Showing 138001 words to 141000 words out of 296192 words

Chapter 47 - GABA DA GABANTA

jakarta, tana kallon titi.


"Meenal, idan kunje ki kula da kanki sosai, ban da yawo, banda rashin ji, ki yi ta Addu'a Allah ya baku nasara, ya sa a samu abin da aka je nema"

"Amin, zan kiyaye idan Allah ya yarda"

"Yauwa Meenalina, yau zan samu Coffee ɗin dare?"

Ta ce "To, amma a dining zan ajiye maka, ka fito ka sha, ni bana son abinda zai haɗani da ita, kuma ni gaskiya tsoro nake ji, kullum in dinga zuwa falonka, ga Hajara ta saka mini ido, kuma idan matarka ma ta ga ina yawan zuwa wurinka ta ritsani ni me zance mata?" Sai da ya bari ta gama wassafa bayananta sannan ya kuma cewa "Can i get a Coffee tonight?"

A duk lokacin da yayi irin wannan, ta san yana son tabattar mata he is serious. Jinjina masa kai tayi alamar eh, ya cigaba da tuƙinsa sannan ya ɗan nisa ya ce "Idan na baki umarni, ko na nemi abu a wurinki, bana buƙatar ki kawo mini ko wane irin excuse, ina fatan kin gane?"


"Eh na gane, kayi haƙuri" bai ce mata komai ba suka cigaba da tafiya.


Gaba ɗaya a wannan karon karatun jarrabawa ba ya yiwa Fadila daɗi sam, dan abubuwa da yawa idan Yazid ya koya mata tafi ganewa kuma ta riƙe, amma wannan karon ita kaɗai take karatunta, gashi wayar ta sa ma taƙi shiga gaba ɗaya, kullum sai a ce mata tana rufe. Tana matuƙar tausayinsa da jin damuwar rashin zuwansa makaranta, amma babu wanda ta gayawa, ciki har da Yusra, dan ita bata son Yadda Yusra ke ƙoƙarin nuna mata cewar tana son Yazid.



Yau kamar Hajiya Zainab ta san Alhaji Ahmad ya shirya ganin Amina, taƙi yafiya ta je ta kwanta, ta saka shi a gaba a kan lallai sai ya bata kuɗin da ta nema a wurinsa na zata ƙara jari, shima kuma kamar ya san da wata a ƙasa sai ja mata rai yake, ya ce yau ya ce sai gobe, ba kuma dan ba shi da su ba, sai dai ya ce a cikin satin zai bata, sannan hankalinta ya kwanta, ta amince ta sako masa wata hirar kuma.

"Baban Khalil, yau na yiwa Khalil mata"

Daddy ya ce "To, Mata a ina kenan?"

" 'yar ƙanwar hajiya Salma ce, yarinyar nutsatsiya da ita, na yaba da ita sosai ga ta 'yar babban gida"

Ya ɗan kalleta sannan ya ce" Shi Khalil ɗin ya amince da hakan ne?"

"Ai kamar punishing ɗin sa zan a kan abin da yayi mini, kuma na san ba zai ƙi ba zai so ta ya manta za waccan yarinyar"

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ok, shikenan, Allah ya tabattar da Alkhairi"

Ta gyara zamanta ta ce "Amin, amma nan kusa nake son a kai kuɗin aure, ko kan mu tafi umarar nan ne"

Daddy ya ce "No, akwai wani abu da nake yi, sai na kammala zuwa idan kun dawo daga umarar, zan ga uban yarinyar tukuna"

To shikenan na gode sosai. Tayi maganar tana murmushi, ita dai idan har kaga walwala a fuskarta, to an biyewa ra'ayinta ne, ko da kuwa son zuciya ne. Suna nan zaune suna hira, Amina tayi sallama ta kai masa tea.

Hajiya Zainab ta kalleta a wulaƙance ta ce "Waye ya saki wannan aikin, an ce miki muna buƙata ne?"

Daddy ya yi saurin cewa "Ni nayi musu Magana ɗazu, na ce a kawo mini tea, zan yi aiki da daddaren nan"

"Ok ban sani bane" tayi maganar ba tare da zurafafa bincike ba. Amina dai ta ajiye kayan shayi tayi waje abinta, taji daɗin tarar da Hajiya Zainab da tayi, ba damar Daddy ya tsareta ya hanata tafiya.


