Showing 90001 words to 93000 words out of 296192 words

Chapter 31 - GABA DA GABANTA

Ya koma taro baƙinsa.

Amina dai gaba ɗaya a tsorace take, wannan gidan sai ayi garkuwa da mutum ma ba wanda ya sani, Amina ta ci Abinci, ta gama amma zaman ya isheta, dan haka ta kwanta a nan ƙasan carfet, wani nannauyan bacci ya kwasheta.

Ya ɗan jima a tsaye a kanta yana kallonta, sannan ya durƙusa daf da ita
"Amina ki tashi kiyi sallar la'asar mu tafi" A hankali ta buɗe idonta, firgigit ta tashi zaune, saboda ganin Alhaji Ahmad a tsaye a kanta.

Miƙewa tsaye tayi, tana murza idonta.

"Ni mu tafi kawai"

"Ba zaki sallar ba?" Ta ɗaga kai alamar eh.

Ta durƙusa zata ɗau kwanon da taci Abinci ya kalleta ya ce "Bar shi a nan, za a gyara komai insha Allah, muje sai kin yi salla zamu tafi, biyar da rabi fa"

Hankalinta bai kwanta ba sai bayan tayi sallar,  taga sun fita daga gidan sun hau titi sosai, sun fito daga gidan nan.

Suna tafe a hanya Daddy ya ce "Naji daɗi sosai, kin fitar da ni kunya, suna ta godiya, Allah yayi miki albarka, Ahmad ya gode sosai"

Ta ɗan kalle shi "Waye Ahmad?" Ta tambaya, dan ta manta sunansa ne.

"Baban Fadila da Aminatu" murmushi tayi ta ce "Au na manta sunanka ne"

Ta kashingiɗa a jikin seat, tana lumshe ido.

"Kin gaji ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Eyya, sannu to, and please wannan ma sirrinmu ne, kin taimakawa Daddynki, ya fita kunyar abokansa is our secret"

"Tom, ba zan faɗawa kowa ba insha Allah" tayi maganar tana murmushi.

Ya zura hannu a aljihunsa, ya zaro kuɗi a envelope ya miƙawa Amina.

Ta kalleshi ta ce "Na menene wannan?"

"Kuɗi ne na baki, tukuicin abin da kika mini ne, na katse miki karatun ki kin mini aiki"

"Ai dama dai sai ka nuna banbanci duk da kace ni 'yar ka ce" tayi maganar tana tura baki.

"Banbancin me fa?"

"Idan kasa Fadila aiki biyanta kake?"

Mamakin Amina yake, sam yanzu bata shakkarsa, ko shakkar faɗa masa magana.

"Eh to, na kan mata tukuici da wani abu, dan na faranta mata rai"

"Ai ni kayi mini abubuwa da dama, kana ciyar dani, ga wurin kwana, ga kuma karatuna, me zai sa sai ka kuma bani wani abu?"

"Wannan ai duk daban"

Ɗan shiru Amina tayi sai kuma ta ce "Daddy"

"Na'am 'yar Daddy"

"In roƙeka wani abu?"

"Kan ki tsaye makuwa, me kike buƙata?"

Nan ta labarta masa, gidan da ta wuce ɗazu da safe, ana fito musu da kaya.

"Yanzu me kike so ayi?"

"Dan Allah ka biya musu, tunda kana da kuɗi"

"Waye ya ce miki ina da kuɗi?"

"Kai ka gaya mini sayar da kuɗi kake, kuma kalli motarka da gidanka, ai dai kana da kuɗi sosai"

Murmushi yayi, ya shafi dogon gemunsa, da yake baƙi da fari kaɗan kaɗan a cikinsa.

"Daddy baka ce komai ba"

"Sai na tambayi mata ta, idan ta amince sai a biya musu"

Haɗe rai Amina tayi ta ce "Ashe ba za a biya musu ba kuwa"

"Me kike nufi?"

"Ai wannan matar 'yar hana ruwa gudu ce, ba zata taɓa barin ayi abin arziki ba"

Daddy ya haɗe rai ya ce "Matar tawa ce 'yar hana ruwa gudu?"

Amina shiru tayi tana ɗan kallon gefe dan da zata samu dama, sai ta ɗuɗɗurawa Hajiya Zainab Ashar dan ta huce.

"Kayi haƙuri, amma wallahi bata da....

"Ke!" Ya daka mata tsawa da sai da ta razana ta kalleshi.

