Showing 231001 words to 234000 words out of 296192 words
san me zasu je ya tarar ba ko irin karɓar da Mummy zata yi musu ba.
Haka nan ya dake, suka cigaba da tafiya.
Zakiru yana ganinsu yayi ta koɗa Khalil yana masa kirari da ango ango.
Cikin fargaba da ɗar-ɗar ya yi wa Hafsa jagora zuwa cikin gidan.
Hajara ya tarar a falo tana ta aiki, tana ganinsu cikin fara'a ta tsaya suka gaisa da Khalil, ya tambayeta Mummy na nan? Ta ce masa eh tana sashinta.
Da sallama suka shiga falon Mummy, suka tarar da ita tana zaune a gaban system tana aiki, ɗaga kai tayi ta amsa musu a ciki.
Har ƙasa Hafsa ta durƙusa tana gaida Mummy, amma Mummyn ta bita da wani irin mugun kallo ta ɗauke kanta, jikin Hafsa yayi sanyi sosai, kuma ta kasa tashi daga durƙuson da tayi.
Khalil cikin ƙarfin hali ya ce "Mummy ina kwana"
Ta mayar da dubanta kan Khalil ta ce "Me ka zo yi mini?"
Ya ce "Amm, dama zuwa nayi na kawo miki ita mu gaishe ki"
"Me na gaya maka lokacin da zaka yi auren nan?" Tayi maganar tana tsareshi da ido, Khalil Yayi shiru ya sunkuyar da kai.
"Tambayarka nake me na gaya maka?"
Still bai iya cewa komai ba.
Ta ɗan ƙura masa ido sannam ta ce "Tun da ba zaka faɗa ba ni bari na tuna maka, ai na gaya maka muddin kayi auren nan, sai dai ka nemi wata uwar, dan haka ka tashi ka bani wuri, ni ba sirikata bace ba, kaje can ka ƙarata ba dai ka bi son zuciyarka ka auri wadda kake so ba, 'yar gajiyayyun mutane, to kuje can ku ƙarata kar ka sake kawo mini ita gidan nan wai da sunan gaisheni, ga 'yar uwarka nan zata share mini hawaye ta auri wanda nake so, na zaɓa mata kai kuma na sallamawa mai awara kai, bani ba kai na bar mata kai. Kuma ba bar mata kai nayi ba ina nan zan waiwayoka ba zan zura ido ka zauna da jinin tsiya ba ba zai yiwu ba, tashi ki kwashi kayanki ku bar mini gabana"
Hafsa ta daskare a wurin, ta kasa magana, Khalil ya buɗe baki zai yi magana amma cikin tsawa ta ce "Ka bar mini falo nace, tattarata ku bar gabana, kar ki ma sake ɗaukar kanki a matsayin sirikata"
Hafsa ta miƙe ƙafa na rawa, ido ya ciko da hawaye, tayi gaba Khalil ya durƙusa ya ɗauki kwandon kayan Abincin ya biyo bayan Hafsa.
Hajara kuwa tana ganin zuwan su Khalil taje ta gaya wa Amina, Amina ta san za a rina dan matar nan bata da mutunci wulaƙanta 'yar mutane za ta yi, tunda ba sonta take yi ba.
Amina na ganin sun fito, fuskokinsu babu walwala amma Amina ta washe baki ta nufi Hafsa tana faɗin "Oyoyo amaryarmu, sannunku da zuwa ba dai har kun fito ba?"
Khalil ya ce "Eh tafiya za muyi".
Amina ta ce "Au da bamu haɗu ba kawai sai kuyi tafiyarku?"
Ya ce "No, zamu shigo ku gaisa ai"
Amina ta ce "Ba wani mu gaisa, a nan zamu wuni, sannunku da zuwa" ta janyo hannun Hafsa zuwa sashinta, yadda Amina taga idon Hafsa cike da hawaye, ya ƙara tabatta mata da wulaƙanta ta Hajiya Zainab tayi kamar yadda ta saba.
A falo suka zauna, Amina ta ce "Khalil jiya Daddy ya gama mita, wai tun da ka tafi ko a waya baka kirashi ba"
Khalil ya ce "Wayar ce ta faɗi, screen ɗinta ya fashe"
"Aikuwa da tuni ka ganshi a gidanku, na ce ya ɗan bari tukuna. Sister Hafsa ya gida ya baƙunta?"
