Showing 33001 words to 36000 words out of 296192 words

Chapter 12 - GABA DA GABANTA

nan kamar wani maye, duk in da yarinyar nan take yana nan, tai ta sawa ana dizga shi, ni gani nake kamar sonta yake yi".

Captain ya ce "Wallahi ƙila ƙarya take masa, ka san yarinyar 'yar wulaƙanci ce, ta gama raina shi, ni dama ƙanwata yake so, matar da ta auri wannan ta huta, mutum sai haƙuri kamar me".

"Aikuwa in dai wannan shegiyar ce ba zata taɓa son sa ba, idan ta auri irinsa cutarsa zata yi, wai ita 'yar mai kuɗi wata banza da ita".

Captain ya yi dariya Ya ce "Kai dai kawai ba kwa shiri ne".

Tun yana iya ƙunshe tarin da yake, har ya kasa ya miƙe da sauri, saboda ya ɗau excuse ya hanzarta barin ajin, amma kan ya kai ga haka, ya silale ya faɗi a wurin.
Nan 'yan ajin suka waiwaya dan ganin meke faruwa, sai dai Yazeed ko motsi ba ya yi, lecturer ya sa a ɗauke shi a fita da shi, ya samu wadattaciyar iska, dan da alama He is asmatic.
Ita kuwa Fadila ko waiwayawa ba ta yi ba, balle ta san waye ya faɗin.

Mintuna sha biyar, malamin ya ƙarƙare lectures ɗinsa, Fadila ta zari jakarta ta yi waje, dan gidansu Yusra zata je, saboda yau Yusra ba zata shiga school ba.
Har ta gota in da ta ga 'yan ajinsu suka yi cincirindo, kawai sai ta ji tana son sanin waye ya samu asmatic attack ɗin.
Ta koma da baya ta leƙa Yazeed ta gani a kwance, babu alamar yana numfashi, idanunsa a rufe!


AYI TA HAƘURI DA NI RASHIN POSTING A KAN LOKACI, KU SANYA NI A ADDUOINKU, ALLAH YA BANI INGANTACCIYAR LAFIYA.

TO GET THE LATEST UPDATE OF THE BOOK, FOLLOW ME ON WATPAD
AYSHERCOOL7724
AREWABOOKS
AYSHERCOOL7724
08081012143GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P10

Zaro idanu Fadila ta yi, ganin Yazeed tamkar ya mutu, a mimmiƙe a wurin, jikinta ne ya yi wani irin sanyi, ta tuna yadda ta ji muryarsa yana roƙonta, ta bashi wurin zamanta saboda ba ya son zafi.
Cikin rawar baki Fadila ta ce "Class rep ba za a kai shi Clinic a duba shi ba?".

"Eh, A motar Hamisu muke so a kai shi, kuma motar tayi faci, sun je a gyara a zo tafi da shi".

Cikin rawar murya ta ce "Kaga ku ɗauko shi da sauri, muje a kai shi a tawa motar". Babu wanda ya taɓa zaton Fadila zata iya abin Arziƙi haka, ganin yadda ta uzzurawa Rayuwar Yazeed.
Cikin hanzari ta yi gaba, ta je ta buɗe motar, aka ɗauko Yazeed aka sa shi a motar Fadila, amma ta haɗe rai ta ce Mutum biyu ne kawai za su shiga, dan ba zata kwashi ƙartin banza a motar ta ba su hautsina mata ciki da warin hammata ba. Aikuwa Fadila ta sha zagi a wurin samarin ajin nan, ba ta bi ta kan su ba, ta take motar da ƙarfi ta bula musu ƙura, ta bar harabar wurin da gudun tsiya.

Suna tafe lokaci lokaci, numfashin Yazeed yana dawowa, sai dai baya wuce ƙirjinsa, ga wani irin sound da fitar numfasin nasa ke fitarwa kamar numfashin zai rabu da gangar jikinsa.

Gaba ɗaya hankalin Fadila a tashe yake, tana ji a ranta idan Yazeed ya rasa ransa, to tana da kamasho a cikin faruwar hakan.

"Fadila ya naga kin fita daga cikin School, ba Clinic ɗin School za a kai shi ba?" Cewar Captain da ke rungume da kan Yazeed.

"Gara a kai shi wani Asibitin, i don't want too much wahala, akwai asibitin da muke da retainership file, a nan muke ganin likita, bari muje can kawai".

