Showing 234001 words to 237000 words out of 296192 words

Chapter 79 - GABA DA GABANTA

shiga shi kuma ya zagaya mazaunin direba ya kunna suka bar makarantar.
Kan su kai Asibitin duk Fadila ta firgice, sai koke-koke take yi, tana riƙe kanta.
Yazid ji yake kamar ya cire mata ciwon, ya dawo da shi jikinta, yadda take yi ɗin nan zaka tabattar tana jin jiki sosai.

Suna zuwa asibitin aka karɓesu da gaggawa, kasancewar sun san Fadila nan da nan suka karɓeta, aka kwantar da ita.
Doctor Aliyu na ganin Yazid ya ce "A'a mutumin, yau kuma kai kawota?" Yazid ya ɗan yi murmushi.

Sosai take kuka tana kiran sunan Mummy.
Doctor Aliyu ya ce "Fadila ya isa haka, meyake damunki?"

Cikin kuka ta ce "Ni ka ƙyaleni, ina Yazid?"

Aliyu ya ce "To Yazid ɗin ne zai baki magani ko ni?"

"To ba kana kallona ba, ka ƙi yi mini komai, Zid ka mayar da ni gida in mutu a can"

Yazid yayi ƙasa da murya ya ce "Zan maida ke, Addu'a nake yi miki, amma kiyi shiru kin ji" ta fashe da kuka ta ce "Bana gani sosai"

"Zai daina in sha Allah, kiyi addu'a"

Ta ce "To, amma kaje gidanmu ka kira mini Mummy"

Ya ce "To shikenan, zan je in sha Allah" tana ta wannan surutan, gaba ɗaya Yazid ya shiga damuwa, ya zuba mata ido sai rawar sanyi take saboda zafin zazzaɓi"

Doctor Aliyu ya ce "Ka kwantar da hankalinka, zafin ciwo ne amma nayi mata allurar bacci, za tayi bacci zazzaɓin ma zai sauka"


Yazid ya ce "Allah ya sa"

Doctor Aliyu ya auna Bp ɗin Fadila, amma ya ganshi ya hau sosai.

Doctor Aliyu ya ce "Ya aka yi jinin Yarinyar nan ya hau haka?"

Yazid ya ce "Ban sani ba, nawa ya nuna?"

Aliyu ya ce "160/90mmgh, ya hau sosai, bari in je in Kira babanta yakamata su sani, ina ga a nan zamu riƙeta"

Jiki a sanyaye Yazid ya ce "To shikenan"

Bayan fitar Doctor Aliyu, Yazid ya matsa gaban gadon ya zuba mata ido. Sai yanzu ya lura da yadda ta ƙara ramewa.

Kamar mai raɗa yaji tana kiran sunansa.

A hankali ya matsar da kunnensa bakinta dan jin me take cewa.

"Yazid! Bana son sa ka gaya wa Mummy!!"

Ras gaban Yazid ya faɗi, ya kira sunanta amma yaga bacci take she's unconscious, amma tana ta nanata "Bana son shi!!"

Tofa!



AYSHERCOOL
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA.
08081012143



72


Jiki a sanyaye Yazid ya ce "Fadila, me kike cewa ne?"

Kasancewar bata hayyacinta bata san meya ke faɗa ba, a cikin baccin ta cigaba da kuka tana cewa bata son shi.

Tunani ya shiga yi, waye bata so ɗin ko Kankiya ne? Amma ai Kankiya ya bar makarantar ma tun bayan da abin nan ya faru babu daɗewa. Ya bawa kansa amsa.

Doctor Aliyu ne ya shigo ya miƙa wa Yazid takarda, ya ce yaje Pharmacy ya karɓo maganin.

Yazid ya karɓa je Pharmacy aka bashi maganin, ya tambayi kuɗinsa aka ce masa ai akwai kuɗi a family file ɗin ba sai ya biya ba.

Ya koma ya kai maganin ya tambayi, doctor Aliyu ya kira gidansu Fadila.

