Showing 249001 words to 252000 words out of 296192 words

Chapter 84 - GABA DA GABANTA

"Meenal, na daɗe banga nutsatsen yaro da ya burgeni ba kamar yaron nan, yana da dattaku"

Amina tayi farat ta ce "Kaga abin da nake gaya maka ko?" Ya ce "Tabbas na gani kam" a ranar ne kuma Hajiya Zainab ta saka Daddy a gaba da zancen sai an mayar da kuɗin Auren Fadila.
Amina ta samu wannan damar ta cewa Daddy idan har ya mayar da kuɗin nan ba tare da ya hukunta Fadila ba, haka zasu cigaba da zubar masa da mutunci.
Ta bashi shawarar ya sanya Fadila ta fito da wani mijin idan ya mayar da wannan kuɗin, ya karɓi shawararta ya bi, amma Fadila ba ta kawo miji ba, dan haka Amina ta ce yayi bincike a kan Yazid idan har ya yarda da nagartar sa ya aura mata shi.
Daddy ya ce "Amma yin hakan kamar nayi mata auren dole ne, tun da ba ita ta kawo shi ta ce ta na so ba"

"Ba auren dole bane ba, da bata son shi ba zata saka ka taimake shi ba, yakamata ka hukunta su a kan abin da suke aikatawa".

Aikuwa Daddy ya sanya aka yi masa bincike, Yazid ba shi da wata matsala kowa sai alkhairinsa yake faɗa. Sai dai Daddy ya shiga damuwa yana ganin Fadila zata sha wahala, saboda Yazid ba shi da shi, idan har zai aurawa Fadila Yazid sai ya bashi aikin yi. Nan ma Amina cikin kissa ta nuna masa ai hakan ne zai sa tayi hankali, ta gane Cewar a kowane lokaci Allah zai iya karɓe dukiyar kuma shikenan ba zata rayu ba.
Daddy yana ta jujjuya maganar, Hajiya Zainab ya shuka masa rashin mutunci, baban abin da ya ƙara ƙular da shi, yadda Hajiya Zainab da Fadila suka je gidan Yazid suka ci wa matarsa mutunci, saboda kawai 'yar talakawa ce, hakan ya sanya ji shawarar Amina ita ce hanyar da zai bi ya hora Fadila.
Daddy da kansa ya tafi unguwar su Yazid, kamar yadda ya sa aka yi masa bincike a kan Yazid, ba tare da shi Yazid ɗin ma ya sani ba.
Ya saka direbansa yayi masa sallama da Yazid, ko da Yazid yaga Daddy, ruɗewa yayi yana fargabar ko laifi ya yi.
Sai dai ganin fuskar Daddyn ɗauke da fara'a, ya sanya ya saki ransa.
Daddy yayi masa iso zuwa cikin motarsa, Yazid ya risuna yana haida Daddy.
Daddy ya amsa masa sannan ya ɗora da cewa "Yazid na san zaka yi mamakin ganina a gidanku, ba tare da ka san dalili ba, sai dai ba abin mamaki bane ba, kamar yadda na saka aka yi mini bincike a kanka, da irin rayuwar da kake gudanar wa a makaranta, har alaƙarka da 'ya ta na sani, tambaya zan yi maka guda ɗaya, kuma nake son ka bani amsarta tsakani da Allah, kana son Fadila?"

Ɗan Jimmm Yazid yayi cikin jin nauyi ya jinjinawa Daddy kai.

Daddy ya ce "Yanzu idan na aura maka ita kana da wurin ajiyeta?" A dirirce cikin rashin fahimta Yazid ya ce "Daddy bani da kuɗin aure a yanzu, karatu nake yi bani da tsayayyiar sana'a sai buge-buge kuma Fadila ba ta sona"

Daddy ya ce "Amsa kawai nake so ka bani"


Yazid ya ce "A'a bani da wurin ajiyeta a yanzu, sai dai a garin su babanmu ina da gona".

Daddy ya ce "Kar ka damu, ranar juma'a idan Allah ya kaimu, kaje da magabatanka, babban masallacin juma'a na Dutse zan aura maka ita, sadaki kawai zaka kawo duk abin da kake da shi idan ta tare daga baya ka yi mata, ga dubu ɗari biyar ka rage kayi wani abun, amma daga yau har zuwa ranar ɗaurin aure, kar ka kuskura ta san da wannan maganar"
Yazid zai yi Magana, Daddy ya girgiza masa kai, ya ajiye masa kuɗin ya ce yaje ya sallameshi.
Tamkar shashasha haka Yazid ya koma gida, yan ganin abin wani irin banbarakwai, yarinya 'yar gata kamar Fadila za a yiwa irin wannan auren?.

