Showing 135001 words to 138000 words out of 296192 words
tayi kuka da taga zata tafi ta bar Inno.
A motar da Alhaji Ahmad ya ke Amina ta shiga, yara suka taru suna ɗaga musu hannu suka bar ƙauyen.
"Daddy, wai yana ganka da 'yan sanda kamar zaka kama mai laifi?"
"Saboda tsaro, ai a ƙa'ida ina yawo da su saboda tsaron lafiyata, yanzunma dan doguwar tafiya zan yi ne, amma Allah ne ke karewa ai"
Ta ɗan kalli Daddy ta ce "Mmn kayan nan sun maka kyau, kamar wani ango sai ƙamshin turare kake"
Daddy ya gyara hular kansa ya kalleta ya ce "Kamar wani ango ko? Zaki maimaita a gabanta"
Amina ta tsuke fuska ta ce "Ita wa?"
"Lovely Zeena"
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Lovely manya"
"Ke, kin fiye tsaurin ido fa, wai me matata tayi miki ne kike kishi da ita?, gaya mini gaskiya what is in your mind about her husband?" Yayi maganar muryarsa can ƙasa.
Amina ta kalleshi ta ce "Like?"
"Nothing" daga nan yaja bakinsa yayi shiru.
Ko da suka isa cikin garin Kano, maimakon su wuce gida, guest house ɗinsa suka wuce.
Amina ta kasa yin shiru ta ce "Daddy ya na ganmu a nan kuma, ba gida zamu wuce ba?"
"Eh ba gida zamu wuce ba" yayi maganar ransa a haɗe dan kar ta sake yi masa wata tambayar.
Gaba ɗaya ba haka ta so ba, da aka yi parking ma bai ce ta sauko ba, dan kanta ta sauko tabi bayansa.
Sai da suka je tsakiyar falon gidan, sannan ya kalleta ya ce "Ki shiga wancan ɗakin, kiyi sallolinki, za a kawo miki Abinci ki huta da la'asar Zakiru zai zo ya kai ki gida"
Jiki a sanyaye ta ce to, dan ita duk ba haka ta so ba.
Ta ware mayafinta ta yafa sosai, tayi sallar azahar, tayi adduointa, ta kira Inno ta sanar mata sun sauka, yanzu zasu ƙarasa gida, sun ɗan jima suna waya sannan Amina ta kashe wayar.
Ajiye mayafinta tayi a kan gadon dake ɗakin, ta tafi gaban mudubi tana duba fuskarta, ta kwance ɗan kwalin kanta tana sake gyara shi, kawai aka turo ƙofa, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya sai ta ɗan rikice, gashi tayi nesa da mayafinta da ke kan gado.
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe, kamar wanda aka yiwa dole ya ce "Zo ki karɓa" yayi maganar yana miƙo mata leda.
Kasa motsi tayi daga in da take tsaye, saboda kunya da ta gama mamayeta.
"Meenal, am talking fa"
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, ta fara tafiya a hankali, tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, ta ƙarasa in da yake tsaye ba tare da kalleshi ba.
"Menene? Ya naga kina sunkuyar da kai meyafaru" Yayi maganar tamkar bai san meya sanyata cikin ɗari-ɗari ba.
"Babu komai" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.
"Ga Abinci nan, da kin yi sallar la'asar kije haraba Zakiru na jiranki, ni zan tafi yanzu, zanje wani wuri"
Ta karɓi ledar hannunsa ta ce "Na gode"
Kamar yadda ya gaya mata, bayan sallar la'asar ta tarar da Zakiru a harabar gidan yazo ɗaukarta, ita har mamaki ma take yi, Daddy baya tsoron ko Zakirun ya gayawa Hajiya Zainab cewar suna yawo tare, har gidansa ya kai ta.
Zakiru bai nuna mata komai ba, sai tambayarta ya ta baro mutan gida, a haka har suka isa gida.
Baba na ganinsu ya taso da murnarsa zuwa wurin motar, Amina ta fito tana masa murmushi tare da gaishe shi.
Ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Ya hanya, ya babar taki?"
Amina ta ce "Lafiya lau Baba, kamar kar in dawo gida da daɗi"
Baba yayi murmushi ya ce "To ko zaki koma ne?"
"Ai Baba ba dan wannan tafiyar ta makarantar mu ba, da ba zan dawo yanzu ba"
"To shikenan, maza shiga ciki ki samu ki huta"
Amina ta juya ta ɗau Akwatinta da Zakiru ya fito mata da ita, Baba sai sannu yake masa, Amina ta ja Akwatinta zuwa cikin gidan.
