Showing 21001 words to 24000 words out of 296192 words

Chapter 8 - GABA DA GABANTA

fito da Amina, ko in je har birni in ɗauko miki 'yan doka su kama ki. Kuma bari kiji in gaya miki ko kuna so ko ba kwa so, ko tana nan ko bata nan sai an ɗaura mata Aure dan ubanta Hassan".

Saminu ya ce "Haba Baba Bala, a fara mayar da hankali wurin gano in da Amina ta shiga mana, wannan faɗan ai duk ba shi ne abun yi ba".

Aikuwa ya dawo da idonsa kan Saminu "Au munafuki Algungumi, ashe kana nan, bana raba ɗaya biyu da haɗin bakinka yarinyar nan ta gudu, dan na lura da take takenka, ance har tasha take zuwa wurinka".

"Me za ta je tasha ta yi mini, iyakacina da iyalan Malam Hassan saƙo ne su bani in kai masa ko ya bani in kawo musu, kaga tafiyata ba zaka ɓata mini suna ba, Babar Amina Allah ya bayyana ta" dag haka Saminu ya fice, yana jinjina lamarin mugunta na 'yan uwan mahaifin Amina, su b ta ɓatan yarinyar suke ba, ta yadda za a ɗaura kar sunan su ya ɓaci suke yi.

Malam Rabi'u Jarmai ne ya zo har gidansu Amina yana bala'i a kan idan har ba a ga Amina ba, a dawo masa da kuɗinsa, idan an ganta a san abun yi.

Kawu Bala ya dinga ba shi haƙuri ya ce "Haba Jarmai, ka kwantar da hankalinka za a ganta duk in da ta shiga, idan ma ba a ganta ba, za a ɗaura muku aure a haka, duk in da ta shiga da Aurenka a kanta idan ya so ds ta dawo sai a daƙumota a kaita gidanka".

Jaramai ya ce "Amma ka raina mini hankali, tana nan baku kula ba ta gudu saboda kun mayar da ni mahaukaci, sai a aura mini gaibu, ni ba zan yadda da wannan sagegeduwar ba, na baku daga nan zuwa ranar Lahadi, idan an ganta to idan ba a ganta ba, ku san yadda za kuyi ku sallame ni".

"Ke Fadila, jarida zazzafa" cewar Amra da ta samu Fadila a Cafeteria.

Fadila ta ce "Jaridar me fa?".

"Bayan fitar ki daga class, Mutumin nan ya ce ayi Attendance, 30mrks duk wanda baya nan babu shi a 30mrks ɗin nan, ba kawai sai gayen nan yayi miki ba"

"Wane gayen?".

"Wannan Zaidu yake ko Yazeed, wanda aka ce shi ya ci class work, aikuwa ya gano shi ya ce da ke da shi ba ku da 30mrks ɗin nan".

Fadila ta ja tsaki ta ce "To uban waye ya sashi yayi mini? Allah ya ƙara"

"Kai mutuniyar baki da dama, Allah ya ƙara ma zaki ce?".

"Idan ba Allah ya ƙara ba me zance? Ni muje class ɗin ma in ƙare masa ta tas kar ya sake mini shishshigi a lamurana".

Aikuwa Amra ta dinga zigata, suka nufi aji, suka tarar da shi yana wurin zamansa, yana motsa bakinsa a hankali da alama karatu yake yi.

"Kai wurinka na zo" Fadila ta yi maganar tana tsare shi da manyan idanunta.

Ya ɗago kai ya kalleta, ba tare da ya ce komai ba.

"Uban waye ya saka ka yi mini Attendance? Na ce maka ina buƙata ne? Ai ni malamin nan ya gama mini komai da kaima ya soke naka Attendance ɗin, uban shishshigi kawai" lumshe idanunsa yayi a hankali, ba tare da ya ɗago ba, balle ta sa ran zai tanka mata.

"Da kai nake magana fa"

"Wai ni?" Yayi Maganar yana kallonta.

"Au duk maganar da nake, baka ma san da kai nake ba saboda ka raina mini hankali?".

"Yi haƙuri" ya faɗa a taƙaice.

"Aikin banza kawai" ɗan murmushin gefen baki yayi, tare da kau da kansa gefe, dan tuni idanun sauran 'yan ajin ya dawo kansu.

Class rep ya ce "Haba babbar yarinya, duk ajin nan babu wanda ya tuna da ke ya yi miki Attendance sai shi, amma sai taimako ya zama faɗa?".

