Showing 171001 words to 174000 words out of 296192 words

Chapter 58 - GABA DA GABANTA

ɗan ƙare masa kallo, sannan ta ɗan ja hancinsa, caraf ya riƙe mata hannu.

Dariya tayi ta ce "Idonka biyu dama?"

Ya ɗaga mata gira yana murmushi, ba tare da ya buɗe idonsa ba.

Ta ce "Ina kwana Babban mutum"

Bai amsa ba, yayi kissing ɗin hannunta da ya riƙe.

"Ka sakar mini hannuna, kar in makara fa"

Sai yanzu ya buɗe idonsa ya yinƙura ya ce "Jirani na zo na kai ki"

Tayi saurin dafa shi ta ce "No, ka kwanta kayi baccinka, Zakiru zai kaini"

"Ok"

"Daddy wai yaushe zaka bani wayata ne tun da mun dawo"

"In kin dawo, ki tuna mini zan baki, and na aika an karɓo miki gifts ɗinki, da suke makarantarku, suma idan kin dawo duk zan nuna miki, sai a nunawa Malam Hassan, kin samu kuɗi masu yawa sosai Meenal, Allah ya ƙaro ɗumbin nasara"

Murmushi tayi masa ta ce "Amin Daddy, amma komai na samu kai ne tsanin nasarata, ba zan manta wannan ba, Allah ya ƙara buɗi, Allah ya sa kafi haka, ya sanya ka gama da duniya lafiya, na gode ƙwarai dagaske" Yadda tayi maganar harda ƙwalla a idonta, ya sa jikinsa yayi sanyi.

"You deserve more than this from me Meenalina, you mean a lot to me. Yanzu nawa zan baki na makaranta"

"7 thousand" ta faɗa tana dariya.

"7thousand ɗin sun isheki"

Ta jinjina masa kai.

Ya ce taje ta buɗe drower, ta kusa da kayansa ta ɗauka, ya nuna mata in da mukulli yake.

Da ta buɗe ta sha mamaki, kuɗi ne zunzurutunsu a ciki. Ta ɗebi dubu bakwai ta ajiya masa mukullin.

"Kin dai tabattar sun isheki ko?"

Ta ɗaga masa kai, alamar eh. Sannan ga ɗora da cewa "Na gode sosai, dama dubu biyu nake so, dubu biyar kyautar ta zan yi".

"Idan Baba zaki bawa, karki damu, zan bashi, ki riƙe wannan kiyi amfani da shi"

"To ni idan na riƙe me zan da su? Sadaka zan yi mana da su"

"Funny you, shikenan a dawo lafiya, Allah ya karɓa mana"

Ta ce "Amin".

Kitchen ta koma, in da ta bar Hajara tana iyo, a tekun mamaki. Kamar babu wani abu da ya faru Amina ta ce "Hajara ungo"

Hajara ta waiwayo ta kalleta, ta kalli kuɗin da ta miƙo mata ta ce "Na menene wannan?"

"To ki karɓa mana"

Hajara ta karɓa, ta duba dubu biyar ne cif "Me za ayi da su?"

"Naga wata yayi nisa ne, ba ayi albashi ba, ki riƙe ko wani abun ki saya ki aikawa yaranki"

Hajara ta dinga yi mata godiya, kamar ta durƙusa.

"Hajara dubu biyar ce fa, karki damu sai na dawo"
Hajara ta dinga kwarara mata addu'a, sai da Amin ta fice Hajara ta jujjuya kuɗin ta ce "Wato ta karɓo kuɗin aikinta na jiya, harda bani kasona a ciki, kenan yarinyar nan kwaɗayin kuɗi ne ya sanya ta yarda ta bada kanta? Kai amma wannan mutumin tsohon banza ne. Allah ya sa ta cigaba da bani karɓa zan yi.

Abu kamar wasa, shaƙuwa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin Abdul da Yusra, dan har mahaifiyarta ta san shi, ta gabatar mata da shi a matsayin abokin Khalil.
Abdul da ya samu 'yan kuɗinsa, sai yaje ya yi mata sayayya ya kai mata, Yusra duk da itama gwana ce wurin iya tsiwa, amma tana matuƙar girmama Abdul da jin nauyin sa, gashi abu kamar wasa, ya fara jin strong feelings a kanta, amma yana tsoron yadda zai gaya mata, kar ta ce bata son shi kamar yadda Fadila tayi, kuma yana gudun Khalil yaji haushi, baya son abotarsu ta samu matsala sam.