Doctor Aliyu ya ce "Na kira su, lambar mamanta a kashe babanta kuma bai ɗaga ba".

Yazid ya koma wurin Fadila ya zauna, yana ta saƙa da warwara, ya ɗan zuba wa Fadila ido, tayi rama sosai da sosai.
'kenan dalilin damuwarta kenan, kusan kullum cikin kuka?'.

Haka yayi ta wasi-wasi har la'asar Fadila bacci take, bata farka ba, Yazid ya tashi yaje yayi salla ya biya ya sayo wa Fadila fruit da kwalin exotic, in da Allah ya taimake shi da 'yan kuɗi a jikinsa.

Cikin ikon Allah ya koma babu daɗewa, ta fara motsi zata tashi.

Yayi saurin ƙarasawa gaban gadon nata, yana kiran sunanta.

Miƙa tayi, Yazid ya kawar da kansa ƙasa, ta kalli Yazid ta ce "Baka tafi ba?"

Ya ce "Eh, sannu ya jikin?"

"Da sauƙi ina, Doctor Aliyu?"

Ya miƙe ya ce "Bari naje nayi masa magana, ko zaki ci wani abun kan yazo?"

Ta ɓata rai ta ce "Ni bana ci, ka kira mini shi".

Yazid ya tashi, ya kirawo mata Doctor Aliyu.

A tare suka shigo ɗakin da take, Aliyu ya kalleta ya ce "Sannu ya jikin?"

"Da sauƙi, ka kira mini Mummyn?"

Aliyu ya ce "Wayarsu bata shiga, amma zan sake kira meya yake yi miki ciwo yanzu?"


"Kaina ne yake ciwo haryanzu wallahi, ga ƙirjina yayi nauyi"

Doctor Aliyu ya zauna ya ce "Yauwa yanzu gaya mini, yi min bayani, meke damunki jininki ya hau?"

Ta waro ido ta ce "Hawan jini kuma?"

"Eh, jininki ya hau, gaya mini meke damunki?"

Jikinta ya ɗanyi sanyi, amma ta kasa magana.

Aliyu ya ce "Talk mana"


Ta ɓata rai ta ce 'Bakomai, ni ka sallameni kawai in tafi gida"


Yazid ya ce "Jikin naki a haka zaki tafi?"

"Eh ni gida zan tafi"

Yazid ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri ki zauna"
Ta galla masa harara ta ce "Ba zan zauna ɗin ba"

Aliyu ya ce "Ke masifaffiya, yana ta ɗawainiya da ke tun da ya kawo ki yake zaune yana kula da ke, amma kina masa masifa ba za a sallame ki ɗin ba"

"Kar ka sallame nin, tafiya zan yi da kaina"

Aliyu ya ce "Sannu Yazid, kana haƙuri da wannan fitsararriyar, ka fasa da ita zan baka ƙanwata"

Duk da yadda take fama da kanta, wata uwar harara ta gallawa Aliyu ta ce "Koma wace kai ka sani, na gaya maka ni ba saurayina bane ɗan ajinmu ne"

"To, Allah ya baki haƙuri, bari na sake trying lambar gidanku, ki samu ki ci wani abu, kan a baki magani"

Ba tace masa komai ba, Doctor Aliyu ya fice daga ɗakin.

Ta kalli Yazid ta ce "Ka daɗe sosai a asibitin nan, ka tashi ka tafi na gode"

Yazid ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, kinga ga Fruit na sayo miki ko zaki iya sha"

Haka nan taji ya bata tausayi, ta ce "Bani ayaba in ci"

Ya ɗauka ya miƙa mata, sai ɗan yamutsa fuska take yi.

Ya kalleta cikin kulawa ya ce "Ya aka yi, ya naga kina yamutsa fuska?"

Kamar za tayi kuka ta ce "Zazzaɓin ya sauka, amma kaina ciwo yake yi, kuma wai jinina ya hau ni abin ya bani mamaki"

Ya kwantar da murya ya ce "Meke damunki har haka da jininki zai hau? Meyafaru ne?"

