Showing 126001 words to 129000 words out of 296192 words
makaranta.
Aikuwa yana zuwa ya tarar da ita da duku-dukun nan tan mopping a falo.
Wutar falon aka kashe, hakan ya sanya ɗakin ya gauraye da duhu, da sauri ta waiwaya dan ganin meke faruwa.
Taku taji ana tunkaro in da take, sai dai ko ba a gaya mata ba, ƙamshin turarensa ya sanar mata da shi ne.
Sai da ya zo in da take sannan murya ƙasa-ƙasa ya ce "Good morning"
Shiru tayi taƙi Magana.
"Am talking fa, kuma kina jina"
Cikin basarwa da shagwaɓa ta ce "To meye yasa zaka tsorata ni?"
"Saboda abin tsoron baya baki wahala ko? Wai me nayi miki ne kike wani fushi da cin magani?"
"Ni ba fushi nake ba"
Yayi murmushi, ya sake sunkuyowa daidai tsawonta har tana jin numfashinsa a wuyanta ya ce "Faɗi gaskiya dai, idan ba fushi kike ba, meye na ignoring messages ɗina, ko dai ko dai?"
"Ko dai me?" Ta faɗa a tsorace saboda yadda jikinta yayi sanyi.
"You are jealous dear, stop pretending"
Kunna wutar lantarkin falon da aka yi ne, ya sanya su ɗagowa.
DOMIN SAMUN POSTING KULLUM GARZAYO KI BIYA KUƊIN VIP, KU TUNTUƁENI TA KAN LAMBAR WAYATA
AYSHERCOOL
08081012143.GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD AYSHERCOOL7724
43
Gaba ɗaya suka waiwaya dan ganin waye haka? Gaba ɗaya hankalin Amina ya riga ya gama tashi, Hajara ce a tsaye a wurin makunnin ƙwan, ganin duk suna zuba mata ido kuma sai ta hau kame-kame tana faɗin "Amm.... Ban san.."
Ɗauke kai Daddy yayi daga kallon in da Hajara take, ya mayar kan Amina ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Karki manta anjima zan aiko a kai ki banki, a buɗe miki account"
Noƙe faɗa tayi ta ɗan tura baki ta ce "Ni ba zani ba"
"Me kika ce?"
"Bakomai" ta faɗa taka sake tura baki.
Murmushi ya yi ya wuce sashinsa, Amina ta cigaba da mopping ɗin ta suka mayar da Hajar daidai da kujerun da suke falon.
Gaba ɗaya Hajara rasa abin yi tayi, a baya tunane tunanenta sun fi karkata ga zargi, amma a yau ta sake tabattar da abin da ke tsakanin Alhaji Ahmad da Amina wata alaƙa ce mai ƙarfi da girman gaske, wadda da alama alaƙar tayi ƙarfi sosai da sosai.
Kamar yadda Daddy ya ce, da kansa yaje makarantar su Amina, bayan an tashi sukaje banki, aka yi mata duk abinda yakamata, ya saka kuɗi a ciki naira dubu ɗari biyu.
Mamaki ne ya cika Amina ta ce "Daddy wannan maƙudan kuɗin me zan yi da su, idan Baba ya gane fa?"
Daddy ya ce "Ta yaya Baba zai gane, sai dai idan kece zaki gaya masa, kuma ai ba wasu kuɗi ne masu yawa ba, Zakiru zai kai ki ki sayi duk abin da kike so, ban fiye son shiga wurare bane saboda identity ɗina, ba dan ke ba wurare da yawa ba zan iya zuwansu ni kaɗai ba, kuma ni bana son a takura rayuta duk in da zaka sai da masu baka kariya"
"Amma meyasa baka so a ganka? Kar a ganmu tare aje a gayawa Maman su Khalil ko?"
Ya ce "Eh, kin san bana son ɓacin ranta da damuwarta"
"Eh amma ni kana son ganin nawa" tayi maganar da iya gaskiyarta.
"Mhmm, me yasa kike haɗa kanki da ita? Ita matata ce ke kuma"
Sai yayi shiru.
A ƙule Amina ta ce "Eh ita matarka ce, ni kuma 'yar aiki ba talaka mara galihu"
"Yauwa Ashe kin sani, amma ni bance miki talaka mara galihu ba" yayi maganar da salon ya sake kunna Amina.
Aikuwa ta kai ƙololuwa dan taji haushi ba kaɗan ba.
