Showing 165001 words to 168000 words out of 296192 words
bane ba, ga ƙananan shekaru a wannan lokacin.
Ina iya ƙoƙarin tsare gaskiya, a kan aikina nan ma ya nemi ya janyo mini matsala, saboda bana karɓa ko bayar da cin hanci.
Na samu abokin mahaifina da nake masa kallon uba, nace masa ina son yin resigning ni wannan mulkin ya isheni, amma ya ce mini bai lamunce ba.
Babban abin da ya ƙara tsolewa masu adawa dani ido, shi ne yadda na samu kusanci da shugaban ƙasa sosai, yana ji dani dan a lokacin ya kusa haifata, amma sai ya tsallake manyan carbinet ɗinsa yayi shawara yayi dani.
Abu kamar wasa, bayan suka da nake fuskanta, har aka fara nema a taɓa lafiyata ta hanyar yi mini barazana daban daban, a haka da ƙyar muka shekara takwas.
Duk da wannan ƙalubale, mutane suna sona sosai da sosai, har wasu sun yi zaton ko zan tsaya takara, amma nace ba zan iya ba. Muna barin mulki, nace ba abin da zai sake mayar da ni harkar siyasa ba zan iya ba.
Na koma na samar da kamfanina na A.M dutse construction limited. Nake kwangila. Cikin ikon Allah kamar wasa kamfanina ya karɓu, nake samun ayyuka ta ko ina, har gwamnati ina yiwa ayyuka.
Khalil ma irin karatuna yayi, na so ya karɓi harkokina ni in samu in huta, amma na lura irin halina ne da shi, baya son dogara da kowa, ya ce shi nasa aikin yake so, shi ne na samar masa aiki a Abuja, amma shima yana nan yana ƙoƙarin buɗe nasa kamfanin, ina son in taimaka sa ya buɗe, ya haɗa kai shi da wannan abokin nasa, su tafiyar da kamfanin, ina son Yaron yana da nustuwa sosai"
Amina tayi ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa wannan matar taka ta bari, with due respect sir, kayi haƙuri da abin da zai fito daga bakina a kan matarka, wallahi matarka ta fiye son kanta da yawa, idan baka yi da gaske ba ka amfani dukiyarka a duniya ba zaka amfaneta a lahira ba. Gaba ɗaya ka sakar mata ragamar gidanka ba irinta ake sakarwa ragamar gida ba. Ita duk wanda zai raɓoka ya ci arziki bata so, duk wannan tarin dukiyar ya zata yi da ita idan ba ta bari anci ba?"
Shiru Daddy ya yi, ya janye Amina daga jikinsa ya juya mata baya.
FOLLOW ME ON WATPAD
@ ayshercool7724
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Arewabooks@ ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724
53
Ba tayi fushi ba, ta koma bayansa ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, ta saƙalo hannunta a ƙirjinsa, cikin sanyin murya ta cigaba da yi masa magana.
"Daddy, na san wataƙila maganganuna su yi maka tsauri, amma ban gaya maka domin cutar da zuciyarka ba, so nake ka duba lamarin nan. Tun da na fara aiki a gidanka sau ɗaya naga kaje garinku, Shima ɗaurin Aure kaje, sannan kuma sau ɗaya kacal na taɓa ganin 'yan uwanka sun zo gidanka, anya kuwa Daddy rayuwa zata tafi a haka?.
Ko da iyayenka basa raye, 'yan uwansu da abokan mu'amalarsu yakamata ace suna zuwa inda kake, amma kullum ba mai zuwa wurinku ba kuma kwa zuwa wurin kowa, baƙi sai wanda aka zaɓa ake karramawa hakan ba daidai bane ba, dukiyar da ake taƙama da ita lokaci ɗaya Allah na iya durƙusar da ita ba fata nake maka ba, amma dan Allah kayi haƙuri idan maganganuna sun ɓata maka rai"
Daddy bai ko yi motsi ba, balle ya tanka maganganun da tayi masa. Yayi shiru yana sauraren yadda take wasa da gemunsa, tana masa magana kamar wata babba har bacci ya kwasheta.
Jin alamar tayi bacci ne, ya sanya ya tashi zaune ya zame ta daga jikinsa, ya kwantar da ita, ya ya dafe kansa yayi shiru, yana ta lissafa maganganun Amina.
