Showing 228001 words to 231000 words out of 296192 words
gani ba, ka san ina ta saka Daddy a gaba ya shiga Maganar auren, ina ga bayan bikin har garinsu zan je gaida Babanta, dama can mutumina ne muna mutunci da shi"
Abdul ya ce "Ka ga ikon Allah ko, shiysa waulaƙanci ba shi da daɗi, ga yadda ka dinga hantararta lokacin da zamu kaita makaranta, gashi yanzu tayi maka rana ai"
"Aikuwa dai gashi na gani".
Sha ɗaya da rabi baƙi suka yi ta dawowa gida, ana ta hira ana shewa.
Yadda Amina ta shiga sashinta, Alhaji Ahmad sai kallonta yake yi, tayi masa kyau sosai da sosai, kamar ya tsokaneta yadda ya saba amma ya maze ya haɗe rai.
Amina ta fara cire abun hannunta tana faɗin "Yallaɓai lafiya kuwa? Ya na ganka haka, kuma ko ka ɗan leƙo mana wurin Dinner".
Rai a ɗan ɓace ya ce "Wato shi ne kika je kuka raba abin faɗa a wurin biki ke da Zainab, ki ka je a gaban mutane kuka yi hayaniya har kuka saka security suka koreta ita da ƙawayenta meyasa kike biye mata ne? Ko kunyar idon mutane ba kuji ba?"
A ɗan dirirce Amina ta ce "Ni ban yi rigima da ita ba ai lokac........
"Ya isa, ba yadda aka yi nake son ji ba, ni fitina ce ba na so, dan Allah kuyi haƙur a gama bikin nan lafiya, kowa ya watse sai ku cigaba da duk abin da kuka ga dama, amma dan Allah kar ku zubar mini da mutunci a idon mutane. Idan kin sauya kayan ɗan samon abin da zan ci, zan tafi in nemi wurin kwana" ko kula shi Amina ba tayi ba, ta wuce ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka.
Ta sauya kaya ta fita ta shiga Kitchen ɗin sashinta, ta fara ƙoƙarin ɗora girki.
'yar autar su Alhaji Ahmad, mai suna Hajiya Bilki, wani ambassador take aure bata ƙasar gaba ɗaya, ko bikin Amina ba ta zo ba, sai bikin Khalil da ta zo suka haɗu da Amina.
Familyn suna jin tsornta, har yayyaenta suna shakkarta saboda faɗanta, duk 'ya'yan gidansu suna da haƙuri amma banda Anty Bilki.
Suna shigowa daga wurin dinner nan, tun a falo ta fara faɗin ina "Zainab ɗin take? Ita har tana da bakin yiwa wani gorin talauci? Da zata kwaso wasu 'yan tasha su ciwa yarinya mutunci a gaban iyayeta, ko ta manta mun san asalin balbela ne?"
Ana ta bawa Anty Bilki haƙuri, a kan a bar zancen, amma ta ce ba za tayi shiru ba, Anty Fauziyya kuwa ta cigaba da zigata tana faɗin "Gaya mata dai, munafuka Ai mu Allah ne ya kawo mana maganinta, baƙar mara mutunci kawai"
Har part ɗin Hajiya Zainab Anty Bilki ta je, ta dinga zazzagata masifa.
Sanin cewa Hajiya Bilki ta damata ta shanye a rashin mutunci ya sanya tayi shiru da bakinta, suka ƙare mata tas.
"Tsawon shekarun nan ke baki san a ƙule muke da ke ba, kin rabamu da ɗan uwanmu kin kankane komai, to su ƙawayen naki baki gaya musu asalinki ba? Kina yawo da yunwa ba suturar kirki takalmi ya siɗe, Allah ya jiƙan Gwaggon mu ta janyo ki inuwa, amma saboda butulu ce ke bayan mutuwarta kalli yadda kika mayar da ɗanta, Hajiya har ta bar duniya tana kukan rabata da ɗanta da kika yi, ba kunya kin hau kan stage kina cin mutuncin sirikar ki, tir da halinki wallahi".
Tsit hajiya Zainab tayi, Hajiya Bilki tayi mata wankin babban bargo, sam bata san ta zo garin ba, dan rabonta da ita sun fi shekara Goma.
Hajiya Bilki na fita, Hajiya Zainab ta tafi wurin Daddy tana kuka.
Ta tarar da shi Amina na haɗa masa tea, Aminan fuskarta babu walwala.