"Banda rigima irin taki, ina na taɓa ganin wannan ƙarfin hali in ba a wurinki ba, nace kina son mijinta kince me zaki da tsoho".
Cikin tsiwa ta ce "Allah ya kiyaye in yi kishi da wannan matar, ta kasheni da bala'i wadda ba ta san darajar ɗan Adam ba"
"Zaki fara ko? Ban gaya miki bana so ki dinga duk wata magana da zata shafi matata ba".
Amina ta ce "Amma ai kai ka fara bani ba, wallahi Daddy seriously yakamata ka kula sosai, Allah ya baka dukiyar da zaka amfanar da al'umma, amma an gindayeta wuri ɗaya daga ita sai iyalanta, duk wanda ya raɓoka zai mora an dinga yi masa gori kenan da kallon banza, wallahi idan baka gina lahirarka ba daga ranar da ka mutu, wanan dukiyar aka raba musu, su sadaka ma Allah ya kai ladan kabarinka sai wanda ya dubi Allah.
Na san naganganuna sun yi tsauri da yawa, amma dan Allah kayi haƙuri Daddy, wallahi gaskiya nake gaya maka. Dan Allah yanzu dan Allah ya baku arziki ya dace aje aci mutuncin 'yar mutane dan Khalil ya ce yana sonta, ba a gabana aka yi ba, amma yadda ya zo yana faɗar zancen naji zafi sosai saboda nima tsatson talaka ce, da na motsa a gidan nan sai kyara da gori, wallahi Daddy kaf mutanen da ke aiki a cikin gidanka suna yi ne dan basu da wata sana'ar da zasu samu su rufawa kansu asiri, ban da haka mai zai sa ka zauna a gabanka ana kiran mahaifinka nusari, soko da sauran miyagun maganganu?" Ta ƙarasa maganar hawaye mai ƙarfi suka ƙwace mata.
Ba ƙaramin tasiri maganganun Amina suka yi a zuciyarsa ba, duk da ba wata babba bace ba, amna wasu lokutan tana da matukar hangen nesa da son faɗar gaskiya. Yana jinta tana kukan Amma bai rarrasheta ba kuma bai ce mata komaia ba, har tayi ta gama tayi shiru.
Wasa² rashin sanin halin da Yazid yake ciki ya addabi Fadila, tun tana dannewa har ta kasa ya kai ga ta kira Yusra a waya. Ta zayyanewa Yusra duk abin da ke faruwa.
Yusra ta ce "To ni yanzu da kika kirani me kike so in yi miki? Da kina da lambarsa ne ma sai a kirashi, ko kuma ki tanbaya a 'yan ajinku ko akwai mai lambarsa"
Cikin damuwa ta ce "An bani lambar na kira baya shiga"
"Wai to meye duk kika bi kika ɗaga hankalinki?"
Fadila ta ce "Haba Yusra, kamar ba a gabanki kinga halin da yake shiga idan ba shi da lafiya ba, ko da yake ke lokacin da kika zo ya farfaɗo, ni da muka kaishi Asibiti ban zaci zai rayu ba, yau fa ina miki maganar yafi sati baya zuwa school, aikuwa duk abin da zai san ya yaƙi zuwa makaranta ba ƙaramin abu bane ba"
"Na gane, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, ki cigaba da Addu'a Allah ya sa yana lafiya, da an san ko unguwarsu ne ma da anje an tambayi in da gidansu yake"
Fadila ta ce "Ni banji wanda yace ya san unguwarsu ba, shikenan dai sai anjima" ta ajiye wayar tare da dafe goshinta, gaba ɗaya tana cikin zullumi.
Khalil dauriya kawai yake yi, ko yaje zuwa wurin aiki sai dai baya iya wani abin kirki, lamarin Hafsa ha tsaya masa a rai nesa ba kusa ba, yana matuƙar sonta da tausayinta, baya son ta faɗa hannun wanda bai san ƙaddara ba, tsananin yardar da tayi da shi ne ya sanya ta gaya masa wani babban sirri na rayuwarta, da baga gayawa kowa ba sai shi, yanzu gashi Mummy ta shiga ta fita, yanzu da wani ta gayawa wannan sirrin ba shi ba, ha zamana kuma bai aureta ba, shikenan haka zai ta kallonta da abin koma yayi ta yaɗawa a gari.
