Showing 252001 words to 255000 words out of 296192 words

Chapter 85 - GABA DA GABANTA

tana mini wahala, dan makarantar kanta sun fi ƙarfi a kan ilimin addini, amma duk da haka ban sare ba, na ɗorawa raina ina son yin karatun.

A lokacin babu waya, dan haka ban san halin da Inna da Huzaifa suke ciki ba, duk da abin yana damuna, Baba yana zuwa kawo mini ziyara sai ya ce mini kowa yana nan lafiya ba sai na zo ba gida ba, in zauna in yi karatuna dan cika burin mahaifiyata.

Kusan watanni huɗu ina makaranta ban je gida ba, Baba ya hanani, gashi an shigar wata na biyar, Baba kuma ya shafe lokaci bai zo ba, na tayar da hankalina na ce zani gida.

A ka bani kwana uku a makaranta.

Sai kuma Yazid yayi shiru ya sunkuyar da kansa.
Cikin ƙosawa Fadila ta gyara zama ta ta ce "Cigaba mana"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Da na koma gida, Allah ya yiwa Babar Gwani rasuwa, wato Innarmu. Naƙuda ta kamata Baba baya gari, matan gidan nan aka rasa mai kaita Asibiti. Tun lokacin da take da cikin kasancewar mahaifinmu ya ɗan fara wayewa da wasu al'amura na zamani, ya bar Inna ta je awo, kuma a wurin awon an sanar mata da ta fara naƙuda ta je Asibiti kar ta haihu a gida, ni da ita take gaya mini haka, amma ba su taimaka mata ba, dama tana halin rashin lafiya naƙuda ta risketa, tayi jijjiga ta rasu, ta bar ɗan jaririn, kamar yadda na samu labari har ta mutu tana tsaka da naƙuda addu'a take yi mini, Allah ka cika mini burina a kan Gwani, Allah ka shirya mini 'ya'yana ka duba mini ka tsare mini shi, da shi da ɗan uwansa Allah ka zama gatansa. Da ire-iren wannan addu'a ta cika.

Baki ba zai iya bayyana halin da na shiga ba, na tarar da Huzaifa ya yi baƙi, ya rame na nemi a nuna mini mai ta haifa amma aka ce washegari shi ma ya koma.
Duk yadda na so na yi tawakalli na kasa, na shiga ɗakinta na tatarao kayanta na saka a gaba na dinga kuka.
Bayan an share zaman makoki, dangin mahaifiyata suka ce zasu tafi da Huzaifa, tun da yarone a ƙarami, bai fi shekara takwas zuwa tara ba, amma matan mahaifina suka ce, kar ya yarda a kai masa ɗansa cikin maguzawa. Aikuwa mahaifina ya hana su, mahaifiyarsa ta so saka baki, amma ta yi shiru saboda duk 'yan'yanta shi ne mai kuɗi ba ta son ɓacin ransa.
Sai dai tun a wurin zaman makokin Inna, na fuskanci sauyi daga wurin Baba, kamar ba ya son ganina, da ya ganni sai ya kawar da kansa, idan na zauna a wuri sai ya tashi, ya yi ta hantarata na rasa dalilin haka, amma na bar shi da kawai alhinin mutuwar Inna ne.

Duk da ƙarancin shekaru na Huzaifa, ya dinga ce mini "Gwani, Inna ta ce kayi karatu, ka cika mata burinta" Na rungume Huzaifa ina kuka, ina tunanin yadda zan bar shi a gidan shikaɗai.
Mahifina ya koma kan kasuwancin sa, ba tare da ya mini ko sallama ba. Ga wasiyyar Inna a raina ga tausayin Huzaifa, tabbas da ya dauke Alqur'ani da da shi zan tafi makarantar mu.

Tun ina gidan ban koma ba, abinci sai an ga dama ake bamu, a daddafe na kwan goma, Huzaifa yana nanata mini in koma makaranta.
Dauriya da juriya ce kawai ta sanya ni na koma makaranta, na ji duniyar ta isheni, ta daina mini daɗi, bana gane komai, karatunma da ƙyar nake yi, Allah ya jiƙan shugaban makarantarmu Malam Umaru mai allo, ya dinga rarrashina yana bani haƙuri.