"Kaga saurara mini babu ruwanka da ni, ai ba da kai nake ba, na gaya masa ina buƙatar taimakonsa ne? Ya ji da tsummar rayuwarsa kan yayi tunanin shiga rayuwata ya taimaka mini".

"Dalla class rep ka daina shiga sabgar yarinyar nan, gaba ɗaya ba ta da kunya Wallahi" cewar wani matashi shima mai ji da kansa, wanda suke kira da Babson.

"Lokacin da aka raba kunyar ni ba a haifeni ba, idan an raba kana nan zaka iya ɗebar mini a taka".

Babson ya ce "Ni kike gayawa haka?".

"Na gaya maka ɗin waye kai? Banza useless"

Ganin Babson ya miƙe ya hayayyaƙowa Fadila, kuma bakin Fadila ya ƙi mutuwa, sai cigaba da tunzura Babson take.

Yazeed ya miƙe ya riƙe Babson ya ce "Ɗan uwana dan Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta. Fadila ba mutuncinki bane ki dinga rigima da mutane mussaman maza, muryarki al'aura ce, sai ɗagata ki ke yi...

"Dalla yi mini shiru, ji yadda kake ambatar Sunana kamar kai ka raɗa mini, idan ba ka kiyayi shiga sabgata ba saina kwarfeka na bi ta kanka a gaban mutane"

Dariya jama'ar wurin suka fara, tana fama da kayan rama, kamar a busheta ta faɗi, amma ta kalli zabgegen namiji kamar Yazeed ta ce zata kwarfe shi.

Babson ya ce "Dan Allah ku ƙyaleni in tattaka wuyan yarinyar nan, in kawo ƙarshen fitsararta".

"Sai dai kayi ka kaɗai, ƙazami mai warin hammata kawai" ba dan Yazeed yana riƙe da Babson ba, da ba abin da zai hana ya yiwa Fadila mahangurɓa.

Baba sai kiran wayar Saminu yake, a kan batun tahowar su tare da Amina, Saminu ya tabattar masa da cewar Amina ta ɓata an nemeta an rasa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Baba Hassan ya dinga maimaitawa, tare da dana sanin rashin zuwansa ƙauye akan lokaci, take ya fara dana sanin zaɓar aikin nan a kan zuwa ƙauye wurin tilon 'yar sa.
Gaba ɗaya Baba ya rasa abin yi, jikinsa banda rawa babu abin da yake, banɗaki ya fara zagawa yayi gudawar fargaba, sannan ya ɗauro alwala ya zo ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa, sannan yayi tunanin mafita. Baba Hassan mutum ne mai matuƙar tawakalli, dan haka ba lallai ka karanto damuwar da yake ciki a halin yanzu.

"Baiwar Allah, ke tun safe na ga mota ta sauke ki, amma kin zo nan kin duƙunƙune a nan, lafiya kuwa?".

Amina da ke jin jiki ta kalli mutumin ta ce "Dan Allah a tashar nan kake?"

"Eh a nan nake".

"Dan Allah ka san wani Saminu, ɗan garin Shanono, direba ne shima"

Yayi shiru sannan yayi ajiyar zuciya ya ce "Gaskiya ban san shi ba, amma ke ina zaki je?"

"Wurin Babana na zo, kuma Saminun ne kawai ya san in da Baban yake".

"Idan ba zaki damu ba muje in baki masauki mana"

"Nace maka ina buƙatar masauki ne? Ka bari na gode kawai".

Amina na nan zaune ta ji ana cewa wani Sarkin tasha, miƙewa ta yi tabi bayan Sarkin tashar, zuwa wani Office da ya shiga, ba tare da ya san tana bin sa ba.

Yana ƙoƙarin zama ya ga Amina a tsaye a bakin ƙofar ofishin, ta zuba masa ido.

"Lafiya kuwa?".

"Dan Allah yayana tambaya nake"

"To Allah ya sa lafiya, ya sa kuma na sani"

"Dan Allah ka san Saminu direba, yana zuwa daga Shanono?".

"Ahh na san Saminu wani dogo baƙi, yana jan mota KIA?"

"Eh shi, dan Allah idan kana da lambar wayarsa ka kira mini shi"

"Eh ina da ita, amma ta sayarwa ce"

"To nawa ce?" Amina ta faɗa da mamaki.

"Eh, amma ba da kuɗi ba, ƙofar ofishin nan kawai zamu rufe, mintuna kaɗan sai in baki wayar ma kyauta".