Hafsa ta ƙaƙalo murmushi cikin sanyin muryarta ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah"
"Masha Allah, ya gajiyar biki? An sha hidima"
"Alhamdilillah"
Amina ta miƙe ta ce "To mai zan kawo muku ne? Ina da tea idan kuma girki zan yi muku shikenan"
Khalil ya ce 'No, mun karya ga ma abinci mun zo da shi, tafiya za muyi"
Amina ta ɓata rai ta ce "Saboda me? Bafa nisa Daddy yayi ba, zai dawo ɗaurin Aure ya je, kuma wani irin zuwane wannan? Ai gara ka barta mu wuni a nan zaman kaɗaicin nan babu daɗi"
Khalil ya sunkoyo daidai kunnen Hafsa ya ce 'Habibty, na barki tare da ita ba zaki takura ba?" A son Hafsa gara su koma gida, amma ganin yadda Amina ta karɓeta ya sanya ta ce "Eh ka barni"
Duk miskilancin Hafsa, haka Amina ta dinga janta da hira, tun tana ɗan ɗari-ɗari, har ta samu ta ɗan sake suka yi ta hira da Amina, ganin ta sake ne ya sanya Khalil ya ce bari ya barta yaje ya dawo, kan nan ma Daddy ya dawo.
Amina ta saki jiki da Hafsa, har ta dinga bata labarin ƙauyensu da yadda ta gudo wurin Babanta a birni.
A hakan Hafsa ita ma ta ɗan ɓincina mata wani sashi na rayuwarta, Amina taji tausayinta ƙwarai da gaske, gashi Allah ya bata miji mai sonta in da zata huta, amma uwar miji ta sako ta a gaba.
Amina ta ce "Kiyi haƙuri, kin san ita rayuwa ba a taɓa barin ɗan Adam haka, sai da jarrabawa".
Hafsa ta ce "Amma Anty Amina gani nake rayuwar aurena tana cikin barazana, idan Mummy ta yiwa Khalil aure, kamar zata ƙara tsanata"
Daɗi Amina taji, an kirata da Anty, har ana tambayarta abu. A ranta ta ce 'In dai wannan matar ce, zuciyarta kamar ta sheɗan ba Allah a cikinta, ba tare da saninta ba na auri mijinta, yanzu Allah ya ƙaddar auren ɗanta da na talaka, amma ba tayi hankali ba' a zahiri kuma ta ce "Karki damu, ba wanda zai yiwa wani abu sai abin da Allah ya hukunta zai same shi, se me? ta aura masa mata dubu ma idan ta na so, ke ai kanki kawai kika sani, tunda dai yana sonki, ko mata nawa ya aura kiyi ƙoƙarin kiga kin yi maintaning matsayinki a wurinsa, idan ma ta aura masa in ma bata aura masa ba, idan mai hange hange ne zai auro wata, kawai kiyi fatan idan ma auren zata yi masa ta aura masa shashasha, nifa kin ganni idan na shige sashina sai na manta ina da abokiyar zama, ayyukan gabana sun ishe ni, na kula da mijina da sabgogina, yanzu admission nake jira, kema kar ki zauna da kin samu dama ki cigaba da karatunki kawai in dai zai yarda".
Hafsa ta ce "Eh zai yarda, yana ma yi mini zancen, amma ya ce na bari ya nutsu daga hidimar bikin nan da yayi"
Amina ta ce "Haka ne biki akwai hidima kam, Allah ya baku zaman lafiya"
Har bayan la'asar ita Mummy ma sam bata san Hafsa na gidan ba, baga tafi ba, Bayan la'asar Khalil ya dawo, a lokacin ma Daddy ya dawo.
Daddy yayi murna sosai da ganinsu, mussaman Hafsa yayi ta yi musu Addu'a da saka albarka, tare da yi musu nasiha a kan haƙuri da juna.
Sai da aka yi sallar isha'i sannan suka rako su Khalil, har mota.
Fadila da taga wucewarsu abin ya bata mamaki, dan bata ma san sun zo ba.
Sashin Mummy ta tafi, tana mamakin yadda suka zo, amma basu zo wurin Mummy ba.
"Mummy"
"Na'am ya aka yi?"
"Mummy Yaya Khalil na gani da matarsa, zasu tafi yanzu kuma banga sun zo wurinki ba"
Cikin mamaki ta ce 'Ban gane sun zo zasu tafi ba dama basu tafi ba?"
Fadila ta ce "Dama kin san sun zo ne?"