A falo ta tarar da Hajiya Zainab da ƙawayenta su Turai, sun ci Abinci duk sun bar kwanukan.
Amina ta ce "Ina wuninku?"
A yamutse suka amsa mata, dan Hajiya Zainab bata amsa ba, sai ma kallonta da tayi ta ce "Zo ki kwashe kwanukan nan"
Mamakine ya kama Amina, Hajiya Zainab dai ba makauniya ba ce ba, taga Akwati a hannunta yanzu ta dawo, amma saboda tsabar son ta wulaƙantata wai ta zo ta kwashe kwanuka.
"Ko ba zaki zo bane, kika cake a wurin kina kallona?" Amina ta jingine Akwatin, ta zo tsakiyar falon, ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen, ta zo kuma kwashe sauran, Mummy ta kuma kallonta ta ce "Idan kin gama, na fito da labulaye na barsu a kan gado, zaca cire na part ɗina gaba ɗaya a sanya wannan, Carfet ɗin bedroom ɗina ma, zaa a canza wani, wannan fita da shi za ai, Zakiru ya kai shi Car wash.
Amina kawai ta jinjina kai ta tashi, ta kai kwanukan ta dawo ta ja Akwatinta.
Hajara ce ta fito daga ɗakinta, sanye da hijjabi alama salla tayi, ta washe baki tana faɗin "Amina ashe kin dawo ya hanya?"
"Lafiya lau Hajara, ya aikin?"
Hajara ta kwaɓe fuska ta ce "Aiki gashi nan, kin tafi kin barni, matar gidan nan da alama akwai abin da yake damunta, kullum cikin sauke mini kwandon bala'i take, da na motsa sai hantara, haka ita ma 'yar ta ta, kai wanan masifa ni Hajara wanan mutane kamar gadonta suka yi"
Amina ta ɗan taɓa baki ta ce "To Allah ya kyauta".
Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ita kuma wannan 'yar aikin taki daga ina na ganta da uwar akwati?"
"Wai nan ƙauye ta je"
Turai ta ce "Ni fa gani nayi tana wani ƙara kyau"
"Ke ni bar ni da zancen banza, Hajiya Salma, ya batun yarinyar nan da kika ce in haɗata da Khalil, da wuri zan duk abin da ya dace, kan ya lallaɓa ya koma wurin waccan shahshashar ban sani ba"
Hajiya Salma ta ce "Karki damu duk ranar da kika shirya, ki zo muje kiga yarinyar"
"Allah ya kaimu jibi, zan zo muje"
Amina ta shiga aikin canza labulaye, kamar yadda Hajiya Zainab ta umarce ta, Amina ba ta gama aikin nan ba sai bayan sallar isha'i, gaba ɗaya ta gaji.
Kasancewar tafiyarsu ta ƙarato, ya sanya Amina ta duƙufa cigaba da bitar karatun da tayi, ana sallar isha'i, ta shige ɗakinta, hatta Abinci a ɗakinta ta ci.
Wajen sha ɗayan dare ta ga kiran Daddy, ta ɗaga ta saka wayar a handsfree taƙi magana.
A hankali ya ce "Meenalin Daddy"
"Na'am"
"Au na zaki kulani ba, ki ka ɗaga wayata ki ka yi shiru?"
"Ai kaima watarn haka kake mini"
"To naji, zan samu tea?"
Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni gaskiya a gajiye nake, daga dawowata aka sani canza labulaye da Carfet, da nayi niyyar ko girki na yi maka, amma ko akwatina ban ajiye ba aka sani aiki"
"Waye ya saki aikin?"
"Ai kai ma ka sani"
"To shikenan naji, da safe idan Allah ya kaimu, ki mini girki kin ji Meenalina, am missing your delicious food, kuma kinga kin fi kowa sanin Abincin da ya dace da ni"
Ta yi wani murmushi kamar tana gabansa ta ce "I Will in sha Allah"
"Ranar Wednesday zaku tafi, so ki cigaba da shiri, idan da wani abu da kike buƙata ki sanar da ni"
"Eh, abu ɗaya nake so"
Cikin zaƙuwa ya ce "What it is?"
"Your presence their" tayi maganar a shagwaɓe.
"Rigimar ce ko, sai da safe" ya kashe wayar. Ajiye wayar tayi tana cigaba da mita, ta mayar da hankali ga karatunta.
