Showing 201001 words to 204000 words out of 296192 words

Chapter 68 - GABA DA GABANTA

exams, ya sanya take gida, kusan kullum sai Baba ya kirata ya ji ya take.
Kullum idan taje makaranta tayi exams, gidansu Azima take wucewa, Ammi na kaita wurin wata mata 'yar Chadi tana mata gyaran jiki.
Jikinta yayi kyau sosai gwanin sha'awa.
Ta gama gyare-gyaren da zata yi a ɗakinta, ta fito falo ba tsammani taga su Hajiya Turai a zazzaune, Hajiya Zainab na gefe idanun nan jawur kamar an hura wuta.
Da fari sai da gaban Amina ya faɗi, amma ta maze ta ratsesu ta nufi Tv stand, ta ɗauki abin da zata ɗauka.

Hajiya Salma ta ce "Ga munafukar nan, algunguma tazo birni ta sha jar miya, ji yadda tayi ƙalau har da aure mai gida, shashasha mai kama da bulugari"

Amina ta yi murmushi ta ce "Wallahi nafi ƙarfin a kirani da mai kama da bulugari, sake kalla dai da kyau, ai wani kaya sai amale"

Hajiya Turai ta tafa hannuwa ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, haka kike zaune Zainab, baki kamata kin naɗa mata duka kin ɓata kamanni ba?"

Kamar Amina ta sharesu taji abin da ta zo yi ta bar musu falon,  amma taji cin mutunci yayi yawa, dan haka ta ce bari ta haɗasu tayi maganinsu.

Ta kallesu ta ce "Nifa bani da laifi a wannan abun, bani nace ya aureni ba. Wataƙila da kuna bata shawarar da ta dace, da mijinta bai aureni ba, wa zai ƙi auren mutumi Kamar Alhaji Ahmad, mutum nagartacce gashi tubarkallah mai kyau, ni ban auri mijinta dan in wulaƙanta ta ba, duk wutar ɗaukar fansar cin mutuncin da take mini ni da ubana na cigaba da ruruwa a zuciyata. Amma ki sani idan kika cigaba da cin zarafi na, zan rama abinda kike mini cikin kwanciyar hankali.
Kuma ina fatan ki cigaba da hawa keken ɓeran da suke ɗoraki a kai, ki cigaba da treating ɗin mijinmu kamar yadda kike yi yanzu, ni kuma haka na ƙara bani damar mallakar sa. Ki sani daga lokacin da kika yi yinƙurin kai hannunki jikina da niyyar ki dakeni, tamkar kina wasa da igiyar aurenki ne, dan a yadda yake ɗin nan, duk abin da zai masa shamaki da kasancewa da ni zai iya maganinsa, ni kuma ba zan so kashewa uwarɗakina aurenta ba. Allah ne ya bani mijin mashiririciya na aure"

Gaba ɗaya sai suka ƙame a wurin, aka rasa mai bakin magana.

"Zainab abinda kike ciki kenan a cikin gidan nan?"

"Gashi kuna gani da idonku"

Hajiya Salma ta ce "Lalli yarinya ta samu wuri, yanzu ni dai ki san ƙaryar da za a yiwa iyayen Kursum, dan sun saka rai sosai da sosai. Sannan a satin nan zan yiwa Baban Salim magana, azo ayi maganar auren su Fadila tun kan ita ma yayi sadakarta kamar yadda ya yiwa Khalil"
"Salma kaina ya kulle, ƙwaƙwalwata na saƙa mini miyagun tunani a kan Yarinyar nan, dole na shirya mu tafi Nijar ɗin nan, rashin lafiyar nan dake damuna ya sanya bance ayi tafiyar ba, ina fama da tsananin ciwon kai"

"Hmm ai a haka baƙin ciki zai kasheki, jajigewa zaki yi, ki saka rana mu tafi Nijar, kuma karki kuskura ki ɗaga masa ƙafa, ki tayar masa da hankali ki hana shi nutsuwa"

Suka yi ta zigata da rashin mutunci kala kala.



Khalil yana jin yadda yayi kewar Kano sosai da sosai, yana tafe yana kalle-kalle, yana tuna soyayyar sa da Hafsa, da yadda yayi matuƙar kewarta.
Da Azahar ya isa gida, sai dai Zakiru ne ya buɗe masa ƙofa saɓanin malam Hassan, bai damu ya tambaya ba, ya bawa Zakiru jakarsa shi kuma ya shiga cikin gidan.

Kai tsaye sashin Mummy ya nufa, sai dai kallo ɗaya yayi mata, ya shiga damuwa, saboda tsananin ramar da tayi.

