Showing 111001 words to 114000 words out of 296192 words

Chapter 38 - GABA DA GABANTA

fuskarta ta ce "Girl ya dai? Na ganki rai a ɓace".

Fadila ta zauna tana ɗan hura hanci.

"Ke wai meye ne?" Yusra ta faɗa tana sake tattara hankalinta a kan Fadila.

"Kin san wani abin takaici da raini?"

"A'a sai kin faɗa"

"Yazid fa sona yake" ta faɗa cike da takaici.

"Au da da nake gaya miki baki yadda ba? Me yayi miki ne?"

"Wai Allah ya bani miji nagari ko shine"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce "Gaskiya Fadila baki da wayo, ke ce baki da tunani wasu lokutan, idan ba sonki yake ba mai zai saka yayi ta bibiyarki har ya dinga taimaka miki, yayi ta miki abubuwan da zai burgeki" Fadila ta ɗan yi shiru ta ce "Lalli bani da hankali, kawai na ɗauki alaƙarmu ne a friendship, ni mai yasa mazan nan suka rainani, amma Yazid tsaurin idonsa ya kai in da ya kai, ina shi ina mace kamar ni?"

"Kar ki cika baki malama, tun da ya fara bijirowa a mafarkanki da kika gaya mini, akwai alamar cigaba da tarayyarku ka iya sanyawa ki fara son shi, saboda gayen yana da kirki sosai"

"Ashe kuwa da Mummy ta kwaɗani ta cinye, kin san a tashin hankalin da Yaya Khalil yake dan ya ce yana son mai awara, hmm naga wautar Yaya Khalil"

Yusra ta ce "Ikon Allah, shi kuwa Yaya Khalil meya yi masa zafi?"

"Oho masa, duk yadda suke da Mummy,tayi masa fata fata, ko cikin gida ba ya iya shigowa, ba kiga ko jiya bai shigo wurin birthday na ba. Ina gama alhakinki ne"

"A'a kar ki ce haka Fadila, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi"

"Amin dai, da nazo na gaya miki maganar nan har naji sanyi, ni wallahi tausayi yake bani ma, Kankiya ya sako shi a gaba da yawa a kaina, ni kuma bana son a lalata masa karatunsa saboda ni, amma shi ma Kankiya tara sh nake, idan ya kaini bango sai ya rasa aikinsa wallahi"

"A'a Fadila ki bi a hankali dai"

"Ai a hankalin nake bi, ke kin san da ba a hankalin nake bi ba, Kankiyan shi da koyarwa a jami'ar nan har Abada, banda ke babu wanda ya san abin da ke tsakanina da shi, sai Yazid, shi kuma wannan ko ban gaya masa abu ba, ganowa yake kamar aljani"

Yusra ta ce "Do you know one Funny thing? Kin iya faɗar sunansa wallahi, har wata madda kike Yaziiiid"

Tsaki Fadila tayi ta ce "Ke bana son wulaƙanci, bana son duk wani abu zai sake haɗani da shi, kowa yayi rayuwarsa kawai".

Yusra ta ce "Shikenan, tunda kin huce yanzu a kan yadda kika zo mini"

"Bari kawai ya ƙular da ni ne, da wani shegen takalminsa irin na danƙon nan, sai uban saka jallabiya kamar limamin harami"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce A'a kar ki zafafa dai"

Fadila ta kai kusan twenty minutes tare da Yusra, sannan ta koma department ɗin su.

Da idanun Yazid ta fara cin karo, kallo ɗaya zaka yi masa, ka gane jikinsa yayu sanyi, guntun tsaki tayi ta wuce wurin zamanta.

Ƙarfe biyu daidai, aka tashi daga makaranta, Amina tayi sallama da 'yan ajinsu, ta fito gate.
Wata uwar mota ta gani a bakin gate ɗin makarantar ta su a tsaye, da wasu 'yan sanda biyu a jikin motar.
Bata kawo tunanin komai a ranta ba, ta cigaba da tafiya. Ji tayi kamar ana binta a baya, ta waiwaya taga 'yan Sandan sun biyota.
Gabanta ne ya faɗi , tana sake dubwa taga wa suke bi.

Ɗaya ɗan sandan ya ce "Amina ko?"

Idanuwa waje Amina take binsu da kallo, tana tunanin meye haɗinta da 'yan sanda suka biyota makaranta.

"You Are under Arrest!!!"

AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
            BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

PAGE 39


Ƙara waro manyan idanuwanta ta yi ta ce "Arrest for what ni Amina?" Tayi maganar bakinta na rawa.