"A gaban nawa zaki zagi uwar 'ya'yana" ji tayi kamar ta ce "Nima a gabana take zagin babana' amma ya koma mata Alhaji Ahmad ɗinsa, dole ta haɗiye maganarta.

Parking ya yi ya kalleta ya ce "Fitar mini daga mota"

"Gida da nisa fa daga nan" ta faɗa kamar tayi kuka.

"I don't care, get out" ya faɗa in a serious tone. Buɗe motar tayi a fusace, ta fice ranta a ɓace.
Ɗan guntun murmushi yayi, ya ja motarsa yayi gaba.

Da ƙafa Amina ta nufi hanyar gida, tana tunanin yadda zata ƙarasa gida a ƙafa.
Ran Amina ba ƙaramin ɓaci yayi da abin da Alhaji Ahmad ya mata ba, yana ta mata kirki, amma dan ta faɗi magana a kan waccan azababbiyar matar ya mata wulaƙanci, duk wahalar da tayi masa, amma bai gani ba, meye ya hana ita 'yar lelen matar tasa tayi masa?.
Haka Amina tayi ta zancen zuci tana mita a ranta.

Horn ɗin motar da ta ji yayi mata yawa a kunnuwanta ne, ya sanyata waiwaya.
Murmushi me motar ya sakar mata, gani tayi kamar ta sanshi, ta hau tunanin a in da ta san shi.

"Gida zaki ne?"

"Eh" ta bashi amsa.

"Kamar baki gane ni ba, Bilal ne na nan layinku, muna gaisawa fa idan zaki tafi makaranta" sai yanzu ta tuna shi, yana yawan yi mata adawo lafiya, idan zata tafi makaranta.

"Sannunka ya kake?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, taho mu ƙarasa".

Ɗan shiru Amina tayi, yamma tayi liƙis, ta san yanzu haka Baba ya fara tunanin ina ta tsaya, kuma idan ta ce da ƙafa zata ƙarasa kuma, magariba zata rufa mata.
Dan haka bata da zaɓi illa tabi Bilal.
Suna tafe a hanya yana mata hira, ita gaba ɗaya hankalinta baya kansa, fatanta kawai su ƙarasa gida.

Suna zuwa ƙofar gidan, Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar tana masa godiya. Bilal ya ce "Bakomai, muje nima in gaida Baban"

Amina dai ba ta ce masa komai ba, baya son gwaleshi, bayan ya taimaketa.

Tare suka shiga cikin gidan, sai dai Baba baya nan, Dan an fara kiraye kirayen sallar magariba.

Amina ta kalleshi ta ce "Ina ga ya tafi masallaci, na gode sosai".

Bilal ya ce "To ko zaki bani lambar wayarki?"

"A'a ai bani da waya" suna cikin maganar, sai ga Alhaji Ahmad ya fito zai tafi masallaci, tun daga nesa ya fara yi musu wani irin kallo, musamman Amina, Amma Amina ta basar ta mayar da hankalinta kan Bilal.

TOFA ME KUKE TUNANI.
MASU SAN POSTING KULLUM, SU BIYANI IN BUƊE MUSU VIP, ZAN DINGA POSTING KULLUM INSHA ALLAH

AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

PAGE 32-33

Duk da Amina ta sha jinin jikinta da irin kallon da Alhaji Ahmad ya yi musu, amma ta maze ta ƙi ko ɗaga kanta, balle ta nuna ta san ita yake yiwa wannan kallon.
Bilal ya gaida Alhaji Ahmad, amma ya amsa masa sama-sama ya fice, Amina na ganin fitar Alhaji Ahmad, ta yiwa Bilal sallama ta shige cikin gida.

Fadila kuwa tun da Kankiya ya Kori Yazid daga ajin, hankalinta yake a tashe, ta rasa meya kamata ta yi, tamkar a kan ƙaya take haka ta dinga jiran Kankiya ya fita ita ma ta fita, ganin ba shi da niyyar fita ne, ya sanya ta tashi ta nemi excuse zata fita, amma Fafur Kankiya ya hanata, ji tayi tamkar ta je ta shaƙe shi ta gwara kansa, wata irin tsanarsa ta ninku zuciyarta.
Sai da yayi kusan awa biyu da wani abu sannan ya bar ajin, yana fita Fadila ta fita, ta dinga duddubawa ko zata ga Yazid, amma babu Yazid babu dalilinsa, duk in da ta san zata ganshi ta duba amma bata ganshi ba, hakan ya sa tayi tunanin gida yayi tafiyarsa, alamar yayi zuciya.
Tunani ta dinga yi, wani irin hukunci yakamata ta yiwa Kankiya, wani mataki yakamata ta ɗauka a kansa, amma sai ta yi tunanin kar tayi wani abu a kai, ya kuma cutar da Yazid, haka nan ba tare da ta yanke shawarar komai ba, ta shiga motarta ta tafi gida cike da damuwa.
  A gidanma kasa sukuni tayi, gashi ita ba lambar Yazid ba, balle ta kira shi a waya taji meyafaru bayan fitarsa daga aji ba.
Tana tsaka da wannan tunanin, sai ga kiran Kankiya, ji tayi kamar tayi jifa da wayar, amma tayi yaƙi da zuciyarta ta ɗaga.

