Showing 225001 words to 228000 words out of 296192 words

Chapter 76 - GABA DA GABANTA

yake yi, ya zamana ko Abincin kirki ba ta iya ci, sai dai ta ɓuya tayi kuka.

Hankali kwance Amina take shirin auren Khalil, dan mussaman ta buga nata invitation ɗin. Tana yada habaici a falo, tana faɗin "Abu namu na yaran talakawa sai in da ƙarfinmu ya ƙare, dole muyi shiri tunda mun samu duniya abinka da ba a saba ba"

Duk wata barazana da tashin hankali da Hajiya Zainab take yi a gidan nan, ba wanda yake saurarta, ga su Turai sun kai ta wurin malamai daban daban amma abu ya gagara yiwuwa, daga Auren Khalil har batun Amina babu wanda tayi galaba a kai.

'yan uwan Daddy kuwa ranar da za a kai lefe, har da wasu daga 'yan uwan Amina suka zo suka cika gidan, sai guɗa suke da sanya albarka suna yiwa Khalil fatan alkhairi.
Har maƙwabta suka dinga shigowa suna ganin kayan kan a tafi kaiwa, wanda da waya basu damar shiga gidan ma, balle a gayyacesu wani sha'ani, wannan karon kuwa duk tsukin babu wanda Amina bata aikawa da katin gayyata ba.

Ƙarfe huɗu na yamma, aka kai kayan lefen nan na Hafsa, ita ma maƙotansu da wanda ba a rasa ba, sune suka haɗu suka kai lefen.
Khalil ya sai kaji da kuɗin da zasu bayar na tukuici ya bawa Hafsa, dan su fita kunya.

Aikuwa surutu ya karaɗe unguwar su Hafsa, wai lefenta har da gwal, mai awara tayi goshi zata auri mai kuɗi.

Khalil yayi ƙoƙari, duk da gidansa bai kammala ba, Daddy ya ce zai bawa Khalil gida ya zauna a Kano, kan ya kammala gininsa, amma sai dai shi Khalil ɗin ya sai musu furnitures ya saka, idan ya kammala gidansa na can Abuja, zai sai wa Hafsa kayan ɗakinta, idan ya so duk lokacin da suka zo Kano, sai su dinga sauka a can.
Abdul ya taimakawa Khalil sosai, dan gidan da Daddy ya basu ba laifi mai kyau ne sosai da sosai.
Khalil ya sai komai, da aka zuba a gidan, duk da Khalil ba da kuɗin Daddy ya dogara ba, yana da abin yi, kuma Daddy da 'yan uwa da abokai, sun taimaka masa amma yaji jiki, dan biki ya ɗauko gagarumi wanda ba harkar ƙari a cikinta.

Ya zama very busy shi da Abdul, kusan kodayaushe suna tsakanin Kano da Abuja saboda shirin biki.

Har gida Yusra ta zo ta samu Fadila tana yi mata mita "Yanzu ke Fadila shirin bikin Yaya Khalil ɗin, amma ki kasa gaya mini, ko mu shirya wani abu, sai a bakin Yaya Abdul naji"

Fadila ta yamutsa fuska ta ce "Ke, ni rabani da wannan sabgar bikin, ba ita ce a gabana ba"

"Ban gane ba, ba zamu yi ko wani anko ni da ke ba, mu gayyaci mutane ba?"

"Girl, Mummy fa ba son auren nan take yi ba, bana tunanin ma zamuje"

Cikin mamaki Yusra ta ce "Ban gane ba zaku je ba, bikin Khalil ɗin, ɗan uwanki tilo a duniya kice ba zaki ba, to saboda me? Wai ma meyasa Mummy bata son auren nan ne?"

"Yusra, yarinyar fa awara take sayarwa a titi, Mummy akwai wadda ta zaɓa masa amma ya zage wurin Daddy suka haɗa kai da munafukar Yarinyar can zai auri wannan"

Yusra ta ce "Haba Fadila, wannan ra'ayin Mummy ne fa, ke meye naki a ciki, ko Mummy bata so amma ace ran aurensa babu ke babu Mummy a wurin bikin tsakani da Allah haka ya dace? Gaskiya ba zai yiwu ba, zan bugo mana kati mu raba, aure ko na dole ne ai abin farinciki ne"

"Yusra, ina cikin damuwa ba zan iya zuwa wurin nan ba, ni komai ya daina yi mini daɗi"

"Subhanallah, meyafaru kuma?"