A haka na cigaba da karatu, ina tunanin halin da ƙanina yake ciki, da ƙyar na yi watanni biyu, kayan Abinci na suka ƙare kaf, ga Baba ya daina zuwa makarantar gaba ɗaya ganina.
Wani ɗan makarantarmu da muka yi makaranta tare a garinmu da yaje gida ya dawo, yake sanar mini wai akwai matsala a gidanmu ƙanina babu lafiya. Ranar ko baccin awa guda ban ba, gari na wayewa na nemi izini na tafi garinmu. Da na je gidan mu ba wanda ya saurareni, balle ya iya gaya mini abin da ya faru, sai a waje ake gaya mini, wai Huzaifa na babban Asibitin cikin gari.
Kuɗin hannuna ba su taka kara sun karya ba, na tafi Asibitin da aka gaya mini, sai da ƙyar na gano a in da aka kwantar da Huzaifa.
Na tarar da shi Kansa da hannunsa duk bandeji, ga ƙafarsa ma haka.
Cikin tashin hankali na ƙarasa wurinsa, na riƙe shi cikin kuka na ce "Gwani Huzaifa, meyafaru da kai haka?"

Leɓensa a bushe ya kalleni, ya riƙo hannuna da hannunsa mai lafiya ya riƙe, amma bai ce komai ba sai hawaye da ke bin gefen idonsa.

Na kuma matsawa na ce "Waye yake zaune a wurinka"

Ya girgiza kai ya ce "Ba kowa, Baba uwani ce ta zo ta tafi, amma ba ta kula da ni ba ta bani ruwa"

Cikin kuka na ce "gayamini, meya sameka ƙanina".

Huzaifa ya ce "Zan gaya maka, amma kar ka gayawa kowa"

"Ba wanda zan gayawa"

Huzaifa ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Sani ɗan gidan Yaya Gaji ne, da muka je ɗiban ruwa bayan gari, ya hankaɗani a rijiya, ya gudu ya barni, ban san yadda aka yi na fito ba, na ganni a nan, wannan masu saka farar rigar sun ce na karye a hannu na da ƙafata, a biya kuɗi a gyara mini."

Na sake matsawa na rungumeshi ina kuka, shi ma cikin kukan ya ce "Baba bai zo ya ganni ba, kuma Inna Gaji ta ce ta gaji da zuwa wurina, dan Allah Yaya kar ka tafi ka bar ni a nan"

"Babu in da zanje Huzaifa, ina nan a wurinka".

Muna cikin wannan halin wani likita ya shigo, ya kalleni ya kalli Huzaifa ya ce "Ɗan uwanka ne?" Na jinjina masa kai alamar eh.

Cikin faɗa ya ce 'Amma 'yan gidanku ba su da mutunci, mun gaya musu a zo a biya kuɗi mu ɗora yaron nan, ayi masa hoton kai da na ƙirji da sauran tasa tasai, ya zubar da jini sosai kalli yadda fatarsa tayi haske saboda rashin jini, kuma idan yayi tari gudan jini ne yake fita, amma sun yi buris kamar an kawao dabba an ajiye,mai jinya ma babu, Mutanen karkara sai dai su haifi 'ya'ya amma ba a iya kula da su ba".

Na kwantar da murya na ce "Dan Allah likita ka yi haƙuri, ina ga babanmu bai sani ba, amma zai iya biyan ko nawa ne, bari zan je gida na gaya masa".

Likita ya ce "Ka hanzarta, dan muna buƙatar ganin baban naku, ance babar yaron ta rasu, amma ai yakamata ya sanya ido a kan yaransa, ya za ayi a tura wannan ɗan mistitsin yaron ɗiban ruwa a rijiyar ƙauye da bata da ɗauri balle murfi ba dole ya faɗa ba?"