Cikin rashin samun mafita, da rashin karsashi Khalil ya kira Mummy a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ya samu ga ɗaga.
"Yau ka ga dama ka neme ni kenan?" Yaji muryarta maimakon ko gaisawa ta bari suyi.
A saɓule ya ce "A'a ba haka bane, bani da lafiya ne"
"Eh, ko ba baka da lafiya ba? Kana fama da ciwon so ko, gubar Asirin da suka zuba suka baka a Abinci bata sake ka ba, to ka sani in kai sun shanye ka ni basu shanye ni ba".
"Mummy dan Allah duk a bar wannan maganar, ni kiranki nayi na gaisheki"
"Ka riƙe gaisuwarka bana so, jibi in Allah ya kaimu zanje naga iyayen yarinyar da na zaɓa maka, next za a kai kuɗin Aurenka da ita"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah Mummy kar ki mini haka"
"Ai tuni ma an riga an yi, idan ka ga dama kayi mini biyayya, idan ba ka ga dama ba kabi 'yar matsiyata mai awara a hanya!!
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
46
Baki na rawa Khalil ya ce "Dan girman Allah Mummy ki tsaya ki ji"
"Ubanka zan ji, rufan baki zaka gane kurenka"
Ta kashe wayar, Khalil ya dafe kansa yana jin wasu zafafan hawaye suna zubo masa, ba tausayin kansa yake ji ba, tausayin Hafsa ya fi cika masa zuciya, saboda bai san wane irin mutum Allah zai haɗa Hafsa da shi ba.
Kankiya ne zaune a office ɗinsa tare da wasu abokan aikinsa, suna ta hayaniya da surutu.
Suka ɗan tsagaita Kankiya ya ce "Wallahi baku ga rashin mutuncin da yarinyar nan tayi mini ba, duk yadda ɗalibai ke shakkata amma ta yarfa ni yarinyar nan, wallahi ban da ina sonta da saina wahalar da ita wallahi"
"To kai Kankiya, ya aka yi ka bari har ta rainaka haka ne?"
Kankiya ya ɗan taune leɓensa na ƙasa ya ce "Bari kawai TJ, ni ban taɓa ganin yarinyar da na nuna ina so ba, sai ita, amma sai wulaƙantani take yi, ta tsaya tana saurar wani sakaran yaro, dan ina sonta ne, ba yadda zan iya da ita, kuma da alama babanta mai faɗa aji ne, shi Wannan Yaron zan wulaƙanta in ga ta tsiya"
TJ ya ce "Ka bari sai exams, kai ta gara shi, kana dawo da shi"
"Ai ba sai ka faɗa ba, nace no Attendence no exams, kuma na hana shi zama a ajina, naga idan na taɓa shi tana jin haushi"
Suka cigaba da tattaunawa a kan Yadda Kankiya zai yi da Yazid.
Kamar yadda Daddy ya buƙata, da sassafe kan Amina ta tafi makaranta, tayi girki, ta je ta shirya a dining.
Ta koma ɗakinta ta tura masa saƙo "Na gama Abinci, ka fito in ganka kan in tafi"
Yana zaune ya idar da azkar, yana duba muhimman saƙonni a wayarsa, saƙonta ya shigo ta what's app.
Murmushi yayi ya kirata video call, tana tsaye ɗaure da towel, tana jira ko zata ga saƙon Daddy kan ta shiga wanka, sai ga video call ya kirata, bisa rashin sani tayi zaton Voice call ne, kawai ta ɗaga kiran.
Da fari bata lura ba, ta ajiye wayar tana neman comb, tana ta hello. Sai da ta ɗago ta ga kyakkyawar fuskarsa ta bayyana a kan screen ɗin wayarta. Wata 'yar ƙara ta saki ta cilla wayar kan gado, tare da dafe ƙirjinta, gaba ɗaya ba ta sa Video call ne ba ta ɗaga kiran, ya ganta babu mayafi yanzu kuma ya ganta daga ita sai towel.
Wani Irin haushi ne ya kama Amina, gaba ɗaya taji wata irin kunya da haushin kanta sun kamata, tare da zargin kanta mai yasa bata duba ba ta ɗaga, yanzu ma sai ya yi zaton ko tana sane ta ɗaga kiran.
