Showing 198001 words to 201000 words out of 296192 words
ya tura ƙofar ɗakin, a zaune ya tarar da ita a kan gado, tayi uban tagumi.
A hankali ya ƙarasa in da take, ya zauna a kusa da ita, ya janyota jikinsa amma kamar ya haɗata da wuta, a fusace ta fizge ta ja gefe.
"Wallahi Ahmad ka kuma gangancin taɓani, sai na illataka kai saboda tsabar rashin mutunci da rashin kunya har kana da ƙwarin gwiwar tunkarar in da nake ka haɗa jikinka da nawa, kaje ka ƙarata a wurin waccan 'yar matsiyatar"
Daddy ya ce "Calm down please, Zainab duk abu kece matata ta fari, kuma ba zan so duk wani abu da zai tarwatsa kan iyalina ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki fuskance ni. Rana ɗaya gaba ɗaya kin fita hayyacinki ki rame lokaci guda"
"Kaga bana son wannan soki burutusn naka, ji nake kamar zuciyata ta fashe, na tsaneka Ahmad bana ƙaunarka ko son ganinka bana yi, na tsani mai sonka ma dalla tashi ka fita ka bar mini ɗaki".
"Na ji ba kya sona, ba komai ni ina sonki, amma kiyi haƙuri ba zan fasa baki haƙuri ba, naji na yi miki laifi na karɓa amma ina neman Afuwa, dan Allah kiyi haƙuri ki samu ko Abinci kici"
"Wallahi Ahmad kai ba ƙaramin munafuki bane ba, da can da in ci Abinci da na mutu ba ruwanka, sai yanzu zaka wani lallaɓani wai naci Abinci, ni zaka yiwa fuska biyu saboda rashin tsoron Allah?"
Munanan kalaman da Zainab ke amfani da su a kansa, ba ƙaramin ciwo suke masa ba, yana ta dannewa yana cigaba da rarrashinta amma sai cigaba take da gasa masa su yadda take so. Bai sake ce mata komai ba, ya tashi ya bar mata ɗakin.
Wayewar garin Allah, Amina ta saka a ka fitar da Abincin daren jiya da basu ji ba, aka bayar, tayi girkin safe ta ajiye musu, sannan ta je ta kaiwa Daddy nasa.
Ganinta da uniform ya sa Daddy ya ce "Baby har zaki iya zuwa makaranta?"
"Eh mana, yau zamu fara exams fa, ga Abinci nan ka karya, idan an tashi ina gidan su Azima, da magariba sai ka ɗaukeni"
"Ok shikenan, hakan ma yayi, a dawo lafiya, Allah ya bada sa'a, in sha Allah yau zan cika miki alƙawarin abin da kika yi ta nacin nan a kansa"
Waro idanuwanta tayi waje ta ce "Da gaske Daddy?"
Ya jinjina mata kai.
Jikinsa ta faɗa tana murna ta ce "Allah ya biyaka da Aljanna my love, kai mutum nagari Allah ya ƙara wadata da arziƙi Hubby"
Murmushi yayi ya rungumeta Sosai ya ce "Amin Meenalina, kema Allah ya saka miki da alkhairi da ankarar da ni abubuwa masu muhimmanci. Allah ya kawo mana wasu twins ɗin da kin gama exams Baby"
Rufe fuska ta shiga yi, saboda kunya da ta kamata.
"Ba zaki ce Amin ba"
Ɓoye fuskarta tayi a ƙirjinsa ta ce "Ni kunya nake ji"
Dariya ta bashi ya ce "Kunya kuma, madam kice Amin kawai".
"Na faɗa a zuciyata ai"
Yayi murmushi ya ce "Zo ki tafi kar ki makara, ba dan wancan uzurin ba, da ni zan kai ki, ki tafi da magungunan ki ki samu ki sha. Allah ya kiyaye hanya"
"Amin Dear na" ta tashi daga jikinsa ta fice tana ɗaga masa hannu.
A yadda Fadila take jinta, da halin da Mummy take ciki, bata ji zata iya zuwa makaranta ba.
Kafin Daddy ya fita, sai da ya kuma leƙawa wurin Hajiya Zainab, ta sake ƙare masa zagi da cin mutunci, ya fita ransa babu daɗi sam.
Ƙarfe tara, Fadila yunwa ta gallabeta taje dining ta tarar da Abinci, ta karya, ta kuma komawa wurin Mummy tana cigaba da bata haƙuri. Da ƙyar ta ɗan ci Abinci kaɗan, Fadila ta koma nata ɗakin.
