Showing 279001 words to 282000 words out of 296192 words
shi zan biya mana, kiyi haƙuri na yi alƙawarin yi miki tausa idan muka isa"
Jinjina masa kai ta yi, tun kan su bar Kano ta cinye ƙanzonta, da aka tsaya salla kuma, Hajiya da Yazid ne suka ci Abincin, wai ita ba ta ci tuwo take so, ƙarshe ta ɓuge da shan sprite da yalo.
Yazid duk da a takure ya ke shi ma a motar, amma ya gyara zamansa ya ce "Kwanta a kafaɗata sai ki yi bacci, naga idonki ya yi ja sosai".
Dan Hankalin Yazid ya kwanta, ta ɗan zame ta kwanta a jikinsa, amma gaba ɗaya zaman motar nan babu daɗi, ga matsi ga zafi.
Aikuwa wani wahalallen bacci ya ɗauke ta, Yazid kusa ko motsin kirki baya yi dan kar ta tashi.
Ba su suka isa garin nan ba, sai wajen goma saura na dare, Fadila ta riga ta gama gajiya tilis.
Ba laifi gidan kakannin Yazid yana da kyau, duk da ginin ƙasa ne amma tsaf da shi.
Suna zuwa gidan Fadila kamar ta faɗi, saboda wani irin jiri da take fama da shi.
Nan da nan suka hau yarensu na fulatanci, da ba abin da Fadila take ganewa.
Ba ta san mai suke faɗa da yaren ba, ta ga wata mata ta ƙaraso ta rungumeta, cikin gurɓatacciyar hausarta tana musu sannu da zuwa.
Cikin wani ɗaki suka shiga, in da suka tarar da wata dattijuwa, ita ma sai fulatanci take yi, kai da gani ka san suna cikin farinciki.
Kasancewar da wuta, ya sanya Fadila ƙarewa ɗakin kallo, tsaf da shi sai ƙamshin turaren wuta da ya haɗe ƙarnin man shanu.
Da hausa Dattijuwar take faɗin wannan ce sirikar tawa? Sannu da zuwa, ke kika auri jikana matso kusa da ni"
Yazid dai tuni ya nufi wurin yin salla, Fadila kuwa bayan an gama wannan gaishe gaishen, da yaren da ba ji take yi ba, da ƙyar ta yi alwala sallar ma a zaune ta yi, saboda ta wahala.
Ta nemi wuri ta kwanta, wata mata mai kama da Hajiya wadda tun shigowarsu Fadila ta ji ana cewa Dada ce ta shiga da abinci, tuwon Alkama ne da miyar kuɓewa ta sha kifi.
Duk san tuwon da Fadila ta gama kwarmato a mota, amma ta ce ita ba ta ci bacci take ji.
Cikin harshen fulatanci, Kakar Yazid take cewa ba ta ji daɗi ba matar Yazid ta ƙi cin abinci.
Hajiya ta ce "Kiyi haƙuri, tana da juna biyu ne, bakomai take iya ci ba" ai nan ta ƙara murna, can kuma sai hawaye saboda tuna Inna wuro mahaifiyar Yazid.
Yazid sun daɗe suna hira, sannan mijin Dada ya zo suka tafi in da za a sauki Yazid.
Yazid sai Addu'a yake yi, Allah ya sa kar ciwon Fadila ya tashi a garin nan cikin wannan dare.
Lafiya lau har Asuba, Hajiya ta tashi Fadila ta haɗa mata ruwa mai zafi ta yi wanka tayi alwala ta yi sallar asuba ta koma bacci.
Surutunsu ne ya tasheta, Yazid ya zo tuni, suna ɗakin yana kallonta a kan gado tana ta bacci.
Ga gadon na da katifa mak spring, ba abin da yake mata daɗi irin yadda idan tayi juyi, spring ɗin yake sama yana ƙasa da ita.
Bayan ta tashi suka gaisa da Mutanen gidan, Sannan ta fita tsakar gida wanke baki.
Tsayawa ta yi tana kallon 'yar guntuwar katangar gidan, kasancewar Fadila doguwa ce, tana ganin gidajen waje, sai da ko ina shanu ne a garin.
Ta gama brush ɗin ta miƙe, taga Yazid a bayanta.
Ya ƙarasa in da take yana faɗin "Ina kwana dear?"