Jiki a sanyaye haka tayi wanka, ta fito ta shafa mai ta saka uniform, ko karyawa ba tayi ba, ta ɗau jakarta, ƙarfe bakwai da kwata ta lallaɓa ta fice, tana fatan kar su haɗu. Sai dai tana fitowa ta ganshi a kan kujerar da ke facing ɗin ƙofar da zata fito, ya zubawa ƙofar ido.
Ji tayi tamkar ta koma ciki da gudu, amma ya riga ya ganta, ta fito kanta sunkuye, ko ɗago kai ta kasa yi balle ta kalleshi, ta dinga jin tamkar ƙasa ta tsage ta shige ciki.
Kanta a ƙasa haka ta ce masa ina kwana, amma ya ƙi amsawa ya cigaba da kallonta. Har ta kai ƙofa ya ce "Amina" ta tsaya cak bata waiwayo ba.
"Zo" yayi maganar fuskarsa babu wasa.
Ta juyo ta dawo kanta a ƙasa, ta zo gabansa ta durƙusa.
Yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Mun yi faɗa ne?" Ta girgiza masa kai.
"To ba faɗa meye yasa kike sunkuyar da kai ko kulani baki ba?"
"Ai na gaisheka baka amsa ba"
"Banji bane, kince in zo ki ganni, kuma na fito baki kulani ba"
Amina ta ɗan yi Jimm ta ce "Dama ba komai"
Fadila ce ta fito, hannuta riƙe da mukullan motarta, da kuma jakarta.
"Daddy good morning"
Cikin sakin fuska ya ce "Morning dirling, how are you?"
Ta kalli in da Amina ke durƙuhe a gaban Daddy, ba ta kawo komai a ranta ba ta ce "Daddy bari in karya in wuce school"
Ya ce "Ok, yaushe za kuyi hutu ne, a fara shirin tafiyarku ke da Mummynki?"
"In the next couples of week in sha Allah"
"Shikenan, Allah ya taumaka ya bada sa'a"
"Amin Daddy" ta nufi dining domin ta karya.
Ya kalli in da Amina ta sunkuyar da kai ya ce "You can go" Amina ta miƙe ba tare da ta ɗago ta kalleshi ba, ta juya ta bar falon.
Amina ta fara zuwa suka gaisa da Baba sannan ta tafi makaranta, da aka tashi sai da ta biya gidansu Azima, ta haɗa Maman Azima da Inno a wayar Ammin Azima suka gaisa, ta bawa Ammin Azima tsarabar.
Ammin Azima ta na matuƙar son Amina, jin ta take tamkar 'yar da ta haifa, sai la'asar sannan Amin ta tafi gida.
Sai da Baba ya yambayeta a ina ta tsaya, ta gaya masa taje gidansu Azima ne ta kaiwa Mamanta tsarabar da Inno ta bayar a kaimata.
Wasa-wasa aka shiga wasan ɓuya tsakanin Amina da Alhaji Ahmad, in dai ta san zata ganshi, ba ta fitowa kuma ta kashe wayarta gaba ɗaya, dan karma ya kirata.
Hajiya Zainab tare da Turai da Salma, suka shirya suka je gidan ƙanwar Hajiya Salma, wato Hajiya Badi'a.
Gida ne na alfarama, kai da ganin gidan ka san suna da abin hannunsu, Mummy ta washe baki, dan irin mutanen da take son su haɗa zuriya kenan, bata fatan talakawa su raɓi zuriyarta sam.
A katafaren falon Hajiya Badi'a tasa aka sauke su, ba laifi ta karɓesu cikin mutuntawa, dama sun san juna Hajiya Zainab da Hajiya Badi'a, su kan haɗu a sha'anin Hajiya Salma, amma ba ta taɓa sanin tana da 'ya mace ba.
A lokacin Hajiya Salma ta yiwa Mummy bayanin cewa, Kursum ba ta gari ne tana karatu a ƙasar waje, shi ya sanya bata santa ba. Sun taɓa hira sosai, sannan Hajiya Badi'a ta kira Kursum dan su gaisa.
Duk ramar Fadila Kursum ta fita, ga ta da wani irin haske gauuu babu kyan gani, kai da ka gani ka san ba farinta bane, tayi fixing nails ta musu fenti, haka ta fito soƙai-soƙai kamar raƙumar dawa.
Cikin iyayi ta ɗan lanƙwasa ta ce "Ina wuninku?"
Suka amsa mata da lafiya ƙalau.