Kawai sai hawaye ya fara bin fuskarta, har da sheshsheƙa.


Yazid ya ce "Yi haƙuri, dan Allah ki daina wannan kukan ya isa haka, kinga baki da lafiya".

"Ni ka ƙyaleni nayi"

Ya ce "No, ba zan iya ba, bana son ganin kukanki, ci ayabar su zo su baki maganin"

Ya dinga lallaɓata sai dai tana ci tana kuka, yana cigaba da rarrashinta.

Sai bayan la'asar daf da magariba sannan Aliyu ya samu Mummy a waya, ya sanar mata da Fadila fa tana Asibiti tun wurin sha biyu.

A rikice ta ɗau mota ta bazamo Asibiti wurin Fadila.

Tana zuwa ta nufi Vip rooms tana dubawa, dan ko Doctor Aliyun bata nema ba, cikin sa'a a ɗaki na uku taga Fadila a ciki, gefenta kuma ga Yazid a zaune.

Da sauri ta ƙarasa gaban gadon da Fadila take kwance tana faɗin "Fadla, lafiya kuwa? Meyasameki garin yaya aka kawo ki asibiti?"

Kasa Magana Fadila tayi, sai kallon Mummy da take yi, hawaye fal idonta.

Yazid ya risuna yana gayar da Mummy.

Ƙarewa Yazid kallo tayi, daga sama zuwa ƙasa ta ce "Waye wannan?" Ta tambayi Fadila maimakon ta amsa gaisuwar Yazid.

"Ɗan ajinmu ne" Fadla ta bata amsa.

Still bata amsa masa ba ta ce "Fadila maimakon ki kira gida, sai a kawoki Asibiti ba wanda ya sani?"

"To Mummy ba duk an kira lambarku bata shiga ba, ke taki bata shiga ba, ta Daddy kuma baya ɗagawa"

Mummy ta ce "Dama ya za ayi ya ɗaga, yana ta waccan banzar yarinyar" ta kalli kayan Fruit ɗin dake kan drower a gefen Fadila ta ce "Wannan kayan fa, waye ya kawo su?"

"Yazid ne ya saya mini" ta bata amsa.


Hajiya Zainab ta kwaɓe baki ta ce "Waye kuma hakan?"

Fadila ta ce "Gashi nan, a kusa da ke"

Ɗan guntun tsaki tayi ta ce "Wai meyasameki ne ma?"

Fadila ta ɓata fuska ta ce "Kaina ne yake ciwo, da ƙirjina".

Yazid ya miƙe ya ɗan risuna ya ce "Mummy ni zan tafi, Ukty as'alullahil azim, rabbil arshil azim an yashfiyaki".

Fadila ta ɗan yi murmushi ta ce "Na gode sosai, na zaunar da kai ka gaida gida".


Yazid ya yi murmushi ya ce "Bakomai, Allah ya ƙara sauƙi"

Har zai fita Mummy ta ce "Kaga, zo ka kwashe wannan kayan ka tafi da su, ka ƙarasa su ka cinye"

Fadila ta ce "A'a bar mini ina so, zan ci"

Mummy ta ce "Ke ba sai a sai miki wani ba, ai naga shi mabuƙaci ne"

Yazid a ƙasan ransa bai ji daɗin abin da Mummyn tayi masa ba, amma ya maze ya ce Bakomai Mummy, Allah ya bata lafiya.

"A'a ba Mummy ba, Hajiya Zainab" Yazid ya jinjina kai ya fice.


Mummy ta mayar da kallonta ga Fadila ta ce "Ke wai waye wannan?".

"Mummy na gaya miki ɗan ajinmu ne, wannan Yazid ɗin ne da nake baki labari kwanaki"

Hajiya Zainab ta tsuke fuska ta ce "Meye alaƙarki da shi?"

