Showing 213001 words to 216000 words out of 296192 words
wa kika bawa?"
"Baƙi nayi na basu"
"To shikenan, babu laifi ai kece"
Ta gyara kwanciyarta ta ce "Mhmmmm, Daddy nikam nayi mamakin yadda lokaci ɗaya Fadila ita ma ta sauya maka, duk da irin soyayar dake tsakaninku ban yi zaton za tayi avoiding ɗinka haka ba"
Daddy ya ce "To ya zanyi, tunda abin da mahaifiyarta ta ɗorata a kai kenan"
"Ni bana son a zargeni da laifin rabuwar kan iyalanka, amma ya batun aurenta ne, naji kace itama zaka zauna da iyayen wansa zata aura ko?"
"Ehh, dan sonake kafin muyi tafiya , mu zauna da su mu tsayar da lokaci".
"Amma kayi bincike a kan wanda zata aura ɗin?"
Daddy ya ce 'Koma waye ba uwatta ce ta kawo shi ba, ita ta zaɓa mata shi ba, na san ba zata zaɓa mata wanda bata so ba ai"
Amina ta ce "Haka ne, Allah ya sanya albarka"
Ya amsa da "Amin"
Har sun fara shirin kwanciya, Amina ta ce "Daddy, yakamata kaje wurin Fadila, ka ɗan kwantar mata da hankali na san tana cikin tashin hankalin rashin sanin in da mahaifiyarta take, ni kaina na fara tsoro ace ba wanda ya san in da ta tafi"
Daddy ya ɗan numfasa ya ce "Amma ai tana da hankali, koma ina take zata dawo, tunda bata da in da yafi nan".
"Haka ne, amma ka san ɗa da uwa, kaje ka ga halin da take ciki". Amina tayi ta lallaɓa shi, ya je ya samu Fadila.
Yana zuwa ɗakinta ya tarar da ita a zaune tana kuka.
Ya ƙarasa in da take ya zauna ya ce "Ki daina wannan kukan haka, is ok, mamanki koma a ina take ina da yaƙinin tana cikin ƙoshin lafiya, tunda da kanta ta fita, kuma na san zata dawo, ki daina wannan koke koken haka"
Jinjina masa kai kawai tayi, ba wa dan zata iya daina kukan ba, sai dan fatanta ya gama maganar ya bata wuri, ta samu ta cigaba da kukan, dan koma menene shi ne sila.
Haka ta nuna wa Daddy kamar ta haƙura, bayan fitarsa kuwa ta cigaba da kukanta, tana yi tana tsinewa Amina saboda ita ta janyo musu wannan lamarin, da suna zaune cikin kwanciyar hankali amma duk tabi ta hargitsa musu gida.
Yazid bayan ya koma gida daga gidan su Fadila ya ga kayan da Amina ta bashi yayi ta mamaki, saboda kai da gani ka san shaddojin manya ne, ga naira dubu ashirin a cikin envelope, har da turare mai kyan gaske.
Mamaki ya dinga yi wacece Amina, saboda Fadila ta taɓa gaya masa Cewar su biyu ne kawai a gidansu ita da yayanta, kuma babu ta in da Amina ke kama da Fadila, balle ya ce ko ƙanwarta ce, haka dai yayi ta mamaki shikaɗai. Da daddare sai da ya kira Fadila, yaji ya ta wuni, amma wayar ta ƙi shiga sam haka ya haƙura.
Washegari da Safe, Daddy ya karya, yana nan a gida, har wurin ƙarfe sha ɗaya na safe, sannan ya fito da niyyar ya fita.
Sai dai yana fitowa ya tarar da Fadila na safa da marwa a falon, idnunta duk sun kumbura alamar bata samu isasshen bacci ba.
Ya dube cikin nutsuwa ya ce "Fadila, meyasa baki tafi makaranta ba?"
Cikin rauni ta ce masa "Mummy bata dawo ba"
Alhaji Ahmad ya ce "Nace ki kwantar da hankalinki, duk in da ta tafi zata dawo, nima na kira wayarta bata shiga, amma ki kwantar da hankalinki, ki zo ki shirya ki tafi makaranta".
Ta girgiza kai ta ce "Daddy ba zan iya zuwa ba"
"Meyasa?" Kawai ta cigaba da share hawaye, ba tare da ta kuma cewa komai ba.
"Shikenan, ki samu ki yi breakfast, Meenal tayi girki, ki samu ki ci, zan san abin yi in sha Allah"
Meenal ɗin nan da Daddy ya ce, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba.
