Showing 81001 words to 84000 words out of 296192 words

Chapter 28 - GABA DA GABANTA

masa kai, shi kuma ya ja motar ya fice.

Har aka yi lectures aka gama, Fadila na ankare da Yazid, a hankali yake komai, bashi da lafiya, faɗa ne ba zai yi ba, gefe guda kuma ta danganta abun da wulaƙanci da malamin ɗazu yayi masa, sai kuma ta tuna Cewar abu ne mawuyaci, kaga wani abu mai kama da fushi a tare da Yazid kome za a yi masa, wannan murmushi dai sai ka ganshi a fuskarsa.

Amina ta koma cikin gidan, tayi sallar la'asar, ta shiga kitchen, dan ta san babu lallai Hajar ta kuma yin wani abun, tunda kusan ita tayi aikin yau.

Tun azahar Fadila ta dawo gida, dan har tayi wanka ta kintsa ta dawo falo ta zauna, suna hira da Mummy.
Da sallama aka buɗe ƙofar falon, daga Mummy har Fadila suka mayar da hankalinsu kan ƙofar, wata farar mata ce ta shigo, ita da wata matashiyar budurwa, suturar da ke jikin matar kawai ya isa ya nuna maka Arziƙi ya zauna.
Suka yi sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana bin su da kallon rashin sani.
Suka ƙarasa cikin falon suka zauna, suka gaisa da Hajiya Zainab, ta amsa ba yabo ba fallasa, dan suma taga ba kalar talakawa bane.
Matar ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Na san ba zaki shaida ni ba, wannan 'ya ya ce Azima, suna Makaranta ɗaya da yarinyarki Amina, na shigo nan unguwar wurin wata ƙawata, Azima ta nuna mini gidan, nace bari in tsaya mu gaisa"
Mummy ta haɗe rai ta ce " 'yar aiki dai ko?"

Maman Azima ta ce "Eh to hakan, ai ɗa na kowa ne, dan in saya ya sanya na ce 'yar ki"

"A 'a ba wata sayawa, meye haɗina da ita da zaki jingina mini ita wai 'ya ta? Aiki kawai take mini" Mamaki ya kama maman Azima, yadda Hajiya Zainab ke zaƙalƙalewa, tamkar wadda aka dangantawa ɗan shege.

"To shikenan na fahimta, 'yar aikin ki, mu gaisa sai in wuce"

A wulaƙance Mummy ta ce "Sai ku jira ta fito, dan dai bani zan tashi in tafi yawon kira muku ita ba, ko kume tashi kibi wannan ƙofar, kitchen na nan, ki kirawota" tayi maganar tana kallon Azima.

Azima ta kalli Amminta, Ammi ta jinjina mata kai. Azima ta tashi, ta ta shiga ƙofar, cikin ikon Allah, ta tarar da Amina na ta aikinta.

"H Shanono" Azima ta faɗa da ɗan ƙarfi, Amina na waigowa taga Azima tayi tsalle ta rungumeta tana murna.

"Azima, ya akai kika zo baki gaya mini ba?"

"Ke sauri muke, Ammi na falo muje ku gaisa zamu tafi"

Cikin mamaki Amina ta ce "Dan Allah dagaske har da Ammi kuka zo, muje in ganta"

Tare suka fito falon da Azima, Amina ta ƙarasa gaban Ammi ta durƙusa tana gaisheta.

Cikin fara'a Ammin ta amsa "Lafiya ƙalau Amina, ya karatu Azima ta ce mini makarantarku ta zaɓe ki, a Quiz ɗin su na ƙasa"

"Eh Ammi"

"To a dage ai ta karatu, Allah ya bada sa'a, Azima ce ta nuna mini layn naku, na ce bari in Shigo mu gaisa"

"Amma kuwa naji daɗi Ammi, bari in kawo muku ruwa ku sha"

"Babanki ya saya ya ajiye ne?" Cewar Mummy, cike da son ta wulaƙanta Amina a gaban mutane.
Jikin Amina yayi sanyi ta sunkuyar da kai, Azima tayi mamakin abin da Hajiya Zainab ta faɗa, dan bata taɓa sanin irin zaman da Amina take kenan ba, saboda duk surutun Amina bata wannan zancen.

Ammi ta ce "Bakomai Amina, a ƙoshe muke ina da ruwa a mota"
Ta ƙarasa maganar suna miƙewa tsaye, jiki a sanyaye Amina ta ce "Bari in rakaku mota".