Yanzu ma waya suka gama, sun shafe kusan mintuna arab'in suna waya, sannan suka yi sallama. Bayan sun yi sallama ne ya kira Khalil a waya.
Khalil ya ɗaga yayi  masa sallama.

Abdul ya amsa ya ce "Kai wai ba zaka dawo garin nan ba, kaje ka shantake a Lagos?"

"Abdul, bana son dawowa ne, mussman idan na tuna ba zan ga Hafsa ba, na san ko naje ba zata saurareni ba"

"Khalil, meyasa baka da tawakalli ne? Dan ba zaka samu Hafsa ba ba zaka zo kaga iyayenka ba, ga kuma ni abokinka duk bamu da amfani ko?"

Khalil ya ɗan ja numfashi ya ce "Ba haka bane, zan shigo idan su Mummy suka dawo daga umara, yanzu dai wata alfarma nake nema a wurinka"

Abdul ya ce "Wace alfarmar kenan?"

"Dan Allah Abdul zaka auri Hafsa?!"

"What! In auri Hafsa kamar yaya?"

"Kayi mamaki ko? Babu wanda zai iya yi mini wannan taimakon sai kai Abdul, dan Allah kar kace mini a'a"

Cikin rikicewa Abdul ya ce "Amma ya za ayi ai haka? Ita Hafsan ba zaka tursasata ba, idan bata sona fa?"

"Ba zata ƙi ba, sai dai idan kai ne ba zaka yadda ba, dan Allah Abdul"

Abdul ya ce "Shikenan naji, ka bari idan ka dawo sai muyi maganar"

Khalil ya ɗanyi murmushin yaƙe ya ce "Yauwa Abdul, na gode sosai zan dawo in Allah ya yarda" suka yi sallama suka kashe wayar.

Jikin Abdul yayi sanyi sosai, yaso ya yiwa Khalil maganar Yusra, amma Khalil ya zo masa da wani sabon abu daban, gaba ɗaya sai lissafinsa ya ƙwace.


Amina ce a ajinsu, ta kifa kanta a kan benci, tana ta baccinta.
Azima ta daki bayanta ta ce "Ke ki tashi, tun ɗazu kike bacci a aji, wai ba kya bacci ne?"

Amina ta ɗago a fusace ta ce "Ban sani ba, kawai kin kama kin tasheni"

"An tasheki ɗin, kika kuma kwanciya sai na tasheki"

"Ke gaba ɗaya wasu lokutan sai a hankali kike"

Azima ta ce "Eh naji, kince mini mutanen gidanku basa nan, balle in ce sune suka hanaki bacci suka saka ki aiki"

Amina ta yi miƙa ta ce "Ba zaki gane ba"

"Ai dama ba zan gane ɗin ba, idan an tashi zamu je muyi printing ɗin Slip na Jamb ko?"

Amina ta ce "Ke ba zani ba, sai Allah ya kaimu da yamma"

"Kai, meyasa?"

"Saboda ɗaya baban nawa ya dawo, zanje gida nayi masa girki"

"Kai Amina kina ji da Daddyn nan sosai"

"Shima yana ji da ni ne, kuma kinga ba kowane Abinci yake ci ba, akwai Abincin da ake bashi saboda ciwonsa"

Azima ta ce "Gaskiya ne, Allah ya bashi lafiya"

"Amin" daga nan Azima ta ɗauko littafi, Amina ta koya mata wasu abubuwan, har aka tashi.



Da rana bayan dawowar Amina daga makaranta, ta shirya ta sha kwalliya, tana jiran dawowar Daddy sai kace matar gidan.
Da ya dawo, dai tarairayarsa take tana nan nan da shi, kasancewar rana ce sosai, Hajara tana can sashensu, Amina suka zauna a babban falo suka ci Abinci, Daddy ya ce idan aka yi sallar la'asar zai kaita tayi printing slip ɗin.
Amina babu kunya tayi ɗare ɗare a kan cinyar Daddy, yana biyewa shirirtarta.
Hajara kuwa da munafurci ke cigaba da cinta, ta leƙa ɗakin Amina taga bata nan, dan haka ta fito falo, dan ta lelleƙa ta ga ko yanzun ma suna tare.
Sai dai a wannan karon ma ta kuma katarin ganin Alhaji Ahmad da Amina tare, ya sanya ƙarshen chocolate a bakinsa, ita ma ta sanya ɗaya ƙarshen a bakinta, suna ci a hankali tana kallon idonsa tana murmushi.
Cak Hajara ta tsaya, ta dafe bakinta, kuma taƙi tafiya ta tsaya ganin ƙwal uwar daka.
Aikuwa suna cin Chocolate ɗin, suna zuwa tsakiya ya haɗe da bakin Amina yana murmushi.

