Showing 168001 words to 171000 words out of 296192 words
ƙofa yaga motar gidna ce, a gaggauce ya buɗe gate ɗin, Zakiru ya shigo da mota, ai kuwa da sauri ya bi bayan motar.
Zakiru na tsayawa, Amina ta buɗe motar ta fito, ta nufi wurin da Baba yake.
"Uwata sannu da zuwa"
Amina ta washe baki, tana jin wani irin farinciki, ganinta ga ta ga Baba, tayi kewarsa ba kaɗan ba.
"Babana, sannu da gida Baba na sameka lafiya?"
"Lafiya lau uwata, ya hanya kun shawo hanya ko?" Amina ba ta sani ba, ko ya san a jirgi a ta dawo ba, ta maze ta ce "Hanya lafiya lau Alhamdilillah"
"To ma sha Allah, an sanar mini cewa kin yi nasara a tafiyar da kika yi, ubangiji Allah ya sanya albarka, ya sa an fara kenan"
"Amin Baba na gode"
Baba ya ce "Maza ki shige ciki, ki samu ki huta, duk da yanzun nan za ayi magariba, ki samu ki ɗan huta".
"To Baba"
Zakiru ya ɗauko mata akwatinta, ya rakata har cikin gidan.
Hajara na ganin Amina ta washe baki "Amina, dama yau zaki dawo babu labari, sannu da zuwa"
"Yauwa, ya gida ya aiki?"
Hajara ta ɗan ɓata fuska ta ce "Gida gashi nan yadda kika bar shi, aiki kuwa kamar ha kasheni. Amina ke da aka ce zaki kwana goma kece ki ka yi kusan wata guda"
Amina ta ce "Ai ita dama tafiya kan kayi kai ke da ita, bayan kayi kuwa ita ke da kai"
Hajara ta ce "Haka ne, ya hanya?"
"Hanya Alhamdilillah, ina mutanen gidan?"
"Jiya da daddare jirginsu ya ɗaga, 'yan bala'i daga tafiyarsu har na ɗan murmuro mutanen nan basu da kirki, sai baƙar zuciya da cin zarafi a ransu".
Amina ta ce "Hajara kena, bari in shiga in ɗan huta"
Har Amina ta ja Akwatinta, Hajara ta lura ai Akwatin ba wadda tayi tafiya da ita bace ba, wannan tafi girma da kyau.
"Amina, wannan galleliyar Akwatin fa?"
"Bamu aka yi" Amina ta amsa mata ba tare da ta juyo ba, ta shige sashensu.
Tun da Amina ta tafi, Daddy yake jin gidan ya yi masa babu daɗi, gaba ɗaya gidan ya yi masa girma, tun baya fi awani da tafiya ba, gaba ɗaya ya ji kewarta ta dame shi.
Bai ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da dare yayi zai kwanta, da tana nan ta san zai yi aiki da daddare, zata ajiye masa abin motsa baki, ko kuma ta hana shi aikin cikin nutsuwa, tayi ta takura masa. Kasa yin aikin yayi, ya nemi wuri ya kwanta, sai dai nan ma bacci ya gagareshi, yayi ta kallon empty space ɗin gadon, ya janyo pillonta, wanda da suka yi faɗa ta daina kwana a jikinsa sai a kan pilon, ya rungume a jikinsa yana faɗin "I miss you Meenalina"
Ɓangaren Amina ma, tana tunanin Daddyn, amma bata bari tunanin nasa ya hanata sabgoginta ba, sai da ta zo kwanciya ita ma, ta fara tuna irin rayuwar da suka yi tare a ɗan wannan lokacin, yadda yake bata kulawa da taraiyarta. Rayuwa suka yi mai ɗauke da tarihin da abune mawuyaci zukata su iya mantawa da shi.
Sai a lokacin kewarsa ita ma ta addabi ruhinta, har ta kasa bacci tayi ta juye-juye, ba tayi zaton haka tayi mugun sabo da shi ba sai yau. A hankali ta furta sunansa "Daddy" ta cigaba da jiyinta, bacci ɓarawone ya saceta ba tare da ya sani ba, a baccin ma banda mafarkin gasu tare babu abin da take yi.
Saboda tsabar ƙawazucin makaranta, a washegari Amina ta shirya, zata makaranta.
Hajata ta ce "Ke Amina daga dawowarki har zaki makaranta?"
"To idan ban je makaranta ba, zaman me zan yi?"