Shi Captain ma abin na Fadila mamaki yake bashi, ganin yadda duk ta ruɗe.

Suna zuwa aka karɓi Yazeed, cikin kulawa aka shiga da shi Emergency room, Nurse ta kawo family file ɗin su Fadila.

Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Fadila wannan kuma a ina kika samo shi?".

"Doctor he is my class mate, ya samu asmatic attack ne, shine nace mu kawo shi nan".

Doctor Aliyu ya gyara zaman glashinsa ya ce "Dama can yana da Asma ne?".

Fadila ta ce "I don't know fa, i have no idea kawai a duba shi ni dai kar ya mutu, amma ga abokansa nan a tambaye su".

Captain ya ce "Ni dai ban sani ba, kin san ba shiga mutane yake ba, balle ayi hira ya faɗi yana da wani ciwo, ko kai Aminu ka taɓa jin ya faɗa?" Ya yi maganar yana kallon wanda suka kawo Yazeed tare.
Aminu ya ce "kai baka sani ba balle ni, ni da banda gaisawa babu abin da yake haɗamu".

Doctor Aliyu ya ce "Baku taɓa ganin yana shan wani magani ba?".

Captain ya ce "Doctor, bawan Allah nan fa ba magana yake ba, ba ya kula kowa ba ya son hayaniya, kaga ƙawarsa nan Fadila ita yake kulawa ita kuma ba ta saurararsa, wataƙila da tana saurararsa, da ita ya gaya mata".

Fadila ta haɗe rai ta harari Captain ta ce "Zan maka rashin mutunci ka kuma haɗani da shi, a ina na zama ƙawarsa? Yanzun ma akwai dalilin da ya sa na tsaya a kan a kawo shi Asibiti".

Doctor Aliyu yayi murmushi tare da girgiza kai, kasancewar sa family doctor ɗin su, kuma nan Asibitin suke zuwa idan ba su da lafiya ya sanya ya san Fadila da halayenta. Gaba ya yi suka bishi a baya.

Suna shiga Emergency, suka tarar da Yazeed kwance an sa masa Nebulizer, yana mimmiƙe a kan gado. Gaban Fadila ya kuma faɗuwa ganin halin da Yazeed ke ciki, ta tuna yadda ta baɗe shi da ƙura da hayaƙin mota, wataƙila ma hakan ne ya sa ciwon ya tashi.

Doctor Aliyu ya cewa Aminu, ya zo ya taya shi a caje Yazeed, ko akwai magani a jikinsa, dan galibi masu irin wannan matsalar suna yawo da magani a jikinsu.
Suka caje jikin Yazeed, jotter shi ce kawai a jikinsa da biro, sai carbi da Naira hamsin, suka ajiye a drower kusa da shi.
Doctor Aliyu ya ce "Na so inga irin maganin da yake sha, amma bakomai bari mu gani zuwa anjima ko zai farfaɗo, na rubuta allurai a yi masa".

Fadila ta ce "Amma Aliyu, kana ganin zai warke gani nake kamar mutuwa zai yi fa" tayi maganar ƙwalla na ciko idanunta.

Aliyu ya ce "Ikon Allah, dama akwai abin da zai raunata miki zuciya haka Madam? Zai warke insha Allah, your besty will recover insha Allah, amma ki dinga kula da shi sosai, kin san ciwon nasu baya son wannan weather, banda yawo ba mask, ko zuwa wurin hayaƙi ko ƙura".
"Dan Allah ka daina haɗani da shi, wai wani besty"
Yayi murmushi ya ce "To na daina"