"Yusra an kawo kuɗin aurena, Daddy ya saka watanni uku kacal, kuma bana son wanda za a aura mini, zaɓin Mummy ne ba nawa ba, bana son nima na watsa mata ƙasa a ido, kamar yadda Daddy da Khalil suka yi, amma wallahi bana son sa zuciyata kamar zata fashe, ina ga bayan bikin nan wai zai zo Nigeria mu gaisa, wallahi bana son shi" Fadila tayi maganar tana hawaye.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, kai wannan al'amri da ban mamaki, ki kwantar da hankalinki Fadila, sai kiga albarkacin biyayyar da zakiyi mata kiga kin dace da auren"

"Yusra in auri wanda bana so? Taya ya zaman auren zai mini daɗi, bayan babu ɗingon son wanda zan aura ɗin a zuciyata, ina ta dannewa in yiwa Mummy biyayya, ko dan tayi farinciki, amma kamar zan cuci kaina wallahi bana son sa"

Rungume Fadila Yusra tayi tana rarrashinta ta ce "Haka ne, jigon kowane Aure soyayya ce, idan babu ita aure baya armashi, amma mu cigaba da Addu'a mu jira hukuncin Allah, amma gaskiya batun kice wai ba zaki wurin bikin Yaya Khalil ba, bai taso ba, ita kan ta Mummy bai kamata tayi haka ba, ɗanta ne fa na fari"

"To ni me zance, gaba ɗaya kaina ya kulla matsalolin gidan nan sun yi yawa, duk a dalilin waccan azzalumar Yarinyar".

Yusra ta ce "A'a kar ki ce haka, komai kika ga ya faru, tsari ne da iko na ubangiji babu wanda ya isa ya yiwa wani bawa abu, face abin da Allah ya ƙaddara masa"
Ta dinga rarrashin Fadilan, har ta samu nasarar ɗaukarta suka ɗan fita, dan Fadilan ta ɗan saki ranta.

Da aka tashi kai katin biki Dutse, Amina har dangin Hajiya Zainab da ta watsar, ta aika aka kai musu cewar suna gayyatar su bikin ɗa.

Ganin rawar kan da Amina ke tayi a kan bikin ne ya sanya Hajiya Salma ta ce wa Hajiya Zainab "Zainab, kinga idan kika ƙi zuwa bikin nan, za ayi abin kunya, ace ke uwar ɗan nan baki je ba, zamu ji kunya, dan tsaf za a zageki ace kishi ne, dan haka gara kiyi haƙuri ki lallaɓa kije, ki gayyaci manyan mata koba komai a ganki a wurin"

Hajiya Zainab ta ce "Ni ba auren nan ne ya dameni ba, ni burina in ga asiran da nayi, sun yi tasiri sun yi aiki, amma shiru har yanzu ba wani labari"

Hajiya Salma ta ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu cigaba da yi ba fasawa za mu yi ba ai, yanzu dai kawai ki fara shiri wallahi, kin san mijinki babban mutum ne kuma kin san za a haska bikin nan sosai, ace ba a ganki ba abin da mamaki za a bi diddigin jin abin da ya faru".
Haka tayi ta lallaɓa Hajiya Zainab, a kan zuwa wurin bikin Khalil.

Hafsa jinta take kamar ba ita ba, wai ita ce zata yi aure, zata auri Khalil mutumin da take matuƙar so a rayuwarta.

Yusra ta ja Fadila suka sayo kayan fitar biki, ta kai musu wurin tela, aka yi musu ɗinki, da sauran shirye-shirye.
Ɓangaren Amina ma, kaya masu tsadar gaske Daddy ya sai mata na fitar biki.

Shi kansa Daddy yana ta gayyatar Manyan mutane, ga sanarwa da ake tayi a gidajen watsa labarai.



Khalil ya je kaiwa Hafsa kuɗin lalle da kitso, tayi sharr tayi kyau sai sheƙi take yi.
Khalil yayi murmushi ya ce "Amarya ba kya laifi, inyee baki yaƙi rufuwa zata auri ɗan beautiful inyeee"

Kunya Khalil ya bata, amma ta ce "Kai ne bakinka yaƙi rufuwa, zaka auri 'yar beauty"

Ya ce 'Haka ne kam, zan auri 'yar beautyna, ubangiji Allah ya sanya mana albarka a aurenmu My wife"

Ta amsa da Amin cikin jin kunya.

Sun yi hira sosai sun daɗe tare, sannan ya bata kuɗin yayi mata sallama, sannan ya tafi gida.