Fadila ta ɗan numfasa ta ce "Kamar dai yadda na gaya miki a baya Mummy, bakomai, Yazid yana taimaka mini sosai a harkar karatu, iyakacinta kenan. Amma ba abin da nake tunani bane ba.


"Au ai kema na ɗauka gajiyayyen zaki ɗauko mini, bayan da sa ranarki a ka, kalli wani matsiyacin takalmi a ƙafarsa, yadda idaunsa suka yi fici-ficin Nan da gani yunwa yake ji"


Yazida data fara ƙosawa da mitar Mummy ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ni ba son Yazid nake ba, ba tsarar aurena bane ba, kawai dai yana da kirki ne"

Doctor Aliyu ne ya shigo shi da wasu Nurses guda biyu, yana ganin Mummy yayi murmushi ya ce "Hajiya, ashe kin ƙaraso"

Mummy ta ce "Eh, na zo tun ɗazu, ya aiki?"

"Alhamdilillah, Hajiya ki ritsa ta tayi miki bayanin meke damunta, jininta ya hau sosai"

Hajiya Zainab ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, kamar ya hawan jini?"

"To gata nan dai ki tambayeta"

Hajiya Zainab ta kalli Fadila ta ce "Fadila garin yaya jininki ya hau, a wannan shekarun naki haka?"

Shiru Fadila tayi a ranta ta na jin dama zata iya gaya wa Mummy abin da yake damun zuciyarta. Amma tayi shiru ta ce ita ma bata san dalilin hawan jinin ba.


Bayan sallar isha'i Daddy yana zaune yana cin Abinci, suna hira da shi da Amina, ta ce "Baby, ɗazu da ka bar samsung ɗinka a gida an kiraka, amma dai ban ɗaga ba.

Yayi murmushi ya ce "Meyasa baki ɗaga ba?"

"To na sani ko wayar ta sirri ce?"

Ya kalleta ya ce "Kina tsoron ko wata ce ta kirani a wayar?"

Amina tayi murmushi ta ce "Idan ma watan ce ta kiraka ina ruwana, normal ne ai"

Ya ce "Ba wani normal, kizo ki isheni da mita da kumbura baki saboda kishi ba"

"Ba wani kishi da zan yi, kowa iya allonsa ya wanke kawai, ni dai na san na riga na sha kwana a nan" tayi maganar tana ɗora hannunta a ƙirjinsa.

Ya saka nasa hannun a kan nata hannun yana kallonta ya ce "Tabbas hakane, kin riga kin sha kwana a zuciyar mijinki Amina, Ahmad na matuƙar ƙaunar ki sosai Meenal, kin kawo haske na musamman a rayuwata, kin fitar da ni daga cikin wani duhu da ya dabibaye rayuwata a kan Zumunci da kuma ciyar da dukiyata. Ina alfahari da ke Allah ya yi miki albarka"

Tayi murmushi ta kalleshi ta ce "Ni yakamata nayi maka godiya, da ka bani fitilar haska rayuwata ta ilimi, ka dinga kula dani, ka nuna mini nima 'ya ce, duk da yadda iyalanka ke ƙyamata, amma baka ƙyamace ni ba, ka aureni, kake ta nuna mini kulawa ni da iyayena. Ni yakamta nayi maka godiya"

Ture kwanukan Abincin yayi, ya ɗorata a kan cinyarsa, ya rungumeta sosai a jikinsa, yana cigaba da gaya mata yadda yake sonta.

Kamar ba babban mutum ba, ya ce "Sweetyna".

"Na'am Daddy" ta amsa tan jan gemunsa a hankali.

"Zan biya mana umara, mu da mutum biyar, kiyi selection wanda kike ganin ya dace mu tafi tare da su".


"Wayyo Allahna daɗi, Allah ya ƙara maka arziƙi Daddy, abin da nake ta buri a rayuwata, ina burin zuwa makka".