Aminu ya yi musu sallama ya tafi gida, Captain ma yace zai je school ya dawo, suka bar Yazeed da Fadila kawai a Asibitin.
Fadila sai kaiwa take tana komowa a reception ta kasa zama wuri ɗaya, tana yi tana leƙawa ɗakin da Yazeed yake, kasa jurewa ta yi, ta shiga ɗakin da Ya ke kwance. Ta taka a hankali, ta ƙarasa gaban gadon da yake kwance, ta kalli abubuwan da aka ciro a aljihunsa, ta ɗauki jottersa da carbinsa ta saka a jakarta, saboda kar idan ya tashi, zasu tafi a manta da su.
Gani ta yi yana motsawa a hankali, ta ƙura masa idanu, tubarkallah idan ta ce Yazeed yana da muni tayi ƙarya. Gani ta yi yana rirriƙe katifar gadon da yake, yana ɗaga ƙirjinsa sama, sai kuma ya saki katifar, yana miƙe mata hannu, amma idanunsa a rufe.
Ƙara matsawa ta yi jikin gadon, tana masa sannu, sai dai bai san me take yi ba, hasali ma bai san meye yake yi ba.
Sai miƙa hannu yake yana riƙo duk abinda ya ji a kusa da shi, cikin sa'a ya riƙo hannun Fadila, hannunsa kamar ba na namiji ba, saboda taushi, sai ta zama kamar wata sokuwa ta rasa abin yi, a hankali yake murza yatsunta, yana jujjuya kansa, hawaye na zuba a gefen idanunsa, ga wani irin gumi da yake tsatstsafowa a goshinsa.
Fadila zama ta yi tamkar wata gunki, wani irin abu ne ya fara kai kawo a jikinta, tun daga kanta zuwa ƙafafuwanta, wani baƙon yanahu ya ziyarce ta, tsigar jikinta na tashi, wani irin yanayi na ratsata, saboda a rayuwarta idan ba Khalil ko Daddy ba, babu wani namiji da taɓa samun wannan kusancin da shi haka, har hannunta a cikin nasa, sai doctor Aliyu, idan ba ta da lafiya zai mata allura ko sa ruwa, shi ma faɗa suke yi da shi, ta ce "Ba zai taɓa ta ba".

Ƙoƙarin zame hannunta take daga na Yazeed, cikin jin zafin ciwo ya matse mata yatsu da ƙarfi, wanda har sai da ƙasusuwan yatsunta suka yi ƙara.
"Washhh Allah, kai dalla ka sakar mini hannuna sai ka karya ni tukuna?" Ta faɗa a shagwaɓe.
Ƙoƙarin miƙewa zaune Yazeed ya fara yi, ya kai hannu zai cire abin Nebulizer, ta riƙe hannunsa ta ce "Ka bari magani fa aka samaka" ta faɗa raunane.
Bai saurareta ba ya cigaba da ƙoƙarin cirewa, da sauri ta fita ta kirawo doctor Aliyu, har Yazeed ya cire Nebulizer ya kifa ya kusa faɗowa daga kan gadon.
Da hanzari Aliyu, ya gyara masa kwanciyar ya mayar masa da Nebulizer, ya je ya ɗauko wata allura ya yiwa Yazeed. A hankali bacci ya kwashe shi.

Aliyu ya ce "Gaskiya ciwon nan nasa ya zama chronic, ki kirawo masa wani daga gidansu mana, a san halin da yake ciki".

"Ni ina na san wani nasa, ɗan ajinmu ne fa kawai".

"I see, amma kin damu da shi da yawa".

"Ni ban damu da shi ba, kawai dai na san koma menene ya sameshi nice sila, idan ya mutu zan iya cewa ina da hannu a ciki shiyasa na damu".

"Shikenan, ki zauna tare da shi, duk abin da kika gani ki mini magana".

Fadila ta ce "to"

Ta koma ta samu kujera, ta zauna a kusa da gadon nasa, ta ɗauko wayarta ta hau chatting da Yusra, a nan take bawa Yusra haƙuri, saboda rashin zuwanta gidansu, kuma ta bata labarin abin da ya faru.





Amina na ɗakinta, sun kammala aiki tayi wanka, ta shirya tana ƙara gyara nata ɗakin, Hajara ta yi sallama. Amina ta amsa tare da kallon Hajara.
"Ki je in ji Khalil".
Amina ta ce "Waye kuma Khalil?".
"Wanda zai kai ki makaranta"

Ta buɗe baki ta ce "Haba da gaske?".

Hajara ta ce "Zan miki ƙarya ne?"

Kan Hajara ta gama rufe baki, Amina ta yi waje, ta nufi falo. Ta tarar da Khalil ya kammala breakfast, Hajiya Zainab na zaune a kusa da shi tana masa hira.

Amina ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa ta ce "Gani".

Bai kalleta ba ya ce "In the next 30minutes, ki shirya zamu je a kai ki makaranta"
Washe haƙora Amina ta yi cikin murna ta ce "Tom, Na gode Allah ya saka da alkhairi, ai ni na shirya ma, bari in je in jiraka".
Hajiya Zainab ta kalli Khalil ta ce "Ban gane ba, kai ne zaka kaita makaranta?, ka bari babanta ya dawo ya kai ta mana".
Khalil ya ce "No, kin san bakomai zai iya yi mata ba, Daddy ne ya bada umarnin hakan".
Tsaki ta yi ta ce "Ni bana son irin haka, a ɗorawa mutum wahalar da ba ta sa ba, ba damar ka janyo mutum ɗaya, sun dinga ɗora maka ɗawainiya da wahalarsu kenan".
Amina da ba ta kai ga barin falon ba, tana jin hajiya Zainab, amma tayi shiru ta wuce ɗakinta, ba tare da ta yi magana ba.

