Showing 282001 words to 285000 words out of 296192 words

Chapter 95 - GABA DA GABANTA

ta gaisheta cikin girmamawa, ta amsa mata ba yabo ba fallasa, ta nufi Fridge.
Hamdala ta yi da taga manyan mangwaro a ciki, ta zauna ta dinga sha kamar mayuwanciya, sannan ta baro Kitchen ɗin.

Sashinta ta koma, ta sake tattaro abin za take buƙata na kayan ta, ta haɗe wuri guda ta kai su falo ta ajiye.
Sannan ta koma wurin Mummy, ɗan kaɗan ta ci Abincin, Fadila na son yin hira da Mummy, amma Mummy ban da zancen kashe mata aure da zubar da ciki babu abin da take yi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Wani hali Yazid zai shiga idan aka kashe auren nan, aka kuma zubar masa da ciki, za a sake jefa shi cikin damuwa.

Fadila ta ce "Mummy, mijina maraya ne rayuwarsa akwai abin ban tausayi....

Kan ta ƙarasa Hajiya Zainab ta ce "Eh, kema na ki uban na ƙoƙarin mayar da ke marainiya ba, kuma mara amfani da ba ta san ciwon kanta ba, ni gani nake ke murna ma kike yi da auren da aka yi miki ko?" Fadila ta yi shiru ta sunkuyar da kai.

Biyar da rabi, sai ga Daddy a sashin Mummy, yana kiran Fadila, Fadila ta amsa ya ce "Maza ta so muje na mayar da ke"

Miƙewa Hajiya Zainab tayi ta ce "Babu wannan maganar, ai kuma ta zo kenan, ba ka isa ba fa"

Daddy ya kalleta ya ce 'Haka muka yi da ke?"

"Da ka tashi aurar da ita, ni wace yarjejeniyar muka yi? Babu in da zata, ta zo kenan ba zan yadda ka sake rabani da ita ba, ban san in da zaka kai ta ba"

Daddy ya ce "Babu in zan kai ta sai ɗakin mijinta, kuma da gani kema kin san ba a wahala take ba, dan haka kar mu zo muna jayayya da ke, har ta kaimu ga ɓacin rai".

Cikin rashin girmamwa ta ce "Ta daɗe ba ta kaimu ga ɓacin ran ba, wallahi babu in da zata je".

Daddy ya kalli Fadila ya ce "Ke kin san yadda muka yi, dan haka ta so mu tafi"

Aikuwa Fadila ta miƙe, ta yafa mayafin jallabiyarta ta nufi in da Daddy yake, dan yanzu haka tana son sanin halin da Yazid yake ciki.

Cikin mamaki ta ce "Fadila, au watsa mini ƙasa zaki yi a ido? Kin zaɓi ki koma cikin tsiya da wahalar da ya zaɓa miki?"

Fadila ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy, amma na riga na yiwa Daddy alƙawarin ba zan yi gardama ba, ina son gobe ma ya sake bani dama na zo na ganku, bana son irin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ku, kuma in da nice ki kwantar da hankalinki, mijina talaka ne amma yana kula dani, babu abin da zai sameni akasin alkhairi, adduraki nake buƙata a duk in da nake Mummy, kiyi haƙuri ki Kwantar da hankalinki"

Daddy ya ce "Alhamdilillah, 'yar ta ki ma har ta fiki tunani da hankali, wuce muje kar muyi yamma".
Fadila ta yi gaba tana goge hawaye, tana yi tana waiwayen Mummy, yayin da Mummy ta yi turus tana bin Fadila da kallo, Fadila ta ɗau sauran kayanta da ta tattara tai waje.

Abin ba ƙaramin ɗaure wa Mummy kai ya yi ba, anya ba asiri ya yi wa Fadila ba? Gaba ɗaya kamar an canza mata Fadilan baki ɗaya.

Babban abin da ya ƙular da Fadila bai wuce yadda yanzu ma tare da Amina za aje mayar da ita ba, ko meye dalilin hakan oho.
Ta buɗe mota ta shiga tana kuka, Daddy ya ƙaraso ya buɗe motar shi ma ya shiga, shi kansa Fadila ta bashi makaki ba kaɗan ba.

Sannu a hankali ya fara jan motar, Fadila sai waiwaya wa take ko Mummy za ta fito, sai ta ji duk babu daɗi na watsa wa Mummy ƙasa a ido da tayi.