"Lafiya lau" ta bashi amsa.
"To yaya, ya gajiya jiya kin yi bacci fa wuri"
Ta ce "Ba dole ba, na gaji ne sosai, a ina ka kwana?"
Yazid ya ce "Gidan Dada, ita ma yayar Inna ce, amma ƙanwar Hajiya ce"
Fadila ta ce "Kamarsu ɗaya, har wannan kakar taku"
Yayi murmushi ya ce bari na yi gaba, kar a fito a ce na yi rashin kunya"
Dariya ta yi ta koma ɗakin, sai sannu suke yi mata, kamar mai ciwo tana amsawa.
Dada ta fita ta shigo da kwanuka, ta ajiye a gaban Fadila, ta ce "Amarya ga abinci nan" Fadila dama yunwa take ji, dan haka babu baƙunta ta fara buɗewa, madara ta gani a cikin wani kwano, kamar madarar ruwa ta kalli Hajiya ta ce 'Hajiya meye wannan?"
Hajiya ta ce "Nono ne yanzu aka tatso shi, aka saka masa zuma, shi zaki fara sha, nan garin da haka ake rainon ciki, ba irin cimarku ta birni ba"
Fadila ta kai kwanon bakinta, ta fara sha, madarar ga garɗi, sai dai da ɗumi sosai, da farko ƙyama ya bata a hankali kuma ta ji ya mata daɗi. Suna can suna hira ta kuma buɗe kwano ɗaya, naman zabo ne a soye fal a cikin tasa.
Duk da yadda Yazid yake ƙoƙarin sayen nama a gida, amma kamar ba ta taɓa cin nama ba, haka ta zage ta na ci.
Garin ba su da wani cigaba, dai dai kyautatawa da karamci, dan daga jin ance ga matar Yazid, ɗan wajen Kubra, maƙota da 'yan uwa suka dinga shigowa ana gaisawa, kowa da abin alkhairin da zai kawo mata ya bata.
Dada da Gwaggo kamar su goya Fadila, duk tsufan Gwaggo da rashin gane mutanenta, amma tana gane Fadila sosai.
Gashi ba Mutane ne masu wata wadata ba, amma irin Abincin da Fadila ke ci a garin, har ƙiba ta fara, naman safe daban na dare daban, madarar nan ta sassafe mai ɗumi kullum sai ta sha ta da zuma, gashi tunda Dada ta bata wani magani, ba ta sake yin amai ba.
Yazid yana son su koma gida, dan tun washegarin zuwansu Daddy ya kirashi, a kan yana son ya zo gidansu, amma Yazid ya gaya masa basa gari, yana son Fadila ta fara zuwa awo, amma ta ita bama ta son tafiya, dan da fari ya zata ma ba zata iya zaman garin ba. A sati guda har gaisuwa da fulatanci da abin da ba a rasa ba ta iya.
Ga ƙibar ciki da kyau, ga na kyakkyawan abinci da iska mai kyau na karkara, dan sosai ta sake da su suka saba.
Wasa² sai da suka yi sati biyu cirr, shi Yazid ji yake kamar a kan ƙaya yake, duk a takure yake, amma ita yadda suke nuna mata soyayya da karamci ya sanya ta ji bata son rabuwa da su.
Da suka tashi tafiya kuwa, Fadila ta samu alkairi sosai da sosai, kakar Yazid har da kukanta wai yaushe za a dawo mata da Fadila, ita dai tana son Fadila.
Yazid ya ce mata zasu sake dawowa in sha Allah.
Ita kanta Hajiya, ta ji daɗin Yadda Fadilan ta dinga nuna wa mahaifiyarsu kulawa, dan duk wanda ka nuna kana son mahaifinsa ka gama masa komai.
Suka shiryo suka nufo Kano. A sati biyun nan kuwa, Mummy ba ta fita ko ina, tana zuba idon ta ina za a kawo mata Fadila, amma ta ji shiru, haka ta cigaba da mita tana matsawa Daddy a kan ya cika alƙawari.
Su Fadila suka dawo gida lafiya, tana ta jin daɗin karamcin da dangin Yazid suka nuna mata.
Sai dai gidan su duk yayi ƙura, Yazid ya zage ya gyara gidan, dan Fadila kwanciya tayi ta ce ita a gajiye ta ke.