Duk shirin da Amina take yi na zuwa ƙauye, da hidmar da take tayi da kuɗi babu wanda ya tambaye ta ina ta samu kuɗi, hatta wayar hannunta da aka wayi gari aka ganta da ita, Hajiya Zainab bata tuhumeta a ina ta samo ba, sai tsananin saka idanu da take fuskanta daga wurin Hajara.
Ita kuwa Fadila abin da ya dameta daban dan baka ba ta Amina take yi ba, dan idan ta ga dama sai ta wuni a ɗaki bata fito ba balle su haɗu.
Musamman da aka tashi daga makaranta, Amina ta tafi gidansu Azima, mamansu ta sa aka kaita wurin masu gyaran kai, aka wanke kan aka yi mata kitso ƙanana masu kyau, aka yi mata lalle ja da baƙi, sai bayan la'asar ta dawo daga gidansu Azima.
'yan kwanakin nan Daddy ya auri zaman falo, saboda kawai ha dinga ganin Amina, yana zaune shi da Hajiya Zainab Amina ta shigo gaba ɗaya ya mayar da hankalinsa kan Aminar, ba tare da Hajiya Zainab ta lura ba.
Amina na zuwa ɗakinta ta ajiye jakar makaranta, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kyan da kitson kanta yayi.
Wayarta dake kan mudubi ce tayi vibrating. Ta janyo wayar ta duba, sai taga saƙon Daddy ne "Lalle yayi kyau sosai, ki shirya mana dinner a dining yau, ina son zan sake gani"
Murmushi Amina tayi tana sake kallon lallen, tare da mamakin ya aka yi harya ga lallen nan.
Emojin murmushi ta tura masa tare da saƙo kamar haka "Ya aka yi har kaga lallen nan?"
"I watch everything about you, dan haka ba abin mamaki bane, zan jira a dining ki kawo Abincin dare in kuma gani"
Tana daga tsaye sai murmushi take tana bashi amsa, ta tura masa "A gajiye nake, Hajara ce zata shirya dining"
"Kin mai da ni kamar wani kakanki ko? Idan baki zo ba ba ke ba zuwa ƙauye, and i mean it"
Ɗan kwaɓe fuska tayi ta masa reply da "Tuba nake ranka ya daɗe, ba zan iya ɗaukar wannan hukuncin ba, zan zo in sha Allah"
Murmushi ne ya suɓuce masa da ganin abin da Amina ta rubuta masa.
"Ba zan haƙura ba, a haɗa mini fruit salad"
Tayi masa reply da "An gama as you wish"
"Wai dariyar me kake tayi ne kai kaɗai, ka tattara hankalinka a kan waya gaba ɗaya?"
Daddy ya ɗago ido ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Ke ma ba taki wayar ce a hannunki ba, hira nake da mutane na"
Ta haɗe rai ta ce "Mutanenka suwa kenan?"
"Nika ɗai nake rayuwa a duniyar ne, babu abokai da 'yan uwa da zan hira da su in murmushi?" Yayi maganar ransa a haɗe, tuna tana lallaɓa shi dan ta karɓi kuɗi a hannunsa ne ya sanya ta bar zancen ta sauya akalar zancen zuwa wani.
"Baban Fadila anya Khalil yana da hankali kuwa?"
Cikin rashin fahimta Daddy ya ce "Kamar yaya kenan?"
Ta ɗanyi ƙwafa sannan ta ce "Ko kiran wayata fa ba yayi, fushi yake da ni kenan?"
"I don't know, bana ce ba, ya kan gaisheni ni dai ta chat"
"Lallai Khalil, aikuwa zan nuna masa nice uwarsa, a kan yarinyar talakawa zai ɗau fushi da ni?"
Daddy ya ce "Idan yana sonta ki ƙyaleshi mana, Khalil fa ba yaro bane ya mallaki hankalinsa, he knows what is right for him, ki ƙyale yara su zaɓi abin da ya dace da rayuwarsu"
A fusace ta ce "Over my dead body, yarinyar fa a bakin titi take sayar da kayan shirme, ai ba kimar gidan nan bace kaje nemawa ɗanka aure gidan matsiyata, Allah ya suttura, haryanzu Khalil bai san me ya dace da shi ba, dan haka ni zan zaɓa masa mace 'yar gidan daraja ya aura"
Daddy ya ɗan gyaɗa kai sanan ya ce "Ba kya ganin hakan zan haifar masa da matsala? Karki aura masa 'yar mutane ya wahalar da ita, tun da ba shi ya ce yana so ba"
"Shi ya isa ya tsallake umarni na? Yaje ya yi ta fushin kar ya fasa, zan maganinsa ne"
Daddy dai be kuma cewa komai ba, ya cigaba da taɓa wayarsa.