Ya waiwaya ya kalli yadda take baccinta hankali kwance, ya dafe kansa yana jin yadda yake masa wani irin zafi.
Yayi shiru ya dinga tunanin wasu abubuwa da yakamata ace tun tuni ya farga ya tuna, ba sai yanzu ba.
Wasa wasa bacci ya gagareshi, yayi ta zazzagawa a ɗakin, ƙarshe ya haƙura ya nemi wuri ya kwanta.
Ya kwanta babu daɗewa, Amina ta tashi ta kalli in da yake kwance, ya lumshe idanunsa, tamkar me baccin gaske.
Ta sauka daga kan gado, ta tafi banɗaki, ta yo alwala ta zo ta tayar da salla.
Har ta kammala sallolinta, da tilawar Alqur'ani, yana kallonta, tayi adduointa ta shafa, sannan ta tashi ta koma kan gadon, ta ɗora hannunta a goshinsa ta dinga karanto masa adduoin kwanciya bacci, sai da ta gama sannan ta ja bargo ta rufe shi, ta nemi wuri ta kwanta abinta.
Duk abin da take yi, har ta gama duk idanunsa biyu yana kallonta, yaji ta ƙara kima sosai a idonsa.
"Mummy nifa gaskiya na fara gajiya, haryanzu wai yarinyar nan ba zasu dawo ba, nafi jin daɗin aikinta a kan na wannan sokuwar" Fadila tayi maganar cikin mita.
Mummy ta ce "Wallahi bake kaɗai ba, wannan Hajarar shegen lalacin tsiya, wai ni ba kwana goma aka ce za su yi ba, yau kusan kwanaki ashirin shiru?"
Fadila ta yamutsa fuska ta ce "Ni da tana nan, da ta haɗa mini kayan nan, Abinci babu wani daɗin kirki, gyaran ɗakina idan wannan ce tayi na zo saina ga datti, ga gandar tsiya ni sai da ta tafi ma, sannan na lura ashe kusan duk ita take aikin gidan nan"
"Ni kaina na gaji da wannan abun, dole a rage wani abu a kuɗin aikin babanta, tun da ba tayi aiki ba a wannan kwanakin"
Fadila ta ja ɗan ƙaramin tsaki, dan gaba ɗaya wannan tafiyar ta Amina ba ƙaramin haushi ta bata ba.
Da safe kamar yadda Amina ta saba, ta shirya musu abin karin kumallo, sai da ta kammala ta koma ɗaki, ta tarar Daddy har yayi wanka ya saka kaya.
"Good morning" ta gaishe shi.
Murmushi yayi mata mai kama da na yaƙe ya ce "Morning dear, kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau Alhamdilillah, your breakfast is ready"
Ya jinjina mata kai ya ce "Gani nan zuwa" ta juya ta bar shi a ɗakin ya ƙarasa shiryawa.
Gaba ɗaya cin abincin kawai yake yi, amma kamar akwai wani abu da yake damunsa, gaba ɗaya yau baya walwala balle yayi ta tsokanarta kamar yadda ya saba yi, ya koma mata Alhaji Ahmad ɗin sa sak.
Duk da kwarjinin da ya yi mata, hakan bai hana ta dakewa ba, ta ɗan taɓa hannunsa. Ya ɗago kai ya kalleta.
Ta ɗan marairace ta ce "Daddy, gaba ɗaya ka sauya meke faruwa ne?"
Ya girgiza mata kai alamar bakomai.
"Dan Allah Daddy idan duk a kan maganar jiya ne, kayi haƙuri ba zan sake yi maka ba"
Ya girgiza kai ya ce "No ba a kanta bane"
"Ba a kanta bane amma naga tun da nayi maka maganar mood ɗinka ya canza?"
Ajiye cokalin hannunsa yayi ya tashi, ya ce "Bakomai fa, sai na dawo" bai tsaya jiran abin da zata ce ba, kawai ya tashi fice daga falon.
Shiru tayi tana ta ƙoƙarin tayi tunani a kan, ko tayi wani abu da zai ɓata masa rai, amma ta kasa tuna komai.
Hajiya Zainab ce tare da manyan aminanta a falon da ke sashenta, sun zo domin su yi mata sallama, saboda tafiya da za tayi umara, sai shewa suke sun hirarrakin su.
Hajiya Turai ce ta ce "Ni kuwa Zainab ina wannan 'yar aikin naki me shegiya rawar kan tsiya?"