Amina ta kalleshi tsaf tayi ajiyar zuciya, kawai ta juya ta bar wurin, tana tunanin wannan wane irin abu ne haka? Babu wanda zai iya yi maka alfarma a birni, sai ya nemi mutuncinka?.
"Da in koma gida a mini wannan Auren, gara in cigaba da yawo a nan" ta faɗa a fili. Ta koma in da ta bar kayanta ta yi alwala tayi sallar Azahar

Tana nan zaune, sai ga wanda ya fara yi mata magana da farko ya dawo wurinta, ya ce "Ke, na gane Saminun da kike nufi, ke 'yar uwassa ce?".

Amina ta jinjina masa kai, alamar eh.

"Ok bari in kira miki shi a waya" ya kira wayar Saminu ya bawa Amina.

"Saminu gani a tashar Kano, dan Allah ka gaya mini ina zan bi inje wurin Baba?".

"Amina, dama nan kika tafi, kin sa ana ta nemanki a gida?".

"Dan Allah ni dai ka taimaka mini, kuma kar ka gaya musu in da nake dan Allah".

"Shikenan, kwantar da hankalinki, kin ganni a hanya na kusa shigowa 1 21Kano, idan na shigo zan kai ki in da yake".

"Yawwa na gode sosai, Allah ya kawo ka lafiya"

Ta miƙawa mutumin wayarsa, tare da yi masa godiya, ta zauna tana jiran zuwan Saminu.
Mutumin nan ya zauna ya dinga yiwa Amina surutu, amma ko uhmm ba ta ce masa.

Sai bayan la'asar Sannan Saminu ya iso, wata irin ajiyar zuciya Amina ta dinga saukewa tana murmushi.

"Yi haƙuri Amina na barki kina jira, Amina wannan ramar da kika yi fa?"

Maimakon ta bashi amsa sai ta hau kuka, Saminu ya ce "Yi haƙuri, share hawayenki, nayi miki laifi nima dan ban gayawa Mahaifinki da wuri ba, kuma da na gaya masa dama cewa yayi in kai masa ke. Muje maza in kai ki"

Mutumin da ya kirawa Amina Saminu ya ce "To Amina ba sallama?" Shiru ta yi masa tana cigaba da share hawaye.

Saminu ya ɗaukar mata kayanta, ya sa a motarsa ta shiga, ya je ya sayo mata gurasa da nama da lemo ya bata, ta riƙe a hannunta amma ta kasa ci. Suna tafe yana bata labarin yadda gidansu ya hargitse, ita duk tausayin Inno ne yafi damunta.

Ko da suka shiga cikin unguwar tudun Yola, rukunin gidajen da Baba Hassan yake gadi, Amina ta saki baki, tana ganin gidaje tamkar a ɗauka a ci.

Da Saminu yayi parking ya ce mata sun zo, nan mamaki ya ƙara baibayeta, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne.

Saminu ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, amma ya ji shiru, ya tura ƙofar suka shiga, lokacin Baba Hassan na fitowa daga ɗakinsa na gadi, a guje Amina ta ruga da gudu ta nufi in da Baba yake ta riƙe hannunsa ta fashe da kuka.

Baba kasa Magana yayi, sai kallon Amina yake yana murmushi, shi dai a duniya ba abin da ya rage masa da yake ƙauna kamar Amina.

Saminu ya ƙaraso yayi masa bayanin komai, Baba Hassan ya dinga yi masa godiya, sannan ya ce dan Allah idan ya koma garinsu, ya haɗa shi da Inno a waya yayi mata bayani, amma bayan ita kar ya gayawa kowa abin da ya faru. Saminu ya tabbatar masa da zai yi hakan, daga nan suka yi sallama ya tafi.

Baba ya zauna Amina ta gaya masa duk abin da ya faru a ƙauye, ya jinjina kai shi kuma ya gaya mata yadda suka yi da Alhaji Ahmad.
Amina ta dinga murna jin batun cigaba da makaranta. Amma Baba ya ja mata kunne a kan yanayin mutanen gidan da halayarsu, A ƙuruciya ta Amina gani tayi ai dan wannan ai mai sauƙi ne.

Baba ya dinga jadadda mata "Sai kin yi haƙuri, rayuwar birni da ta karkara ba ɗaya bace, su mutane ne masu ƙyamar talaka ki iya kan ki, kiyi musu aikinsu su biya miki kuɗin Makaranta".