"Eh na sani, amma ni korarsa nayi"
"Taɓ, aikuwa suna wurin waccan Yarinyar, gasu can Daddy da ita sun yi musu rakiya"
A fusace ta ce "What! Yaron nan kuwa yana da tunani? Au wurinta ma ya koma?. Gaba ɗaya Khalil bashi da tunani ba shi kuma da hankali, amma na san abin da zan yi, zan yi maganinsa kuma ita kanta sai na ja mata kunne a kan Khalil, munafuncin Yarinyar nan ya isheni"
Fadila ta jinjina kai ta bar ɗakin Mummy.
Bayan su Hafsa sun je gida ma, rarrashi da nasiha Khalil ya cigaba da yi mata, dan babu wanda za a yiwa abin da Mummy ta yi wa Hafsa ya ce zai ji daɗi.
Cikin sanyin jiki ta ce "Amma auren nan zai yi mana albarka kuwa, tun da har Mummy bata so"
Khalil ya ce "In sha Allah, zai yi mana kuma ita ma zata sauko" Hafsa dai kawai jinsa tayi, amma ba dan ta yarda da abin da yace ɗin ba.
Ko da Hafsa suka yi waya da Mama, ta gaya mata sunje gidansu Khalil, amma am bata gaya mata yadda suka yi da Mummy ba, dan bata son ɗagawa Maman hankali.
Sati guda da Bikin Hafsa, Mama ma ta tare a gidan Alhaji Ilyas, cikin ikon Allah dama yaran nasa ba ƙanana bane ba, duk da girmansu, dan haka suka yi ta murna da auren da mahaifinsu yayi.
Haka rayuwa ta cigaba da juyawa, cikin jujjuyar lokaci sakannin zuwa mintun, awanni zuwa sa'oi kwanaki da kuma satuttuka suka dinga shuɗewa.
Hafsa ta yi wata guda a gidan Khalil, cikin tsananin so da ƙaunar junansu, sai tattalata yake yi yana nuna mata ƙauna, gefe guda kuma a tsorace take, saboda iƙrarin Mother a kan za ta yiwa Khalil aure, shikenan idan ta yi wa Khalil aure ta kaɗe, dan ta san budurwa zata aura masa, kuma 'yar masu kuɗi, shikenan ita ma ta san wannan rawar kan da yake a kanta, dan yanzu ya aureta ne, amma da ya samu wata zai daina tattalinta.
Ranar da ta cika wata biyu, ya ɗauketa ya kaita har gida wurin Mama, Mama tayi murna sosai da ganin Hafsa, tayi sharrr da ita ta sha kwalliya, ita kanta Hafsa tayi murnar ganin Mama, alamu suka nuna tana cikin kwanciyar hankali tare da mijinta da 'ya'yansa. Da suka tashi dawowa gida, sai da ya kai Hafsa gidansu Abdul suka gaida mahaifiyarsa.
Washegari kuma, Khalil ya saka Hafsa ta kira Amina, dan ta basu kwatancen gidansu a Shanono zasu je gaida Baba.
Amina kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, sai murna take bakinta yaƙi rufuwa.
Tayi musu kwatance sannan ta ce "Khalil, Dutse fa yaushe zaku je?"
Ya ce "A satin nan in Sha Allah"
"To yayi kyau, na gode sosai da sosai, dan Allah idan kunje Dutse har gidan 'yan uwan mamanku kuje, kai kayi zumunci da su".
Khalil ya ce "In sha Allah, ko kina da saƙon da za a kai Shanono"
Ta ce "A'a, ai baifi sati biyu naje, na gode sosai"
Ya ce "Babu komai, kar ki damu"
Ta kaste wayar, Daddy na fitowa daga wanka, tayi tsalle ta rungume shi.
Ya ce 'Tooo, ya aka yi ne?"
"Su Khalil ne zasu garinmu, wai zasu je gaida Babana"
Yayi murmushi ya ce "Ai yayi kyau, yakamata su faranta miki, kamar yadda kika yi tsayin daka a kan kiga bikinsu ya yiwu"
"Kai Alhamdilillah, ji nake kamar nayi rawa wallahi"
Yayi murmushi ya ce "ai kin saba dama"
Su Khalil sun samu karɓuwa sosai a garinsu Amina, Inno ta karrama su sosai da sosai ita da Baba, Khalil yayi musu alheri da yamma suka juyo Kano, Inno kuwa ta haɗa musu kayan tsaraba sosai tana musu Addu'a.
Amina suka yi waya da Baba, ya sanar mata ai su Khalil sun zo, ta dinga murna tana jin daɗi.