Ana ya gobe su Amina za su yi tafiya, Baba ya kira Amina, ya zaunar da ita ya dinga yi mata nasiha mai shiga jiki sosai.

"Uwata, kinga ni dai zuwanki birni na barki ne dan ki samu ki cika burinki, na yin karatu, bani da burin da ya wuce ki samu ingantaccen ilimi, ki samu miji nagari, kin san ɗauki ba daɗi da kuma irin miyagun alkaba'in da aka dinga janyo mana, duk saboda na goyi bayan ki zauna da ni a nan kiyi karatu, dan Allah Amina kar ki bani kunya, kinga in da zaki tafin nan, baki da kowa sai Allah, dan Allah ki mayar da hankalinki, ki nutsu kiyi abin da kika je yi, ki riƙe mutuncinki, ba danni ba ba dan halina ba ki kula da kanki Amina, ki kula da mutuncinki, kije lafiya ki dawo lafiya, dan Allah kar ki watasa mini ƙasa a ido".
Gaba ɗaya jikin Amina yayi sanyi, ta ce "In Allah ya yarda Baba, ba zan baka kunya ba, ba zan aikata duk wani abu da ya saɓawa abin da ka ɗorani a kai ba in sha Allah"
"To madalla, Allah ya bada nasara, Allah ya kiyaye ku, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, ya bada abin da aka je nema, da salularki zaki tafi ko?"

"Eh Baba, sunce zamu iya zuwa da ita"

Baba ya ce "Yauwa, na dinga kiranki, in ji abin da ake ciki, zan so in rakaki ko makarantar ne, amma kin san idan nayi yinƙurin hakan, mutan gidan za su kya cewa nayi laifi"

Amina ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Zan so ka rakani Baba, amma bakomai Allah ya nuna mini ranar da zan rabaka da aikin nan, mu ci gashin kanmu"

Baba yayi murmushi ya ce "Amin uwata"
Sosai nasihar Baba ta ratsa Amina sosai, ta koma cikin gida, gefe ɗaya tana murna za tayi doguwar tafiya ta bar Kano a karo na farko a rayuwarta, wani sashin na zuciyarta tana fargabar ba ta san yadda tafiyar da competitions ɗin su zasu kasance ba.

Amina tayi ta saka ido, ko Daddy zai yi mata sallama ko su haɗu amma bai nemeta ba, gaba ɗaya sai taji babu daɗi hakan, har ta shirya da sassafe cikin goggagun uniform ɗinta, tayi kyau sosai, amma Daddy bai fito ba, a wannan karon Hajara ce ta kai mata Akwati har gaban mota, Fadila na kallonsu suna ta shirin tafiya, amma ko kallo ba su isheta ba. Baba yayi ta yi mata nasiha da Addu'a.

A wannan karon ma, Zakiru ne ya kai ta har makaranta, tuni an fito da zungureriyar motar makarantar su, sauran ɗaliban da ba da su za a je ba suka fito harabar makarantar ana kallonsu, ana ɗaga musu hannu, su Amina suka ɗuru a motar makaranta, suka kama hanya.



KU BIYONI BABBAN BIRNIN TARAYYA DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL



47

Hausawa suka ce tafiya mabuɗin Ilimi, Amina ta ga abubuwa da dama, wanda tun da take bata taɓa barin garin Kano ba, amma sai gata a hanyar babban birnin tarayya Nigeria wato Abuja, suna tafe a hanya ana tsayawa masu uzuri su yi da cin abinci, Baba yana ta kiranta a kai a kai yaji ya hanya, haka ma Ammin Azima tana kiranta, sai kuma ita da take kiran Inno, sai dai sam Daddy bai kirata ko sau ɗaya ba.

Sai Azahar su Amina suka sauka garin Abuja, a wani katafaren hotel da aka kama saboda saukar ɗaliban, Amina ɗakin da aka ajiyesu su uku ne a ciki.
Amina taji shiru, Daddy ya ce mata za a zo a tafi da ita gidan Abokinshi in da zata zauna, amma taji shiru, ita ba rashin tafiya da ita gidan abokin nashi ne ya dameta ba, rashin jin ɗuriyar Daddyna ne ya dameta.

Har zuwa dare bai kirata ba, dan haka ita tayi kasadar kiransa, domin jin ko lafiya.
Sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga wayar, cikin kamilalliyar muryarsa ya yi mata sallama.