"Gaskiya Ahmad ni na gaji da wannan wulaƙanci, me nayi wa 'yan uwanka ne haka? Bayan wulaƙanci da aka yi mini a wurn dinner, bai ishesu ba Bilki ta sani a gaba tana ci mini mutunci a daren nan"
Amina ta kalleta ta ce "Alhakina ne, haka kawai ki ka zo kika mini sharri, wai na sa anci mutuncinki, alhalin ni ko ta kanki ban bi ba da naje wurin"
"Amina rufe mini baki, kiyi abin da na saki ki tashi"
Amina kamar ta fashe saboda ɓacin rai, ta cigaba da haɗa masa tea.
Ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Ke me kika yi musu suke zagin naki?"
"Sai nayi musu wani abu? Ai kafi kowa sanin ba ƙaunata suke yi ba"
"Shikenan, ya isa zan yi musu magana"
Amina kuwa na gama haɗa masa ta tashi zata bar falon.
Ya ce "Ya zaki tafi, baki bani wani cup ɗin ba"
"Matarka ta ɗauko maka" ta bashi amsa ta wuce abin ta.
Ɗan shiru Hajiya Zainab tayi, a ranta ta ce 'Cikin sauƙi na samu maganinki, idan asiri yaƙi cinki, na ɓullo ta hanyar makirci'
Daddy ya ce wa Hajiya Zainab "Ki tashi kije, zan yi magana da su"
Girgiza masa kai tayi ta ce "A'a ni dai mu kwana a nan tare, ba zanje su yi mini wani abin ina can kana nan ba"
"Kamar yaya, ba abin da za suyi miki ai"
"A'a ni dai mu kwana a nan kawai, zan kwanta a kan Carfet, ba sai na koma can ba, da Asuba na koma"
Saboda baya son rigima kawai ya ƙyaleta.
Amina ko ta kan baƙi bata kuma komawa ba, dan ta san kowa a ƙosje yake, an ci Abinci sosai a wurin dinner, tayi kwanciyarta dama ga ɓacin rai Jin shiru yayi yawa, Amina har tayi bacci ta farka Daddy bai shigo ba, ya sanya ta sauko daga kan gadon, ta duba falo ko ya tafi ne bai ko yi mata sallama ba.
Tana buɗe ƙofar bedroom ɗin, ta hango shi tare da Hajiya Zainab, kamar hira ma suke yana ta murmushi.
Jinjina kai tayi a ranta ta ce "Lallai ma mutumin nan, kamar ba shi ne kamar yayi kuka ba saboda cin mutuncin da matar nan take masa ba, aikuwa da ni kuke zancen, in dai makirci ne da ni kike zancen gidan kika tarar.
Ta koma tayi kwanciyarta, tana jin yadda zuciyarta ke yi mata zafi.
Washegari da safe, tun bayan sallar asuba, Amina ta fito falonta, da kalar shigar da ta ga dama.
Kitchen ɗin sashinta ta wuce ba tare da ta kula su ba, Daddy binta yayi da kallo, dan ya san a ƙule take, shi kansa ba yadda ya iya ne, gidansa akwai baƙi ita Zainab ba ta ƙi a zubar da mutunci ba, ko a gaban uban waye.
Amina ta zo zata kuma wucewa, sai cewa tayi "Amina ba gaisuwa ne?"
Amina ta kalleta ta ce "Da can muna gaisawa ne? Mu cigaba a yadda muke a da, bana son takura da kinibibi"
Daddy dai yayi shiru bai tofa musu ba.
Amina ta gama kintsawa, ta fito ta kalli Daddy ta ce "Baby, kayanka na ɗaurin aure na kan gado, zanje in kula da baƙina" da haka ta fice ta bawa iska ajiyarsu.
Gida ya cika da mutane, aka gama haɗuwa aka tafi wurin ɗaurin aure.
Duk zafin Hajiya Bilki da ake faɗa, amma Amina bata gani ba, sai ma tasu da ta zo ɗaya. Wuni aka yi ana hada hada, Amina tama manta da batun wata Hajiya Zainab, saboda yadda jama'a suka cika gidan, ga 'yannuwa ta ko ina, Baba da su Inna har da s Baffa Bala duk sun zo, Amina taga 'yan uwan Hajiya Zainab wanda gara ma nata 'yan uwan sun fisu kyan gani, gaba ɗayansu ba wani na kirki duk kamar wasu gajiyayyu haka suke. A ranar ma su Turai ma sun zo da Hajiya Salma, sai dai ba wanda ya shiga sabgarsu.