Likitan nan ya yi ta sababi ina ba shi haƙuri. Da ƙyar na lallaɓa Huzaifa, ya haƙura na ninka na koma gida a ƙafa, saboda bani da kuɗin mota, na yi sa'a na tarar da Baba a gida. Na gaishe shi amma ya ƙi amsawa sai tsawa da yayi mini, yana tambayata ko lafiya?.
Nan na sanar masa da abin da likita ya ce, abin mamaki duk soyayya tarairya da kulawar Baba ga 'ya'ya musamman idan mutum ba shi da lafiya ba ga matan ba ba ga mazan ba, muddin ɗansa ba shi da lafiya sai ya shiga damuwa, amma a wannan karon sai ya hauni da faɗa, wai na tashi na ba shi wuri. Na shiga tunanin laifin da na yiwa Baba har na fusanci wannan wulaƙanci amma na kasa ganowa, na sake marairaicewa ina masa kuka da magiya, amma ƙarshe ya hau neman madoki.
Matan Babana da ke tsakar gida kuma suka saka shewa suna dariya. Wata uwar yunwa na sakata ta, amma ba ta abincin nake ba, na shiga ɗakin Inna na tattara samirunta, da kwallaye, na fita da su, na je na sayar na sai Abinci na yi kuɗin mota zuwa Asibiti, da niyyar na kai kuɗin idan ya so ko wani abun a fara yiwa Hauzaifa. Amma ina zuwa na tarar da ma'aikata a kansa yana ta aman jini, da wani irin numfashi, wata Nurse tana faɗin wannan yaron da wuya ya tashi, da alama da ka ya dira a rijiyar ko ya samu internal injury a cikin kansa ko kuma dai a ƙirjinsa!!!YAU TAKE JAJIBERIN ZAƁE A NIGERIA, MASU ƘURI'A A HANNU KU TAIMAKA KU ZAƁA MANA SHUGABANNI NA GARI MASU TSORON ALLAH, KUN GA DAI IRIN HALIN HA'ULA'I DA MUKA TSINCI KANMU A WANNAN RINTSIN, TSADAR KAYAN MASARUFI, RASHIN TSARO, YAJIN AIKI DA SAURANSU.
DUK DA BA WANI MUKE ZARGI DA SAMU A HALIN DA MUKE CIKI BA, JARABTA CE DAGA ALLAH.
MUNA FATAN UBANGIJI ALLAH YA ZAƁA MANA SHUGABANNI NA GARI AMIN.





77

Dariya ce ta kusa ƙwacewa Yazid ya ce "Banda ragon azanci, ya zaki saki kayan kuma ki hau rufe jiki? Me ma zan kalla? Ki shirya a nutse"
bin sa tayi da kallo, ta kasa motsawa balle ta ɗau kayan sai ɓoye jiki da take yi.
Ya ƙarasa ya ɗau kayan ya ɗora mata a kafaɗarta.

Cikin tsiwa ta ce "Ni ka fita na saka kaya"

Shiru ya yi mata, ya wuceta ya buɗe sip, ya ɗauko kayansa yana ƙoƙarin sauyawa, alhalin da ba haka yake yi ba, sai ya ɗebi kayansa ya tafi banɗakin tsakar gida.

"Wai me zaka yi haka?"

"Me kika gani a hannuna? Kaya zan saka"

"Kuma a cikin ɗakin nan a gabana?"

Yazid ya ce "Yau naga ikon Allah, kiyi harkarki nayi tawa mana, ina ruwanki da ni ne?"

Ya ƙarasa maganar yana zare singlet ɗin jikinsa.
Juya masa baya tayi, dama kaya ne suke rage masa girma kokuwa dai tsananin kwarjinin da yayi mata ne?.

Kwasar kayanta tayi, ta nufi ɗan mitsitsin banɗakin da ke cikin ɗakin, wanda da ƙyar take iya juyin kirki a cikin sa. Tana daf da shiga taji ya ce "Masha Allah, ƙafafuwanki gwanin ban sha'awa"

Ƙirjinta ne yake dukan uku uku, tana mamakin fitsarar da Yazid ya ke gwada mata, a haka kamar na ruwansa, abin da yayi mata jiya ta tuna a ranta ta ce 'Lallai ma mutumin nan'.

'wai kayan sun gagara ki saka ne, ko sai na shigo na taya ki sawa?"

Shiru tayi masa, ta gama sanya kayan sannan ta fito, ta wani haɗe rai karma ya kawo mata wargi.

Shima basarwa yayi, ya ɗauki mukulli suka fita.
Mamakin irin unguwarsu Yazid take, kasancewar yamma ce, galibin yaran unguwar suna gindin kwata suna suyar awara, wasu na sayar da dankali, wasu wainar fulawa.
Ga azabar lunguna da kwatoci ko ina, ga uban tumaki da awaki, kana tafe kana basu hanyar wucewa, banda kajin hausa da suke nasu shagalin tsakanin layukan.
Sai a lokacin yake tabattar da da tayi yinƙurin guduwa, sai ta sha wahala, wannan unguwar ai tsaf za a yi garkuwa da mutum.