Suna cikin maganar suka jiyo muryar Amina tana faɗin "Daddy kayi mantuwa fa, ka bar wallet ɗin ka" Fadila ta kalli Amina, ita kanta ji take kamar ta shaƙe Amina kowa ma ya huta.
Amina ta ce "Muje na raka ka" Amina ta shige gaba ya bita a baya.
Sai da suka je motarsa sannan ya tsaya ya kalli Amina ya ce "Meenal, na fara damuwa da lamarin nan fa, ban san ina Zainab ta tafi ba, duk ta saka mini yarinya a cikin damuwa".
Amina ta ce "Nima kaina abin ya fara damuna, amma yakamta ace ko fushi take, zuwa yanzu a san in da ta tafi, ko dan saboda Fadilan"
Daddy ya ce "Haka ne, amma kin san ita wasu lokutan bata duba abu ta nutsu kan ta yanke hukunci, ita in dai abu yayi mata shikenan, bana jin Yarinyar nan ta rintsa ko ta ci Abinci"
Amina ta ɗna yi jimm sannan ta ce "Gaskiya bata kyauta ba, ni kaina Fadilan ta bani tausayi, yakamta kayi wani abu a kai"
Daddy ya ce "Kika bibiya tana wurin ƙawayenta, amma dai zan bincika in sha Allah"
"Alright, safe journey Sweetheart".
"Thank you dear" yayi maganar tare da kissing ɗin goshinta, ya shiga motarsa yayi gaba.
Tuni an canza wani maigadin gidan, Zakiru yana nan a direbansa da kula da harabar gidan.
Hajara ma tana nan, da fari Hajiya Zainab ta so ta fatattaketa, amma sanin cewar idan ta fatattaketa babu mai kula da sashinsu, ita da Fadila da sauran ayyuka ya sanya ta barta.
Amina ta dawo ta tarar da Fadila tana waya da Khalil tana gaya masa abin da ya faru, tana ta kuka. Sosai ta bawa Amina tausayi, amma ta san tana tankata zasu yi ba daɗi.
Amina ta je Kitchen, ta sanya Hajara ta haɗowa Fadila Abinci, suka fito falo tare.
Fadila kuwa waya take da Khalil tana. Faɗin "Yaya yakamata kayi wani abu a kai, ko ka kira Daddyn da kanka, dan naga kamar bai ɗau abin serious ba"
Khalil ya ce "Ki kwantar da hankalinki, za muyi waya da Daddyn in Allah ya yarda ba wani wurin ta tafi ba"
"To Allah ya sa, ka kira shi dan Allah"
Amina ta kalli Hajara ta ce "Ajiye mata kayan Abincin" Hajara ta ajiye kwanukan.
Amina ta kalli Fadila ta ce "Ga Abinci nan, babanki ya ce a baki dan haka na fita"
Fadila ta ɗago ido ta ce "Dalla malama kwashe tarkacenki ki bar mini gabana, nace miki ina buƙatar abincinki ne?"
"Idan ma ba kya buƙata a yanzu, a baya kin ci, kuma bana baki Abinci ne dan kin isa ba, duk dan na gyara fadata ne a wurin mahaifinki, ina fatan kin gane. Ni ba irinki bace ba zan wulaƙanta mahaifinki ba, ina biyayya ha umarninsa ne a matsayinsa na mijina, idan kin ga dama ki ci, idan kin so kuma ki watsar ke ta shafa"
"Zaki ga ni ta shafa, sai kin bar mana gida tunda nan ɗin ba gida ubanki bane, ko yau ya ga dama zai iya korarki"
Amina ta ce "Haka ne, Hajiya Zainab ma ba gidan nata tsohon bane, idan aka tashi korar ni da ita za a kora, gashi nan kan a koreta ma ta kori kanta" A zafafe Fadila ta miƙe ta nuna Amina da yatsa ta ce "Wallahi ki shiga hankalinki, ki fita daga sabgata"
"Kuskure mafi girma da zaki sake tafkawa, shi ne nuna ni da yatsa, ki kiyayeni kar ki ƙara" Amina tayi maganar cikin kashedi.
Hajiya Zainab kuwa, wayewar garin Allah da da sassafe suka shirya suka ɗau hanyar Nijar.