Ji tayi kamar ta kashe wayar, dama yana nan normal amma yaƙi kiranta yaji ko sun sauka lafiya.

Muryarsa ta ji ya ce "Yaya kuma ki ka yi shiru? Akwai damuwa ne?"

Wani haushin ne ya sake kamata, wasu lokutan Daddy akwai iya kunna mutum.

"Bakomai" ta bashi amsa a taƙaice.

Ta kasa kuma cewa komai, shi ma kuma bai sake cewar ba duk suka yi shiru, ƙarshe Amina ta gaji ta kashe wayar ta ajiye.

Jin ta kashe wayar ya sanya Daddy sauke wayar daga kunnensa, ya bi wayar da kallo yana murmushi, ya ɗan kashingiɗa ya ce "Meenal kenan, dole ki saba da shiga damuwa a duk lokacin da kika mini laifi, na fuskanci wannan shi ne hukuncin da ba kya so"
Ya sake ɗaukar wayar, ya shiga gallery lock ɗinsa, in da yake adana hotuna, yana kallon hotunan ta, wasu hotunan shi ne yayi mata su, wasu kuma shi ya saka ta tura masa, ya dinga kallon hotunan yana murmushi, ya tsaya a kan wani hotonta da take sanye da uniform, ta goya jakarta tana murmushi, ƙuruciyarta ta fito sosai musamman yadda ta riƙe hannun jakar bayan ta goya jakar.

Ɗora wayar yayi a kan ƙirjinsa, yana jin wani al'amari yana fuzgarsa a game da Aminan.

A yau ne su Fadila zasu fara jarrabawar second semester, sai dai ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin ganin zuwan Yazid, haka nan taji hankalinta ya tashi, bata son ya rasa jarrabawar nan.
Kan ta shiga ajin ta samu wuri ta tsaya, ta kira shi a waya, sai dai wayar tayi ringing bai ɗaga ba.
Haka ta shiga ajin ta zauna, aka farra jarrabawa, amma babu Yazid babu dalilinsa gaba ɗaya sai ta kasa nutsuwa ta kasa rubutun jarrabawar, ji take ina ma zata iya yi masa jarrabawar bata manta taimakon da yayi mata a baya ba.

Jin ɗaya daga cikin invigilator ya ce "Sheikh sai yanzu?" Ya sanya Fadila ɗagowa da sauri.

Kasancewar har da TJ abokin Kankiya, a malaman da suke invigilating ne ya sanya ya dakawa Yazid tsawa ya ce "Get out, saboda ba ka san darajar jarrabawar ba, shine sai yanzu zaka zo jarrabawa, ka yi asararta kuwa, gobe idan kana so ka zo da wuri"

Ɗaya malamin ya ce "A'a yi haƙuri, na san ba zai makara intentionally ba, ya aka yi ka makara Sheikh" Kasancewar malamin sukan haɗa jam'i da Yazid a masallacin makaranta, ya sanya ya san shi.
Yazid ya ɗan yi murmushi ya ce "Afuwan Sir, na biya Asibiti ne an yi mini dressing, idan na makara ba za su yi mini ba"

Malamin ya ce "Meya sameka ake maka dressing?"

Yazid ya ɗan juya ya ɗagawa malamin rigarsa, sai ga plasta da aka saka a rufe masa wurin da aka yi masa aiki ya ce "An mini aiki ne, har sau biyu a wurin, ina zuwa ana wankewa duk bayan kwana uku"

Fadila kuwa sai leƙawa take kamar ita yake nunawa. Cikin tausayawa malamin ya yiwa Yazid sannu, tare da bashi wurin zama, ya bashi booklet ya kai masa question paper da Attendence har wurin zamansa duk yayi, ya yiwa malamin godiya, ya fara jarrabawar sa.

Sai da Fadila taga Yazid ya nutsu ya fara jarrabawa, sannan hankalinta ya kwanta, ta cigaba da tata jarrabawar, sai kuma ta tuna ai akwai abubuwa da yawa da aka yi baya nan, da yaya zai yi jarrabawar? A take ta tuna gwanancewa irin ta Yazid, ba abune mai wahala a wurinsa ba ya cinye jarrabawar ba.

Sai da tayi wannan tunanin, ta samu cikakkiyar nutsuwar cigaba da rubuta jarrabawata cikin nutsuwa.