"Tana Abuja, sun je competition na makarantar da take zuwa"
Waro ido Hajiya Salma tayi ta ce "Ban gane ba wace makarantar ce haka?"
"Makaranta da take zuwa mana, ai tana mana aiki ne babansu Khalil yana biya mata kuɗin makaranta"
Turai ta ce "Amma wannan cimpetiton ɗin ba na makarantun kuɗi ne kawai ba"
"Eh private ce makarantar da take yi"
Turai ta ce "A gaishe ki Zainab lalai kin yi lausi, ni mai zai sa ma na bari a kawo mini 'yar aiki da ta je makaranta, balle ta zauna mini a gida ana biya mata makarantar kuɗi, kin san 'yan ƙauyen nan idan suka kile basu iya iskanci ba"
"Ke ni rabu da ni, ni wannan yar baya gabana, a shekarar nan zata koma ƙauyensu, da zarar ta gama WAec ni yanzu makomar yarana ce ta dameni. Ni yanzu babban fatana shi ne muje mu dawo daga tafiyar nan, a fara maganar Auren Khalil, Hajiya Salma ki yiwa Baban Bashir magana ma, idan Bashir ɗin ya dawo kan mu dawo daga umara shikenan, sa haɗu su gana, idan ma bai dawo ba, babu komai ya nemawa Bashir ɗin Auren Fadila zan ba shi, bani da case da ita"
Hajiya Salma ta ce "Ahh wannan ai babban albishir ne, aikuwa zan gayawa baban nasa, ni ina ga wataƙila ma ba sai ya zo ba, ayi abin da za ayi a tura masa matarsa kawai"
Hajiya Zainab ta ce "A'a, ai idan an yi auren bar mini ita zai a Nigeria sai ta kammala Makarantar ta tukuna, zan aurar da ita yanzu ne, dan kar azo a samu wata matsala, ta yi mini irin ta Khalil"
Turai ta ce "Gaskiya ne, wanan ma dubara ce, Allah ya haɗa kansu baki ɗaya mu sha biki, bikin 'ya'yan gata"
Hajiya Zainab tayi wata dariya ta ce "Bari kawai, ai za aga biki ba muna biki ba, za a warwasa" suka cigaba da dariya suna hira.
Bayan dawowar Daddy ma bata sauya zani ba, still baya wata walwala, duk yanayinsa babu daɗi, ko hirar ma da yake yiwa Amina bai saurareta ba. Aikuwa ta saka shi a gaba tana masa kuka.
A ɗan rikice ya ce "Meenali, menene?"
"To ba kaine ba, ni ban san me nayi maka ba, ka ƙi kulani, nace kayi haƙuri amma duk ka ƙi saurarata ni ya zan yi?"
"Haba Meenal, ba haka bane ba, ai baki mini laifin komai ba, tsakanina da ke sai san barka, wani abu ne yake ɗan damuna kawai, amma ki kwantar da hankalinki"
"Ni hankalina ba zai kwanta ba, idan ina ganinka a haka"
Ya sa hannu yana share mata hawayen fuskarta ya ce "Ki daina kukan nan bana so, a cikin satin nan su Fadila za suyi tafiyar nan, da zarar sun tafi muma zamu koma, ko dan saboda Jamb ɗinki"
Cikin murna ta ce "Da gaske? Kai amma naji daɗi sosai, Allah ya kaimu, ina son naje na ga Baba dama, amma idan mun koma zaka bani wayata?"
Ya jinjin mata kai ya ce "Eh, zan baki abarki"
"Godiya nake yallaɓai, dan Allah kome yake damunka ka barwa Allah, ka daina damuwa kaji?"
"Na ji Meenalina, na dai na in sha Allah"
Amina ta yi murmushi ta ce "Yauwa ko kaifa, idan kana cikin fara'a na fi jin daɗi"
Shima murmushin yayi mata, yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗauko ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa yayi sallama.
Amsa masa tayi sanan ta ɗora da cewa "Baban Khalil, zaka samu damar dawowa kuwa muyi sallama?"