Ta huta ta dinga firfito da kayan tsarabar da aka bata, tana ta murna amma taga Yazid yana hararata.
Ɗan tsuke fuska ta yi ta ce "Me na yi maka?"
Ya ce "Ban sani ba, ƙememe ki ka yi zamanki wai ke ba zamu dawo gida ba a kan lokaci, ki ka sa sai da muka yi sati biyu, ke ko tunanin kina da miji ba kya yi ko?"
Tura baki ta yi ta ce "To me zan maka?"
"Au haka ma zaki ce ko?"
Ɗaga masa gira ta yi, tana saka mazarƙwaila a bakinta.
Yazid ya ce "Allah ya shiryeki, kuma gobe in Allah ya kaimu da safe zamu je Asibiti ki fara antenatal"
Ta ce "To ɗan ustazuna, na ga dai haushina ka ke ji, kayi haƙuri ka ji masoyin"
"Ba wani masoyi, kawai daga zuwa ziyara kika shantake"
"To idan muka dawo kai zaka dinga samo mini madara da zuma ne? Ko zaka dinga ba ni naman nan me daɗi"
"Kwaɗayayyiya dama kwaɗayi ne ya zaunar da ke, salon ace bana ba ki Abinci, a nan komai na sayo miki ko na dafa miki, sai ki ce ke ba kya so".
"Eh naji kwaɗayayyiyar, ni dama ka mayar da ni"
Yazid ya ce "Tashi ki koma sai kin dawo".
Washegari Monday, Yazid yana ta so Fadila tayi ta shirya su tafi, amma ta tsaya a gaban mudubi, tana ƙarewa kanta kallo.
"Zid da na yi ƙiba nafi kyau ko?"
Yazid ya ce "Eh, ta yi miki kyau sosai"
"Kenan dama baka san siriryar mace?"
Tasowa Yazid yayi, ya karɓi kayan ya fara saka mata, dan idan ya biye mata yau ma ba za a fara zuwa awon ba.
Amma a hakan mita ta cigaba da yi, ashe dama kallonta kawai yake baya sonta saboda ba ta da ƙiba.
Ya rakata Asibiti, aka yi mata duk abinda yakamata, sannan suka taho gida, sai dai duk ta ga jikinsa a sanyaye.
"Ɗan ustazuna, meke damunka, na ga kayi wani iri, ko ni ce na ɓata maka rai?"
Ya ce "A'a, baki yi mini Komai ba, Daddy ya ce zai turo a ɗauke ki"
"A ɗaukeni a kaini ina?" Ta yi maganar tana kallonsa.
"Gida za a kai ki, fatana Allah ya sa ki dawo"
Haka nan ita ma sai ta ji tana fargaba. Rungumo shi ta yi a jikinta ta ce "Babu abin da zai faru in sha Allah, ina sonka Zid sosai babu abin da zai rabani da kai da yardar Allah, muje ka rakani ma sai mu dawo tare".
Yazid ya ce "A'a, Daddy ya ce ba tare zamu je ba, yanzu idan mun ƙarasa masu ɗaukarki suna titi suna jiranmu"
Shafa kansa ta dinga yi a hankali ta ce "Ka kwantar da hankalinka, ba wata damuwa in Allah yarda"
Haka suka ƙarasa titin unguwar su, unguwar da har yau Fadila ko sunanta ba ta sani ba, suka tarar da zuƙeƙiyar mota mai tint.
'yan sanda ne guda biyu a motar, suka ƙarasa gaban motar, suka gaisa da Yazid, ta buɗe motar ta shiga, gaba ɗaya sai tausayin Yazid ya kamata, ta dinga ɗaga masa hannu, shima jiki a sanyayen yake ɗaga mata hannu".
Bai san dalilin ɗaukar Fadilan da Daddy ya turo ayi ba, dan bai yi masa cikakken bayani ba.
"Allah ka sa su dawo mini da matata". Ya tafi gida yana ta Addu'a cike da fargaba!
Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA DOMIN YA SAYA.
08081012143
84
Gaba ɗaya jikin Yazid yayi sanyi sosai da sosai, ya kasa sakewa yayi ta tunani daban daban a ransa, ya fara addu'a Allah ya taimake shi ya sanya Fadila ta dawo gareshi.
Sun ɗan yi tafiya mai nisa, sam Fadila bata gane kan hanyar da ake bi, sai dai ganinsu ta yi a gidan Daddy.