"To aikuwa Hajiya ta bar tulin aiki, da zaki yi mata kan ta dawo"
Amina ta ce "Matsalarta ce" ta saɓa jakarta tayi waje, shi kansa Baba bai yi zaton zata je makaranta a yau ba, amma tayi masa baynin an wuceta a wasu abubuwa da yawa a makarantar.
"Yan ajinsu murna suka dinga yi suna shewa, da suka ga Amina ta dawo, dan ko bakomai Amina akwai surutu da abin dariya, kusan kowa ya santa, nan malamai da ɗalibai suka dinga yi mata murnar nasarar da ta samu.
Duk da ta sha tambaya a wurin wasu, na rashin dawowarta tare da sauran ɗalibai, amma ta dinga waskewa tambayoyin nasu.
Abu kamar wasa, Amina damuwa ta isheta, tana missing ɗin Daddy sosai da sosai, gashi wayarta tana hannunsa, balle ta kira shi a waya taji ya yake.
Amina har gidansu Azima taje, Maman Azima tayi ta mitar ta kira wayar Amina amma ba ta shiga, ta yi mata ƙaryar wayar ta lalace.
Ranar taje gidan mai lallen Ammin Azima ta zo, ita ma aka yi mata sannan ta tafi gida.
Kusan sati guda da dawowarta, Amina duk sai da ta yiwa gidan kwalema, ta gyara ko ina.
Saura sati ɗaya Amina ta zana Jamb, ta dage tana ta karatu, wuni take a makaranta sai yamma ta dawo, saboda ta samu isashshen lokaci tayi karatu yadda yakamata.
Ta dawo da yamma, tana shiga falon ta ɗan yi shiru tana nazari.
Hajara ta ce "Lafiya naga kin tsaya a nan?"
"Hajara Daddy ya dawo ko?"
"Me kika gani?"
"Ƙamshinsa naji"
"Ke Amina, wane irin ƙamshinsa kuma?"
Amina ta ce "Ƙamshin turarensa nake nufi"
"Ke yanzu saboda salo har kin wani san ƙamshin turarensa?"
Kai tsaye Amina ta nufi sashin Daddy.
"Ke Amina ina zaki?"
Amina bata tsaya ba, ta wuce sashinsa.
Yana gaban wata cupboard da litatafansa ke ciki, yana duba wani littafi ta tafi da gudu ta rungumeshi ta baya.
Ta ce "Oyoyo Daddy saukar yaushe?"
Ya juyo da ita suna fuskantar juna ya ce "Kamar gaske, murna kike kin ganni bayan kin taho kin barni"
"Wallahi Daddy nayi missing ɗinka sosai, ya aka yi ka dawo? Na san saboda ni ka dawo ko?"
Ya ce "Ni ba saboda ke na dawo ba, wani aiki na dawo yi"
"Ba wani nan, saboda ni ka dawo mana" tayi maganar a shagwaɓe.
Murmushi yayi ya ce "Ya school ɗin?"
"School Alhamdilillah, mun kusa jamb"
"Ma sha Allah, yayi kyau"
Kamar yadda yake mata ita ma ta ɗora hannu a cikinsa ta ce "Ka ci Abinci ko in je in dafa maka"
"A ƙoshe nake, ai ban daɗe da sauka ba"
Sake rungumeshi ta yi ta ce "Nayi missing ɗinka sosai"
Shima rungumeta yayi sosai a jikinsa, yayi zaton idan ya dawo, zata cigaba da fushin nan, amma kamar ba suyi faɗa ba tana ta murnar ganinsa.
Amina ta koma ɗakinta, a gurguje tayi wanka ta sauya kaya, ta koma wurin Daddy.
Hira suke yi sosai shi da ita, ya kama hanunta yana kallon lallenta ya ce "Saboda ni aka yi shi ko kuwa?"
"Tun da Allah ya kawoka ai shikenan ya zama naka" tayi maganar tana murmushi.
Ya kai hannun hancinsa yana sansanawa, "Waye ya yi miki?"
"Gidansu Azima naje, na tarar ana yi musu nima aka yi mini"
"Yawo kike ko?"
Ta tura baki ta ce "Ni ba yawo nake yi ba, gidansu Azima ne fa"
Hannunsa ɗaya ya kai kan leɓenta yana ja a hankali, hannunsa ɗaya kuma riƙe da hannunta, hannun nata ta miƙa ita ma tana ja masa gemu tana murmushi.
"Nayi missing ƙiriniyarki sosai da sosai"
Murmushi tayi tana lumeshe ido, ta buɗe tana kallonsa.