Daddy ya numfasa ya ce "Fadila"
"Na'am ta amsa idonta fal hawaye".

"Kiyi haƙuri, mahaifiyarki za ta sakko ita ma, kamar yadda na fuskanci sauyi a tare da halayenki, ita ma ki dinga yi mata addu'a, daga cikin dalilan da ya sanya na aurar da ke ga mutum mai ilimin addini shi ne fatan samun sauya halayen da kika ta so a kai. Alhamdilillah an samu sauyi, kuma kin yi dauriya da biyayya ƙara haƙuri Allah ya yi miki albarka.
Fadila babu lallai ki samu mijin da zai so ki ya tattalaki kamar yadda mijinki yake miki, na ce a sama masa aiki ya ke ta bani haƙuri a kan kar in damu yana kula da ke. Har CID ne da ni a nan unguwar ta ku da suke kula da motsinku, kuma yaba da jajircewar mijinki bashi da shi amma yana ƙoƙari.
Idan kika yadda mahaifiyarki ta kashe miki aure, na farko dai ba zata iya samo miki miji mai nagartar naki ba, dan kuɗi ba sune kwanciyar hankali ba.
Sannan hakkinsa sai ya kamaku, ga kuma rabo ana sa ran samu a tsakaninku, dan haka ki ƙara haƙuri kin ji autana"

Cikin kuka ta ce "To Daddy"

Amina ta yi shiru, amma duk jikinta yayi sanyi Fadila ta bata tausayi sosai da sosai, ba kowane ɗa ne zai iya jure irin wannan punishment ɗin ba.

Shi kansa Daddyn dauriya kawai yake yi, ya ce "Ai dai kina son sa ko? Zid ake ce masa ko menene?" Yayi Maganar cikin sigar wasa.
Murmushi ta yi duk da hawayen da ke fuskarta.

Ya ce "Ai yana gabana lokacin da ake yi masa kashedin idan wurin budurwa ya je za a gane. Dan Allah Fadila kar ki yi kishi irin na mahaifiyarki, kishi halak ne amma kiyi mai tsafta, mu maza sai haƙuri zaki tara da yawa da ƙyar ki samu wanda baya son samun ƙari, komai kyautatawa da halaccin matarsa, sai dai masu hankalin cikinmu ko mata nawa zasu aura, ba sa manta halarcin matar fari, kuma ba sa wulaƙanta ta, sai dai ya danganta da halin matar. Nan gaba ko Allah ya hore masa ya ce zai ƙara aure, kalleshi kawai kiyi kamar baki damu ba, wannan abu ya fi komai ɓata mana rai, gashi nan ina ta baki satar amsa, kuma banda tarkacen ƙawaye mu mun fi so muga a kodayaushe mune abu na farko a gareku, ku fifita mu fiye da kowa, ku bamu muhimmanci kar ku saka wani abu a gabanmu sai a zauna lafiya, banda kishi na rashin ji Fadila"

Fadila ta ce "Ai ni ya ce ba zai yi mini kishiya ba"

Murmushi Daddy ya yi ya ce "Eh lallai soyayya ta yi daɗi, to Allah ya sa".

Duk da duhun magariba ya rufa, dan sai da suka tsaya Daddy yayi salla, sannan suka ƙarasa unguwar su Yazid, a titi Fadila ta sauke glass tana faɗin "Daddy gashi can" ta ƙarasa maganar tana ɗagawa Yazid hannu.

Slow Daddy ya yi da motar ya tsaya, Yazid ya ta so da sauri, hannunsa riƙe da leda, a kan dakalin wani masallaci yana ta rarraba ido a titi.

Cikin fara'a ya ƙaraso, ya risuna yana gaida Daddy.

Daddy ya ce "Afuwan, na ɗauke maka mata wuni guda ko? Tuba nake" Yazid ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.

Fadila ta buɗe motar zata sauka, Daddy ya ce "To Hajiya, ai kya bari na ƙarasa da ku ko?" Sai kuma kunya ta kamata.

Daddy ya ce Yazid ya shiga ya ƙarasa da su gidan, aikuwa ya shiga, nan suka gaisa da Amina ma.

Fadila ta yi ƙasa da murya tana taɓa ledar hannunsa ta ce "Me ka sayo mana?"

"Kununki ne da nake sayo miki da kuma kifi"

A hankali take faɗin zan ci daɗi.