A ka fara hidmar bikin Khalil, amma duk batun wani abu na ci da sha a wurin biki, Amina Daddy ya bawa ragamar, ita kuma ta haɗa kai da Ammi, dan danƙa amanar samar da Abinda za a ci a wurin taron bikin.

Aka fara hada-hadar bikin Khalil, gida ya cika da jama'a, Amina sai shiga take tana fita, wurin samarwa duk wanda ya zo abinci da wurin kwana.

Gida ya kaure da hayaniya, sai hada hada ake.

Tubarkallah, Hafsa ta sha kyau ranar da aka fara bikin nan, kowace rana akwai shigar da take yi, Ranar dinner ne Hajiya Zainab ta ƙuduri aniyar zata je ita da ƙawayenta, ko dan ta ci mutuncin amarya a wurin.

Amina tana can wurin kwalliya, ita da Azima, wurin Dinner tuni ya cika da jama'a. Amarya da Ango na kan high table, Amarya ta sha kyau daga ita har angon, sai dai wasu daga cikin mutanen haryanzu basu iso ba.

Ana tsaka da gudanar da taro Sai ga Hajiya Zainab da jama'arta, Khalil bai taɓa tsammanin Mummy zata zo ba, duk da gabansa ya faɗi da aka ce ga babar ango nan, amma yaji daɗin zuwan Mummy wurin.

Hajiya Turai ce taje ta karɓe mic daga hannun Mc, ta ce ita zata yi Mc.
Ta dinga zubawa Hajiya Zainab kirari, Hajiya Zainab tana hura hanci.

"To Alhamdilillah, Allah ya kawo mu biki na ɗan gata, ɗan masu da shi, duk da dai kyan ƙwarya ta bi ƙwarya, amma an samu wata ƙwaryar da tayi gangancin bin akushi, to muna son wannan ƙwaryar ta san da cewa ajalinta ya zo, domin ruwa ba sa'an kwando bane, lokacin fashewarta yayi"

Ɗan jimmm Hafsa tayi, tana juya maganar Hajiya Turai.

"Jama'a a tafawa angon nan namu dan Allah, kai da ganin angon nan kaga ɗan gata, zaren ba kalar yadin bane, sai dai abu ne na ɗan yau idan Allah haɗa ba yadda ka iya, amma ramin kura ai sai 'ya'yanta. Allah ya kaimu wata uku i yanzu mu dawo bikin ango da galleliyar amarya 'yar dangi"

Ran Khalil ba ƙaramin ɓaci yayi ba, Hafsa kuwa tuni jikinta yayi sanyi, idonta ya fara cika da hawaye.

Hajiya Turai ta cigaba da cewa "Uwar ango na buƙatar ganin ɗanta a tsakiyar fili, zata yi masa liƙi dj a bamu sauti mai daɗi.

Duk da ran Khalil babu daɗi, amma ya miƙe tsaye, ya riƙo hannun Hafsa, jiki a sanyaye ta miƙe.
Amma Hajiya Turai ta ce "A'a ango kawai muke buƙata ban da ke"

Mc ya ce "Haba Hajiya, ai bikin na ango da amarya ne, ba ango kawai ba".

Khalil bai saurari kowa ba, ya janyo hannun Hafsa zuwa ƙasan stage.

A hankali ya yiwa Hafsa raɗa "Dan Allah kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki kar kiyi kuka please"
Jinkina masa kai tayi, tana sake jan mayafinta na net, tana rufe fuskarta.

Hajiya Zainab ta ƙaraso tsakiyar filin, Hajiya Turai tana ta sake wasa Hajiya Zainab.
Liƙi take yiwa Khalil, yana murmushi,  sai dai suna haɗa ido da Hafsa, ta yiwa Hafsan wani irin mugun kallo, sai da Hafsan ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Hafsa ta ɗarare jikinta, saboda yadda ƙarara suke nuna mata wariya a gaban mutane. Mai hoto yazo zai ɗauki hotuna, Khalil ya matsa jikin Hafsa, amma Hajiya Salma ta janye Hafsa ta ce "Ke matsa, shi da uwarsa za a musu hoto"
Kasancewar Umman Hafsa na wurin, ita ma tuni nata jikin yayi sanyi, ganin cin mutuncin da ake yiwa Hafsa a gaban mutane.
Tashi tayi ita ma taje wurin, ta tsaya ta gefen Hafsa tana yi mata nasiha a kunnenta.
Mai hoto ya ce "Hajiya Yayar amarya ce ke? Naga kuna kama"

Umma ta ce "A'a 'ya ta ce"

Ya ce "Ya aka yi bamu san kin zo ba, ku haɗu da babar ango ayi muku hoto".