Hajara ce tayi sallama, kan su farga ta bankaɗo sai ganinta suka yi a tsakiyar falon, tayi turus tana bin su da ido.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Watpad@ ayshercool7724
Arewabooks@ ayshercool 7724
54
Haɗe rai Daddy yayi, ba tare da ya saki hannun Amina ba ya ke kallon Hajara.
Gaba ɗaya Hajara ta diririce, da ganin abin da ba tayi tsammani ba, ga kuma irin kallon da Daddy yake mata da ta kasa gan ma'anarsa.
"Lafiya?" Ya tambayeta a kausashe.
"Mmm.amm.... Eh dama Zakiru ne ya ce a gaya maka wai baƙinka, sun iso ya kira wayarka baka ɗaga ba"
Daddy ya ce "Na ji, amma daga yau kar ki sake zuwa sashen nan, idan ya kama dole sai kin zo, kiyi sallama idan na miki izini sai ki shigo"
"To..toto in Allah ya yarda" ta juya zata fita, tana sake waiwayowa tana kallonsu, amma babu wanda yayi aniyar daina abin da yake a cikinsu.
Kusan da gudu ta ƙarasa ɓangaren su, ta dafe ƙirji ta ce "Na shiga uku ni Hajara, iskanci a cikin gida da yammacin Allah, kuma da maigida? Lallai Amina masifa ce ke, ubangiji Allah ka tona musu Asiri, kaga tsohon nan tsohon banza dan girman Allah. Ni yanzu da wa zan tattauna wannan zancen ne? Uhmm babu ruwana 'yan gidan ba amana ce da su ba, Zakiru ba shiri muke ba, kuma yana da kusanci da Alhaji, idan na faɗa cewa za ayi ƙarya nake, dama ban isa in tunkari wannan matar mai fuskar shanu ba, in ce zan gaya mata, sai ta kasheni ai".
A ɗan tsorace Amina ta ce"Daddy, ni fa gaskiya ina jin tsoron kar Hajara ta tona mana asiri, dama tun a baya tana yawan saka mini ido, balle yanzu da ta zo ta ganmu a haka"
"Karki damu da ita please, a wurin wa zata tona mana Asirin, she can't do anything, i will intimidate her to keep quiet, ba abin da zata iya yi"
Amina tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, suwaye baƙin naka ne? Nan zasu shigo?"
Ya ce "A'a, suna wancan gidan nawa, wasu mutane ne, za'a ginawa Asibiti, zamuyi magana, nace musu mu haɗu a can"
"Ok to shikenan, amma dai zaka canzaa kaya ko?" Tayi maganar tana kallon kayan jikinsa.
Shima ya kalli kayan sannan ya ce "Me wannan ɗin suka yi?".
"Ni dai a canza wannan kayan, bana son ka fita da su"
"To shikenan, muje ki zaɓa mini wasu" suka miƙe tare, tana gaba yana binta a baya, suka isa bedroom ɗin sa, ta ɗauko masa wasu kayan ya sauya, ta rakoshi har falo.
Kan ya fita ta ce "Me kake so a girka maka da daddare, Coffee ko Fruit?"
"Duk abin da kika dafa ina so"
"To shikenan a dawo lafiya"
"Allah ya sa dear" yayi gaba.
Amina na hangen Hajara a Kitchen, amma ta basar ta wuce ɗakinta, bata sake fitowa ba, sai da aka yi sallar magariba, shi ma ta shiga Kitchen ne domin yiwa Daddy girki.
Hajara sai bin Amina take da kallo, tana son ta yi Magana, amma taga ba fuska Amina ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta sha kunu, aikin gabanta kawai take yi.
Kasancewar baya cin abinci mai nauyi da daddare, ya sanya ta girka masa jallop sphagetti, ta sha kayan ganye sosai da kifi, dan bata fiye barinsa ya ci nama sosai ba, ko tea zata ba shi, sai dai ta zuba masa zuma a maimakon suga, fafur ta hana shi shan lemukan gwangwani, sai wanda ta haɗa masa da kanta, cikin ikon Allah, ba a kuma cewa sugansa ya hau ba.
Hajara ba abin da take yi a Kitchen ɗin, amma sai kaiwa take tana komowa taga iya gudun ruwan Amina.
Bayan sallar isha'i, Alhaji Ahmad ya dawo gida. Amina ta sha wanka cikin riga da skirt na atamfa, ta ɗaura ɗan kwalinta, ta shiga Kitchen ta jera Abinci a kan tray, ta nufi sashinsa, cikin sanɗa Hajara ta bita har falo, taga Amina ta shige sashin Daddy.