"Da Hajji na so biya mana, amma na san maybe lokacin Babyna yana cikin ki, tafiya ba zata yiwu ba" yayi maganar yana shafa cikinta

Tura baki tayi tana murmushi, ya ce au dariya ma na baki, wataƙila yanzu haka ma akwai"

Ta kalli hannunsa ta ce "Bakomai a ciki, sai abincin da naci na ƙoshi, ai yakamata na huta ai".

"A'a gara dai ki haihu, sai ki huta gaba ɗaya, kiyi selecting mutanen, sai ki gaya mini, yanzu fara ɗauko mini wayar tukuna"

Amina ta tashi cikin jin daɗi, taje ta ɗauko masa wayar ta kawo masa.

Dubawa yayi, yaga kiran doctor Aliyu ne.
Cikin hanzari ya kira wayar doctor Aliyun, aikuwa yai sa'a ta shiga. Bayan sun gaisa doctor Aliyu ya ce "Yallaɓai dama na kiraka ne, saboda Fadila da aka kawo Asibiti, ba lafiya daga makaranta, baka ɗaga ba kuma cikin ikon Allah ma dai daga baya wayar Hajiya ta shiga, gashi ma har ta zo"

Daddy ya ce "Subhanallah, meya sameta ne?"

Doctor Aliyu ya ce "Eh, ta zo da zazzaɓi mai zafi ne da ciwon kai, sai kuma muka duba jininta ya hau sosai"

Gaba ɗaya Daddy ya rikice ya ce "Yanzu a wani hali take ciki?"

"Eh, yanzu jikin da sauƙi tama farfaɗo daga allurar baccin da muka yi mata".


Daddy ya ce "Shikenan, gani nan, yanzu zan zo in Allah ya yarda"

Amina ta ce "Daddy meyafaru ne?"

Ya miƙe tsaye yana faɗin "Fadila ce babu lafiya, tana asibiti wai jininta ne ya hau"

Amina ta ce "Subhanallah, me zai sakawa Fadla hawan jini a wannan shekarun? Bari na ɗauko mayafina mu tafi tare"


Daddy ya ce "A'a, na san Zainab tana can, kar muje ta ɗaga mana hankali a Asibiti, na kiraki a waya"

Cikin damuwa Amina ta ce "Shikenan, Allah ya bata lafiya"

Daddy ya amsa da Amin ya fice.



Tuni Hajiya Zainab ta gayawa su Turai Fadila babu lafiya, dan duk sun zo dubata ma, Hajiya Salma ta ce da safe Salim ma zai zo dubata.

Duk yadda Mummy tayi da Fadla a kan ta gaya mata meke damunta, amma taƙi faɗa.

Tara saura na dare, sannan Daddy ya isa Asibitin, sai da ya fara tsayawa a ofishin doctor Aliyu, ya kuma yi masa bayanin abin da yake damun Fadila, sai dai Daddy ya bar batun hawan jinin nata a matsayin ko gado ne tunda yana da shi, Amma Aliyu ya tabattar masa da tana da damuwa ne.

Bayan sun gama magana da doctor Aliyu, ya tafi ɗakin da Fadila take. Da sallama ya shiga ɗakin, ya hangi Fadilan a zaune a kan gadon, tana shan abu a kofi, wanda su Hajiya Salma ne suka kawo mata.

Ya ƙarasa gaban gadon Fadilan cikin kulawa yake faɗin "Sannu Fadila, ya jikin naki?" Fadila ta ce "Da sauƙi"

"Allah ya ƙara afuwa, amma meke damunki haka har kika sa shi a ranki, jininki yake hawa?"

"Ya wuce baƙin cikinka, yadda ka watsr da mu ka kama matarka, saboda tsabar rashin mutunci tun rana tana Asibitin nan, amma aka kirka kaƙi ɗaga waya, sai yanzu da waccan shashashar ta baka dama sannan ka zo Asibitin, saboda tsabar wulaƙanci ba dole jininta ya hau ba" Hajiya Zainab tayi maganar lokacin da take fitowa daga banɗakin cikin ɗakin.