Tana zuwa ɗaki, ta canza hijjabi, ta ɗauko littafi ɗaya a litattafanta da ta taho da su daga ƙauye, da bironta ta samo leda ta zuba su a ciki, ta ɗaure murmushin kan fuskarta ya kasa gushewa.

Hajara sai kallon Amina ta ke "Amina sai kace wadda aka yiwa bushara da zuwa makka, wannan fara'a haka".

Murmushi Amina ta yi ta ce "ni dai na tafi, sai na dawo" tayi waje a guje cike da farinciki. Wuri ta samu a nan harabar gidan ta zauna, tana jiran Khalil, ba ta wani daɗe ba saiga shi ya fito da waya a kunnensa yana waya, bai kula Amina ba ya nufi hanyar gate zai fita, ba ta da zaɓi illa ta tashi ta bi bayansa.

Abdul ne zaune a cikin motarsa, ya ƙurawa gate ɗin ido. Khalil ya ƙarasa ya buɗe gaban motar, ya shiga.
Amina kuwa tsaye ta yi, tana zazzare ido, Abdul ya miƙa hannu, ya buɗe mata motar, ta shiga ta zauna sannan ta risunar da kanta ta ce wa Abdul "Ina kwana?".
"Lafiya ƙalau, ya kike ya gida?".
"Ina lafiya ƙalau Alhamdilillah".
"To Masha Allah, sannunki" ya mayar da dubansa kan Khalil da ke danna wayarsa ya ce "Malam ba gaisuwa ne?"
Hararsa Khalil ya yi ya ce "Dan Allah ja mu tafi, anƙi a gaishe kan".

Abdul ya ce "Haka ka iya, sarkin faɗa" A hankali Abdul ya ja motar suka fara tafiya, cikin motar ga sanyin AC, ga ƙamshin turaren jikinsu, ga ƙamshin droomer, duk ya cika motar, yanayin ya yiwa Amina daɗi sosai, sai kallon gari take ta jikin baƙin glass ɗin motar.

Gaba ɗaya tsarin zubin ginin makarantar ya sha banban da irin zubin makarantunsu na ƙauye, ginin kawai ba ƙarmin burge Amina ya yi ba.
A wurin parking Abdul ya tsayar da motar, Amina na ƙoƙarin buɗe motar, Abdul ya ce "Ki zauna muje mu fito tukuna, ni ya sunanki ne ma?".

"Amina Hassan"

Ya ce "Masha Allah, nice name, ki zauna muje mu dawo".

Amina ta amsa da to. Abdul da Khalil, suka nufi dogon ginin da ke cikin harabar makarantar.

Tana nan zaune a mota, kusan mintuna sha biyar, sai ga Abdul ya dawo, ya buɗe wa Amina motar ya ce "Bismillah zo muje" Amina ta fito daga motar, cike da farinciki tana sake ƙarewa makarantar kallo.

Cikin ofishin shugaban makarantar suka shiga, suka tarar da shi a zaune tare da wasu malamai biyu, sai kuma Khalil.
Har ƙasa Amina ta zube tana gaishe su. Director yayi murmushi ya amsa mata, tare da yi mata umarnin ta zauna.
Ta samu wuri ta zauna, tana cigaba da ƙarewa ofishin kallo, a ranta ta ce "Allah sarki principal ɗinmu, insha Allah sai na gina masa Office irin wannan, mai irin wannan kujerun, shima a dinga sa masa turaruka masu ƙamshi".
Muryar director, ta ji yana tambayarta sunanta da harshen turanci, ta ɗago tare da amsa masa, ya tambayeta sunan makarantarsu, ajinta nawa? Shekarunta nawa? Gaba ɗaya cikin harshen turanci, kuma ita ma cikin harshen turanci take mayar masa.
Gaba ɗaya Khalil bai zaci ko Makaranta ta taɓa zuwa ba, dan a haka ya yiwa director bayani.