Ganin yadda take ta ƙarewa unguwar kallo ne ya sanya Yazid ya ce "Ki tayani addu'a, ubangiji Allah ya yassare muni na saya mana gida a duk unguwar da kike so, mu koma Allah ya kawo mini buɗi"

"Ku koma kai da wa?"

"Ni da matata mana" ya bata amsa

Taɓe baki tayi ta ce "Ka sa a ranka kawai ajiyata aka kawo maka, daga yanzu zuwa Kowane lokaci zamu iya rabuwa"

"Ba kya so na saboda ni talaka ne ko Fadila?"

Ba kara ta ce "Eh, ai kaima ka san ni ba tsarar aurenka bace, na yi wani ƙaramin laifi ne Daddy ya hukuntani ta wannan hanyar, kuma na san ba zai wuce wannan banzar yarinyar ce ta saka shi yayi mini haka ba, dan haka kurum Daddy ba zai mini irin wannan auren ba kamar mara galihu".

Jiki a sanyaye ya ce "Haka ne, amma Allah ya sani, ni dai ina sonki, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" daga haka bai kuma cewa komai ba har suka isa gidan Hajiya.

Ko da suka yi sallama, tana tsakar gida ta gama girki, fuskarta babu yabo ba fallasa, ta karɓesu, ta je ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa musu.

Yazid ne ya fara gaisheta, sannan Fadila ta gaisheta, gaba ɗaya matar ba tayi mata ba, mussaman yanzu da take ƙure Fadilan da ido.
Hira ta shiga yi da ɗanta, amma Fadila ta lura tunda suka yi maganar nan a hanya, duk jikinsa yake a sanyaye.
Fadila ta yi shiru kamar bata wurin, amma a hirar ta su, ta fuskanci akwai matuƙar shaƙuwa da soyayya tsakaninsa da Hajiyar tasa.

Hajiyar ce ta tashi ta ce "Yazid tunda kuna nan, bari na shiga gidan can nayi musu jaje, an haura musu an yashe su"

Yazid ya ce "Subhanallah, Allah ya tsare ya mayar da alkhairi"

Ta amsa da Amin ta ɗau hijjabinta ta saka ta fita.

Tana fita Fadila ta kalleshi ta ce "Ka tashi mu tafi ni na gaji"

Yazid ya ce "Kiyi haƙuri ta dawo dan Allah" tayi shiru bata sake cewa komai ba.

Sai da aka yi sallar magariba, sannan suka yi wa Hajiya sallama suka tafi. Amma har suka je gida Yazid bai kuma cewa Fadila komai ba.

Shi ya ja su suka yi sallar isha'i tare, daga haka suka zauna kowa yayi shiru.
Yazid ya ce "Zaki ci Abinci yanzu ne?"

Ta ce "Eh bari in zuba" ta tashi ta tafi Kitchen da kanta, ta zubo Shinkafa da wake ce da mai da salak, cikin ikon Allah duk abin da Yazid ya dafa ya bata ba musu take karɓa ta ci.
Ta dawo falon ta ajiye Abincin a gabansa, da cokula biyu ta ce "Bismillah mu ci" kallonta ya yi ya ce "Ba zan iya cin Abincin ba, kawai ki ci"

"To ai naga ba abin da ka ci"

"Eh zan ci ne, ki ci kawai bari in ɗan fita zan dawo"

Haɗe rai ta yi ta ce "Wallahi kana fita nima fita zan yi, ni fa tsoron gidan nan nake ji, kawai kayi haƙuri da fitar mu ci abinci"

Ɗan dafe kansa yayi ya ce "Da gaske na ƙoshi fa, ki ci kawai Fadila" zama tashi ta yi ta bar masa falon, dan gaba ɗaya shirun da yayi bai mata daɗi ba.

Bai gaji ba ya bita ɗakin, ya tarar tayi kwanciyarta, ya ƙarasa kan katifar ya riƙo hannunta ya ce "Haba matar, fushi ki ka yi? Ki zo ki ci abinci kar ki kwana da yunwa"

"Ba zan ci ba"

"Tuba nake, Allah ya baki haƙuri zo muje mu ci tare, a baki ma zan baki yauwa Sweetheart" tana tura baki ya lallaɓota ta dawo suka ci Abincin tare. Sai dai ƙasan zuciyar Yazid babu daɗi, idan ya tuna Fadila tana gaya masa bata son sa kuma ba zata zauna da shi ba.
Bayan sun gama ne, Fadila ta hau yi masa surutu.
"Wai yau ba zaka islamiyyar ba?"