Ko da Yazid ya sanarwa da Hajiyarsa abin da ke faruwa, Hajiya ta ce bata yarda ba, wataƙila ma Yarinyar wani abun aka ƙunso za a jona masa.
Amma ya dinga yiwa Hajiya nasiha tare da nuna a baya ita ta damu da sai yayi aure, ƙila Allah ne ya karɓi addu'ar ta. Ya samu ta haƙura a ranar tayi waya garinsu ta ce a sayar da gonar da Yazid ya gada, a kawo kuɗin zai yi aure. Aikuwa suka haɗo masa da ɗan abin gudunmawa, kowa Yazid ya gayawa zai yi aure sai yayi ta mamaki, me yake da shi da zai yi auren?
Da haka aka sai wannan gidan, ya sai wannan kayan ɗakin na hannu a ka gyara su aka zuba. Ranar da za a ɗaura aure ma ya haɗu da ita a makaranta, har hira suka yi, tana bashi labarin yadda ta ji lokacin da bata da lafiya. Yazid yana ta mamakin dalilin babanta na yanke wannan hukuncin haka a kanta.

Alhaji Ahmad bai tashi zuwa Dutse ba, sai daf da lokacin sallar juma'a, kuma banda yayyensa sai ƙannen mahaifiinsa su ne kawai suka sani, aka ɗaura aure ya dawo gida. Bayan ya dawo saboda kar Hajiya Zainab ta kawo masa cikas, ya sanya ya ɗau Fadila ya kaita gidan Yazid da kansa.LITTAFIN NAN NA KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA 08081012143

76



Cikin ƙosawa ta sake cewa "Ka yi
magana mana, ka yi shiru kana kallona"

Ya saka hannu ya karɓi hoton daga hannunta, yana ɗan jujjuya shi sanyaye ya lumshe idanunsa sannan ya buɗe su ya ce "Wato Fadila, duk wanda ya rasa uwa yayi kuka. Shiyasa duk da ina murna na aureki, amma bana jin daɗin nesanta ki da Mummy da Daddy yayi ba. Ita uwa wata kyauta ce daga Ubangiji da bata da madadi.
Inna wuro kenan, ni kuma ina kiranta Innata. Kamar yadda na samu labari Bafulatana ce ta riga a can wani ƙauye a Jalingon jihar Taraba. Galibinsu fulani ne, sai dai galibinsu ba musulmi bane ba, rigar su Innarmu musulmi ne sai dai basu damu da ilimin addini ba, ba abin da suka sani sai kiwo da kuma tallan Nono. Inna tana da yayye mata biyu sai kuma ita ta uku, suke nan a wurin mahaifinsu. A wurin tallan Nono ne da suke shiga garin Jalingo yi Inna ta ci  karo da ilimin addini ta gane Cewar a duhu suke zaune na jahilci, addinin ma basa gudanar da shi yadda ya dace a rigarsu dan haka ta ɗau ragamar neman ilimi.

Idan taje tallan Nono, sai ta zauna cikin makarantu ta ɗau karatu. A lokacin babu wanda ya damu da sai an saka a makaranta kan kaje, ta samu wata makarantar islamiyya tana zuwa.
Ta ƙuduri aniyar yin karatun addini mai zurfi. Domin ya zama babbar malamar ita ma ko dan ta dinga wayar da kan 'yan ƙauyen su. Sai dai wannan buri nata bai cika ba, mahaifina ya haɗu da ita, lokacin da suka je rigarsu shi da wani abokinsa sayen shanu.

Kasancewar dama ba karatu suke yi ba, kuma 'yan uwanta duk da wuri ake yi musu aure, ya sanya ita ma mahaifinsu ya amince da mahaifina a kan ya kawo kuɗin aure a sanya ƙanƙanin lokaci.
Mahaifina yana da mata biyu, mahaifiyata ce ta uku, uwar gidansa Baba Uwani, sai kuma ta biyun Baba Hanne. Babban abin da ya damu mahaifiyata shi ne burinta na karatun addini babu lallai ya cika.
Bayan ta auri Mahaifina, ya tafi da ita garinsu da yake cikin Ranon jihar Kano ta tare a gidansa da ke ɗauke da matansa da kuma yaransa biyar da suka kasance duk mata.