"Ke, da kika samu na barki ku ka gaisa, zaki wuce ki cigaba da yi mini aikina ko saina taso kanki?" Har cikinta haka Amina taji ɗacin dizgin da Hajiya Zainab ke mata a gaban baƙi, sai dai ta kasa daurewa sai da hawaye suka zubo mata, cikin ƙoƙarin mayar da hawayen, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Ammi ku gaida gida, Azima sai mun haɗu a school, next week za'a koma insha Allah, Ammi na gode sosai".

Kasancewar Ammi mai matuƙar son 'ya'ya, ya sanya ita ɗa ko ba nata bane yanzu zai shiga ranta, ba ta son biyewa Hajiya Zainab, zasu iya yin babu daɗi, dan ita ta zo gidan, kuma bata san me hakan zai haifarwa da Amina ba, haka suka bar gidan rai a matuƙar ɓace.

Ko da Amina ta koma kitchen, tana aiki tana kuka, kamar wadda babarta ta mutu.

Fadila ta gyara kwanciyarta ta kalli Mummy ta ce "Mum, meyasa ki ka yi haka? A Arziƙin da yake gidan nan, meye dan an bada ruwa?"

"To uwata, ai naji matar tana naniƙa mini yarinyar ne, gara in nuna mata matsayin yarinyar a gidan nan" daga haka Fadila ba ta kuma cewa komai ba.



Wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Hafsa da Khalil, duk da baya gari, amma kusan kullum suna tare a waya, gashi a wannan karon ya kasa samun excuse of duty ya koma gida, ko dan ya ga Hafsa, saboda yadda ya dinga komawa gida a kai a kai a baya.
Yanzu yana zaune a ɗakinsa yana video call da Abdul, yana sake labarta masa irin so da shaƙuwar da ke tsakanin sa da Hafsa. Har yake ce masa "Ka san wani abu, ina kuma dawowa gida, zan yi magana a gida a san abin yi, dan ginina na nan Abuja ya kusa kammaluwa.

Abdul ya ce "Mhmm haka ne, to yanzu tsakanin Mummy da Daddy, wa zaka fara sanarwa?" Ɗan Jimm Khalil ya yi, saboda Abdul ya tuna masa wani abu da yake yawan mantawa, ya san ko Daddy ya amince ida Mummy bata amince ba a isa an yi auren nan ba.

Nan da nan ya yiwa Abdul sallama, ya ajiye wayar ya dulmiya kogon tunani.

Ɓangaren Hafsa ma tun da Allah ya sa Khalil ya sanar da ita very soon zai turo iyayensa, take tunani wurin wa zai tura iyayen nasa? Dangin mahaifinta da basu ɗauke su a bakin komai ba ko kuma wa? Idan kuma dangin mahaifin nata suka mata sharri a wurin iyayen Khalil fa, mussaman idan suka ga suna da rufin asiri fa? Ire-iren wannan tunanin ya hanata sukuni, kuma ta kasa tattauna shi da kowa ciki har da Mama.


Amina tun tana jiran Daddy ya dawo, har ta fara gajiya, dama a falo take zaman jiran nasa, ta kasa karatun sam saboda damuwa da ɓacin rai, ta zubawa TV ido tana kallon wani Film a MBC2 Captain Philips, gaba ɗaya tausayin jarumin ya cika mata zuciya, ji take tamkar ta shiga ta kai masa ɗauki, bayan damuwar da take ciki, ta ƙara da ta film ɗin da take kallo.
Film ɗin ne ta samu ya ɗauke mata hankali, dan har ta fara tunanin ta ajiye masa Abincin a falo tayi tafiyarta, dan kowa ya kwanta sai ita kaɗai.

Sai wajen goma saura ya shigo Alhaji Ahmad ya shigo falon, ya shigo da sallama, Amina ta ɗan kalleshi ta amsa a hankali ta mayar da hankalinta kan tv.
Be kulata ba ya nufi sashinsa, da sauri ta ce "In kawo Abincin?"

"Dama kin ganni?" Ya faɗa ba tare da ya waiwayo ba.

"Eh" ta faɗa a sanyaye.

"Zan fito in karɓa, ki jirani" ya wuce abinsa.

Kawai Amina ta fashe da kuka, yadda aka mayar da ita kamar wata baiwa, kowa abin da ya ga dama yake mata, banda wulaƙanci wannan wane irin abu ne, bayan wancan jiran da tayi, sai tayi wani again? Ta cigaba da share hawaye, tare da dana sanin zuwanta birni.