Shi kam Khalil ba zai taɓa mantawa da abin da Amina tayi masa ba, ko iya ƙoƙarin ta na samun Hafsa da yayi, ya isa ya dinga ganin kimarta.
Bayan sun huta kwana biyu, Khalil ya kuma ɗaukar Hafsa zuwa Dutse su gaishe su, kuma suyi musu bangajiya, nan ma sun ga kara da karamci, suka dinga murna dan haka nan gari banza Khalil baya zuwa Dutse.
Salim kuwa biki ya nata ƙaratowa yana shiri, sai dai ya fara ƙuluwa da abubuwan da Fadila take yi masa, na wulaƙanci da cin mutunci, dan haka ya fara gaya wa Babarsa abubuwan da Fadilan take yi masa.
Hajiya Salma taji haushin hakan matuƙa, dan haka ta kira Hajiya Zainab a waya.
Hajiya Zainab bata kawo komai ba a ranta ta ɗaga wayar tana faɗin Hajjaju.
"Kin ga Zainab, abin nan idan mai yiwuwa ne ayi, idan ba mai yiwuwa bane ba a bar shi kawai, kince a haɗa auren ɗanki da 'yar 'yar uwata abu bai yiwu ba, zamu haɗa auren yaranmu amma Fadila sai wulaƙanci take yiwa yaron nan, idan fa bata so kawai a bar sabgar nan".
Hajiya Zainab ta ce "Me yayi zafi haka ke kuwa? Mu bi komai a sannu dan Allah, zan yi mata magana" Mummy tayi ta bata haƙuri, ta katse wayar ta tafi ɗakin Fadila.
Da mamaki Fadila ta kalleta ta ce "Mummy, ya na ganki a ɗakina yanzu?"
"Ban sani ba, wato dama munafuntata kika yi, kika ce mini zaki auri yaron nan, amma kike wulaƙanta shi ko? Hajiya Salma ta kirani rai a ɓace ta ce kina wulaƙanta mata ɗa. To kin kyauta kema kije kiyi duk abin da kika ga dama, kuyi ta cusa mini baƙin ciki ke da ubanki da ɗan uwanki tun da haka kuka zaɓa. Ba kwa ƙaunata ba kwa kishina, wai Khalil ya wanke ƙafa ya tafi garinsu yarinyar can, ya kuma je Dutse duk ba tare da sanin na ba, ga baƙincikin babanki kema kuma gashi kin tsiro da naki, na gode" ta juya fuuuuu ta fice ta barwa Fadila ɗakin.
Dafe kai Fadila tayi, kawai ta fashe da kuka, tama rasa me za tayi, 'yan kwanakin nan ni ko bacci bata iya yi, saboda tunanin auren nan, ga Mummy sai shirin biki take, ga shi shi kuma munafuki ya na kai ƙararta.
Take taji wani irin mugun takaici ya tokare ƙirjinta, tayi jifa da littafin hannunta ta cigaba da kuka.
Alhaji Ahmad yana ta shirin komawa Lagos, amma yana tunanin yadda zai bar Amina da Hajiya Zainab a gida, dama a yanzunma yana nan ɗin ba shiri suke ba.
Kwanciyar hankalinsa shine yana wurin Amina, amma duk lokacin da yake a wurin Hajiya Zainab, kwanan tashin hankali suke yi.
Hafsa na kwamce a kan doguwar kujera, Khalil ya ce ta zauna ta huta, yana ta ɗan yin aikace-aikacen da zai iya yi, Hafsa sai dariya take yi masa, yana mopping tana cewa 'gaskiya wannan mopping ɗin, to kar dai in ce a bar mini abina nayi aji haushi, amma gaskiya ba haka ake yi ba"
Yayi dariya ya ce "Aikuwa sai nayi, kuma idan na gama sai kin mini godiya, in gama in je in ɗora girki"
Hafsa ta ce "Kaiii, ashe yau ciki zai ɓaci, za ayi ta gudawa"
"Aikuwa sai na dafa, kuma sai kin ci"
Kamar an wurgota sai ganin Hajiya Zainab suka yi a tsakiyar falon.
Miƙewa Hafsa tayi, gaba ɗaya jikinta ya ɗau rawa, ga 'yar rigar jikinta ba in da ta kai.
"Mu..mu... Mummy sannu da zuwa" Hafsa tayi maganar cikin rawar murya.