A hankali Hajara ta koma, saboda a wannan karon bata san matakin da zai iya ɗauka a kanta ba idan ya ganta, ji tayi ina ma da hanyar da zata silale taje ta gayawa Baba ya zo ya gani da idonsa, amma sai ta tuna gargaɗi da kashedin da Amina tayi mata ɗazu da Safe.

Bayan sallar la'asar, Daddy yau ɗau Amina a mota, ya sanarwa da Baba cewar zai kaita su cire slip ɗin jarrabawa.
Bayan sun dawo, Daddy ya danƙawa Amina tarin kayan karatun da ta samu na kyaututtuka a wurin competition, sai kuma kuɗinta ya ce ba zai bata ba, sai dai ta faɗi abin da za ayi mata da su.

Ta ce "Ina son ka ɗauki dubu ɗari biyu, a kaiwa Inno dubu hamsin, Hajara da Zakiru a basu dubu ashirin, sauran idan zasu isa a saiwa Baba gida a bashi jari"

Daddy yayi murmushi ya ce "To ai duk kin rabar da kuɗin, kuɗin naki baza su a rabar haka ba sannan a saiwa Baba gidan ba, amma zan san abin da zan yi. Sannan ni kuma ki bar kuɗinki Amina ni yakamata na baki bake zaki bani ba"

"Saboda ka raina ko?" Tayi maganar tana haɗe rai.

"Ni na isa in raina? Ban raina ba"

"To ni dai a raba kamar yadda nace, sauran ko jarin a fara bawa Baba, so nake ya tsaya da ƙafarsa in raba shi da wannan aikin da yake"

"Yadda kike so haka za ayi ranki ya daɗe" murmushi tayi tana ɓoye fuska saboda maganar ta sa ta bata dariya.
Babban abin da ya ƙara sanya Amina farinciki, shi ne sauya mata wayar da yayi zuwa wata haɗaɗɗiyar Samsung.
Amina tayi wani uban tsalle ta rungume shi tana shafa bayansa tana murmushi.

Kusan sati biyu, Daddy ya ƙi komawa wurin aikinsa, ya mayar da Amina tamkar matarsa, idan ka zo sai kayi zaton ita ce matar gidan.
Wasu lokutan ida suka bushi iska, idan aka tashi daga makaranta, sai su tafi ɗaya gidan nasa, su wuni a tare sannan su koma gida. Hakan ya ƙara musu tsananin kusanci da soyayyar juna.

Yau suna ɗaya gidan nasa, Kasancewar Asabar ce, ta sanya ta yiwa Baba ƙarya ta tafi wurin Daddy a ɗaya gidan nasa.
Sai dai yau ɗin sai cika take tana batsewa, tun bayan jin cewar su Hajiya Zainab zasu dawo.

"Meenalina, dan Allah ki daina fushin nan"

"Ba dole nayi fushi ba, nasan idan ta dawo tsakanina da kai sai dai kallo, ba kulani zaka dinga yi ba"

Alhaji Ahmad ya ce "Haba Babyna, ya za ayi na ƙi kulaki, kin san matsayinki a zuciyar nan tawa kuwa?"

"Idan matarka tana nan, matsayina mai aikinta, ita da take matarka uwar 'ya'yanka"

"Dan Allah kar ki fara Amina, na san yadda zan tsara mana rayuwar da zamu yi ko bayan ta dawo, ni kaina ba zan iya haƙura da ke ba!!!



(Sai da ku fans ɗina, ina yinku kamar yadda kuke yina kuke ƙaunar rubutuna💞💕)



AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
               NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL

Arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724

55

Hararsa tayi, taji tamkar ta yi masa tsaki, saboda haushin da ya mamaye ilahirin zuciyarta.
Ya kwantar da kai ya cigaba da rarrashinta, yana bata baki a kan zai san yadda komai zai tafi daidai ba tare da wata matsala ba.
  Amina dai kawai jinsa take, ba tare da ta gamsu da maganganunsa ba, dan yadda yake nunawa a kan Hajiya Zainab, tamkar tsoronta yake ji ma.