Amina sai murna take, ashe da rabon burinta zai cika a rayuwa.

Baba ya ce "Muje in gabatar da ke a wurin su".

Amina ta bi bayan Baba da kayanta a bagco, tana ta kalle-kalle, kamar zata faɗi.

Ya yin da Baba ke ta Addu'a Allah ya sa Amina ta shigo a sa'a, ta samu ta kammla makarantar Sakandire ɗin ta.

Ayshercool
08081012143GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P7

Tuni Amina ta manta da zazzaɓin da take fama da shi, dama na fargaba da damuwa ne, ita wancan Auren da ta baro ya fi komai yi mata daɗi, ga kuma wannan abin farinciki da ta zo ta riska, ba ta taɓa zaton abubuwa za su zo da sauƙi haka ba.
Har sun kai bakin ƙofar da zasu shiga cikin falon gidan, Baba ya tsaya ya kalli Amina ya ce "Uwata ina sake jadadda miki, sai kin yi haƙuri kin kauda kan ki, ki kwantar da hankalinki duk abin da suka ce ki yi, babu musu haka wanda suka ce ki bari, banda shishshigi ki zauna kiyi haƙuri mu samu ki kammala makarantar ki lafiya ƙalau".

Amina ta yi murmushi ta ce "Insha Allah Baba ba zan baka kunya ba, zan yi duk abin da kace" ya jinjina kai sanan ya tura ƙofar ya shiga da sallama.

Alhaji Ahmad ne kawai ya amsa, Hajiya Zainab kuwa na zaune, Fadila na kwance a kan cinyarta, tana kallon T.V.

Baba na gaba Amina na biye da shi, suka ƙarasa cikin falon, Amina ta zube har ƙasa ta gaida Alhaji Ahmad, ya amsa mata cikin mutuntawa.

Ta kalli Hajiya Zainab ita ma ta gaisheta, sai da ta yi mata kallon sama da ƙasa sannan ta ɗauke kanta ta amsa da ƙyar.

Alhaji Ahmad ya ce "wannan ce yarinyar taka?".

Baba ya ce "Eh ranka ya daɗe"

Alhaji Ahmad ya kalli Mummy ya ce "Madam, ga yarinyar da na yi miki magana ɗazu, 'yar wurin Malam Hassan, dan haka sai ku haɗata da masu aikinku ku nuna mata aikin da zata ringa yi. Sannan yanzu ana hutun makaranta ne, amma da zarar an koma Makaranta za'a kai ta makaranta insha Allah".

Baba ya ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi".

Amina ma ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi".

"Ba komai, ki nutsu ki mayar da hankali kiyi karatu da kyau kin ji ko?".

"Tom insha Allah na gode sosai".

Duk wannan abun Mummy da Fadila basu tofa ba, Baba Hassan ya gama godiyar sa ya tashi ya koma bakin gate in da yake aikinsa.

Amina na zaune tana jiran a bata masauki, amma babu wanda ya kuma kulata, sai ma cigaba da hirarsu da suka yi.

Kusan mintuna arba'in tana zaune, ga yunwa tana ji, gurasarta na cikin kayanta, tana so ta keɓe ta samu ta ci, amma ba wanda ya kuma saurararta.

Ba tsammani ta ji muryar Fadila tana kiran "Hajara"

Amina a ranta ta ce "Ji wata murya kamar aljana".

Hajara ta ƙaraso falon hannunta riƙe da duster, ta ce "Gani".

"Dan Allah kai yarinyar nan can wurinku, ta zo ta sanya mutane a gaba da kallo".

Sai yanzu Mama ta ce "Ki kaita ɗakin da Asabe ta bari, da safe zan mata orientation"

Hajara ta ce "to" ta kalli in da Amina take, yarinya ɗanya sharaf, tubarkallah baƙa ce mai kyau da ita, sai dai kayan jikinta zai tabattar maka da akwai rangwamen gata.

Hajara ta yi matamurmushi ta ce "Ta so muje ciki".

Amina ta ce "To bari in ɗakko takalmana a bakin ƙofa, kar wani ya samin".

Wani irin kallo Fadila ta yiwa Amina, jin abinda tace, Daddy kuwa murmushi kawai yayi.

Amina ta ɗakko takalmanta silifas ɗan madina mai zanen yatsu.

Hajara ta ɗaukar mata jakarta suka shiga ciki, Hajara ta buɗe wata ƙofa suka shiga wani falon.