"Arrest by Alhaji Ahmad Dutse order" ɗaya ɗan sandan ya faɗa yana murmushi.

Sai kuma tayi saroro tana binsu da kallo, dan ta kasa fahimtar kan lamarin gaba ɗaya.

"Kinga Kwantar da hankalinki, baki gane ni ba ne?" Yayi maganar yana nuna kansa

"Ni ban taɓa ganinka ba balle in gane ka" ta faɗa hawaye na taruwa a idonta.

"Ranar da kuka zo gidan Alhaji Ahmad ke da shi, muna aiki a gate ɗin gidan, ai ni na ganeki shi ne ya ce mu zo mu ɗaukoki, ya aikemu ne ya ce mu biyo mu ɗauke ki"

"Taɓ aikuwa ba zan biku ba, ku 'yan sanda abin yarda ne? Haka kawai ku sani a motar 'yan sanda kamar wata ɓarauniya, naga ai da kansa yake zuwa ya ɗaukeni wataran"

Ɗan sandan ya kalli motar da suka zo da ita, helux ce me baƙin glass, ya sake dubanta ya ce "Lambar motar ta aiki ce, ba tamu ce ta 'yan sanda ba, ta Alhaji Ahmad ce, kuma ba sace ki za muyi ba"

Amina dai cike da tsoro ta ce "Kunga, ku gaya masa mu haɗu a gida, amma ni ba zan hau motar 'yan sanda ba, kalli jikinku da kaki, kawai idan na shiga ku wuce dani prison"

Ɗaya ɗan sandan dai mamakin ƙarfin hali, da kuma taurin kan Amina yake, ɗayan kuma sai lallaɓata yake.

"Kinga bari in kira miki shi a waya"

"Aiko shi zaka kira nan wurin ba zan hau mota da 'yan sanda ba" ta faɗa tana duba hanyar da zata bi ta gudu.

Wayarsa ya ɗan danna, Sannan ya saka a kunnensa.

"Yauwa barka dai yallaɓai, gamu a ƙofar makarantar, mun zo ɗaukanta, amma ta ce ba zata hau mota ɗaya da mu ba, infact ma bata yadda kai ka turo mu ba"

Daddy ya ce "Na san a rina, bata wayar"

Ɗan sandan ya kalleta ya ce "To kinga, ya ce a baki wayar kuyi magana" A ɗan tsorace ta kalleshi ta ce "To idan na karɓa nayi maganar, zaku barni na tafi?"

"Eh, sai abin da ya ce dai"

Kamar wadda ake miƙawa kashi, haka ta karɓi wayar, tana Addu'ar Allah ya sa ba tana Magana wani abin zai sameta ba, ko matsafa ne.

"He..h....hello Daddy"

"Mmwummm" shi ne abin da ya faɗa daga cikin wayar.

Kamar mai tsoron magana ta ce "Daddy kana jina?"

"Mmm"

"Daddy dan Allah kayi magana, wasu ne wai zasu tafi da ni in jika"

"Baki iya sallama ba sai Hello?"
Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa a kan kujerar 3seater.

"Yi haƙuri a tsorace nake ne, 'yan sanda ne fa suka zo zasu tafi da ni"

"Eh laifi kika yi, na turo su su kamo mini ke"

Zaro ido tayi kamar tana gabansa ta ce "Laifi ni ɗin, me nayi da zaka haɗani da police?"

"Sai sun kawoki zaki ji laifin da ki kayi, idan kuma kika cigaba da yi musu gardama, za su saka miki handcuff su sako mini ke a motar su kawoki".

"Na shigesu ni Amina, 'yan fashi fa ake sawa wannan sarƙar, dan Allah kayi haƙuri" tayi maganar cikin shagwaɓa tana marairaicewa.

"Oya, ban da gardama ki biyosu ni na turo su"

Jiki a sanyaye ta ce "To" ta miƙawa ɗan sandan waya, ta bisu, suka buɗe mata mota, ta shiga suka ja suka tafi.

Gaba ɗaya zatonta gidan da suke zasu tafi, amma taga sun sauya hanya.

"Bayin Allah ya haka?" Ta faɗa tana waige waige.

"Meyafaru?" Cewar ɗan sandan da ya haɗata da Daddy a waya.

"Naga mun tafi wani wurin daban, ba Tudun yola zamu ba?"

"Ba nan zamu ba, gidan da kuka je tare ya ce a kaiki"

"Na shiga uku ni Amina" ta faɗa a hankali, tare da sallama cewar wani aikin zai kuma sakata yauma, gashi ta gaji matuƙa yau ɗin nan.