Bayan sun koma gida, Amina taje ta samu Baba, ya na zaune yana jin radiyo.
Amina ta kalleshi cike da ƙauna ta ce "Baba sarkin radio"

Yayi murmushi ya ce "Bari uwata, ai dole mutum ya saurari radio, domin ka san halin da duniya take ciki, kuma kinga mu da ba muyi karatun boko ba, radion nan makaranta ce a garemu"
Amina ta jinjina kai ta ce "Haka ne, Baba magana nake son muyi da kai"

"To uwata bari in kashe radion" Ya kashe radion ya bata hankalinsa yana saurarenta.

"Baba kaga sakamakon nasarar nan da nayi, na samu kuɗi masu yawa, bayan kayan karatu da na samu" Baba ya jinjina kai ya cigaba da sauraron ta.

"To dama kuɗin suna wurin Daddy, sai muka yi magana kaga Hajara da Zakiru duk tare muke aiki da su, nace a basu wani abu a ciki. Shi ma Daddyn duk da yana da kuɗi ai kaga yana ɗawainiya da mu, ko babu yawa shi ma a bashi wani abu" sai kuma ta yi shiri dan taga reaction ɗin Baba.

Baba ya ce "Cigaba ina jinki"

"Yauwa, to da nace sauran kuɗin, a sai mana gida a ƙauye mu baro cikin gidan yawan nan, sannan a baka jari, amma Daddy ya ce mini ba zasu isa ba, sai na ce ko a je ƙauye a mayarwa da Jarmai kuɗinsa, ya dawo mana da gonarmu, sauran kuɗin a biya ayi mana noma ko?"

Baba yayi murmushi irin na su na manya ya ce "To uwata, na ji amma batun aje ƙauye a mayarwa da Jarmai kuɗi ya bada gona bai taso ba, abu wurin shekara guda. Ni ba zan hanaki yin alkhairi ba, kuma kuɗi naki ne, abin da kika yi na kyauta da sadaka daidai ne, sauran ki bayar a saya miki gona, in an tashi a sayar in haɗa da abin da nake da shi ayi miki kayan ɗaki"

"Kayan ɗaki kuma Baba?"

Ya ce "Eh mana"

"Baba Allah zai kawo wasu, yanzu wannan ma ai babu wanda ya san za a samu, dan Allah Baba ni gonarka nake son ta dawo"

"A'a sai dai a saya miki gona, ai ni yanzu babu abin da wata gona zata yi mini"

Amina ta marairaice ta ce "Baba, baka san yadda nake ji a zuciyata zaman aikin gadin nan da kake, ana wulaƙanta mini kai ba, idan aka sai gona, aka noma abin da aka samu so nake ko kiwo sai a zuba maka, ka koma gida ka huta, Baba bana son aikin gadin nan, ni fa ba dan mutanen da na lissafo suma sun cancanci su samu wani abu a kuɗin ba, da duka zan bayar a sai mana gida. Ko kayi jari ka sauya sana'a Baba"

"Allah sarki uwata, Allah yayi miki albarka, komai lokaci ne kinji, ki daina damuwa, watarana sai labari. Ni dai fatana ki kula da kanki, idan lokaci yayi watarana dole na bar gadi, lokacin kin kawo ƙarfi sosai, sai na koma gefe na huta"

"To ai yanzu ma ina da ƙarfi"

Yai murmushi ya ce "A'a da saura"

Ƙarshe dai suka daddale a kan, za a sai kayan Abinci a kai gida, a sai kiwo a zuba.

Amina ta samu Daddy da maganar yadda suka yi da Baba, ya ce mata shikenan babu damuwa.

Daddy ya samu Baba suka kuma tattaunawa da Baba, ba tare da Amina ta sani ba.

Mamaki ne ya cika Inno, ganin uban tarin kayan Abincin da aka kuma aiko musu da maƙudan kuɗi daga birni, a wai Amina ce ta aiko da su, a sanadin karatun boko ta same su.
Baƙi ciki da hassada suka cika zuciyar su Baffa Lawan, duk da idan an aiko da kayan har da su ake ɗibarwa, su karɓe su koma gefe suna ƙananun maganganu.

Yau ya kama su Fadila zasu dawo, bayan shafe kusan wata guda a ƙasa mai tsarki, kuma ya kama Asabar ce ranar dawowar ta su.
Tun safe Amina da Hajara suke ta faman aiki, yayin da Hajara a ranta take son ganin ya zata kaya, alƙar Amina da Alhaji Ahmad zata ɗore ko kuwa Asirinsu zai tonu a wurin matar gidan.
Daren jiya kuwa Amina kusan kwana suka yi, suna rigima da Daddy duk a kan dawowar Hajiya Zainab, saboda ta san da ta dawo zata ɗora daga in da ta tsaya wurin wulaƙanci, da cin mutunci kamar yadda ta saba ita da Fadila.