Sai goma da rabi, Alhaji Ahmad ya leƙo falon ya ce "Yauwa kawo mini falona, ki haɗo mini da apple guda uku, sannan ki taho da littafinki da biro"
Amina ba ta amsa ba, ta tashi tana cigaba da share hawaye. Alhaji Ahmad ya bita da kallo, da tunanin meye ya sakata kuka.

Ta ɗauko kayan Abincin, ta nufi sashin Daddy, tana ta Addu'a, tare da ƙudurce tana kai masa zata ajiye masa ta fito.

Sai dai da ta shiga taga baya falon, ta tsaya saroro tana bin falon da kallo.
Ta wani corridor ya leƙo, ya yi mata alama da hannu ta zo, gabanta ne ya shiga faɗuwa, tabi bayansa tana waige-waige, dan bata taɓa sanin da wurin ma a cikin gidan ba.

Wani ɗaki ya buɗe ya shiga, Amina ta tsaya daga ƙofar tana leƙa ɗakin, ya haɗu ɗakin, an malaleshi da wani irin lallausan carfet, ga wani irin sanyin Ac da ƙamshin turare da ke tashi, sai kuma computer ta kai goma sha biyu a cikin ɗakin.

"Ƙaraso mana" yayi Maganar yana ƙoƙarin kunna wani socket,kamar sokuwa haka ta ƙarasa shiga, tana waige-waige, ya nuna mata in da zata ajiye masa Abincin. Ta zo ta ajiye, zata juya ta fita, ya ce "Zo ki zauna a nan" ya nuna mata kujerar dake gaban wata Computer. Da ƙyar Amina ta ɗan ɗosana ta zauna, fuskarta duk sauran hawaye.

"Kukan me kike?" Ai kamar ya kuma taɓo mata in da yake mata ƙaiƙayi, ta fashe da kuka.
Be kuma ce mata komai ba, ya zuba Abincin, tare da gyara zaman gilashinsa, ya fara ci, sai da tayi ta gama, yana danna system ya ce "Ina jinki, kukan me kike?"

Ji tayi kamar ta gaya masa abin da Mummy tayi mata, amma ta fasa ta ce "Bacci nake ji, kuma kaƙi ka zo ka karɓi Abincin, duk na gaji"

Murmushin gefen baki yayi ya ce "Ko dai ke da matar gidan ne, kike ƙoƙarin hucewa a kaina?"
Wasa ta shiga yi da hijjabinta, ba tayi magana ba.
Ya miƙa hannu, ya kunna system ɗin gabanta, ya shiga wani video, yadda ake koyar da tips na cin quiz a sauƙaƙe.
A nan ta mayar da hankalinta ta nutsu tana kallo, har tana jotting wasu abubuwan a littafinta, shi kuma ya cigaba da cin abinci.

A haka video ya ƙare, ta ɗago tana kallonsa, sai dai hankalinsa na kan system ɗin gabanshi yana dannawa.

"Kin gama gani?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To yi mini bayanin me kika fuskanta?"

Nan ta yi masa bayanin abubuwan da ta fuskanta.

"Masha Allah, kina fahimta sosai".

"To zaka tambayar mini Baba zuwa Abujan, kar in ta wahalar banza ina karatu?"

"Zaki je insha Allah"

"Zaka tambayar mini Baban?" Tayi maganar tana sake tattara hankalinta a kansa.

"Insha Allah, akwai abokina a Abuja, idan ma baya son in da za ajiyeki ne, sai ki zauna a can wurin abokina, zuwa a kammala ku dawo"

"To kai a ina kake aiki?"

"Lagos" ya bata amsa

"Amma aka ce a Abuja kake, kuma meyasa baka koma ba?"

"Eh na koma Lagos da aiki, na zo hutun ƙarshen shekara"

"To wannan computocin me kake da su?" Amina tayi maganar tana kallon ɗakin.

"Bayanai na, dana aikina ne a ciki"

Amina tayi murmushi ta ce "Aikuwa ina son in iya danna computer Wallahi, ka koya mini aikin da kake nima in dinga danna computer"

Alhaji Ahmad ya lumshe idanunsa ya a buɗe su a kan Amina, duk da baya son yawan surutu, amma abin da yafi buƙata a yanzu da shekarunsa suka fara ja, irin abubuwan ɗebe kewa, da zama ayi hira da shi, Hajiya Zainab kuwa hankalinta a kan kasuwancinta da kuma 'ya'yanta suke, bata fiye biyewa zama da shi ba, balle tayi masa hiraraki, shiyasa ya kan tsinci kansa da jin daɗin yawan tambayoyin Amina, da kuma surutan ta marasa ma'ana wasu lokutan.