Ya kalli Amina da ke kwance a jikinsa, sannan ya ce "Ba zan samu zuwa ba gaskiya, ayyuka sun yi mini yawa sosai"
Hajiya Zainab ta ce "To shikenan, wai ni kayi waya da makarantarsu yarinyar nan kuwa, an ce kwanaki goma amma haryanzu shiru, ni gashi zan yi tafiya, bana son in tafi in bar wannan mara kan gadon a gidana ita kaɗai"
Ya shafi gashin Amina da hannunsa ɗaya ya ce "Mun yi waya da malaman makarantar ta su, sun ce a satin nan zasu dawo, wasu dalilai ne ya sanya basu dawo da wuri ba"
"To amma gaskiya zaka rage kuɗi a cikin kuɗin aikin babanta, wannan watan kenan ma babu uban aiki tayi, gaba ɗaya gidan nan ya ƙi fasali saboda bata nan. Zan bar sallahun ayyukana a wurin waccan Hajarar idan ta dawo ta sanar mata".
Daddy ya ce "Shikenan"
Ta ce "Yauwa, kuma ni gaskiyar magana, kuɗin makarantar da kake biya mata ya fi ƙarfin aikin da take yi a cikin gidan nan, dan haka ka sauya mata wata makarantar mai arha, ga ta gwamnati nan, ka biya mata abin daya samu sauran a dinga bata abinta a hannunta, idan tayi cikaken aiki ta samu kuɗinta, idan ba tayi ba kuma ta karɓi na iya kuɗinta, dan wannan makarantar ba ta dace da irinta ba, idan kuma wannan makarantar take so ubanta ya biya mata"
Amina ta kalleshi ido cikin ido, tana jin zafin maganganun da Hajiya Zainab ke yi, idanuwanta suka ciko da hawaye.
Girgiza mata kai ya shiga yi, ya ƙara rungumeta a jikinsa, yana shafa bayanta da sigar rarrashi.
Ya ce "Shikenan za a duba, idan na dawo gida, kuma kuka dawo sai muyi magana".
"Yauwa, saura kuma abu ɗaya, magana mai daɗi"
"Ok ina jinki"
"Fadila ta samu miji fa"
Daddy ya ce "A ina?"
"Ɗan gidan Hajiya Salma Bashir, shi ne yake sonta, idan Allah ya kaimu muka dawo, da maganar aurenta da na Khalil duk za a haɗa"
"Ma sha Allah, Allah Ya sanya albarka, zan yi bincike a kan lamarin"
"Wane irin bincike kuma, Bashir ɗin ai ɗan Hajiya Salma ne, ba shi da wata matsala, mahaifinsa zai zo da kansa kuyi magana"
"Shikenan, yadda kike so haka za ayi ranki ya daɗe"
"Hmm, na so in ganka muyi sallama, anyway stay safe, sai anjima"
Ya ce "Ok Allah ya bamu alkhairi"
Yana ajiye wayar Amina ta saki kukan da ya maƙale mata, ta tashi daga jikinsa.
"Am sorry dan Allah Amina ki rage yawan kukan nan, ke ba kya tsoron kanki ma ya dinga ciwo"
A hasale ta ce "To yayi ciwon mana, ina ruwanka ne? Kana jin ai abin da matarka ke cewa, ka mayar da ni makarantar gwamnati, tun da ina 'yar talaka babu ni babu jin daɗi sai wahala, ga kwantai aiki kuma ta bar mini in koma in yi mata. Duk bautar da mahaifina yayi a gidanka tsawon shekaru ba shi da kima a idon matar nan"
Gaba ɗaya Daddy ya rasa abin da yake masa daɗi.
"Meenal, yanzu kinga na cireki daga makarantar? Ko kuwa kinga na majar da ke makatantar gwamnatin?"
"Amma ai a gabana ka amsa mata, kuma ita a gurinka ai bata laifi, komai ta ce tana so sai ka yi mata, shikenan a gidanka da wurin iyalanka talaka ba shi da amfani sai na ya yi muku bauta? Gaskiya na gaji" ta fashe da kuka tana sheshsheƙa.
Ya lura da ta ƙulu sosai da sosai, dan haka ya miƙe tsaye ya ɗauketa, ya ɗorata a kan kujera 3seater, ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, yana matsawa a hankali.
"Meenal, kin san ba zan taɓa yin abin da zan cutar da ke ba, so kike na biye mata asirnmu ya tonu ne? Ta tayar mini da hankali ta tayar miki da naki?"
"Ni ina ruwana idan asirin ya tonu, iykaci na san ƙauyenmu zan koma, laifin da bai kai wannan ba ta mini gori ta ce zan koma ƙauyenmu ina ga wannan?"