Kalata ta wurin uba tana nan a raye, amma a lokacin bata garin Rano, tana wani wurin tana aure bayan rasuwar kakana, dan haka babana yana da yayye biyu maza, sai ƙanwarsa mace.

Mahaifiyata na da matuƙar haƙuri da kawaici, mabaifina yana sonta sosai da sosai, hakan ya sa ta bijiro masa da son ta koma makaranta, amma ya ce bai yadda ba abin zai zama surutu a gari.
Tun da mahaifina ya auro mahaifiyata matansa suka sakota gaba, suke nuna mata ƙiyayya a fili. Idan baya nan suyi ta sakata aiki mai wahala. Mahaifina tsayayyen mutum ne a kan gidansa, yana da rufin Asiri sosai a garinmu an san shi sosai yana da kuɗi, yana dillancin dabbobi har zuwa kudu da maƙotan Nigeria, gidanmu ba a yunwa ko rashin sutura, sai dai ba a damu da ilimi ba sam.
A na haka mahaifiyata ta samu juna biyu, sai dai ba wanda ya sani, saboda ba ta laulayi daga ita sai mahaifina suka sani.
Babu wanda ya farga mahaifiyata na da juna biyu, sai ganinta kawai suka yi tana naƙuda. Ta yi doguwar naƙuda bata haihu ba, Babana ya ɗauke ta zuwa Asibitin cikin gari, dan duk da rufin Asiri na mahaifina yana cikin karkara da iyalansa.
Mahaifiyata ta haifi ɗa namiji, Mahaifina yayi murna sosai da sosai, zai samu magaji, mahaifiyata kuma murnar da take yi, shi ne Allah ya cika mata burinta a kan yaron nan, ya zama masanin addinin Muslunci sosai.
Tun da suka koma gida sai ƙananan maganganu, mussaman da suka ga yadda mahaifina ke ta rawar kai a kan haihuwar.
Ranar suna mahaifiyata ta roƙi mahaifina ya saka mini suna Yazid.
Mahaifina bai sani ba, sunan wani babban malami ne a cikin garin Jalingo da Innata ke zuwa masallacin sa jim wa'azi.
Son da yake yiwa mahaifiyata ya sanya shi ya amince, ya sanya mini suna Yazid.

'yan garinsu mahaifiyata sun zo, duk da fulani ne amma wasunsu ba musulmai bane ba suka zo taron suna, mahaifina sai da ya yanka manyan raguna da saniya, aka dinga ci ana rabar da naman a garin, ko baka je suna ba, abu ne mawuyaci ka kasa cin naman da aka yanka da kuma abincin suna.
Matan Babana suka kuma mahaifiyata a gaba, abin mamaki a wannan karon har da facaloli, suna mata gorin wai 'yan uwanta maguzawa ne.

Mutanen gari suka dinga yi wa matan mahaifina Allah sarki, duk wannan wahalar yaransu mata ne, lokaci ɗaya daga zuwan mahaifiyata ta fara haihuwar namiji, idan babana ya mutu ba zasu samu komai ba.
Kasancewar mahaifiyata ba sawa ba fitarwa, ya sanya bata damu da abin da suke yi ba, sannan bata nuna kara a kaina kasancewata ɗan fari.
Ba abokan zaman mahaifiyata ba, hatta 'yan uwana yayyena, suke kishi da ni, basa son na raɓesu.
Tun ina ƙarami mahaifiyata ke mini kirana da Gwani Yazidu magajin malam.

Bayan na fara tasawa, ɗan abin da mahaifiyata ta sani na ilimin addini ta fara koya mini, hatta magana tayi iyaka ƙoƙarin ta bakina ya buɗe da la'ilahailallah. Irin koyon maganar nan na yara, da bisimilla istigfari ta dinga koya mini bakina ya buɗe da su, bana zuwa ko ina ba wanda yake ɗaukata kullum ina tare da mahaifiyata hakan ya sanya nayi saurin iyawa.

Shekaruna uku a duniya, Innata ta matsa a kan lallai mahaifina ya kaini makaranta, ya nuna mata nayi ƙanƙanta da yawa amma ta dage, da ƙyar ta bari na shekara huɗu. Ya sakani a wata makarantar addini da take ƙauyenmu, sai dai akwai nisa sosai daga gidamu zuwa makarantar dan haka mussaman yake biya malamin makarantar kuɗi, ya dinga sawa ana zuwa a ɗaukeni ko a dawo dani.