Nan malaman nan suka fara yiwa Amina interview, sai dai duk ta basu mamaki, saboda kaifin basirarta, gashi duk abin nan cikin harshen turanci suke yi, kuma ko tangarɗa babu a bayanan nata da turanci.

Aka yi mata tambayoyi a fannin lissafi, gaba ɗaya tayi soliving ba tare da amfani da calculator da aka bata ba.
Director ya ce "Kai Khalil kace gifted ku ka kawo mana? Alhamdilillah na yi farinciki sosai da sosai, yanzu zamu bata aji, ƙarfe biyu muke tashi daga makaranta, na ji daɗi sosai na yaba da ƙwazanta, insha Allah zamu yi ƙoƙarin bata ilimi yadda ya dace, yanzu za'a kaita aji insha Allah".

Amina ta ce "Ai bani da litattafai, littafi ɗaya na ɗauko".

Director ya ce "Kar ki damu, duk kayan rubutu mu zamu baki, har da jakar Makaranta ma"

Amina ta sake faɗaɗa fara'arta ta risuna ta ce "Na gode, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata".

Suka amsa da Ameen, babban abin da ya ƙara burge su da Amina, shi ne yadda take da tarbiyya da ladabi sosai.

Suka fito daga Office ɗin tare da director, da su Khalil.

Abdul ya kalli Amina ya ce "Idan an tashi daga Makaranta, kar ki je ko ina, ki tsaya a wurin da muka ajiye mota yanzu, zamu dawo mu ɗauke ki, saboda kinga baki san hanya ba".

"To yaya Na gode, Allah ya biya muku buƙatunku na Alkhairi, ya sa ku gama da duniya lafiya, Allah ya shiga lamarin ku, ya saku farinciki kamar yadda ku ka sani" ta ƙarasa maganar har da hawaye a idonta, dan ba zata iya misalta farincikin da take ciki ba.

Abdul ya yi murmushi ya amsa da "Ameen, ki dage kiyi karatu da kyau Allah ya bada sa'a, ga wannan in an fito break ki sayi wani abun" yayi Maganar yana bata ɗari biyar.

Girgiza masa kai ta yi ta ce "A'a na gode zan iya zama har a tashi ban ci komai ba, a ƙoshe nake" tayi gaba tana ɗaga musu hannu. Wani irin murmushi ne ya suɓucewa Abdul, yarinyar ta burge shi, duk da ɗan karen surutunta, amma acting ɗinta zai tabattar maka da ga gidan tarbiyya take.
Tsakin Khalil ne ya dawo da shi daga tunanin da yake, ya bi bayansa zuwa mota, suna tafe Abdul na yiwa Khalil hirar Amina da yadda ta burge shi. Banza Khalil ya yi masa, dan tun haɗuwar sa farko yarinyar ta yi masa tsiwa yake jin haushinta, ga ta da shegen surutu da iyayi kamar jefaffiya.



An samu numfashin Yazeed ya daidaita, sai bacci da yake yi, saboda allurar da aka yi masa, har azahar Fadila ta je ta yi salla ta dawo bai farka ba, tana nan zaune taga ya fara motsawa a hankali, ta zuba masa dukkanin idanunta, dan babban fatanta dama shi ne taga ya tashi ya warware. Captain ya kira Fadila a waya cewar 'yan ajinsu zasu zo duba Yazeed, amma tace ya ware an sallame shi, saboda bata son ƙananan maganganu.

A hankali ya buɗe idanunsa, yana ƙarewa ɗakin kallo, ya kalli hannunsa dake ɗauke da canular anyi hanging ɗin drip.
A hankali ya juya ɗaya ɓangaren, ya yi tozali da fuskar Fadila, sai da gabansa ya faɗi, ƙoƙari yake ya gane, zahiri ne ko mafarki.
"Sannu" ta furta kamar an mata dole.
Ya jinjina mata kai alamar yauwa.
"Ina ne nan?" Ya yi maganar yana kallonta.
"Da ina ya yi maka kama?"
"Yi haƙuri gani na yi ban san environment ɗin ba, dan Allah zan sha ruwa" ya ƙarasa maganar da sigar magiya, tare da tashi zaune ya jingina.
Kamar ya yi mata dole, ta tashi ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin, ta ɗauko ruwan roba mai sanyi ta miƙa masa. Ruwan sanyi ƙarara dan haka ya karɓa ya ajiye a gefe.
"Ba zaka sha ba ka sa na ɗauko?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Yayi mini sanyi da yawa"
Doctor Aliyu ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Yazeed a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login