A ƙofar gidan suka tarar da Daddy, zaune a cikin mota shi da Amina, ɗan sandan ya kalli Fadila ya ce "Ranki ya daɗe ga Alhajin can"
Fadila ta buɗe motar ta fita, ta nufi wadda su Daddy ke ciki, Amina ta ɗan ƙura mata ido, Fadila sai cukuikuye hannu take a cikin hijjabinta tana ɓoye cikin.
Duk da ta yi farinciki da ganin Daddy, amma tana ganin sa tare da Amina, ranta ya ɓaci, ta tuna irin auren wulaƙancin da aka yi mata. A hankali ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga ta zauna, sannan ta ce "Daddy ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, ya mai gidan na ki?"
Fadila ta ce "Yana nan lafiya"
Shi kansa Daddy yayi mamakin yadda Fadila tayi ƙiba, dan a yadda take ba zaka taɓa cewa zata yi ƙiba ba.
Ba wanda ya kuma kulata a tsakanin shi da Amina, dama Fadilan ma ba ta kulata ba.
Daddy cikin tsuke fuska ya ce "Zan kai ki gida kiga mahaifiyarki, amma muddin kika kuskura ki ka yi wani misbehaving, matakin da zan ɗauka ba zai miki daɗi ba, kuma ban yarda ki gaya mata waye mijin da na aura miki ba" bai jira mai Fadila za ga ce ba ya ba motar suka bar wurin.
Suna tafe suna hirarsu shi da Amina, Amina na ta cin dubulan, duk da yadda Fadila ke jin kamar ta jefa Amina waje dan haushinta take ji, amma zuciyarta ta dinga raya mata ta roƙi Amina ta sanmata dubulan ɗin nan saboda ranta ya biya. Amma ta dake ta daure ta kawar da kanta gefe.
Daddy ya na son yayi wa Fadila hira, ya yi mata tambayoyi saboda ba ƙaramin kewarta ya yi ba, amma yana gudun aikata hakan, azo a samu matsala daga baya.
Ko da suka shigo layinsu, gani take tamkar ta yi shekaru masu yawa rabonta da layin, hatta gidan ma duk yayi mata wani iri.
Daddy na yin parking ta a fito jiki na rawa, ta nufi cikin gidan da sauri, har da tuntuɓe, tausayinta ya kama Amina.
Ta kalli Daddy ta ce "Allah sarki, Allah ne kaɗai ya san yadda ta rayu tsawon wannan lokacin ba tare da gani ko kiran mahaifiyarta ba, gaskiya ta cancanci yabo, ta yi haƙuri kuma ta yi biyayya"
Daddy ya yi murmushi ya ce "To lawyer, amma koma dai meye ai ba a wahala take ba, kalli yadda ta koma fa"
Amina ta ce "Haka ne, amma duk da haka gurbin uwa daban yake".
Ita kuwa Fadila da gudu ta ƙarasa sashin Mummy, ko nauyin cikin bata ji, a falon Mummy suka haɗu, Fadila ta faɗa jikinta tana kuka.
Rungumeta sosai Hajiya Zainab ta yi, ita ma ta fashe da kukan.
"Fadila, ina ya kai mini ke tsawon wannan lokacin, da kika kasa ɓallowa ki dawo gida, hankalina duk a tashe ban san in da kike ba, na shiga damuwa sosai"
Fadila ta ɗago tana faɗin "Mummy, babu yadda za ayi na iya zuwa, ya ce idan na zo bai nemeni ba bai yafe ba, ni kaina na yi kewarki Mummy".
Gani ta yi Mummy tana ƙare mata kallo, daga sama har ƙasa, ta miƙa hannu ta janye hijjabin Fadila, sai ga ciki ya fara tasawa"
Waro ido Hajiya Zainab ta yi ta ce "Fadila da gaske aure yayi miki? Shi ne har kika yadda ki ka yi ciki, a garin yaya ki ka samu Ciki Fadila?"
Fadila ta yi shiru tare da sunkuyar da kai ƙasa.
"Sannin yadda aka yi ta samu ciki ba huruminki bane ba, tun da dai aurar da ita na yi, ba wai sakinta na yi a duniya haka ba" suka jiyo muryar Daddy, Hajiya Zainab ta kalli in da Daddy ke tsaye, Fadila kuma ta sunkuyar da kai kamar mara gaskiya.