Da ita da Hajiya Salma, da kuma Hajiya Turai, suna tafe suna gaya mata yadda aikin malamin yake kamar yankan wuƙa. Gaba ɗaya idon Hajiya Zainab ya rufe, ba abin da ke zuciyarta illa taga bayan Amina da Alhaji Ahmad, ta wulaƙanta Amina tayi yadda take so da Daddy, dan a yadda take ji a ranta bata ƙi a kashe Amina ta huta da baƙin ciki ba.
Fadila na nan a ɗakinta zuciyarta a cunkushe, ji take ita ma tamkar ta bar gidan, saboda yadda zuciyarta ke mata babu daɗi, ga raɗaɗin miyagun maganganu da Amina ta gaggaya mata da suka sake haɗuwa suka dagula mata lissafi suka haifar mata da wani irin ciwon kai mai zafi.
Tana kwance idanunta a lumshe, saboda zafi suke mata a dalilin kukan da tayi, tana jin yadda wayarta ke vibrating, ta buɗe idonta da ƙyar, ta ɗauko wayar tana zaton ko Mummy ce, amma taga wata lamba daban. Har zata share sai tayi tunanin idan kuma Mummyn ce ta kirata fa?. Da sauri ta ɗaga wayar ta saka a kunnenta.
"Assalamu alaikum warahmatullah, Ukty"
Jin muryar Yazid bata Mummy ba ya sanyta yin shiru.
"Kina jina kuwa?"
"Eh" ta faɗa a taƙaice.
"Ina fatan kina lafiya?"
"Lafiya lau"
Ya ce "Ok, amma ya aka yi baki shigo school ba yau?"
"Bana jin daɗin jikina ne, shiyasa"
"Subhanallah, to Allah ya baki lafiya, kukan da kika yi ma zai iya saka ki rashin lafiya. Ki daina kukan nan haka"
"To"
Yazid ya ce "Yauwa ukty, sannan kiyi mini godiya Sister ɗinki ta bani kuɗi da kaya, da fari dai nace ba zan karɓa ba, amma ta matsa kiyi mata godiya dan Allah"
Fadila cikin rashin fahimta ta ce "Wace sister tawa kuma? Ai ni bani da wata sister"
Yazid ya ɗan yi Jimm sannan ya ce "Wata wadda ta fito bayan kin shiga gida, har ta karɓi car keys ɗinki a hannuna fa"
Wani malolon takaici ne ya ƙule Fadila, bayan da ta gano Amina ce, yarinyar ta fiye rawar kai, da neman gindin zama. Fadila ta ce "Ok, na sha magani ne, zan ɗan kwanta"
Ya ce "Alright, ba damuwa Allah ya baki lafiya" ko amsawa ba ta yi ba ta kashe wayar tana tsaki.
Hajiya Zainab tare da su Turai ne a gaban wani mutum, yana zaune a kan wani buzu, yayi rawani sai wani kasko a gabansa da yake ta fidda hayaƙi, gefe kuma ga ƙasa a cikin wani abin katako.
Ya dubi Hajiya Zainab bayan sun gama gaya masa abinda ke tafe da su.
"Hajiya ai ba a zama haka, kin yi sake da yawa, da fari a tsaye kike amma daga baya kika ga kamar kin gama shanye shi ki ka miƙe ƙafa"
Hajiya Zainab ta ce "Haka ne, amma yanzu meye abin yi?"
Ya ɗan kalleta sanann ya ce "Babu damuwa kar ki damu, komai zai zo da sauƙi, zan yi miki wani aiki a nan, sannan zan baki wani ki tafi da shi.
Ba wani abu ne mai wahala ba, zaki saka laya ne a hanyar da kika san Yarinyar zata taka ta wuce, da kanta zata bar gidan, sai turaren da zan baki, shima ki dinga turarawa zata ji kamar ana hura mata gida sai ta bar gidan ba zata iya zama da shi ba.
Shi kuma zan baki maganin da zaki dafa shi da nama ki bashi ya ci komai zai zo ƙarshe. Sannan zan baki wani ruwa, zaki dinga ƙara ruwan rijiya a kai kina sha kina wanka, sai yadda ki ka yi da shi".
Hajiya Zainab ta ce "Malam na gode sosai, nawa zan biya kuɗin aikin?"
Ya ce "Ai ba damuwa, wanan ne zuwanki na farko ki bayar da duk abin da ya samu"
Hajiya Zainab ta ɗauki kuɗi masu yawan gaske, ta ajiye masa, suma suka faɗi nasu buƙatun, ya basu magani suka tashi suka tafi.
Sai a dawowa sannan Hajiya Amina taga uban surƙuƙin wurin da suka je, dare yayi musu a hanya, sai Hotel suka kama suka kwana.