A ranar Hajiya Salma ke gaya wa Fadila, ai jibi Salim zai zo dan yanzu haka yana ƙasar ma Washegari zai iso Kano.
Fadila ji tayi kamar ta ce mata yayi zamansa bata san zuwan, amma ba yadda ta iya haka ta haƙura ta yi shiru tana yaƙe.
Bayan an yi ɗaurin aure aka yi wunin biki, tun ƙarfe shida su Anty Bilki suka tafi ɗauko amarya.
Mama ta yiwa Hafsa nasiha sosai da sosai, duk da ita Maman ba a ranar zata tare ba, sai bayan sati da tariyar Hafsa, gashi in da Maman zata zauna da in da Hafsa zata zauna, akawai nisa sosai da sosai.
Hafsa ta sha kuka kamar ba gobe, Mama tayi mata addu'a sosai, sannan aka ɗauketa zuwa gidan Alhaji Khalil.
Tun a ranar wasu daga cikin baƙin duk suka riga suka tafi, sai waɗanda ba a rasa ba.
Su Inno ma duk suka kama hanya suka tafi Shanono a ranar, su kansu 'yan Dutsen da suka je suka ga gidan Khalil, duk daga can suka dinga tafiya, suka yi ta yaba kirki da karamcin Amina.
Khalil kuwa abokai sun rakashi gidansa, wanda suka kai Hafsa suna ta yaba kyau da tsaruwar gidan.
Abdul ya tsaya yayi musu nasiha tare da yi musu fatan alkhairi, yayi musu sallama ya tafi.
Bayan Khalil ya dawo daga rakiyar Abdul, ya dawo bedroom ya tarar da Hafsa a in da ya barta cikin mayafinta tana ta goge hawaye.
Ya cire babbar rigarsa, ya dawo kusa da ita ya zauna, ya sauke mayafin da ke kanta, ya saka hannu ya ɗago fuskarta da ta jiƙe sharkaf da hawayen, ya girgiza kai ya ce "Madam, haryanzu kukan bai ƙare ba? Ko dai na murna ne?"
Duk da kuka take yi, sai da ɗan tura baki jin abin da ya ce.
Rungumeta yayi ta gefe, yana lumshe ido, tare da furta "Alhamdilillah, Allah ya cika mini burina, bayan shan gwagwarmaya har na riga na fidda rai da samunki, amma da yake Allah yayi Rabona ce ke, sai gashi Allah ya bani ke"
Ita ji tayi duk ya takurata, yadda ya rungumeta ta dai yi shiru, ba ta ce komai ba.
"Zo muje muyi alwala muyi salla"
Ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin ɗaukar mayafinta, ya ƙwace mayafin ya ajiye ya ce "Hijabi Queen, ai an ɗaura" yayi maganar cikin murmushi, suka yi alwala suka dawo suka gabatar da salla. Yayi musu Adduoi sosai da sosai.
Sai dai Hafsa ta ci kazar da ya kawo, ta kafe ta ce ita ba ta jin yunwa.
Ya ce "Shikenan, kya ci lokacin da kike so, ki sha madarar to"
Ta ce "To" ita ma yana kallonta ta sha kaɗan ta ajiye masa. Shi kuwa Khalil dama yunwa yake ji, dan haka ya zauna ya ci ya ƙoshi abin sa.
Ya yi ta lallaɓata tamkar ba abin da zai yi mata, ta saki jikinta ta kwanta har bacci ya fara ɗaukarta, yana kallon yadda ta kwanta da kayan jikinta bata sauya ba.
Rigimar Khalil ɗin ce ta farkar da ita daga baccin da take yi, haka tayi 'yan koke-kokenta ta ƙyaleshi yayi bajakolin soyyyarsa.
Washegari a gidan Daddy kuwa, Amina da wuri ta tashi tayi girki, ta ɗauko fulasanta masu kyan gaske, ta zuba Abinci, ta bawa Zakiru ta ce ya kai gidan Khalil.
Zakiru ya ce"Allah sarki, Allah mai yadda ya so, Allah ya ja zamaninki a gidan nan uwar ɗakinmu, mu aurarki da aka yi mu aka yiwa wallahi, kowa ma kyautata masa kike, yanzu duk wulaƙancin matar nan, amma kika yi girki a kaiwa Sirikata?"