"Mummy baki da lafiya ne?" Yayi maganar ba tare da yayi ko sallama ba, saboda yadda ya firgita.

Ɗagowa tayi ta kalleshi, da sauri ya ƙaraso inda Mummy ta ke, yana ƙoƙarin zama a kusa da ita cikin kulawa da tausayawa.

"Idan ka zauna mini a nan, sai na zabga maka mari"

Cikin Mamaki Khalil ya ce "Mummy meyafaru ne?".

"Ni kake tambaya, ubanka ya auri 'yar matsiyata ya kawo mini cikin gida, shi ne kai kuma kuka haɗa kai kaima zaka auri 'yar matsiyata, ka tashi ka bani wuri, kaje ayi maka aure, amma ba da yawuna ba"

"Wallahi Mummy ban gane me kike nufi ba, dan Allah meyafaru ne?"

"Ni zaka rainawa hankali, tashi ka fita ka bar mini ɗaki, tashi bana son ganinka. Saboda mace Khalil tun da ka sanya ƙafa ka bar gidan nan, baka sake waiwayowa ba sai yanzu, ka kyauta, kaje kai da uban naka kuyi duk abin da kuka ga dama, ku kasheni ku huta".

"Mummy.....

Ta katse shi ga hanyar cewa "Ka tashi ka bar mini ɗaki na gaya maka".

Jiki a saɓule, Khalil ya tashi ya fita, amma sam bai gane a kan me take wannan maganganun ba, ya kasa gane ina maganar ta ta ta dosa.

Lokacin da ya fito, Amina nata shirya Abinci a dining.
Kallo ɗaya Amina tayi masa, ta gano ya fuskanci matsala a wurin Hajiya Zainab, gaba ɗaya jikinsa a saɓule.

"Khalil ashe ka dawo?"
Khalil ya waiwaya ya kalli inda Amina take ya ɗan kawar da kansa ya ce "Yauwa".

"Ka dawo a dai-dai, mun gama abinci".

Dama Khalil yunwa yake ji, ya ce "Ok bari ina zuwa".

Ta cigaba da sabgoginta, Khalil ya dawo ya zauna ya fara cin Abinci, ya kammala ci, yana ta ƙoƙarin neman layin Abdul.
Amina ta sake fitowa ta zauna a kujerar da ke facing ɗin ta Khalil ta ce "wannan lokacin ka daɗe sosai ba ka zo gida ba"

"Eh aiki ne yayi mini yawa"

"Ban sani ba ko kun yi wata maganar da Daddy, amma zan so ace nice wadda zan fara yi maka wani albishir. Duk da ban sani ba ko kaima kana jin haushina".

Khalil ya ce "Meyasa zan ji haushinki me kika yi mini?"

Ta ce "Shikenan, mu bar wannan maganar, Daddy ya kai maka kuɗin aure 4days back"

Khalil ya ɗan yi saroro ya ce "Kuɗin aure kuma?"

"Eh, an kai maka kuɗin aure gidan su Hafsa"

"Ya aka yi kika san Hafsa?"

"Ba abin mamaki bane, ina tayaka murna"

Cikin mamaki da farinciki Khalil ya ce "Ya aka yi Daddy ya san da batun Hafsa? Amma dan Allah da gaske kike yi?"

"Idan baka yarda ba, in ya dawo ka tambayeshi"

Khalil ya ce "Subhanallah, ji nake kamar ina mafarki fa".

"Ke wace irin daƙiƙiya ce, kin bi uba kin dawo wurin ɗa, meye haɗinki da Khalil kuma?" Cewar Fadila da dawowarta kenan, ta tarar da Amina da Khalil.

Khalil ya ce "Wace irin magana ce kike yi haka Fadila? Magana kawai muke yi"

A fusace Fadila ta ce "Kai dai ban san meke damunka ba, Yarinyar da ta aure mana uba, ta jefa mahaifiyarmu a cikin halin ƙunci da damuwa, ta tafiyar da sashin farincikinmu ita ce har kake da damar zama kayi magana da ita?"

"Yaushe na fara wasa dake, da har kike gaya mini maganar da kika ga dama, shi Daddyn da ya aureta ba shi ya ga zai iya ba?meye abin wani tayar da jijiyar wuya, ni banga abin ɗaga hankali ba".

Cikin mamaki Fadila ta ce "Au haka ma zaka ce?"

Amina ta katse zancen ta hanyar cewa "Idan kayi confirming ina jiran tukuicin albishir"

Murmushi Khalil yayi ya ce "To shikenan".