Cikin ikon Allah nan da nan, kasancewar ƙwaƙwalwar yarinta, na dinga ɗaukar karatun Alkur'ani da malamin ke tsaye a kaina yana koya mini.
Tamkar ɗan ƙaramin ɗansa haka ya mayar da ni, ya kan ɗorani har a kan cinyarsa yana koya mini karatun Alkur'ani.

Sai dai ƙiyayyar da ake nuna mini a gidanmu  ta sanya bana sakewa ko a cikin yara, dan ko tsakar gida na fito wasa, sai yayyena su ci zalina.
Kullum ina naniƙe da Innata ko ina makaranta.
Batun gata a wurin mahaifina ba a magana, duk abin da ya ɗinka sai ya ɗinka mini, ga mahafiyata ma bata wasa da Abincin da zan ci, bata bani cimar banza, gashi da ƙananan shekaruna amma girmamani take saboda sunan da aka saka mini.
Daga cikin abin da yake ƙonawa mahaifiyata rai, shi ne yadda abokan zamanta kan kirani da jikan maguzawa saboda a danginta akwai wanda ba Musulmi ba, cikin izgilanci idan ta kirani magajin Malam, sai suce ko kuma jilan maguzawa ba.


Sai da na shekara bakwai a duniya, sannan mahaifiyata ta kuma haihuwa, ta sake haihuwar ɗa namiji, aikuwa matan gidan nan tamkar su kasheta, saboda 'ya'ya maza take haifa. aka saka wa jaririn sunan Huzaifa.

Duk da Inna ta kuma haihuwa, hakan bai hana ta daina sona ba, tare da cigaba da kula da mu.
Ban fi shekaru goma ba, Mahaifina ya fara tafiya da ni wuraren kasuwancin sa, idan yana gari wasu lokutan haka yake zamansa yayi ta hira da ni, yana mini hirar kasiwancinsa duk da ba ganewa na ke yi ba. Ya biya aikin umara ni da shi ya tafi da ni.
Hakan ya ƙara rura wutar ƙiyayyata a zukatan matan gidan, kamar su cinye ni su huta. Inna tana yawan gaya masa ya dinga ƙoƙarin yin adalci a tsakanin yaransa bai kamata ya tafi da ni umara ba. Amma buɗar bakinsa ya ce mata "Su 'ya'yan su da nake aurarwa na ke kashe musu kuɗi nawa na taɓa bawa Yazid, ina adalci a tsakanin su"

Ƙanina Huzaifa shima ya fara tasawa, sai dai halina da na Huzaifa ba iri ɗaya bane ba. Huzaifa yaro ne mai ƙiriniyar gaske, ga ta'adin tsiya, Inna tana can tana aiki Huzaifa zai fita tsakar gida ya shiga neman magana a tsakar gida.

Su kama mutan gidan su kama Huzaifa su yi ta duka suna zagi, abin da yake matuƙar ƙona mini rai, in ga an daki ɗan uwana. Duk rashin maganata ina jin haushin in ga an taɓa gudan jinina.
A lokacin na kai shekaru goma sha uku, ina haddar Alqur'ani sosai da sosai, tun Huzaifa na shekara uku nake tafiya da shi makarantar mu. Idan muna gida kuma ina koya masa karatun.

Ba zan manta watarana ba, babbar yayarmu da aka yi mata aure tuni, mai suna Yaya Gaji ta zo ita da yaranta.
Suna cikin wasa tare da Huzaifa da yaranta, faɗa ya kaure a tsakanin sa da ɗanta Sani, yayyensa suka haɗu suka dinga dukan Huzaifa, da ƙyar na ƙwace shi, na kalli ɗaya daga cikin yayyena da har da su a dukan Huzaifa, abin da ban taɓa ba nace "Allah ya saka maka" ba tsammani na ji saukar mari yayata mariya ta mareni tare da ɗorawa da zagina. Duk ƙanƙantar Huzaifa da yaga an mari yayansa, haka ya fara kaiwa Mariya duka, haka na janye Huzaifa muka bar tsakar gidan.

Sai dai ko mintuna goma ba ayi da dukana da Mariya tayi ba, ta ƙone a hannu da ruɗen tuwo, a take ta kurma ihu, ba a ɗau tsawon lokaci ba hannun ya saɓule a take.