Amina ta ce "Zakiru kenan, baka rabo da zolaya ka kai musu dan Allah kar rana tayi".
Zakiru ya karɓi kwanuka, ya tafi ya kai gidan Khalil.
Shi kansa Khalil yayi mamaki, da Zakiru ya ce masa ai Amina ce ta saka a kawo musu Abinci.
Bedroom ya nufa, in da Hafsa ke bacci, yana shiga ya tarar da ita ta tashi.
Yayi murmushi ya ce "Ashe kin tashi, dama tashi ki zan yi, Amina ta aiko mana da Abinci"
"Wace Amina?"
Khalil ya ce "Amaryar Daddy"
Hafsa ta ce "Wai meyasa baka ce mata Anty ne? Tana da kirki sosai"
"What? Anty kuma to ai ko ke kin girmeta"
Tayi murmushi ta ce "Ko ma yaya ne, ai Daddy ne yake aurenta, ta cancanci a girmamata ko dan albarkacin Daddy"
Ya ce "To naji, sauko muje muyi breakfast" yayi maganar yana miƙa mata hannu ta taso, suka nufi falo.
Hafsa sai kallon Khalil take yi, ko zai sauya mata, amma taga babu abin da ya canza mata, sai ma lallaɓata da yake yi cikin tattali da kulawa.
Ganin tana ta kallonsa ne ya sanya ya ce "Ya dai, ko na ƙara kyau ne?".
Girgiza masa kai tayi, a dai-dai lokacin da hawaye ke zubowa a idonta.
A rikice ya ce "Hafsat menene? Me nayi miki kuma?"
"Am very sorry Khalil, kowace mace da ta san kanta, babban burinta shi ne ta kai mutuncinta gidan aure, amma ni Najib ya cuceni tayi maganar tana rushewa da wani irin muka, mai ban tausayi.
"Dan Allah Hafsa bana son iri wannan maganar, ni kin ji nace miki wani abu? Impact waye ya ce miki baki zo da mutuncinki ba?" Ya rungumeta sosai a jikinsa ya ce "Dan Allah ki cire wannan tunanin daga zuciyarki, Khalil ke yake so ba wani abu daban ba, kuma ni komai normal just forget dear, ba abin da zan ce miki sai ubangiji Allah ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka, ina sonki sosai da sosai kuma saboda Allah, Allah ya bar mini ke har ƙarshen rayuwata, ke duk balahirar da ta faru jiya, still kina tunanin baki da daraja a idon mijinki, ki Kwantar da hankalinki kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyata, bari na baki abincin da kaina a baki".
Khalil yayi ta ƙoƙarin kawar mata da duk wani tunani daga zuciyarta.
Wajen sha ɗaya na safe, su Anty Bilki suka yi wa Amina sallama, kamar kar su tafi, tayi ta nanata wa Alhaji Ahmad "Wallahi Engineer a riƙe mana amarya da mutunci da amana, dan ba zamu lamunci duk wani cin kashi da za a mata ba, yanzu muka san kayi aure"
Daddy ya ce "Naji, A sauka lafiya masifaffiya" shi kansa Daddy yaji daɗin yadda yaga 'yan uwansa sun taru sun cika gidan, rabom da ya hakan har ya manta.
Anty sai da suka je gidan Khalil, suka kuma ganin amarya sannan suka tafi gida.
Amina sai da ta tabbatar komai yayi normal, an gyara ko ina a gidan, sannan ta samu nutsuwa.
Daddy ne ya shiga sashinta ya tarar tana cin abinci. Tayi kyau sosai a cikin atamfarta da aka yi mata ɗinkin riga da skirt.
"Shi ne kike cin abinci bani ko, ba ƙoshi zaki ba ai" Ya zauna kusa da ita, amma Amina ta miƙe ta nufi bedroom.
Yayi murmushi ya ce "Na san a rina ai"
Ya tashi yabi bayan ta, yana shiga ya tarar da ita tana cin Abincin tana kuka.
Ya karɓe plate ɗin ya ajiye a gefe guda, ya tsura wa kyakkyawar fuskarta ido, da hawaye ya samu muhalli a kumatunta.
Gyara zamansa yayi yana share mata hawayen fuskarta.