Ta sake riƙe baki ta ce 'Abin da nake zargi dai ya tabbata, amma Amina sheɗaniya ce, yarinya ƙarama haka, amma kalli tana lalacewa da maigida, amma Hajiya Zainab duk wayon nan nata ya zama na banza, sun mayar da ita albasa.
To amma ya aka yi suka yi wannan shaƙuwar, naga dai ita bata gari shima haka? Kuma dai da Hajiya Zainab tana nan abin nasu bai kai haka ba, ko dai a wani wurin suke haɗuwa tun a baya, taɓ Allah ya nuna mana ranar tonon asiri mu sha kallo".
Tun da ta shigo yake binta da kallo, tayi kyau sosai, kayan sun karɓi jikinta yadda yakamata.
Ta ajiye kayan a ƙasa, ta nufi in da yae ta zauna a kusa da shi ta ce "Sannu da zuwa, ya baƙin naka?"
"Baƙi lafiya lau, har sun tafi ma"
"To kun daidaita ɗin da su?"
"Eh mun daidai ta, har sun bada 70% na kuɗin, idan aka kammala zasu bayar da sauran"
Ta ce "Alhamdilillah, Allah ya yi jagora, ya sanya a yi a sa'a"
"Ameen Meenalina, naga sai wani ƙara kyau kike, meye sirrin ne?"
Kamar za tayi kuka ta ce "Wane kyau Daddy, karatu ya sakani a gaba, ko isashshen bacci bana yi, ina son na samu maki sosai a jamb ɗina"
Ya gyara zamansa tare da matso da ita kusa da shi ya ce "Zaki yi nasara in sha Allah, ba na jinki, idan har ɓangaren himma ne, Allah ya bada sa'a i will make sure na cika alƙawarin da nayi, na cigaban karatunki"
Ta ɗan kalleshi ta ce "Ka fasa cireni daga makarantar da nake? Dan ni a ɗar ɗar nake, na san a kowane lokaci ana iya sauya mini makaranta"
Girgiza kai ya yi ya ce "Please, mu bar wannan maganar, bana son abin da zai rusa mini farinciki ki saka mu fara faɗa, mu fara cin Abinci tukuna"
Ya miƙe tsaye, ita ma ya miƙar da ita, suka nufi wurin Abincin.
Ta zuba musu a plate ɗaya, da kansa ya dinga a baki, yana ci yana mata santi, yana sake koɗata a kan iya girki.
Amina kuwa sai ji take yana fasa mata kai, tana jin daɗin yadda yake yaba mata. Sai da ya tabattar ta ƙoshi, ya kashe wutar falon, sai hasken TV suka cigaba da hira, yana mata hirara aikinsa, nasarori da ƙalubale, suna nan zaune har kusan goma na dare, a lokacin ta haɗa masa Coffee ta hau cinyarsa ta zauna, ta saka cokali tana ɗebo coffeen ta hura da bakinta, yayi sanyi sannan ta bashi a baki.
Alhaji Ahmad jinsa yake tamkar yanzu yake kan ganiyarsa ta matashi, gaba ɗaya kasancewarsa da Amina, ya sanya ya dinga jinsa na musamman, duk da tarin ƙuruciyarta da wautarta wasu lokutan, amma Amina tana da baiwa da hikimomi daban daban.
Sai da ya shanye tsaf, sannan ta ɗau tissue ta goge masa baki, ta ce "Alhamdilillah, mun ci mun ƙoshi, sai mu ɗan jira ya faɗa maka, sai kaje ka kwnata nima na je na ɗan yi karatu na kwanta.
"Kije ki kwanta a ina?" Ya tambayeta.
"Ɗakina mana"
"You are not going anywhere, muna nan a tare" yayi maganar yana kwantar da ita a jikinsa.
"Daddy mun fa dawo gida, idan aka ankare fa akwai hatsari a yin hakan, kayi haƙuri Please"
"Babu wani hatsari, kefa kika ce saboda ke na dawo, naji na yadda saboda ke na dawo, kuma sai ki tafi ki barni, impossible"
"Idan an yi magana ka ce mini rigimammiya, yanzu waye me rigimar tsakanin ni da kai?"
Yayi dariya ya ce "Ke kika koya mini, da rigima da rikicin gangan, ƙaƙalo faɗa ba dalili"
Ta ɗan tura baki ta ce "Duk ni ɗin?"