Khalil ya kira Daddy a waya, yana tambayarsa a kan ɓatan mahaifiyarsu, Daddy ya ce ya kwantar da hankalinsa, saɓani suka samu tayi zuciya ta fita amma ya san zata dawo.
Gefw guda kuma Daddy ya cigaba da shirye-shiryen tafiyarsa da shi da Amina.
Wasa-wasa tun Daddy yana basarwa, sai da aka kwana uku babu Hajiya Zainab babu dalilinta, gashi saura kwana biyu tafiyarsu, Fadila ko Abinci bata iya ci, balle ta je makaranta.
A kwana na huɗu suna zazzaune a falo, Daddy na rarrashin Fadila, duk tayi wani iri saboda damuwa.
Amina tayi juguum, dan abin ya dameta sosai saboda ita ce silar fitar Hajiya Zainab.
Suna nan zaune, suka ga an buɗe ƙofa, Hajiya Zainab ce ta shigo, hankalinta kwance.
Gaba ɗaya suka bita da kallo, Fadila kuwa ta tashi da gudu ta rungumeta tana faɗin "Mummy Ina kika tafi haka?"
Alhaji Ahmad ya kalleta ya ce "Zainab daga ina kike tsawon wannan lokaci, ba tare da na san in da kika je ba?"
"Au tambayata ma kake, baƙin cikin da na ƙunsa ne, na tafi naje na sha iska"
"Kuma shi ne zaki kashe wayoyinki, kalli halin da kika saka Yarinyar nan"
"Koma dai menene ai gani na dawo, dama na tafi ne dan na huce, kuma Alhamdilillah" tayi maganar tana danne fushinta, dan so take ta shawo kansa, har ta dafa naman nan ta bashi ya ci.
Girgiza kai kawai yayi, baya son ya biye mata, su dinga zubarwa da juna mutunci a gaban 'yar su.
Ta janye hannun Fadila zuwa ɗakinta, ta shiga rarrashinta.
"Am sorry Baby, baƙin cikin babanki ne ya isheni naje na huta, kiyi haƙuri na tayar miki da hankali"
Tayi ta rarrashin Fadilan, duk da Fadilan tayi mata mita saboda tashin hankalin da ta shiga.
Sai da taga Fadila ta samu nutsuwa, sannan ta fara tunanin yadda za tayi da Alhaji Ahmad.
Da yamma yana sashinsa tare da Meenal, Hajiya Zainab ta kira shi a waya. Yayi mamakin ganin wayarta.
Ya ɗaga yana tunanin dalilin da ya sanya ta kirashi.
"Hello Dear"
Daddy ya ce "Yau kuma?"
Ta ce "Eh mana, meye naga kamar kana mamaki?"
"Ai abun ne dole ya bani mamaki, ni da aka ce ba a ƙaunar ganina"
"Just forget please, kwana biyun nan na huce ai, i want my husband back"
"Anya kuwa kece?"
"Nice mana, ina son kazo kayi mini kwanaki na"
Ya ce "Hmm, to shikenan tunda ke kika buƙata, dama ni ban wulaƙantar da ke ba, i will be with you"
Tayi murmushi ta ce "Sai ka zo"
Yayi murmushi ya katse wayar yana jinjina kai.
Amina na jinsa, amma tayi kamar bata ji ba, ta cigaba da kallonta.
Satar kallonta yake yaga wani action zata yi, amma tayi banza da shi.
Ya san halin Amina a kan kishi, ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Meenal" ta kalleshi ba tare da ta amsa ba.
"Yau zan koma wurin yayarki"
Ta ce "Wow, hakan yayi kyau shi ne adalci, Allah ya taimaka" ta mayar da hankalinta kan kallo.
Tashi yayi daga in da yake a zaune, ya koma kusa da ita ya zauna, ya ce "Meenal"
Ta waiwayo ta kalleshi, ƙoƙarin ɓoyewa take, amma tsagwaron kishi yake gani a idonta.
"I know is not easy, but" ta ɗora yatsanta ta girgiza masa kai sannan ta ce "Mijinta ne fa na aura, me zai sa naji haushi kuma, ni dama ka je yanzu kwa fi sasantawa sosai, dan bana son yadda al'amuran gidan nan suke tafiya" ta miƙe tsaye ta ce "Zan je na cigaba da shirya kayana na tafiya, idan da wani abu you can let me know" daga haka ta wuce bedroom ta bar shi a wurin.