"Am sorry dear, ba nayi abin da nayi ne, dan na ɓata miki rai ba, duk nayi ne saboda na tsare mutuncinki, kar in bada wata ƙofa da zata tada jijiyoyin wuyanta, ta zubar mana da mutunci ba ki ɗaya. Baki ga yadda familynmu ke yabonki, ba nayi ne dan na baƙanta miki ba, sai dan kar ki biye mata".
Cikin kuka ta ture hannunsa daga fuskarta ta ce "Amma shi ne kuka kwanar mini a falo, saboda tsabar cin fuska"
Danne dariyarsa yayi ya ce "To ai ba abin da yafaru, na san ranar a wurinki nake, duk dan a zauna lafiya ne, idan ma abin da kike tunani kenan to bai faru ba"
Ta tura baki ta ce "Idan ma ya farun ina ruwana?"
"Bai ma farun ba, idan ma ya farun sai in biyaki abin ki yanzu" ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da kissing ɗinta.
Ta tura baki ta ce "Ni ka bari"
"A'a ba zam bari ba sai kin huce" ya lallɓata daga fushin da take yi.
Ya ɗauko Abincin ya cigaba da bata tana ci.
Saboda tsabar masifa, a washegarin biki, su Turai duka dawo gidan, suna sake ziga Hajiya Zainab a kan yadda zata yi da Khalil da matarsa, da yadda za ta cizguna musu, har Hafsa ta haƙura ta rabu da Khalil ɗin, babu tunanin komai ta dinga ɗaukar shawarar ta su.
Fadila tana zaune a ɗakinta, tana duba litattafanta, saboda suna da teses a satin nan, amma ba abin da take ganewa, karatun kawai yi take yi, ga shi tun a daren jiya Mummy ta sanar mata da cewa wai Salim zai zo.
Ƙarfe huɗu na yamma, Mummy ta zo ta sameta a ɗakinta, wai ta shirya ga Salim can ya zo.
Turus Fadila tayi, kamar ta ɗaura hannu a ka tayi ihu, duk ta ɓata fuska kamar tayi kuka.
Mummy ta zauna a kusa da ita ta ce "Haba Autata, ai na san ba zaki bani kunya ba, shiyasa nake alfahari da ke yarinyar kirki" Tausayin Mummy ne ya kamata, dan haka ta sanya a ranta ko dan farincikin Mummy za tayi haƙuri ta auri Salim.
Ta ce "To shikenan Mummy, zan yi yadda kike so in sha Allah"
"Yauwa yarinyar kirki" jiki ba ƙwari Fadila ta tashi ta shirya, tana ta fargabar yadda zata ga Salim.
Jiki a sanyaye Fadila ta nufi harabar gidan, in da Mummy ta gaya mata Salim yana harabar gidan a kan fararen kujeru.
A hankali ta ƙarasa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun.
Kallo ɗaya tayi masa, wani takaici ya ƙuleta, ita sirirya shi siriri kamar ba namiji ba, ba wani kumari a tare da shi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi mata, tamkar ɗan iska yana ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa.
"Barka da wannan lokaci amaryata"
Fadila ta ɗan yamutsa fuska, ta amsa masa.
Haka ya dinga zuba mata surutu, ba tare da tana tanka masa ba.
Ya ƙaraci surutansa da iyayinsa tare da tsare-tsaren sa, yayi mata sallama ta tashi ta koma cikin gida.
A ɗakinta ta zauna kamar tayi kuka, gaba ɗaya Salim haushi ya bata sam bai yi mata ba.
Mummy kuwa ta koma wurin Fadila dan jin yadda suka yi da Salim.
Fadila bata nuna mata komai ba, ta nuna mata ta amince da batun Salim, amma ƙasan zuciyarta a cunkushe yake da haushin Salim.
Kwanan Hafsat biyar a gidan Khalil, kwanaki biyar ɗin nan a jere Amina ta cigaba da aika musu abinci, Khalil ya ɗauketa ya ce bari suje su gaida su Mummy.
Tun da Khalil ya ce zasu je gaida Mummy, Hafsa take faɗuwar gaba.
Amma haka ta dake, ta tashi tun wuri ta hau girki, ta zuzzuba a manyan flask.
Ya ɗauketa a mota suka tafi gidan su Khalil!!!
AYSHERCOOL
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, KU TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA DOMIN KU SAI NAKU.
08081012143
71
Ba Hafsa ba, hatta shi kansa Khalil ɗin a tsorace yake, dan bai