Ƙarfe goma na safiya, su Hajiya Turai suka iso gidan, gaba ɗaya yadda suka zo gidan kamar masu shirin zuwa ya ƙi.
Har bedroom suka iske Hajiya Zainab, duk tayi wani iri.
Hajiya Turai ta ce "Zainab, gaskiya kinyi sake, ke kuwa kina me wannan ɗanyen aikin ya faru a gidanki? Idan ban manta ba kwanaki na ja miki kunne a kan wannan Yarinyar, amna ki ka yi biris da ni, kika nuna mini ba abinda zai iya, ga shi kwaikwaya miki rashin mutunci da rashin daraja, amma Allah wadaran halin Alhaji Ahmad, wannan ai ba budurwar zuciya bace sai dai ace bunsurar zuciya ce da shi.
Wato a baya ya buga ya buga, kin toshe bai samu kafa ba, shi ne ya ɓullo miki ta bayan gida, kai maza sai Allah"
Hajiya Salmanta ce "Uhumm ai ni gaba ɗaya kaina yama kulle, na rasa abin yi, namiji ƙanin ajali, buhun ƙaya kenan, mugu ɗan masara ana kayanka kana kayan gemu"
Hajiya Zainab ta rausayar da kai ta ce "Ban taɓa zaton Ahmad zai yi mini haka ba, na rasa mema zan sam na huce, tun jiya nake zaginsa amma zuciyata ta ƙi samun salama"
Turai ta ce "Ina ita munafukar Yarinyar take?"
"Ina na san musu, ni tun jiya ban kuma fita ko falo ba"
"Au barinta kika yi ta kwanar miki a gida? Baki ci ubanta kin korata ba"
"Hajiya Salma, al'amarin nan ya zo mini a bazata, Yarinyar nan fa a tsaye take, bata da mutunci ko kaɗan ban gane hakan ba, sai da wannan abun ya faru. Kin san mutumin nan har warning yake mini, wai in gayawa Fadila ni da ita ba ruwanmu da matarsa, Yarinyar nan idan ban bi a sannu ba ƙarshe ni ta koreni daga gidan, dan da biyu ta aure shi, dan ta rama abin da nake wa ubanta"
Turai ta ce "Ke Auzibillahi wane irin ta koreki daga gidan, ai sai dai ita ta fita ta bar shi, nijar zamu tafi wurin malamai dan ubanta sai bi daji tsirara tana hauka"
Hajiya Zainab ta ce "Hauka kuma, ni ba ruwana, kawai ta bar mini gida, yayi mata korar wulaƙanci"
Hajiya Salma ta ce "Ke dalla can banza kawai, idan ya saketa daga baya suka kuma jonewa fa, ta haukace ta bi bola kawai. Kuma ki buɗe masa wuta da rashin mutunci da tashin hankali, ki hana shi kwanciyar hankalin da zai zauna ya ji daɗin Auren, ki buɗe masa wuta ba sani ba sabo"
Haka suka cigaba da hure mata kunne, da ɗorata akan keken ɓera.
Amina kuwa tana gidan su Azima, suna falo sun ci Abinci suna hira, Daddy ya kirata yake tambayarta, ta sha maganinta kuwa?
Ta ce masa yanzu zata sha, bayan ta ajiye wayar, ta duba jakarta ta ɗauko ledar maganin.
Ammi ta ce "Baki da lafiya ne?"
"Eh amma na warke?"
"Mhmm meya sameki haka ne?"
Shiru Amina tayi ta fara kame-kame, ɗaya bayan ɗaya Ammi tabi magaungunan da kallo, ta kalli Amina ta ce "Idan kin sha maganin ki sameni a ɗakina" Amina ta amsa da to.
Kamar yadda Ammi ta umarceta, haka taje ta sameta a bedroom ɗinta.
Ammi ta kalli Amina sannan ta ce "Amina, maganin meye wannan, ki gaya mini gaskiya meye ya faru?"
Amina ta ce "Bakomai, ai na warke zazzaɓi nake yi"
Ammi ta ce "Amina, 'ya na ɗaukeki, garin yaya haka ta faru bayan baki tare ba"
Amina a ranta ta ce "Na shiga uku da wannan tereren bankaɗar, kowa sai ya san halin da nake ciki, ya aka yi Ammi ta gane wani abu?'