Ta kalli Hajiya Salma ta ce "Mummy, yau nace zan zo gidanki"
"Ba wani nan, dan kin ganni ne shi ne zaki wani ce yau zaki zo gidana"
Nan suka gabatar mata da Hajiya Zainab, da abin da suke buƙata, har muƙaman Alhaji Ahmad sai da aka gayamata, suka nuna mata hoton Khalil.
Ba kunya a gabansu ta ce musu ta amince, da ma duk samarin nata ba wani tsayayye sai watsatstsu, ga Khalil ya haɗu ta ko'ina, a nan Hajiya Zainab ta tabattarwa da Hajiya Badi'a cewar kan su tafi umara, ko da zarar sun dawo, za a kawo kuɗin Aure.
Kursum ta ce "To amma shi yaushe zai zo?"
Hajiya Zainab ta ce "Kar ki damu, da zarar ya shigo Kano, zai zo ku gaisa"
Hajiya Salma ta ce "Kaga mara kunya tambaya ma kike yaushe zai zo ko?"
Kursum ta tashi tana murmushi ta bar falon gaba ɗaya.
Makarantar su Amina suna ta preparing ɗinsu a kan tafiyarsu, suna ta gaya musu ƙa'idojin da zasu kiyaye, da jadadda musu ranar tafiya kar wanda ya makara.
An tashi daga makaranta, Amina na tafe da ita da Azima, wata Perfect ta sanar da Amina ana nemanta a Office ɗin director.
Ba tayi tunanin komai ba, ta cewa Azima ta jirta ta je ta dawo, sai dai tana shiga da Daddy ta fara tozali, idonsa cikin nata, tayi saurin ɗauke idonta ga sunkuyar da kai ƙasa.
Ta ƙarasa ciki, ta gaida director ta gaida Daddy ya amsa mata yana kallonta.
Director ya ce "Amina, an zo musamman ana kafa mana dokoki a kanki, mu kula da ke sosai".
Amina dai ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta.
Daddy ya ce "Idan kun isa can Abuja, in kun sauka, za a tura direba ya ɗuke ki sai lokacin da zaku fara competition ɗin za a dinga kai ki, ba zaki zauna a hotel ba"
Ta jinjina masa kai kawai.
"Shikenan tashi mu tafi gida" ta miƙe ta bar Office ɗin, Daddy yayi sallama da director, ya bi bayan Amina.
Azima kuwa da ta gaji da jira, sai tayi tafiyarta, saboda kwanan nan kusan kullum cikin kiran su Amina ake, saboda tafiyar da za suyi.
Daddy ya ƙaraso ya buɗe motar, ta shiga shi ma ya zaga ya shiga.
Gaba ɗaya ta zama wata iri, kamar ba ita ce take masa surutu kala-kala ba, ta koma kamar wata baƙuwa ta kasa sakin jikinta, ko haɗa ido taƙi bari su yi.
"Kin gama guje-gujen?" Ta girgiza kai.
"Yi magana mana" tayi shiru ba tace komai ba.
Murmushi ya yi ya ce "kawai kiji kamar babu abin da ya faru, banga komai ba ki manta" wata Kunya ce ta sake kama Amina, ya dai ganta da towel ɗin kenan?.
'yanzu gaya mini me kike buƙata, mai zan saya miki?"
Zumɓura baki tayi ta ce "Ni bana son komai"
"Meyasa?"
"Bayan kace ba zaka ba"
"To ai Khalil zai je, zai wakilceni"
"Ni Khalil ɗin da baya kulani, ni kai nake son ka zo"
Ya ɗan shafi gemunsa, wanda hakan ya zamo kamar ɗabi'arsa ya ce "Ni wurin aiki zan koma, idan Khalil ɗin ma ya zo ai duk ɗaya ne"
Ɗauke kanta tayi tana tura baki, ita ba haka take so ba.
Ɗan leƙa fuskarta yayi ya ce "Meenali na"
"Ba wata Meenalinka"
Yayi murmushi ya ce "Tawa ce mana"
"Amma na roƙi abu ka ƙi yi mini" tayi maganar tana masa wani irin kallo, da yake kai wa zuciyar Alhaji Ahmad wasu irin saƙonni.
"Ke idan baki yi rigima ba ba kya jin daɗi ne?"
"Kaifa kace in dinga tambayarka abin da nake so"
"To ai duk cikin abin da kike tambaya wannan ne kawai ba zai yiwu ba"
Ta ce "Ai shikenan" tayi maganar tana sake ƙanƙame