Ya haɗe rai ya ce "Ya haka ne? Ina rarrashinki kina sake botsarewa, Zainab fa matata ce, kuma uwar 'ya'yana so kike na dinga ɓata mata rai saboda ke, meyasa ba zaki bari mubi komai a sannu ba?"
"Eh ko ba matarka ba, ita matarka ce mana, ni kuma karuwarka ko, mara daraja da 'yanci, na gode ba laifin kowa bane laifina ne da na biye maka"
Daddy ya dafe Kai ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa zaki canza mini fassara ne?"
Tayi masa shiru ta cigaba da kuka, kamar ance mata Inno ta mutu.
Takaici ne ya ishe shi, ya tashi ya bar mata wurin gaba ɗaya.
A daren ranar kwana suka yi, babu wanda ya tanka wani, bai ma shiga ɗakin ba, sai da ya tabattar da tayi bacci, sannan ya shiga ya kwanta.
Da safe kuwa har ya fita ba ta tashi ba, balle tayi masa abin breakfast, dan haushinsa take ji, sai da rana ne kan ya dawo ta yi masa girki.
Kwanaki uku babu wanda ya nemi ɗan uwansa, duk da kowannensu abin yana damunsa, amma Daddy yan ganin shi ta yiwa laifi yakamata ta bashi haƙuri, ita ma kuma tana ganin shi ne yayi mata laifi da yake biyewa matarsa da ke neman taci zarafinta.
Da daddare ya sameta a ɗaki, har ta kwanta, sai da ya hau gadon sannan ya ce mata "Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da yamma, zaki koma Kano, jirgin ƙarfe biyar"
Zumbur ta tashi zaune tana faɗin "Alhamdilillah" ta sauka daga kan gadon da sauri, ta kunna fitilar ɗakin, ta sauke sabuwar Akwatin da ya sai mata, wadda ta fi ta ta, ta da girma. Ta buɗe wardrobe ta shiga haɗa kayanta.
Ta shiga toilet ta kwaso underwars ɗin ta, ta zo duk ta haɗa komai a daren, yana kallonta bai ce mata komai ba, tayi ta gama sannan ta kashe fitilar ta dawo ta kwanta. Girgiza kai kawai ya yi, bece komai ba.
Washegari kamar tayi janyo la'asar, dan tun azahar ta kammala shirinta, ta fito da Akwatin falo, ta zauna tana kallon agogo tana jiran la'asar tayi.
Daddy kuwa kallonta kawai yake, yana sake jinjina tsagwaron ƙuruciya irin na Meenalinsa.
Bayan sallar la'asar, direba ya kira Daddy a waya ya ce ya shirya zai kai Amina airport.
Daddy ya yi masa umarni da ya zo ya ɗauki Akwatin Amina ya kai mota.
Amina kuwa ji take kamar ta taka rawa.
Daddy ya kalleta ya ce "Shikenan hankalinki zai kwanta ko?"
Ta ce "Eh"
"Shikenan yayi kyau, Allah ya tsare ki gayar da mutan gidan"
"Yauwa za suji" tayi gaba cikin sauri ta shige motar, dan kar ma ya ce a fasa tafiyar.
Yana nan tsaye har motar ta tashi, suka bar gidan. Daddy ya ɗan lumshe idanunsa ya ce "I will miss you dear, ina fatan kema kiyi kewata Meenalina"
Amina jin ta take tamkar ta shekara bata garin Kano, abin mamaki da ta sauka, already Zakiru na filin jirgin yana jiranta.
Suka gaisa da Zakiru, suna tafe yana tsokanarta ya ce "Amina kinga yadda ki kayi ƙiba kuwa, me suke bakuna can Abujan kika zama haka ne?"
Murmushi kawai tayi ta ce "Shinkafa mana"
"Eh ba shakka kam, shinkafa da kayan daɗi dai, ke baki ga yadda ki ka ƙara ƙiba ba masha Allah, kin ƙada haske sosai"
Ita dai ba tace masa komai ba, sai murmushi amma ita kanta ta san tayi ƙiba sosai daga tafiyarsu zuwa yanzu.
Kasancewar Baba ma ya san yau zata dawo kamar yadda Daddy ya gaya masa, ya sanya ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana dakon ganin tilon 'yar ta sa, kamar yayi tsuntsuwa ya je ya taho da ita.
Yana jin horn ɗin mota, ya tashi da sauri, ya leƙa ta