Suna nan suna jarrabawa, Kankiya ya shigo yana zazzagaya su, yana wani muzurai da zare da ido, ya zo kan Fadila ya tsaya, yana kallon abin da take rubutawa, haushi ne ya kama Fadila, dan ko san ganin Kankiya bata yi, ta janye takardarta ta ajiye biron tare da haɗe rai.

Yayi ƙasa ƙasa da murya ya ce "Ina son ganinki yau, idan kun gama jarrabawa"

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Ba zan zo ba"

"Kin san me rashin zuwan naki yake nufi kuwa?"

"Ban damu ba, kaje kayi duk abin da kaga zaka iya yi".
Yayi murmushi ya ce "Kar in ɗau matakin da zuciyarki ba zata iya ɗauka ba"

"Nace kaje kayi duk abin da ka ga dama, kuma ka matsa daga kaina kan in yi Magana da ƙarfi in janyo hankalin mutane kanmu"
Ganin da gaske take zata aikata abin da ta ce, ya sanya shi yin gaba, yaje ya tsaya a kan Yazid ma, ya ƙure shi da ido, amma Yazid bai ko ɗago kansa ba, balle ya kalleshi, ya cigaba da rubutunsa.

Yau ma bayan kammala jarrabawar, Fadila sai da ta tsaya jiran Yazid, ya fito yana takwa a hankali kamar wank basarake, nan kuwa cuta ce ta sanya shi hakan, 'yan ajin suka yi ta masa sannu.
Sai da ta bari ya ƙaraso in da take tsaye sannan ta ce "Sannu ya jiki?"

Fuskarsa babu yabo ba fallasa ya ce "Da sauƙi Alhamdilillah"

Cike da tausayawa ta ce "Allah ya ƙara lafiya, amma kana jin sauƙi ko?"

Ya kalli cikin nasa sannan ya ce "Eh da sauƙi sosai, gashi ina iya tafiya sosai, kuma har nayi exams ma"

"Haka ne, amma nace naji kace sau biyu ana maka aikin, ko ka zo muje Asibitin nan da na kai ka ranar, su dubaka idan da wani sai suyi maka"

Ɗan ƙureta da ido yayi sannan ya ce "Kar ki damu, Asbitinmu na talakawa ma suna kula dani, na gode sosai" daga haka bai kuma cewa komai ba ya tafi.

Gaba ɗaya gani take kamar Yazid ya canza daga yadda ta san shi a baya.



Kafin fara gudanar da competitions ɗin da aka kai su Amina Abuja dominsa, aka ɗaukesu a motar makaranta zuwa wuraren shaƙatawa daban-daban, da buɗe ido.

Amina tana ta rehasal na abubuwan da zasu gudanar a wurin competitions, malamnsu na ta ƙara dagewa wurin tabattar da sun iya komai, saboda an gayyaci manyan mutane sosai.

Ranar farko da debate suka fara, Amina tayi rawar gani, ta burge da yawa daga cikin mutanen da suka je wurin, tayi ƙoƙari sosai da sosai tayi abin da ake so, tana da confidence ga kuma demonstrating na abin da take faɗa, wanda yake nuna kai tsaye daga zuciyarta take debate ɗin, a wannan karon makarantar su Amina ta samu nasara a kan Makarantar da suka kara tare, da maki mai tazarar gaske.

Sai azahar aka kammala na ranar, aka yi ta kaɗe kaɗe da raye-raye dan nishaɗantar da ɗaliban da kuma mahalarta taron.

Bayan su Amina sun koma masaukinsu, malamansu suna ta jinjinawa ƙoƙarinta, tare da sake ƙarfafa musu gwiwa.

Bayan sun koma ɗakin da suke, Amina tayi wanka tayi salla, ta nemi wuri ta kwanta, saboda ba yunwa take ji ba.
Knocking ɗin ƙofar ɗakinsu aka yi, Amina ta tashi ta buɗe, wata malamarsu da suka zo tare ta gani a tsaye, ta kalli Amina ta ce "Ki ɗauko kayanki ki zo"

Cikin rashin fahimta Amina ta ce "Ina zani?"

"Ki ɗauko kizo, dai ki gani"

Amina ta koma ɗakin, ta shiga tattara kayanta, wanda suke ɗakin suna ta tambayarta ina zata je, amma ta ce musu ita ma ba ta sani ba, ta ja akwatin ta futa ta bi bayan malamar.