Kamar yadda Daddy ya gaya wa Amina, yana dawowa daga sallar isha'i ya nufi dining yayi zamansa, yana jiran Amina.
Sai dai ko da Amina ta kammala girkin, ta shiga tayi sallar isha'i, Hajara ta je ta fara shirya kayan Abinci.
Ba tare da ya kalli Hajara ba ya ce "Turo mini Amina ta ƙarasa kawo Abincin"
"To" ta amsa gwiwa a saɓule.
Ta tarar da Amina a Kitchen, ta zuba ruwa tana sha, "Alhaji ya ce ki ƙarasa kai sauran Abincin"
"Ban da abu irin naki dama Hajara, ni da ki ka barwa girki nayi ai sai ki bari in ƙarasa ladana, amma na zo na tarar kin fara kaiwa" ta wuce ta ɗauki plates, da jug ɗin da ta yi fruit salad ta fice.
Hajara tayi ƙwafa ta ce "Ayi dai mu gani, Allah ya tona muku asiri muga ƙaryar iskanci"
Cikin sa'a Amina ta tarar Hajiya Zainab da Fadila ba su fito cin abincin ba, sai shi ka ɗai a dining.
"Kana ta kallona idan na faɗi fa?" Amina tayi maganar tana jere plates ɗin hannunta.
"Nace ki kawo Abinci in kuma ganin lalle, amma kika turo wata ko?"
Amina ta girgiza kai ta ce "Bani na turota ba"
Ya ce "Well, mu ga lallen"
Ta ɗago masa dogayen yatsunta, da suka lalle baƙi da ja.
"Wow Masha Allah, a yiwa lallen nan kuɗi zan saya"
Ta ce "Ai an riga an biya mai lallen, Babar ƙawata ce ta biya"
"Na san an biyata, wani biyan zan yi ai na musamman"
"Ni dai a'a ka daina bani kuɗi haka"
Muryar Hajiya Zainab suka jiyo tana waya, nan da nan Amina ta nutsu ta fara ƙoƙarin barin wurin, Da kallo Daddy ya raka Amina, yana jin ba daɗi zuwan Hajiya Zainab ta katse musu hira.
"Nifa gaba ɗaya na kasa gane kan yaran nan, kowanne da salon tsirfar da ya tsira, shi wancan yayi zuciya ya bar gida ya daina kula kowa, ita wannan ta tsiri zaman ɗaki, da rashin walwala na tambayeta wai pressure ne na karatu wannan wane irin abu ne?"
Daddy ya ce "Wani abu na damunta ne?"
"Yo ni ina na san mata, 'yar ganin dama, koma wani abu na damunta sai ta ga dama ai zan sani"
Alhaji Ahmad ya miƙe ya ce "Ba zai yiwu wani abu na damunta, kuma a zura mata ido ba.
Ɗakin Fadila ya nufa, yayi knocking sannan ya shiga, tana zaune a kan Carfet ɗin ɗakinta, hannunta riƙe da littafi tana kallo.
Alhaji Ahmad ya ƙarasa yana faɗin "Autana, karatun kike yi haka?"
"Eh Daddy" ta faɗa a sanyaye.
Shi kansa ya karanto damuwa a tatare da Fadilan, duk da gwnaace wurin iya tsiwa da surutu idan ta ga dam, but her silent part dominate the other side of her.
"Amma ya ban ganki a dining wurin Dinner ba?"
Tayi murmushi ta ce "Bakomai Daddy, kawai ina son yin karatuna a cikin nutsuwa ne, da kuma cin abincin nikaɗai kar wani abu ya ɗauke mini hankali"
Daddy ya ce "No, i want see you by my side, ta so muje in tabattar kin ci Abinci, sai ki zo ki cigaba da karatunki kinji sweetheart"
Tamkar ƙaramar yarinya, haka Daddy ya lallaɓota suka fito, ya riƙo hannunta zuwa dining yana yi mata hira.
Mummy ta kallesu ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Eh, da yake babanki ne ai gashi nan kin fito, ni da kika raina ce mini ki kayi in ƙyaleki ai"
Daddy ya ce "Please Madam, karki damar mini baby" yayi maganar yana zaunar da Fadila a kan kujera.