Mariya ta sha jinya dan kamar hannun ba zai warke ba, shi kuwa Huzaifa kamar an sake tunzura shi kullum rashin jinsa gaba yake yi.
Hatta Innarmu suna yawan yin faɗa da Huzaifa, ni kuwa ko Inna bana son na ga tana taɓa mini Huzaifa.

Gaba ɗaya hankalina baya kan kasuwancin da mahaifina ke ta janyo ni kan harkar. Ina nan na mayar da hankali a kan karatu na, tare da kula da ƙanina abin ƙaunata.
Kwatsam! Matan mahaifina suka tsiro da wani camfi, wai in dai aka taɓawa Inna 'ya'ya sai wata masifa ta afkawa mutum, bayan jikan maguzawa da suke kirana da shi, suka fara ƙoƙarin laƙaba mini maita ni da mahaifiyata.
Ina da shekaru goma sha huɗu, na sauke Alƙur'ani hadda, malaminmu ya fara batun a turani makaranta cikin gari, domin samun cigaba da karatuna na addini.
Mahaifina ya fara iƙirarin karatun ya isa haka, yana son ya sakani a kan kasuwancin sa sosai, amma mahaifiyata ta cigaba da lallaɓa mahaifina, a kan ya bar ni na cigaba da karatun.
Son da yake yi mata ya sanya wasu lokutan, baya son yin abin da zai sanya ta cikin damuwa. Makarantar da zan tafi ta kwana ce, amma zallar ilimin addini ne ake koyarwa a ciki.
Inna tana ta yi mini shirye shiryen tafiya, ni kuma kewarta da ta ƙanina ta fara damuna, ina son karatuna amma kuma ina ƙaunar iyayena da ƙanina. A nata shirin tafiyata ne, a lokacin  kuma Innarmu ta fara wata irin rashin lafiya, ga kuma tsohon ciki, ga wasu irin ƙuraje da suka fara fito mata a jikinta.
Nan na ji ba zan iya tafiya na bar sanyin idaniyata a wannan hali na rashin lafiya ba.

Inna ta dafa kafaɗata ta ce "Haba Gwani ɗan Inna magajin malam, ba ka son Inna ta yi alfahari da kai, ka zama babban malami?"

"Inna ina so, amma baki da lafiya fa"

"Bakomai, kar ka damu zan ji sauƙi in sha Allah"

Huzaifa ya kalli Inna ya ce "Inna, wai almajiranci za a kai yayana, ni gaskiya zan bi shi in da za shi"

Inna ta ce "A'a ba almajiranci bane ba, karatu zai je yi"

Huzaifa ya fara kuka ya riƙe ƙafar Yazid ya ce "Gwani Dan Allah kar ka tafi ka barni, dukana su Mariya zasu cigaba da yi, kuma wa zai kaini makaranta? Da wa zan dinga cin abinci?".

Na durƙusa na rungume ɗan uwana, ina rarrashinsa. Inna ta matsa na tafi makaranta.

Ta riƙe hannuna ta ce "Allah ya yi riƙo da hannunka, Allah ya shiga lamarinka ka mayar da hankali sosai Yazid, Allah ya baka ilimi mai amfani"

Baba da kansa ya kai ni makaranta, tare da Malamina na garinmu Malam Kabir, makarantar babbace, kuma boko ce da islamiyya a haɗe. Dama idan ɗaliban Malam Kabir sun yi sauka, wanda suke buƙatar ɗora karatunsu, wannan makarantar Malam Kabir ke tura ɗaliban sa, saboda yana da connection da su.
A nan shugaban makarantar ya yiwa babana bayanin makarantar an buɗe ɓangaren boko ma, idan yana buƙata in haɗa duka.
Baba ya ce a bani zaɓi idan ina so, nan na ce masa ina so, babana ya biya komai, kuɗin makaranta ta sai da Baba ya tafe na shekara uku, saboda Babana yana da arziƙi dai-dai gwargwado. Iya kayan Abinci da na tafi da su kuwa, ba a magana ya bani kuɗi masu yawa, ya rungumeni yana cewa Gwani Yazid zan yi kewarka sosai zan dinga zuwa ina dubaka.
Ni kaina na ji babu daɗi tafiyar Babana, ga kuma kewar Innata da ƙanina Huzaifa.

Na mayar da hankali sosai a kan karatuna, sai dai ni bokon nan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login