Sai kuma ta matsa jikinsa take raɗa masa "Kayi missing ɗi na ko?" Yazid ya yi murmushi ya girgiza mata kai.

"To me ka zauna yi a titi kana jira?"

A hankali ya ce "hutawa kawai nake yi"

Hannu ta kai ta matse masa hanci a hankali ta ce "Ba wani nan" Daddy yana kallonsu ta mudubi, kawai ya ɗan yi murmushi, kamar ba yanzu ta gama koke-koke a mota ba.

Har ƙofar gidansu Yazid suka isa, Amina ta jinjina wa Fadila haƙurin da ta yi na zama a gidan nan, saboda yadda take ji da kanta a baya.

Yazid ya ce "Amma dai Daddy ai zaku shigo ko?"

Daddy ya kalli Amina ya ce "Mu shiga?"

Amina ta ce 'Ai ko ba zaka shiga ba, ni zan shiga na yi salla".

Yazid ya ƙarasa yana buɗe gidan, Daddy ya buɗe boot ɗin mota, ya kalli Fadila ya ce "Zo ki taya antynki ɗaukar kayan nan"

Ba ƙaramin ƙulewa Fadila ta yi ba, amma ba yadda ta iya, ta zo ta taya Amina ɗaukar fulasan abinci.
Ganin bayan motar ta yi shaƙe da kayan Abinci ɗanye, Daddy ya yiwa Yazid alama da ya zo.
Yazid ya ƙaraso yana risunawa, Daddy ya ce "Yazid ka samo yara su shigar muku da kayan nan, sai a biya su".

Yazid ya ɗan yi turus yana kallon kayan, Daddy  ya ce "ya na ga kayi shiru?"

Yazid cikin sanyin jiki ya ce "Daddy muna da abinci, ina ƙoƙarin ajiyewa idan mun shiga ma zaka ganix

Daddy ya dafa kafaɗar Yazid ya ce "Yazid ba gazawarka na gani ba, kawai na baku ne dan na tallafa maka".

Yazid ya ce "Daddy kar zuciyata ta mutu ne"

Daddy ya yi murmushi ya ce "Ai kai jarumi ne, kuma na yaba da ƙoƙarinka kar ka damu" Ba dan Yazid ya so ba, haka ya yarda ya karɓi kayan nan aka shiga da su cikin gidan.

Amina ta yi alwala, Fadila ba tare da ta kulata ba ta bata darduma domin ta yi salla.
Sai dai Fadila sai kallon cikin Amina take yi, ya yi girma sosai kamar ta kusa haihuwa, da ƙyar take sallar ma.

Daddy har cikin gidan ya shiga, shi kansa Daddy ya ga gidan yayi ƙanƙanta, amma farincikin da ke kan fuskar Fadila ya tabbatar masa da tana cikin farinciki.

Daddy ya shiga falon ya zauna, aka yi sa'a aka kawo wuta.

Yazid ya ce yana zuwa, ya fita Fadila suka yi ta hira da Daddy. Ba a jima ba sai ga Yazid ya dawo hannunsa da leda ya sayo manyan lemuka, ya shiga Kitchen ya haɗo kwanukan Abinci, da flask na girkin da yayi da rana ya zo ya jera.

Daddy ya ce "Ohh, Yazid sannu da aiki, ke Madam meye aikin ki ne na ga shi yake yin komai".

Fadila ta ce "Daddy bani da lafiya fa"

Daddy kawai ya girgiza kai, shinkafa da miya ga kayan ganye da kifi, Yazid ya ajiye musu.

Amina ta sake ta ci Abincin, dan ba ta iya cin Abincin da ta girka.

Har ku san tara na dare, Daddy ya ce Yakamata su je su gaisa da Hajiya.

Amina ta ce "Yakamata a ɗebarwa Hajiyan Abincin nan a kai mata ita ma".

Daddy ya ce "Haka ne, Fadila ɗauko kwano ki zuba mata".

Sai a yanzu Fadila ta san meye a cikin fulasan, wainar masa cikin fulas, ga uwar miya mai rai da lafiya ta sha nama, gefe kuma ga fulas ɗin dubulan.
Fadila ta ɗaga kai ta kalli Amina, a rant ta ce "Wai ita a dole ga me kirki, to in dai ni ce kin yi a banza"

Hajiya kuwa ta yi murnar ganin Alhaji Ahmad, suma ta karrama su, sai wajen goma na dare su Daddy suka tafi.