"Amincin Allah ya tabatta a gareki amaryata" ji tayi kamar ya watsa mata wuta a zuciyarta, ko muryarsa ba ta ƙaunar ji sam.

"Me ka kirani kayi mini, wai ban maka kashedi a kan kirana ba?"

"Kina fushi da ni dan na kori saurayinki daga aji ko? Ai abinda na gaya miki ne Fadila, muddin ba zai rabu da ke ba, zan ta wahalae da shi ne"

"Wai kai waye ya gaya maka Yazid saurayina ne? Babu wani abu mai Kama da soyayya tsakani na sa Yazid, kuma bari in gaya maka wani abu, wallahi muddin baka kiyaye ni a kan batun soyayyar nan ba, sai na maka abin da har ka mutu ba zaka manta ba*

Yayi dariya ya ce "Ni ma kuma zan yiwa Yazid ba, dan naga a duniya idan ana son ɓacin ranki, to a taɓa Yazid"

Sai kuma yayi ƙasa da murya ya ce "Haba Fadila, duk ke kika saka al'amura suka zama so complicated like this, ni ina da kishi sosai da sosai, shiya sa ba zan iya jure ganinki da wani ba, wallahi idan Yazid ya fita daga harkarki babu ruwana da shi. Yanzu gaya mini yaushe zan zo gidanku?"

"Abudrrasheed Kankiya, banda ina ganin darajar alli da duster, da sai na nuna maka wacece Fadila, na lura rashin sanin wacece ni ya sanya kake mini karan tsaye yadda ka ga dama"

"Hmmm, koma dai menen ai nasan ke mutum ce, kuma duk matsayinki dole zaki aure wataran ƙarƙashin inuwar wani, Fadila mu daina samun wannan saɓanin, in daina wahalar da ɗan mutane, ki fita harkarsa ki bani dama in gwada miki soyayya"

"Shikenan, ni da kai mu zuba mu gani,ka koma ka ƙarewa kanka kallo, sannan ka ƙare mini kallo kasan wacece ni, kan kace kana sona ka san matsayina tukuna, wallahi ka cigaba da takura masa zan nuna maka abin da zan iya yi a kai"

Kankiya ya yi ajiyar zuciya ya ce "Saboda shi Yazid ɗin duk kike gaya mini wannan maganganun?"
"An gaya maka ɗin, kayi abin da zaka iya" daha haka ta kashe wayar , tana jin tamkar ta sa a ɗaure Kankiya, ita tausayin Yazid take ji, idan aka ɓata masa career an cuce shi, amma Kankiya na son amfani da wannan damar ya tilasta mata ta so shi, bata taɓa tausayin wani ɗan Adam a rayuwarta ba, kamar yadda take tausayin Yazid. Ita kawai kyawawan halayensa take kallo, sai taga kamar idan aka cutar da shi ba a yi masa adalci ba, yana da halaye masu kyau, ba ya cutar da kowa to shi mai zai saka a dinga cutar da shi.
Ta tuna irin kasadarsa mussaman a ɗakin jarrabawa, dan kar wani ya faɗi, da tsananin biyyarsa ga malamai, amma hakan bai hana a dinga dizga shi a gaban aji, ba tare da duba halayensa masu kyau ba.
Dafe goshinta tayi, ji tayi kamar kanta ya fashe Saboda rasa mafita.

Ɓangaren Khalil ma yana cikin ɗumbin damuwa, Hafsa ta buɗe what's app a wayar da ya bata, har tayi masa magana ta what's ɗin, sai wani ƙara lallaɓa shi take, tana bashi kulawa ta mussaman, da Adduoi, nasiha gami da kalaman soyayya, wanda hakan ke ƙara masa sonta a ransa. Gaba ɗaya Mummy ta ɗauke masa wuta, ta daina shiga harkarsa, duk dan saboda yana son Hafsa.