Tana ta zancen zuci, har suka isa gidan, parking suka yi a cikin gidan, wurin ajiye motoci, Amina yau har da motocin da bata gani ba wacan karon ta gani yau, har mamakin yadda Daddy yake yi da motoci take.

Suka buɗe mata ta fito, ta ɗaga kai ta kalli gidan sannan ta ce "To yana ina Daddyn?".

"Ki shiga, yana ciki"

"Ciki ina kenan?"

Ɗan sandan ya fara ƙufula da surutunta da tambayoyi, amma ya daure ya ce "Hanyar da kuka shiga wancan karon, ita zaki bi.

Cike da fargaba da salati, Amina ta nufi hanyar da suka bi tare suka shiga gidan a wancan karon.

Babu kowa a makeken falon, sai dai ko ina fes da shi. Ko yana ina oho? Ta tambayi kanta da bawa kanta amsa.

Wata siriryar hanya ta bi, zuwa falon da ya saka ta jera Abinci ranar da yayi baƙi.
Ta tura ƙofar ta shiga, ya ɗago idonsa ya kalleta a cikin uniform ɗinta, riga da skirt sun mata kyau sosai, sai uwar jakarta ta goyo. Shi kuma yana sanye da yadi mai taro taro maroon, kansa babu hula, yana shan ruwa a kofi.
Girmansa da kwarjininsa suka cika mata ido, ta ƙarasa cikin falon, ta durƙusa ta ce "Ina wuni?"

"Ban ganshi ba" ya bata amsa.

Ɗagowa tayi tana mamakin irin amsar da ya bata.

Ya ɗan ɗage mata gira ya ce "Yes, ban ga yini ba, ko in ce yana gidan biki ko?"

Amina ta sunkuyar da kai, saboda haka kawai take jin ta takura, wannan keɓewar tasu bata dace ba.

"Na saka an kamo mini ke, saboda laifin da kika yi mini".

"Laifi kuma?" Tayi maganar a ɗan raunane.

"Eh laifi mana, ai ke ba kya daina laifi, na fuskanci kina da taurin kai"

Amina tayi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa, dan ita dai bata san laifin da tayi ɗin ba.

"Me nace miki game da tsaya da wani, dan tsabar rashin ji kuma a titi, zaki tafi makaranta"

Sai yanzu ta tuna, da safe ya gansu tare da Bilal, ta ɗago ta ce "Daddy tsaya ka ji nayi maka bayani"

"A zaune nake ai, ba wani bayani da zaki yi mini, ba kya jin Magana ne kawai, kuma zan gayawa Malam Hassan ɗin abin da kike"

Ta marairaice ta ce "Ka tsaya ka ji dan Allah, wallahi shi ne ya biyoni wai sai ya rakani, ai kaga ba zan kore shi ba, wulaƙanci babu kyau"

Alhaji Ahmad ya gyara zamansa ya ce "Ni meye ya hana ki nemi in rakaki?"

"Ni a wa? Ni dai dan Allah kayi haƙuri, ka sa a mayar da ni gida"

"Aminatu ba kya ji sam, sai na ɗau mataki a kan abin da kika yi"

"Wallahi Daddy ina ji, kayi haƙuri, ni ban san ya zan masa ba, amma zan gaya masa ka ce kar ya sake shiga harkata"

Kan Alhaji Ahmad yayi magana, aka kira shi a waya, ya sa hannu ya ɗaga wayar, ya kai kunnensa.

Ba ta jin me ake cewa daga cikin wayar, ta dai ji yana cewa "Jiki Alhamdilillah, ya yi sauƙi jinin ma ya sauka, shi ma sugarn nawa ya sauka sosai"

Amina dai ta sake gyara zamanta, tana ɗan satar kallon Alhaji Ahmad.

"Eh, da ina tunanin zan ɗan je wata ƙasar in ɗan huta, amma a yanzu na samu wata Cartoon me Sani nishaɗi"
Dariya yake sosai a wayar, sannan yayi sallama da wanda suke wayar, ya ajiye, ya kalli Amina a ya ce "Oya, a ɗan sama mini abin da zan ci, kan ki tafi"

Ɓata fuska Amina ta yi, ta ce "Dan Allah Daddy..." Sai kuma tayi shiru.

"Ina jinki" ya faɗa yana danna wayarsa.

"Kaga Baba bai san ina nan ba, kuma ni Hajara tabi ta saka mini ido, gani take wani abu ne a tsakanina da kai"

"Wani abu kamar me?"