"magana fa nake Amina"
"Ammi ai ban gane a kan me kike magana ba"
"Laaa kun ga 'ya zata raina mini hankali? Meya haɗaki da maganin ƙarin jini na masu ciki"
A zuciyarta ta sake cewa "Wayyo Allah na shiga uku ni Amina'
A fili kuma cikin jin kunya ta ce "Ammi ai ya zube'
"Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru Amina? Ke ba kya gudun ayi miki mummunar fahimta tunda ba kowa ya san kun yi aure ba, kuma uwargidanki ta sani ki shiga uku? Tun da ba kirki ne da ita ba".
"Ai yanzu ta sani"
"Kamar yaya?"
Nan Amina ta gaya wa Ammi komai, Ammi tayi salati tana mamakin yadda abubuwa suka gudana.
Ammi ta numfasa ta yi ta yiwa Amina faɗa a kan gangancin da tayi, saboda ba kowa ya san sun yi aure ba.
Ita dai Amina tayi shiru ba ta kuma tofawa ba.
Kamar yadda su Hajiya Turai suka ɗora Hajiya Zainab a kan keke ɓera, ta cigaba da zuba wa Alhaji Ahmad rashin mutunci daban-daban.
Amina dai ta mayar da hankali, a kan jarrabawar ta, tana cigaba da kula Alhaji Ahmad.
Tun yana lallaɓa Hajiya Zainab yana bi ta kanta, har ya watsar da ita, ya cigaba da sabgoginsa.
Yayi mata maganar tariyar Amina, ya tambayeta a wani ɓangaren take son zama a gidan, amma tayi masa banza sai cin mutuncinsa da tayi ma.
Amina kuwa tana tuntuɓar Ammi, da Hajiya Maryam, a kan shirye-shiryen walimarta na tariya da kammala makarantarta.
Alhaji Ahmad ya tambayi Amina, furnitures ɗin da zai canza mata.
Amina ta ce "Ni ka bar mini na sashin naka sun isheni"
"A'a, sabuwar amarya a baki tsoffin furnitures"
"Ba wata sabuwar amarya'
"Sabuwace mana" yayi maganar yana murmushi.
"Daddy, ni dai ka bari ko babu yawa Baba ya sai mini ba sai ka saya ba"
"Saboda me ba zan saya miki ba? Duka furnitures ɗin gidan ma sauyawa zan yi, dan haka ba ruwanki, ba alhakin Baba bane ba, na bawa Hajiya Maryam kuɗin kayan lefenki"
"Wayyo daɗi, duka ni kaɗai, Kana ji da ni Daddy"
"Ba dole na ji da ke ba 'yar Babyna"
suka Cigaba da hirarsu, cikin soyayya da kulawa.
Hatta Fadila sai ta ga dama take gaida Daddy, saboda haushinsa take ji, ya jefa Mummy cikin halin damuwa.
Amina rayuwarta take yi a gidan hankali kwance, ko shiga sabgarsu bata yi, sai dai wasu lokutan Hajiya Zainab idan suka haɗu ta kan ci mata mutunci. Amina sai dai ta ce "Ni ba zan biye miki ayi ɓarin mutunci ba, ko bance miki komai na riga na gama da ke, zagi da cin mutuncin da zaki yi mini, ba zai canza komai ba. Dan haka ki cigaba kar ki fasa, kece a wahale bani ba. Kuma zan cigaba da baki mamaki a gidan nan ta in da baki zata ba, su kansu 'ya'yan da kike taƙama da su, idan har baki canza hali ba, suma sai na rabaki da su, saboda wautarki"
Hajiya Zainab ji take kamar ta kashe Amina ta huta da baƙin ciki.
Yazid ya lura da mood ɗin Fadila a 'yan kwanakin nan, bata walwala ku san kullum yanayinta babu daɗi, hakan ya sanya yake jin shima babu daɗi a ransa, sai dai ba ya jin zai iya zuwa ya tunkareta yaji damuwarta.
Hajiya Zainab na zaune a falo, tana shan shayi, gaba ɗaya bakinta babu daɗi, abu mai ruwa-ruwa kawai take iya sha, a cikin abin da bai fi sati biyu ba gaba ɗaya ta zabge, ta fita hayyacinta.
Alhaji Ahmad ya fito daga sashinsa, Amina na binsa a baya, kallo ɗaya tayi musu ta kawar da kanta taji kamar ta ɗora hannu a ka ta zabga ihu, Yarinyar da sai dai ta bata umarni a da, ta ci mutuncin ta son ranta, wai ita ce yau ta aure mata miji, da alama ma hankalinsa a kwance yake.