Mummy kuwa ta sha mamakin abin da Fadila ta yi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi sai dai ta fara tunanin ko Asiri aka yi mata idan ba haka ba yadda za ayi Fadila ta yi haka.

Hajiya Turai ta kira a waya, gaba ɗaya jikin Mummy a sanyaye yake.

Hajiya Turai ta ɗaga wayar tare da yin sallama.

Mummy ta amsa jiki a sanyaye.

Hajiya Turai ta ce "Yaya, ya dawo miki da ita ɗin ne?"

Mummy ta ce "Hajiya Turai, akwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin, Turai ya dawo mini da Fadila da ciki, kuma ta zaɓi babanta a kaina, dan ta zaɓi komawa in da ya aurar da ita, duk da ƙoƙarin da nayi a kan na riƙeta kar ta koma amma yarinyar nan ta watsa mini ƙasa a ido, kuma wallahi da alama wani talakan ya aura mata".

Turai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, wallahi Zainab wannan yarinyar da mijinki ya aura ita ta rusa miki gida"

"Turai ni yanzu ba ta wannan nake yi ba, ta yadda 'ya ta zata dawo gareni nake, idan Fadila ta haife cikin nan shikenan"

Turai ta ce "Yanzu kin gano in da take ne? Kuma waye mijin?"

"Wallahi ban sani ba, tun da ta zo fa bacci take yi, ni gaba ɗaya kamar an canza mini Yarinyar nan, ban gane kanta ba kamar ba Fadila ba, shikenan ba Khalil ba Fadila?" Tayi maganar cikin ƙunci da ɓacin rai.

"Kiyi haƙuri, yanzu dai ki fara mayar da kai mu gano a in da take, amma tukuna ma ko sunan unguwar da take baki sani ba, ko lambar wayarta".

Cikin karaya Mummy ta ce "Na gaya miki kamar wadda ake hurawa wuta, ko hirar kirki ba muyi da ita ba, gaba ɗaya ma ƙin sakin jiki tayi da ni"

Hajiya Turai ta ce "Ke bana raba ɗaya biyu, an asirce miki 'ya wannan maganar ba ta waya bace ba, bari sai mun zauna tukuna".

Ta ce "Shikenan sai anjima".





Fadila kuwa Yazid ya dinga yi mata mita, yana mata faɗa, ganin ta zage tana rawar jiki tana cin abin da Amina ta dafo ta kawo mata, amma sai wulaƙanci take yi mata, yayi ta mata nasiha da nuna mata abin da take yi ba daidai bane ba.
Bayan ya sakko daga fushin wucin gadin da yayi da ita ne, yake tambayarta ya gidan ya kuma Mummy.

Shareshi ta yi bata kula shi ba, Ya ce "Magana fa nake miki".

"Ina ruwanka da ni, ba faɗa ka ke yi mini ba"

"Na yi miki faɗan, ke gaskiya ce ba kya so ko?"

Tayi shiru tana cuna baki, Nasiha Yazid ya shiga yi mata, a kan abubuwan da take yiwa Amina.



Khalil kuwa hankalinsa a kwance yake, ya samu nutsuwa sosai da sosai, ya samawa Hafsa makaranta, yake ta ƙoƙarin biya mata kuɗin makaranta a Kaduna, duk sati biyu take zuwa Abuja in da yake ta yi weekends, ga ɗawainiyar ciki, amma kasancewar ta saka kanta ya sanya ba ta jin wahalar hakan.
Su kan zo Kano idan aka yi hutu, sai dai bai fiye kaita gidan Mummy ba, sai dai shi ya je shi kaɗai.

Daddy ya gaya wa Khalil batun auren da ya yiwa Fadila, Khalil ya tausayawa Mummy, dan abin da take gudu ne duk ya baibaiyeta.
Daddy ya ce masa kan su bar Kano, ya je gidan Fadila su gaisa.

Yazid ya ji daɗin zuwan su Khalil, kamar ɗan uwansa ne ya zo, sai murna yake yi.
Zama da Yazid da yawan nasiharsa a greta ya sanya ta sakarwa Hafsa fuska, har suka ɗan taɓa hira, Fadila har da tambayar me za ta dafa musu?

