai typhoid ga malaria duk a jininta, yakamata ku kula sosai, saboda wannan zazzaɓin illa ne a gareta da kuma ɗan cikinta"

Yazid ya jinjina kai cike da jin nauyin Hajiya da ke zaune a wurin.

Daga ƙarshe likitan ya ce "Zasu zauna har zuwa dare, ayi ta saka mata drip har jikinta ya ɗan yi ƙwari"

Yazid ya yiwa likitan godiya. Hajiya ta kalli Yazid ta ɗan girgiza kai ta ce "Allah ya inganta, sai ayi ta kula da ita, naga cikin nata da laulayi ya zo" Yazid ya sunkuyar da kai yayi shiru kamar mara gaskiya.

Fadila ta yi juyi ta ce "Zid"

Ya amsa da "Na'am, sannu"

"Yauwa, wai ciki ne da ni ko?"

"Mm haka suka ce"

"To dama ana yin haka ne? Watanmu uku da aure kuma cikina wata uku,ba sai an daɗe ake samun ciki ba?"

Yazid ya rasa amsa da zai bata, Hajiya ta riƙe hannun Fadila ta ce "Kiyi shiri da bakinki kin ji, sannu Allah ya inganta ya raba lafiya"

Fadila ta ce "Amin, Allah ya sa kaina ya daina ciwo"

Hajiya ta ce "Amin ya Allah, ko zaki ci wani abun ne?"

Fadila ta girgiza kai ta ce "Ina jin yunwa, amma idan na ci amai zan yi"

Haka suka cigaba da kula da Fadila, sai bayan magariba aka sallamesu, ga ɗan samu ƙwarin jikinta, suka tafi gida.

Yazid murna kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, saboda farinciki da samun cikin Fadila, sai lallaɓata yake yi. Sai dai abin tausayi duk da wannan wahalar da ta wuni tana fama cikin dare kuma aljanu suka hanata bacci.
Yazid ya fara wani tunani a kan lamarin nan na Fadila, dan yana ruƙiya yana cire wasu wasu kuma suna zuwa.

Washegari kuma cikin ikon Allah ta tashi jikinta da sauƙi sosai, da wuri Hajiya ta zo dubata, ta damo mata kunun gyaɗa ya sha madara ta kawo mata.
Fadila ta dinga kallon Hajiya tana jin ƙaunar matar a ranta, mussaman yadda tayi ɗawainiya da ita.
Tunani tayi a ranta, ta san da Mummy ce babu lallai ta yiwa ɗan wani haka, tana kewar mahaifiyarta tana son ta ganta, ko ba komai tayi mata nasiha a kan wasu abubuwan.

Hajiya ta daɗe a gidan, har Maryam ta shigo duba Fadila ita da Antynta.

Makarantar su Fadila kuwa sun yi cigiyarta har sun gaji, an kira lambarta bata shiga, gashi ita ba ƙawaye ba balle ace ga wadda ta san gidansu. Yazid yana jin ana ta cigiyarta amma bai ce komai ba yayi shiru da bakinsa.

Kwanaki biyu Fadila laulayi yayi sauƙi, sai rigima da kwaɗayi ba ta cin Abinci sam, ga Yazid abubuwa sai a hankali amma haka duk abin da tak so shi yake yi mata.

Yau ta tashi da cewa ita Cake ɗin Yusra zata ci, dan haka idan ya je makaranta ya je ya samu Yusra da nufin shi ne zai sayi cake ɗin

Duk abin da Fadila take so shi yake mata, sai dai idan ya aka zo wurin yin Adduoi ne idan ta yi masa taurin kai a nan ne suke yin faɗa.

Bayan ya je makaranta, suka samu free period, ya tafi department ɗin su Yusra, cikin sa'a ya ganta a kan barandar ajinsu a tsaye. Tana ganinsa ta yi murmushi tana faɗin "Wata sabon gani Yazid, ka ɓuya yadda Fadila ta ɓace kaima bana ganinka"

Yazid ya ɗan yi murmushi yana tanbayarta ya karatu.
Ta ce "Alhamdilillah, ka ga sai neman Fadila ka yi ka rasa ko?, almost 3months kenan, ni kaina ban san in da take ba, wai laifi ta yiwa Daddynta, ka san da har an kawo kuɗinta, ta tubure ta ce bata son mijin, shi ne Daddy ya ɗauketa, ni daga bayan nan kamar ji na yi amce wai ya yi mata aure, amma na san hakan ba mai yiwuwa bane ba, dan Allah ka tayamu da Addu'a Allah ya sa ya haƙora ya dawo mana da ita, baka ga yadda Mummy ke cikin damuwa ba".