"Ranar fa da ka ce in kai maka shayi na daɗe, bina ta dinga yi tana tambayata wai ya aka yi na daɗe, da ranar da ka ce ba zan tayata aiki ba, duk ta bi ta saka mini ido, ita ma ka dinga sakata aiki kar ta zata da wani abu a tsakanin mu"

Dariya ta ga yana yi, ya ce "Akwai wani abu a tsakaninmu mana, tsoron me kike ji?"

"Ni meye a tsakaninmu?"

Ya ɗan yi murmushi ya ce "Kinga, yanzu dai tashi ki je kitchen, ki sama mini wani abun in ci"

Ɗan tsuke fuska tayi, tana jin Daddy ya takurata.

Daddy ya ɗan zuba mata ido ya ce "Ko in haƙura?"

"A'a zan yi" ta faɗa a sanyaye.

"Yauwa Cartoon ɗin Daddy, a taimakawa Daddy"

"Cartoon kuma?" Ta faɗa tana ɗan tura baki.

"Eh mana, tashi da sauri, dan ki kammala da wuri mu tafi gida"

Amina ta ajiye jakarta, ta nufi kitchen,  sai da ta ɗan tsaya tana tunanin mai zata girka, wanda zai iya ci saboda ciwonsa.

Ta cire ƙaramin hijjabinta ta rataye ɓalle rigar saman ta rataye, ya zama daga ita sai rigar uniform ta ciki, da skirt ɗinta, sai kuma hular hijjabin, kana ganin gashinta da ta ɗaure da ribbon.
A nutse ta fara gudanar da aikinta, tamkar tana kitchen ɗin gidanta.


Gaba ɗaya Yazid bai fahimci lectures ɗin yau ba, saboda yana cikin damuwa, yayi mamakin abin da Fadila ta gaya masa, bai taɓa tunanin jin wannan maganganun daga bakinta ba.
'banda abinka kai ma Yazid me ya aikeka, ina kai ina ina wannan yarinyar, suturar da take sawa kawai, ta isa ta nuna maka ruwa ba sa'an kwando bane' wata zuciyar ta tunasar da shi.
Haka nan jiki babu ƙwari, ya ja jiki yaje yayi sallar azahar, daga nan ya wuce gida.

Khalil kuwa tun da Allah ya sanya ya sauka a garin Abuja ƙarfe tara na safe, ya wuce gidan da yake zaune a can garin Abujan, ba im da ya kuma fita ya je, sala ce kawai take fito da shi daga gidan, ko Abinci ya kasa yin order ya ci, loka lokaci ya kan buɗe saƙonnin Hafsa da take turo masa a baya, da hotunanta ya zuba musu ido. Maganganunta ha dinga tunawa, da take jadadda masa na ya riƙeta da amana. Har ga Allah ya ci burin auren Hafsa ya zauna da iga saboda Allah, ya sama mata farinciki, amma Mummy ta ɓata komai, babu Wanda za aayi masa abin da Mummy ta yiwa su Hafsa ya iya haƙuri, sai dai idan ba shi da zuciya.
Duk yadda Khalil ya so ya yi tunanin mafita kasawa ya yi, ƙarshe ma kansa ne ya fara ciwo, amma ya kasa yadda zai iya cigaba da rayuwa ba tare da yana cigaba da magana da Hafsa ba, ya ɗauki wayoyinsa duka ya kashe su, ya ajiye.

Amina ta gama girki, sai aikin yanka salak da take yi, tana ta decoration ɗinsa a tray.
Ji tayi kamar motsi a bayanta, ta juyo gaba ɗaya dan ganin meke motsi a bayanta, sai taga Daddy ne ke shigowa.
Tsananin kunya ce ta kama Amina, saboda jikinta babu hijjabi, sai rigarta ta uniform 'yar ciki, kuma rigar ta kama jikinta sosai. Da sauri ta kai hannu tana kare ƙirjinta, ta juya da sauri, sai kuma ta tuna shi kansa skirt ɗin a matse yake, kuma tayi stock in ɗin rigar.
Murmushi Daddy ya yi, ya nufi fridge ɗin kitchen ɗin, still Amina ta kasa sakewa, sai ɓoye ɓoye take.

Muryar Daddy ta jiyo yana cewa "Me kike ɓoyewa ne? Ai ni ba ke nake kallo ba, na gaji da jirane na zo na ɗauki fruit ne, ina jin yunwa sosai".

Kunya ce ta sake kama Amina, har ta kasa cigaba da abin da take yi, dan bata taɓa zaton jin hakan daga bakin Daddy ba.