"Yau Alhamis ai ba islamiyya, kuma na so naje na ɗau nawa karatun, amma kin ce idan na fita zaki fita ni kuma bana son ki tafi ki barni" dariya tayi ta ce "Ai dan kar ka tafi ka barni ne, tsoro nake ji amma ba in da zan iya zuwa, na san ma idan na fita ɓata zan yi".

"Unguwar talakawa dama, idan ba wanda ya saba zama a ciki ba, na za gane kanta ba".

Ta basar da zancen ta ce 'Wai duk wannan karatun naka, kai ma zuwa kake yi ana kuma koya maka?"

Yayi murmushi ya ce "Eh mana, ai shi ilimi kogi ne ba a ƙure masa".

Ta ce "Haka ne, to duk wannan litattafan na uwar ɗaki ka iya su?"

Ya ce 'Alhamdilillah, duk na iya wasu kuma ina bincike a kansu ne".

Ta ce "Lallai ka na da ilimin addini sosai"

"Idan na dawo da daddare kema sai na dinga koya miki"

"To, zaka koya mini larabci ma?"

Ya ce "to zan saka miki kuɗin laraba, ki dinga biyana, sannan na koya miki"

Dariya take, shi kuma ya zuba mata ido, yana jin daɗin yadda yau ta saki jiki da shi sosai.
Ɗan shiru tayi sannan ta ce "Wai ina familynka, ko kaima auren dolen aka yi maka kamar yadda Daddy yayi mini, ko Mummy bata san ya aurar da ni ba?"
Jikinsa ne yayi sanyi, Ya ɗan kalleta ya ce "Auren dole aka yi miki fa ko? Ni ba na dole aka yi mini ba, tun da ni ina son ki sosai. Familyna suna wani wuri mai nisa sosai"

"To amma naga basu zo ba?"

"Eh za su zo wataran"

Ta ɗan yi hamma tare da miƙa, ta tashi tsaye ta ce "Bacci ya zo, sai da safe"

"In zo mu kwanta tare"

"A'a ba kyau" tayi maganar tana shigewa bedroom ɗin.

Murmushi yayi a hankali ya ce "Ya ubangiji Allah ka ƙara sanya salama a zuciyar matata ta zauna da ni, ni kuma ka bani ikon kyautata mata".




Al'amura sun yi nisa, tsakanin Abdul da kuma Yusra, dan sun samu fahimtar juna, dubu ɗari takwas ya bayar na komai da komai banda sadaki.
Aikuwa Abdul ya ga kara, dan iyayenta sun nuna farincikinsu sosai da sosai, dan a yadda suke nunawa su farincikin 'yar su ya fiye musu komai. Suka nuna masa kar ya takura kansa duk abin da Allah ya bashi ya kawo musu.
Sun sami fahimtar juna sosai da soyaya a tsakaninsu. Yusra kullum cikin yi masa zancen Fadila take, na haryanzu ba a san in da take ba.
Yayi ta rarrashinta yana kwantar mata da hankali, yana nuna mata ai Fadila ba wani abu ne ya sameta ba, tun da dai Daddy ne ya ɗauketa.




Khalil yana ta shirin komawa Abuja, amma yanayin jikin Hafsa ne ya hana su tafi, dan wataran sai Mama ta zo ta wuni tare da ita, tana shan wahala sosai da sosai akan laulayin nan.
Gefe guda kuma zuciyarsa na matuƙar tausayin Mummy, duk ta firgice kamar wadda aka ce an sace Fadilan.
Da kansa ya kira Daddy a waya, yana masa magiyar yayi haƙuri ya taimaka ya gayawa mahaifiyarsu in da Fadila take.

Alhaji Ahmad ya ce "Kana ji na Khalil?"

"Eh Daddy"

"Tun tasowarku, na kasance ina biyewa abin da kuke so da wanda mahaifiyarku take so, na yi haƙuri na ɗau hakan bakomai ba, dai daga baya na gano illar da hakan da yake da shi a rayuwarku, mussaman Fadila da take mace, Fadila 'ya ta ce, ba zan yi abin da zan cutar da ita ba, dan haka ka ƙyaleni ina sane da abin da nake yi, hakan tamkar hukunci ne ga mahaifiyarku da ita kanta Fadila, kana sane da yadda suka saka na karɓi kuɗin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login