Amina ta ce "Kai, sanyi sosai, naga lokacin bazara ne, amma sanyi sosai nan"

Hajara ta ce "Na'ura ce take sanyaya ɗakin ai"

Amina ta ce "Ok ita ce A.C air condition?" Hajara ta kalli Amina jin ta yi turanci ta ce "Eh ita ce".

Ta kai Amina ɗakin da Asabe ta bari, ɗan madaidaici ne da ƙatuwar katifa, akwai mudubi da banɗaki a cikin ɗakin.

Hajara ta ce "Ga ɗakin ki nan"

Amina ta zaro ido ta ce "Wannan duk ni kaɗai? Amma tare zamu dinga kwana a ɗakin ko?"

"A'a kowa da ɗakinsa, ga banɗaki nan bari in kawo miki sallaya ko zaki salla, bari in je kitchen in samo miki Abinci"

"To Na gode" bayan fitar Hajara, Amina ta dinga kallon ɗakin, ta leƙa banɗakin tas da shi.

'Allah sarki Inno, da na san haka zan samu komai a wadace da mun taho tare, wannan aljannar duniya haka?"

Ta shiga banɗakin, ta dinga taɓe- taɓe, Dan Amina akwai rawar kai wasu lokutan, hakan ne ya sanya take iya wasu abubuwan.

Ta yi alwala, ta yi sallar magariba, ta janyo kayanta tana ƙoƙarin ɗauko gurasarta ta ci, sai ga Hajara ta shigo da kwanuka, ta ajiye a gaban Amina, sannan ta zauna kusa da Amina ta ce "Ya sunan ki ne?".

"Sunana Amina".

"Masha Allah, ni kuma Hajara"

Nan Hajara ta dinga bawa Amina labarin yanayin mutan gidan, tare da sukar Hajiya Zainab da Fadila, ita kuwa Amina hankalinta sam baya kan Hajari, yana kan daddaɗar doya da miyar ƙwan da Hajara ta kawo mata, lokaci guda kuma tana tunanin Inno.

Daren ranar Amina kasa bacci ta yi, saboda tsoro da rashin sabo, haka ta kwana da fitila a kunne.

*************
Alhamdilillah kwanakin nan Hafsa tana yin ciniki sosai, dan har da dankali take haɗawa yanzu bayan awara. Dan har da miya take haɗawa idan mutum yana so ya siya da miya.
Wata mota ce tayi parking a ɗan gaban in da Hafsa take suyar awarar ta, mutumin ya sauke glass ya leƙo da kansa, ya kalli Hafsa yayi mata alama da taje.
Kallo ɗaya ta yi masa gabanta ya faɗi, ta ɗauke kanta ta cigaba da abin da take yi irin ba ta ganshi ɗin nan bama.
Wani almajiri ne yaje kanta ya tsaya ya ce "Wai ki zo inji mai motar can".

"Kace masa ba zan zo ba"

Almajiri ya koma ya sanarwa mutumin saƙon Hafsa.

Mutumin ya ce "Ka nuno mata ni kace ni nake kiranta".

Ko da yaron ya zo ya kuma sanar mata saƙon mutumin, ta kalli yaron a fusace ta ce "Zaka matsa daga kai na ko sai na kwaɗeka?"

Ba shiri yaron ya matasa ya bar wurin, da Hafsa ta iya tsare gida bata son wargi.

Mutumin ne ya fito daga motar ya ƙaraso kan Hafsa ya tsaya, ya dubeta a wulaƙance ya ce "Ke ni nake miki magana ki ka share ni?"

Ko nuna ta san ƙurar da ta kwaso shi ba ta yi ba, ta cigaba da fifita wutar gabanta.

"Aikin banza wulaƙatancciya, a haka zaki ƙare rayuwarki a wahala, daga ke har mahaifiyar ki haka zaku ƙare, kaɗan ma kuka gani, muddin ina raye sai kun fito titi kuna bara"

Wani murmushi ta yi mai ciwo, ta cigaba da sabgar gabanta.

Ya dinga jifanta da miyagun maganganu, a gaban mutane.

Mai shayin da ke gefen in da Hafsa ke sana'arta ne ya ce "Haba bawan Allah, ta yi shiru ba ta tanka maka ba, sai ci mata mutunci kake a gaban mutane ya haka ne?"

"Kaga saurara mini, ba da kai nake ba, ba ka san meye tsakanin mu ba"

"Koma meye tsakaninku wani abu ne da ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login