Cikin takaici Hajiya Zainab ta ce "Amma ta yaya mutane zasu yadda aure ta yi, bayan babu wanda ya san da hakan?"
Daddy ya ce "Ai ba dole ne sai kowa da kowa ya sani ba, tun da mun cika sharaɗin abin da Addini ya tanada, gata nan zuwa yamma zan mayar da ita"
Jin Daddy kawai Hajiya Zainab ta yi, dan ba ta ga abin da zai sa ta bari ya sake ɗauke Fadila daga gabanta ba.
Ya juya ya fita ya bar ɗakin, jan Fadila ta yi zuwa ɗakinta, ta rufe bedroom sannan ta kalli Fadila ta ce "Fadila, wai ɗan gidan wa ma ya aura miki ne?"
Jiki a sanyaye Fadila ta girgiza kai ta ce "Mummy ba ɗan kowa bane ba, ba shi da komai sai Allah, amma ban rasa ci ba ban rasa sha ba da abin da zan saka jikina"
Mummy ta ce "Ke! Wai yana ga kina acting kamar kina son auren, bayan auren dole yayi miki, a ina mijin yake kuma waye shi?"
Fadila ta ce "Mummy ko na gaya miki ba zaki gane shi ba".
A hasale ta ce 'Ke dalla ki mini bayani a ina yake, mara tunani da ga zuwa kin ƙunso ciki kamar abin da kike jira kenan, ke ko kishin kanki ba kya ji kuma ba kya tausayina, maimakon ki ɓallo ki gudo amma kika miƙe ƙafa, har da ɗaukar ciki, to bari ki ji na gaya miki, ba in da zaki koma daga nan, kuma wannan banzan cikin sai an zubar da shi. Wato saboda dai ya nuna mini ban isa ba, shi ne ya aurawa Khalil 'yar talakawa ya rabani da shi, kema ya samo wani wahalallen ya aura miki, dan cin zarafi, to bai isa ba yayi kaɗan ba in da zaki koma".
Fadila ji ta yi tamkar ta cewa Mummy, dan Allah ta ƙyaleta tana son aurenta, amma ta yi shiru, dan kar su ɓata.
Hira suka dinga yi, Mummy na cigaba da alwashin sai ta wulaƙanta Amina kamar yadda ta kassara mata iyali, kuma ko ta tsiya sai ta kashe auren da aka yiwa Fadila.
Ita Fadila hankalinta yana can kan Yazid, ba ta san a wani hali yake ba, ta san shi da saurin rikicewa, ta kasa manta yadda ta ga fuskarsa ta sauya da zata tafi.
Ta tafi ɗakinta, ta je ta yi wanka, ta saka wasu kayan, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta, ita kanta ta san ta yi ƙiba sosai ta yi murmushi ta ce 'Su ɗan ustazuna an iya raino, duk na yi ƙiba" sai kuma ta shafi cikin jikinta ta ce "Allah ya kawo mini abin da ke cikin nawa lafiya, ina son na ganka amma Mummy ta fara iƙrarin rabani da kai"
Duk da yadda ta so ta zauna su yi hira sosai da Mummy, amma ta kasa saboda baccin da take ji, ga sauran gajiyar hanya na tafiya Jalingo da suka yi.
Hajiya Zainab kuwa ta kasa ta tsare, tana tunanin yadda za ta yi da cikin Fadila, da kuma shirin ko ta kwana a kan sai dai su yi wadda za su yi ita da Alhaji Ahmad, amma ba zata taɓa bari ya kuma ɗauke mata Fadila ba.
Sai la'asar Fadila ta tashi, Hajiya Zainab ta shirya mata Abinci, Fadila ta kalli Mummy ta ce "Mummy ni bana son wannan Abincin, idan na koma gida na san Hajiyarsa ta aiko mini da tuwo, ni yanzu da zan samu ƙosai ne ma dai da sauƙi"
"Ke dalla can rufe mini baki, sai ka ce wani cikin arziƙi to bari ki ji na gaya miki, sai kin rabu da cikin nan, maza ɗau Abinci ki ci".
Fadila ta ce "To bari na yi salla"
Bayan ta yi salla kuwa, ficewa ta yi ta tafi Kitchen, ta tarar Hajara na ta aiki, Hajara