Gaba ɗaya fushin da Mummy take yi da shi, bai yi masa daɗi ba, hakan ya sanya, ya kuma ƙoƙarin zuwa ya rarrasheta, sannan yayi mata bayanin halin da su Hafsa ke ciki, ko Allah ya sa ta fahimce shi.
Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mummyn, ya tarar da ita a kan gadonta, tana danna Computer, gefenta kuma ga calculator, da alama kuɗi take ƙirgawa.

Tun da ta ɗaga kai ta kalleshi sau ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da abin da take yi.

"Mummy sannu da aiki"

"Yauwa" ta amsa a daƙile ba tare da ta kalleshi ba.

"Mummy wurinki na zo"

"Ai na ganka, ina kuma jinka"

Khalil ya ɗan gyara zama tare da sosa kai ya ce "Mummy, dama game da Hafsa ne, yarinyar nan da aka ce miki an ganni a wurinta, Mummy yarinyar marainiya ce ne, Da mahaifinta mai abin hannunsa ne, kan ya rasu ya saya mata kadarori, sai dai bayan rasuwarsa dangin mahaifin suka ƙwace komai, shiyasa kika gansu a haka, amma tana da kirki da kuma hali mai kyau, ba ta da wata matsala yarinyar"

Ai tamkar dutse yayi wa wannan dogon jawabin, dan danna calculator kawai take tana shigarwa cikin Computer.

"Mummy ba ki ce komai ba"

"Me kake so in ce maka, ai kai an shanyeka, ni kuwa ba a shanye ni ba a hayyacina nake, nayi mamakin wurin wani malami suka je haka, da har ka iya zuwa ka tunkare ni ni Hajiya Zainab, kake mini wannan maganar banzan, ban sani ba ko orphanage Home ka buɗe, zaka fara rainon marayu da marasa galihu, da har zaka yayi mo min wannan shirgin tsiyar, Khalil banda rashin hankali irin naka, ina kai ina mai suyar Awara a titi, ba bu ilimi mai zurfi, ta gama zaman titi maza sun gama kalleta, in anjima ta ci kwalar namiji, kuma ka ce mini ita ce sirikata,ai kai ma ka san kayi ƙarya"

"Mummy wallahi ba haka Hafsa take ba, tana....

"Dalla rufe mini baki, ina magana kana wani kwantar da murya ce, cece, ni zaka lallaɓa in anince da auren 'yar matsiyata, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, daga yau babu kai babu yarinyar nan, na yanke duk wata alaƙa da take tsakaninka da ita, wallahi na bibiya na tarar ba ka rabu da ita ba, hukuncin da zan yanke maka ba zai maka daɗi ba"

"Mummy dan Allah, ki duba lamarin nan"

"Ni kake cewa in duba lamarin nan, wato sihirin har ya kai ka fifita ta a kaina"

Cikin rauni ya ce "Ba haka bane Mummy, wallahi ba suyi mini asiri ba, suna buƙatar tainako ne Mummy, kuma muna son juna sosai"

Mummy ta jinjina kai ta ce "Da kyau Khalil, suna buƙatar taimako ko, sannu gwamnati kowa naka, tashi ka fita ka bar mini ɗaki" ta nuna masa hanyar fita.

Zai kuma magana, ta sake haɗe rai ta nuna masa hanyar ficewa, haka ya haƙura ya bar mata ɗakin zuciyarsa babu daɗi.

Amina kuwa ba ƙaramin haushin abinda Daddy yayi mata taji ba, haka ta shiga ɗakinta, tayi alwala tayi sallar magariba, ta shiga kitchen ta hau aikin Abincin dare, kasancewar Hajara ce tayi na rana tunda ita tana makaranta.
Gaba ɗaya Amina a gajiye take, tunda kusan wuni tayi aikin da Daddy ya sakata, aikin da a ƙarshe ya sakamata da direta a titi yayi tafiyarsa saboda tayi maganar matarsa.
Ta gama girkin, ta kai dining, ta ɗau na Baba ta tafi ta kai masa, ta tarar da Baban a cikin ɗakinsa na gadi, yana jin radiyo.

Har zata fita, Baba ya kirawota, ta dawo ta zauna tana kallonsa.
Ya ɗauko wata 'yar jaka ya miƙa mata, ta sa hannu ta karɓa, ta buɗe jakar wani babban kwalin waya ta gani a ciki, ta saka hannu ta ciro wayar tana kallon Baba.
"Baba wannan wayar fa?"

Baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Alhaji Ahmad ne ya bani, ya ce in baki, wai saboda ki samu sauƙin karatu, sai dai har ga Allah ni bana son ki mallaki wayar hannu yanzu, amma bana son yi masa jayayya kuma naji ya ce saboda karatunki, ina fatan dai ba roƙonsa ki ka yi ba?"

"Haba Baba, ka san bana roƙo, wallahi ni ban roƙe shi ba"

"To sai kiyi masa godiya, duk da nima nayi masa"

"To, insha Allah zan masa"

Ta tashi tana jujjuya wayar ta bar ɗakin Baba.

Har ga Allah tana matuƙar son waya, mussaman duba da yadda ƙawayenta ke da wayar, amma ita ba ta da ita, sai dai da ta tuna da abin da Daddyn ya yi mata, sai haushi ya kamata har ta ce "Mayar masa zan yi, ban so" ta jiye wayar a gefen katifarta tana harar wayar tamkar Alhaji Ahmad ɗin ne a gabanta.

Washegari da Safe Amina bata da niyyar zuwa lesson, ta tashi ta hau aikace-aikacenta, ta shiga kitchen ta ɗora sanwa, ta yi girkin safe ta kammala, ta zo ta shiryawa masu gidan nasu Abincin, sannan ta kaiwa Baba nasa ta dawo, ta fara mopping ɗin falo.
Hajiya Zainab ce ta fara fitowa, Amina ta gaisheta ta amsa mata da ƙyar kamar an yi mata dole, sai kuma Fadila ta fito, Alhaji Ahmad ne ƙarshen fitowa, ba tare da Amina ta kalli in da yake ba, ta gaishe shi, yana jinta ya shareta, kamar ba da shi take ba.
"Good morning Daddy" Fadila ta faɗa tana ƙoƙarin haɗa tea.

"Morning sweetheart, how are you"

"Am fine Daddy"

Ya ɗan ƙara kallon Fadila ya ce "Meke damunki ne, you look dull today"

Fadila ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Nothing much, stress ne na school kawai"

"To Allah ya bada sa'a, yau weekends ki samu ki huta sosai"

"Ok Dad"

Ya mayar da hankalina kan Mummy ya ce "My Z ina Khalil ne?"

Mummy da ta kai loma bakinta, ta ƙarasa taunawa sannan ta ce "ƙyale shi kawai"

'in ƙyaleshi kamar yaya, ban gan shi a wurin cin Abinci ba"

"Ka san halinsa wasu lokutan, maybe bacci yake yi"

"Is ok" Daddy ya faɗa yana cigaba da cin Abincinsa. Yana yi yana satar kallon in da Amina ke mopping, tayi kicin kicin da rai, ko kallon in da suke bata yi, aikinta kawai take.
Ɗan guntun murmushi yayi, ya cigaba da cin Abincinsa.

Bayan sun kammala ci, Mummy ta miƙe tsaye, ta kalli Fadila ta ce "Fadila je ki shirya muje ki rakani gidan Hajiya Turai"

Fadila ta ɗan tsuke fuska ta ce "Mummy ki je ki kaɗai, ni bana son fita"

"Aikuwa sai kin je, tashi maza muje"

Fadila tana tura baki, haka ta tashi, ya wuce ɗaki, dan ta fara shirin yiwa Mummy rakiya, idan ba haka ba ta san halin Mummy, idan ta dinga mata mita sai taji babu daɗi.

Suka wate suka bar Daddy a falo, Amina kuma na zaune na goge TV.

"Ke da waye jiya na gani a tsaye a gidan nan?" Amina ta ɗaga kai ta duba falon, amma bata ga kowa ba, dan haka ta san da ita yake, maida kai tayi ta cigaba da aikinta.

"Ko in zo in maimaita miki ne?"

Ta ce "Ba kowa"

"Kina nufin ƙarya nake kenan?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ke da waye?"

"Bilal ne, a nan layin yake, bayan ka ajiye ni a hanya, ya ɗauko ni"

Alhaji Ahmad ya ce "Ban tambayeki wannan ba, abu ɗaya nake son gaya miki, kar ki sake kawo mini wani gida, kin zo gidan nan ne dan kin yi aiki da karatu, idan saɓanin haka ne a ranki, to zan sanar da Malam Hassan tun wuri ya san matakin da zai ɗauka,  karki ƙara kawo mini wani gida kinji na gaya miki, idan kuma aure kike so sai kiyi bayani, amma gidana ba wurin tara maza bane"

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login