Amina a ranta ta ce 'Wato su dai maza duk in da suke halinsu ɗaya ne, wato yana goyon bayan abin da mahaifinsa yayi, shi bai ga aibunsa ba. Lallai na samu damar da zan ɗanɗanawa Hajiya Zainab abin da ta ɗanɗanawa dangin Alhaji Ahmad, idan ta cigaba da wannan shirmen to tabbas 'ya'yan ma duk sai na ƙwace su, ai GABA DA GABANTA!".

Khalil na fita kai tsaye gidan su Abdul ya wuce.
Abdul yayi mamakin ganin Khalil.

"Kai mutumina, saukar yaushe babu ko kiran waya, angon Hafsatu bada kanka a sare".

Khalil ya kalleshi da mamaki ya ce "Au kaima ka san wannan zancen wai dan Allah da gaske ne ko wasa?"

"Ban gane ba, kana nufin baka sani ba?"

"Wallahi ban sani ba, ni ɗazu na dawo, Mummy na ta yi mini faɗa, ni ban gane a kan me take faɗan ba, sai kuma waccan Yarinyar da aka ce Daddy ya aura, 'yar Malam Hassan, take gaya mini"

Abdul ya ce "Au, ni bama muyi zancen ba, Yusra ta gaya mini wai Daddy yayi aure".

Khalil ya ce "Kai nifa ya gaya mini, na sani lokacin ina Abuja nayi rashin lafiya, har dubani suka zo yi tare, Daddy ya gaya mini yayi aure, ya gaya mini ita ya aura"

Abdul ya waro ido ya ce "Amma ya aka yi kai shiru ba wanda ka gayawa?"

"To Abdul me zance? Shi Daddy ai ya san dai-da ya san meye ya dace da shi, ni banga dalilin da ya sanya Mummy zata ɗaga hankalinta haka ba. Amma dan Allah Abdul ya aka yi ka san zancen kai kuɗin nan, kaina ya kulle meke faruwa ne?"

Abdul ya ce "Nutsu na yi maka bayani"

Khalil ya gyara zamansa, ya tattara hankalinsa a kan Abdul.

Abdul ya ce "Daddy ne ya zo har inda nake, yayi mini tambayoyi a kan alaƙarka da Hafsa da abubuwan da suka faru a tsakanin ku, lokacin kayi mini zancen wai na auri Hafsa, Daddy ya ce kar na ɓoye masa komai.
Na gaya masa komai. A nan yake gaya mini cewar yayi mamakin rashin gaya masa da baka yi ba, sai Amina ce ta gaya masa, nayi mamaki da naji ya ce Amina ce ta gaya masa, so ban dai matsa sai na ji ba. Bayan 'yan kwanaki ya kirani, ya sanar da ni cewar yayi binciken da yakamata a kan Hafsa, yaje wurin dangin mahaifinta sun tsaya yi masa wasa da hankali.
Abin ban tausayi limamin unguwar su ne ya karɓi kuɗin auren nata, bayan sun gama ɓatata a wurin Daddy, Daddy ya kuma yi mini bayani, na gaya masa abinda na sani a kanta, ya koma wurin Mamansu, ta gaya masa irin zaman da suka yi da dangin mahaifinta, shi ne yaje suka yi magana da liman ya bashi kuɗin Auren, babban abin da Daddy ya sake burgeni da shi, shi ne ya ɗauke musu kayan ɗaki, ya ce 'yar sa ce".

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Khalil ya sauke, ya ce "Abdul meyasa baka gaya mini ba?"

"To ai lokacin ana ta turka-turka, abun bai tabatta ba tukuna, yanzu da ya tabatta ba gashi ka ji ba"

"Abdul, tashi muje ka rakani gidansu Hafsa"

Abdul ya ce "A wannan uwar ranar, ka bari dai yamma tayi".

Sujudu shukur Khalil yayi a wurin, sai sauke ajiyar zuciya yake, kamar wanda aka biyawa bashi.

Abdul ya ce "Lallai mutumina ka shiga da yawa"

Khalil ya ce "Abdul, ba zaka gane ba, nikaɗai na san me nake ji"

"Naga alama, dan haka yakamata kaje ka yiwa Daddy godiya"

"Wannan dolene Abdul, amma dai yanzu ina nan sai naje naga Hafsa tukuna, na rasa me zan yi dan murna".

"Godiya zaka yi ta yiwa Allah kawai".


Fadila kuwa wurin Mummy ta wuce, tana cigaba da mitar abin da Khalil yayi.
Mummy ta ce "Ai ba tun yanzu ba, na gane Cewar Khalil bayan ubansa yake bi, da ni suke zancen, daga shi har shi, duk sai nayi maganinsu wallahi".