"Ba ka ce komai ba"

"Me ma kika ce?"

"Aikin da kake a computer zaka koya mini, nima in dinga taɓawa"

"Sayar da kuɗi nake" ya bata amsa yana murmushi.

"Sayar da kuɗi kuma, ta yaya za a sayar da kuɗi kuma?"

"Ana yi mana, ni ina sayarwa" yayi Maganar yana murmushi.

Amina ta ɗan yi shiru ta ce "Ban taɓa ji ba".

"Yau ai gashi kin ji" ganin tana hamma ne ya sanya ya ce "tashi kije ki kwanta".

Amina ta tashi ta nufi hanyar fita.

"In biyoki da kwanukan ne?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi dan ta ji".

Ta waiwayo ta dawo ta kwashi kwanukan tayi waje.

Kashe komai yayi, ya tashi shima ya bar ɗakin, sai dai ya bar shi a buɗe bai rufe ba ya tafi ɗakinsa.

Da safe Alhaji Ahmad ya shirya da wuri, dan yana da wani uzuri na gaggawa.

Hajiya Zainab tayi masa rakiya, yana shirin fitowa ya tuna ƙaramar wayarsa a ɗakin Computers ɗinsa ya barta, ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Duba mini wayata a ɗakin aikina please"
Ba tare da ta ce komai ba, ta tafi ɗauko masa wayar.
Sai dai data tashi dawowa, yayi tozali da littafin Amina da ta bar shi a ɗakin a hannunta, ta nufo shi tana masa wani irin kallo da ya kasa tantancewa.


AYSHERCOOL
0808102143GABA DA GABANTA

BY

AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)





PAGE 28-29




Sai da hantar cikin Alhaji Ahmad ta kaɗa, saboda tsananin tsoron da ya shiga, har wata ƙishirwar wucin gadi ce ta kama shi, amma cikin dakiya da maziya ya maze ya bari ta ƙaraso.
"Meye wannan nake gani haka?" Tayi maganar tana nuna masa littafin.

Cikin rashin fahimta ya kalleta ya ce "Ban fahimta ba"

"Littafin 'yar aiki na gani a ɗakin aikin ka".

Alhaji Ahmad ya miƙe tsaye ya ce "Eh, na shiga zan yi amfani da ɗakin, amma duk yayi ƙura, duk da ba na shiga sai ina buƙatar yin aiki, ai Yakamata ki dinga sakawa ana gyarawa, ko gogewa ne ayi, ganin ba ayi hakan bane ya sa na bawa yarinyar umarnin gyarawa, ina ga mantawa tayi da shi a ciki". Har zuciyarta ta ji ta gamsu da bayanin da yayi mata.

'haka ne, hankalina ne bai kai a gyara ɗin ba, kuma nafi son idan za a gyara ɗin, a gyara ina wurin kar ayi maka ɓarna. A dawo lafiya"

"Yauwa na gode" ya amsa cikin mazewa ya juya ya bar Falon, yana yiwa Allah godiya da ya rufa masa asiri.


Amina kuwa da shirirtarta, tunani ta dinga yi a kan ta yaya ake sayar da kuɗi, kamar yadda Daddy ya gaya mata, amma bata iya gano ta yadda za'a sayar da kuɗi ba.
Lesson ɗin da take zuwa Makaranta ta fara gajiya, dan babu hutu sam, ga aikin gidan nan ba afuwa, kullum da abin da za'a ƙaƙalo a saka ka.



Yau Fadila a makare ta zo ita ma, motarta ta so ta bata matsala a hanya, sai dai tana zuwa ta tarar da kankiya ne a cikin ajin, bata ko bi ta kansa ba ta shiga ajin, sai dai ta hango Yazeed a wurin zamanta, a jikin window.
Tuno ranar da tayi masa wulaƙanci tayi, har ciwonsa ya tashi, dan haka ba tace masa komai ba ta zauna a kusa da shi. Wani irin warning glance sir Kankiya yayi mata, amma ta share shi, ta ciro littafinta daga jaka.
Gaba ɗaya annurin fuskar Kankiya ya ɗauke, ya ɗaure fuska gashi baya son ya aikata wani abu, da zai sa wani ya fuskanci son Fadila yake, kuma yana adawa da Yazid.
Haka ya gama lectures ɗin yana harar Fadila, ita kuwa ta nuna sam bata san ma me yake yi ba.
Bayan fitarsa ta ɗan saci kallon Yazid, ta basar, shikuwa ƙamshin turarenta ya hanashi sukuni.
Littafinta ya janyo, ya juya bayan yayi rubutu "Ina kwana ukuty?" Kallonsa tayi, gata gashi maimakon yayi mata magana, amma saboda wani salon rainin hankali shine ya rubuta mata.