Suka ƙarasa falon, Daddy ya zauna, Amina ta zauna a kusa da shi.
Ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Hajiya ina kwana?"
"Ya kwana a ɗakin uwarki" ta bawa Amina amsa.
Amina murmushi tayi ta ce "Na gode"
"Zainab, ba zaki taɓa canzawa ba ko? Yarinyar nan na ƙoƙarin mutunta ki, amma sai zubar da mutuncinki kike yi, ai shikenan dama ina son sanar da ke, in Allah ya yarda jibi, za a fita da furnitures ɗin gidan nan gaba ɗaya. Zan zuba sababbi sannan akwai walima na tariya da kammala makarantar Amina. Zata zauna ne a part ɗina shine nata ɓangaren. Sannan sai kuma maganar raba kwana".
Tamkar saukar wuta haka ta dinga jin zubar maganganunsa a zuciyarta, ko kunya baya ji.
"Ban gane zata tare a ɓangaren ka ba, idan har kana son zaman lafiya, ka kaita duk in da kake so ka ajiyeta, amma banda gidana".
Daddy ya ce "Ba zan raba kan iyalina ba, a nan zata zauna, kuma kamar yadda na tambaye ki da farko, kina son part ɗinki ko in canza miki, baki zaɓa ba, dan haka Amina zata tare a sashena"
Miƙewa tayi a zafafe ta ce "Baka isa ba, kayi kaɗan wallahi sai ta bar gidan nan ka kaita koma ina ne, amma ba gidana ba"
"Ba shawararki nake nema ba, hukunci ne da na yanke, lokacin da nake binki ina lallaɓaki wata ƙila da kin kawo wannan maganar, da nayi amfani da ita, amma yanzu lokaci ya ƙure, a komai ke nake fara bawa dama kan ita, amma sai ki sake da taki damar.
Ina son idan wanda zai auri Fadila sun shirya, su zo su sameni muyi magana da su. Zan tsayar da lokaci, dai dai da lokacin auren Khalil.
Na kai masa kuɗin aure, na tsayar da watanni biyu kacal".
"Ka tsayarwa da Khalil aure ban sani ba, wai me ka mayar da ni ne? Wai wace yarinyar ce ma tukuna, naga dai ita baban Kursum ɗin baya gari?".
"Yarinyar da kika je ki ka ciwa mutunci a gaban jama'a, saboda ɗanki yana sonta. Nayi bincike bata da wani aibu. Bai kamata mu dinga tursasawa yaranmu saboda son zuciya ba. Ita dai Fadilan idan tana son wancan ɗin, su zo muyi magana. Na gama da maganar Khalil yarinyar da yake so zan aura masa, ba wadda kike so ba, tunda bake zaki zauna masa da ita!!!
AYSHERCOOL
08081012142GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
63
"Ahmad me kake nufi da ni ne? Ahmad so kake ka haukata ni? A kan me zaka aurawa Khalil 'yar matsiyata. Wato kai ka auri 'yar matsiyata shine zaka aurawa ɗana, wallahi baka isa ba Ahmad, ba zaka mayar da ni mahaukaciya ba" tayi maganar bayan ta ci kwalar Alhaji Ahmad.
Buɗe baki Amina tayi, tana binsu da kallo.
Ƙwayar idonta ya kalla, wadda babu abin da yake gani a ciki, sai zallar tashin hankali da masifa, duk sun ƙanƙance, sun yi ja sai huci take hawaye na zuba daga idonta.
A hankali ya sanya hannunsa, yana ƙoƙarin ɓanɓare hannunta daga kwalarsa, amma ta riƙe shi gam, sai huci take tana cigaba da masifa, idanunta kamar zasu yo waje, dan azabar baƙin ciki.
"Ki cikani, kar ki mini illa, wuyana yana zafi"
"Ba zan sake ka na Ahmad, sai ka gaya mini dalilin da ya sanya zaka kaiwa ɗana kuɗin Aure gidan matsiyata, saboda ka tozatarni, bayan wanda kayi mini"
"Ai na gaya miki dalilin, saboda kin san ni mutum ne mai son abin da 'ya'yana suke so"
Cikin ƙaraji ta ce "Ƙarya kake yi, wallahi ƙarya kake, ba ka son su, kuma 'ya'yana ne ba naka ba"
Yayi murmushi ya ce "Ai ba da su kika zo ba, kuma bake kaɗai kika same su ba, dan haka ba a canzawa tuwo suna" ya ƙarasa maganar bayan yayi amfani da ƙarfi wurin cire hannunta daga wuyan rigarsa.