Wani kallon banza tayi mata ta ce "Ba shakka, kin zo kin samu wuri kin miƙe ƙafa, kai kuma har ka zama bawa ko? Wato Khalil saboda baka neman albarka saboda ka nuna mini ban isa ba, ka wanke ƙafa ka tafi har Shanono wurin wancan matsiyatan ni kake wulaƙantawa ko Khalil".
Jiki ba ƙwari Khalil ya ce "Mummy ba haka bane...
"Rufe mini baki, munafuki" ya sunkuyar da kansa ƙasa, yana sake mamkin hali irin na mahaifiyarsa.
"To bari kaji in gaya maka, wallahi ba za a taru a mallake mini kai ba, ban haifawa kowace mace bawa ba, ka tattara kayanka ka koma wurin aikinka, wallahi na bincika baka koma ba, hukuncin da zan maka sai ya baka mamaki, kuma ban yarda ka bar garin nan da ita ba, ke kuma ki fara lissafa kwanakin da suka rage miki a gidan nan, dan yadda yake wannan rawar kan a kanki, nan gaba sai abin da Allah yayi, ina ga zai iya dukana ma saboda ke".
Khalil ya haɗa hannayensa biyu ya ce "Mummy dan Allah kiyi haƙuri, kinga bama ta jin daɗi, na miki alƙawarin da ta ji sauƙi zan koma"
"Au har ya kaimu ga fara jayayya ko Khalil? Da kan ka aureta sai ka tafi ka shafe kwanaki ban saka a idona ba, amma saboda ita ka fara yi mini musu ko? Khalil kar ka ƙure ni nayi maka baki fa"
A gigice ya ce "Shikenan, Kiyi haƙuri zan koma in Allah ya yarda".
"Kar ma ka koma kaga yadda zan yi da kai, sakarai" yadda ta shigo ta zazzage musu masifa, ko zama ba tayi ba ta juya ta fice. Dama tsarin da tayi, idan ya bar garin zata san yadda zata yi ta kori Hafsa, dan bata ƙaunarta ko kaɗan.
Mummy fa ta tatara Fadila ta fita a sabgarta, hakan ya sake jefa Fadila cikin tsananin damuwa, ko Abinci bata iya ci, karatunma ta ajiye bata iyawa gashi test suke yi a makarantar.
Da ƙyar a daddafe ta iya yin test ɗin yau, saboda azabar ciwo da kanta yake yi.
Bayan sun gama test suna da sauran lectures, sai dai ba zata iya jira ba, kuma gaba ɗaya ko son zuwa gida ba tayi, saboda ta san damuwa zata je ta kuma tarar wa.
A hankali ta tashi ta bar ajin, saboda yadda hayaniya tayi yawa a ajin.
Wani ajin da babu kowa taje ta samu ta zauna, sai da kanta ha cigaba da yi mata wani irin matsanancin ciwo, ga ƙirjinta yayi nauyi, da ƙyar take numfashi.
Har Yazid ya shiga aji, suna jiran malamin da zai shigo musu, yaga kiran Fadila.
Ɗaga wayar yayi yana mamakin dalilin kiran nata, dan harara ce take haɗa shi da ita a kwanakin nan.
Yana ɗagawa yaji muryarta sama-sama ta ce "Dan Allah ka zo level 4, bani da lafiya ka zo ka kaini gida"
Cikin hanzari Yazid ya tashi, ya bar ajin ya nufi level 4, a can ƙarshen ajin ya hangota ta kifa kanta.
Ya ƙarasa in da take da sauri yana kiran sunanta. Ɗago idonta tayi sun yi jawur, hawaye ne kawai ke fita daga idonta.
"Subhanallah, Fadila meyafaru ne?".
"Bani da lafiya, na kira Yusra bata ɗauka ba ina ga suna lectures ne, dan Allah ka kaini gida kaina zai fashe, dishi-dishi nake gani"
Yazid ya ce "A'a mu dai je Asibiti, in da kika taɓa kaini ɗin nan, ta so muje" jiki na rawa ta tashi tsaye, ya sa hannu ya karɓi jakarta, sai dai jiri ya kwashe ta, Yazid ya riƙeta.
Aikuwa ta fashe da kuka ta ce "Bana gani sosai fa"
Yazid cikin damuwa ya ce "Sannu, tashi mu tafi daure".
Da ƙyar ta iya tsauwa, ta riƙe gefen rigarsa suka fito a hankali.
Suka ƙarasa wurin motarta, ya duba jakarta ya ɗau mukulli ya buɗe motar, ta