Ai bata gama tunanin ba ta ji shi a tsaye a bayanta, ji tayi tamkar ƙasa ta tsage ga shige dan jinta take a wani yanayi da ta kasa tantance wane irin yanayi ne haka. Gaba ɗaya ƙamshin turarensa ya cika mata hanci, idan tayi ƙwaƙwƙwaran motsi babu abin da zai hana jikinta ya haɗu da nashi.

Miƙa hanunsa yayi, ya ɗauko wuƙa ɗaya a cikin jerin set ɗin wuƙaƙen, dake gefen Amina.

"Calm down, ba taɓa ki zan yi ba, wuƙa zan ɗauka" ya faɗa a kunnenta a hankali.

Ƙiri-ƙiri Amina ta kasa cigaba da aikin, saboda yadda Daddy ya hanata motsi.

Ringing ɗin wayarsa ce ta cika kitchen ɗin, a tunanin Amina zai matsa ne, amma ga mamakinta sai taga bai matsa ba, ya ɗaga wayar ya sanya a kunnensa.

"Hello Madam" ya faɗa yana kallon gashin Amina.

"Kayi nisa ne" kasancewar Yana kusa da Amina, tana iya jin abin da ake cewa a wayar, jin muryar Hajiya Zainab a wayar ne ya sanya hantar cikin Amina kaɗawa.

Daddy ya ce "Ya aka yi?"

"Eh zan fita ne, idan ka dawo akwai Abinci a dining"

Ya ɗan shafi gemunsa ya ce "Ba za'a jira in dawo ba?"

"A'a sauri nake, ban san lokacin da zaka dawo ba"

Atishawa ce ta ƙwacewa Amina, kan Daddy ya katse wayar, tana ƙarewa kuma ta ce "Alhamdilillah" sai kuma ta ɗan zaro ido, tuna waya Alhaji Ahmad ya ke.

"Kai da waye ne naji kamar muryar mace" Daddy ya koma gefen Amina, ya ɗan kalli Amina sannan ya ce "Na je wurin Alhaji Sambo ne, ma'aikatansa ne"

Hajiya Zainab ta ce "But it seems that you are so close to the lady that sneeze"

"And who told you she is Lady? Sakatariyarsa ce ta shigo Office ɗin"

"Take care" ta faɗa cikin isa ta katse wayar.

Ya zubawa Amina ido, ta ɗan ɗago ta kalleshi, ta mayar da kanta ƙasa.

"Kin sani ƙarya, Shi ne kika ƙaƙalo atishawa ki ka yi, dan ta san muna tare ko?"

Amina ta ce "Ni ba ƙaƙalowa nayi ba, zuwa tayi"

"Yanzu idan nace miki ƙazama ki ji haushi, a kan Abinci na kika yi atishawa ko?"

"A'a, ai na kawar da kaina, kuma kai ne ka ke wurin shiyasa ban matsa ba"

"Yarinya idan asirinki ya tonu a wurinta, kina bibiyar mijinta sorrynki Amintako"

Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni mai zan yi da mijinta? Kuma ai bani na kawo kaina ba, kai kace a ɗauko ni"

"A'a yarinya faɗi gaskiya dai, kina bibiyar dattijon mijinta, ba ruwana ni"

"Taɓ, ni mai zan yi da tsoho? Ni yaro zan aura"

"Haba?" Daddy ya faɗa yana kai ayaba bakinsa.

Ta jinjina masa Kai.

"Lallai kin samu kanki, da Allah bai sa kin auri Jarmai ba, dole ki faɗi haka"

Waro idanunta Amina tayi ta ce "Daddy ina ka san Jarmai?"

"Ina ruwanki matar yara, ƙarasa mini aikina, yunwa nake ji sosai fa" Ya juya ya bar kitchen ɗin.

Mamaki ne ya cika Amina, ya aka yi Daddy ya san Jarmai.

Ta tsaya ta saka rigarta ta uniform, da hijjabinta, ta dinga kai kayan Abinci tana kaiwa gaban Daddy tana ajiyewa.

"Ƙarasa ladanki mana, ki zuba mini"

Amina a ɗarare dai ta zuba masa shinkafa kaɗan, ta zuba masa ganye cikin plate.

"Wow, kina kula da dattijon nan sosai, God bless you dear"

Ita dai Amina ta takure, tana jiran ya gama, ya bata umarnin tafiya, dan ta gaji da zaman nan.

"Matso muci tare"

Amina ta girgiza masa Kai "Na ƙoshi"

"Aikuwa ba zaki tafi gida ba, muna nan zuwa bayan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login