"Eh mana, oya tashi muje mu kwanta"
Amina ta ce "Naji, amma bari na fita da kwanukan nan, na canza kaya"
"Na ƙi wayon, bar kwanukan a nan" ya tashi tsaye da ita a jikinsa, ya kashe socket ɗin TV, suka wuce bedroom ɗin sa.
Alhaji Ahmad ko kunyar Amina baya ji, Kodayake ya riga ya sanya ta saba da shi, tun a lokacin suna tare, he make her feel free with him, so he enjoys the night with her, making her more comfortable with him.
Bayan sallar Asuba, bata kwanta ba, domin zata makaranta, bayan Daddy ya koma bacci, ta sauka daga kan gadon, ta nufi sashin su.
Tana zuwa babu ɓata lokaci, tayi wanka ta fito Kitchen, dan tabattar da ta kai masa Abinci kan ta tafi makaranta.
Hajara tana ta yanka doya zata fara soyawa.
"Hajara ina kwana" Amina ta gaisheta a lokacin da ta shiga Kitchen ɗin.
Cikin mamaki da kallon tuhuma, Hajara a ta ke bin Amina da kallo.
"Hajara lafiya naga kina kallona a haka, kamar na canza miki?"
"Kin canza mana Amina, a ina kika kwana jiya da daddare?"
Ras! Gaban Amina ya faɗi, amma da yake idonta ya riga ya buɗe ta dubi Hajara ta ce "A ɗakina mana"
"Amina kiji tsoron Allah, ki tausayawa kan ki, ki tausayawa dattijon nan mahaifinki, mutumin nan fa ba zai aureki ba, kawai yana amfani da ke ne da ƙuriciyarki dan cinma muradinsa, mahaifinki ya kawo ki kiyi karatu, amma kike biyewa mai gidan nan kike bashi kanki? Wallahi Amina idan baki nutsu ba, zan samu Malam Hassan in gaya masa abin da kike yi, idan kika ja masa abin kunya ba ki yiwa kanki adalci ba".
Jikin Amina ne yayi sanyi da maganganun Hajara, mussman maganar Baba, da kuma irin ɗauki ba daɗin da aka sha da su Kawu Bala, tabbas idan Baba ya san abin da take aikatawa, bata san ina zata saka kanta ba, kunyarsa ma kawai ta isheta, su Baffa Lawan kuwa za suyi musu dariya ne, ga uwa uba Inno. Amma saboda tsabar iya gwanancewa a iya rainin hankali Amina ta sake kallon Hajara ta ce "Ke ya aka yi kika san cewa bashi kaina nake yi?"
"Amina karki raina mini hankali, meye a tsakaninki da shi? Ko kin manta a yanayin da na ganku jiya, yau kuma ƙarewa a sashimsa kika kwana"
"Meye shaidarki a kan hakan?"
Saroro Hajara tayi tana cigaba da mamakin sauyawar Amina.
Amina ta nisa ta ce "Ki Ƙaddara ma na kwana a ɗakinsa, hakan na nufin bibiyarmu kike kina saka mana ido ko? To bari kiji na gaya miki, ki sakawa zuciyarki kamar baki ga komai ba, ko kya samu ki cigaba da harkokin ki cikin nutsuwa. Idan kina da wata hanyar ta samun kuɗi, zaki iya zuwa ki tona mana asiri, idan kuma baki da wata hanyar kina iya rufe bakinki, mu cigaba da harkokinmu, idan kuwa kika cigaba da bibiyata da saka mini ido, to tabbas zan saka ya sallameki daga gidan nan, idan kuma kika kuskura ya san cewa zaki tona mana asiri, wannan shi zai ɗau mataki a kanki da kansa bani ba, ki saka wannan a ranki".
Amina ba ta saurari me Hajara za ta ce ba, tayi abin da ya kawota ta bar kitchen ɗin.
Hajara ta daɗe a tsaye tana mamaki, sai da doyar da ta zuba a mai ta fara ƙauri, sannan ta farga ta cigaba da aikinta, jikinta har tsuma yake yi, mussman da ta tuna idan ta bar gidan nan, bata da wani aikin yi, to a ina ma zata dinga samun abinci mai kyau tana ci?.
Sai da ta gama shirinta tsaf cikin uniform, sannan ta kai masa duk abin da zai buƙata falonsa, ta shiga bedroom ɗinsa, domin ta ganshi kafin ta tafi.
Ta