Da magariba, Daddy da kansa ya tafi airport ɗaukosu, Fadila na ganinsa ta rungume shi tana murna, kamar ta shekara bata ganshi ba.

Ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Sweetheart ya hanya?"

"Alhamdilillah, ashe kana gari na zata direba ne zai zo ya ɗaukemu"

Ya ce "Eh na shigo gari jiya" yayi maganar a taƙaice.

Ai tun a mota, ta fara buge-bugen waya, tana sanarwa su Hajiya Turai sun sauka yanzun nan, gasu a hanyar gida.
Bayan ta gama wayar Daddy ya ce "Haba Madam, daga dawowarki ko gida baki je ba kin fara kiran waya, ai kya bari muje gidan ku huta, in ganku sosai da sosai, tunda mun kwana biyu bama tare"

"Lallai ma kai ɗin nan, kai da wataran sai ka shafe wata uku baka ganmu ba, bamu ganka ba, shi ne yanzu kake wani ga zance ga magana. Kuma idan ban gaya musu ba suwa zan gayawa, ai gara sun san mun sauka lafiya hankalinsu ya kwanta" girgiza kai yayi, ya cigaba da tuƙi, ita kuma ta cigaba da mita.

Ko da suka isa gida, tare suka shiga falo, Zakiru tare da Baba ya biyo su da Akwatunansu.
Hajara na ganin Hajiya Zainab, ta washe baki ta risuna tana gaisheta, sai dai kamar yadda ta saba a wulaƙance haka ta amsa mata gaisuwar, irin wanzuwarta a wurin da rashinsa duk ɗaya a wurinta, take Hajara ta haɗiye murmushinta a ranta ta ce "Shegiyar mata, ai Allah ya ƙara ma abin da mijinki yake yi, mai baƙin hali kawai".

Ai kan sallar isha'i, tuni su Hajiya Turai, da wasu daga ƙwayenta suka cika gidan, suka dinga hayaniya, kamar ba a lokacin ta dawo ba.
Ita dai tunda Amina ta fito ta gaishesu,taga Hajiya Zainab tayi mata kallon banza, ba ta sake komawa ta kansu ba, ta koma ɗakinta tayi zamanta, Sai Hajara ce ta kai musu Abinci.
Gaba ɗaya hayaniyar ta ishi Fadila, ta wuce ɗakinta ta rufe ƙofa, domin ta samu nutsuwa, Alhaji Ahmad kansa sai bar musu gidan yayi, kamar ana taron biki.
Tun a daren ta fara kwance abin da ta zo da shi, ta hau yi musu rabo.

Alhaji Ahmad kuwa, bayan ya fita yayi sallar isha'i, Amina ya kira a waya, suka daɗe suna waya sai da ta tabattar masa da sun tafi, sannan ya dawo gidan.
Ko da ya dawo gidan, yana son sun ɗan yi hira, Hajiya Zainab ta ce ita a gajiye take bacci take ji.

Washegari sai bayan sallar Azahar sannan Fadila ta sanarwa da Yusra cewar sun dawo, Yusra tayi ta murna, ta ce anjima zata zo ta ganta.

Ganin da Hajara tayi kamar Amina na cikin damuwa, ya sanya ta dinga murna a ranta tana cewa Allah ya ƙara. Bayan Amina ta bata kuɗi masu yawa kan dawowar Hajiya Zainab.

Abdul yana ta son ya gaya wa Yusra yana sonta, amma ya kasa bai san ya zata ɗauki abun ba, kasancewar Khalil take so a farko, kuma shima a baya Ƙawarta Fadila yake so, bai san ya zata karɓi abin ba, ga kuma Khalil da yake ƙoƙarin bijiro masa da wani abu daban.

Washegari kamar yadda Yusra ta alƙawarta, taje gidansu Fadila domin ta ganta.
Da Amina ta fara karo a falo, Amina na ganinta tayi murmushi ta ce "Chef Yusy"

Yusra ta ɗan kalleta ta ce "Fadila tana nan ne?"

"Eh tana nan, ina son zan shiga classes ɗin ki na girki ya za ayi?"

Yusra tayi murmushi ta ce "Sai kin zo"

"To amma nawa zaki rage mini, kinga ni bani da kuɗi sosai"

Yusra ta ce "Duk kuɗin da kika samu? Naji

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login