"Ka mayar da ita cikinka, ƙarewar Baby ma"
"Eh ba ruwanki da mu" Alhaji Ahmad yana matuƙar ɗaukar al'amuran Fadila da muhimmanci, dan wasu lokutan bai fiye damuwa da Khalil kamar yadda ya damu da ita ba, yake gudun abin da zai ɓata mata rai ba.
Sosai ya dinga ƙaƙalo hirarraki yana yi mata, a haka har ta ɗan saki jiki ta ci Abinci sosai, har zuciyarta ta fara raya mata ko ta gaya wa Daddy, abin da ke faruwa amma kawai ta share, ta kamala cin abincin ta tafi ɗakinta.
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau ne Amina zata je garinsu, tun bayan watanni tara da ta shafe bata garin nasu duk da ba rabuwar daɗi aka yi ba, kuma bata san wane irin karɓa za suyi mata ba, hakan bai hanata yin murna da farin ciki ba, na zuwa ganin gida da zata yi, musamman ganin Inno, da shi ne babbar damuwarta.
Da Asubar fari, ta ɗau akwatinta ta kai jikin motar da za su yi tafiyar a ciki, ta tsaya suna gaisawa da Zakiru, Zakirun hana tsokanarta "Ke fa yau kamar salla take a wurinki, zaki je gida"
"Zakiru waya ƙi gida, kowa ya bar gida ai ba bisa son ransa bane ba, gida akwai daɗi sosai"
Zakiru ya ce "Haka ne, Alhaji yayi mini maganar zan cigaba da koya miki karatu yana biyana, yaushe zamu fara ne?"
"Ehh, nima mun yi maganar da shi, ka bari in dawo daga ƙauye, sai mu sanya lokaci, yadda ba zai shafi aikin da muke ba, kar ya zama abin magana".
Zakiru kamar Amina ta taɓo masa in da yake masa ƙaiƙayi ya ce "Ke dai bari, wannan gida Allah ya nuna mana iyakar wannan mata, ke dai kije ki shirya da wuri, yanzun nan mu kama hanya"
Gyaran murya suka ji a bayansu, Zakiru ya ɗa rikice yan risunawa ya gayar da Alhaji Ahmad.
"Bamu wuri" Daddy ya faɗa ransa a haɗe, Zakiru ya bar wurin, Amina ta tsaya tana kallonsa.
"Can't you greet me?" Yayi maganar yana tsareta da ido.
Ta ce "To ai gani nayi ka haɗe rai"
"Ba dole in haɗe rai ba, kawai kin zo nan kina ta zuba da wani"
"Daddy Akwatina fa kawai na kawo ya saka a mota"
"Eh daga nan kuma kika tsaya surutu ba, kin gama shiryawar ne?"
Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Eh, na shirya kaya kawai zan saka"
Ya ɗan tsareta da ido sannan ya ce "Ki kula sosai, zan dinga kiranki a waya in ji idan kun sauka"
"To in sha Allah" tayi maganar tana kallon ƙasa.
"Yauwa, banda yawo idan kin je ki zamanki a gida idan ba in da ya zama dole ba, bana son yawo ki zamanki a gida kin ji"
Ta ɗaga masa kai alamar eh.
"Talk"
"To Daddy" ta faɗa a shagwaɓe.
"Idan ma kika tafi yawo, za a gaya mini kuma zan haɗu da ke, maza kije ki ƙarasa shiryawa kiyi breakfast, kuzo ku tafi" Amina ta jinjina kai, ta wuce ciki.
Cikin lokaci ƙalilan, ta kammala kintsawa, ta karya tana ta murna, Hajara ta rakota, har suka fito Hajiya Zainab bata tashi ba, dama lokacin tashinta bai yi ba.
A kan baranda suka tarar da Daddy, yana tsaye yana danna waya, Baba kuma yana gefensa a tsaye.
Murmushi Amina ta yiwa Baba ta ce "Baba tare zamu tafi?"
Baba ya girgiza kai ya ce "Ai ni naje na kuma komawa, ke kaɗai zaki tafi"
Tare da Daddy suka rakata har mota, cikin ƙasa da murya Daddy ya ce "Saura kije ki saki baki, kiyi ta hira da shi a mota" ba ta ce komai ba tayi shiru.
Ya ce "Safe journey"
Ta amsa masa da