Hajiya Salma ta ce "Mun maka kama da wanda zasu jera da matalauta ayi hoto?"

Khalil ji yayi kamar ya tsaga ƙasa ya shige, kunyar Mama da Hafsa suka kama shi, ya rasa in da zai saka ransa.

Tuni mutane suka fara ƙananan maganganu, wasu suna Allah ya ƙara, kwaɗayi ya kai Hafsa in da za a wulaƙanta ta.
Kusan a tare Amina ta iso wurin, ita da wasu daga cikin familyn Daddy da suka je wurin kwalliya.

Anty Fiddausi aka fara labartawa rashin mutunci Hajiya Zainab da ƙwayenta ke ta yiwa amarya, alhalin ita uwarta tana wurin tana gani.

Ran Anty Fiddausi ya ɓaci matuƙa, ita da ƙannen Daddy da aka gaya musu zancen tare.

Anty Fiddausi ta ce "Dole mu nunawa matar nan iyakarta a wurin nan"

Ta kira Amina a waya ta ce "Ɗan jira kar ki shigo tukuna, zan saka a sanar da shigowar ki, ina fatan akwai isassun kuɗi a jakarki"

Amina ta ce "Eh, amma Anty lafiya kuwa?"

"Matar mijinki ce da ƙwayenta ke ta yiwa amarya da danginta wulaƙanci, zata ga tsiya ina zuwa"

Anty Fiddausi ta je ta samu Dj, ta ce masa "Kai, ka karɓi mic ka sanar da zuwan Amrayar Alhaji Ahmad Musa Dutse wurin nan, sunanta Hajiya Amina Hassan, ka wasa mini ita, ka koɗata a matsayin 'yar gaban goshin Alhaji Ahmad, kuma uwa a wurin ango, ka san dai irin yadda kuke yi idan kuna son ku samu kuɗi, idan har kayi hakan, zaka samu kuɗi"

Aikuwa jiki na tsuma, yaje ya karɓo mic a wurin Hajiya Turai, ya koma kan stage.
Ya dinga wasa Amina, ya dinga koɗata a matsayin amarya 'yar gaban goshi, shalele ta gaban motar Alhaji Ahmad Dutse, amarya ba ta laifi ko ta kashe ɗan masu gida, amarya a gidan Engineer kuma uwa a wurin amarya da ango baki ɗaya, ina amfani da wannan dama wurin gabatar muku da Hajiya Amina Hassan, duk mai sonki shi Engeener yake so, mai so ya samu a wurin Engineer yayi tsani da Hajiya Amina. Baya ganin kowa idan ba ke ba, duk sauran mata bururruka yake ganinsu ke kaɗai ce macen da yake gani, ba wata mata a gidansa in bake ba, idan ma akwai to Yasin buranya yake ganinta".

Wata uwar ashar Hajiya Turai ta lailayo, yayin da wurin biki aka ɗau shewa, Amina kuwa shigowa tayi cikin ƙasaita, tayi kyau matuƙa ga ƙiba da tayi, hakan ya sanya kayan suka karɓe ta sosai da sosai.
Ta shigo tare da jama'arta, duk da kasancewar Amina yarinya ce, amma manyan mata ne suka shigo tare da ita, abinka da mutum mai fara'a da kuma ungo ya sanya take da mutane sosai da sosai.
Amina na ƙarasawa in da suke, ta rungume Hafsa tana faɗin "Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, ya baku zaman lafiya, ina miki murna 'yar uwata" ta sake rungume Hafsa.
Ta buɗe bakin jaka, ta fara liƙa wa Khalil kuɗi shi da Amarya Hafsa.

Jama'ar Amina ma da dangin Alhaji Ahmad, suka dinga yi musu liƙi.
Aikuwa Dj ya kuma ware maƙogwaro yana wasa Hajiya Amina.

"Godiya nake Hajiya Amina da jama'arta, ba Allah ya ƙara danƙon soyayya, duk mai ƙoƙarin kawo tangarɗa tsakaninku Allah ya mayar da shi takalmin sanyawar ki, ki taka shi yadda kike so.