Banza tayi masa taƙi kulashi. Ya sake rubuta mata 'Ya kika yi shiru, ko in tasar miki daga wurinki, naga kin haɗe rai?"

Babban abin da ya bata mamaki,bai wuce yadda yake rubutun da irin handwriting ɗinta ba. Kallonsa tayi cikin mamaki tana sake kallon rubutun, ba wanda zai ce ba nata bane.
Ganin tana kallonsa tare da kallon rubutun ne ya sanya shi ɗage mata gira ɗaya.

"Talk" ya sake rubuta mata.

"Bani littafina, tun da kurmancewa kayi yau"

Murmushi yayi ya ce "Ban kurmance ba, azumin magana nake".

Ta zura littafin a jaka, ya miƙo mata wasu takardu, tasa hannu ta karɓa tana dubawa.
Presentation ɗin da za suyi ne, na 'yan group ɗin su gaba ɗaya yayi musu, kuma a rubuce ya kai fullscap bakwai,tabi tsararren rubutun nasa da kallo, sannan ta kalleshi cikin mamaki 'Wai duk daga jiya zuwa yau kayi wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amma ai ka wahalar da kanka da yawa, wannan uban rubutun haka? Shikenan Sai mu kai Cafe a buga?"

Duk da yau baya son yin Magana, amma yaji daɗin yadda ta yaba ƙoƙarin sa.
Dan haka ya ce "Eh, da ina da babbar waya ko system, da a ciki zan mana sai ayi printing, kowa a bashi wanda zai yi presenting"

Fadila ta ce "System ɗina na mota, bari in ɗauko sai in fara typing ɗin, kar aikin yayi maka yawa" ƙarara yake ganin tausayawa a idonta.

"Muje in rakaki" Suka tashi suka jera zuwa in da motarta take, ta buɗe ta ɗauko system ɗin sannan suka dawo aji.
Ya nemi wuri ya zauna, ta buɗe system ɗin ta kunna, hotonta ya bayyana a kan lock screen, ta saka password sai ga wani ya bayyana a wallpaper ɗin ta, ba ƙaramin tafiya da Yazeed hotunan suka yi ba.

Amra ƙawar Fadila a baya, banda yanzu da ta daina shiga sabgar ta, saboda Amran na da wasu halaye da ba su yi mata ba, ta ƙaraso in da su Yazid suke zaune, suka gaisa sama-sama da Fadila. Sannan ta kalli Yazeed ta ce "Yaya Yazid dan Allah wurinka na zo, 'yan group ɗin mu zaka ɗan taimaka mana a kan presentation ɗin da zamuyi"

"A yanzu dai aikin namu yake yi, kuna iya jira zuwa ya gama" Fadila ta bata amsa.

"Bafa da ke nake ba" Amra ta mayar mata da martani.

Yazeed ya ce "Afuwan Amra, bari in kammala namu, sai in zo"

Guntun tsaki Fadila tayi, ta cigaba da operating system ɗin.
Janyo System ɗin gabansa yayi, dan a ganinsa bata sauri a typing ɗin, tunda ya zuba yatsunsa a kan keyboard ɗin nan yake sarrafasu cikin gwanancewa kamar wani inji. Fadila ta ƙureshi da ido, shi kusan komai ya iya, ana batun Mutane gifted bata taɓa gazagata hakan ba, sai a kan Yazeed.

Ji tayi kamar ta tambayeshi a ina ya koyi computer, amma ta basar.

Lokacin sallar azahar yayi, Yazeed ya ce "Zai je yayi sallah, idan ya dawo zai cigaba.
Ta tashi ta bashi wuri, ya tafi salla, ita ma tashi tayi ta bar System ɗin a wurin saboda careless, ta tafi yin salla da cin abinci.
Bayan ya dawo ya tarar da komai yadda ta barshi, ya zauna ya tattara mata litattafanta, minimising yayi, ya zubawa kyakywar fuskarta da ke kan screen

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login