"Mummy ni dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki samu ki daina wannan damuwar, dubi duk kin rame kamar ba ke ba"

"Hmm Fadila kenan, bana fatan Allah ya gwada miki abin da nake ji a zuciyata, ke dai kawai ki cigaba da Addu'a".

"Haka ne Mummy, amma dan Allah ki dinga ragewa, bana jin daɗin ganin fuskarki a haka"

Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Shikenan na daina"



Abdul ya hana Khalil tafiya wurin Hafsa, sai wajen biyar na yamma.
Ya saka kayan Abdul dan baya son komawa gida a samu wata matsalar, wata dakakkiyar shadda sky blue ta Abdul ya saka da hula, yayi kyau sosai da sosai.

Hafsa na tsakar gida, ta gama girkin dare, tana yiwa Mama da ke ƙulla kuka hira.
Yaro ne yayi sallama ya gaida Mama ya ce "Wai Hafsa taje in ji Khalil"

Wani uban tsalle Hafsa tayi ta ce "Mama Khalil"

Mama tayi murmushi ta girgiza kai ta ce "Eh Khalil"

Gaba ɗaya Hafsa sai ta manta da batun kunya, da ma tsaf take tayi wankanta.
A gurguje ta canza kaya ta zari mayafi tayi waje.
Yana tsaye a ƙofar gidansu, ya zuba mata ido, ita ma kallon nasa take yi gani suke tamkar a mafarki komai yake faruwa.

Kawai Hafsa ta fashe da kuka.
Shi ma Khalil ji yayi kamar ya tayata kukan, amma ya dake ya ce "Da abin da zaki karɓeni kenan? Kuka kuma Hafsat"

Sake ƙaro sautin kukan tayi, har da sheshsheƙa.

"Shikenan, ya isa haka ƙaraso" ta ƙarasa suka zauna a dakalin gidansu.

"Babyna kinga ikon Allah ko?"

Kasa Magana Hafsa tayi, sai kuka da ta cigaba da yi.

"Dan Allah ki daina kukan nan haka, ki so kike nima nayi?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki daina muyi magana"

Ta share hawayenta, ta kalleshi ta ce "Ina wuni"

Yayi murmushi ya amsa mata ya ce "Ya kewata?"

"Daina tuna mini, tsawon lokacin nan kawai dai gani nan ne dai, amma ban san yadda zan misalta maka halin da na shiga ba"

"My dear, baki ga yadda na rame ba? Rashin lafiya nayi sosai har da zuwa Asibiti, na kira lambarki ba adadi, kin daina ɗaukar wayata. Anyway yanzu dai komai ya wuce sai godiyar Allah, ina mai kuma sake baki haƙuri a kan abubuwan da suka faru".

"Bakomai ai ya wuce, tun da Daddy ya ce mini ba wata matsala, Mahaifinka mutumin kirki ne, duk da yadda dangin ubana suka dinga ɓata ni a wurinsa amma hakan bai hana ya amince ka aureni ba, bani da bakin yi masa godiya Allah ya sa ya gama da duniya lafiya, bani da bakin yi masa godiya"

"Karki damu, kema kin zama 'yar sa"

"Haka ne, amma Mummy kuwa ta amince?"

Khalil ya ce "Ta amince mana, ai shi ya sanya Daddyn ma ya bada goyon baya, Allah ya sanya mana albarka, inye amarya ba kya laifi" rufe fuskarta tayi da hannayenta tana murmushi.

Hira suka sha ta soyayya, da kewar juna. Sai da aka yi kiran sallar magariba, sannan Abdul ya zo ya ce "To tsuntsun soyayya, ai sai ka tashi mu tafi a barta ta huta"

Hafsa ta ce "Laa Yaya Abdul, dama tare kuke?"

"Eh tare muke mana, ya barni a cikin mota a kan layi ya manta dani, tsawon awanni".

Murmushi suka yi, Khalil ya ce zasu je su yi salla, su dawo su gaida Mama.

Haka kuwa aka yi, bayan sun yi sallar Magariba, suka koma gidan su Hafsa.

Mama ta rasa in da zata saka ranta da daɗi, ta dinga kwarara musu addu'a, ta bawa Daddy labarin abin da dangin mahaifin Hafsa suka ce wa Daddy, wai yawon banza take bata kwaɓarta har cin kwalar maza take ba mutunci ne da ita ba.
Amma Daddy ya ce bakomai su karɓi kuɗin auren, amma suka ce ba zasu karɓa ba, mahaifiyarta ba ta ganinsu da mutunci.
Da yadda Daddy ya dawo wurin limamin unguwarsu, ya bada kuɗin auren Hafsa.
Mama ta dinga zabga masa godiya, sai da kunya ta kama Khalil.