Turai ta miƙe ta daki tebur ta ce "Dole mu san abin yi, sai mun watsa taron nan"


(KAI MASIFAR HAJIYA ZAINAB NA BANI TSORO 🙄)

AYSHERCOOL
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, KU TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA DOMIN SAYA 08081012143
70

Hajiya Turai ce ta fara zage zage, Anty Fiddausi tayi hanzari ta fita waje, bodyguards ɗin da ke waje suke tsaron wurin, taje ta sanar da su su zo su fitar musu da Hajiya Turai da Hajiya Zainab.
Aikuwa ƙartin nan suka zo suka tasa su a gaba suka yi waje da su, Mummy ta bisu tana bala'i ta ce "Akan me za a korar mata mutaneta".
Su Khalil kuwa suna can basu san me ake yi ba, ana can an hargitse da hayaniya da liƙi da raye-raye babu wanda ya san abin da ke faruwa.
Hajiya Zainab bin su tayi ta bar wurin, suka bar wurin bikin baki ɗaya suna masifa.

Hajiya Zainab suna tafe sai basu haƙuri a hanya, suka rakata har gida, sannan suka tafi.
Gidan babu Mutane sai ɗaiɗaiku, Hajiya Zainab ta nufi sashin Amina, tana zuwa kuwa ta tarar da Daddy yana nan.
Babu tsammanni ya ga Hajiya Zainab a kansa, yanayin yadda take huci ne, ya sanya ya gane tashin hankali ne ha kawota ba abin arziƙi ba.

"Kai ka saka matarka ta ci mini mutunci a wurin bikin ɗana?"
Daddy ya kalleta ya ce "Ban gane ba, ni na je wurin ne balle na san me aka yi?"

"Ai dole ka faɗi haka mana, taje ta haɗa kai da 'yan uwanka sun ci mini mutunci ni da mutane na, a gaban mutane, wallahi ka tsawatarwa danginka da matarka su fita daga sabgata, aka dinga ci mini mutunci har da kirana buranya a bikin ɗana amma aka kori jama'a ta, wace irin rayuwa ce haka?"

Daddy ya ce "Shikenan na ji, zan yi musu magana Allah ya baki haƙuri, hakan bai isheta ba, sai da ta yi ta gama sannan ta fice, ya girgiza kai kawai yana mata fatan shiriya.

Yusra da Fadila basu je wurin ba, sai bayan da Mummy ta bar wurin da jama'arta, dan haka basu san meyafaru ba. Sai bayan sha ɗaya sannan aka watse daga wurin.

Abdul ne ya ɗauki Khalil da Hafsa a motarsa, zasu kai Hafsa gida.

Suna tafe a hanya, Khalil ya lura da jikin Hafsa a sanyaye yake, tayi shiru tana kallon gefe guda.
A hankali Khalil ya ce "Hafsat" ta ɗago ta kalleshi.

"Ya aka yi ne?" Kasa magana tayi, sai girgiza masa kai kawai da tayi.
Jiki a sanyaye ya ce "Hafsa, na san abin da ya faru a wurin biki ne bai miki daɗi ba, amma dan Allah ina roƙonki kiyi haƙuri, komai zai wuce" still ba tace masa komai ba, jin tayi shiru ne ya sanya ya haskata da fitila, yaga tana share hawaye.

Take jikinsa ya sake yin sanyi, ya kai hannu yana share mata, duk ta ɓata kwalliyar.

"Dan Allah, ba dan ni ba kar ki saka abin nan a ranki, zai wuce in sha Allah"

Cikin kuka ta ce "Dama haryanzu Mummy bata sona amma ka ɓoye mini?"

"Hafsa meye amfanin na gaya mikin ne? Kuma ba yadda kike tunani ba dan Allah kiyi haƙuri, na sani babu daɗi amma kiyi haƙuri"

Mamaki take, ce mata yake zai wuce kamar bai ga yadda aka ci mata mutunci a gaban mutane ba.

Ƙoƙarin cigaba da share mata hawayen yake yi, amma ta janye jikinta, ta koma gefe ta mayar da hankalinta kan titi.

A haka suka ƙarasa gidansu, ta buɗe motar ta fice ta shiga cikin gida.

Khalil yayi ajiyar zuciya ya ce "Kai Allah ka kawo mini ɗauki"

Abdul ya ce "Kayi haƙuri Khalil, komai zai wuce a cigaba da Addu'a, Allah zai kawo mafita"

"Abdul dole yarinyar nan ta ji babu daɗi, dan Allah kalli cin mutuncin da ƙawayen Mummy suke yi mata a gaban mahaifiyarta, yadda ka san na zabgawa Turan nan mari"

"Easy man, kayi haƙuri, ai ga matar Daddy nan tayi maka kara"

Khalil ya ce "Ai ni Yarinyar nan tayi mini komai, ba ƙaramin mutuncinta nake

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login