A harabar hotel ɗin suka tarar da malaman makarantarsu, "Yauwa Amina, kin ɗauko komai naki ko?" Cewar Sir Patrick.

Amina ta ce masa "Eh"

"Mun yi waya da director, dama kan mu taho an ce mana idan mun zo za a zo a ɗauke ki" Sai a yanzu Amina ta tuna batun zama a gidan abokin Daddy, ta gyaɗa cike da gamsuwa da bayanin da malamin yayi mata.

Wata mota ce haɗaɗɗiya, mai baƙin glass tayi parking a gabansu, direban ya fito ya ɗau Akwatin ya saka a boot ɗin motar, ya buɗe mata ta shiga, tana ɗagawa malaman nasu hannu har suka bar harabar hotel ɗin, Amina ta gaida direban da harshen turanci, kasancewar shi ba bahaushe bane ba.

Amina a ranta ta jin jina cewar da alama shima abokin Daddyn babban mutum ne kamarsa.

Wata unguwa suka shiga, mai ɗauke da wasu irin haɗaɗɗun gidaje, kamar ba hannu ne ya ƙerasu ba, layin da suka shiga kuwa ko ina security ne suke kaiwa suna komowa, da wasu irin murguza murguzan karnuka, masu ban tsoro da suke sintiri a layin.

Bata gama mamakin gidaje da karnuka ba, direban ya tsaya a bakin wani ƙaton gate, ya shiga da motar cikin gidan, yayi parking a tsakanin wasu manyan motoci dake harabar gidan.

Harabar gidan kawai ba ƙaramin tafiya tayi da Amina ba, saboda yadda aka ƙawata shi, sai dai cikin gidanma akwai irin wannan karnukan, hakan ya sa taja ta tsaya a wuri ɗaya tana rarraba ido.

Direban ne yayi mata jagora zuwa cikin gidan, zuba ido Amina take taga mutan gidan amma taga bata ga alamar kowa ba.

Direban ya kalleta ya ce ta tsaya a nan ta jirashi, yana barin wurin tsoro ya kama Amina, ganin babu alamar motsin kowa.

Bai daɗe ba ya dawo ya ce ta biyo shi.

Amina ta kasa jurewa ta ce "Wai kuwa akwai mutane a gidan nan?"

Ya ce "Eh, muje ki gani wurin mutanen zan kai ki" ya karɓi trolleynta, Amina dai cikin zuciyarta Addu'a ta fara yi, saboda abin ya fara bata tsoro.

Wani falo ya buɗe suka shiga, wani irin sanyin AC ya daki Amina, ta tsaya tana kallon ikon Allah, wata uwar Tv dake falon kusan rabin bango, komai na falon na musamman ne.

Direban ya kalli Amina ya ce ta ƙarasa .

Ta kalleshi da mamaki ta ce "In ƙarasa ina? Ina mutanen gidan?".

Wata kujera ya nuna mata, bata hango waye a kai, bai jira me zata ce ba ya juya ya fice.

Gyaran murya yayi ya ce "Ƙaraso mana, ba a yanka mutane a gidan"

Waro ido tayi jin muryar Alhaji Ahmad.

Da ɗan ƙarfi ta ce "Daddy"

"Na'am Meenali" washe baki tayi tare da mamakin ganinsa. Shima murmushin yayi mata ya ce "Ƙaraso mana"

Ƙarasawa tayi ta zauna a kusa da shi, kamar yadda yayi mata nuni.

"Daddy dama zaka zo?"

"Eh mana gani na zo, saboda Meenalina ta ji daɗi"

Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Amma shi ne Daddy ko ka kirani kaji ya hanya, nayi ta kiranka baka ɗagawa?"

"Kin manta da kin mini laifi kenan?"

"Laifin me nayi kuma? Tayi maganar a marairaice.

"Nace ki kawo mini tea, nace kar ki kawo mini saina kiraki ina son muyi magana, amma kika daidaici ina tare da Madam kika kawo mini kika yi tafiyarki"

Cikin shagwaɓa ta ce "Kuma wannan har ya kai laifin da zai sa ka ƙi kiran wayata kaji ya nake nayi tafiya mai nisa?"

Yayi murmushi ya ce "Har kuka sauka ina kiran malamanku ina jin halin da kuke ciki, ke punishing ɗinki nake

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login