Har ga Allah Daddy baya son zaman doya da manjar da yake da Hajiya Zainab, dan haka yaji daɗin sakkowar da tayi. Gefe guda kuma bai ji daɗin mood ɗin Amina ba, duk da tayi ƙoƙarin dannewa.
Kai tsaye sashin Hajiya Zainab ya tashi ya tafi, ya tarar da ita kamar bai taɓa yi mata wani laifi ba, ta sha kwalliya tayi shar da ita, ta karɓse shi hannu bibbiyu tana ta nan nan da shi.
Sosai suke hirar yaushe gamo shi da ita, yana yi mata nasiha da rarrashinta a kan abubuwan da suke faruwa. Sai ta nuna masa ita bata buƙatar wannan zancen.
Da daddare yaje yiwa Amina sallama, saboda zai kwana a sashin Hajiya Zainab.
Yayi knocking ɗin ƙofar bedroom ɗin, saboda ya ji ta a kulle.
Amina ta zo ta buɗe masa, kamar kullum ta haɗe cikin sleeping dress ɗinta, tana ta ƙamshi.
Sai dai fuskar nan babu walwalar.
"Kin sallameni ne da kika rufe ƙofa?"
Ta ce "Eh mana, me yayi saura kuma?"
Yayi murmushi ya ce "Zuwa nayi na ganki"
"Ka ganni ai, kaje ka kwanta kar ka kasa tashi da wuri gobe in Allah ya kaimu" tura ta yayi cikin ɗakin yabi bayanta, ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ya rungumeta a jikinsa.
A hankali ta bawa hawayen idonta damar zubowa, wanda take dannewa kar su fito.
"I know what you feel my dear, but am sorry I know you are too young for this, a shekarunki kamata yayi ace ka kaɗai ce, amma kowane bawa da yadda Allah yake tsara masa rayuwa, kiyi haƙuri Babyna"
"Bakomai Daddy, tunda ina sonka, zan so ka da rahamar Allah kayi mana adalci, at least naji sanyi a raina da kayi hugging ɗina, good night kaje kar ta kuma yin fushi" ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce "I love You sweet"
"Love you more baby" tayi maganar tana murmushi. Kamar kar su rabu haka Daddy ya bar ɗakinta.
Gaba ɗaya sai taga ɗakin ya mata girma, tayi 'yan koke kokenta, ta haƙura ta cigaba da tasbihi har tayi bacci.
Daddy yayi mamakin tarairaya da rarrashi da ya gani a wurin Hajiya Zainab. Bai kawo komai a ransa ba sai ma farinciki na canzawa da tayi.
Da gari ya waye da sassafe, Hajara tayi manakin ganin Hajiya Zainab a Kitchen, da duku-duku abin da bata taɓa gani ba kenan.
Da kanta tayi girki ranar, taje ta shirya a dining, ta banka wannan turarrn tun daga sashinta har falo sannan ta koma sashinta.
Amina kuwa gaba ɗaya kasa baccin safen ma tayi, bayan ta kammala tilawarta da adduointa sai ta fito falo.
Wani irin ƙauri ne ya daki hancin Amina, wanda ya sanya mata wani irin sarawar kai, ta hau tari.
Da ƙyar tarin ya tsagaita, taje ta bubbuɗe window, da ƙofa saboda ƙaurin ya fita, tana mamakin wane irin ƙauri ne haka.
Mamaki ne yakamta da ta ga dining da Abinci, a ƙarfe bakwai.
Ƙarasawa dining ɗin tayi, ta na bubbuɗe kwanukan.
Wani haɗaɗɗen farfesun nama Amina ta gani, ɗan kaɗan a cikin flask, take taji ranta ya biya, taji idan ba ta ci naman nan ba, zata iya mutuwa ta hau haɗiye yawu.
AYSHERCOOL
08081012143LITTAFINA NA KUƊI NE, ₦500 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
AISHA ADAM
JAIZ BANK
KO KU DUBA AREWABOOKS.
Har Amina zata rufe flask ɗin ta juya, ta kuma tsayawa tana kallon naman, sam bata kawo Hajiya Zainab ce ta dafa ba, ta zaci Hajara ce ta tashi ta kammala aiki da wuri ko akwai in da take son zuwa.
Amina ta ɗauki spoon, ta ɗan ɗiba ta saka a bakinta. Ya ji spices sai ƙamshi yake, duk da akwai wani ɗan ɗaci da tayi zaton kawai bakinta ne.
Amina ta