Da ƙarfi ya danƙi hannunta, ta jata zuwa sashinsa, sai turjewa take tana gaya masa duk maganar da ta zo bakinta, ta ƙazafi da rashin daɗi .
Amina ɗan taɓe baki tayi, tana sake jinjina jaraba irin ta Hajiya Zainab.
A bedroom ɗinsa yayi birki, ya haɗa hannayenta, ya riƙe su da hannunsa ɗaya, ta yadda ba zata iya ƙwacewa ba.
"Zainab, nine munafuki azzalumi ko, ko kunya ba kya ji kike irin wannan maganar, kike nuna ban isa ba a gaban kishiyar ki, ke baki san raini zai janyo miki ba"
"Kar ka sake cewa kishiyata, nafi ƙarfin kishi da wannan 'yar matsiyatan, kuma sakina zaka yi, kuma wallahi baka isa ka aurawa ɗana 'yar matsiyata ba kamar yadda kayi"
"Kin makara ai, na riga na gama magana, amma yakamata ki sake tunani a kan abin da kike yi, hakan ba mafita bace, ƙaddara ta riga fata, kiyi haƙuri ki zauna mu cigaba da rayuwarmu, ina sonki Zainab, ban ƙara aure dan in wulaƙanta ki ba"
Jarumin namiji baya saki Zainab, da zan sake ki tun a abubuwan da kika yi mini a baya, da tuni na rabu da ke, sai dai na lura ke mace ce mai mantuwar gaske, ba kya duba gaba, ko tuna baya abinda ya zo miki shi kawai kike yi, dan Allah ki daina ki nutsu ki kwantar da hankalinki, ni ba zan wulaƙanta ki ba, kece uwar 'ya'yana kuma matata ta fari, matsayinki na nan daram bai sauya a zuciyata, amma meyasa kike so ki fitine ni, ki fitini kanki, a kan abin da nuna jarumtar ki zai ninka darajarki a idona"
"Jarumta kace, to Allah ya tsinewa jarumtar, ka cikani malam".
Hannunsa ɗayan, ya sanya yana shafo gefen wuyanta, yayi murmushi ya ce "Am missing You so badly, kece sila koma menene, kece kika bada ƙofa" gaba ɗaya Alhaji Ahmad ya gama raina mata hankali.
Ƙoƙari yake ya rungumeta ya rarrasheta, amma fafur taƙi ta dinga kuka tana ci masa mutunci, ba shiri ya rabu da ita ya fice.
Sashin su Amina ya tafi, ya shiga ɗakinta yayi mata sallama, saboda cigaba da shirye-shiryen tariyarta.
Sai dai ya tarar Amina ta cika tayi fam, tana danna wayarta.
"Meenal, zan tafi in sha Allah zuwa la'asar zan dawo"
"A dawo lafiya" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.
"Ya dai naga kin haɗe rai?"
"Bakomai" ta bashi amsa.
"Ban gane babu komai ba, amma ai ba haka muka tashi da ke ba yau, ko na yi miki wani abun ne?"
Aikuwa kamar ya taɓo mata in da yake mata ƙaiƙayi ta ce "Ba kaine ka biya kaje ka daɗe ba, bayan kuma magana muke ba"
Ɗan buɗe baki yayi cikin mamaki ya ce "Meenalina, haka za muyi da ke?"
Tura baki tayi tana hararsa.
Ya ɗan rausayar da murya ya ce "Shikenan, tunda ke ma ɓata mini rai zaki yi, bari da an kammala walimar na tattara na koma Lagos, tunda haka kuke so" ya yunƙura zai tashi, ta riƙe hannunsa cikin nata.
"Dan Allah kayi haƙuri, kawai ji nayi ina jin haushi, amma ba zan sake ba, kar ka tafi Lagos ka barmu"
"A'a komawa Lagos ya zama dole ai, tunda ba kwa son ganina, so kike hawan jinin ya ƙarasa ni"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi muna sonka, dan Allah ka daina faɗar haka na daina kaji"
"Is ok, sai na dawo"
"Safe journey ranka ya daɗe, Allah ya tsare mana kai, ya kiyayeka a duk in da kake"
"Amin Sweetheart, kiss me before I leave"
Kissing ɗinsa tayi, sannan ta tashi ta raka shi, har mota ya tafi.
Duk wannan abin da ake, Fadila bata sani ba, tana makaranta.
Kasancewar Amina yau bata da