Yazid cikin sanyin jiki ya ce "Allah sarki, in sha Allah tana in da ake kula da ita, Allah ya daidaita"

Yusra ta amsa da "Amin, kaga ga bikina ya ƙarato amma bata nan, tare muke shirya kowane tsare-tsare da zamu yi da bukukuwanmu, she's my best friend amma yanzu bata nan ina cikin damuwa" tayi maganar a sanyaye.

"Eyya kar ki damu, ki kwantar da hankalinki zata dawo Very soon in sha Allah, yaushe ne bikin?"

"Saura four months, zan auri abokin Yayanta, amma har yayan nata shi ma bai san inda take ba"

Allah sarki abota ba ƙarya ba, sosai fuskar Yusra ke nuna tana cikin matsananciyar damuwa.
Ina ga mahaifiyar ta kuma da ta kawota duniya, akwai yiwuwar ya je ya samu Daddyn Fadila ya bashi haƙuri ya sassauta mata hukuncin da yayi mata ko dan albarkacin masoyanta.

Yazid ya ce "Dama na taɓa cin irin vanilla cake ɗinki a wurin Fadila, shine nake so amma ban sani ba ko kina bada na dubu ɗaya"

Murmushi ta yi ta ce "Ko kyauta ka ce na baka ai zan baka Bestyn besty, kar ka damu gobe in Allah ya kaimu ba zan shigo school ba, amma zan bayar a kawo maka in sha Allah"

Ya ce "Madalla na gode sosai da sosai, ga dubun" ta girgiza masa kai ta ce "Ka bar shi kawai za a kawo maka in sha Allah".

Yazid ya ce "A'a dan Allah ki karɓa, abinki na sana'a"

Yusra ta ce "Fadila ma idan ta ci bata biya, kar ka damu" tayi maganar tana murmushi.

Ta wani fannin halinsu ya sha banban ita da Fadila, amma wasu lokutan Yusra ta fi sauƙin kai.

Yazid tayi ta mata godiya, sannan ya koma aji, yana ajin ne Daddy ya kira shi a waya, ya ce masa idan babu abin da yake yi yana son ganinsa.

Hakanan Yazid ya ji gabansa ya faɗi, ya shiga fatan Allah ya sa lafiya.

Bayan sun kammala lectures sun tashi, ya tari abin hawa ya tafi gidansu Fadila, suka gaisa da Zakiru, ya sanarwa da Zakiru cewar wurin Daddy ya zo.

Zakiru ya kira Daddy a waya ya sanar masa yayi baƙo, ya cewa Zakiru ace masa ya shiga.
Zakiru ya sanar da Yazid saƙon Daddy, Yazid ya doshi cikin gidan.

A falo ya tsaya yana duru-duru da tunanin ina shiga, Mummy ce ta fito daga sashinta, hannunta riƙe da jug, kallo yayi mata ya ga ta yi wata irin rama sosai da sosai, duk da ba wani sosai ya ganta a baya ba amma ta rame.

Durƙusawa yayi yana gaisheta, ta kalleshi a wulaƙance ta ce "Kai kuma daga ina zaka shigowa mutane gida haka har cikin falo?"

"A'a Mummy, dama Daddy ne ya ce yana son ganina"

Cikin mamaki ta ce "Ya ke son ganinka kai a wa? Me kayi masa yake nemanka".

Amina ce ta fito, dan jikinta ya bata wataƙila Hajiya Zainab ta hana shi shiga.

"Yazid sannu da zuwa, ƙaraso shigo yana ciki Daddyn"
Yazid ya ɗan risuna ya ce "Mummy bari in je" Tsaki Mummy ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Yazid kuwa ya bi bayan Amina zuwa katafaren falonta.
Ta nuna masa kujera ta ce "Bismillah zauna, bari na kira shi"

Ta juya ta nufi bedroom, Yazid ya ɗan ɗaga kai yana kallon falon, ya jinjina kai ya ce dole Fadila ta ce wannan gidan nasa ba gida bane ba, amma cikin ikon Allah ta haƙura ta zauna.