Khalil ya ce "Allahu Akbar, Daddy ya iya punishment, su Fadila an nutsu"

Hararar Khalil tayi ta ce "Ka ga ka kiyayeni, na gaya maka".

Hafsa ta ce "Ba sai kin dafa mana komai ba, kar mu saki wahala".

Yazid ya ce "Ba wata wahala, ai baƙinmu ne ku"

Fadila ta ce "Ina da komai na Abinci, ku faɗi abin da kuke so".

Hafsa ta ce "Duk abin da kika dafa zamu ci"

Fadila ta ce "To shikenan" ta tashi ta fita tsakar gida aikin girki, Hafsa ta biyota tana tayata.

Ranar wuni suka yi tare, Fadila ta ji daɗin zuwansu, dan rabonta da Khalil har ta manta.

Duk da Hafsa miskila ce, amma ta ji daɗin sakin fuskar da Fadila ta yi mata, dan tsakar gida suka dawo tare suka ci Abinci, suka bar su Yazid a ɗaki.

"Fadila mijinki yana da kirki, Allah ya sanya yayi miki halacci kamar yadda kika yi haƙurin zama dashi gashi da karamci"

Fadila ta ce "Ai a raina bana tunanin zai mini wani abu makamancin butulci, ya daɗe yana sona fa, Ashe Allah ya ƙaddara sai ya aureni" Fadila ta yi ta bata labarin abubuwan da suka dinga faruwa a makaranta tsakaninta da Yazid.

Hafsa ma sai ta fara bata labarin yadda suka haɗu da Khalil, har kamata da 'yan sanda suka yi ya karɓota, a haka har labari ya gangaro har wani daga cikin halin da suka shiga na matsin rayuwa.

Zuru Fadila ta yi da ido, tana jin Hafsa, da irin ƙalubalen rayuwar da ta fuskanta ita ma bayan rashin mahaifinta.

Wata irin kunya da nadamar abin da suka dinga aikatawa ita da mahaifiyar ta ne ya kamata, gaskiya sun yi kuskure sosai da sosai, wasu mutanen na fama da rayuwa da tsananin buƙata, amma ba su taimake su ba, sai ma sake jefa su cikin wata damuwar ta hanyar muzgunawa.


A zahiri Fadila ta wayance, tana ɗan rarrashin Hafsa.
Gaba ɗaya tausayin Hafsa ya kamata, tare da dana sanin abubuwan da suka aikata a baya.

Bayan la'asar suka shirya zasu tafi, idon Fadila ya cika da hawaye, Khalil ya ce "Ke kuma menene?" Ta girgiza masa kai alamar bakomai hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka fara zubo mata.

Jan hannunta yayi zuwa soro, ya kalleta ya ce "Fadila menene? Auren ne ba kya so ko?"

Ta ce "A'a Yaya Khalil, ina son aurena, kuma ina son mijina, yana kula da ni fiye da tunaninka, kawai dai ina missing ɗinku ne, kuma wallahi nadama nake yi Yaya Khalil abubuwan da muka yi a baya, yanzu matarka take bani labarin rayuwarta, idan ka ji labarin Yazid ma abin tausayi, gashi dukkanin su babu wanda ban taɓa cizgunawa ba, dan Allah Yaya Khalil ka ɗan nema mana yafiyarta dan Allah"

Khalil ya rungumeta a jikinsa yana share mata hawaye ya ce "Hafsa ba ta da matsala, kar ki damu kin ji".

"Wallahi na yi nadama sosai da sosai, sannan dan Allah Khalil ka ɗan taushi Mummy ta yi haƙuri, ta fara iƙrarin zata kashe mini aure ranar da muka je, dan Allah Yaya Khalil ka ɗan tayani tausarta, bana son watsa mata ƙasa a ido, amma wallahi ina son aurena da mijina, Yazid tun muna makaranta yake sona, dan Allah ka bata haƙuri, wallahi ina sonta sosai ita ma, amma dan Allah ta barni na zauna da mijina ni duk talaucinsa ina son sa"

Murmushi Khalil ya yi, ya goge mata hawaye ya ce "Shikenan, kar ki damu komai zai wuce in Allah ya yarda"

"To yaushe zaku dawo?"

Khalil ya ce "Sai dai kuma ku zo mana kan mu koma"

"To shikenan, zan tambayi Zid zamu zo in sha Allah, amma kar ka gaya wa Mummy in da nake, idan ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login