Alhaji Ahmad bai tanka mata ba, ya sake kallon Fadila ya ce "Yanze meye yake miki ciwo?".

Ta ce "Kaina ne, kuma da sauƙi sosai"

Hajiya Zainab ta cigaba da yi masa tijara.

"Ai wallahi kaji kunya, baka da wani basaja da zaka yi mana, dan abin kunya 'yarka na Asibiti baka damu ba, balle ka zo ka ganta saboda kana naniƙe da mace"

Daddy ya miƙe ya ce "Fadila Allah ya ƙara Afuwa, zan dawo da safe kin ji ko?" Ta ɗaga masa kai alamar to, ya fice ya bar ɗakin da Fadilan take.


Duk da Daddy ya tafi, amma Hajiya Zainab ta zauna ta cigaba da mita.

Yana komawa gida, Amina ta dinga yambayarsa ya me jiki, Ya tabattar mata jikinta da sauƙi, ƙila ma a sallameta gobe in Allah ya kaimu.

Washegari da safe Fadila tana ta mitar ita a sallameta, amma Doctor Aliyu ya ce sai yamma zai sallameta.


Wajen ƙarfe tara na safe, ciwon kai ya fara tasowa Fadila, ta fara koke-koke. Sai da aka yi mata wata allura sannan ta ɗan samu releif.

Amina kuwa da wuri ta tashi, tayi girki ta tashi Daddy ta ce ya tashi suje su duba Fadila, amma Daddy ya ce ba zai je da ita ba, sai dai tayi haƙuri idan sun dawo sai ta dubata.

Yauma dai da Daddyn yaje Asibitin, sai dai bai samu tarbar arziƙi a wurin Hajiya Zainab ba, haka ya gama zamansa ya tashi ya tafi.
Yazid kuwa bayan yaje makaranta, lectures ɗaya aka yi, ya tafi domin ya sake duba Fadila a Asibiti.

Sai dai ko da yaje Asibitin, still kallon banza ya samu daga mahaifiyarta, ita kuwa Fadila murmushi ta yi masa ta ce "Ya na ganka makarantar fa?"

"Zuwa nayi na ganki sai in tafi, na kira wayarki bata shiga"

Ta ce "Ai wayar tana mota, jiki yayi sauƙi sosai, za a sallameni ma in sha Allah"
Hajiya Zainab ji take kamar ta ce Yazid ya tashi ya tafi, sai wani iyayi yake yana larabci, yana fama da wasu tsumman kayansa.

Salim ne yayi sallama shi ma yazo duba Fadila, tana ganinsa taji kan ta ya kuma sarawa, wani baƙin ciki da takaici suka tokare mata a ƙirjinta, ko sunansa bata ƙaunar ji, balle tayi arba da shi.
A tsaye ya gaida Hajiya Zainab, ya ja kujera ya zauna.
Wani irin banzan kallo yake yiwa Yazid, wani abu Fadila take gani a idon Yazid, da ta kasa fassara ko menene.

Yazid ya tashi yayi musu sallama ya fice. Hajiya Zainab ma ta fita ta basu guri.

Salim ya kalli Fadila ya ce "Baby ashe baki da lafiya?"

A fusace Fadila ta ce "Ban sani ba, mara mutunci kawai, ka saka mahaifiyata ta dinga fushi da ni, wai ina wulaƙantaka, idan ina wulaƙantaka idan ba zaka iya ba, ai sai ka rabu da ni, na meye zaka kaini ƙara?"

Kwantar da murya yayi ya ce "Haba amaryata, yanzu dai kiyi haƙuri kwantar da hankalinki, ni gani nayi ma kin wani rame" yayi maganar yana ƙoƙarin zama a gefen gadon da take.

A fusace ta ce "Meye haka ne?"

Ya ce "Kamar yaya? Naga kina wani matsawa, ba dai ke zan aura ba? Meye dan na taɓa ki, ai ni zan aureki, ke

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login