Khalil ya ce "Bakomai Mama, ubangiji Allah ya nuna mana lokacin".


Wasa-wasa har Abincin dare Su Khalil suka ci a gidansu Hafsa, kamar zasu cinye juna shi da Hafsa.

Abdul ne yayi musu sallama, dan Khalil ya zo su tafi.

A soro suka tsaya, yana sallama da Hafsa ya ce "Amaryata, ya batun shirye-shiryen da za muyi ne?"

"Kaje gida ka huta, idan ka dawo mayi magana"

"To shikenan, ina fatan yanzu zaki ɗauko wayarki ki kunna, ko wata zamu saya?"

Ta ce "A'a tana nan"

Khalil ya ce "Shine ko kirani a waya, ki gaya mini an kawo kuɗin"

Ta ce "Yanzu ba ka shi ka sani ba, kaje kar Yaya Abdul ya gaji, ka tsayar da shi da yawa"

"Shikenan ƙanwar Yaya Abdul, sai da safe za muyi waya"

Tayi murmushi ta ce to shikenan.

Suka yi sallama, su Khalil suka tafi, suna tafe a hanya Khalil jinsa yake kamar an ɗaura auren, yadda abubuwa suka dinga tafiya kamar ya shirya su. Lallai Addu'a bata faɗuwa ƙasa banza.

Abdul ya dinga yi masa mita ya tsayar da shi, Khalil yana ba zai gane ba, yana son ya sanar da shi batun Yusra, amma yaji nauyin hakan.


Khalil na zuwa gida ya ga motar Daddy, alamar yana gida, sai da ya kuma tambayar Zakiru, ya tabattar masa da Daddyn yana gida. Ya duba agogon wayarsa, ya ga ƙarfe goma saura na dare.

Ko da yayi parking, ya fito kai tsaye sashin Daddy ya wuce.
Da sallama ya shiga falon, Daddy ya amsa masa, yana zaune shi da Amina tana zuba masa shirme yana murmushi.
Khalil na shigowa ya tafi da gudu ya rungume Daddy.

Murmushi Daddyn yayi shima ya rungume shi.

"Daddy na gode, na gode Allah ya biyaka da gidan aljanna, naji abin da kayi mini, ka sai mini kima a idon sirikaina, na gode Daddy".

"Bakomai Khalil, ina fatan daga yanzu ka daina rashin lafiya tun da ka samu abin da ka ke so?"

"Na daina Daddy, ina sonta sosai Daddy, ina tausayinta. Ban yi zaton zaka nema mini aurenta ba"

Ita kanta Amina murmushi take yi, dan ita Hafsa tafi jiyewa Daɗi, koba komai ita ma ta dandali arziƙi ta huta.

Daddy ya ce "Amina zaka yiwa godiya, ita ta sanar mini da halin sa ake ciki, amma mai ya sa tun farkon lamarin baka sanar mini ba?"

Amina ta ɗan zabura ta ce "Daddy ya gaya maka fa, kace sai Hajiya ta amince"

Dadyy ya ce "Shigar masa zaki kenan? Shikenan dai, Amina ce ta dinga shiga tana fita, a kan lallai ka samu abin da kake so. Naji tausayin yarinyar sosai bayan naji labarin abin da ya faru, daga ita sai mahaifiyarta suke fama da rayuwa, Amina ta saka pressure har Allah ya sanya dai aka kai kuɗin Auren"

Khalil ya ce "Aikuwa a bakinta na fara jin maganar, na zata ma da wasa take mini. Na Gode ubangiji Allah ya saka miki da alkhairi, yadda kika yi silar farinciki da yayewar damuwata ni da Hafsa"

Amina ta ce "Ai bakomai, ba abin damuwa bane, Allah ya sanya alkhairi, sai azo a fara shiri, lefe za ayi na gani na faɗa, dama Daddy ya ce "zai yi furnitures, kai kuma sai kayi lefe ni kuma zan yi kayan Kitchen" tayi maganar tana dariya.

Daddy ya ce "A wurin wa zaki samu kuɗin kayan Kitchen ɗin?"

"A wurin Daddy mana, Allah dai ya ƙara arziƙi ranka ya daɗe" Amina tayi maganar tana jinjina masa da hannunta.


"Wallahi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login