Daddy ne ya fito fuskarsa ɗauke da fara'a, ya ƙaraso cikin falon.
Yazid ya zube gwiwowinsa a ƙasa yana gaida Daddy.

Daddy ya amsa masa tare da saka hannunsa a nasa suka yi musabaha.

Daddy ya zauna cikin murmushi da kulawa ya ce "Yaron kirki na takuraka na maka kiran gaggawa ko?"

Yazid cikin murmushinsa ya ce "A'a bakomai Daddy, ai ban san kun dawo ba, da na zo sannu da zuwa"

"Kar ka damu bakomai, ya karatun ya matar taka?".

"Tana nan lafiya Daddy".

Amina ce ta zo ta jerewa Yazid Abinci, suka kuma gaisawa ta zauna a kusa da Daddy.

Daddy ya ɗan dubi Yazid ya ce "To Yazid ya ake ciki? Ta haƙura ta zauna ko akwai wata matsala idan da matsala ka gaya mini, a san abin yi dan na san idan akwai ɗin ma kai ba faɗa za ka yi ba"

Yazid ya ce "A'a Daddy, babu wata Matsala"

"A'a Yazid, kar ka yi mini hakinku na Fulani, kar ka yi kara ko ka ɓoye mini wani abu, ka gaya mini bakomai. Ni na san halin Fadila kamar yunwar cikina, na san kana nan kana fama da ita. Na yi mamaki ma da ta zauna tsawon wannan lokacin ba ta dawo ba" Yazid yana shirin yin Magana wayarsa ta fara ringing.

Ya ciro wayar ya ga Hajiya ce, ya kalli Daddy ya ce bari ya amsa waya.
Daddy ya jinjina masa kai.

Ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa, kasancewar ba ya ji sosai ƙasa-ƙasa yake jin muryar Hajiya, ya sanya ya saka wayar a hansfree.

"Hello Hajiya, ina jinki"

Hajiya ta ce "Yauwa, dama matarka ce ta zo ta sani a gaba, wai na bata waya zata maka magana"

Yazid ya ce "Ok to"

A shagwaɓe muryarta ta daki dodon kunnensa "Hello Zid"

"Mmm"

"Ka karɓo mini cake ɗin?"

"A'a ai kinga yau na gaya mata, sai gobe in Allah ya kaimu zata kawo"

"Mhmmm to ni fa yunwa na ke ji, Hajiya ta dafa doya ta bani, amma na kasa ci"

Ga Daddy a zaune a wurin, gaba daya kunya ta kama Yazid a hankali ya ce "To me zaki ci?"

"Idan kana da kuɗi, ka sayo mini mangwaro, sai abarba ta kan masu talla amma rabi nake so"

A taƙaice Yazid ya ce "To"

"Wai ya na ji kana amsa mini wayar da ƙyar ne kamar wanda ya je gidan sirkai, Zid ko wurin budurwa ka je?"

"A'a"

"To kayi magana mana"

"Gashi ina yi"

Fadila ta ce "Wallahi idan wurin budurwa ka je ka dawo zan gane"

Yayi murmushi ya ce "Ni ban je wurin kowa ba"

Fadila ta ce "Zid"

"Na'am"

"Ka ce kana sona idan ba wurin budurwa ka je ba"

Tayi maganar cikin shagwaɓa.

Cikin harshen larabci ya ce "Zan faɗa idan na dawo gidan"

Da hausa ta ce "Ni ban yadda ba, kuma ka taho mini da rake, idan ka dawo zan gane in da ka tafi ai"

Sauke wayar yayi a ƙasa kamar ya nutse da kunya.

Amina a ranta ta ce "Su o'o an gamu'

Daddy kuwa murmushi ya kasa barin fuskar sa ya ce "Lallai na yarda babu wata matsala, sai haƙuri ka san su rigimarsu ba ta ƙarewa"

Amina ta ce "Ai ku ɗin ne sai ana haɗa muku da rigima"

Daddy ya ce "Ai shikenan, Allah ya ƙara mana haƙuri"

Amina ta ce "Yazid, sai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login